YAR MAKIYAYA
CHAPTER 2
Duniya kowa da abunda ya dameshi, na gasgata hakan ganin yadda halayen y’an uwa uku ya sha Banban musamman Ameer wanda kowa ya shaida shi ba k’aramin magulmaci bane.
Domin ganin wasu halayen na wad’annan y’an uwa dole na garzaya na kutsa kai ciki don ganin yadda zasu karb’i bak’on d’an uwansu ( *The crazy Prince*) Suraj. +
**** ****** *****
Da sallama ya shiga falon yana mai cije baki cikin nuna alamar ya takura saboda jin haushin wayar sa dake sake ruri a karo na biyu. Abubakar kad’ai ne ya amsa Sallamar yayinda Saeed da Ameer suka k’ura wa takalman kaf’an shi ido baki sake, ganin yadda suke kallon shi yasa ya dubi k’afafun nashi.
“Is that what I think it is?” Saeed ya tambaya cikin d’aga murya yayinda Ameer ya k’undume dariyar da taso kufce masa yace
“Of course it is a cow’s dung!” Cikin d’aga murya yayi maganar kafin ya fece da dariya.
“Kashin shanu fa! A ina ka samo wannan kai da yau shigowar ka gari am sure ko fita baka yi ba!
Dariya Suraj yayi ya sake duban takalman karo na biyu yace “Oh wannan wai? D’azu na taimaka wa wata shine ban sani ba na taka”.
Duk’a wa yayi ya cire takalman kafin kyafta ido wata mai aiki ta d’ebe su daga wajen for cleaning , sannan ya k’arisa cikin falon ya nemi waje ya zauna suka gama gaisawa da Abubakar Saeed da Ameer kuwa hanci suka toshe tsabar neman magana hakan yasa Suraj ya k’ura musu ido, amma sai ya kai zuciya nesa ya mik’a ma Saeed hannu su gaisa. Kamar wanda aka mintsina Saeed ya mik’e tsaye ya nufi upstairs Ameer kuwa ya tuntsire da dariya ya mik’e tun kafin ma Suraj ya mik’a masa hannu su gaisa.
Haba Bro! Ka gama taimakon wata K’azama har hakan yayi sanadiyyar da ka tako poop sannan zaka mik’a masa hannu ku gaisa? Ko ni nan bazan yarda ba, tukunna ma kasan yadda tun shigowar ka kake k’arin daud’a it will be better in zaka fara freshening up kafin mu gaisa” Ameer yana isowa nan a maganar shi ya kwashi wayoyin sa ya fice yana y’ar fito.
Tuni bugun zuciyar Suraj ya sauya, idanuwan sa suka kad’a ya mik’e da zummar barin wajen zai koma side nasu though bazai ji dad’in zama chan ba saboda Oummin shi bata nan , dama chan ita kad’ai ne abokin shi wanda ke tolerating d’in shi kuma ta d’auke shi a yadda yake without a complain. Ko da yake uwa ce fa.
Har ya fara takawa ya nufi k’ofa Abubakar ya k’ira shi ganin abunda Saeed suka yi bai ji dad’i ba
“Daman ina son fita saboda yau za’a kawo kaya warehouse I will be glad in ka zo Mun fita tare daga nan zan sa wani daga cikin servants ya nuna maka gari am sure you’ll like it”. Murmushi Suraj yayi gami da jinjina kai ya juya ya bar falon har kamar zai yi tuntub’e ,ko mota bai jira ba balle takalman shi da aka tafi cleaning, duk saurin da yake driver yana bin bayan shi da motar duk hadimai se kallon shi suke yadda yake cikin b’acin rai, yawancin hadiman sun fi alak’anta fushin Suraj da su Ameer dan babu wanda bai san halin su ba.
Abubakar yana tsaye daga tall French window dake falon yana kallon yadda fushin Suraj ya bayyana k’arara har ya bar harabar gidan ya nufi nasu side d’in.
Duk gaisuwar da masu aikin gidan ke masa bai ko kula d’aya daga cikin su ba ya nufi k’ofa yayinda cikin zafin nama wani security ya bud’e masa k’ofa nan ma ya shige rai a b’ace kai tsaye Upstairs ya nufa yana cire buttons d’in rigar shi ,falo zuwa falo corridor to corridor har ya isa flat nashi , nan yake zama duk lokacin da yazo Belel. Jefa rigar yayi kan gado ya fad’a bayi. Ya dad’e kafin ya fito inda ya riske akwatin sa ajiye da alama yanzu aka shigo da shi, nan take ya janyo ya d’auki kayan da zai sa sannan ya kimtsa kayan a wardrobe. Farar shirt ya saka k’irar lacoste da bak’in Armani jean ya feshe jikin shi da kala kalan turaruka masu sanyaya zuciya sannan ya saka wani black and white snicker a k’afar sa wanda ya dace da kayan jikin shi. Camerar shi ya d’auka da waya ya fice daga d’akin ya nufi downstairs ,ganin babu kowa wajen yasa ya fice waje , ko da driver ya hango shi sai ya tuk’a motar ya nufi inda yake.
“Take a day off bani key ni kad’ai nake son fita I want to be alone all by myself”.
Driver na jin haka yace “but Young Master yau shekaru biyar fa rabon ka da garin nan da de ka bari na kai ka kaga gari na yau kad’ai”. Suraj bai saurare shi ba ma yayi shigewar sa mota ya ja kai tsaye ya nufi hanyar main gate wanda zata sada shi da cikin garin Belel……
💗💗💗💗💗💗
B’angaren Laila kuwa tashin su daga bakin ruwa gari suka nufa sun dade basu isa ba saboda wasannin da sukayi ta yi har lokaci ya k’ure yamma ta soma yi gari ya yi sanyi. inda ake saye da sayarwa suka nufa, wuri ne mai d’aukar hankali, ga cikowar mutane kowa da abunda ya kawo shi, da gudu suka nufi wajen da ake d’ayar da tsuntsaye iri daban daban a keji sautukan da suke yi gwanin ban sha’awa hakan yasa Laila Lumshe idanuwa, a hankali murmushin sa yake zuwa mata, kyakkyawan fuskar sa ma’abociyar kyau ,ganin bata da niyyar farfad’o wa daga mafarkin da ta shiga yasa Zubaina ta faka mata duka a gadon baya, har saida ta razana hakan yasa suka fara guje guje su buge wancan su hankad’e Wannan cike da nishadi.
Motar sa yayi parking daidai kasuwar garin wanda ya kasance waje ne mai ban sha’awa cike da koren ciyawa kowa ya kafa y’ar rumfar sa yana Sana’a, maza da mata kowa buzy ,camerar shi ya d’auko ya kutsa kai yana ta d’aukar hotuna yana Murmushi ,wasu kyawawan tsuntsaye ya hango a keji ya yi snapping da camera sannan yaci gaba da d’auke d’auke hotuna bai ankara ba yaji an bankad’e shi har saida suka zube a k’asa daga shi har wanda ta buge shin ,gaba d’aya wajen kallo ya koma kansu wasu da suka san shi suna fad’in “Wannan ai Yariman mu ne”……Mun ga how bully Saeed da Ameer are, da kuma yadda suka yi treating Suraj wanda hakan ya fito fili k’arara ya nuna cewa Suraj is not welcomed. Mun kuma ji yadda b’acin rai yasa ya fice daga gida to find peace of mind a karo na biyu ya ci karo da dream gal d’in shi Laila. Amma wannan karon sedai muce kayan marmari ya fad’a madara a”! +
***** ******* *****
Suraj’s POV:
Duk yadda nayi k’ok’arin kare kai na daga fad’uwa k’asa abun yaci tura ,I can’t not because bani da k’arfin yin hakan se dalilin electrifying shock da ya faru tsakanin mu the moment she touched me, a hankali take d’aga kanta daga kifa shi da tayi a kafad’a na hakan yayi sanadiyyar da numfashin ta mai d’umi yake brushing fuska ta, ta dad’e idanuwan ta a cikin nawa which gave me access to those shiny emerald green eyes, which makes her different from other ladies.
Ta yanke min duk tunanin da na shiga ciki lokacin da ta mik’e da kyar tana k’ok’arin daidaita tsayuwar ta.
Wani d’an saurayi da bazai wuce sa’an Suraj ba ya taho sanye da rigar sa y’ar Shara ya mik’a wa Suraj hannun ,kama hannun yayi ya mik’e yana mai godiya amma kafin ya gama kakkab’e jikin sa ya d’ago Laila bata wajen babu inda bai juya ba amma bai ganta ba.
“Laila kenan! Haka take kullum komai a wajenta na nishad’i ne ,sam bata da wata matsala a rayuwa, ai chan kusa da tsaunin chan gidan su yake” D’an saurayin nan ne yake magana yana gyara zaman hular sa hakan yasa Suraj ya tattaro attention ya bashi cike da mamaki yace “Toh wa kuma ya tambaye ka? Ammm… Ina nufin ya akayi kasan abinda nake son tambaya?”
Gyara tsayuwar shi saurayin yayi sannan yace “In har akwai so na gaskiya to fa ka sani sam baya b’uya a fuskar mai shi, yadda ka k’ura mata ido ya yi bayanin komai”
Tab’e baki Suraj yayi yana kallon saurayin na wasu y’an dak’ik’ai har ya fara tsarguwa
“Ya kake kallona haka? Ni d’in fa ba Laila bace”
Suraj ya d’auki camerar shi yana goge wa yace “Toh kai d’in waye”?. Saurayin ya gyara tsayuwa kafin yace “yanzu kayi batu me amfani! Sunana Junaidu kuma manomi ne ni, kai harta kayan marmari na itatuwa ina Norman su in kana so se in kaika ka gani” Murmushi Suraj yayi yace ” Ba yanzu ba Junaid yanzu abunda nake buk’ata kawai shine ka nuna min gari, yau shekaru biyar kenan rabona da Belel komai ya chanja amma kowa ya chanja, I want to see more of it”
Shawo gaban shi Junaid yayi yace “dan Allah komai zaka fad’a ka fad’a amma kayi magana da yaren da zan gane se wani turance ni kake yi”.
Dariya sosai Suraj yayi yayinda yaci gaba da d’aukar photuna yace “Naji yi hak’uri yanzu de muje ka kaini wajen da yafi ko ina kyau da burge wa waje me cike da soyayya ba irin wancan gidan Sarautar ba wanda mutanen cikin sa basu damu da mai k’aunar su ba kad’an daga cikin su ne suka san me soyayya yake nufi ina so ka kaini wajen da zan ji kamar kar in tafi wajen da zan ji tamkar in k’are rayuwa ta a ciki inda zanji kalamai masu kwantar da zuciya”
Duk maganganun da Suraj ke yi Junaid ya saki baki kamar wawa yana kallon sa har ya gama sannan ya matso kusa da Suraj yace “Ah Lallai! Babu makawa kai na daban ne! Nasha jin labarin yadda aka k’awata cikin Masarautar chan da kayan k’awa iri daban daban duk da ban tab’a shigar sa ba, amma yau ga wanda yafi chanchanta ya zauna cikin ta yana gudun ta tabbas kai na daban ne, A matsayin ka na yarima a Belel duk inda ka buk’aci in kai ka ni Junaidu zan kai ka ballantana ma inda na fito kake tambaya, zan kai ka wajen da a nan aka haifi soyayya kuma inda zaka samu soyayyar asali”.
Murmushi Suraj yayi yace “nagode” ya kai hannu zai taya Junaid d’aukar kwandon vegetables da ya siyar Junaid yayi wuf ya rik’e “ina ni ina barin Yariman Belel ya d’auki kwandon kayan mita? Bar hannun da ya saba yayi abunsa” Suraj ya d’ago ya dubeshi na wasu dak’ik’ai sannan yace “miye aibu a ciki dan aboki ya taimaka wa abokin sa? Yau na shigo garin nan ko y’an uwana ma basu karb’e ni ba, Kaine mutum na farko da ka fara sake jiki da ni nayi zaton na samu aboki kuma duk aboki bazai ji kyamar abokin shi ba”. Jin haka yasa Junaid ya mik’a masa kwandon ya d’auki d’aya shima sannan ya shige gaba suka fara tafiya, Junaid na ta surutu.
LAILA:
A karo na biyu naji bak’on yanayin da ban saba ji ba, wannan karon ba dalilin dabbobi muka had’u ba komai da ya faru Zubaina ce sila ,in da ban biyo ta ba,in da ban tsaya kallon tsuntsaye ba,in da bata doke ni ba sam bazan samu wannan damar ba ,numfashin sa ma’abocin k’amshi da kyawawan idanuwan sa masu d’auke da yanayi na soyayya su na fara arba da, da kyar na iya mik’e wa daga jikin sa amma kafin na ankara naji an fisgo ni da gudu, ko ba’a fad’a ba Zubaina ce , Mun dad’e lab’e cikin wata rumfa, naga yadda yake juye juye yana neman gani na ,ko haka ma ya ishe ni don haka na ja hannun Zubaina muka soma nausa wa zuwa gida.
Cike da farin ciki Mara misaltuwa………..Who said friends are hard to find by a person with a pure heart? We’ve got another being admits our characters.( Junaid ) saurayin manomi mai son barkwanci.
******* ******** *******
Saman tsauni ne mai tsayin gaske sai korayen ciyawi lufluf masu kyaun gani, da gudu suka haura Laila na gaba Zubaina tana biye da ita , kutsa kai sukayi cikin fararen tumakin dake kiwo a wajen a take dabbobin suka tarwatse kowa yayi nasa waje yayinda su kuma suka zube a k’asa se haki suke yi suna dariya. Jin takun mutum da sukayi ne yasa duk mik’e
“Baba! ” Cewar Laila d’an dattijon da aka k’ira da Baba ya yi Murmushi, sandar dake hannun sa ya mik’a mata yace “Ki kora dabbobin gida ni zan shiga daji neman sassak’e ” cike da ladabi Laila ta amshi Sandar, yayi ta sa musu Albarka suka wuce gida inda yake chan k’asan tsaunin Unguwar su take…
Tun k’arfe hud’u Abubakar ke k’ok’arin k’iran Suraj a waya amma bata ko shiga hasali ma wayar sa a kashe take don haka ya tura d’aya daga cikin yaran sa su duba ko bacci yake nan ma de basu ji motsin kowa ba haka ya hak’ura ya tafi zuwa warehouse d’in don duba kayayyakin da aka kawo.
Junaid kuwa tafiya suke ta dokawa har suka iso mashigar Unguwar su Suraj bashi da aiki da ya wuce haska pics.
Duk da yamma tayi, bazaka gaza ganin how lively wajen yake ba, yara da manya kowa yana harkar gaban sa, tun diga farkon Unguwar yara suke biyo su Junaidu suna k’iran sunan shi hakan ya burge Suraj ainun ya washe baki yana dariya, wasun duk suna ta kama Suraj, kamar yadda Junaid yake wasa da su haka Suraj yayi ta wasa da su da kyar Suka sulale jiki suka bar yaran, chan gaba suka hangi majalisa cike da kamilallun dattijai a tare suka duk’a har k’asa suka gaida su Junaidu ya gabatar da Suraj lamarin da ya basu mamaki domin ko da Sau d’aya basu tab’a ganin yarima mai sauk’in kai irin sa ba gashi baya kyamar talaka ba kamar su Saeed ba wanda sun san halin shi sarai gashi kuma duk al’amarin da ya shafi talakawan k’auyen shi yake ji da shi hakan ya bashi daman musu kallon hadarin kaji yake taka su yadda yake so tunda yayan shi Abubakar bai cika zama ba sannan Ameer k’arami ne shiyasa yake cin karensa ba babbaka gashi Ameer daman ka barshi kawai da gulmar sa da bully.
Cike da isa ta chafko Wuyan rigar shi da hannu d’aya d’ayan hannun kuwa ta rik’e kafad’a gami da k’ank’antar da idanuwa ta cije baki tace “A bisa wanne dalili zaka bangaje ni ka wuce?”. Cike da masifa take maganar hakan ya maida hankalin Suraj wajen da take ,take zuciyar sa ta fara harbawa Junaid ya tafi da gudu don kwatar wanda aka shak’e ,hakurin duniya an bata tak’i hak’ura ta d’ago kai zata yi magana karaf idanuwan ta suka had’e da na Suraj ji tayi kamar wanda ya bata umarni cike da tsiwa ta sake shi sannan ta dube shi chan k’asan mak’oshin ta tace “tsk! Yi hak’uri” ,daga nan kai a k’asa ta kad’a kan dabbobin ta wuce tana satar kallon Suraj ta gefen ido saida ta tabbatar sun wuce ita da Zubaina suka kwashe da dariya suka sa gudu.
Suraj ya dad’e a Unguwar banda shan dariya babu abunda yake saboda karamci da son mutane da barkwanci irin na mutanen wajen tare suka yi sallar Magariba da isha sannan ba tare da nuna kyamar su ba Innar Junaid ta zuba musu dambu suka ci harda santi. Har inda ya bar motar shi d’azu Junaid ya raka shi sannan suka yi sallama ya ja ya tafi.
K’arfe Tara saura ya yi parking daidai main entrance ya fito yana wasa da key yana Murmushi shi kad’ai har an bud’e masa k’ofa zai shiga yaga kamar mutum a tsaye ta gefe dan haka ya tsaya chak kafin ya juyo idanuwan sa cikin na Ameer tsaye ya nad’e hannu a kafad’a ya jingina da pillar fuskar shi d’auke da shu’umin Murmushi wanda daga gani mutum yasan ba na tsakani da Allah bane. Kallon da yake yi wa Suraj ba na arzik’i bane kuma kallo ne da zai sa mutum tsarguwa ,Ameer bak’in kunama ne, koren maciji cikin ciyawa, sosai Suraj yake tsoron halin sa saboda ba mutum ne da za’a yarda da shi ba.
Ba tare da ya ce komai ba Suraj ya nufi k’ofar a karo na biyu har ya sa k’afa Ameer ya ce
“Mhmm ! A place full of love ko? Tabbas!”
Sai da k’irjin Suraj ya buga Ras! Amma ya dake ba tare da ya juyo ba ya shige ciki ya banke k’ofa.
Wannan shu’umin Murmushin Ameer ya sake yi kafin ya juya ya bar gurin bayan yayi snapping yatsun shi as in zaka gani d’in nan.
Wurgi yayi da key d’in cikin zafin nama ya kai duka a bango hakan yasa knuckles nashi ya kukkuje har da jini. Mamakin da yake yi shine yadda akayi har yasan hirar da yayi da Junaid tabbas Ameer ya cika munafuki na k’arshen zamani. Juya wa yayi zai wuce upstairs karaf idanuwan sa cikin na Dad irin kallon da yake mishi ne yasa Suraj yai tunanin tabbas akwai wani abu a k’asa kuma ko ba komai ba sai an fad’a ba Ameer had something to do with it. Jiki a sanyaye ya k’arisa inda yake ya zauna sannan ya gaida shi.
“Where have you been?” Shine amsar gaisuwar da Suraj yayi , gashi Dad yayi tambayar ne in an authoritative tone hakan ya sake tabbatar masa cewa akwai matsala Amma dayake shima Suraj irin murd’add’un mutanen nan ne yana dai dai da ko wacce tambayar da Dad zai masa sanin cewa Bai yi wani abu da zai sab’a k’aida ba…….