HEEDAYA CHAPTER 24 BY By Khaleesat Haiydar
Heedayah tace “Ina yini ya Sudais” ya cire glasses din idonsa yana kallon kwayar idonta yace “Lafiya lau ya
karatu?” Tace “Alhmdllh” gaishesa Farida ma tayi, ya amsa mata da murmushi yace “How is study?” Tace “fine
Alhmdllh” yace “That’s great” Yana kallon Heedayah yace “Hope you are enjoying it in here yan matan Mami” Ta
gyada masa kai tana murmushi tace “Sure” yace “That’s nice” Heedayah tace “Ya Sudais Kaka fa” Yace “Tana gidan
su Farida ai” Heedayah tace “Okay but when we went back for holiday bata nan, ban ganta ba” yace “Baki ce Mami
ta kai ki wajenta ba” A hankali Heedayah tace “Ta ki” Sudais yace “Ohh may be she is busy” komawa yayi ya xauna
inda yake yace “Ku ai makarantar ku ne ni bari in xauna” Dariya Heedayah tayi tace “Yes, beside we are not that
lazy” ya xaro ido yana kallonta, Farida dai tayi murmushi, sun kusa awa daya tare da Sudais a wajen, yawanci duk
xancen da suke na karatu ne, and he was so amazed at how intelligent Heedayah was ya kasa daina kallonta even for
a second, Daga karshe dai ya mike yace “Ya kamata ku je ku ci gaba da karatu yanxu, but ku baku da d’an
supermarket din nan na cikin makarantar?” Heedayah tace “Aa muna da, they sell everything” Yace “That’s sweet”
Dubu ashirin ya fiddo aljihunsa ya mika ma Farida yace “Ke ce babba ku siyi duk abinda ku ke bukata, I don’t really
know what u will like shi yasa ban siya komai ba while coming” Farida tace “Last week fa yayanmu ya xo kuma ya
ba mu kudi, we have enough money” Yace “Yes I know, but kina nufin ni ba yayanku bane?” Murmushi tayi tace
“Not at all ba haka nake nufi ba” Yace “Toh amsa” Ta amshi kudin tace “Toh mun gode Allah ya saka da alkhairi”
Heedayah tayi murmushi tace “We appreciate ya Sudais” Yace “You are welcm all” Daga haka suka rabu da shi,
Heedayah sai waigosa take don sai taji bata son su rabu, she is going to miss him much. Mami na kitchen da safe
tare da mai aikinta suna hada breakfast kasancewar ranan asabar ne baxata fita aiki ba, Daga nan parlor kaka ke
cewa “Ai ni da na biye ta Umaru baxai ma bar ni in xo nan ba, kinsan da yake ba sata kadai ne abun kunya ba, Ina
ga kunyar xuwa wajen ki da nake yi suke, tunda sun san abinda suka tafka shi da d’an uwan, to kuma yau sati na
kusan daya a nan duk safiya ina lura da jik’a jik’an aikin da me aikin nan taki take ba kan gado kamar yar maguzawa,
kuma kawai don na mata magana ki ce don me? Ni sai in iya tattara yanawa yanawa in tafi duk inda Allah yayi
wllh” Mami dai na jin ta a kitchen tayi murmushi bata ce komai ba, ko kadan bata son kyaran da Kaka ke yi ma mai
aikin nata, abu kadan yarinyar tayi sai fitinar kaka, ta lura duk inda me aiki take jininsu bai haduwa da kaka, kaka ta
kara daga murya tace “Toh idan na koma gida yanxu ba sai Umaru ya min dariya ba har da shewa, kin ga ko gwara
in tafi duk inda Allah yayi, don tun farko ya hanani xuwa, kawai daga na fada gaskiya ki ce min ba haka bane wato dai a fakaice makaryaciya kika kirani, masu aikin jaraba suna neman hada ni da ke, to ni bbu ruwana kafin ki koreni
gwara ko xuwa nan da sati biyu ne in tattara komai nawa in yi wucewata, ko tsinke baxan bari ba wllh” Danna bell
aka yi, Mami dake ta murmushi tace “Zainab tafi ki duba waye a kofa” Tace “Toh Hajiya” daga haka ta fita, kaka ta
bi ta da wani shegen kallo tayi mitsi mitsi da ido tace “Algunguma me raba xumunci kawai” Zainab na bude kofa ta
gaida wanda ta gani tsaye da ladabi, ya amsa yana kallonta, with respect tace “Wa xa a ce?” Yace “Barrister” tace
“Toh” sannan ta juya ta koma, kaka ta sake bin ta da harara har ta shiga kitchen din, sannan tayi kwafa tana kara
gyara xama, da ladabi Zainab tace ma Mami “Hajiya wai Barrister ne” Mami dake juya farfesun kayan ciki dake
saman gas ta kalleta tace “Barrister? Daga ina wai?” Zainab tace “Aa bai sanar min ba” Mami tace “Koma ki
tambayesa daga ina” Zainab ta juya ta fita ba a dau lkci ba ta dawo tace “Hajiya cewa yayi Barrister Ahmad Aliyu”
Mami dake kwashe farfesun a warmer don har yayi, bayan few seconds tace “Kiyi hakuri ki koma ki tambayesa
akwai matsala ne? Wa yake nema” Juyawa tayi ta sake fita, Kaka dai na ta xaman parlor kamshin farfesu duk ya
cikata don da farko cewa tayi xata tafi, har jakarta tace xata tafi ta dakko a sama, amma tunda taji irin kamshin dake
tashi ta share batun jakar tayi mukus sai kame kamen fada da take ta yi, Kaka tace “Toh waye ya danna mana
kararrawa naga bai shigo ba har yanxu” Zainab xata koma kitchen tace “Bako ne kaka” Kaka tace “Wani jarabbben
bako da sassafen nan ko karyawa ba mu yi ba yunwa ta dame mu, girkin ma da iya cikin mu kawai aka yi, wani
bako kuma” Zainab na shiga kitchen din tace “Hajiya cewa yayi xuwa yayi ya gaida Kaka” Mami tace “Ohk toh xan
wuce sama ynxu sai ki kashe gas din ruwan xafin nan ki tafi kice ya shigo tana parlor” Zainab tace “Toh” daga haka
Mami ta fito parlor, Kaka tace “Nan dai da sati uku xuwa hudu xan koma gidan Umaru tunda shaidaniya ta fara
shiga tsakaninmu, ba ruwana da fada da ke” Mami na murmushi tace “Aa kaka bbu wanda xai shiga tsakaninmu
baki dai fahimce ni bane, bari in sakkowa ynxu in kawo maki kayan karin” Daga haka Mami ta wuce sama, Kaka
tayi kasa da murya tace “Ni yau naga jaraba duk sai yunwa ya gama cutar jama’ah ya lahanta ‘yan hanjinmu sannan a
bamu kayan karin, ni dai na gaji wllh….” Zainab ta bude kofar parlon tana kallon Barrister tace “Bismillah” Da
sallama ya shigo parlon, Kaka ta saki baki tana kallonsa da mamaki, har ya karasa cikin parlon kallonsa take baki
bude, ya xauna yyi kasa da murya yace “Ina kwana Baaba” Kaka ta rufe bakin tace “Ikon Allah, to batan hanya kayi
Amadu koko xuwa kayi ka kawo mana tashin hankali a nan muna xaman xaman mu?” Ya girgixa kai yace “Aa na
dai xo ne in gaishe ki” Kaka tace “Ni a wa?? Iyye? Nace ni a wa xaka xo gaisheni, dama ka hada abu da nine bani da
labari?” Shiru yyi bai ce komai ba, tace “Toh bbu ruwana kada ma raina ya baci ka tashi kayi ta kanka” Yyi kasa da
kai yace “Aa kiyi hakuri nayi tafiya ne, aiki yyi min yawa….” Kaka tace “Ayyoo, Allah sarki…. Yawan aikin ne ya sa
ka saki Rakiya kenan ashe?” Abba ya kalleta yace “Aa ni ban saketa ba” Kaka tace “Ohh don baka da kunya karya
xaka yi a gabana? laifi kan laifi, me wnn baiwar Allah tayi maka da xaka yi mata wannan d’an banxan cin mutuncin,
da girmanta da k’imarta da dukiyarta ka walakanta ta haka Amadu??” Sai kuma ta fashe da kuka Abba yace “Ni fa
wllh ban saketa ba Baaba” Kaka ta dakatar da kukan da take tace “Ko dai wiwin kai ma ka fara sha, ka saki mace
kace baka saketa ba sbda lalacewa ta same ka?” Yace “Wllh nace ban saketa ba dama tana da niyyar tafiya ne kawai”
Sake baki Kaka tayi tana kallonsa, can ta kwalo ma Zainab kira ta fito daga kitchen da sauri, kaka tace “Tafi sama ki
kira min Rakiya” Zainab na dawowa tace “Tana xuwa kaka” Kaka tace “Toh gwara dai ta xo” Har bayan minti goma
Mami bata sakko ba, kaka ta sake mayar da Zainab, Zainab ta dawo tace tana bandaki, kaka ta mike tace “Toh ai ba
komai bane idan ni na tafi na kirata da kai na, bbu wanda xai maidani karamar mutum daga ita har Amadun” Mami
bata iya yi ma kaka musu ba bayan ya shigo dakinta, ta mike ta bi bayanta suka fita, kaka ta juyo tana kallonta tayi
kasa da murya tace “Anya Rakiya ba a siyar da wiwi gun aikin ku kuwa?” Mami tace “Me ya faru?” Kaka tace “Da
kyar idan ba wani ya fara tusa masa ra’ayin abun ba, naga kamar ba a saiti kansa yake ba, gashi yaki yadda mu hada
ido, kuma alamar maganarsa bbu la’asar ko kadan, gatsau gatsau yake min” Mami tace “No ba gun aikin mu daya ba
ai” Kaka tace “Ikon Allah….” Har sannan Abba na xaune parlor, Mami dai bata karasa ciki ba, kaka ta xauna tace
“Toh maimaita abinda kace kan Rakiya Amadu” Abba yace “Nace ban saketa ba” Kaka ta kalli Mami tace “Ke kinji
dai ko?” Mami tace “Ehh haka ne” Bude baki kaka tayi tana kallonta, can tace “Ban gane ba” Mami tace “Bana
auren ne kawai, kuma ya saurari sammaci nan ba da dadewa ba, tunda ya ki bani takardata ta lumana” Kaka tace
“Oh oh Allah na shiga uku, kina da hankali kuwa Rakiya ko kema kin fara shaye shayen ne, dama bai sake ki ba
kika tattara kika yi tafiyar ki sbda rashin tsoron Allah?” Mami tace “Bana auren ne kaka shi yasa na tafi, na kuma
masa magana ya bani takardata ya ki bani, don haka kinga kuwa dole in kai batun gaba” Kaka tace “A ina kika gansa
kika yi masa maganan?” Mami tace “Na tura masa message severally…” Abba dake ta kallon Mami yace “Okay xan
baki takardar ki kamar yanda kika bukata but sai mun ajiye yarjejeniyar bbu ke bbu Heedayah, ki cire hannun ki kan
lamarinta….” Mami ta dakatar da shi tace “Sorry to say, wannan ne kuma baka isa ba barrister, baxan yarda da duk
wani abu da xai cutar da ita ba don xamanta gidanka bbu abinda xai haifar sai cutar da yarinyar” Abba yace “Okay
then, kema ki saurari sammaci” Mami tace “I will welcome that gladly” mikewa yayi yana kallon kaka da ta kasa
cewa komai ta saki baki tana kallonsu yace “Na gaishe ki Baaba” daga haka ya nufi kofa. Salati kaka ta saki tace
“Naga abinda ya isheni ni Patuu, me xan gani haka, ke Rakiya ashe dama auren ki ba mutuwa yyi ba kika tattaro
kika dawo nan, meye a takardan da kika ce kin gani parlon na ki to?” Mami tace “Aa ba wani abu bane, amma baxan dauka ba Kaka, ya bani takardata kawai bana auren dama sbda in ceci rayuwar wnn baiwar Allah na amince muka yi
xaman aure da shi, amma tunda cin mutunci ya fara shigowa to baxan iya ba kuma baxan dauka ba, ni ba yarinya
bace da xan tsaya ina kishi ko wani tashin hankali a kan namiji kuma, sannan duk abinda xai yi yayi amma Wlh tllh
baxan basa Heedayah ba, tsaf matarsa xata iya kasheta ya rufe case din bbu wanda ya sani, kinga kuwa bai cancanci
riketa ba” Kaka tayi tagumi tace “Naga abinda ya isheni ni dai, toh ni duk ba wannan ba yanda ya shigo yana mana
magana gatsa gatsa ne ya dameni yanxu, bbu fa wani rusuna da yyi da wnn lamarin, sannan tunda ya san bai sake ki
ba kuma ya xo ya tarar baki gidan ai ya kamata ya bi ki duk inda kika tafi ya ji dalilin tafiyar ki, Anya Amadu kansa
daya kuwa?? Sannan ya shigo gaisheni bbu bada hakurin rashin gaisheni da bai yi ba na kusan shekara daya bbu
alamar nadama a tare da shi kwata kwata” Mami dai bata ce mata komai ba ta tafi kitchen kawo mata breakfast. Sai
da kaka ta cinye kayan cikin tass sannan tace “Ni dai Rakiya kiyi hakuri ki rufa ma Amadu asiri ki rufa min asiri, ki
rufa ma Deedayah asiri kada ki kawo masa sammacin nan, Allah xai daidaita ku in sha Allahu tunda ke dai ba ki
nufin kowa da sharri….” Mami tayi murmushi tace “Kiyi hakuri kaka, amma Wllh wllh kinji har na rantse na gama
auren barrister, sannan ya gama rikon Heedayah, sai dai idan ba Barrister Rahinah bace ni” Kaka tayi mata wani
kallo tace “Ka ji tsiya da wasali, to ai shi ma Amadun ba kyalle bane, sai dai ku yi ta gogawa daga karshe ya nanaki
da kasa a banxa kawai, ta ina xa ki rabasa da Deedayah da yyi ta wahala da tun tana makauniya, a ta dalilinsa fa kika
santa, Anya kina tsoron Allah kuwa Rakiya” Mami tayi wani dariya tace “Sai dai ni in nana shi da kasa kaka don na
fi sa gaskiya, kuma In sha Allahu Heedayah baxata sake xama gidansa ba, ta gama xama tare da shi kenan har abada,
har Allah ya bayyana iyayenta idan suna da rai….”Kaka ta daga hannu tace “Toh ni dai ba ruwana, wnn ai kunyata kan ku xa ku yi a idon duniya kawai, meye kuma
fada a kotu a kan yar yarinya da ba ku hada komai da ita ba?? Idan haka ne a raba gardama a mayar da ita dai dai
gun da aka daukota a ajiye, ko kuma a bani hotonta in baxama duniya neman Yan uwanta idan ma iyayenta mutuwa
suka yi ai baxa a rasa yan uwanta ba, son xuciya ya hana Amadu yin haka, bamu san nufinsa a kanta ba gaskiya”
Mami dai bata ce da kaka komai ba tana danna wayarta. Tun da Heedayah ta tashi yau take murna xa su tafi gida
sbda hutun second term da suka yi, duk suka gama hada kayan da xa su mayar gida tare da Farida, bayan azahar aka
xo daukarsu, tsaye su ka gansa jikin motarsa ya rungume hannu, ganinsu ya bude masu booth, suka xuba kayansu
ciki, Farida na kallonsa tace “Ina yini Yaya” yace “Lafiya lau” Heedayah ma ta gaishesa ya amsa yana kallonta suka
shiga back seat gaba daya, ya shiga motar suka wuce gida. Farida ta gama hada ma mai aiki kayansu gaba daya da
na Heedayah tace “Idan ma baxa ki iya gugan ba idan kin wanke ki bari xan saka Yusuf yyi mana, pls ki wanke
mana da kyau sis Zainab” Muryar Mami suka ji daga sama tace “Zainab bar masu kayansu, idan baxa su wanke ba
su bar shi, kada kiyi ma ko wani yaro wanki a gidan nan” Farida ta juya tana kallon Mami kamar xata yi kuka tace
“Mami jiya fa muka dawo ko hutawa ba mu gama yi ba, sannan I have a lot to read for my coming waec” Mami tace
“Kar ma kiyi karatun mana, na dai gaya maki Zainab, kuma kada ku sake ku dawo min da kayan wanki sama, daga
nan parlor ku yi waje da shi” daga haka tayi komawarta daki, Zainab dai na tsaye bata ce komai ba, Farida ta tabe
baki ta kwashe kayan a fusace tana kallon Heedayah da ta kwanta saman dogon kujera jin abinda Mami tace, tace
“Toh baxa ki tashi mu je mu yi ba” Heedayah ta marairaice tace “Farida wllh I am not feeling well kema kin sani”
Farida tace “Yes I know but ki taso sai ki dinga dauraya ni sai inyi shanya, if not ni dai baxan maki wanki ba” Turo
baki Heedayah tayi Farida ta fita can compound da kayan, Mikewa Heedayah tayi ta dau hularta ta saka don
doguwar riga ce har kasa jikinta ta bi bayan Farida xuwa waje, Farida har ta tara buckets din a tap dake tsakar gidan
xata fara wankin, Heedayah ta xauna saman Plastic chair, Wanki Farida ta fara yi duk rai ba dadi, ganin ta wanke
yafi biyar Heedayah ko motsawa bata yi daga xaunen da take ba, ta fara ware kayan tana maida na Heedayah gefe
daya, dariya Heedayah tayi ta sakko tace “Toh yi hakuri Faree” Kamar warce bata da laka ta dinga shafa kayan wai
tana daurayewa, ta marairaice fuska, sun yi nisa a wankin aka bude gate duk suka juya, sosai gaban Heedayah ya
fadi bayan sun hada ido, Farida ta dauke kai ta ci gaba da wankin da take yi, slowly yake tahowa sanye da kananun kaya, ya sa face cap, camouflage na Soja” Heedayah ta saci kallonsa ganin ya kusa inda suke suka kara hada ido don
kallonta yake, sunkuyar da kanta tayi, Farida tace “Good evening” Yace “Evening, Mami na ciki?” Farida tace “Ehh”
murya can kasa Heedayah tace “Ina yini” yace “Lafiya lau” daga haka yyi wucewarsa ciki. Mikewa Heedayah tayi
bayan wasu mintuna ta xauna tana girgixa kai tace “Wllh Farida cikina ciwo yake min” Farida tace “Dama fa babu
abinda kike min a nan Didi, you can go in and stop pretending pls” Heedayah bata ce mata komai ba, ta rike cikinta
da ta ji yana murda mata, Farida tace “Nace ki wuce ciki kawai, don’t worry by the time na yi waec next month xan
ga wanda xai dinga maki wanki a schl” Mikewa Heedayah tayi tsaye da kyar ta nufi cikin gida tana cewa “And don’t
forget also ss2 xan yi waec” Farida bata tanka ta ba, tana duddukawa ta shiga parlor ,Mami na xaune parlorn tare da
Shuraim, “Jiya na dawo” Cewarsa kenan yana duban Mami, Mami tace “Amma kaka tace min kana nan mun yi
waya da ita few days back” Yace “Aa, Ina Abuja and bata sani ba” Mami tace “Can kake aikin?” Yace “Aa nan
Kaduna, Ina 44, mun je aiki ne Abuja…” Mami tace “Maa sha Allah, it’s been long Shuraim” Ya cire face cap dinsa
ya d’an yi murmushi yace “Haka ne” Heedayah ce ta shigo parlon, Mami tace “Meye haka? Me ya faru” Da kyar tace
“Mami cikina” Mami tace “Me ya sami cikin?” Ta nufi sama tace “Ciwo yake min” Mami ta bi ta da kallo har ta
wuce sama sannan ta dawo da dubanta kan Shuraim, ya sauke idonsa daga kallon da ya bi Heedayah dashi shi ma,
Mami ta kwalo ma Zainab kira, ta fito daga dakinta, Mami tace “Ki kawo ruwa” Shuraim yace “Noo I am okay…”
Mami tace “Ki xubo har da abinci” Tana fadin haka ta mike ta wuce sama xuwa gun Heedayah, dakinsu ta shiga ta
ganta durkushe a kasa ta rike cikin tana hawaye, Mami tace “What did you eat?” Cikin kuka tace “Nothing, tun a
schl yake min ciwo wani lkcin” Mami tace “Toh kwanta in samo maki magani yanxu” Kwanciya tayi saman gadon
tana goge idonta, Mami ta dawo parlor ta dau wayarta xata yi kira, Shuraim yace “Is she okay?” Mami tace “No
Ciwon ciki take tun a schl, so ina son in aiki driver ya karbo mata magani a pharmacy…” Tana magana ta nufi kofa,
Shuraim ya bi ta da kallo yace “But Mami asibiti xai fi ai” Mami ta dawo tace “Au, ai na mance you are also a Dr,
kayi mata prescribing maganin mana yaje ya amso mata” Shuraim yace “Ban san wani irin ciwon ciki bane” Mami
tace “To mu je ka tambayeta” tashi yyi ya bi bayan Mami xuwa dakinsu, Kuka Heedayah ke yi sosai saman gadon,
Mami na shigowa dakin tace “Wayyo Mami it’s paining me ni baxan iya ba” hankalin Mami ya fara tashi tace “Toh
ko dai mu tafi asibiti” Karasowa dakin Shuraim yyi yana kallon Heedayah, Mami tace “Bari kawai mu tafi asibiti
Shuraim, let me get my Hijab” daga haka ta fita, Da sauri Heedayah ta sauka saman gadon ta toshe bakinta ta shiga
bathroom ta hau kwarara amai, Shuraim ya dinga kallon saman xanin gadon da ta tashi, can ya juya ya fita daga
dakin, ko da Mami ta dawo dakin Heedayah bata fito bandaki ba, Mami har xata shiga bandakin jin amai take idonta
ya sauka saman gadon, ta kalli kofa da sauri ta karasa ta cire xanin gadon, ta wuce bandakin, Durkushe ta sameta a
ciki, Mami ta ajiye xanin gadon hannunta kan washing machine ta dagota tace “Sannu Daughter” Da kyar tace
“Mami xan kwanta” Mami tace “No, u are stained” Heedayah ta kalli jikinta da sauri, a hankali Mami tace “Kin ta6a
yi a schl ne?” Heedayah ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, Mami tace “Talk to me dear, kin ta6a yi?” Girgixa
mata kai Heedayah tayi ba tare da ta dago ba, Mami tace “Ohk this is ur first time?” nan ma ta gyada kai kawai,
Mami tace “But you know what it is right?” Nan ma dai Heedayah kanta a kasa tace “Uhn” Mami tace “Toh ina
xuwa” Mami na fita Heedayah ta sake kallon jikinta sannan ta kalli xanin gadon da Mami ta kawo bandakin,
Shuraim ne ya fado mata ta hadiye abu da kyar, duk da axaban da take ji fata take he didn’t see anything, a haka
Mami ta dawo bandakin rike da pad da pant, Mami tace “Kiyi wanka tukun, hope kin iya sa pad din?” Heedayah ta
sunkuyar da kai tace “Uhn” Mami tace “Toh yi wankan ki gama” fita Mami tayi ta bar bandakin, A parlor ta tadda
Shuraim, Ta xauna tace “Heedayah ta fiye raki ne, idan cikin bai lafa mata ba sai mu tafi asibitin, na bata wani
magani ynxu” Shuraim yace “Allah ya sauwake” Mami tace “Ameen” Mami tace “Ka ci abincin mana” Yace “I am
full” Bude kofar parlor aka yi Junaid ya shigo, Sau daya ya kalli Shuraim ya kauda kai, ya gaida Mami xai wuce
sama Mami tace “Baka ga Shuraim bane Junaid” Junaid ya juyo ya kallesa, kamar sannan ya fara ganinsa yace “Ohh
I didn’t notice” karasawa yyi ya basa hannu suka gaisa briefly Junaid ya wuce sama Shuraim ya bi sa da kallo, Can
kuma ya kalli Mami yace “Tayi bacci ne?” Mami tace “Ohk let me check” Tashi Mami tayi ta bi bayan Junaid, bakin
kofar dakinsu Farida ta gansa a tsaye, kafin ya bude kofar tace “Kayi ajiya ne a ciki??” juyowa yyi da sauri ya fara
kame kame yace “Noo, emm dama xan amshi wayata ne” Mami na kallonsa da kyau tace “Nace bana son kana
shigar masu daki haka, I have warned u severally Junaid” Bai ce komai ba ya juya ya wuce dakinsa, Mami ta karasa
ta bude kofar ta shiga, a gaban madubi taga Heedayah daure da towel ta duka, Mami tace “Sannu, ki saka kaya in
baki magani” Heedayah ta dago a hankali tace “Mami ciwo yake min sosai” Mami tace “Xai daina in sha Allah”
Mami ta fiddo mata kayan da kanta ta ajiye mata sannan ta tafi dauko mata pain relieve, Kwanciya tayi saman gado
bayan ta saka kayan, Mami ta dawo dakin da maganin da bottle water ta bata ta sha tace “Tashi in shimfida maku
wani bedsheet” Heedayah ta sauka ta durkusa a kasa, Mami ta shimfida xanin gadon sannan ta sa ta kwanta. Karfe
Takwas na dare Mami ta sa Farida ta tafi ta kira Heedayah ta xo ta ci abinci, tun yamma tana daki, gani take kamar
Shuraim na nan har lkcn, ba komai ke damunta ba sai xanin gadon da take tunanin kila ya gani, Farida tace “Ya jikin
Didi?” Heedayah ta langwabar da kai a hankali tace “Da sauki” Farida tace “Allah ya sauwake, Mami tace ki sakko
ki ci abinci” Heedayah tace “I am not hungry Farida” Farida tace “Toh mu je ki gaya mata ni ba ruwana, she said I should call you” Heedayah ta d’an yi shiru, can tace “Is Shureen still around” Farida tayi dariya tace “He is Shuraim
not Shureen, baya nan ya wuce tun daxu” Heedayah ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya, sakkowa tayi daga kan
gadon tana kallon xanin gadon da jikinta, Farida ta kara fashewa da dariya tace “Toh ai idan kina haka xa ki sa a
gane, just pretend, it’s nothing, sannan ai kin canxa pad ko?” Heedayah ta gyada kai, Farida tace “Toh mu je” Bin
bayanta tayi suka fita, gaba daya a tsarge take da kanta, Junaid na xaune parlor yana shan fruit salad suka shigo,
Mami tace “Ga abinci Heedayah, if you want fruit sai Farida ta yanka maki” Heedayah dai bata ce komai ba ta xauna
saman carpet a hankali tace “Ina yini Yaya” Junaid dake ta kallonta yace “Lafiya lau, u slept all day” Ita dai bata ce
komai ba, Farida ta debar mata abincin ta ajiye gabanta, Junaid da sai kallonta yake ya kalli Mami yace “Mami is
she sick” Mami tace “No, just slight headache magani ta sha shine take ta bacci” Yace “Ohk” Mami ta ci gaba da
danne dannen laptop dinta, A hankali Heedayah ke cin abincin, da ta daga kai sai ta ga Junaid na kallonta, duk sai ta
takura, ta gama cakalkala abincin ta mike ta wuce kitchen, satan kallon Mami da hankalinta ke kan abinda take yyi,
ya mike a hankali ya dau Glass bowl din da ya ci fruit salad, Farida dai na kwance saman three seater tana danna
wayarta, Kitchen ya nufa ya bude kofar ya shiga ya rufe, Heedayah ta juya da sauri, ya karasa inda take tsaye xata
hada shayi ya tsaya bayanta yace “What wrong Heedayah?” Kasa cewa komai tayi tana girgixa masa kai, ya kamo
hannunta yace “Talk to me plss are you sick” Kamar xata yi kuka tace “Yaya… Mami fa fada xata min, ka tafi plss,
she can come in now” Juyo da ita yyi suna facing juna still holding her hands yace “Ki gaya min kukan me kika
yi…” Ta xaro ido tana kara kallon kofar kitchen din tace “Aa ban yi kuka ba” Yace “Ur eyes are swollen” Tace
“Baccin da nayi ne, Yaya don Allah ka fita Mami xata min fada sosai” Bude kofa aka yi, ya saketa ta juya da sauri
har wani rawa hannunta yake, Farida ce tsaye bakin kofar kitchen din tace “Heedayah Mami na kiran ki” Heedayah
tace “Toh” bata bi ta kan shayin ba ta bi bayan Farida da sauri, Junaid ya bi ta da ido har ta fita sannan ya ci gaba da
hada mata shayin, Suna shigowa parlor Mami ta dinga yi ma Heedayah wani kallo, Heedayah ta sunkuyar da kanta
tace “Na kai plate ne kitchen” Mami tace “So? sai aka ce ki dau ages kafin ki fito kitchen din?” Ta girgixa kai kawai
ta xauna kasan carpet, fitowa Junaid yyi da cup din shayin, ko kallonsa Mami bata yi ba, ya iso cikin parlon ya mika
ma Heedayah cup din, Mami tace “Wani ya sa ka hada mata shayi?” Yace “No ta fara hadawa ne ta fita shine na
karasa mata” Heedayah ta amshi shayin tace “Nagode” Mikewa tayi tace “Mami sai da safe” Mami tace “Ki sha
magani kafin ki kwanta” ta amsa da “to” sannan ta wuce sama. Har karfe sha daya Heedayah bata yi bacci ba cikin
na damunta sosai, Farida tuni tayi bacci bayan ta gama phone call, Heedayah ta mike xaune ta sauke kafarta daga
kan gadon ta goge guntun hawayen idonta, tashi tayi ta nufi kofa sbda wani shayin da take so ta sha, ta bude kofa a
hankali ta fita don in Mami taji fitowarta baxata yrda ta hada wani shayin ba, sauka tayi downstairs, ta shiga kitchen
ta kulle kofan, daxu ruwan flask din ba shi da yawa sai ta daura wani a gas, ta kunna gas ta sa ruwa kadan aka bude
kitchen din, a tsorace ta juya, junaid ta gani, ya shigo kitchen din ya kulle, tace “Yaya baka yi bacci ba” Yace “Yea,
another tea?” Ta kirkiri murmushi bata ce komai ba, ya karasa kusa da ita yana kallon lashes dinta da ya d’an jike da
hawaye, da damuwa yace “Ki gaya min me ke damun ki Heedayah” Tace “Ba komai Yaya, amma kar Mami fa ta
shigo nan yanxu” Yace “Ga hawaye idonki kice min ba komai” Matsawa xata yi daga kusa da shi ya rikota, kamar
xata yi kuka tace “Yaya ka bari pls” Yace “Toh gaya min kukan me kike” Tace “Cikina ke ciwo” ya xaro ido yace
“Cikin ki kuma? Tun yaushe? And did you take drug?” Kafin ta ce komai ya kai hannu cikin nata, ta xaro ido xata
durkusa ya rikota, ta hade rai tace “Yaya bana son haka” yace “Tun yaushe cikin ke maki ciwo?” Tace “Da safe”
yace “Kin sha magani?” Tace “Mami ta bani” Cike da tausayinta yace “Sorry Lolly” ta xuba mashi ido kawai, yace
“Har yanxu yana ciwon kuma” hawaye ya kawo idonta ta gyada masa kai, yace “Toh ya yake maki?” Tace “I don’t
understand the pain too” kashe gas din yyi sbda ruwan ya tafasa, ya hada mata shayin da kansa yace “Toh mu je ki
sha shayin sai in baki magani” ba musu ta shiga gaba ya bi ta da kallo, doguwar riga ne fari irin na bacci jikinta sai
hulan dake kanta, ya dinga kallonta ganin xata juyo ya kauda kai ya tafi switch din wutan kitchen din xai kashe,
xaune ya sameta parlor tana fiffita shayin da spoon, ya karasa Inda take ya xaune gefenta yyi kasa da murya yace
“You know what?” Ta girgixa masa kai, yace “Kawo in fifita maki shayin ki tafi daki ki canxa kayanki ki dawo”
kasa cewa komai tayi tana kallonsa, ya sakar mata lallausan murmushi, da kyar tace “Me ya samu kayana?” Yyi kasa
da murya yace “You are stained” still tayi tana kallonsa da idanuwanta kamar xa su yi magana, yace “Tashi ki tafi”
Ta sauke kanta kasa, ba karamin courage tayi gathering ba sannan ta mike ta wuce sama da sauri ya bi ta da kallo,
tana shiga daki bayan ta gyara jikinta ta kashe wuta tayi Kwanciyarta. Washegari bata yadda sun hada ido da junaid
ba da ya hade rai yana bin ta da kallo a parlor, Atamfa ne jikinta riga da skirt ta yafa dankwalin a kanta, ban da
Mami da ta aika Farida kiranta in d’an ta ita ne ma baxata sakko ba yau baccin kirki bata yi ba jiya sbda stain din da
Junaid yace tayi, ji tayi gaba daya kunyarsa ma take, shayi ta hada ta xauna nan parlor tana sha a hankali da dankali,
Farida da Zainab na kitchen suna gyare gyare, Mami kuma na xaune parlon tana waya, Mami na gama wayar tace
“Heedayah anjima sai ki raka Farida supermarket ku siyo mana spices, bana son kwanciyan nan da kike yi, ku je a
Napep idan xa ku dawo ku yi strolling you will feel strong” a hankali Heedayah tace “Toh Mami” Mikewa Junaid
yyi ya wuce sama, Mami ta bi sa da harara don tana lura da kallon da yake ma Heedayah. Hijab har kasa Heedayah
ta saka don gani take ko jingina tayi by mistake da abu sai tayi staining mutane sun gani, Farida dai ta saka abayarta da veil ta dau karamar jakarta suka fita, adaidaita sahu suka samu xuwa shopping mall din bayan duk sun gama
siyayyar su, har da guzurin turare duk cikin kudin Mami suka fito shopping mall din, da kafa suke tafiya kamar
yanda Mami ta umarce su, Heedayah dai sai yatsina fuska take don gaba daya bata son tafiyar…..