Gangar jikinsa na aura32

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA

Chapter32

Ranar da za’a tafi aikin Hajji tun da asuba Mahajjata suka tashi suka yi wankan niyyar Hajji suka sa haraminsu da sassafe suka fara shiga motocinsu suna tafiya Minna. Direban su Haisam ya baiyana tunda sassafe don haka Hannah da Haisam suka fito sanye da haraminsu sai wata karamar jaka dauke da *yan kayayyakinsu kadan suka shiga suka tafi. Yadda ake fadar wahalar aikin Hajji Hannah bata ga wuyar ba saboda komai na su daban ne da sauran Mahajjata, domin suna tare da Ambassadon Nigeria da Iyalansa a Minnah, shemarsu ba a wajen da ta *yan Nigeria suke ba suna can gaba kusa da wajen jifan shaidan taku daya biyu zasu yi suje wajen jifan shaidan sabanin ta sauran Alhazai wadanda sai sunyi tafiyar miles da yawa kafin su isa wajen. Ga Haisam na rike da ita babu wanda yake murkusheta ko taka ta. Sunyi aikin Hajjinsu a nutse cikin sauki, sannan kowa ya fara neman hanyar garinsu.
Haisam da Hannah sun dawo Makka inda suka karayin kwana biyu a hotel dinsu daga karshe suka je suka yi dawafin bankwana suka zuba dilar kayan a mota suka nufi Jiddah. A gidan Ambassador suka sauka nan ma suka yi kwana biyu sun shisshiga kasuwannin Jiddah kamar su Baba Sharif da sauran kasuwanni da ke Jiddah. Ana gobe zasu tafi suka je tekun da ke nan Jiddah (beach) nan fa iska mai sanyi take kadawa ga larabawa nan da matansu da *ya*yansu suma suna zazzaune suna ciye-ciye da shaye-shaye lemuna da gahawa da dabino. Haisam da Hannah da *ya*yan Ambassador su biyu kanana Husain da Hussaina suma suka shimfida katuwar darduma suka baje kayan marmari dana kwalaye iri-iri suna ci suna hira. Husain da Husaina kanana ne *yan kimanin shekara shida, Husain ya jingina a jikin Hannah ya ce “Aunty Hannah bama so ku tafi dama kuyi ta zama anan tare da mu. Hannah tayi dariya ta shafa kansa ta ce “Husain ayi haka kuwa, muyi ta zama a gidanku mu ma fa *yan gidanmu suna can suna jiranmu mu dawo. Sai dai idan ka yarda in tafi dakai. Husain ya ce “Eh na yarda zan biku. Su duka suka tuntsire da dariya, Haisam ya ce “Kin samu da lallai a fadawa Mamarka ka hado kayanka. Hussaina ce ta tabe baki alamar zata fashe da kuka wai taji ance za’a tafi da dan Uwanta Husain. Haisam ya ce “Lah Hussaina kuka zaki yi don ance za’a tafi da dan Uwanki to share hawayenki ki daina kuka baza mu tafi dashi ba. Hussaina ta goge hawayenta tana dariya sai ta ce da Haisam “Uncle zaka bar mana Aunty Hannah anan? Bama so ta tafi. Haisam da Hannah suka tuntsire da dariya. Haisam ya ce “Lallai ma yarinyar nan kin fiye wayo na dauka yanzu kike kuka karmu tafi da dan Uwanki wato sai dai in bar muku tawa *yar Uwar ko? To naki, in bar Hannah anan in tafi Nigeria inje inyi me? Ai gara ace an kwashe mutanen Nigeria Kakaf an kawosu Saudia ni kuma a barni da Hannah a Nigeria mu biyu muna shawagi a kasar. Hussaina sake shawara ko kuma ki sake neman wata alfarmar ta wani bangaren banda wannan. Hannah tayi  tsai tana kallon Haisam kallon da yake kashe masa dukkan sassan jikinsa wanda har cikin zuciyarsa yake
 jinsa. Tayi dan murmushi ta sunkuyar da kai kasa ta ce “Tuntuni wannan bayanin naka ya wuce fahimtar Hussaina bata ma san me kake ce mata ba sai dai wacce ake yi dominta ita take gane abunda kake nufi. Haisam ya mayar mata da irin kallon da tayi masa ya lumshe ido ya ce “Alhamdulillah tunda wacce nayi dominta tasan abunda nake nufi. Hannah ta mike taja hannun Haisam suka fara tafiya a cikin yashi lubus yayin da ruwan teku yake yin kukan kura feshin ruwan yana feso musu. Tafiya suke a hankali suna hira Hannah ta kashe murya ta ce “Nawan, na dade ina mamaki amma ba’a mamaki da ikon Allah saboda ikon Allah ya wuce haka. Kiftawar ido da budewa yayi yawa a wajen Ubangiji Ya zamar da mai kudi talaka, Ya zamar da talaka mai arziki, Ya zamar da bawa Sarki Ya maishe da mai lafiya marar lafiya Ya canja kunci izuwa farin ciki. Haisam ya ce “Haka ne gaskiya ne. Hannah ta nisa ta ce “Akwai lokacin dana zamana a cikin kunci da tashin hankali, gabas da yamma kudu da arewa, sama da kasa duk inda na waiga sai bakin ciki da tashin hankali babu wanda zan gani naji dadi a rayuwata, babu mai lallashina, babu mai kwantar min da hankali. Na cire rai da kara samun walwala a rayuwata, nayi sallama da farin ciki nayi ban kwana da soyayya tunda wanda nake so ya ce min good bye ya tafi ya barni. Abu daya na rike shine Allah Yana tare dani kuma ko bai yimin sakayya a duniya ba nasan zai bani a lahira musamman ranar da nazo gidanka maimakon in ganka sai aka ce mun ka rasu hakika a ranar na sake tabbatarwa nayi bankwana da farin cikin duniya, ko me na zama nan gaba ko dawa Allah Ya hadani bana jin zan sake son kowa a duniya. Ba zato ba tsammani gaba daya Allah Ya juya mun rayuwata daga tsantsar bakin ciki izuwa tsananin farin ciki, na godewa Allah ina sake yiwa Allah godiya fatan Allah Ya hadamu a Aljannah ni da kai da Aunty Ramlah da Mahaifana masu sona da Iyayanka. Ta zubo da hawaye sharr daga idanuwanta. Haisam ya jawota suka zauna yasa hannu yana goge mata hawaye ya ce “Hannah kenan gaki yarinya mai hankalin manya. Addu’a bata faduwa kasa sai dai jinkiri. Ina addu’a Allah Ya hadani dake kullum dare da rana wani lokaci har in nemi yawun bakina in rasa, makogwarona ya bushe hawaye ya kafe amma shuru Allah bai hadamu ba sai bayan da duk muka fitar da rai, muka cire rai akan farin cikin rayuwa sannan Allah Ya hadamu, hakika Allah Yana ikonSa Yana kuma yin yadda Yaso a lokacin da Yaga dama, Allah Shine abin godiya mu gode maSa. Bayan sun gama zagayen su, su ka dawo wurin Husain da Hussaina su ka zauna suka ci gaba da ciye-ciyensu suna hira har karfe goma da rabi na dare sannan suka nufi wajan da direba yake suka shiga suka tafi. Bayan shigar su dakin da aka sauke su, suka yi wanka suka kwanta. Hannah ta jawo wayar dake dakin (land line) ta bugawa Ramlah sukai ta hira har Haisam yayi barci ya barta suna waya suna ta kyalkyala dariya yana mamakin me suke cewa a hirar. Hannah ta nunawa Ramlah tana farin ciki da zasu dawo gida su ganta. Har karfe biyun dare suna hira sannan suka yi sallama.
Washegari da misalin karfe goma sha biyu na rana jirgin su Hannah ya taso daga Jiddah zuwa Kano sun ci sa’a kuwa suna isa suka iso da dilolin kayansu da suka auno. Shehu direban su ne da Amratu, Karimat amaryar Yaya Habib da Yaya Habib su ka zo taryar su da motoci biyu su ka zo, aka shirma kayan a daya suka shiga daya suka tafi. Tun daga get suka fara ganin an lillika wani abu mai kyalkyali suna shiga farfajiyar gidan suka ga an kewaye ginin gidan da kyalkeli an rubuta WELL COME BACK HAISAM & HANNAH. Gefe guda kuma balo ce aka huhhura da yawa akayi runfa da ita a tsakiya an ajije wani tebur dauke da wani katon kek an rubuta a jikinsa WELL COME BACK HAISAM & HANNAH. Sunyi mamaki matukar mamaki ganin yadda jama’a suka taru, ashe liyafa Ramlah ta hada saboda murnar dawowarsu. Kujeru aka zuzzuba a farfajiyar gidan, can gefe Mahaifiyar Haisam ce da Mahaifiyar Ramlah da sauran tawagarsu a zazzaune. Gefe guda kuma matar mai girma gwamna ce Haj. Nusaiba Idris da babbar kwarta Rauda Shitu da sauran kawayensu. Gefe kuma Ramlah ce da manyan kawayenta Hidaya, Aysha Sulaiman, Hauwa Mamman da wasu da yawa daga cikin kawayensu. Mamaki marar misaltuwa zaka iya gani a fuskokin Haisam da Hannah.
Suna fitowa daga mota Ramlah ta taso da sauri tazo ta rungume Haisam, ta rungume Hannah ta kama hannayensu zuwa cikin gida bangarenta yayin da *yan waje suka dau tafi raf-raf-raf. Daga shigar su wata kayatacciyar shadda irin ta jikinta ta dauko musu dan su saka suyi anko su uku. Cikin sauri suka fada ban daki da suke dakunan suka yi wanka su ka dauro alwala, bayan sun idar da salla su ka cankama ado da wannan kayatacciyar shaddar wadda ta sha surfani da danyen zare. Kalar shaddar ruwan zuma ce ta yiwa Ramlah da Hannah matukar kyau. Haisam ma abun sai wanda ya gani musamman ma da ya dora hula kalar shaddar. Ramlah ta fito da su zuwa farfajiyar gidan inda jama’a suke, hakika wanna ma’aurata sun burge jama’a, jikin *yan gulma yayi sanyi, masu tsananin kishi sun fara yayyafawa zuciyarsu ruwan sanyin cewar kishiya ashe abokiyar zama ce. Bangaren Mahaifiyar Haisam su ka nufa su duka suka durkusa a gabanta su ka gaisheta da kawayenta, suna amsawa cikin fara’a da farin ciki suka yi musu sannu da zuwa bayan nan sai su ka dinga zagayawa wajan jama’a suna gaigaisawa. Hannah da Nusaiba suka rungume juna, lallai Nusaiba ta kasance tana tsananin kaunar Hanna tun suna yara. Raudah tayi nadama sosai akan abunda ta yiwa Hannah ada, har yanzu ta kan kasa sukuni sosai duk sanda suka hadu da Hannah. Hannah nata kokarin janta a jiki dan ta saki jiki da ita kamar yadda suke da Nusaiba. Daga nan suka nufi bangaren kawayen Ramlah wato su Hidaya, Hannah tayi mamakin yadda taga sun mika mata hannu sun gaisa faram-faram, suka yi musu sannu da zuwa, Ramlah ta jasu zuwa wajen kek dan su yanka. Bayan an kirga daga daya zuwa uku Hannah da Haisam suna rike da wuka su ka luma a cikin Kek su ka yanka aka tafa musu cikin farin ciki masu hoto da bidiyo suna ta dauka, *yan hidimar gidan ne suke fitowa da lemo kala-kala suna ajiyewa baki a kan teburan da ke gaban su wasu kuma na ajiye abinci da snacks kala-kala. Bayan anci ansha sai shahararren makadin da aka dauko ya fara buga kayan kidansa wato Shaba dan Kwalisa ya ware murya ya fara rero wakar “Uwar gida ran gida Haisam yana miki rawa. An yi rawa an cashe Haisam ya likawa Ramlah da Hannah kudi lokacin da suke tsakiyar fili har magariba ana cashewa sannan kowacce ta fara hada kayanta don kama hanyar gidanta.
Bayan dawowarsu Hannah da kwana uku sun gama baccin gajiya sun huta sosai sannan suka fara ware kayan tsaraba kowacce dila aka bude, sannan Hannah ta fara warware kowa tasa kasancewar Hannah tasan tsarabar da suka suyowa kowa. Akwati guda aka cikawa Ramlah da tsaraba, tayi mamakin wannan tsaraba wanda ko ita taje abunda zata suyowa kanta kenan. Abunda ya kara bata al’ajabi wata akwati daban Hannah ta ciko da kayan jarirai (Uni set) masu matukar kyau ta bawa Ramlah ta ce na Baby ne idan ta haihu. Ramlah tayi matukar godiya da nuna farin cikinta a fili. Wata katuwar akwati aka kai gidansu Haisam tsarabar Hajiyar Haisam da Babansu da Amratu da Izziddin, suma sunyi godiya kwarai. Ta tura direba ya kai wa Yaya Habib da matansa da yaransa gaba daya kowa da tasa, suma sun gode. Ba tare da Ramlah ta sani ba Hannah ta aikawa Mahaifan Ramlah turarruka (designers) da kannan Ramlah kowa da abin da ya dace da shi. Sai kuma tsarabar kawayenta Nusaiba da Rauda suma da *ya*yansu kakaf sai da ta bawa kowa tasa. Kama daga masu gadi zuwa masu share-share, da goge-goge, masu bawa fulawa ruwa da masu kwasar sharar gidan babu wanda Hannah ba ta bawa tsaraba ba suma suna murna suna godiya. Himilin kaya Hannah ta lufga cikin wasu tuma-tuman akwatina guda uku wannan tsarabar *yan Uwanta na Niger ne. Tana so taje tun kafin suyi tafiya tayi musu sallama Haisam ya ce sai sun dawo daga tafiya, yanzu gashi sun dawo taga yana mata kame-kame wai ba yanzu ba ta bari sai ta gama jarabawar Jamb tunda lokaci ya kusa ta zauna tayi karatu. Ramlah na taya shi bata hakuri akan ta bari bayan sai ta gama jarabawa sai ta tafi a nutse. Wasu litattafan karatu Ramlah ta suyowa Hannah na karatun Jamb din da zata yi, subjects hudu zata yi akwai English, Physics, Biology da Chemistry kuma Ramlah tayi mata Register a wata makaranta da ake bayar da horo na musamman (lesson) akan Jamb. Don haka Hannah ta hakura da tafiyar har sai bayan ta zana jarabawar. Kullum karfe hudu zuwa shida Haisam da kansa yake kai Hannah makarantar da take lesson ya jirata ta gama ya dawo da ita.
Hannah ta kasance tana karatu haikan domin har ta fara manta karatun da suka yi a sakandire amma yanzu karatun da take yi shi yake tuno mata da karatunta na baya. Lokacin da za ta zana jarabawa ya rage kwana uku Haisam yaje Jamb ofis ya karbo mata center ta. A management za tayi dan haka ranar litinin da sassafe bakwai na safe acan tayi mata. Haisam ya kawo ta kafin ta fito daga motar ya sumbaci kumatunta yayi mata fatan alheri Allah Ya bada sa’ar jarabawa daga karshe ya ce mata da zarar ta gama ta kirashi a waya ya zo ya dauketa Hannah ta shiga dakin jarabawa aka miko mata question paper da answer sheet sai kawai tayi murmushi da ta karanta tambayoyin kamar cin tuwo yafi su wahala a gurinta. Nan da nan Hannah ta ciccike ta gama, ta zauna kamar minti talatin bayan ta gama tana zaune kawai tana kallon masu hada zufa da cizon biro da kallon sillin taji tausayinsu wasu dan babu yadda za tayi ta taimake su ta basu amsa. Ta so ace wani ya rigata mikawa amma har ta gaji da zama babu wanda ya gama har yanzu, sai ta mike taje ta kaiwa masu tsaransu sunyi mamaki da su ka ga har ta gama daya daga cikin Malaman ya ce ta sake zama dai ta duba ko tayi mantuwa. Hannah ta ce babu komai ta gama. Tana fitowa daga dakin jarabawar sai ta nufi hanyar get din fita dai-dai kantin wata bayerabia taga benci, bayan ta gaishe da matar cikin fara’a ta roketa zata
 zauna ta jira maigidanta zaizo ya dauketa. Bayan ta zauna ta bude jakarta ta zaro wayarta, bugu daya taji Haisam ya dauka shima yayi mamaki da yaji ta ce ya zo ya dauketa ta gama. Ya ce gashinan zuwa yanzu-yanzu.
Daya daga cikin Mamalam da suke tsaransu a dakin jarabawa ta hango ya nufo inda take, yana karasowa yayi musu sallama suka amsa sai ya yiwa Hannah lallausan murmushi ya ce “Minti biyu dan Allah *yan mata za muyi magana. Cikin mamaki Hannah ta tambaya ta ce “Ni? Ya gyada kai ya ce “Eh ke, dan ke na fito. Hannah ta harareshi ta ce “Malam yi hakuri ba zan iya zuwa ba sabo da kana magana ne da matar aure yanzu ma haka ina jiran mijinane zaizo ya dauke ni. Kamar
 ta dabawa mutumin wuka a kirji, haka ya zabura ya rike kirji yana fadin “Subhanallahi yanzu ke matar aure ce, yanzu kina nufin kina da aure? Karki boye min fada min gaskiya. Hannah ta sake gyara mayafinta ta ce babu zancen wasa tsakanina da kai Malam ban sanka ba, ba ka sanni ba, yaya za’ayi in yi maka wasa? Ya rike baki yana sosa keya da daya hannun fadi ya ke “Subhanallahi yanzu ke matar aure ce, yaya za’ayi kenan? Ni gaskiya na gani kuma ina so zan iya fadawa cikin wani hali dan wallahi a rayuwata ban taba ganin yarinyar da na kamu da santa ba a *yan mintina. Cikin fushi Hannah ta mike ta kalli matar nan mai kanti ta ce “Madam sai anjima zan bar wajan nan. Matar na cewa “Ah ba yanzu kika yiwa maigidanki waya ba ya zo ya dauke ki, ya za’ayi ki tafi? Hannah bata iya juyowa ta bata amsa ba saboda kallon da mutumin ya ke yi mata yayi yawa, ta kada kai ta nufi get din fita ba tare da ta san inda zata ba. Tana fitowa ta tsaya cak ta kalli gabas da yamma sai ta hango wata *yar yarinya wacce shekarunta basu wuce goma ba tana tsugune a jikin katanga ga faranti da kwanika akai da alama dai mai tallar abinci ce. Yarinyar kuka take haikan cikin sauri Hannah ta nufi inda yarinyar take tana karasawa wajen yarinyar babu abinda ta fara gani a jikin yarinyar sai shatin bulala har wani wajen zaka iya hango jan jikin fatarta ta fashe.

Barka da sallah in advance

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *