HARSASHEN SO CHAPTER 28

HARSASHEN SO 
CHAPTER 28
Kuka Abas yakeyi kamar ransa zai fita dashi da sauran abokanansu “yan duniya suka shiga cikin gidan. 
Tunda Mama tajiyo ihun Abas gabanta ya fara faduwa kalmar “innalillahi wa”inna ilaihir raji”un take ta maimaitawa tare da samun wuri ta zauna dan jinta takeyi kamarzata fadi, tasan babu lafiya dan duk lokacin da taji kukan Abas tasan akwai damuwa. 
Da gudun mai nuni da tashin hankali ya shiga cikin palon, inda Mama take zaune a saman kujera yaje gabanta ya zauna tare da rike kafafuwanta ya dora fuskarsa saman kafar yana mai ci gaba da kuka mai tada hankali. Cikin kuka Mama tace me kuma ya samu Mansur dina ne Eye? Kin yin magana yayi yaci gaba da kuka mai daga hankali, daga daki gwaggo ta fito da gudunta har tana faduwa tayo dakin Mama itama kukan takeyi tare da cewa me kuma ya faru ne? 
Cikin kuka Abas ya dago kansa tare da cewa, Mama wani abokinmu ne yaje ya sato kudi mu bamu san kudin sata bane ba, dama ni da’aka bani nace bana ansa amma shi Mansur ya amsa shine yanzun yana fita “yan sanda suka nannadeshi sun tafi dashi ……………… wai sai an biya wannan kudaden. Salati gwaggo tayi tare da cewa kudi kuma har nawa ne? Abas yace gaskiya kudin suna da yawa na gaske, Mama ko banda kuka babu abinda takeyi dan Baba yace wallahi duk lokacin da Mansur ya sakejawo fitina saidai ta jare akanta shi kam ya gaji da iskancin sa duk satin duniya akwai abinda Mansur zaiyi yaja aci masa kudi. 
Cikin damuwa Mama tace Allah ka shirya min Mansur dan albarka annabin rahma S. A. W. nidai na gaji fitar Mansur ta hanani zaman lafiya, fitinar dare daban na safe daban. 
Kallon Abas tayi tare da cewa, Abas tafi idan Babansu ya dawo zaije wurin “yan sanda, zaro idanuwa Abas yayi tare da cewa Mama ai wani wuri suka tafi dashi daban dan sunce iskancinsa yayi yawa horo mai tsanani zasu masa, babban nasu ma cewa yayi kullum farce 
daya da hakori daya za’a cire masa iskancinsa yayi yawa. ‘ 
Tashi Abas yayi jiki babu kwari ya fita, sauran “yan iskan abokanansu suka rufa masa baya, yana tafiya yana kuka, a bakin kofa suka hadu da Baba kallo daya yayi musu ya daure fuska ya wuce, suma fita sukayi simi simi kamar munafikai. A palon Mama ya samesu sai koke koke sukeyi, zama yayi daya daga cikin kujerun palon sannan ya kalli gwaggo yace ya akayi ne? Cikin damuwa gwaggo ta rattafawa Baba bayani, dan gajeran tsaki yayi tare da cewa ai na rantse a lamarin Mansur na cire hannuna Allah yasa ma su kashe shi na huta, banda fitina babu abinda haihuwar Mansur ya jawomin, Gwaggo tace haba Alhaji wannan wane irin rayuwa ne, ai hannunka baya rubewa ka ciresa ka yar, cikin tashin hankali Baba yace inji uban wa? Tuni ma ka cire dan iska kayar 
tunda baya da sauran wani amfani baya aiki kuma ya lalace sai dan banza wari dazai isheka dashi
Gwaggo zatayi magana ya daka mata tsawa harsai data razana, yace da Allah rufewa mutane baki, game da lamarin Mansur ko waccenku a cikinku zata hadu dani, yana fadin haka ya mike yabar palon a fusace, 
Itama gwaggo bayansa tabi dan bashi hakuri, ita kuwa Mama cikin tashin hankali ta koma dakin baccinta, bata so Mansur ya kwana dan kar a cire mata hakorin da, “yan kunne da sarka na gold masu tsadar gaske ta dauka sannan ta fita daga gidan ba tare da sanin Baba ba. 
Kai tsaye gidansu Abas ta nufa da zumarta bashi “yan kunne a siyar a anso Mansur, cikin kidimewa ta shiga gidan k0 sallama babu, dukansu suna zaune a sakar gida harda Mansur, da kallo ta bishi tare da cewa auta? Cikin dakiya yace Mama ya akayi ne? Wurin ta isa tare 
da cewa Abas yace min hukuma sun tafi dakai …… 
Daure fuska yayi tare da cewa Eh ai an fada miki amma baki taho da wuri ba saboda kema kin kagara na mutu, to ta Allah ba taki ba wallahi. Mama tace kayi hakuri haka Babanku yace bazai bada kudin ba fada ma yayi amma ga “yan kunne na nan da sarka da 
sune na kawo Abas ya siyaryakai kudin a taho dakai. 
Mansur yace to ai yanzun sai ki bayar a siyar a kaiwa mutane kudinsu,jikin Mama na kyarma ta mikawa Mansur tare da cewa ka dawo gida da wuri kaji autana, cike da rashin kunya yace to naji tafi saina taho,juyawa Mama tayi ta tafi, Tana fita suka fara murna Abas yace aje a siyar dasu ni nama dade banje zance ba, Mansur yace nima kudin anko zan kaiwa budurwata tana kallona as babban yaro zan kasa biyan 30k, ihu sukayi dukansu tare da tashi suka nufi kasuwa, Siyen banza akayi wa “yan kunne aka basu kudin, tun a gaban wanda ya siya suka raba kudin kowa ya kama hanyarsa, shi kuma Mansur gida ya koma yayi wanka yadan matsa turare aka gyara kai komai dai yayi shi a tsare, dakin Baba ya shiga cikin sando da tafiyar munafirci, a pale ya dauki makullin motarda Baba yafiji da ita a rayuwarsa,
Da sauri ya fita daga palon dan Baba baya palo yana ciki, da gudu ya fito babu wani bata lokaci ya shige mota yaja yayi tafiyarsa, sai gidansu Halimatu, waya yayi mata cewa ya iso, 
a yamutse tace tana zuwa. 
Saida ta mula tasha iska ta fito tana yauki tana isa sai kace diyar wani shege, bude mota tayi ta shiga ta zauna daidai da daidai sannan tace sannu da zuwa. 
Yawwa, ya kike? Lafiya qalau, shiru na wani lokaci sannan tace kwana da yawa ina ka boye? Kuma ina ka samo wannan motar ne? ‘Dan yatsina baki yayi sannan yace Yaya nane 
ya sayamin lta, cikin kware wa ta bariki Halima tace to Ina tawa ne? Mansur yace ba ga tawa nan ba sai mu rika hawa tare ba, Halima tace A, a, ai mota dan mutum daya akayi ta, kawai dai kana so ka nunamin Yayanka kai kaidai ne Yayanka, dan haka wannan mota tawa ce Yaya saiya sake siya maka wata. Ita a wasa tayi maganar amma shi a matsayinsa na babban yaro gani yakeyi idan bai bata motar nan ba ya zama sakarai. Duk kudin gidansu da wadatuwar arzikinsu mace ta tambayi abu a wurinsa bai bata ba ai ya zama sakarai, murmushi yayi tare da mika mata makullin motar yace ina miki murna Allah ya tsare, irin abun nan da mata sukeyi idan sun samu banza, tadan ware idanuwanta tare da cewa wow kai amma na gode wai da gaske kake? Ba tare daya bata amsa ba ya saka hannunsa a aljihu ya ciro kudin da zai bata ya bata, godiya ta karayi sosai tare da bin Mansur da kallo. Bude motar yayi ya fita tare da cewa ni zan wuce, godiya ta sakeyi sosai tare da ce masa to idan dai harda gaskiya kana so na da gaske to ka aiko don Allah, dama abinda yake hadamu fada kullum idan nace ka turo sai kace min saika tara kudi, Mansur yace Allah zan 
aureki haka Babana yace sai Yayana ya farayin aure sannan za”amin. 
Halimatu tace to Allah yasa yayi da wuri ko muma zamu shige sahun manya, murmushi Mansur yayi ba tare daya sake cewa komai ba yayi tafiyarsa, tana hangensa harya isa bakin titi ya hau abin hawa, 
Ajiyar zuciya tayi tare da sake kallon motar sosai sannan tace Allah kasa Mansur ya zama mijina dan wallahi shi bawan mace ne, duk macen data sameshi a matsayin mijin aure ta more…. Mansur kuwa gida ya nufa kansa tsaye ba tare dayaji fargaba ko wata tashin hankali ba, tunda ya shiga gidan yakejiyo masifar Baba amma wannan baisa hankalinsa ya tashi ba, Mama da Gwaggo suna ta bashi hakuri, 
Shi kuwa Mansur hannunsa yasa ya ciro sigarinsa a aljihu ya bata wuta, saida yaja ta sosai sannan ya wuce ta gabansu yana fito, karar sautin futon yana Fita hayakin sigarin 
yanayo masa rakiya., Cike da masifa Baba yace dan ubanka ina ka kai min mota ta tun dazu ina so zan fita mutane suna ta jirana saida kaga an wanke min ita sannan ka dauka, shima cikin masifar yace nawa ka siyeta ne? Kwantar da murya Baba yayi tare da nuna kansa yace ni kake tambaya nawa na siye mota ta? Mansur yace dole zan tambayeka mana tunda barayi sun kwaceta dole nasan ko nawa ka siya dan in biyaka kayarka, ya karasa maganar shima cikin daga murya kamar yana fada da abokinsa, ‘ Baba yace to k0 uwarka bazata iya biyan kudin motar nan ba, Mansur yace wannan kuma kaine ka sakota bakinka akaji ba,aji a bakina ba danni nasan darajarta, yana fadin haka yayi gaba, Baba yabi bayansa tare da jawoshi yaci gaba da dukansa, saida yayi masa lullusar Fitar hayyaci sannan yace ina mota ta dan uwarka? Ya dandana zagin. 
Cikin kuka Mansur yace to tunda ka daki kudin motarka bara ma a fada maka gaskiya, 
wallahi kyautarta nayi kuma duk cikar duniyar nan babu wanda ya isa ya ansota, ci gaba da dukansa Baba yayi tare da cewa kana hauka ne kasan kudin motar nan kuwa? Wai Mansur so kakeyi ka kasheni ne? Mansuryace da munji sauki a raba gado a bani abinda Allah ya cidani, 
Jin kukan Mansur yasa Maryam fitowa da gudu taga ko lafiya, wani irin kallo yayi mata tare da cewa ke saina ci uwarki wallahi, Baba yace kaci uwarta din, ba tare daya bawa Baba amsa ba yaci gaba da cewa kuma tunda nan ba gidan ubanki bane saikin bar gidan shigeya mai sigar mayu, sakinsa Baba yayi tare da kara wanwanka masa mari, yana sakinsa yabi Maryam da gudu, ihu tayi tare da kwalkwalawa da gudu tayi dakin uwarta ta kulle kofa, a kofar daki ya tsaya yaci gaba da durawa uwarta zagi. Baba kowa juyawa yayi yaci gaba da masifa wa Mama, shiru tayi bata ce masa komai ba, ji yayi kamar itama ya rufeta da duka, amma bai iya dukan mace danshi wallahi mata 
tausayi suke bashi ganin mace yakeyi kamar tangaram kana tabata zata fashe. 
Dan ya dannawa Mama bacin rai taji yanda yaji yasa yace kuma idan har baki biyani kudin motar nan ba saina kulle dan iskan yaron nan dan duk iskancin da yakeyi kece kike sashi,juyawa yayi ya fice cikin tsananin kunar zuciya, 
lta kuwa Mama ajiyar zuciya tayi tare da goge hawayen idonta yanzu yanzun nan tayi ramuwar kudi tun ba’a kwana ba Mansur ya sakejawo mata wata ma, kuma idan dai har Alhaji ya tafi da Mansur ya rufesa bata san inda zata saka rayuwarta ba,juyawa tayi ta koma ciki gwaggo tabi bayanta cikin tausayawa. 
‘Dakinsa ta nufa Gwaggo tana biye da bayanta, cikin sanyin zuciya tayi sallama amma Mansurya watsa mata harara harsai da taji nadamar zuwanta dakin, isa tayi bakin katifarshi ta zauna a gefe sannan tace
Auta so kake dai ka kasheni k0? Kullum abinda nake fada maka baka ganewa ko? Kullum haka kake so ana min wulakanci a gidan nan saboda kai? Na rantse da Allah duk ranar dana zazzageka daga rayuwata karyarka ta kare a cikin duniyar nan, 
To ki zazzage mana. Duniya da fadi Mama wata ma tana can dan da zai jawo mata fitanar takeso Allah ya bata amma bata samu ba, inama laifi an baki ni, wani ma kamarni yana can hauka yakeyi ya bige uwarsa ya zagi ubansa amma suna kaunarsa, to wai duka ma miye laifina? Kawai dai na gane hassada akemin kuma hassada itace gishirin rayuwa idan basai nayi kudi ba shege nake. Kuma wallahi wannan motar ban biyanta kuma kema baki biyanta ki barshi idan ya gaji da babatunsa yayi shiru.
Wanka masa mari Mama tayi tare da cewa tsinannan nan in Allah ya yadda na faraja maka alkunutu saika lallace, murmushi Mansur yayi tare da shafa inda Mama ta maresa yace kije kija mana k0 wani ya hanaki, amma shawara daya zan baki ni duk wanda ya tisoni gaba wallahi lalacewa yakeyi dan haka ki rufe idanuwanki daga kan Mansur idan ba haka ba kema to dinki 
Cikin kunar zuciya Mama tace nima zan lalace kenan ko? Mansur yace idan kin zabi hakan,juyawa yayi ya kwanta bai sake magana ba, ita dai Mama har a ranta tana san Mansur amma bakin halinsa yasa take ma marinsa, yanzu ko ta yanke hukunci daina marinsa dan taga tana marinsa yana wani bubbudawa tunaninta karta maresa wata rana ya rama, shi kuma har abada babu wannan tsarin a zuciyarsa, abinda kawai yake damunsa 
daukar Bashir da akayi aka rabasu, Wanda suke kwana wuri daya su tashi, suci abinci tare duk inda Bashir zai tafi dashi yake tafiya, har wanki Bashir shine yake wanke kayan Mansur duk abinda Mansur yake so Bashir ke masa bai san babu ba, baya nema ya rasa, ko laifi Mansur yayi idan Baba yana masa fada Bashir kuka yakeyi baya so yaga dan uwansa a cikin damuwa, komai nasa na Mansur ne, tou shi ganin Bashir ya tafi ne yakejin bakin ciki an rabasu, wani zuwa da Bashir din yayi Mansur yana masa magana daga baiji ba yana magana da mutane shine yace wai ya fara samun kudi harya farajin warinsa, Saida Mama ta karayiwa Mansur dundun ta kara dukansa sosai sannan ta fita daga dakin, dan gajeran tsaki Mansur yayi tare da gyara lullubinsa yaci gaba da bacci. Gwaggo kuwa hakuri ta kara bawa Mama sannan itama ta wuce dakinta. 
Mama kuwa tana zuwa dakinta Bashir ta kira ta fada masa abinda Mansur yayi, hakuri yayi ta bawa Mama tare da fada mata tayi hakuri shi Mansur yaro ne, Bashir ya kara da cewa zaizo cikin satin nan in Allah yadda, maganar Bashir tasa Mama ta samu sauki a 
zuciyarta har tayi bacci. 
Da safe kuwa yana tashi wanka yayi, ya dauko wata arniyar shadda mai tsada da burgewa wanda akayi mata aiki na hankali da natsuwa har daukar ido takeyi saboda kyawunta da sabintar ta, da dai alama yau ne ranar farko daya fara sakata ajikinsa, 
Cikin mulki da isa ya fito sai zabga kamshi yakeyi mai daukar hankali, dakin gwaggo ya fara shiga suka gaisa tare da kara maimata abinda ya faru jiya, cikin natsuwa yacewa gwaggo wallahi ba komai bane kawai hassada ce shi mai gida yake nunamin, cikin mamaki ta kalleshi tace Baban naku ne yake maka hassada Mansur? Mansur yace sosai ma ashe baki da labari? Aini tuni na ganosa kuma nasan zaman da nake dashi, zama yayi saman kujera sannan yaci gaba da cewa gwaggo in banda hassada munafirci da madagwarci miye dalilin ya dauke Yaya ni ya barni anan sai kace wani kare dai. 
Yanzun yaushe rabon da kikaga yamin dinki? Tou k0 wannan kayan najikina nina siya abuna dakaina, tunda ya mayar dani abokin takararsa mu zuba dani dashi nidai nasan shegen makonsa bai bari yayi ma kansa komai, shi baici ba iyalinsa basu ci ba, komai dai a samu kudi a boye sai kace ramin kabari da gawa, kinga ranar duk da Allah ya kashe sa a ranar duk ma”aikatan gidan nan zasuyi da nasani suji dama nine Mai gidansu tun farko, 
wasan langarya fara daga yau, kedai ki barni na isko sa kofar gida labari zaizo a kunnenki gwaggo ta. “ 
Kallonsa Maryam tayi tare da girgiza kanta, ba tare daya kalleta ba yace ai bayan Baba nasan ina da makiya sosai a gidan nan, da wata munafika gata can bayanki, wallahi banda nakejin kunyarki gwaggo waccan shegiyardiyar dasai tabargidan nan, cikin rarrashin Gwaggo tace Allah ya baka hakuri, Mansur yace ai bawai naji wani iri bane kawai dai gaya miki 
nayi dan nasan tana Iya daddaKa guba wata rana ta bani lnCi In mutu, Gwaggo tace wane ita, ita din banza, Mansur yace banzar gaske kuwa haushinta nakeji yanzu dai taci arzikinki amma Allah ya hadamu a tsakar gida zata gane idan ni abokin wasanta ne ana dukana shegiya tanamin dariya, yana kaiwa nan yayi waje, 
Tunda ya fito ma”aikatan gidansu suka fara zubewa dan gaisuwa, baije dakin Mama ba dan gaba yakeyi da ita saboda ta masa fada jiya, kofar gida ya fita, Baba yana tsaye a waje irin dai haka “yan maula sun taru sosai kowa yana jiran a dan bashi wani abu,shi kuma Baba yana magana da wani mutum ne, tunda Mansurya fito “yan maula suka fara, arrrrrrrrr ga Mai gida uban masu gida, kabeji mai riga da yawa ka saka dubu ka bada dubu, dogo fari angon Halimatu da yardar Allah, mai kyautar kudin kamar yana sadakar kasa, mashekiya in bata tari iska ba sai kaikayi ya rufeta ga Mai gidan masu gida, 
Dariya “yan duniya Mansir yayi kankankannnnn ………. da wutsiyar idonsa ya kalli Baba dake kallonsa sannan ya kalli marokan yace kudai gaya masa Mai gida baya da tsara, murmushi Baba yayi dan lallai ya gane babu abinda ke damun Mansur sai yarinta, banda yarinta waye zaiyi takara da ubansa har yana masa haibaici, 
Wani ne yace Mai gida nidai kam ina kamun kayanjikinka, Mansur yace na baka, wani yace agogo wani takalmi komai na jikinsa saida aka kamesu, yace ku jirani ina zuwa, gida ya koma ya ciro kayan ya sake sanyo wata matsiyarjadda sannan ya fito ya basu kayan, kirari sukaci gaba dayi lumshe idanuwa Mansur ya karayi cikin jin dadin kirarin yace kaima na baka najikina, duk Baba yana tsaye yana kallon ikon Allah,
Baba yana tsaye saida Mansurya bada kaya kala biyar, komawa yayi gida bayan ya gama rarrabar kayan, da Gwaggo suka hadu tana fitowa daga kicin tace tou ya naga kuma ka cire gayan naka? Wata munafikar dariya yayi sannan yace duk na bada shaggu Gwaggo, ai banga amfani ajiye sitira ba ka saka a ganka kawai ka bayar shine cikar ariziki, a daidai lokacin da Baba zai wuce, Mansurya daga murya yaci gaba da cewa amma sai kiga wasu sun kama kaya suna ta tattalinsu suna adawa kamar kudi a hannun makaho, kinsan Allah gwaggo kawai wani mutun dana sani tun ina yaro yake saka wasu kaya har yanzun bai bada kwancensu ba. Da Baba yake. 
Murmushi Baba yayi bai kalli inda suke ba ya wuce abunsa, saida ya kari iskancinsa a 
wurin sannan ya shige gwaggo tabi’ bayansa da kallo tare da masa addu”ar shiriya, 
Bayan sati biyu kuwa wani babban tashin hankali gagarumi Mansur yaje yajajjagowa kansa, talauci da warin babu ya damesu dama a gidansu su Mansur ake samun kudi to yabi duk hanyar da yasan za’a samu ba’a samu ba, sai abokinsu yace su bari yaje ya dauko “yan kunnen Mamarsu, dan karamin a kwatine take ajiyar zinari duk wani’ abu daya shafi gold a ciki take adanawa, dan haka yaje ya dauko musu sukaje suka siyar suka raba kudin kowa miliyan daya da kwata, Kowa yaje yayi hidimarsa, bayan sun gama bishasharsu da kudin shi dayan abokin yana komawa gida ya isko Mamarsa sai suma takeyi ana shafa mata ruwa, ganin tashin hankalin da mahaifiyarsa take ciki yasashi fada shine ya dauka kuma ya fadi yanda sukayi da kudin. 
Shi kuwa Mansur yana gida damuwa ta damesa dan duk lokacin daya ga Bashirji yakeyi kamar ya zare masa rai, kiri kiri ya kulle dakin yace bai kwana tare dashi, dole wani dakin Bashiryaje ya kwanta, cikin dare suka ji jiniyar motocin “yan sanda, suma dole a kofar gida suka tsaya dan ganin gidan Ogane za’a kamo mai laifi. Shi kuwa Baba tunda yaji haka ya fito dan ganin meye ya kawo “yan sanda kofar gidansa da wannan lokaci, Baba na fita suka fara bashi girma, bayan sun gama ne ya tambayesu yanda akayi, babu munafirci suka bude masa gaskiya, 
Baba yace ku jirani ina zuwa, da hayagaga ya shiga cikin gidan wannan ihu yasa duk wanda yake gidan mai bacci ko wanda yake ido biyu saida ya fito tsakar gida har Mansur ba”a bari ba. Cikin tashin hankali yace Umma Suleim kin haifomin barawo, cikin damuwa Mama tace wane barawo kuma? Nuna Mansur yayi sannan yace “yan kunne sukaje suka sata a gidan mutane shege dan iska barawo, ai tun kafin Baba ya rufe baki tuni Mama ta sulale, ta yanke jiki ta fadi kasa feff, cikin tashin hankali Bashiryayi kanta kafin ya isa tuni takai kasa, da gudu ya isa yana cewa Mama ………… ‘ A hankali Bashir ya saketa tare da juyawa inda Mansir yake tsaye ya shakeshi yaci gaba da dukansa duka bana wasa ba na raba mutum da ransa, yana dukansa yana cewa wallahi idan Mama ta mutu na rantse da Allah saina kashe ka, tuni gwaggo ‘ta koma da gudu dakinta ta dauko ruwa tazo tana shafawa Mama, a hankali Mama ta bude idonta, jiri jiri ‘taga Mansur ya dauko wuka yayo kan Bashiryana cewa saina kasheka, wannan tashin hankali yasa Mama ta kara zukewa ta koma kasa sumamma, 
Wannan wane irin tashin hankali ne inji gwaggo, Bashir kuwa saidai ya shiru Mansur ya dannawa kasa shi, shi kuma Mansur sai ikirari yakeyi cewa wallahi nima saina kashe ka, banza dan iska, dakel Baba ya rabasu, amma Mansur yace wallahi shine ajalin Bashir, 
Bashir kuwa gyara zaman rigarsa yayi tare da cewa kayi addu”a Mama ta rayu dan wallahi ta mutu nine zan kashe ka, idan mutum yana mutuwa fiye daso daya saina zare 
ranka so babu adadi banza dan iska dakiki barawo, 
Cikin bacin rai Mansuryace kaine barawo banza ko an fada maka inajin tsoronka ne? ‘Dan gajeran tsaki Baba yayi sannan yaja Bashir suka fita tare, Bashir da kansa ya biya kudin sannan ya koma gida ba tare da an tafl da Mansur ba, inda Mansur din yake Bashir ya koma yana masa nasiha, dan gwaggo ta samu Mama ta farfado ita da Maryam sunkaita dakinta, Bashir nasiha da gaskiya yakewa Mansur amma sai Mansuryace na ramse da girman Allah duk ranar daka sakemin magana wallahi wallahi wallahi azim saina caka maka wuka a makoshi. 
Bashiryace bazan bari ba, nace Mansur! Mansur!! Mansur!!!, wukar dake hannun Mansur ya yanka ma Bashir wuya da ita, sharjini yace salama alaikum, da sauri Bashir ya rike wurin tare da cewa innalillahi wa”inna ilaihir raji”un, cikin karfin hali Bashir yayi murmushi tare da kallon dan uwansa yace Mansur,? Ni zaka kashe ? Me nayi maka ne? Cikin tashin hankali Baba ya isa wurin tare da kama Bashirya nufi mota dashi ba tare dasu Mama sun sani ba. 
Mansur kuwa dakinsa ya nufa cikin bacin rai, yana gunguni, komai baiji ba a ransa ko nadamar abinda yayi duk tashin hankalin da dan uwansa ya shiga baisa yaji saduda a rayuwarsa ba. 
Lokacin da suka isa asibiti tuni Bashirya galabaita, ba’a wani sha wahala ba aka amsheshi dan Baba sananne ne, Baba yana nan aka shiga dashi dakin aiki har aka fito dashi, banda ajiyar zuciya babu abinda Baba keyi, godiya yake ma Allah daba ajijiya Mansur ya yanki Bashir ba da tuni ya mutu. 
Gado aka bawa Bashir satin su daya a asibiti aka sallamesu, har aka sallmesu Baba bai fadawa su Mama abinda ya faru ba, ranar da suka dawo gida Bashir yaga Mansur yana wucewa kansa a sama sai fito yakeyi irin dai yanda “yan iska da suka raina iyayensu sukeyi, murmushi Bashiryayi tare da matsawa kusa da Mansur ya bashi hannu, Assalamu alaikum dan uwana. “ Wassalam makiyi ya akayi ne? Murmushin karfin hali Bashiryayi da gefen bakinsa sannan yace nine makiyinka? Mansuryace sosai ma kuwa kuma ina so ka sani daga yau don Allah ka daina shiga harkata idan kuwa ba haka zaka gane, 
Tun daga wannan ranar Mansurya dainawa Bashir magana, amma haduwa goma sai Bashir yacewa Mansur barka da hutawa dan uwana, baya amsawa kuma Bashir bai damu da rashin maganar ba, yana dai masa magana ne kawai saboda shine babba. 
Shirye shiryen bikin Bashir aka farayi dashi da Hauwa”u, dan Baba yace ya bari yayi aure ya tafi da matarsa haka zaifi masa dadi, ai shima Mansurya daga hankali duk bala”i sai 
anyi masa aure bai ajiye ba kuma bai bawa kowa ajiya ba amma aure yakeso ko ta yaya,
Baba yace bazai masa aure ba, amma Bashiryace ba komai shi zai masa aure, Mama bata so haka ba kwata kwata amma Bashir yace kada ta damu kawai ta barshi kila ma idan 
aka masa auren zaiyi hankali, 
Shirye shirye biki aka farayi amma Baba yace wallahi Mansur bazai auri Halimatu ba yarinya karuwa “yar tasha, Baba yace wallahi Maryam zai aura masa tunda bada kudinsa zaiyi auren ba, Mansuryace ayimin gori dan takamar za”amin aure, Baba yace anyi maka ka bari idan ka samu naka kudinka saika auro duk wanda kake so, 
Mansur yace to wallahi idan ka hadani aure da waccan tsinaniyar yarinyar nice ajalinta, Baba yace ka kasheta ina nan ina jiranka, itama Maryam idan hankalinta yayi dubu ya tashi jin za”a hada aurenta da Mansur, ta samu Gwaggo ta fada mata dama dai Bashir ne ita tana sansa, 
Kwantar mata da hankali Gwaggo tayi tare da nuna mata shima Mansur zasu zauna lafiya, bata da yanda zatayi dole ta hakura, hidimar biki akeyi ta mutunci Bashir ya kashe kudi na tashin hankali da bada mamaki, lefe biyu yayi dana Maryam dana Hauwa”u kuma komai iri daya yayi bai banbanta ba, Katafaren gida Baba ya basu yace duka matansu anan zasu zauna, haka akasha shagalin biki aka kai amare dakinsu. Hankalin Mama kuwa a tashe yake dan bataji dadin hada Bashir da Mansur gida daya ba tasan halin Mansur kwata kwata baiyi ba, amma shi Baba yayi haka dan ko matansu zasu daidaita tsakaninsu su zauna lafiya. Hmm wannan hadin baiba domin Baba yayi dan gyara ashe batawa yayi bai sani ba, 
Duk abinda za”a bukata Bashirya ajiyesa a gidan nan, da daddare kuwa Bashir daya shigo saida ya biya ta dakin Mansur yayi masa saida safe, bai amsa ba haka Maryam wanda takejin tsoron Mansur kamar ranta zai fita saboda tsoro, ‘ Cikin damuwa ya nufi dakinsa, Hauwa”u ta gansa cikin damuwa dan haka ta tambayesa me yake faruwa? Saida ya saki dan gajeran tsaki sannan ya bata labari yace banajin dadin abinda Mansur yakeyi wallahi, ita dama haushin Mansur takeji dan haka ta karkace ta gyara zama tare da fara shiryo makirincinta dan bata so su zauma gida daya da Mansir. Sannan ta fara cewa. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *