HEEDAYA CHAPTER 10 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 10 BY By Khaleesat Haiydar

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Washegari karfe goma saura na safe Mumy ta gama shiryawa xata fita office, Tana duban Karime a parlonta tace 

“Toh ni xan wuce aiki yanxu, sai ki saka ido sosai ki kula da duk abinda nace maki, karfe sha biyu na yi ki daura 

maku girkin abinda xa ku ci dai dai cikin ku, ita kuma Heedayah xuwa nan da sha daya abinda ki ka ga na hada mata 

jiya sai ki hada mata ki xuba Madara amma ban da sugar” Karime tace “Toh in sha Allahu Hajiya” Mami ta dau 

jakarta ta nufi kofa tace “Sai na dawo” Karime tace “A dawo lafiya” Har Mami ta fita ta juyo tace “Kar ki bari ta bar 

parlon nan komai xakiyi kiyi mata a nan parlon, bana son ku fito” Karime tace “Toh in sha Allahu Hajiya” Mami ta 

kulle kofarta ta wuce, A main parlor suka hadu da Mumy tana ma mai aikinta magana cikin tsawa, matar da baxata 

wuce Karime ba sai rawa jikinta yake tana bata hakuri, Mumy na ganin Mami ta dakata da masifar da take, idon da 

suka hada yasa Mami tace “Mun tashi lfya?” Mumy tayi murmushi tace “Lafiya lau wllh, ya kwanan Baby” Mami 

tace “Alhmdllh, ya na su Rabi’ah” Mumy tace “Lfya lau, sun ma wuce makaranta ai” Mami tace “Toh maa sha Allah, 

na fita…” Mumy tace “Toh Allah ya kiyaye hanya” Mami ta amsa da Ameen sannan ta fita parlon, Mumy ta bi ta da 

kallo har ta rufe kofa, ta wani ta6e baki ta kalli Sajida mai aikinta cike da masifa tace “Kin tashi a gabana ko sai na 

gaura maki Mari, ‘yan aiki ko ‘yan wahala, wllh bana son in sake tuna maki sharan dakin yarana idan ba haka ba ni 

ynda ake canxa sutura haka nake canxa ku don ma ki ji” Mai aikin ta mike da sauri ta tafi dakinsu Rabi’ah, Shuraim 

dake xaune dining ya ajiye cup din hannunsa ya mike ya dawo parlon, Mumy tace “Amma dai yau baxa ka fita aiki 

ba….” Yace “Sai da yamma….” Mumy tace “Na ji ma Baffan naku yyi tafiya ko?” Shuraim yace “Ehh yana Abuja” 

Mumy ta ta6e baki, Shuraim yyi kasa da kai yace “Mumy ki dinga hakuri da mutane don Allah, barin wa ennan 

bayin Allah, they don’t deserve the way u are treating them, they never wished for their selves to be maid, and don’t 

forget no condition is permanent, su Rabi’ah yara ne da baxa su iya gyara dakinsu ba idan sun tashi? Ba fa aikin da 

suke yi a gidan just gyaran dakin ma sai an masu?? This is….” Dakatar da shi tayi cikin tsawa tace “Rufe min baki 

malam, ni xaka taso kayi ma fada?” Yace “Ni ba fada na maki ba, I am telling you what I think is right” Ta kuma yi 

masa wani tsawan tace “Baka isa ka gaya min what to do and what not to do ba, out of my sight now…. Duk 

walakanci da cin fuskan da ubanka ke min a gidan nan ka ta6a tunkararsa ka gaya masa what is right? Sai ni 

marainiyar wayon ka, to baka isa ba ne….” Shuraim ya shafa kansa bai dai ce komai ba yyi wucewarsa dakinsa, ta bi 

sa da wani irin harara tace “Wawa kawai….” Karfe sha daya da rabi Karime ta fito hada ma Heedayah cornflakes, 

Mumy ce xaune parlor da Hajiya Sadiya, Karime ta duka har kasa ta gaisheta, da fara’a Mumy tace “Lafiya lau 

Karima, ya aiki” Karime tace “Mun gode Allah” Mumy tace “Toh madalla” Karime ta gaida Hajiya Sadiya ita ma ta 

amsa sannan ta mike ta wuce kitchen, Hajiya Sadiya na kallon Mumy murya can kasa tace “Ita ce mai aikin” Mumy 

ta gyada mata kai, Hajiya Sadiya ta jinjina kai alamar gamsuwa, can sai ga Karime ta fito rike da cornflakes da ta 

hada, Mumy tace “Ga kwai can da na soya a kitchen ki dauka, na ci ya isheni gashi ba almajirai a nan” Karime tace 

“Toh Hajiya Nagode” xata koma kitchen din Mumy tace “Toh ajiye kofin cornflakes din kar ya xube, ta ajiye ta 

wuce kitchen din da sauri da sauri, Mumy ta kalli Hajiya Sadiya dake mata magana cikin rada, Mumy ta gyada mata 

kai kawai, Karime ta fito dauke da tulin kwai a plate, Mumy tace “Ki fito da ita mana ta sha cornflakes din a nan, 

gashi nn ma duk ya jike….” Karime ta d’an fara kame kame, tace “Hajiya dama Madam tace kar take fitowa ne, 

komai xa mu yi muyi a can ciki” Mumy dake saurarenta sosai tace “Ayyo, toh tunda ita ta kawo ki ba ni ba shkkn kai 

mata ciki, dama so nayi in d’an sa ki gyaran bangarena ne, shi sa nace ki fito da ita nan sbda a sa mata ido, amma 

dauka ki wuce xan yi da kai na, na aiki tawa mai aikin kasuwa ne dama shi yasa” Karime ta d’an risina tace “A’a ba 

haka bane Hajiya kiyi hakuri, d’an dai gyaran bangaren ki ai xan maki, bari in kawo ta nan din” Mumy tace “Aa kar 

uwar dakin ki ta ga kin karya mata doka kiyi laifi….” Karime tace “A’a da wuri ae xan yi in gama” daga hka ta wuce 

ciki, sai ga ta ta fito da Heedayah dake sanye da wando iya gwiwa da karamin riga an daure mata kalabanta waje 

daya, she look more of a half cast sbda irin haskenta, dai dai fitowar Shuraim waya kare kunnensa da ganinsa kasan 

fita xai yi, Karime ta ajiye ta nan gefen Mumy ta dauko cornflakes din ta sa mata a hannu tace “Toh gashi ki sha 

masaran naki ‘yar kyakkyawa” Shuraim dai sai kallonsu yake walking slowly, Heedayah ta laluba cokalin ta deba 

content din cup din ta kai baki, girgixa kai tayi ta fito da na bakinta saman tafin hannunta da sauri tana yamutsa karamin bakinta tace “Yyi soakkk…..” Mumy ta saci kallon Hajiya Sadiya ta dalilin hakan kuma ta hango Shuraim 

da ya tsaya don bata san ya fito ba duk da kamshin turaren sa da ya gauraye parlon, Karime na kallon Heedayah tace 

“Kika ce?” Heedayah na kara tofar da sauran na bakinta tace “Xai sa in yi amai, it’s soft” Mumy tayi murmushi tace

“Kai yaro ma dai, wai tana nufin ya jike, ki hado mata wani kawai” Karime tace “Au… toh…” Sannan ta dau cup din 

ta wuce kitchen da sauri, ba a wani dau lkci ba ta dawo da wani Cornflakes din a cup ta mika ma Heedayah, sannan 

ta kama hannunta ta juye na bakin ta da ke kai kan nata hannun, Heedayah ta fara shan cornflakes din, Karime ta tafi 

kitchen ta xubar da na hannunta ta dawo tana kallon Mumy da ladabi tace “Ina xa a gyara maki?” Mumy tace “Ki 

tafi sama xaki ga kofofi duk ki shiga ko wanne ki share ki goge” Karime ta risina tace “Toh Hajiya” daga haka ta 

wuce sama, Shuraim ya karasa dinning ya xauna, Mumy ta d’an kalli Inda yake, sai kuma ta juya tana kallonsa da 

kyau tace “Ba fita xaka yi ba?” Ba tare da ya kalleta ba yace “Ehh ina jiran Umar ne…” Mumy tace “Toh ba sai kaje 

can gidan nasu ka samesa ba” Shuraim yace “Yace in jirasa a nan….” Mumy tace “Toh ma yaushe ku ka fara fita da 

Umar?” Shi dai Shuraim bai ce komai ba, Mumy ta kalli Hajiya Sadiya tayi tagumi, Hajiya Sadiya tace “Ni da ka 

d’an taimaka Shuraim ka amso min MTN nan waje naga da wani me kiosk a layin…” Ya kalleta sannan yace “Toh 

bari in maki transfer kawai….” Hajiya Sadiya tace “Aa kar ka wani ba kanka wahala, ga kudin ka amso min” Yace 

“Gashi ina yi, na ma yi ynxu” Hajiya Sadiya bata sake ce masa komai ba, Mumy dai ya girgixa kafa take, Tasss 

Heedayah ta shanye cornflakes din cup din tace “I want to take water” Mumy ta d’an kalleta tace “Sai jira ta xo ta 

baki ai” Shuraim dai yana ta danna wayarsa, har Karime ta fito bayan kusan minti talatin, tace “Hajiya duk na gyara 

na goge” Ba tare da Mumy ta kalleta ba tace “Sannu” Karime ta daga Heedayah tace “Mu je ki kwanta lkcn baccin ki 

yyi” Heedayah tace “Xan sha ruwa” Karime ta ja ta har xuwa gun da fridge din dinning area yake, Heedayah ta taji 

ta taka abu me tudu, tsayawa tayi ta kara kai kafarta kan abun, Shuraim ya dauke idonsa daga kan screen din 

wayarsa yana kallonta, ta kara takasa, ta kuma takasa just wanting to know what she’s matching, ta kara cire kafarta 

ta kara mayarwa, Karime dai na kokarin dauko mata ruwa a fridge bata ma san me ake ba, Heedayah ta duka ta sa 

hannu tana lalubawa ta ji me take takawa, dagota yyi ya rike duk hannunta biyu ya bugesu da karfi, sannan ya ja 

kunnenta daya fuska daure yace “Dutse aka ce maki kike takawa??” Kara buge hannunta yyi ya ja kunnenta ta fashe 

da kuka sosai, Karime dai ta ja gefe bata ce komai ba, cikin kuka Heedayah tace “Sai na gaya ka da Mami, ni ba Ina 

ce baby na taka ba” Ya buge bakinta ya tura ta can kusa da Karime, duk wnn abun Mumy na kallonsu amma bata ce 

komai ba, Karime ta kama hannun Heedayah bayan ta dau ruwan tace “Kayi hakuri Yallabai, bata sani bane” Ya 

hade rai yace “Ku fita gabana ke da ita” Karime ta bar wajen da sauri tana rike da hannun Heedayah dake rusa kuka, 

Sai da ta xo wuce Inda Mumy take, Mumy tace “Sai hakuri, ita tsiwa shi kuma saurin hannu, haka nan dai” Karime 

ta wuce part din Mami rike da Heedayah dake Shessheka, Sai da suka shiga ciki Mumy tace “Ai kaga irinta, ba dai 

ana ganin ni bala’e’iya bace, to gashi tun ba a je ko ina ba bakin yarinya ya fara budewa tana ma mutane fitsara, ai 

kadan kayi mata na so ka yi mugun xaneta ne, rashin idon ya ci uwarsa, wllh idan yarinyar nan ta samu waje duk 

taka ku xata yi a gidan nan, kuma ubanku baxai ce komai ba tunda idonsa ya rufe…. Kai kuma ka xo ka xauna ma 

mutane a parlor ka hanasu sakata da can kana xaman parlon nan ne ko neman magana???” Shi dai bai ce mata komai 

ba, can ya mike ya nufi kofa yace “Sai an dawo” daga haka ya fita parlon, Hajiya Sadiya tace “Ai kuma ya lalata 

mana shirin yau sai mu tari gaba….” Mumy da ranta ya kara baci tace “Ni fa da ba don idon da kika dinga min ba 

gabansa ma xan iya duk abinda xan yi, to tsoronsa nake ji ko ubansa xai min?? Wllh ke ce kika hanani” Sadiya tace 

“A’a ke dai, ai komai yana son sirri a rayuwa, ni sai naga kamar da wata manufa ya xauna parlon har ya ki fita siyo 

min kati, ni kinga ko godiyar katin ban masa ba ma, ke dai kawai ki sa ma ranki salama ba dai duk ana tare a gidan 

ba, kuma da alaman jawo hankalin yar kauyen nan ba abu bne me wuya, da ganinta xata so abun duniya ne sosaiiii, 

bbu abun hanxari a wannan lamarin mu bi komai a sannu….” Mumy tace “To ko da wata manufan ya xauna akwai 

yanda xai yi da ni ne balle ma bbu wata manufa kawai coincidence ne, ke baki ga irin jibgar da yyi mata ba ynxu 

bbu ko shakka bbu, da kyar idan hannuwanta basu tashi ba, ai ko kadan bai bada goyon bayan kawota da ubansa yyi 

ba, kawai dai kin san sa da xurfin ciki ne, Amma har ynxu ina lura ba wani shiri suke yi da uban ba duk kan wnn

case din….” Hajiya Sadiya tace “To ke dai kiyi ga kyautata ma wnn yar kauyen, step by step xa mu yi ta abun mu 

bbu wanda xai xarge mu ko da kuwa alkali ne shi ba lauya ba, lkci daya farat din da kika so ayi da farko shi xai ja a 

xarge mu, amma kinga wnn bbu wanda xai kawo mu a rai” Mumy tace “Haka ne kam” Hajiya Sadiya ta mike tace 

“Yanxu dai xan wuce, gobe in sha Allahu xan xo da karfe sha daya” Mumy tace “Toh Allah ya kai mu din, ina nan 

ina jiran ki” Har bakin gate Mumy ta rakata sannan ta dawo tana jin ranta fari fat…. Karfe uku da ‘yan mintuna Mami 

ta dawo gidan, Bbu kowa parlor ta shiga part dinta, Karime na xaune saman kujera tana ta kallon tashar Hausa ga 

dambun nama cikin leda a hannunta tana ci cike da jin ddi, Heedayah kuma na rakube kasa a xaune ta kwantar da 

kanta saman kujera, Karime ta mike da sauri ganin Mami tana mata sannu da xuwa ta amshi ledan hannunta da 

handbag dinta, duk idon Mami na kan Heedayah da ta mike da sauri jin shigowar Mami, Mami tace “Karime ya xa 

ki bar ta ita kadai xaune a kasa??” Cikin rawar Karime tace “Aa, sauka tayi Hajiya ai tare muke, naga kamar ta fi son 

kasan ne” Mami tace “Meye wnn a hannunki??” Karime ta hadiye abu da kyar tana kara tuna warning din Mumy 

tace “Aa ba wani abu bane, dama naje wanke filet ne sai na hadu da Sajida Hajiyar da take ma aiki ta bata dambun nama shine ta debar min a leda, har nace ta bari amma ta tilasta ni na amsa, shine na shigo na tsam ma Hinda sai na 

ke cin sauran yanxu” Mami tace “Bbu wani alaka tsakanin ki da kowa na gidan nan banda gaisuwa, kin ji me nace?” 

Karime tace “In sha Allahu Hajiya, dama ni ba ruwana da kowa tun safe muke nan xaune, to naje wanke wanke 

shine….” Mami bata tsaya kara saurarenta ba ta kama hannun Heedayah suka wuce ciki, Karime gabanta sai faduwa 

yake, ta isa a hankali jikin kofar dakin ta makale don jin me Mami xata ce mata….. Har dai ta gama labenta bata ji 

komai ba, ta koma ta xauna, nan ko tsoro ne ya kara shiganta da ta tuna Mami fa na iya Kiran Sajida kila ta 

tambayeta, nan ko ko maganan kirki bai hada su da Sajida ba tun jiya da ta xo, Mami ta gama sauya kayanta ta 

xauna gefen gado tana kallon Heedayah da tayi shiru tace “Me ya same ki daughter?” A hankali Heedayah tace 

“Mami wnn Mutumin ya dokeni a hannuna kuma ya ja min kunne….” Hawaye ta fara tana Shessheka, Da mamaki 

Mami tace “A ina ya gan ki?” Cikin kuka sosai tace “Xan sha ruwa, shine ya ja min kunne na, yanxu kuma hannuna 

na min ciwo” Mami ta daga hannunta tana kallo snn ta fita dakin xuwa parlor, da sauri Karime ta mike tace “Hajiya 

a debo abinci ne?” Mami tace “Me ya fitar da Heedayah daga bangaren nan?” Karime da cikinta ya hautsine tace 

“A’a Hajiya bata fita ba, da yake in taji alamar xan fita yin wani abu sai tace sai ta bi ni baxata tsaya ita daya ba, ni 

kuma tausayi take bani sai in kasa fita in bar ta, wllh a tare nake yin komai da ita ki kirata ki tambayeta, wllh 

Hajiya….Mami tace “A kan wani dalili kuma aka doki hannunta kina wajen?” Karime dake xufa daga ciki tace “Cewa tayi 

xata sha ruwa muka tafi can inda firiji yake a parlor, to cikin rashin sani ta taka wani bawan Allah dake xaune wajen 

Ina tunanin shi ma d’an gidan ne, shine shi kuma rashin hakuri ya buge mata hannun ya xata da gangan tayi hakan 

kila” On a serious note Mami tace “Ki saurareni da kyau ki ji, ko da wasa bana son Heedayah ta sake fita parlon nan 

bana nan, ba komai yasa na dauke ki aiki ba sae don ki kula da ita don ni bbu abinda ya gagareni na aikin gida, 

shima daukan ki da nayi don bana xaman gida ne, Banda haka ni baxan dauke ki ba….” Hakuri Karime ta dinga ba 

Mami tana duke a kasa, Mami tace “Gargadi na karshe nake kara maki, ko nan da kofa kar ki sake fitar min da 

yarinya, idan kuma kinga baxa ki iya aikin ba ki sanar min tun wuri in san abun yi…..” Mami bata kuma saurarenta 

ba ta wuce daki, Karime ta sauke ajiyar xuciya ta xauna nan kasa a hankali har sannan gabanta na faduwa, a wannan 

marran wa xai daukeka aiki ya biya ka dubu ashirin, aikin ma raino kawai, sai dai can cikin garin Abuja kila, tunanin 

hakan yasa tayi tagumi tana tunanin ynda xata kara rike aikinta hannu bibbiyu… Mumy na kitchen da Sajida wajajen 

biyar da wani abu kasancewar ranan ta amshi girki tun xuwan Mami gidan, masifarta da ihu da take ma mai aikin 

har parlor, kmr jiran mistake take ta fara fada ba ji ba gani, bude kofar kitchen din aka yi ta juya tana kallon kofar 

fuska daure, Sudais ne tsaye sanye cikin kananun kaya hannunsa rike da leda sai makullin mota, ta saki fuska tace 

“A’a… kai kuma daga ina haka….” Yana murmurshi yace “Daga gida, Ina yini Mumy?” Tace “Lfya lau, ya su Hajiyar 

ka?” Yace “Suna gaishe ku” ta rike ha6a tace “Yaushe rabon ka xo gidan nan Sudais, anyaa….” Ya shafa gashin kansa 

still smiling yace “Mumy ae sbda aiki ne, ina su Rabi’ah?” Tace “Basu dawo islamiyya ba, nasan ynxu ma suna 

hanya…” Yace “Ohk…” Daga haka ya juya ya bar bakin kofar kitchen din, har xai xauna parlor sae kuma ya nufi part 

din da Kaka tace masa nan ne wajen Mami, Mumy ta ajiye wuka da albasan hannunta ta bi sa da kallo cike da 

mamaki har ya isa bakin kofar Mami ya kwankwasa a hankali, ba a dau lkci ba Karime ta bude kofar, da farko ca 

take Shuraim ne sbda resemblance din su, ta gaishesa da ladabi ta basa hanya, ya shiga parlon dake ta kamshi ta 

kulle kofar, Mumy dake ta lekowa har taga shigansa ta kai hannu ha6anta idonta ya kankance, sai kuma ta ajiye wuka da albasan hannunta ta fice kitchen din xuwa bangaren ta…. Sudais na kallon Karime da ta koma gefen da take 

xaune ta xauna yace “Babu kowa ne?” Tace “Aa suna ciki” daga haka ta mike ta nufi kofar dakin ta kwankwasa a 

hankali a d’an tsorace, Mami ta bude kofar tace “Ya aka yi?” Ta sunkuyar da kanta yace “A’a dama bako ki ka yi” 

Mami ta kalli parlon suka yi ido hudu da Sudais karasowa cikin parlon tayi ya gaisheta da ladabi, ta amsa da fara’a 

tana masa sannu da xuwa tace “Ya su Kaka da mutan gidan?” Yace “Suna gaishe ku” tace “Maa sha Allah muna 

amsawa, welcome” Mami tasa Karime ta kawo masa ruwa da drink a fridge, ta xauna kan kujera tana kallon film da 

ake a tv, Bayan few seconds tace “Kai ne kayi karatu Malaysia koh?” Yace “Eh Degree” tace “Maa sha Allah, 

Barrister yace min chemical engineering kayi right?” Yace “Ehh haka ne…” Tace “Good, it’s a nice course” yana 

shafa kansa a hankali yace “Heedayah bacci take?” Mami tace “A’a tana ciki” yace “Dama kaka ta bada sako a kawo 

mata ne” Mami ta mike tace “Allah sarki, tana ciki, let me get her” daga haka ta wuce dakin sai gata ta fito da 

Heedayah, har gabansa ta kai ta sannan ta dau wayarta da ke ring kan kujera tace “Give me few mins let me pick a 

call” yace “Alright Ma” daga haka ta wuce daki, Heedayah ta wara idanuwanta jin muryar sa tana tattaba Hannunsa 

cikin siririyar muryarta tace “Ka xo gidan mu yau koh?” Ya dafa forehead dinta yace “Nima ai gidan mu ne….” Ta 

kyalkyale da dariya tace “Aa, gidanku ai gidan wnn matar nan ne me fada” Sudais ya ja hancinta yace “Sunanta kaka, 

idan ta ji ki xata xane ki ba ruwana” Ta wara ido tace “Toh kaka…” Ya dau apple daya cikin apples din da ya kawo 

mata ya sa a hannunta, tana jujjuya apple din tace “Is it an Apple?” Yace “Yes” ta langwabar da kai tace “Me ya sa 

baka kawo min Chocolate ba, ni ina son shi” Yace “Wnn ya fi Chocolate dadi ai” yana fadin haka ya xaunar da ita 

gefensa ya ciro cincin kulle a leda ya bata a dayan hannunta yace “Kaka tace a kawo maki” Tana juya ledan tace 

“Meye shi?” Yace “Cinye apple din sae ki ci ki gani” Mami ta fito daga daki ta dawo parlon ta xauna, Mami na 

kallonsa tace “Ka fara aiki ne?” Yace “Na ci gaba da masters ne…” Mami tace “Maa sha Allah, a ina kake yi?” Yace 

“UK, na dawo yin wani abun ne yanxu” Mami tace “Anytime soon xaka koma kenan?” Yace “Ehh in sha Allah, nan 

da sati biyu” Mami ta gyada kai convinced, can tace “Shi kuma Shuraim fa?” Yar dariya yyi yace “Shi yana aiki… 

clinic din Baffanmu yake” Mami tace “Alright, Duk Allah ya bada sa’a” Yace “Ameen” Heedayah ta kamo hannunsa 

cike da damuwa tace “Are you travelling?” Yace “Yesss” ta 6ata fuska a hankali tace “Xaka tafi ka bar ni kenan?” 

Yace “Aa… Ai ba ddewa xan yi ba Heedayah” Mami tayi murmushi tace “Sai ya tafi da ke kawai Koh?” ta xaro ido 

tace “Ehh Mami plss, I like him with Yaya, ki ce ya tafi da ni” Mami tace “To xa ki bi sa” Daga karshe Mami ta bar 

masu parlon ta koma daki to answer more calls, Heedayah tace “Baka gaya min sunan ka ba…..” Ya shafa kansa yace 

“Ki ce min yayanki….” Ta kai hannunta chest dinta tace “Yayana?” Yace “Yess… Cutie” Apple dinta ta fara ci cike da 

jin dadi, jin an fara kiraye kirayen Magrib yace “Xan je Masallaci in dawo” tace “Toh plss ka dawo fa” yace “Xan 

dawo” Sudais na fita… Sajida mai aikin Mumy tayi knocking, Mami ta fito parlor lkcn, Karime ta bude kofar ganin 

Sajida sai da gabanta ya fadi, Sajida tace “Ina Hajiya?” Karime ta matsa bakin kofar tace “Ga ta ciki….” Sajida ta 

shiga ta gaida Mami da ladabi ta ajiye warmers din hannunta tace “Gashi Hajiya tace a kawo maki” Mami tace “Ohk, 

to an gode” Sajida ta mike ta fita, murmushi kawai Mami tayi tana ci gaba da danna wayarta, don kowa girkinsa 

yake a gidan ba hadawa aka yi ba…. Tare Sudais ya shigo da Shuraim daga masallaci, Mumy dake xaune parlor ta 

hade rai ganin Sudais, Shuraim ya gaisheta snn ya wuce dakinsa, Sudais yace “Mumy xan xo in wuce yanxu, xan 

masu sallama can ciki” Mumy ta amsa masa ciki ciki, ya wuce part din Mami ya sanar mata xai wuce, Heedayah na 

bedroom lkcn Mami ta kai ta tayi sllh, Mami tace “Abinci fa?” Yace “Aa I’m okay ma” Tace “Are you sure, ka tsaya 

fa ka ci abinci” yana murmushi yace “Sure am okay…” Tace “Toh shkkn mun gode Sudais” Yace “Heedayah tana 

ciki?” Mami tace “Ehh sllh na kai ta tayi” yace “Toh na wuce” daga haka ya fita parlon… Mumy bata tanka sai da 

safensa ba balle tayi masa tayin abinci yyi murmushi ya fita abun sa. Sai bayan isha Mami ta bude warmer din da 

Sajida ta kawo, wainar shinkafa ce da miyar taushe da ya ji nama da kayan hadi a diff but same warmers din, Mami 

ta kalli Karime tace “Gashi fa idan xa ki ci” Karime tace “Toh Hajiya” Mami ta xuba ma Heedayah shinkafa jollof 

da tayi… Karfe tara Mami ta sallami Karime ta tafi ta kwanta, Karime tayi mata sai da safe cike da ladabi sannan ta 

fita xuwa dakinsu da Sajida, Karime na kokarin kwanciya sai ga Mumy ta shigo dakin, Sajida ta mike da sauri 

ganinta tace “Xa a maki wani aikin ne Hajiya?” Mumy ta wani hade rai tace “Dalla rufe min baki kamar wata me yin 

abun arxiki, yaushe aka kawo yarinyar nan Karime, Amma dubi duk ta haddace abubuwan da tasan take yi, satin ki 

na uku kenan amma banda matsala bbu abinda kike bani da ciwon kai, ga sauran wanke wanke can kin bar ma 

uwarki ta xo ta karasa min a kitchen” Ita dai Sajida bata ce komai ba kanta a kasa, Mumy tace “Karime xo in d’an sa 

ki aiki don Allah yar albarka, bana son bacin rai gwara in sa wanda xai min da kyau…” Karime ta mike da sauri har 

tana tuntube tace “Toh Hajiya me xa a maki” Sajida dai ta bi ta da kallo bata ce komai ba, Mumy tace “In ji dai 

Uwar dakin ki baxata neme ki ba, kin gama mata komai koh?” Karime tace “Ta sallameni tace in je in kwanta bbu 

abinda xa ayi mata” Mumy tace “Yauwa toh kar in je maki matsala, kin san yanayin rayuwar yanxu” Mumy ta fita 

Karime ta bi bayanta da sauri… Har bedroom dinta ya shiga da karime, kayan guga ne tule kan makeken gadon 

dakin, Mumy ta sauke tsadaddun akwatuna tace “Wa e nnan kayan xaki jera min cikin nutsuwa a akwatunan nan, ba 

sake sa su xan yi ba shi sa xan mayar akwati” Karime tace “Toh Hajiya….” Mumy ta kishingida gefen gado tana shan 

grapes da ke plate a beside drawer, Karime sai jera kayan take cike da nutsuwa, Mumy tace “In ji dai Uwar dakin taki bata baki matsala na ga kina da hankali kuma komai a nutse kike yi ba kamar wancan tawar ba dake bani ciwon 

kai” Karime tace “Eh to Hajiya, kinsan duka duka jiya na xo gidan, amma naga kamar bata da sake ma jama’a kamar 

dai yanda kike…” Mumy tace “Haba?” Karime tace “Wllh, in nayi ma yarinyar ba dai dai ba ko yaya sai ta gyara min 

cikin bacin rai…” Mumy tace “Ikon Allah…. Duk wnn saukin kan naki??” Karime tace “Wllh, fitowar da nayi da ita 

daxu ma sai da ya kusa ja min matsala tace kar in kuma fitar mata da ita….” Mumy tace “Ikon Allah, kinga dai duk 

rashin damuwana ko ga maciji bata son mu dinga yi ni dai bana biye mata tunda ina da ilimi na nasan abinda nake yi, 

Kuma kinsan gaba daya satin ta daya da yan kwanaki a gidan nan, kwanan nan Mai gidana ya aurota amma sai take 

min kamar ta rigani shigowa gidan nan, komai Isa Isa kuma a walakance….” Karime da ta mike ta bude baki tace 

“Ikon Allah, kwanan nan? Ni ma xata kun yi shekara da shekaru tare ai ganin ynda take komanta” Mumy ta gyara 

xama tace “Wani shekara, yau kwananta takwas in gaya maki, kuma yarinyar nan da kike gani agola ce ta kawota 

gidan, shine ake mana fi’ili da ita, ni dai bana kulata sbda Allah na saka a gabana, Kinga dai d’ana na fari sannan ga 

‘yan matana biyu, to me kuma xai dameni da ita??” Karime ta rike ha6a tace “Gaskiya kam, ita da ko tsinke ma bata 

da a gidan, abincin da kika aiko mata daxu ma bata ci ba bata bari yarinyar ta ci ba ni ta bama” Da mamaki Mumy 

tace “Haba???” Karime tace “Wllh, Kuma tace Idan na gama in wanke kulan in ajiye maki a kitchen, in mun hadu 

gobe ince maki ta gode” Mumy ta sauke ajiyar xuciya tace “Toh ai shkkn, ni saboda Allah nayi, ai ya ga xuciyata, ita 

ta sani” Karime tace “Kwarai kuwa…” Mumy tace “Banda asiri gaskiya ne ina ita ina Mai gidana, asiricesa tayi fa ta 

auresa ta shigo da yarinyar nan, har ynxu xancen da nake maki ba ma wani shiri da Mai gidana duk ya watsar da ni 

da ‘ya yana, komai ita ce kan gaba” Karime ta bude baki tana kallon Mumy tace “Ikon Allah, Allah sarki, gaskiya 

kina da hakuri Wai….. Ni dama ina ganin yanayinta nasan baxata yi kirki ba” Mumy ta sauke ajiyar tace “Ni dai 

Allah na rike” Jin an bude kofar parlor Mumy tayi shiru haka ma Karime, Mumy ta mike da sauri tace “Waye??” 

Bandaki ta bude ta nuna ma Karime ta shiga da sauri, sannan ta fita parlon, Shuraim ne tsaye parlon, Mumy tace “Ya 

aka yi?” Yace “A’a Aunty Rukayya ke son magana da ke ta kira wayar ki baki amsa ba….” Mumy tace “Toh xan 

kirata, wayar na silent ne nan parlon…” Yace “Okay ke da waye a ciki?” Mumy tace “Ni da waye a ciki Kuma? 

Sajida ce tana min gyaran kaya” Yace “Toh sai da safe” tace “Allah ya tashe mu lfya” yace “Ameen” daga haka ya 

fita ta juya ta koma daki, kitchen Shuraim ya wuce don hada shayi ya ga Sajida tana wanke wanke, ya tsaya yana 

kallonta sannan ya tafi gun da cups suke ya dau daya ya hada shayin ya fita parlor ya xauna, sai kusan sha daya 

Karime ta gama gyaran kayan Mumy, Mumy ta hada mata kaya set uku tace “Gashi ki boye wnn kiyi ta tara abun 

ki….” cike da jin dadi Karime tace “Kai Hajiya wllh na gode, Allah ya saka maki da alkhairi, wannan kaya har 

haka??” Mumy tace “Ke dai ki ja bakin ki kiyi shiru, ko Sajida ma kar ki nuna ma, gobe xan samu Ghana must go in 

baki ki dinga boye kayan ki a ciki” Karime tayi ta mata godiya har ta fita dakin cike da murna….. Shuraim dake 

xaune parlor har sannan ya juya jin footstep yana kallon direction din, Kallon Karime dake tafiya kamar munafuka 

yyi ya dauke kai, ta shige dakinsu da sauri ta kulle. Washegari da safe Mami ta gama duk abinda xata yi ma 

Heedayah kafin ta fita, tana lura tun jiya Shuraim bai xo yace a fito da ita karatu ba, Karfe tara Mami ta fito parlor 

tana kallon Karime da ta gyara parlon tsaf tace “Ni xan wuce, xuwa anjima sai ki hada mata abun nan a cup ki bata 

idan ta tashi bacci, kuma kin da ji abubuwan da na gaya maki jiya ki kula don Allah Karime, anjima ki dafa maku 

duk abinda ku ke so” Karime na murmushi tace “In sha Allahu Hajiya, Allah ubangiji ya kiyaye hanya” Mami tace 

“Ameen” daga haka ta fita parlon, Xaune taga Mumy main parlor tana waya, Mumy ta dakatar da wayar suka gaisa 

faram faram Mumy na tambayarta kwanan Heedayah, Mami ta tambayeta na su Rabi’ah sannan tayi mata sallama ta 

fita parlon, Karime dake goge gogen kayan kallo bayan fitar Mami ta ta6e baki maganganun da Mumy tayi mata jiya 

kan Mami na dawo mata ashe ma kwace mijin mutane tayi ta shigo gidan, ci gaba da abinda take tayi tana yan wake 

wakenta, tana gamawa kuma ta hada kakkauran shayi a cup don Mami ta siyo kayan shayi ta ajiye nan parlonta sbda 

frequent shan shayin Heedayah, ta yanka tikeken bread ta xauna tana ci duk da dumamen da ta ci da sassafe, ta gama 

shan shayin kenan aka d’an bude kofa, juyawa tayi da sauri suka yi ido hudu da Mumy, Karime ta mike da sauri tace 

“A’a Hajiya ce, shigo mana, ta fita ai…” Murya can kasa Mumy tace “Ina yarinyar tata take?” Karime tace “Au tana 

can ai tana bacci, sai sanda ta tashi” Mumy ta karaso parlon tana murmushi tace “Karyawa kike yi kenan” Karime 

tace “Ehh wllh, gashi nan d’an ruwan shayi ta xuba min ta bani d’an kucilin biredi in karya” Mumy tace “Ga bredi 

can bangarena banda abun ki, har kayan shayin ma ai akwai, ki je ki hado wani idan baki koshi ba” Karime na washe 

baki tace “Allah sarki Hajiya to nagode kuwa….” Mumy na kallon eye drops dake ajiye wajen tv a parlon tace 

“Wancan Kuma menene, wa ke ciwon kunne?” Karime tace “Aa na yarinyar ne naga ana diga mata a ido…” Mumy 

tace “Ohhhoo na ciwon idon kenan” Karime tace “Kila, daya da safe daya da daddare haka naga ake yi kullum, daxu 

ma sai da ta diga mata da sassafe…” Mumy dake ta kallon eye drops din tace “Ikon Allah….”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *