HEEDAYA CHAPTER 13 BY By Khaleesat Haiydar
Www.bankinhausanovels.com.ng
Shuraim na xaune bedroom dinsa hannunsa rike da wayarsa yana dialing number wani colleague dinsa, bayan sun
gaisa Shuraim yace “You called bana kusa Najeeb” Bayan few seconds Shuraim yace “Ehh na sani, I will be there
soon in sha Allah” Daga haka suka yi sallama ya katse wayar, mikewa yayi yana kallon agogo dake nuna karfe goma
da few minutes ya fita dakin, kitchen ya fara shiga ya hada shayi sannan ya fito ya nufi part din Mumy, duk wutan
parlon a kashe yake da na dakinta, daga can uwar daka cikin muryar bacci tace “Waye wannan?” Yace “It’s me
Mumy, kinyi bacci ne?” Tace “Toh me xan jira” yace “Okay, Xan wuce hospital ne ynxu in sha Allah” Tace “Okay
are you spending the night there?” Yace “No xan dawo anjima” Ta mike xaune da sauri tace “Karfe nawa yanxu da
xaka je asibiti har ka dawo, why not spend the night there, ni bana son tafiyar daren nan gaskiya” Ya d’an yi shiru
sannan yace “Toh shkkn sai da safe” Tace “Allah ya tashe mu lafiya, pray before leaving” yace “In sha Allah” daga
haka ya fita parlon ya kulle mata kofa….. Abba ya gani xai shiga bangarensa, Abba yace “Ohk Baka tafi ba?”
Shuraim yace “Yanxu xan wuce” Abba yace “Alright sai da safe” Shuraim yace “Allah ya kai mu lfya Abba” daga
haka Abba ya shiga part dinsa, Shuraim ya xauna parlor ya gama shan shayin hannunsa ya kai cup din kitchen ya
dauko makullin motarsa ya fita gidan, sai bayan da Mai gadi ya bude masa gate ya bar compound din ya tuna da
rigar sanyinsa don garin da sanyi kuma ko kadan baya son sanyi, yyi parking a nan kofar gidan ya sauka motar ya
koma cikin gidan, bedroom dinsa ya tafi ya dauko rigar sanyinsa sannan ya dawo parlor, har ya nufi kofar fita sai
kuma yayi hanyar dakin kaka ya bude kofar, a kashe ya ga wutan dakin, ya danna hasken wayarsa that’s so dim yana
kallon dakin, Kaka na kwance hannunta rike da carbi tana bacci har da minshari, ga mamakinsa idon Heedayah biyu
tana kwance lamo saman gadon, ya karasa cikin dakin yana haska fuskarta, mikewa tayi xaune jin motsi, a hankali
tace “Mami” shi dai yana tsaye yana kallonta, Ta sake cewa “Mamii” Kaka ta gyara kwanciya tace “Kya ci kanki”
daga haka ta ci gaba da baccinta, tuni Shuraim ya kashe hasken wayar sai da ya ji ta ci gaba da minshari sannan ya
kara haska dakin, Heedayah dake xaune fuskarta kamar xata yi kuka cikin sanyin murya tace “I want to take tea
plsss” Juyawa yyi ya fita dakin ya kulle kofar a hankali, sannan ya bar gidan, slowly yake driving har ya bar
anguwar gaba daya. Tun tafiyar Shuraim Heedayah bata koma ta kwanta ba, har da d’an hawayenta tana gogewa da
bayan hannunta, duk motsin da tayi sai kaka ta gyara kwanciya tace “Kya ci kanki” ita dai ba sanin nufin Hausan ma
tayi ba, tana xaune har sha biyu saura ta ji an bude kofar dakin…. Sai kallon direction din take ta ji an kamo
hannunta, ta mike tsaye tana tattaba hannun tace “Mami ke ce, I want to take tea…” Kaka ta tabe baki ta gyara
kwanciya tace “Kya ci kanki dai” fitar da ita aka yi dakin still holding her hand, ba musu take tafiyar har sannan tana
laluba hannun da ya riketa, sanyin da taji na shiga jikinta sbda yar rigar jikinta yasa ta fixge hannunta tace “Ina xa
mu je??” lkci daya aka dauketa xata yi ihu aka rufe bakinta gamm, bata kuma yunkurin yin ihun ba, next thing taji
an saka ta a mota an rufe, motar na fara tafiya ta kwala ma Mami kira, nan ta dinga ihun Mami da karfi amma ba a ce mata komai ba, ta gaji tayi shiru, can ta fara laluba cikin motar har ta ji ta ta6o me tukin, a hankali tace “Who are
you??” Jawota yyi ta fado kansa ya maida ta front seat, kin sake sa tayi ta kai fuskarta jikinsa perceiving his perfume,
yyi parking ya dau goran ruwa ya bude ya kai bakinta, rike goron tayi hakan ya sa ya sakar mata, ta d’an kurbi abun
ciki, bata sauke goran ba sai da ta shanye content din ciki tas, shi dai driving dinsa kawai yake slowly, ta kai hannu
tana ta6a sa bayan ta ajiye goran tace “Who are you?” Bai tanka ta ba, tace “Kai Yaya ne?” Still ba a ce mata komai
ba, ta kara cewa “Yayah?” Nan ma shiru, driving kawai yake avoiding check points a hanya, har dai ya isa wani layi,
kallon gate din layin dake kulle ya dinga yi, can ya gyara parking ya kashe motar yana kallon Heedayah, lamo tayi
kan kujeran idonta rufe har ta fara bacci, ya bude side dinsa ya fita ya xaga xuwa inda take ya bude motar ya
daukota ya daurata saman shoulder dinsa, ta bude ido a hankali sai kuma ta kara lumshewa, ya shiga layin ta
karamin gate, har dai ya isa bakin wani gate ya tsaya ya ciro makulli aljihunsa ya bude gate din da hannu daya ya
shiga sannan ya kulle gate din, ginin bungalow ne me girma, ya bude parlon shiga gidan da makulli ya shiga, yana
bin ko ina da kallo ya wuce daki, bbu bedsheet saman gadon da ya d’an yi kura ya bude press ya fiddo wani xanin
gado yayi spreading dinsa with one hand ya kwantar da ita gently, bude ido tayi sai kuma ta mike xaune da sauri
tana hade kafa tace “I want to ease my self” tsayawa yyi yana kallonta kamar bai gane turancin da tayi ba, ta fara
kokarin sauka daga kan gadon tace “I want to urinate” ya kalli kofar bathroom dake cikin dakin sai kuma ya kama
hannunta suka wuce ciki…. Bayan sun fito tana rike da hannunsa tace “Shikenan mun bar kaka a can gidansu Mami,
she will be looking for me faaa” Ji tayi ya kwantar da ita saman gado, ta yi rub da ciki ta lumshe ido, bude idon tayi
da sauri jin an daga rigarta tace “Yayah” Lkci daya taji xafin shigan alluran xata tashi a tsorace ya ki barinta hakan
yasa ta fashe da kuka tana kwala ma Abba kira, yana gamawa ya mike ya kashe Ac dake dakin ya kunne fan ya
kashe wutan ya fita dakin ya kulle ya bar ta tana kuka. Tun karfe daya saura Mumy ke xaune dakinta idonta kyam,
ga wayarta a hannunta, wayar ne yyi haske ta daga ta kai kunne da sauri, lkci daya ta mike tace “Har kun taso, to
bari in je in bude gate din” tana fadin haka ta katse wayar ta mike ta tafi gun window tana kallon tsakar compound
da yayi tsittt, a hankali ta bude kofar dakinta ta fita har xuwa main parlor, sai da ta gama kare ma parlon kallo
sannan ta nufi kofa ta bude a hankali ta fita, gate biyu ne gidan, daya a baya, daya kuma a gaba, sai dai an fi shekaru
biyu ba a bude gate din bayan ba, can Mumy ta nufa tana yi tana dube duben tsakar gidan duk da tasan kowa na
gidan na bacci har masu gadi, tana isa gate din taji sa a bude, she was so very suprise, ta leka wajen gate din, bbu
kowa layin sai street light da ya haska ko ina, to wa ya bude gate din, ko dai dama a bude yake all this while ba’a
ta6a lura ba, but this is suprising, jawo gate din tayi a hankali amma bata yi jamming ba ta juya da sauri ta koma
cikin gidan…. A parlor ta ci karo da kaka, gabanta yyi wani irin faduwa, Tayi hanyar kitchen da sauri pretending
kamar daga kitchen din ta fito, Kaka da tayi kicin kicin da fuska tace “Maryam kina ganin wannan kishiyar ta ki ko?
Halan bata sanni bane bata san halina ba, wllh xan tara mata jama’ah idan bata fita hanyar Deedayah ba a gidan nan,
meye xata bi dare ta shigo ta dauke ta kamar ita ta tsinto mana ita, wai ma uwar me ta hada da Deedayan nan ne ma
tukun, farkawa fa nayi naga bbu yarinyar an dauketa, to wllh ki taso min Amadu inji ko shi ke sa ta raina ni daga
shigowarta gidan ko sati biyu ba ayi ba….” Mumy tayi kasake tana kallon kaka, can dai tace “Ban gane ba kaka,
yarinyar bata cikin dakin ki ne yanxu?” Kaka tace “Leka ki gani mana, xan maki karya ne?” Mumy tace “Aa to ki
shiga bangarenta ki dauko ta kaka, wnn ai rainin hankali ne, ikon da take nunawa kan yarinyar ai ya fara wuce gona
da iri” kaka na jin haka ta tafi bangaren Mami cike da kwarin gwiwa ta bubbuga kofar, ta bubbuga yyi sau hudu
kafin Mami ta bude, Kaka ta wani sha kunu tace “Ina yarinyar da kika dauke a dakina Rakiya?” Mami tace “Yarinya
kuma, wace yarinyar kaka?” Kaka ta kalli Mumy tace “Kinji ko Maryam, bata ma san yarinyar da ta dauke ba, to ni
baxan biye maki ba da girma na, Deedayah xaki fiddo min” Mami tace “Heedayah da kika tafi da ita daxu muna
parlon barrister?? Ae ba a kawota nan ba” Kaka ta gwalo ido tace “Toh ni kuma bata dakina yanxu, ban ganta ba
wllh” Kasa cewa komai Mami tayi tana kallon Kaka baki bude, kaka ta saki salati ta tafi bangaren Abba da sauri shi
ma ta tado sa, yana fitowa tace “Amadu kai ka shigo ka dauke Deedayah dakina muna bacci?” Abba na kallonta da
mamaki yace “Heedayah kuma, ba xuwa kika yi daxu kika tafi da ita ba” Kaka ta kara Rafka wani uban salatin ta
daura hannu a ka tace “Wllh farkawa nayi ban ganta a dakin ba Amadu, don Allah a rufa min asiri a dudduba ko taje
ta shige wani wajen ne ba a sani ba, kasan makaho” Kaf gidan bbu inda ba a duba ba amma bbu Heedayah bbu
alamarta, su Rabi’ah duk an tasosu su ma, Mumy da hankalinta ya fi na kowa tashi ta rakube kitchen tafara kiran
waya, ana dagawa tace “Kai oga Salahu ku dakata an nemi yarinyar ko sama ko kasa bbu a gidan ba a san wanda ya
dauketa ba, ku dakata xan kira ku, ku dakata tukun” Bata jira cewarsa ba ta katse wayar tana xufa…. Duk iya duban
da xa ayi a gidan nan anyi har tare da masu gadi amma ba a ga Heedayah ba, daga karshe kuma aka ga second gate
din gidan a bude, kaka ta rushe masu da matsanancin kuka tace “Wayyo na shiga uku yanxu cewa xa ayi tayi a
dakina ta 6ace, don girman Allah a rufa min asiri a nemota, idan hukuma ma suka ji haka ba kyaleni xa su yi ba,
duniya duk a dauka ace na sace makauniya, wllh farkawa nayi naga bbu ita sai pillow….” Abba dai na tsaye ya ma
kasa cewa komai, ya rasa tunanin da xai yi but xa a iya ganin tashin hankalin fuskarsa, likewise Mami dake ta kallon
gate din da ke bude, Mumy kuwa salati ta dinga yi tana cewa “Anfi shekara uku ba a bude kofar nan ba, a ina ma
aka samo makullin aka bude?? Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un…. does it mean we are not longer safe cikin gidanmu kenan, waye xai dauke wnn yarinya ni Maryam” Mami tayi mata wani kallo sannan ta shige cikin gida, kana ganinta
kasan she is not going to let this, daren ranan nan dai bbu wanda ya rintsa a gidan, Kaka kuwa ta lula cikin anguwa
neman Heedayah, bbu yanda Abba bai yi da ita kan kar ta fita dare ne amma taki sauraran kowa tayi ficewarta tana
kuka… Gaba daya Mumy ta rasa irin tunanin da xata yi, amma hankalinta ya fi na kowa tashi, can sai ga kaka ta
dawo wujiga wujiga da takalma da Hijabi a hannu wai karnuka sun biyo ta… Karfe hudu Shuraim ya shigo gidan
ta dalilin kiransa da Abba yyi, Kaka ta fashe masa da wani sabon kukan ta rikosa tana cewa “Wllh tare muke kwance
Shureen wai farkawan da xan yi naga bbu ita, an sungumeta….” Shuraim dai ya kasa cewa komai sai kallon kakar
tasa yake, can ta sake sa ta koma gun Abba tana Kuka wai ta shiga uku kar hukuma su daure ta, Shuraim ya jingina
da bango a hankali ya rungume hannunsa, he looks disturbed also, Ana kiran sllh dama Mami ta bar gidan…. Bayan
an idar da sllh sai ga Baffa da Sudais sun shigo gidan, Baffa ma is speechless just as his brother, Kaka dai tun
hawaye na xuba har ya daina xuba yanda take kukan kai kace yarinya ce, Sudais ko karasowa cikin parlon ma ya ki
yi yana tsaye daga bakin kofa, at the end kawai ya fice daga gidan gaba daya, Baffa na kallon kaka yace “Don Allah
kiyi hakuri Baaba, in sha Allah xa a ganta, bbu abinda xai sameta” cikin rawan murya kaka tace “Toh kai sai kayi
fatan abu ya sameta dama? Wllh wanda ya saceta cikin gidan nan yake, dama kaf gidan banda ni da Rakiya bbu me
sonta, ko shi Amadun bamu san xuciyarsa ba” Abba ya kalleta ta gefen ido bai dai ce komai ba, Baffa yace “Da karfe
nawa kika lura bata dakin?” Kaka tace “Daya saura minti goma, Ina fitowa parlo kuma Maryam na fara sanar ma
cewar ban ga Deedayah ba” Abba ya kalli kaka yace “A ina kika ga Maryam din” Mumy ta amshe da sauri cike da
karfin hali tace “Na fito shan ruwa kitchen muka hadu” Abba ya kalleta, ya dauke kai ya sake kallonta sai kuma ya
mike ya wuce bangarensa, Shuraim dai kansa na kasa, Mumy na daga xaune amma duk cikinta ya hautsine da kyar
take xaune har lkcn, ba a dau lkci ba Abba ya fito yana kallon Baffa yace “Mu tafi Dr” Mikewa Baffa yyi, kaka ma
ta mike da sauri rike da hijab dinta tace “Ae da ni xa aje duk Inda xa a je tunda a dakina komai ya faru, salon in ki
bin ku a xargeni ace dama ni na sace ta, gwara duk inda xa ku in bi ku” Sai bayan fitarsu Mumy na kallon Shuraim
cikin karfin hali tace “Aliyu wa xai dauke yarinyar nan, wllh ni dai ban san komai kan wnn lamarin ba, naga kuma
kowa kallona yake, dama ni na dauketa baxan damu ba, amma wllh ba ni bace, kaga kallon da barrister yyi min irin
kamar da sa hannuna gun 6atar ta” Hankali tashe take maganan, shi dai Shuraim kansa na kasa, can ta mike ta wuce
bangarenta, yana rike da car key dinsa ya bar parlon ya tafi gun motarsa dake waje…. Hajiya Sadiya da kanta kasa
cewa komai tayi, Cikin rawar murya Mumy tace “Sadiya ni fa ban ta6a shiga rudani irin wnn ba, sannan kuma abun
mamaki gate din bayan ma a bude na samesa…..” Sadiya ta d’an yi shiru snn tace “Shuraim na gidan kuma koh?”
Mumy tace “A’a baya nan, tun tara da wani abu ya tafi night duty ba sake shigowa gidan ba sai Asuba uban ya kirasa
ya dawo…” Sadiya tace “Kaiii, wnn lamari akwai lauje cikin nadi…..” cike da damuwa Mumy tace “Ni ki saurareni
Sadiya, ta ya xan wanke kai na cikin lamarin nan, wllh sai kinga, ko magana xanyi sai inyi ta rawan baki… Ni nasan
kowa ma ni yake xarga, ni kuma ba a ma kai ga xuwa dauke yarinyar nan ba aka nemeta aka rasa…. Ga dai abun
farin ciki amma bbu daman farin cikin tunda ni ake xarga” Sadiya tace “Bari xan kira ki yanxun nan” daga haka ta
katse wayar….. Cikin bacci Heedayah ta ji hannu a kanta, ta bude idanuwanta da kyar ta kamo hannun tace “Mami I
want to ease my self”Abba yyi kasa da murya yace “Noo Rahinah, ba sai an kai ga haka ba, this is almost a family issue, ni nasan me xan
yi, in sha Allah Heedayah will be back home….” Mami ta katse sa ta mike tace “Family issue barrister? ni fa I’ve
already made up my mind, allow me to do what I am suppose to do, matarka knows Heedayah’s Whereabout, ta san
komai a kan bacewar yarinyar nan, so why do we all have to pretend, sorry to say, ba ruwana da wani family issue I
am doing my work tunda kai baxa ka iya ba, idan ‘yan sanda suka je suka daukota they will interrogate her ta fada
masu inda aka kai ‘yar mutane, period!!!” Abba ya mike yace “But you can’t look into my eyes and tell me xaki sa
ayi arresting matata Rahinah” Mami tace “I am sorry barrister, I’ve got no other option, yanayin aikin ne haka kai ma
ka sani, nima gobe idan nayi abinda ya cancanci ayi arresting dina, allow them to arrest me…” Kallonta kawai yake,
Kaka dake can wani gefe cikin haraban police station din tare da Baffa ta fyace majina tace “To ni dai yunwa nake ji,
kar wata cutar taje ta kamani a banxa in cuci kai na, ko ‘yar yagwat da nama ai ya kamata ku siyo min in xauna in ci
daga nan, shi ciki ina ruwansa da 6atar mutum, Karfe takwas fa ake nema yanxu ban karya ba…. su kuma wa encan
xancen me suke har yanxu kamar 6atar yarinyar bai damesu ba?? Ai ko d’an mage ne ya 6ata sa nuna damuwar su,
amma tun daxu suna ta hira ka duba fa” Baffa ya kalli Mami da Abba bai dai ce komai ba, Kaka tace “Su ma shegun
‘yan sandan ca suke ‘yar kaza ce ta 6ata da baxa su maida hankali ayi abinda ya kamata ba, ni ba ruwana shiga xanyi
in fada masu gaskiya….” Baffa ya dakatar da ita yace “Xa mu je can gidan ne dasu ynxu, yanxu duk xa mu wuce…”
Kaka tace “Atoh gwara dai mu je din, ni dai tunda na biyo ku ai bbu wanda xai xargeni dai ko?? ita kuma wancan
matar dake ta shiga da fice kamar Yan uwanta ne ‘yan sandan Allah ya sa….” Shiru tayi ganin Mami da take magana
a kai ta nufo su, Kaka tace “Ya ake ciki Rakiya? Ni fa hakurina ya soma karewa, basu da taimakon da xa su mana ne,
in je gun Ta salla?” Mami tace “A’a xa mu je gida ynxu da ‘yan sandan kaka, iya bincike ya nuna bbu wanda ake
xargi kan bacewar Heedayah sai Hajiya Maryam….” Kaka ta wani tabe baki tace “Lallai!!! To da baxa a xargeta ba?
muguwa ce fa, a jiyan da daddare ma daga waje naga ta shigo bansan uban me taje yi waje tsakar dare ba…. Idan ba
rashin gaskiya ba menene wannan din??” Kaka ta fashe da kuka sosai tace “Kilan lkcn ta mika Deedayan ta dawo…
Dama tun ba yau ba kowa yasan Maryam bata da Imani, Kuma axxaluma ce, akwai wata mai aiki da tayi da dadewa
sai da ta kusa kashe mata ido daya, da kyar Amadu ya shawo kan kess din, sannan ta ta6a aiken Mai gadi mota ta
kwashe gantalalle a titi ya karairaye, shi ma dai Amadu ya shiga ya fita aka rufe kess din, sannan kwanaki shi ma da
dadewa taje gidan kitso tasu ta hado su da matar wani babban mutum, Maryam ta tattakure ta sharara ma mata mari,
in takaice maki dai awowin Maryam uku a seff, da kyar Amadu ya shiga ya fita aka yi belinta sannan ya kashe kess
din, Kinga kuwa ai Maryam takadiriyar mace ce, mu dai kawai muna xaune da ita ne saboda su Shureen” Mami
dake ta sauraronta tace “Yanxu ma ita xa a je daukowa don ita ce first suspect kan 6atar Heedayah….” Kaka ta saki
kabbara da karfi tace “To da pa?? ai dama ita ce ni dai tunda ba a xargeni ba Alhmdllh, a xargi kowa ma, har shi
Amadun….” Mami ta juya ganin Yan sanda biyu sun fito ta nufi motarta da su, kaka ta bi bayanta da sauri tana cewa
“To dama idan ba ke ba wa xai tsaya kan maganan nan, Amadu dama tun yana karami wani solobiyo ne, lauyancin
ma Allah ne ya basa ba wayonsa ko dubara ba” duk wannan abun Abba na tsaye daga inda yake yana kallonsu, haka
ma Baffa da ya ki cewa komai, Baffa ya sauke ajiyar xuciya ya nufi d’an uwan nasa…. Heedayah ta daga kai jin an
amshi cup din shayin da take sha, tace “Ban shanye ba ai tooo” Yana rike da hannunta suka fito parlor, tace “Tell me
who you are…. Yaya that gives me chocolates? Or Yayana, yayana din Farida?” Jin bai bata amsa ba, ta tattaba
hannunsa tana turo baki tace “Ka ji mana, tell me” Jan bakinta taji anyi ta kai hannunta da sauri tace “Ouchh, me na
yi?” Bai ce mata komai ba, ta warce hannunta tace “Nasan waye” ya tsaya yana kallonta, can ya durkusa kusa da ita
ya jawota dabb da shi ya kai bakinsa kunnenta, murya kasa sosai kamar me rada yace “Waye?” Tayi shiru kamar
tana son gane muryan, can ta fara komawa baya a hankali tace “I don’t know you” jawota yyi ta fasa ihu tace
“Maminaa” ya dauketa kamar yar baby suka fita parlon har kofar gida inda yyi parking, front seat ya bude ya sata
ciki ya daura hannu saman lips dinsa yace “Shiiiii” he could see how afraid she is, hawaye ya kawo fararen idonta
tace “Plss take me back to Mami, ban san ka ba” rufe motar yyi ya tafi ya sa ma gidan makulli sannan ya dawo ya
hau motar ya bar layin… Wayarsa ne ya fara ring, ya kalli wayar ganin me kiran sa ya samu waje me kyau yyi
parking sannan ya dau wayar ya fita waje don amsa kiran, bayan few mins ya dawo cikin motar ya d’an kalli
Heedayah sannan ya ci gaba da driving dinsa….. Rirrikesa Heedayah tayi jin alamar wucewa xai yi ya bar ta bayan
ya saukar da ita daga motar, cikin kuka tace “Don Allah don’t leave me ka kai ni wajen Mami da Abba first,
plsssss…” Ya cire hannunsa daga nata ya koma gun motarsa walking very fast, within a twinkle of an eye ya bar
anguwar… Heedayah ta fashe da kuka sosai jin tafiyar motarsa ta dinga kwala ma Abba kira tana yarfe hannu, Mumy
ce ta fito daga cikin babban gidan a rikice bayan kiran da Abba yyi mata yace ta bar gidan, hijab ne har kasa a jikinta
ko kayan kirki bata sa ba da makullin mota a hannunta, tsabar rudewa mancewa tayi da motar a compound ta fito bakin gate da kafa, karo ta kusa ci da Heedayah dake kuka sosai tana laluba inda take, Mumy ta ja baya a d’an
tsorace tana kara kallonta, lkci daya ta saki salati ta riko hannunta tace “Kee wa ya ajiye ki a nan, wa ye ya dawo
dake???” Heedayah ta dakatar da kukan da take jin muryarta, Mumy na kalle kalle kamar munafuka tace “Nace wa
ya ajiye ki a nan?? Ina yake???” Heedayah dai bata ce komai ba sai shessheka take, Mumy ta kwalo ma mai gadi
kira a rikice, ya fito da gudu yana amsawa, tace “Isiyaka wa ya ajiye yarinyar nan bakin kofa, daga ina ta fito?” Ya
matso da sauri yana kallon Heedayah da kyau yace “Ikon Allah ba ita ake nema ba Hajiya?” Mumy ta daka masa
tsawa tace “Cewa nayi wa ya ajiye ta a nan kana tambayata tambayar banxa, waye ya dawo da ita” Yace “Wllh wllh
Ina ciki Hajiya ban san daga Inda ta fito ba, Banda yanxu da kika kirani ni ban san ma akwai mutum a nan ba”
Mumy ta fashe da kuka sosai tace “Kai shaida ne isiya yanxun nan na fito na ganta tsaye bakin gate din nan, ni ban
san daga Inda ta fito ba, ban san wa ya ajiye ta ba” Isiya ya rike ha6a yace “Ikon Allah, to waye ya maido ta kuwa?”
Mumy na goge idonta tana kalle kalle kamar munafuka ta marairaice tace “Amma kaga ba lallai kowa ya yrda a
bakin gate muka ganta ba isiya… Ni dai kai ne shaidana fitowata kenan daga cikin gida na ganta, yanxu ka shiga da
ita ciki ni xanje can in dawo, maxa ka kai ta ciki” tana fadin haka ta kara gaba da sauri tana hade hanya, isiya ya bi
ta da wani kallo kafin ya ta6e baki yace “Da dai ba a san ki bane Hajiyaa, Lallai na yarda Allah na fitar da me kyau
cikin mara kyau….” Yana fadin haka ya girgixa kai ya kama hannun Heedayah ya shigar da ita cikin gidan yace
“Allah dai ya kubutar dake yarinya, da yake baki da hakkinta sai gashi Allah macecin ki, irinta macecin ki” sai da
Mumy ta tabbatar ta shiga adaidaita sannan ta kira Abba, yana dagawa ta fashe masa da kuka sosai tace “Wllh
barrister ka ga gashi an maido yarinyar nan kamar daga sama, ni dai ban san komai kan lamarin nan ba ban san wa
ya dauketa ba ya sake maido da ita yanxu, Ina fitowa bakin gate muka ci karo da ita wllh wllh iyakar gaskiyata nake
gaya maka isiya ne shaida na, tare muka ganta rakube gate tana kuka, Mu dai bamu san ta yaya ba” Abba da ke
xaune mota tare da Baffa suna dawowa gida da farko kasa ce mata komai yayi, can dai yace “Yanxu ke kina ina?”
Tace “Ga ni a adaidaita xan tafi gidan Aunty Zuwaira” yace “Toh ki tafi can din, Heedayar na gida yanxu haka?”
Mumy tace “Wllh kuwa, tana can na baro ta tunda kace in bar gidan” Abba bai ce komai ba ya katse wayar, Abba ya
jinginar da kansa da kujeran motar yyi shiru, Baffa da ke jin duk yanda suka yi da Mumy a waya da yake a hands
free Abba yasa, ya sauke ajiyar xuciya, Abba yace “Ba Maryam ta dau yarinyar nan ba….” Baffa yace “Ba ita ta
dauketa ba, amma she knows everything about it….” Abba ya kallesa yace “Not much, matata ce na san when she is
lying and when she is not, nasan Maryam bata son yarinyar nan xa ta ma iya sawa ayi abinda ya fi dauke Heedayah,
but this time around ba ita bace, I will have to go deep into this matter” Baffa dai bai basa amsa ba…. Salatin da kaka
ta saki bakin kofar parlor ya sa Mami ta karaso da sauri ‘yan sanda biyu na biye bayanta, Heedayah suka gani xaune
saman kujera a parlon ga Karime da Sajida da su Rabi’ah duk a parlon, Shuraim na tsaye daga wajen dinning ya
rungume hannunsa, Kaka tace “To ni dai Allah ya isa cutan hanjin ciki na da aka sa nayi na bar su da yunwa basu ji
ba basu gani ba, tunda uwata ta haifeni ban ta6a kai wa karfe tara ban karya ba sae da wnn yarinya ta 6ata, gashi
yanxu har wani jiri nake ji kamar xan kwanta gadon asibiti….” Bbu wanda ya kalli kaka, Mami ta karasa gun
Heedayah dake xaune tayi shiru hawaye bushe a idonta, kafin tace komai daya daga yan sandan yace ce “Ita ce
yarinyar?” Mami ta mike so surprise ta girgixa kai tace “Ita ce, she is the one….” d’an sandan yace “We are going
back to the station with her, but before then a gidan nan suspect da xa mu dauka take??” Mami tace “Ehh nan ne”
Shuraim ya kalli Mami ta gefen ido, Kaka ta nufi bangaren Mumy tace “Mu je in kai ku dakinta, ko ba Maryam
ba….” Yan sandan suka bi bayanta xuwa bangaren Mumy, bbu kowa parlon da daki da ma bathroom, Kaka har da
duba karkashin gado da cikin press din kaya, ta dudduba bayan labule, bata yarda ba sai da tasa suka dage katifar
gadon, Kaka na hada xufa tace “Ta tsere, kaga ta sa an maido da yarinyar ta gudu, to Allah ya isa wahal da mu da
tayi, Allah yyi mata abinda tayi mana….” Yan sanda suka fita dakin, nan dai suka dudduba sauran dakunan cikin
gidan amma bbu Mumy, Kaka na kallon Shuraim tace “Toh Shureen ga uwarka dai ta dawo da Deedayah ta gudu….”
Calmly yace “Ita tace maki ita ta dauketa??” Kaka ta nufesa da sauri tace “Kar ka min rashin kunya, kana min xan sa
‘yan sandan nan su casa min kai yanxun nan su tafi da kai caji ofis” Khadijah ta sunkuyar da kanta tana dariya kasa
kasa, Kaka tace “Atoh, ka yi mana, ya naji kayi shiru, xageni mana” Su kansu ‘yan sandan sai da suka yi murmushi,
Mami dai ko kallon kaka bata yi ba, Yan sanda suka dau Heedayah tare da Mumy xa su koma station, kaka ta dauko
Hijab ta bi bayansu, Mami na kallonta tace “Kaka kiyi tsayawarki ki k’arya mana….” Kaka tace “Ce maki nayi
yunwa nake ji, a fara abu da ni kuma sai a ki karewa da ni” Mami bata kuma ce mata komai ba ta bi bayan ‘yan
sandan suka fita, Kaka na biye da su da sauri. Hajiya Sadiya ta rike ha6a tana kallon Mumy da tayi tagumi tace
“Ikon Allah, wllh wanda ya dauketa a gidan yake, bbu shakka ya gano komai ne yyi hakan, kuma ba kowa nake
xargi ba illa Shuraim” Mumy ta dago da sauri tace “Shuraim?? Shuraim dai, A’a Shuraim baya ma gidan hakan ya
faru, yana can asibiti” Hajiya Sadiya tayi wani dariya tace “Dai dai ma kenan tunda baya gidan, wato shine ya bi
dare ya sadado ya dauketa….” Mumy ta mike tace “Haba Shuraim baxai ta6a yin haka ba, Bai san ma komai kan
wannan plan din namu ba, to idan ma ya sani Allah na tuba meye hikimar dauketa balle bai sani ba, he has nothing
to do with the blind girl a gidan, ko kallonta ma shi bai yi, Yan gidan ma yaushe ya samu lkcn yi masu magana balle
makauniyar? Bai ta6a kallon inda take ba ma” Hajiya Sadiya tace “Wllh ko rantsuwa nayi baxan yi kaffara ba Shuraim ne ya dauke yarinyar nan, idan ma xaki yarda ki yarda, wnn d’an naki baki san kyar yake kallon ki ba ko?
to wai idan ba shi ba Aljanine xai shigo ya dauketa? Ke ki duba lamarin nan fa, sannan kince a bude kika ga gate din
bayan gidan ba wai 6allawa aka yi ba, waye yasan wani inda makulli yake?? Gwara ki ajiye wnn batun na cewa
Shuraim baya kula kowa a gidan, Kuma in har yaron nan naki na gidan nan bbu abinda xa a yi ma wannan
yarinyar….” Mumy dake tsaye ta kasa cewa komai tace “Shuraim Kuma, Shuraim????” Hajiya Sadiya ta ja tsaki tace
“Ai sai ki yi kuma, kema kinsan duk shirunsa shegen wayo ne da shi snn kinsan he is never in support of anything
bad…. Tsaf shi xai dauketa sannan ya maidota bayan yaga duk an watse a gidan” Mumy dake xufa ciki da waje tace
“To kuwa xan ci ubansa la’ada waje, xan ji ko shi ya haifeni ko ni na haifesa” Hajiya Sadiya tace “Atoh wnn dama
dai ta wuce kuma, sai mu tari gaba, ga asara, ga xargin ki da kowa ke yi a gidan, ga kuma ‘yan sanda na nemanki…”
Mumy ta fashe da matsanancin kuka tace “Ni wllh da ma ni na dauketa ko a jikina, amma bani bace sannan gashi
kowa kallon ni na dauketa yake min, ga dai ta nan na hadu da ita a gate da xan fito amma sbda tashin hankali ko
tunanin cutarta ban yi ba, kai a lkcn ji nayi na fi kowa farin ciki da dawowarta don wnn ba karamin case bane gashi
kaka ta ga shigowana daga waje, da dai kattin sun shigo sun bubbuge kowa ne sun dauke yarinyar da Rabi’ah kamar
yanda muka shirya daga baya sai su sako Rabi’ar ai kinga bbu shegen da xai xargeni, to ba a kai ga hakan ba aka
nemeta aka rasa, Amma wllh idan har da gaske Shuraim na da sa hannu a dauke yarinyar nan sai na nuna masa ni na
haifesa….. Sai ya yaba ma aya xakinta” Hajiya Sadiya tace “Ni duk ba wnn ba Maryam, yanxu dai daga nan har
xuwa wata biyu ko daya da rabi babu ruwanki da yarinyar nan, tsakanin ki da ita ido, ko magana ba dole kiyi mata
ba, sai mun bari kowa ya sakankance sannan sai a shammace su….” Mumy na share idonta tace “Tunanin da nayi
kenan nima, shi kuma Shuraim don ubansa dama masters din nan dai da baya son yyi yanxu shi xai tafi yyi, ga
Sudais har ya kusa gamawa, to dolensa sai ya tafi shima yyi, ko ya ki ko ya so wllh tllh sai ya tafi….” Hajiya Sadiya
tace “Shkkn wllh, kinyi maganinsa cikin sauki” Mumy ta nemi waje ta xauna tace “Ita kuma wnn karuwar yanxu
nake da lkcnta a gidan nan, na amince xan banxatar da batun makauniyar har na yan watanni ita kuma yanxu xa mu
fara gogawa da ita” Hajiya Sadiya tayi dariya tace “Ki goga da wa? Matar da in ta fita tun safe sai yamma, ai bata da
wnn lkcn sai dai makauniyar” Kiran Abba ne ya shigo wayar Mumy ta gyara xama da sauri ta daga ta kai kunne
cikin sanyin murya tace “My Barrister