Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter 31
Haisam da Ramlah suka hau kallon-kallo, Haisam ya ce “Ina kuma wannan zata je babu sallama. Ramlah ta ce “Ka bita ka gani, ina jin gidanta ta tafi da alamar kuka take yi. Haisam ya ce “Ai kukan ma ta tafi zata yi ya isheta domin gwanar kuka ce na tabbata ta tuna maraicinta ne zata ga kudin bashi da amfani a wajenta saboda sunzo lokacin da babu Mahaifanta. Ramlah ta girgiza kai ta ce “Allah Sarki jeka ka bata hakuri kada ta damu haka Allah Ya rubuto mata yaya zata yi duk mai rai mamacine kowa jiranta yake banda abun Hannah bai kamata ta dinga damuwa ba tunda Allah Ya bata miji tamkar Uwarta da Ubanta. Haisam ya ce “Iyaye daban ne da miji Ramlah karma ki hada. Ramlah tayi dariya ta ce “Miji dai irin na Hannah zan iya cewa daya ne da Iyayenta tunda tun tana karama yake rainonta baya so ko kuda ya tabata zai iya hallaka duk wanda ya nemi ya takura mata saboda tsananin so da kulawa da yake mata. Haisam ya mike tsaye daga kan kujerar da yake zaune yana dariya ya ce “Raudah ta cika gulma haka ta fada miki? Suka sake tuntsirewa da dariya dukkanninsu. Ramlah ta kara da cewa “Baka ji masu iya magana na cewa fini da gidan Uba in fiki da gidan miji ba? Ai duk masu gata a wajen Iyayen nan borori ne a gidan mazajensu. Irin su Hannah marayu su kuma su caba da miji mai tsananin son su. Haisam ya juya ya fara tafiya ya nufi kofar fita. Ramlah na biye da shi a baya. Ta ce “Kayi shiru sai murmushi kake baka ce komai ba. Haisam ya ce “Aunty Ramlah kin cika son magana me kike so ince miki? Ta ce wai dana ga hira muke sai ka dan tayani hirar kayi min musu kace Rauda karya take ba’ayi haka a Kazaure ba. Haisam ya ce “Kishi! Kishi!! Ya motsa kumallon mata ai gara ki amayoshi, yanzu fa nake yabonki kin nunawa su Hidaya baki da kishi ni kuma kinzo kina son tutsiyeni. Ramlah ta ce “A’a ba haka bane ni dai nasan kana son Hannah da yawa fiye da… Yasa hannu ya toshe bakinta ya ce “Kema ina sonki kima daina tunanin wani abu kinji ko. Suka tuntsire da dariya Ramlah ta daga gira ta ce “Naji dadin amsarka na gode tunda na fita daga sahun masu son maso wani. Haisam yayi dariya ya fice, Ramlah ta rufo kofar ta shiga cikin gida. Haisam na fitowa ya nufi bangaran Hannah ya taba kofar yaji a datse yasa hannu a aljihunsa ya dauko mukulli ya bude ya shiga ya tarar babu kowa a falon sai ya nufi sama kan bene. Ya tura kofar dakin ya shiga a can karshen gado ya hango Hannah a kwance ta takure tana rusar kuka yayi sallama ya shigo ta dago da sauri suka hada ido Haisam sai ya girgiza kai ta sake kifa kai yayin da kuka mai tsanani ya rufo mata. Ya karasa gareta ya rada mata a kunne cikin sanyayyar murya ya ce “Goge hawayenki, bana so in sake ganin hawaye a idanuwanki zamu yi wata magana. Bayan kamar minti uku kukan da Hannah take yi ya tsaya. Can Haisam ya dago kanta suka hada ido sai ta sake kwantar da kanta a kirjinsa yana shafar lallausan gashinta ya ce “Hannah meye yasa ki kuka? Karki boyemin ki fadamin gaskiya kuma bana so ki sake rushemun da kuka. Tayi dan murmushi cikin sanyayyiyar murya ta ce “Nayi kuka ne saboda farin cikin da yayi mun yawa da wadannan kudi masu dunbin yawa daka bamu ni da Yayata. Haisam ya ce “Dalilin kukan ki na biyu kenan baki fadamin na farko ba, ina ganin babban dalilin da yasa ki kuka shine Allah Ya kawo miki kudi mai dunbin yawa a lokacin da babu Mahaifanki wadanda za ki bawa suma suci gajiyar arzikin da Allah Yayi miki. Haka ne ko ba haka bane? Hannah ta gyada kai ta ce “Hakane. Haisam ya ce “Yauwa na gode baki boye mun ba, Hannah kina da ilimi, kina da tunani da hankali matuka bai kamata ki dinga damuwa akan kaddara da jarrabawar da Ubangiji Allah Ya rubuto miki ba. Hakuri da tawakkali da kika yi a baya shi zaki ci gaba duk lokacin da irin wannan tunani ya fado miki a rai kiyi sauri ki kawar ki sawa ranki Allah Ya dauke ran Mahaifanki Ya mayar dake marainiya gaba da baya akan haka Yaso Ya ganki, amma sai yayi miki canji da wani mutum a matsayin mijinki kuma mai kaunar yaga farin cikin ki tamkar Iyayenki. Hannah ina ganin ko *ya*yan cikina bazan jisu a raina ba kamar yadda nake kwana in yini dake kullum a zuciyata ina ta sake-saken yadda zan faranta miki, daidai da sakon daya bana so ki shiga matsala. Bacin ranki ko kukanki tamkar dalmar wuta ake soka mun a zuciyata ki taimakeni Hannah ki daina saka kanki cikin damuwa domin damuwarki tana jawo mun mummunar damuwa. Tsakaninki da Mahaifanki sai addu’a nima kuma nayi miki alkawarin zan dinga taya ki da yi musu addu’a har karshen rayuwata. Ta dago ta dubeshi kallo mai kunshe da tsananin so da kauna tasa bakinta a gefen kumatunsa, ta sumbace shi ta rungume shi.
Ranar da Hannah da Haisam zasu tafi da misalin karfe goma na safe Ramlah da kanta take tuka motar ta kaisu filin jirgi tana daga musu hannu har suka hau jirgi suka tafi Abuja. Ita kuma ta dawo gida, haka ta kasance gidan shiru babu dadi sai ita kadai. Washe gari taje gidan su Haisam ta roki Hajiyarsa ta bata Amratu tazo ta tayata zama suka taho tare. Babu abinda Ramlah tasa a gaba yanzu sai shirye-shiryen yadda za’ayi ta fara gudanar da shirinta a gidan rediyo wato shirin nan nata mai taken SOYAYYA GASKIYA CE. Tana ta sintiri gidan rediyon nan mai farin jini wato FREEDOM RADIO domin bincike tasan yadda za’a sayar mata da filin da zata dinga gudanar da shirye-shiryen duk sati. Sun karbeta da farin ciki sun kuma zabar mata lokacin da suka ga ya dace ta dinga gudanar da shirin sannan sunyi mata alkawarin zasu fara yi mata tallar shirin kafin ranar da zata fara gudanar da shirin. Ramlah bata damu da dunbin kudin da zata dinga kashewa ba duk sati na sayen filin da zatayi shirin burinta shirin ya samu karbuwa a wajen jama’a sakon da take so ta isar ga al’umma ya isa gare su.
Duk ranar lahadi misalin karfe tara zuwa goma da rabi Ramlah zata dinga gudanar da shirin, sannan kuma duk ranar laraba da daddare a maimaita shirin. Wannan ne sati na farko da Ramlah zata fara gudanar da shirinta, jama’a da dama sun matso da akwatinan rediyonsu kusa da su don jin wannan sabon shirin da ake ta tallarsa kullum wannan gidan rediyo. Ga hirar kamar haka.
FREEDOM RADIO: Assalamu alaikum Jama’a ni Hajiya Hassana Hassan Safiyanu Gumel zan gabatar da wannan sabon shirin tare da Malama Ramlah Haisam Shitu. Malama Ramlah Haisam sannu da zuwa.
Ramlah: “Salamu alaikum.
Haj Hassana: Malama Ramlah jama’a da dama sun kagu suji wannan shirin saboda suna jin tallar shirin mai taken SOYAYYA GASKIYA CE. Zamu so mu fara dajin takaitaccen tarihinki, da kuma dalilinki na kirkiro wannan shirin, da ma’anar kalmar SOYAYYA GASKIYA CE.
Ramlah: murmushi, “asSalamu alaikum jama’a ni sunana Ramlah Shitu, shekaruna Ashirin da shida nayi makarantar nursery da primary wato secondry a kasar America bayan mun dawo nan kasa Nigeria na shiga jami’ar Bayero (B.U.K) na yi digiri akan harkar yada labarai (Mass communication).
Haj Hassana, dariya: “Ashe ma kema ta gidan ce *yar jarida.
Ramlah, dariya: “Kwarai kuwa nima *yar Uwar kuce *yar jarida. Don haka nema naga ya dace nima in bada tawa gudun mawar duk da ni ba ma’aikaciyar gidan redio bace ko talabijin naga ya kamata inyi amfani da karatuna inzo in bada tawa gudunmawar ga al’umma. Kamar yadda kika tambayeni meye ma’anar SOYAYYA GASKIYA CE, kuma meye dalilina na kirkiro wannan shirin? Dalilina na kirkiro wannan shiri shine, sai don kawai naga *yan Uwana Musulmai, Hauswa samari da *yan mata yara da manya muna da matsala wacce muke nema a wayar mana da kai akanta. Matsalar kuma ita ce ta mace-macen aure da rashin samun zaman lafiya a cikin zaman aure, zaki ga ko an zauna ba’a rabu ba to zaman ma babu dadi kaga miji da matarsa kamar ba suna son juna suka yi aure ba sun zama abokan gaba kowa na kokarin ya cusgunawa dan Uwansa shima ya rama laifin da dayan yayi masa, babu fahimtar juna. A gaskiya Hausawa basu yadda soyayya gaskiya ba ce. Zaki ga da zarar anyi aure shikenan soyayya ta kare sai zaman hakuri ko zaman *ya*ya to gaskiya ba haka bane. Yaune ranar farko da muka fara gudanar da shirin bazai yiwu in faiya ce muku komai ba a yanzu sai a hankali zanyi muku bayanai dalla-dalla. A yau dai abunda zan fara yin bayani akai shine, Mecece soyayya? Dawa ya kamata kayi soyayya? Kuma yaya za’ayi soyayya ta dauwama har abada?
Soyayya ita ce kaga mutum mace ko namiji kaji kana son ta ko son sa saboda Allah, ka zauna dashi saboda Allah, kana kula da halayensa abunda yayi mai kyau ka kara karfafa masa gwiwa ya ci gaba. Idan yayi abu marar kyau ka hana shi cikin nasiha da dabaru. Kana sonsa a lokacin da bashi da shi. Kana tunani a kullum yaya zaki faranta masa rai ku taimaki juna a lokacin da dayanku yake tsananin neman taimako. Mutum ba’a gama masa halitta har sai ranar daya mutu don haka kada ka guji dan Uwanka don wani tsautsayi ya same shi halittar ta canja. Ma’ana akwai hatsari na mota akwai wuta duk mutum zai iya nakasa idan soyayyar gaskiya ce baza ka tsaneshi ba, wannan ita ce ma’anar soyayya.
Haj Hassana: Malama Ramlah munji ma’anar soyayya, sai ki gaya mana dawa ya kamata kayi soyayya?
Ramlah, murmushi. Ko mace ko namiji ya kamata kasan dawa ya kamata kayi soyayya ma’ana kaso mai sonka. Soyayya takan fada kan mutumin ko mutumiyar da ita kuma bata da ra’ayinka kunga akwai matsala kenan.
Haj. Hassana. Wato kina nufin kenan kar a yi son maso wani?
Ramlah. “Yauwa zaki ga wani lokaci mace tana son namiji shi kuma baya ra’ayinta duk da dai ba’a cika samu ba, an fi samun namiji nason mace amma ita bata sonsa. Shi kuma zaka ga Allah Ya jarrabeshi da tsantsar sonta ita kuma bata sonsa, duk wata hanya da zai bi yaga ya mallaketa zai yi ta bi, ya yi ta shisshige mata yana mata kyaututtuka amma ita baya burgeta saima tsana da haushinsa yake sake lullubeta kuma har abada bazai burgeta ba saboda bata sonsa a zuciyarsa. To abu na farko daya kamata shine ya kyaleta yaje ya nemi mai sonsa itama ta auri wanda take so kada ya damu karya kullaceta bayin kanta bane domin soyayya abace wacce Allah Yake sakawa a zuciyar bayinSa. Hakika bana karfafawa jama’a gwiwa akan su nacewa wanda baya son su ina ganin hakuri shine babban magani, kaje ka auri mai sonka. Amma muddin aka takura akayi mata dole ko akayi masa dole, in namiji ne baya so, to lallai za’a samu mummunar matsala bayan auran. Saboda aure yafi yin karko in namijin da macen suna son junansu. Daga karshe zanyi magana akan yaya za’ayi soyayya da dauwamammiya har abada?
Soyayya zata iya dauwama har karshen zaman miji da matarsa har tsufa bata gushewa , shine da farko akwai kyautatawa. Namiji da mace kowanne yana neman kyautatawar dan Uwansa. Na biyu kulawa, mace ta kula da mijinta ta kowanne bangare, misali dafa abincin da zai ci tsafta ce ruwan shan sa, makwancinsa, ban dakinsa, tufafinsa, kulada dukkan yanayinsa na farin ciki ko na bakin ciki, ki kwantar masa da hankali ki lallashe shi har yaji wasai. Haka ma namiji ya kamata ya kula da matarsa gwargwadon karfinsa. Cinta, shanta, mahallin da zata zauna, lafiyarta ya kaita asibiti in bata da lafiya ita da yaranta. Kalamai masu dadi, wasa da dariya, tufafin da zata sa na fita kunya dai-dai karfinsa da magana mai dadi ba kullum zai fita ba da fada. To in har duk wadannan abubuwan suka samu tsakanin miji da matarsa zasu dauwama cikin farin ciki da son juna kullum.
Haj Hassana. “Gaskiya Malama Ramlah kin faiya ce mana manyan matsalolin da suke addabarmu a wannan al’umma tamu. Yanzu kuma zamu bude layin wayoyinmu don jin ra’ayin masu sauraron mu. Masu tambaya ko karin bayani. Sai dai don Allah jama’a ayi tambaya akan abunda muke tattaunawa yanzu, a cikin shirinmu na SOYAYYA GASKIYA CE.
Ramlah tayi mamakin ganin yadda ake ta bugo waya anata yabawa da shi mata albarka, wasu kuma suna tambaya akan matsalolinsu da suka dade suna nukurkusarsu sai yanzu Allah Ya kawo musu mafita. Ramlah tayi amfani da iliminta da tunaninta ta basu shawarwari har sai da suka gamsu. Daga karshe suka yiwa masu sauraro sallama akan sai sun hadu a wani sabon shirin wani satin. Ramlah ta fito farfajiyar gidan rediyon inda ta ajiye motarta kafin ta bude motar ta shiga, sai wayar hannunta ta hau ruri tana dubawa sai taga Hidaya ce take yi mata waya. Ta matsa gami da yin sallama cikin shesshekar kuka Hidaya take magana ta ce “Ramlah zo gidana kiga halinda nake ciki. Cikin rikicewa Ramlah take tambaya “Lafiya, me ya faru?
Hidaya ta ce “Ga danyen jego ina yi ko arba’in banyi ba ga tashin hankalin kishiya, shine Hajiyar su Habib tazo tayi min tas a gidan nan wai ita bazata yadda a kara zamar da danta zararre ba kamar yadda aka zamar da Haisam wai in har nasan bazan zauna lafiya da amaryata ba lalle ba dole in bar gidan, ga Habib nan hankalinsa a tashe a kullum. Ramlah ta hau lallashin Hidaya ta ce gata nan ma zata so gidan yanzu.
Daga Freedom radio sai gidan Hidaya Ramlah ta garzaya ta shafe awa uku tana lallashin Hidaya ta bata shawarwarin yadda zata zauna da kishiyarta lafiya.
Bayan tafiyar su Hannah da wata guda, Ramlah taji labarin an fara sayar da form din Jamb. Don haka ta garzaya Banki ta suyowa Hannah, ta cike mata domin Hannah ta sanar da ita irin cours din da take so first choice ta ce Medicine, second choice Biochemistry.
Hannah da Haisam kullum suna yiwa Ramlah waya da daddare suyi ta hira suce suna missing dinta sosai. Sun shaida mata sunje Dubai da London yanzu kuma suna America. Ramlah tayi musu fatan alheri da fatan su dawo gida lafiya. Daga America sai suka wuce Saudia don yin aikin Hajji. A lokacin saura sati biyu ayi arfa. Kasancewar Ambassadon Nigeria dake Saudiya abokin Baban Haisam ne don haka waya kawai Haisam yayi masa cewar gasu nan zuwa. Don haka kafin jirginsu ya sauka a filin jirgin Jiddah an turo motar da zata dauke su. An basu masauki a Jiddah Haisam ya ce ai Madina zasu wuce kai tsaye baza su zauna ba. Mota da direba aka basu suka tafi Madina Hannah tayi matukar farin ciki da ta ganta a cikin wannan gari mai albarka fiye da duk kasashen da suka zazzaga. Kamar a mafarki ta ganta a shabbaki harma gata ga Kabarin Annabi Muhammad (S.A.W) ta rike katangar kabarin ta rungume tayi kuka ta yiwa Allah godiya. Sannan tayiwa Mahaifanta addu’oin nema musu gafara da rahama a wajen Mahaliccinsu. Hannah tayi mamaki matuka ganin yadda Haisam yake mata ko Sarauniya sai haka.
An yiwa mazan Larabawa shaida wajen kulawa da matansu, sune masu rike musu takalma su rike musu yara da duk wasu kaya ita dai macen balarabe tafiya take sunke a cikin bakar abaya ta rufe dukkan jikinta har fuskarta, yana biye da ita yana kakkareta kada wani ya tabata, duk da wannan kulawa da ake yi musu sai suka ga ba komai bace akan yadda suka ga Haisam na yiwa Hannah. Haisam na rike da hannun Hannah gam duk inda zasu je ko tsinke baya barinta ta rike shi da direba ne masu rike kaya idan yaga kamar mutane suna tahowa ta daya bangaren sai kaga yayi sauri ya dawo gefen, a jima ya dawo bayanta yana kareta ya dawo gabanta ya komo daya bangaren nata yana kareta wai shi a dole kada wani ya tabata ko kar a tureta ta wahala. Haka suka sami kwana takwas a Madina duk sun kai ziyara zuwa wuraren da ake zuwa kamar Bakiyya, Masallacin Kuba da Dutsen Uhudu inda Kabarin su Sayyadina Hamza (A.S) yake. Haka duk kantin da suka shiga Haisam yayi ta jidowa Hannah kaya har hana shi take yi, ya ce shi dai sun yi masa kyau sai ya siya mata idan akwai guda biyu iri daya sai ya saya musu su biyu da Ramlah. Haka kantin gwal yayi ta saya mata har diamond ita da Ramlah da Mamarsa da kanwarsa Amratu. Kafin su bar Madina sai da suka yi dilar kaya katuwa aka daure musu akasa a mota suka nufi birnin Makka. Daga shigarsu Makka kai tsaye suka wuce kayataccen hotel din nan na masu hannu da shuni wato Intercontinental Hotel wanda ko a Larabawa ma sai wane da wane ne suke iya kama wannan hotel saboda tsadarsa, gashi gaf da Harami yake. Bangare guda Haisam ya kama a Hotel din ma’ana ga falo, dakuna biyu kowanne da toilet a ciki ga kicin da kayataccen darning area. Lallai duk wanda ya budi ido ya ganshi cikin hotel dinnan zaiyi tunanin ba’a cikin wannan duniyar yake ba sai dai ya kwatanta da Aljannah. Kayansu kawai suka sauke sai suka nufi Harami daman sun riga sunyi wanka sunyi niyya tun daga can Mikati tsakanin Madina zuwa Makka sun saka haraminsu. Suna shiga Harami sai suka yi Umara. Suka gama aikin Umara lokacin Sallar azahar ce sai suka bi Limamin Masallacin Sallah, wato Sudes.
Bayan an idar sai suka dawo hotel dinsu suka sa aka yo musu odar abinci kala-kala har da direban suka hadu suka ci, bayan sun gama sai Haisam ya dauko kudi mai yawa ya bawa direban ya ce ya koma Jiddah sai ranar da za’a fita Minnah ya zo ya daukesu da sassafe. Tunda ga su ga Harami ga kantina akusa babu inda zasu je da mota. Direba yayi ta godiya saboda yaji dadi sosai a wajen Haisam kayan da Haisam ya dinga saya masa a Madina shima sai da yayi akwati guda tasa. Suka yi sallama ya tafi. Haisam da Hannah sun kasance suna ta hutawarsu cikin wannan katafaren hotel sai lokacin Sallar la’asar suke fitowa su sami Sallar Jam’i sai suyi ta dawafi har magariba, bayan Sallar magariba sai su jira lokacin Sallar isha’i. Bayan an idar da Sallar isha’i sai su fito suyi ta shiga kantina suna siyayya. Nanma haka kayan da Haisam ya dinga sayawa Hannah abun baya lissafuwa. Haka Hannah duk danginta kowa da sunansa ta sisiya musu tsaraba komai dozin suka dinga siya. Bayan dilar da suka yo a Dubai da London da America da Madina duk sun aunasu Nigeria ta awan Kago wato Jirgin kaya.
Hmmmmmm