UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 3 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 3 BY SHATU

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Shi ne last speaker a program din, ya karba mic din ya Kara introducing Kansa, muryar sa a hankali, tone dinta very gentle, hatta tafiyar shi zai tabbatar maka da nutsuwar da yake da ita. Part din shi shi ne na quiz da zaayi tsakanin SS1 da SS2. Dukka participant din Suka fita, Ashe a class din mu baa Yi delegating ba, in fact mu bamu San da maganar bama kwata kwata. Seda aka Kira class teacher din mu yace ga wadda zatayi. Hankalina Yana kan Na’ila dake cemin na tashi naje kawai ko ni ko kuma Cynthia, nace Mata ni fa gaskiya ban shirya ba.+

” Safiyya Abdullahi Gumel from SS1a”

Haka naji muryar shi cikin kunnena, nayi saurin kallon Na’ila dake dariya kasakasa, haka Rayha da ita already ta fita, lokacin da ya Kara Kirana lokacin na tashi Babu yadda zanyi, kaina a kasa sannan na Bata rai na Isa wajen da aka aje min. Bayan an Dan Yi briefing din mu akan rules din aka fara, ana gamawa muka koma seat dinmu Na’ila tace min

” Kin burge ni wallahi, karatun ki yau ya cecemu”

Nayi murmushi ban ce Mata komai ba, seda wani ya Kara presentation kafin aka gama hada gift din sannan aka fara fadar Wanda Suka ci. Ni ce first position a science classes, Rayha Kuma second position a commerce. Aka bamu wrapped gifts dinmu sannan muka sakko, har na zauna Usman Dikko ya Kira sunana, na bawa Na’ila gift din sannan na hau na tsaya gefen shi, cikin tsaftataccen turanci yace shi Bai taba ganin wadda take solving physics cikin dakiku kadan iri na ba, so na burge shi ya ciro kudi a aljihun shi ya Mika min, Ina murmushi na karba sannan yace

” Keep it up,you have high potentials”

Na gyada kaina sannan na sakko daga karshe aka Gama muka koma hostel, tun a hanya ake tambayata wai nawa ya bani ni kuwa ko irgawa banyi ba, ni da Na’ila da class rep dinmu muka je wajen class teacher dinmu muka bashi kudin da gift, daya irga 10k ne. A lokacin ji nake kamar million ya bani, Ranar da akai hutu min fito muna zaune se ga Rayha tazo tace min nazo , har na fara janyo trolleys dinmu tace

” Ba daukar mu aka zo yi bafa”

Cikin rashin fahimta nace

” To waye ke Kirana?’

Se tayi dariya tace wai idan naje na gani, haka na bi bayan ta har muka je can gefe karkashin wata bishiya, Yana tsaye ya juya bayan shi da wayar shi a kunne da alama Yana waya ne, jkin shi sanye da bakin jeans da jar top wadda ta dan kamashi har ta bayyana shatin singlet dinsa da abs dinsa. Na Bata Rai Dan muryar shi tasa na gane waye Usman Dikko ne, na kalla Rayha Ina hararta, ita Kuma se zare mini Ido take, na girgiza Kai Ina Mata wani kallo dangerously. Juyowa yayi ya maida wayar shi cikin aljihu sannan ya dubemu se nayi kasa da kaina na gaishe shi, ya amsa Yana fadin

” Ashe ku twins ne?”

Na gyada kaina se mukai shiru Kuma, ganin hakan Rayha tace

” Sofy lemme check ko Baba yazo”

Kafin na fadi abinda ke Raina ta fada, se Naga yayi murmushi yace

” Safiyya relax Mana, bana saida kan mutane”

Bance komai ba Amma gaba daya na takura, Shima ya lura da hakan se ya Ciro wani card bayan wayar shi ya rubuta Abu a jiki ya miko min yace

” Idan kinje gida you call me, kinji?”

Na gyada Kai Babu musu Amma a raina cewa nake lallai ma wallahi bazan Kira ba, in fact yadda card din ma zanyi.

” A wanne gari kuke?”

Ya katse min tunani na, na dago nace

” Funtua”

Se yace min

STORY CONTINUES BELOW

” But kamar Gumel a jigawa ne ko?”

Na gyada kaina yace

” That’s great, jeki kada Baba ya nemeki, make sure kin kirani”

Na gyada Kai na juya na tafi, Ina zuwa Baba Yana zuwa so se muka karasa muka rungume shi, ya shafa kanmu Yana tambayar mu makaranta da karatu, as usual muka je gurin class teacher dinmu ya mikawa Baba hannu Suka gaisa sannan ya karba result Dina, Yana ta Kara cewa Baba I’m a good student, dukda Babu position Amma ni ce me highest average score a class dinmu, haka muka je gurin nasu Rayha Shima haka ya fada yace dama sciences tayi se Baba yace banking and finance take son Yi, so dole ya batta tayi commerce, yayi murmushi yace

” Your daughters are extremely good, they’ll shine”

Baba yayi Masa godiya sannan ya Taya mu muka dakko kayan mu muka saka a booth, ni na shiga gaba Rayha na baya tana bawa Baba labarin quiz din da mukai, Yana ta jin dadi. Seda ya Mana sayayya sannan muka wuce gida, har lokacin hannuna Yana rike da card din, Yana parking muka fito muka ja kayan zuwa part dinmu, Anisah na makaranta, Ammi na kitchen ta fito tana murmushi tareda rungume mu, sannan muka Shiga da kayan mu ciki, muna zaune Baba ya shigo ko magana Bai yiwa Ammi ba itace ma tace Masa sannu da zuwa, ya amsa ciki ciki ya wuce daki, ta zauna kan kujera tana duba result dinmu sannan taji Kiran Baba daga daki, da ta Shiga mu Kuma se muka koma daki mukai wanka muka shirya cikin Kaya sannan muka dawo parlor,bayan na boye card din sannan muka ci abinci, Ammi tace muje part din Rumasa’u ta haihu. Rayha tace

” Me ta Haifa?”

Ammi tayi murmushi tace

” Ta Haifa mace, ku dauka abincin nan ku wuce Mata dashi”

Muka ciccibi basket din muka tafi, mukai sallama sannan muka Shiga tana zaune tana Shan tea, wadda ke zaune da ita ta gama wanki tana shanyawa kan dryer, muka Shiga tana fadin

” Yan makaranta sannun ku da zuwa”

Muka karasa muka gaishe ta, tace

” Ga kanwar taku “

Ni na dakko ta an kundundune ta cikin shawl, na bude fuskar ta, yadda kuka San fuskata aka cire aka saka Mata, Allah ya rufawa yarinyar asiri data biyo Babarta Bata Isa ace Mata kanwar mu bace. Na bawa Rayha nace

” Allah ya Raya ta”

Muka aje ta muka koma bangaren mu, da daddare Baba ya shigo na kai masa gift din mu da kudin da Usman ya bani, Baba yace ai da na nuna Masa Usman din ya Masa godiya. Kwanan mu biyu akai suna, dama tunda ta haihu Ammi me Bata abinci haka Baba yace, Kuma kullum kamar yadda alaadar bahaushe take ita take zuwa ta yiwa babyn wanka safe da yamma. Ana gobe suna da safe Ammi Dani mukaje Yi ma babyn wanka, Muna zaune da Baba Dayyiba Ammi ta Mata wanka ta tafi, Anty Rumasa’u ta fito daga daki ranta a bace, inaga Bata lura cewar Ina gurin ba, tace

” Baba wai kinji wai sunan Hajara zaa sakawa yarinyar”

Babar ta kalleni taga kamar hankalina na kan wasan da nake yiwa yarinyar, se tace

” To Banda abinki,meye Dan ya saka sunanta. Kina ganin yadda take wahala daku”

Ta Bata Rai tace

” Wallahi dariya zaayi min, ace an saka Mata sunan kishiya ta, inama laifin sunan Mami”

Baba ta girgiza Kai tace

” Ba sunan Safiyya kenan ba, ta Yaya zai maimaita suna daya akan Yara biyu. Kuma ni Banga aibu ba, ni da kike ganina sunan kishiyar uwata aka saka min, Kinga dadin Zama kenan, me yasa yaran yanzun kuke haka ne, Mata kin takura Mata kin hanata sakewa da mijin ta, itada yaranta na Miki kokari Amma baki gani. Keda safiya kuji tsoron Allah fa! Matar nan gidan ta ne ita Kika samu a gidan ta Amma kin dauka tsabar duniya kin daura Mata, meye matsalar ki ne”

Ta Mike tana Kara tamke fuskarta tace

” Kullum magana daya, wallahi ko jikin ta take yanka take bani, sunanta bazai canja ba kishiya ta ce, Kuma wallahi zai ga tashin hankali idan ya sakawa yarinyar nan Hajara ko kuma ayi suna biyu!”

Ta koma daki tana ta zage zage, se naji duk hankalina ya tashi, na aje yarinyar ban cewa Baba Dayyiba komai ba na tafi part din mu, Ammi ta fito daga parlon Baba nace Mata

” Ammi Baba na ciki?”

Tace

” Eh!”

Se na Shiga ba same shi Yana aiki cikin system din shi na gaishe shi ya amsa ba tareda ya kalleni ba, gabana nata faduwa Ina tunanin yadda zai karba maganar tawa. Yace

” Uwata ya akai ne?”

Nace

” Baba dama..wanne suna zaka sawa babyn?”

Ya dago ya kalleni yace

” Sunan Ammin ku Gwoggo tace a saka Mata,akwai wani abin ne”

Se na girgiza kaina kawai dama nayi tunanin decision dinsa ne na roke shi ya fasa Amma tunda na Gwoggo nasan Dole ne, yayi yai na fada Masa menene nace Babu komai.Har na tashi Zan fita yace min+

” Sofy ko akwai wani Abin ne”

Se nace

” Baba Naga Anty Rumasa’u kamar Bata so”

Se yayi dariya yace

” Sofy haka Mata suke Babu abinda zakayi ka burge su, ita da sunan ta nace Zan saka ai ba zatayi fada ba”

Se nayi Dan yake kawai nace to Allah ya kyauta. Na tashi na tafi bayan yace min na tura Masa Ammi, na same ta tana maida kayan Anisah cikin wardrobe dinta Wanda aka kawo daga gurin guga. Kayan aje ta tashi ta nufi dakin shi, na kalla Rayha nace

” Rays wai sunan Ammi zaa sakawa yarinyar Anty Rumasa’u”

Tayi ihu tace

” Amma naji dadi, Allah ya Raya ta yayi Mata albarka”

Nace

” Amma kinsan tana nan tana throwing tantrum wai kawayenta zasuyi Mata dariya”

Rayhana ta Bata Rai tace

” Ki  sakarya! Se tayi ai Hajara Babu dashi”

Ganin Bata ma fahimci abinda nake nufi ba yasa kawai na bar maganar, Ammi ta dawo ta zauna tace

” Ya akai Kika San sunan da zaa sakawa babyn?”

Nace

” Naje naji Baba Dayyiba na fada”

Se ta girgiza Kai tace

” Bana son a saka sunana, da ace Baban ku yayi shawara Dani Dana Hana shi saboda nasan fada zaayi”

Na Dan ja jikina kusa da ita na taba kafadar ta nace

” Ammi duk kin rame, karki bar wannan abin ya dameki bake Kika ce ya saka sunan ba. Dan Allah kiyi hakuri”

Se idanunta suka fara kawo ruwa, se ta Mike ta fita, kamar ruwa ya cinye mu hakan mukai shiru kowa da abinda yake tunani. Da yamma Baba ya dawo da kayan Miya da nama, da kaji. Duka muna parlor muna daga kayan da aka kawo Mana da zamu saka jibi ranar suna. Baba ya shigo muka Masa sannu da zuwa, ya zauna yace da Ammi

“Ga kayan Miyan na kawo”

Ta girgiza Kai tace

” Baban Sofy why not ka Kai Mata kayan, ni fa bana son tashin hankali”

Yace

” To yanzun waye yazo nata? Kece matar gida ai ke ya kamata kiyi”

Ta dalla Masa harara tace

” Se yau kasan ni matar gida ce kenan?”

Kusan lokaci daya muka bar musu parlon, daga karshe tace nazo na Rakata can, muka tafi tana daki itada kawar ta, ni na shiga nace tazo Ammi na parlor. Ta Dan Jima sannan ta fito ta zauna ko magana Bata Mata ba. Ammi tace

” Baban Sofy ya kawo kayan Miya da sauran, me kike so a dafa?”

Wani mugun kallo take zabgawa Ammi tunda ta fara magana,

” Komai ke zai kaiwa kamar kece Kika haihu? Ni na rasa wannan masifar duk kin bi kin kaonanaye komai, sunanki zaa sakawa yarinyar. To wallahi baki Isa ace abincin ma ke zakiyi ba”

Raina a matukar bace na bude baki da niyyar gagayya Mata magana Ammi ta girgiza min Kai sannan tace

” Rumasa’u..”

STORY CONTINUES BELOW

Ta daga Mata hannu ta janyo wayatta ta fara Kiran layin Baba, Ammi ta mike ta nufi kofa Nima nabi bayanta, Baba Dayyiba ta biyo Ammi tana fadin

” Hajiya Hajara kiyi hakuri, yaran yanzun se addua”

Ammi tace

” Babu komai Baba, idan kin gama kizo ki dauka kayan Miyan”

Daga haka ta wuce, Muna Shiga Baba ya kirata akan ta kwashe kayan ta Kai can,a take tace Masa ba zata kwasa ba idan Rumasa’u ba zata dauka a barshi a gurin, tana Gama fadin haka ta kashe wayar. Nida Rayha muka kwashe kayan tas muka Kai saboda ni ban son tashin hankali. Amma wannan abin da akai Raina yayi masifar baci. Da daddare Baba ya dawo ya tadda Ammi a daki

” Hajara wai me yake damun ki ne? Dazun Ina kiranki Kika kashe sannan nace dake ke zakiyi girkin ki mayar Mata!”

” Baban Sofy na gaji, na gaji da wannan abubuwan! Dama ka Kara aure ne Dan ka ci min mutunci ko kuma ka aure ta Dan ka nuna min iyakata?”

Se ta fara kuka ta cigaba da fadin

” Baban Safiyya ban Yi expecting hakan ba, banyi tunanin akwai ranar da zaka daga min murya ba, me nayi maka? Ka daina kulani, baka min magana, abinci se ranar da kayi niyya zaka ci! Me nayi maka? Idan nayi maka laifi ka fada min ni Zan baka hakuri, Amma wannan rayuwar daka daukar Mana it will affect su Sofy sannan zasu daina ganin girmanka, I want to save your image Dan hakan duk wulakanta Dani da zakai kada ka Bari su gani…”

Ta goge hawayenta sannan ta fita ta barshi a tsaye yana jin kamar Kiri zai dauke shi. Washegari gidan ya fara cika da Yan suna, Ammi tace dukka mu zauna kada mu fita ko Ina, Ina study room Ina fitar da phrases daga cikin wani comprehensive passage Dana karanta, Rayhana ta shigo, Zama tayi gefena ta aje abinda ban taba expecting zata gano inda na boye ba, hannuna na kai na dauke card din nace

” Meye matsalar ki Zaki dinga min bincike”

Tayi dariya taan tafa hannunta tace

” Twin ! So he gave you his number Amma baki Kira ba. Kece me matsala bani ba”

Na yayyaga card din in pieces nace

” Karatu nake Dan Allah ki tafi”

Tayi dariya tace

” Twin kenan! Bakya ganin kamar measure din is extreme, tambayar ki kawai nayi Amma kin yaga. Ko dai abinda nake zargi ne tsakanin ku..”

” Allah ya kiyaye meye abin burgewa a tare dashi?”

Se ta fita ta barmin study room din Dan yadda na hassallo Nima har mamaki nayi, me yasa na yaga na tsugunna na tattara Amma Babu yadda zaayi ta hadu balle ta bani abinda nake so, a zuciyar naje na jefa cikin bin sannan na fice zuwa parlor, da gudu na karasa na rungume Anty Safara’u dake zaune tace

” Uwata sarkin karatu”

Ammi na murmushi tace

” Se abinda yayi gaba”

Anty Safara’u ta shafa kaina tace

” Haka ake so Allah yayi muku albarka”

Na kawo Mata ruwa da abinci sannan na dauki kayanta na kai bedroom din Ammi na dawo nace Mata

” Mama Ina su Amra?”

Tace

” Se gobe zasu taho”

Na gyada Kai na koma daki Ina murna, Anty Safara’u ta dubi Ammi tace

” Ya ake ciki Ammi, Ina fatan komai dai ya Zama resolved dukda yanayin da na sameki Bai nuna hakan ba”

Ammi tayi murmushi me ciwo tace

” Komai Kara baci yake Mama, na rasa me yake damun kan Baban Safiyya. Na rokeshi idan na mishi laifi ya yafe min Amma yadda yake treating Dina is really getting out of hands”

Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta Dan Bata baki kafin tace

” Dole kiyi adjusting, nasan kinada banbanci keda Rumasa’u Amma Dole Zaki dauka abinda takeyi, maza da kike ganin su wawaye ne, they’re after some little tactics, zamani ya canja Dole mu bar old methods mu dauki sabbi idan ba hakan ba, yaran da muke rainawa zasu karbe gidan. Tasowar ku da Rumasa’u ba daya bane, wayewar ku da exposure dinku da banbanci so ki daina ganin Dan kin Haifa Sofy kin Zama uwar Mata, no you’re still young and good looking, jikin ki na nan tas to tsoron me kike ji Hajara? Kawai kema ki sabunta ya gane kema tsohon hannu ce”

Ammi ta tsaya kamar wata wawiya tana kallon Anty Safara’u, seda ta gama tace

” Bai kwana dakina, idan nazo Zan kwanta nashi se yace wai na takura Masa, kamar ni yake fadawa haka”

” Me yasa bazai fada ba? Bayan ya dandana Abu da supplements ke Kuma kince natural Zaki zauna, yanzun maza natural Bata rike su kici ki Sha Amma kada ki cutar da kanki kada Kuma kije wajen wani Neman taimakon, namiji yayi karya ki bar imanin ki akan shi”

Zakiyi tunanin Ammi will heed da maganganun, a farko tayi kokarin Yi Amma da Baba ya nuna Bai ma lura ba se ta watsar saboda Bata da courage se suka Kara komawa gidan jiya. Anyi suna yarinya Hajara dai aka saka Mata, Anty Safara’u tace ana ce Mata Ayaan! Na rasa dalilin da yasa fate din mace ke canjawa lokacin da mijin ta ya Kara aure, datajar ta ta ragu a idanun shi haka Kuma zai saka hannu yayi fatali da wasu nauyi da ya rataya a kanshi nata. A iya tunanina na Yan shekaru na na kasa fahimtar abinda hakan yake nufi. Se ya tattara dukka hankalin shi ya mayar kan amarya Yana ganin cewar ita UWARGIDA taco zamanin ta, na yadda da hakan Amma a addinan ce Dole ne kayi adalci tsakanin matanka Koda ace Gap din shekara dari ne tsakanin su, they deserve equal treatment Amma saboda wasu mazan Basu masan meye auren ba se su kuntatawa dayar ita Kuma dayar tana daga shoulders ita ce gimbiya a gurin miji. Wannan abin dake faruwa da Ammi yayi mugun staining aure a gurina, at some point gani nake auren bashi da amfani indai Zan Kare kamar Ammi, indai bakin cikin da nake ji shi Ammi keji tabbas bazan iya jurewa ba, a wasu lokutan Kuma zuciyata na Raya min gwara na aura me Mata Kinga bazan Kare a UWARGIDAN BAHAUSHE ba. To Amma abinda yafi tsaya min shi ne gwara na Zama UWARGIDAN na gyara tsarin komai a kaina, nasan bazan canja rayuwar mutane ba Amma ni a Karan kaina Zan iya canjawa.+

Mun koma makaranta, Baba Bai kaimu ba se ya samo wani abokin aikin shi yace ya Kai mu, sunan shi Bature Dan asalin Funtua ne. Yazo har cikin parlor mun Gama shiryawa Suka shigo da Baba ya zauna, ni kuma na fito daga dakin Ammi Ina taje kaina, Ina ganin shi nayi saurin komawa da baya. Ammi ta fito Suka gaisa aka kawo Masa abinci yaci kafin Kuma muka fito dashi zuwa mota. Ammi ta Mana addua da fadan kullum sannan muka tafi, kawai se naji kuka ya taho min, abinda ban taba Yi ba tunda nake. Har na Shiga gaban Dan Rayhana ta riga ta shiga baya. Har muka bar gida Ina kuka, Rayha dake baya tace

“Wai ke twin kukan me kikeyi ne?”

Dr Bature yace

” Kiyi shiru kinji, watarana se labari”

Na musu banza Dan ji nake kamar zuciyata zata fita daga kirjina. Seda muka kusa Bakori sannan na daina kukan, na idanuna har fuskata sunyi jawur. Bature se ya fara bamu labarin lokacin Yana secondary idan aka kaishi makaranta kafin Wanda ya kaishi ya Isa gida shi ya riga da ya dawo, nayi ta kallanshi da mamakin yadda wannan gentle guy din was rough once a rayuwar shi, yace Mana haka zai gudu wajen kakar shi se ya kusan cinye wata daya idan time din visiting yayi se ya koma school. Ranar da Baban shi ya gane ya mishi dukan da seda yayi black out. Bansan lokacin da na fara dariya ba, yace

” To kinga baya wuce ba? Yanzun I’m a medical officer soon Zan Zama resident. Ya wuce education is the powerful weapon”

Ya sauke mu makaranta ya Kara Mana kudi sanann mukai sallama ya tafi, hostel mukaje muka kintsa but har lokacin bana cikin yanayi me dadi. Washegari Monday very early na fita class saboda Ina son kadaice kaina, ni bansan meke damuna ba Amma Raina Babu dadi. Ina zaune mutane Suka fara shigowa har ajin ya shiga, Rayhana ta shigo ta kawo min wafers da juice tace

” Ko me ke damunki kiyi hakuri, just eat kinji.”

Nace Mata to sannan tayi min murmushi ta tafi, a hankali Kuma se na Dan rage damuwar especially karatu ya dauken hankali. Tunda muka dawo banga Usman ba, Amma inata ganin sauran corpers din, da farko nayi tunanin ko ya gama service dinsa ne Amma ganin colleagues dinsa se nake ta wondering me ya faru over the time har Bai dawo ba. Se da muka fi one months munata karatu na dage sosae inayi.

Ranar Thursday mun tashi a class na kulle locker na ta class sannan na dauka sauran juice Dina Dana Sha tun safe na fito Dan tafiya hostel, kamar ance na kalla can wajen admin, se na hangi bayan shi Yana tafiya gently, Babu tantama nasan shi ne. Abun mamaki I found myself starting at his back, a wani yaren abuna mamaki se na samu kaina da kallon bayan shi har seda ya kule, na lunshe idanuna sannan na juya na nufi hostel a sanyaye. Muna zuwa na cire uniform nai wanka nai sallah sannan na kalla Na’ila nace

” Ina Twin?”

Tace

” Taje masallaci, Zaki ci abinci?”

Na girgiza Kai na nace

” I want to take a nap”

Se ta tafi ni Kuma na kwanta Babu jimawa bacci ya daukeni, hayaniyar su ta tashe ni, na Mike nace

” Kin dawo?”

Tace

” Eh! Ga sako”

Ta fada tana miko min wata katuwar leda, na karba Ina Mata gesturing inji wa? Budewa nayi na Ciro karamar leda da turare a ciki me suna Oasis, se wata ledar me su maltesers a ciki da kananan gwangwanin Pringles, na aje gefe na janyo wadda tafi nauyi, na bude Naga yajin daddawa ne se nama da kuma calenders ta wata cute Baby alamu na suna ne, da idanuna nabi calender seda gabana ya Fadi ganin abinda aka rubuta… Welcome A’isha Usman Dikko! Na Kara kallar fuskar yarinyar, tamkar shi yayi kaki ya tofar she’s just his look alike. Na aje Ina jin wani yanayi Dan bansan yazan fassara muku shi ba. Na Jima in a daze kafin na dago nace

” Twin dama Yana da aure?”

Rayhana ta zauna itada Na’ila suka bi calender da Naman suna Wanda shi ne shaida.

” To menene Dan yana da aure, it’s normal”

Na’ila ta fada, se Rayha tace

” Ke Na’ila yakike maganar so casually bafa cewa yayi Yana sonta ba”

Tayi dariya me kyau sannan tace

” You guys are naive, ko Dan zaku ce na fada muku wallahi son Sofy yake”

Nayi saurin rufe Mata baki tareda binta da harara nace

” Ki gani a kanki me zanyi dashi, inshallah bazan aura Wanda yake da Mata ba”

Na Mike na tattare kayan na aje na bar Naman Dan nasan zai iya fiyaya. Muka Gama Shirin prep sannan mukai sallar laasar muka fita zuwa class. Tunda na zauna a seat Dina na saka chemistry din gabana nake kallo, na kasa hassalla komai se tunanin banza da wofi nake, na girgiza kaina wanting to revive myself Amma da na fara karatun se wani Abin ya dameni se na koma tunanin karshe dai se da nayi addua sannan na danyi concentrating. Naso mu hadu dashi Amma ban samu na ganshi ba se washegari ya fito very early Nima haka, na sameshi zaune a seat Dina, nayi saurin gaishe shi ya amsa Yana murmushi tare da Bina da kallo har na zauna gefen shi, rana ta farko da naji kunyar uniform dinmu Babu hijab se wani scarf. Gashi tuni jikina ya fara budewa, girly hormones se aiki suke, se duk naji kamar kallona yake Amma idan na dago se Naga hankalin shi na kan wayar shi. Ganin yayi shiru nace

” Sir Naga sako nagode. Allah ya Raya A’isha”

Ya kalleni Yana murmushi se Kuma ya Bata Rai yace

” Bayan na baki number ta baki kirani ba, ni fushi nake dake”

Nayi murmushi nace

” I lost the card”

Se yace

” Nasan haka Zaki ce, anyi mini haihuwa shiyasa kikaga ban dawo ba, she’s A’isha Amma Zaki iya ce Mata Afaf”

Nace

” Allah ya Raya ta”

Mun danyi Hira kadan yace min Yana level 3 akai Masa aure shiyasa, ya aura Yar abokin baban shi sunanta Kubra, Kuma Afaf ce yarinyar su ta farko, a raina nace being a married man yasa naji haushin ka nake ji. Bai Gama bani labarin ba student Suka fara fitowa se ya tafi , na koma seat Dina na zauna.Kwanci tashi Babu wuya a wajen ubangiji term ya Kare, duk kokarin da Usman yake ganin ya kafa gwamnatun shi a gurina Abin ya gagara, kwata kwata nuna Masa nake ni banma San me yake cewa ba, bana fahimtar abinda yake nufi. Saboda yadda yake yawan zuwa gurina da favoring Dina yasa mutane musamman Yan class dinmu suka fara fahimta suna questioning Dina. Sede I’m not friendly shiyasa mutane ke Dan shakata, Babu Wanda zai zo ya tambayeni sede ayi gulma ko kuma a tambayi Na’ila ko Rayhana. Ana gobe hutu min zo class Ina zaune a seat Dina na samu wani novel Ina karantawa, gaba daya hankalina ya tafi kan novel din naji Na’ila ta taba ni, dagowa nayi tareda rufe novel din nace+

” Yaushe Kika shigo?”

Ta zauna seat din cynthia dake gefen nawa,

” Sir Usman na nemanki, Yana staff room”

Na Bata Rai nace

” Tohm Zan je”

Se ta gyada Kai tareda juya litaffin hannuna taga sunan, tace

” Ke dama art kikai saboda literature”

Nace

” Tab har wani art ma, barni da physics da chemistry”

Se ta koma class dinsu Dan art student ce, hankalina na mayar kan karatun da nake ba tareda niyyar zuwa Kiran ba, ban Kuma dagowa ba seda class rep dinmu tazo tace naje messenger staff room Yana Kirana. Mikewa nayi na dauki littafin na fita, Dan tsohon na tsaye yana jirana, na gaishe shi yace Usman ke nemana, I’m trapped so dole na bi bayan shi muka tafi, dake yawancin malaman suna kokarin hada results dinmu yasa duk se corpers a ciki. Tunda na shiga na Bata rai Amma shi kuma fuskar shi murmushi ne akan ta, na karasa na gaishe shi ya amsa sannan yace

” Safiyya gobe se gida”

Na gyada Kai na bance komai ba, bansan dalilin da yasa idan nayi niyyar Masa Abu da zarar nazo se na kasa, Yana da kwarjini I just have to say that. Yayi murmushi tareda mikewa yace

” Idan kinje Zaki kirani”

Ya fada yana marairaice fuska,for an unknown reason se naji wani unfamiliar yanayi a tattare dani, na sauke kaina Ina Wasa da hannuna, yayi murmushi yace

” Please!”

Se na gyada Kai kawai, yayi dan chuckling yace

” Nagode, it means a lot”

Se na dago na kalleshi sannan nayi murmushi nace

” Zan tafi, Ina so zanyi karatu”

Na fada Ina waving Masa hannuna da littafin, karba yayi yace

” Baki gajiya da karatu? You’re nerd”

Na gyada Kai sannan ya miko min littafin na Masa sallama, har na fita inajin gaze din shi akaina, washegari muka koma gida, a raina nace yanzun Zan koma dealing with another situation. Baba Bai zo ba se Dr Bature ne yazo, muka gaida shi Yana fadin

” Yan biyun oga!”

Shi yayi Mana clearance Yana ta Mana murnar result dinmu, muka nufi gida, har ciki ya Kai Mana kayan mu Suka gaisa da Ammi sannan ya tafi, Ammi Babu laifi tayi kyau ta danyi kiba kadan. Wannan hutun haka mukai yishi cikin farin ciki Dan Baba da Ammi sun shirya kamar da. Ayaan nata girma dukda babarta ba wani kawo ta take ba Amma mukam da kanmu zamu dakko ta mussaman ma Anisah dake zaune a gidan. Bayan mun koma school Dr Bature ya maida mu ya Zama tamkar shi ne driver dinmu, wannan ya saka muka fara sakin jikin shi especially ni, daya lura ni mutum ce me son karatu se ya dinga kwao min novels da kuma text book da zanyi amfani dasu. Se muka Zama so close har idan Ina son Abu zam Kira na fada mishi. A wañnan lokacin Anty Rumasa’u ta shirya tafiya Kaduna mu Kuma muka tafi Gumel. A Daren Dr Bature yazo gida munata hada Kaya, ni Ina kitchen Ina kwashe stew da zamu tafi da ita, se Kuma ta Gwoggo wadda Ammi ke Mata duk lokacin da aka samu me zuwa. Baba da kanshi ya leko kitchen yace nazo Bature na jirana, seda nayi tsalle sannan na fita, hakan kurum nake jin farin ciki duk lokacin da muke tare dashi. Ina fitowa na same shi da Anisah suna Hira, nayi sneaking daki na dakko hijab sannan na fito zuwa parlon bayan na fadawa Ammi, na dakko Masa ruwa na aje Masa nace

STORY CONTINUES BELOW

” Baka ce kana call ba?”

Yayi murmushi yace

” Littafi na kawo Miki”

Ya Miko min, na karba Ina ta murmushi kamar bakina zai yage, nayi Masa godiya sannan yace na gaida Ammi ya tafi. Daki na wuce na nunawa Ammi dake zipping trolley da kayan Anisah ke ciki tace

” Sofy meye tsakanin ku keda Bature”

Na fara zazzare idanu, nace

” Ammi me Kika gani?”

” Ba wannan na tambaye ki ba, meye tsakanin ku na tambaya”

Na Bata Rai na aje books din jikina na Dan Bari nace

” Ammi kuma nace wallahi Babu komai”

“Zanci ubanki idan Kika min karya, ki maida hankalin ki kina jina ko?”

Nai Mata shiru kawai ta gama fadan ta sannan na nufi kofa Dan fita, ta kwada min Kira

” Sofy!”

Na juyo Ina Kara tamke fuskata, ta Harare ni sannan tace

” Wa zai dauke littatafan da Kika bari? Zan Kara ganin yazo gurinki a gidannan kina rawar Kai karya ki zanyi”

” To Ammi ni fa Bai ce min komai ba he’s just nice saboda yasan Ina son books”

Na fada Dan Naga fushin da daure fuskar ba zaiyi aikin ba, kwashe books din nayi na fita, jera su nayi cikin shelf ba tareda na bude ba Dan fadan da Ammi tayi min yasa Suka fita akaina.

Nidai bazan adar da cewar Anty Rumasa’u tana asiri ba, saboda zato zunubi ne Kuma bani da hujjar da Zan Kare kaina idan na zarge ta. To Amma something sounds odd, cikin yanayin jin dadi muka tafi Gumel, tunda muka dauki hanya Ammi da Baba ke Hira suna sako mu a ciki, Baba ya tambayi ni da Rayha ambition dinmu, Rayha dama kowa yasan nata she wants banking and finance, daya tambaye ni se nace Masa Bio medical engineering nake son Yi. Baba yayi shiru kafin yace

” Engineering kuma? Why not medicine”

Na girgiza Kai nace

” Ni shi nake so ko kuma Vet-medicine”

Se Ammi tace

” Gwara vet din tunda nan ABU ma suna Yi”

Baba yace

” Gaskiya kam Dan medical engineering din duk southern universities suke offering. Though naso ace University daya zamuyi Amma Babu damuwa Allah ya tabbatar muku da alkhairi”

Muka amsa da Amin, se yamma muka Isa Gumel, gida straight muka wuce seda muka shirya sannan muka je gidan Gwoggo, ta dinga murna ta rungume mu tana fadin min Dade bamu zo ba gashi duk mun girma. Se wajen Sha daya na dare muka koma gida. Washegari garin ya fara cika saboda sallar Gani da ta rage kwana daya. Tun safe muke ta aikin abinci, se yamma muka Gama se ga Anty Rumasa’u ta dawo, muka gaishe ta, ko amsa mu batayi ba ta ce Ina Ammi muma se muka Mata banza ba Wanda ya kulata, ta gaji da tsayuwa se ta yo kaina zata dakeni, daidai shigowar Ammi da Anty Hadiyya da Suka dawo daga gidan Gwoggo, Anty Hadiyya ta fara rike hannunta tana fadin

” Me ya faru?”

Wata harara ta Mata sannan ta kalli Ammi tace

” Ki jawa yayanki kunne wallahi duk wadda ta min rashin kunya se naci uwarta”

Ko uffan Ammi Bata ce Mata ba, se ta dauki Ayaan ta fice, Ammi ta tambaye mu abinda ya faru muka fada Mata se tace Allah ya rufa asiri, Anty Hadiyya mamaki tayi sosae. Da daddare Baba ya dawo Yana tambayar mu abinda ya faru tsakanin mu, se tace Masa sede ya tambaye mu ita Bata gidan Amma ga abinda ta samu, se Bai Kara cewa komai ba. Washegari tun laasar muka kammalla Shirin mu, yaran Anty Safara’u Suka zo Wanda Suka saanin mu, su biyu. Gidan Gwoggo muka je parlonta cike da yayanta da kuma jikokin ta. Muka gaishe su sannan na Dan zauna can Kuma na fito tsakar gida Dan Shan iska, se naji alamar an zauna gefena, na dago na dube shi, tamkar Bai ganni ba hakan yake Danna wayar tashi, na dan Yi tsaki yadda bazai jini ba nace

” Yaya Ismail Ina wuni”

Ya Dan kalleni sannan yace

” Lafiya! Are you Sofy or Rayha?”

Na Bata rai Dan dalilin da yasa bana shiga sabgar shi kenan, Yana ji da kanshi saboda jikokin sarkin Kano ne, ga Ummaah naturally tana da mulki da izza shiyasa kusan duka yayanta haka suke, but annoying abun shi ne duk lokacin da muka hadu zai ce wai no Sofy ce ko Rayha? Kafin na bashi amsar da bani da niyyar Sega Ummaah ta karaso, yayi saurin tashi se na kalle shi kafin Nima na tashi tsaye fuskata Babu walwala na gaishe ta. Ita Kuma a duniya na sani basai wani ya fada ba tana sonmu, Bata son maman mu Amma tana sonmu sosae. Ta amsa bayan ta rungume ni ta dubi Yaya Ismail tace

” Ka fito kenan?”

Ya shafa kanshi yace

” I wanted to see her”

Se tayi murmushi tace

” Allah ya bada saa!”

Ban amsa ba Dan bansan wa yake nufi ba, se na Mike Zan tafi se yace

” Ki zauna mana, ina Zaki je?”

Nace

” Gurin Ammi Mana”

Se ya Mike yace

” Let’s go then, Nima Ammina ce ai”

Ba yadda zanyi haka muka jero Ya daga kanshi sama, kana kallon shi kasan girman Kai zaiyi!Muka jera muka nufi kofar da zata fitar damu daga sashen Gwoggo, duk yawancin aunties dinmu ko kuma Wanda Suka girme ni se na gaishe su, hannun shi yasa riko hannuna, nayi saurin kwacewa Ina zumbura baki nace

” Ni dai karka Kara taba ni”

Se yayi murmushi yace

” To ki daina gaida mutane, just focus muje gurin Ammin”

Bance Masa komai ba na hango, Yaya Nasir Yana tahowa, a cikin raina na fara adduar Allah yasa ya tsayar dashi na samu na gudu, aikuwa Allah ya karba adduata, Yana zuwa ya Mika masa hannu yace

” Man kwana da yawa”

Na gaida Yaya Nasir Yana murmushi yace

” Grandma kece Kika girma haka? Mashaaa Allah kin Zama Yan Mata”

Nayi murmushi Ina rufe fuskata saboda kunyar kallon da yake min, ganin hakan Ismail ya gyara murya yace

” Dude lower your gaze!”

Yaya Nasir ya kalleni sannan ya kalle shi yace

” Grandma should I borrow him for an hour? Na Jima ban ganshi ba”

Na gyada Kai na Ina murmushi, baban shi cousins suke da Baba, ya Jima baya Nigeria Dan ni kaina bansan yaushe ya dawo ba. Na juya Zan bar gurin naji muryar Yaya Ismail yace

” Sofiyya!”

Na juyo se yace

“Kar kiyi nisa”

Na gyada kaina na juya na tafi, ban Kai ga fita daga gidan ba muka hadu da Ammi da Yan uwanta da Suka zo daga Dan ladin gumel. Na gaishe su Ina tambayar su Baba da  Alhaji, suka amsa ni sannan Suka shiga ciki ni Kuma na nufi wajen kallon Hawa, gurin a cike yake dam da mutane daga garuruwa daban daban, Gumel is famous a wañnan aladar tasu.

A bangaren su Yaya Nasir,wani secluded spot suka samu suka zauna, Nasir yace

” Dude baka da kirki baka Neman mutane”

Ismail yayi dariya yace

” Dukkan mu zaka ce, Kai da zaka tafi Babu sallama shiyasa na yada Kai”

Suka Dan taba Hira, Nasir yace

” So Sofy fa?”

Ya Harare shi yace

” Ina sonta, Zan aureta!”

Nasir ya gyada Kai yace

” I’m happy! Amma kana ganin Ummaah zata yadda kasan basa shiri da Ammin ta”

Se ya dage kafadar shi irin ko a jikin shi yace

“Matsalar su ce wannan! Ni Bai dameni ba. What I know Ina son Sofy Zan Kuma sure ta”

Nasir yace

” Kabi a hankali dai, baa zuwa gurin mace da girman Kai”

Se yayi dariya kadan yace

” Ka dameni!”

Bamu Kara haduwa dashi ba Dan daga nan se na koma gida, ni kadai nayi zamana Ina karanta PQ na waec, nayi nisa sosae dan tunda na shiga SS2 nake Abu daya. Saboda duk hankalina ya koma kan final qualifying exam din. Se bayan Isha sannan Ammi suka dawo, Ina zaune kan sofa na baje da scientific calculator hannuna, naji sallamar su, na amsa Suka shigo Ammi ta rike baki cikeda mamaki tace

” Dama kina nan? Munata nemanki”

Nayi murmushi nace

” Tun dazun na dawo, gajiya nayi”

STORY CONTINUES BELOW

Rayha ta cire takalman kafarta tace

“Kede wallahi ki dinga Shiga mutane, meye abin guduwa”

Ban amsa ta ba nace

” Ammi nayi girki, na zubo Miki?”

Ta gyada min Kai sannan ta Shiga cikin bedroom, Ammi na fara zubawa sannan na zuba Mana dukka cikin katon tray, mun fara ci kenan naji sallamar Baba da Yaya Ismail, na janyo dankwalin lace din dake jikina na lullube kaina dashi sannan muka amsa sallamar, Suka shigo abin mamaki Ismail ya tsugunna har kasa ya gaida Ammi, sannan ya zauna muka gaishe shi, Baba ya dube ni yace

” Ina Kika tafi anata Neman ki?”

Nayi murmushi nace

” Baba karatu na dawo nakeyi”

Ya girgiza Kai tareda kallon Ammi data Mike zata kitchen ta kawo Masa abinci yace

” Ki dinga Mata fadan karatunnan”

Ammi tace

” To ya zanyi, ai sede addua kawai”

Rayhana ta Taya Ammi kawo abincin, nikam ko Gama ci banyi ba na tattara kan books Dina nayi daki saboda kallona da Ismail yake min it’s making me nervous. Bansan yaushe ya tafi ba Dan tunda na Shiga ban Kara fitowa ba. Su Ammi har nayi bacci suna Hira itada Baba, Yana ta Bata labari sede naji dariyar su a hakan na Gama karatun nayi bacci. Washegari Rana ce da a tsawon rayuwata bazan taba mantawa da ita ba,Rana ce wadda Zan iya Mata lakani da bakar Rana saboda Rana ce da ta dasa min tabo cikin zuciyata. Ni na fara tashi bayan munyi sallar asuba, mun koma. Ina fitowa nayi wanka kamar kullum sannan na Shiga kitchen na dafa tea nasan zaa kawo abinci daga cikin gida. Komawa parlor nayi na zauna na dakko biology na na fara karatu hannuna da wayar Ammi Ina browsing wasu abubuwan. Bayan wajen mintina talatin naji sallamar Baba, na gaishe shi fuskar shi a murtuke ya amsa sannan yace

” Ina Hajara?”

Nace

” Bata fito ba inaga bacci takeyi”

Ya girgiza Kai sannan ya Mika min ninkakkiyar paper yace

“Ki Bata idan ta gama baccin asarar, ku Kuma ku shirya anjima zamu koma Funtua”

Na amsa Ina jin Raina Babu dadi wai baccin asara, dukda nasan baccin ba me amfani bane ba Amma ai bazai Fadi haka a gabana Bai dace ba. Na aje paper gefe sannan na cigaba da abinda nake, fitar shi Babu dadewa Sega Ammi ta fito, na gaishe ta tace min

” Kamar muryar Baban ku naji ko?”

Na gyada Kai nace

” Ni na zata Yana nan se kawai Naga ya shigo”

Tace

” Tunda ya tafi masallaci yace min zaije gidan Gwoggo, me yace?”

” Yace mu shirya anjima zamu tafi”

Ta gyada Kai tace na tashi su Rayhana kada yazo Basu shirya ba, har na nufi dakin mu se na nuna Mata paper nace yace na Bata, na shige dakin na tashe su sannan na fito, Ammi Naga a tsaye jikinta na rawa hatta hannunta dake rike da paper rawa yake, nayi saurin karasawa daidai lokacin ta sake paper a kasa ta rufe bakinta da hannun ta, na  riko ta Ina fadin

” Ammi menene? Me ya faru”

Bata cemin komai ba se ta karbe hannunta ta nufi dakin ta, Rayhana ta fito ita da Anisah jin salatina bayan na karanta content din dake paper, Zama nayi saboda wata hajijiya dake neman fadar Dani a kasa, Rayha muryar ta can kasa saboda bacci tace

” Me ya faru? Me ya samu Ammin”

Na Mika Mata takardar sakin Ammi, Baba ya saki Ammi na furta a hankali idanuna na kawo ruwa, itama ta karanta se ta fara kuka ta nufi Ammi dake daki, ni na kasa motsawa se kuka da nake Yi a hankali, bansan yadda Zan hada idanu da ita ba, it’s a big unexpected blow! Baba ya saki Ammi Babu wani dalili, min Zama Babu uwa kenan.

” Ammi Ina zakije?”

Naji Rayha na fada Mata se nayi saurin mikewa na Shiga ciki, ta canja Kaya ta saka hijab tace min

” Uwata ku hada kayan ku Kar yazo Yana jiran ku, ni Zan tafi se munyi waya”

Na rike hannunta Ina kuka nace

” Ammi tafiya zakiyi ki barmu? Dan Allah ki tsaya Baba yazo it’s must be a misunderstanding bake Hajaran ba”

Nayi ta kuka da hannunta cikin nawa, Anisah ma se ta fara kuka ganin munayi, Rayha nayi se Ammin ma ta fara Taya mu, ta goge fuskarta ta Mike tace

” You girls should take care of yourselves kunji? Zan kiraki”

Wannan scenerio shi ne worst abinda na taba gani a rayuwata, muna kallo ta fita daga gidan ta barmu mu kadai, Rayha ta koma daki da gudu ta fada gado, Anisah tace min Yunwa take ji, na rike hannunta fuskata da idanuna sunyi jawur na tafi kitchen na hada Mata tea na Bata, zuciyata tayi min nauyi tayi wani baki ji nake kirjina Yana min zafi tamkar na saka hannuna na Ciro zuciayr na daurayeta!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *