TAGWAYE
CHAPTER9
Rigijip! Tasauke a jikin Mahaifinta tamkar daga sama tafad’o. Daddy dake tseye tareda Ma’inah suna tattaunawa baisan hawaba bare sauka Jin Maisha yayi kurun tasauke ajikinsa, duk tabi tayimasa rauni dashike daman jikin nasa ba ‘karfine dashi sosai ba. “I’m now a millionaire daddy“ tafada tana wani washe baki da Farinciki. “Ohh wow congratulations my dear” Daddy ya furta dakyar jikinsa babu ‘karfi.
Hakan yasa Ma’inah tagane saukar da Maisha tayi ajikinsa tamasa rauni, Batareda ta tankamata ba, rike hannun Mahaifin nata tayi tanacewa Daddy ya’kamata mukoma gida idanunka sun nuna alaman rashin lafiya atattare da Kai…
Ai kuwa bata karasa furucintaba Maisha tashareta da wata dan banzan Mari wacce hausawa suke ‘kira “Yar Gabadaya”. “Banza Masu mahaifi se kiji’ka shi ki sha tunda ke kadei ce ya mallaka munafukan Allah da Annabi… “Ma’isha kinfi kowa sanin banson wannan halin naki dakike nunawa Kuma a gaban Daddy, kinfi kowa sanin rashin lafiyarda Daddy keyi, hawanjini gareshi…. Dasauri ta katseta “Tohh sannu Uwata, Ma’inah Sarkin hankalin duk duniya.
Duk wannan hayaniyan dasuke Daddy bai tankamusuba tsayawa yayi shiru tamkar baya wajen, Se yanzu da Maisha tagama zagegen datake tarike hannunsa tanacewa “Daddy
muje in nuna maka sabon ofishi na ta Manager, CEO Zaid ya nadani manager mai kulada
Abuja housing interior Decorations. Juyowa tayi, tabugawa Ma’inah harara “Rabuda wannan Yar farar kafan Mrs Right. Babu Inda zanje. Ya kifto hannunsa ‘Na gaji dawannan rashin jituwar taku inaga lokaci yayi daya kamata ku kasheni ku huta I’m tired Nagaji da wannan duniyar gaba daya. Da wannan maganar yayi waje, ‘kansa na bala’in bugawa jikinsa kuwa wani sanyi sanyi yakeji tamkar barin duniyar gaba d’aya zayyi alokacin. Jiri ne ya kwasoshi inda yasauke ‘kasa flat yakwanta tamkar matacce.
Ambatan sunansa sukayi alokaci d’aya “Dadddddy…. lnda aguje suka ‘karaso lnda yake bansan katafi kabarni, Kai kadei neh mai Sona anan garin karka tafi kabarni Daddy l really need you…
Why I’m l feeling some how, why I’m i stressed? Zaid ya tambayi ‘kansa “There must be something wrong” yafada yana kallon abokinsa Asad dake zaune shiru shima Yana bin
Zaid da kallo domin yafl kowa sanin abokin nasa “You are always stressed so inaji bakomai wannan yanayin kane akullum there is no need to worry CEO. Yafad’a yayinda yake kurban coffee wanda
yadade ahannunsa. “Come on Asad trust me I’m really feeling some how, kodei Umma ce take aikata wani gagarumar laifi kuma achan?”. Yafada jikinsa a sanyaye. “
Mikewa Asad yayi “Zaid abar wannan maganarya isa haka, ya’kamata mutafi gida because you are not okay. Dawannan maganar yafara tattara takardunsa dake zube asaman teburin duk yashiryasu cikin jaka guda sannan yamike Kai tseye yarike hannunsa tareda cewa; Come on Bro let go you need to rest.
Jinjina Kai Zaid yayi Sannan yamike yana ‘kokarin rike hawayen dasuka taro cikin ldanunsa amma ya’kasa, Kai tseye yabarsu suna zuba. “You need to calm down first; Asad yashare masa hawaye sannan yazaro Tissue yaba’sa
ahannu “Umma tana gidan_yari, believe me babu wani abunda zata ‘karayi dayardan Allah.
“Excuse me sir and sorry for the interruption CEO akwai matsala…. Seketeri ya bankado ‘kofa kai tseye yashigo yana nunfashi sama sama.
Asad ne yamike yana tambayarsa “Meye yafaru? please go away kuje wajen Assistant na tabbata koma menene he can handle it CEO yana bukatan hutu just get out please. “Asad : Zaid yakatseshi inda yajuya yana tambayan Seketeri abundake faruwa.
“Akwai matsala CEO, Someone just collapsed, yanzu ambulance yazu aka tafi dashi Asibitinmu na nan cikin company. ZMZ Hospital.
“Waye? Kuma meye ya tsameshi anan cikin confanin na? Zaid ya fada cikin rudani. “Kodei attacking dinsa akayi; Asad shima yafada cikin daurin Kai. “No Sir is not an attack, Mahaifin sabbin yan aikin nan namu ne, New AHID Maganer dakuma Masinjarka. Ma’inah Sambo Maidugu kenan? Zaid ya tabe baki. Look Asad I need to be there please take care of everything here Bye.
Babbar Jacket dinsa yad’auko lnda yafito aguje yagana sauka ‘kasa. Emma Samson, Li Yong, Umar Sarkaki, dakuma Gu jun pyo (Masu kula dashi) sune suka biyosa abaya har tseda yakai filin motocinsa anan suka bude masa kofa yashige suma suka shige ta’su abar hawan. Minti hamsin ce takaisu wajen Inda suka mara Masa baya ya fio yana taflya ahankali ahankali.
Zzai… Zzzzad.. Zaid Muhammad Zabir the mo…. mmos… most beautiful creature in the world ppp… Pl… plea… pleasese come to me I love you so much;
Sake kurban wine dake hannunta tayi yayinda ta riskeshi gam ta rungumeshi tana hawaye “Zaid Please help my father, Daddy is my hero idan ya rasu ina zan samo kudin dazan ringa kashewa ina zuwa chasu he is my image Zaid please help me. Dasauri yacire hannayenta ajikinsa yana kokarin chanza hanya “Ma’inah stay away from me. Yafad’a ahankali kamar yedda yasaba. Li Yong ne yashige gabanta yana magana da yaren Chinese wanda Maisha ta’kasa gane abunda yake nufi. Mayar masa Zaid yayi shima dayaren sannan suka fara tafiya.
Zaid I love you please come back. Ma’isha ta’kara shige gabansu abige, tana kad’a idanu tana kallon sama. Gu jun pyo… Yes Sir, ya amsa Cikin ladabi da biyayya. Take care of her b ….. Bai ‘karasa furucinsaba Ma’inah ta’karaso wajen tana kuka yayinda tanufo wajensa aguje.
Ma’inah… Zaid ya ambaci sunanta cikin sanyin murya lnda yajuyo ya’kara ganin Maisha dake zaune a ‘kasa tana fama da kwalba. Hawaye ne yaji sun cika masa ido yana tuna irin wulakancinda yama Ma’inah acikin bainin jama‘a.
Ma’inah tana zuwa Inda yake yadaga hannayensa duka biyu yana kokarin rungumarta batareda sanin cewa gun mahaifiyar ta take zuwaba. Saida tawuceshi sannan yajuye yaga mahaifiyarsu abayansa itama tana hawaye. Ma’inah na riskanta tayi banza da ita tamkar fada sukeyi inda tawuce gun Maisha aguje tana kokarin kamo’ta domin amai da ita gida. Dakyar tasamu tajanyota “Ma’isha kitashi kikoma gida you are really drunk my dear har yanzu daman Baki dena wannan halin naki na shaye shaye ba”… Ahaka ta janyota har tseda suka kai wajen motoci suka sata aciki, Driver yajasu kai tseye suka koma gida. tun Bai ‘karasa cikin d’akinba yaduba mara lafiyan juyowa yayi afusace yafice babu wanda ya sallama. Mota aka bude masa, Ransa abace yashige abaya yazauna yawani sha zamansa ta cross leg wacce yasaba.
Keyarsa yadafa yanata lissafai iri iri a zuciyarsa “So Maisha ce tazo gidana jiya and she pretend to be her twin sister Ma’inah, This girl is really an evil, devil self, na tsani mata,l really hate girls because they are all thesame.
Yana wannan maganar yamike cikin bacin Rai da Bakin ciki “I don’t know why I’m always getting more reasons to hate girls gaskiya mata basuyiba, Na dawo Nigeria musamman domin nafara wata sabuwar rayuwa amma abun yacitura the memory of my past always come back to me, Na tsani Kai na Kuma na tsani rayuwata. Awannan lokacin hawaye ne suka fara gangarowa cikin kyakkyawar Idanunsa duka biyu suna zuba babu control yaso yarike feelings d’insa tun ranar dasuka dawo yake kokari domin yamance abubuwnda sukafaru achan ‘kasarsu Amma da dukkan alamu babu yedda za’ayi su guce gabad’aya a kwakwalwarsa. Cikin Wannan yanayin yake har tseda suka kai office sannan ne yayi kokari yagoge Idanunsa sannan suka ‘karaso. Shigowarsa masu aiki a awajen dik suka mike suna girmamashi saida yahauro sama sannan kowa yakoma Bakin aikinsa.
Yana haurowa CEO Villa bai tsaya ko inaba se ofishinsa, Takardu, Computer, files dasauran ababen dasuke kan teburinsa ya watso ‘kasa inda flawowi duk suka parpashe dama sauran glasses.
‘Karar datafito cikin ofishin ne yabige kunnuwan dikkan masu aiki asama bangaren Villa. Nan da nan sojoji, yan Sanda dama sauran ma’aikata suka taho alokaci d’aya “Boss lafiya meye yafaru anan? CEO What’s wrong Boss? Kowa da ta’sa tambayan suna mamakin abunda ya tsameshi bayan dik yan Sanda na zagaye da ofishin nasa. “You people should please and please get out of my side before the count of two. 1… Jijiyoyin wuyansa duk sun bayyana yayinda ya’kara cewa; I don’t need you baku tsinanamin da
komai ba yan sandan nan wajen duk na tsallameku you are fired ko kad’an banajin dadi you can’t even make me happy you people are all useless just get out of here Yana magana ne iya karfinsa wanda idan ba ganinsa kayi da idanun kaba zaka musa cewa ba Zaid Muhammad Zabir wanda muryarsa take ciki ciki tamkar mace yake wannan irin matsifar ba.
lnnalillahi wa inna ileihi rajiun’ Asad yana shiga abunda yafara fad’a kenan domin cikekken abokin Zaid ne tun suna ‘kanana ya’san abunda ke damunsa kuma dukda shi kansa ba ragemasa Zaid keyi idan yana cikin bacin rai ba, Sedei ya’san hanya mafi sauki dayakebi ya kwantar masa da hankali: “Kowa yakoma bakin aikinsa I will handle him‘. Yafada cikin sanyin murya.
Babu wanda ya’kara wata magana, fitowa sukayi dikkansu daya bayan daya kowa yakoma aiki.
Bayan duk sun fice Zaid yad’au wata kwalbar flower yana kokarin jefowa,
“Zaid karka yarda kajefo flower nan just keep it…
“Asad will u lecture me? go ahead why did u stop? kai ka sayo shin kodei da kud’inka muka hada aka gina confanin, Answer me. Zaid ya mayar masa da martani Kai tseye.
Jakarsa Asad ya tattaro batareda yace komaiba rike hannunsa kawai yayi yafara tafiya. Zaid shima bai tan‘kamasa ba binsa yake abaya har tseda suka kai filin motoci sannan yakifto hannunsa “A’sad wai mahaukaci neni? Girgiza kai Asad yayi dasuari yace” A’a lafiyarka kalau Zaid. Then why are you treating me like this A’sad. “Sorry Zaid I’m just trying to protect you kafi kowa sani banson ganinka ahaka ya’kamata ka chanza Zaid you really have to start a new life here: Ya’karasa kalmar ne cikin mota lnda yazauna yanacewa; Zaid please kayi hakuri mutafi gida gobe ka dawo wajen aikin naka. “
Babu abunda yafad’a, shigewa yayi kurun yazauna taredashi abaya sannan driver yafara tuki.
Alhaji kai kakejanyowa kanka wannan ciwon hawan jinin dake daminka, inbanda kai da abunka meye yasa kake d’aurawa kanka damuwar dabata shafekaba? Ma’isha da Ma’inah yara ne ‘kanana kuma haryanzu da kuruciyarsu ya’kamata kayimusu uzuri please Alhaji you know we all need u because you are the head of this family.
Jinjina Kai Daddy yayi taredacewa “Bakomai Safeenah akwai matakin dazan d’auka daganan kuma Insha Allahu Maisha bazata sake aikata wani laifi makamancin wannan ba.
Haba Alhaji kadena sa damuwa aranka, yanzu kadawo gida kuma daga asibiti ka kwantar da hankalinka kadena tuna batun Maisha ko Ma‘inah just concentrate on getting better,
and you need to be strong Alhaji. Tabe Baki tayi ahankali tace; Kiriniya da Kisisina tamkar sabuwar kishiya…
Magana kikeyi? A’a cewa nayi Allah yabaka lafiya mijina.
Sallamar Ma’inah suka amsa alokaci d’aya, Wajen Daddy tanufo Kai tseye ta rungumeshi “Daddy you need to get better please daman tun farko nafad’a maka karka biyoni wajen aiki amma tsausayi ta aikata halinsa. Yata ki gafartamin dukkan laifukan danake aikarta miki kinji’ Ma’inah please trust me l love you so much wannan sauyawar da nayi wallahi da dalili Wanda na tabbata zaki gani anan gaba…
Bata ‘karasa furucintaba yayinda Daddy yadakatar da ita inda yamike dakyar yarike hannun Ma’inah tareda cewa; Safeenah I’m sorry is too late to cry nafada miki hukuncinda nayi niyar dauka tin jiya Sabida haka pretendings d’inki na banza ba’zasu hanani aikata abinda nayi niyar yi ba… Bude kofan dakin yayi a fusace yajanyo Ma’inah suka fice.
“How dear you Alhaji, Momy tabiyo su “Alhaji wallahi bazan taba bari ka rabani da Yataba, Alhaji magana nakeyi ko bakajina ne? Bai tankamata ba, haka ya janyo Ma’inah suka fita. Daga nan Momy ta zube a kasa se kuka take tana mamakin sauyawar da mijinta yayi, kwata kwata ya chanza daga Alhaji Sambon ta yakoma wani daban “Saminu is the only solution to this problem dole shi zan ‘kira yadedei tamu kokuwa nakai ‘karansa gun waliyinshi “Momcy lafiyarki kuwa dawa kike magana? naga babu kowa anan. Ma’isha tashige, cikin yanayin ko inkula tawuce kitchen nan tad’au kayan mar_mari tadawo parlour tazauna tana Sha abinta inda takebin wakar datake saurara awayarta.
“Ma’isha, Shikenan kin rabu da Yar uwarki ma’inah har abada Mahaifinki yadauketa yakaita wani wuri wanda acewarsa ko rundunar yan sandan duniya muka biya anemeta baza’a taba ganotaba sedei kawai ….. Haba momcy. Ma’ishah ta katseta “Meye natada hankali in taso jirgi Yakaita bangon duniya ni bata shafeniba please don’t ruin my day. Dawannan maganar tamike inda ta dau wayarta tana bin wakar Bank Alert dake ta’sowa cikin sifikar wayarta.
Tuki Daddy yake dakansa har tseda suka kai wata babbar mansion (Muhammad Zabir mansion) rubuce asaman ginin, wanda take haska dikkan garin Abuja. Tsahon benen gidan yasa ko a ina kake agarin Abuja zaka iya hangansa, gini ne na zamani Wacce tafi dukkan gidajen dake amsa suna anan kasar domin tsarinta ta ‘kasar China ce, tsarin gidajen
Beijing. ’ Sake Baki Ma’inah tayi tana bin gidan da kallo tamkar ba’kauyiya, tsarin ginin ne yamatukar tsoratata jitayi kamar gidan aljannu suka shige. Tana biyedashi abaya a razane tana mamakin inda suke kokarin zuwa domin kusan awa guda suka shafa batareda sun ‘karaso ciki inda mutane suke ba. Wata babbar parlour suka ‘karaso inda Kai tseye Daddy yazauna yana ‘kokarin ‘kiran wani awayarsa. Daddy meye mukeyi anan? Kuma meyasa aka tattaro dikkan kayayyakina aka dawo dasu nan gidan?
Ta tambayesa ne atsorace yayinda ta’kara damke hannunsa tanacewa; Daddy ba’nasan zama anan gidan nikadei zan koma gida mucigaba da zama Ni da Kai da Mommy.
Budan Bakinsa cewa yayi ” Daga yau Ma’inah kin dawo nan gidan dazama domin na tabbata zakiji dadin rayuwarki anan fiyeda chan gidana.
Uncle itace Yar taka? Zaid yashigo kai tseye tareda wata yar yarinya mai kimanin shekara biyu zuwa Uku.
Innalillahi wa inna ileihi rajiun’… Wuf!!! Ma’inah tamike cikin tsananin mamaki da rudani ta hadiye miyau, nunfashinta na kokarin tsinkewa yayinda take tambayan Mahaifinta “Daddy a ina kasan shi? Zaid Muhammad Zabir shi ne Ogan mu a office. He is a ghost Daddy I can’t stay here…… Shashu Shaid who is she? Yarinyar tanuno Ma’inah tana tambayan Zaid dake tsaye yawani tabe baki tareda girgiza kai “Look Muna i don’t know her either, but this is my uncle Sambo Maidugu. Ya nuno Daddy dake murmushi yana binsu da kallo.