NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 8
______Shi kuwa Farooq tsabar mamaki sai mutsuka ido yake yana budewa gani yake kamar a film yake kallon su.
can Daddy ya numfasa yace “dama kai niki jira yanzu nike cewa Umar yaje ya kira min ku dan lokacin tafiya ta yayi”.
“Siddeeqah”. Daddy ya kira suna na cikin wata murya mai nuna ana jin tausayin wanda akai wa ita”.
“na’am” nima nace bayan na zare hannu na daga jikin yaya na daga kai muka hada ido da shi
Ya cigaba da cewa “shin kin amince zaki tafi makarantar kwana?”.
Ina wasa da yatsaun hannu na nace “eh na amince Daddy”.
Sai alokacin Momy dake tsaye ta zauna tana fadin “Alhamdu lillah Allah yasa hakan ne yafi alkairi”.
Take yaya Sadeeq ya sauke ajiyar zuciyar da ko wannen mu sai da ya dago kai ya kalle shi, ni kuwa takaici ne ya kamani ganin yadda yake murna zai rabu dani sai kace zai rabu da musifa, lallai ma yaya tabbas zan nuna maka nima macace kuma zan iya yin duk wani abu da mata suke yi wajen burge mazajen su, sosai nayi nisa cikin tsara yadda abubuwa zasu kasan ce, fir gigit nai a dan tsorace na dawo hayyaci na sakamakon tabani da kafa da yaya yai.
Daddy yace “Siddeeqah lafiya tunanin me kike yi haka? bayan na hana ki yin dogon tunani irin wannan, kina yar karamar ki Ko so kike hawan jini ya kama ki? Ki mutu tun kamin lokacin ki yayi?”.
Baki na narawa nace “A a Daddy insha Allah na daina daga yanzu”.
Yace “Masha Allah, Allah yai muku Albarka ni zan tafi ki kula da kanki banda kula kwayen banza karatu ne ya kaiki shi zakiyi “
Nace “to Daddy nagode insha Allah bazan baku kunya ba”.
Sai da ya sallami duka yaran gidan, dama Momy ya ruga ya sallame ta, kana yabi ko waccen mu da kudi masu kauri, Gaba dayan mu muka dunguma zuwa harabar gidan saboda muyiwa Daddy rakiya saida muka ga tafiyar shi sannan muka dawo gida, Momy ta daura daga inda Daddy ya tsaya nasiha take min mai ratsa zuciya jiki na duk yai sanyi, son Momy da kaunar ta yana dad’a ratsa ilahirn jiki da bargo na, saboda yadda take kula dani, da nuna min so da kauna.
Bayan ta gama min nasihar tace “naje na kara shiryawa”.
Kallon Ummi da Khadija nai muka hada ido naga jikin su yai sanyi Umar kuwa harda kwalla, jiki na a sanyaye na mike na haura sama ba wani wankan na sake ba kaya kawai na sauya i zuwa riga da sikel na atamfa dinkin bai min yawa ba kuma bai kamani ba, sannan na dauko hijabi na nasaka ko da na sauko a tsaye na samu Yah Sadeeq da Farooq da wani katon akwati a gaban shi, yana Murmushi yace “yauwa muje ko, ke muke jira”.
tuni kwalla ta fara wanke min fuska ta nace “amma yaya baka kira min Inna ba”.
Shafa keyar sa yai yace “ai na manta gwara da kika tuna min”.
Hannu yasa a aljihu ya ciro wayar sa, amma sai ya rasa wa zai kira sanin Inna babu waya a hannun ta dama da ta Farooq suke gaisawa “saida ya dan bata rai yace “kina da rigima Siddeeqah sanin kanki ne Inna bata da waya”
Goshi na dan dafe, tuna cewar batada wayar.
Yace “amma dai ki bari zan san abin yi tunda ni yau zan koma zan baki number ta idan kinje makarantar sai ki bama wata senior ta kirani sai na hada ku kuyi magana”.
“to” kawai nace
har bakin get su Momy suka rako ni, in rungume wannan in saki wannan haka dai nan ta kuka Khadija da Ummi da Umar suna tayani, yayin da Momy ke bamu hakuri kamar kar mu rabu da juna saboda sabon da mukayi, sabanin Jiddah da ko Allah ya kiyaye hanya bata ce ba sai kallon banza da take bi na dashi, tana cika tana batsewa, yi nai kamar ban gan ta ba saboda yanzu ba lokacin fada bane a gurina.
STORY CONTINUES BELOW
Da kyar yaya ya lallashe ni na shiga mota inajin raina babu dadi, tuni daman yah Farooq ya shiga sannan shima sadeeq din ya shiga mai gadi ya wangale get muka fice, su Momy nayi mana Allah ya sauke ku lafiya.
Yaya Farooq ne ke tukin yayin da Sadeeq ke kujerar me zaman banza ni kuma ina gidan baya ji nike gabad’aya rayuwar ta dagule min tafiya ta fara yin nisa dan barci har ya fara dauka ta
* * * * * * *
Zaune take kan dan madaidaicin gadon ta hannun ta rike da wayar ta sai cije lebe take tana tsaki wai ita Sadeeq zaiki dagawa waya to wallahi bai isa ba tun da yace yana son ta sai ya aure ta ta fada afili yayin da tayi kwafa.
Number Lubansy ta danna ta kira har tafara ringing sai kuma ta kashe saboda tasan itama fushi take da ita baza ta d’auka ba idan tana son su shirya sai dai fa ta shirya taje gidan su, gashi ita kuma yanzu bata jin zata iya fita saboda zuciyar ta babu dadi, safa da marwa ta cigaba da yi gabad’aya ta rasa me zatai, can ta tuna da group din su na madugo aran ta yltace “bari na dan hau online ko na samu na rage damuwa” gefan gadon ta zauna kana ta dauko wayar ta shiga cikin whatsapp din nan ta tarar da sakonni masu yawa amma duk bata tsaya bi ta kansu ba, abinda ya kaita kawai shi take so tayi, bayan ta shiga cikin group din a hankali tafara karanta sakonnin da akayi bata nan bata jima tana duba chart d’in ba ta fahimci cewa fada a keyi sakamakon wata da tayi left cikin sauri da sauri ta cigaba da duba sakonnin har zuwa inda aka tsaya da firar take ta fahimci Baddy ce tai left kuma ana kyautata zaton yar leken asiri ce gabad’aya hankulun officials da members din gidan a tashe yake saboda idan asiri ya tonu ba karamin yaki za ai ba, tuni Zuby ta shiga cikin firan inda har take bada labarin tayi magana ma da yarinyar har take ce mata “hajiya Tubalas ce ta kawo ta”
Hajiya Tubulas da jin an ambace ta, ta shiga auna ashar tana cewa “kada ayi mata sharri ita yanzu ko wuqa a ka sa mata a wuya a kace ta siffan ta kammannin Baddy to sai dai a yanka ta dan bata san ta ba”.
Shugabar kungiyar madugo tace “ya kamata a hada meeting na gaggawa saboda a kawar da wannan gagarumar matsalar”.
Tubulas tace “gaskiya bazai yuyu ba saboda a cikin dokokin kungiya ba a meeting sai ranar litinin din da tazo a cikin karshen wata, kuma kunga yau talata 28 ga wata, nasan kunsan cewa karya doka daya ta wannan kungiyar dai dai yake da tonuwar asirin mu gabaki daya”.
Sai alokacin Turai ta tuna da wannan dokar kuma gaskiyar Tubulas ne karya daya daga cikin dokokin kungiya babban laifi ne dan har gwara su dauwama a cikin wannan tashin hankalin da suke ciki, amma abin dubawa anan shine wata uku da suka wuce duka watan bai kare da litinin ba, kuma da alamar wannan ba ba da litinin zai kare ba, tunda yau talata.
Duk kannin su sunyi na’am da batun Tubulas saboda haka suka ce a nemo wata mafitar amma haka sukai ta fama duk inda suka bi sai suga babu hanya
Zuby dai gajiya tai ta sauka daga online din tana mamakin yadda Baddy ta ci amanar su, tasan tabbas kungiya bazata bar ta a haka ba sai ta dauki mummunan mataki akan ta.
Kofar dakin ta taji ana bugawa da sauri taje ta bude ba tare da ta tambayi wanda yake buka kofar ba, koda ta bude Lubancy ce ta shigo tana wani shan kamshi bakin ta dauke yake da chingom tana taunawa yana kara kas-kas haka dai tai ta yamutsa baki tana yauki, bayan Zuby ta maida kofar ta rufe tazo ta rungume ta tana cewa “aminiya nayi missing din ki”. Lubancy taso sharewa amma saita kasa saboda a matse take tuni itama ta rungumo ta tana sauke ajiyar zuciya, basu tsaya wata wata ba suka shiga cire ma juna kaya suka fada kan gado suna nishi tuni suka fara shafe-shafen juna suna sauke ajiyar zuciya.
idan kida ya sauya, rawa ma canza ta ake yi ganin abin yafi karfi na yasa na fito daga dakin naja musu kofa, ina yi musu adduar Allah ya shirya su dan wannan dabiar bata mutanen kwarai bace wace irin musifa ce wannan da mace take neman yar uwar ta mace yayin da shima namiji yake neman dan uwan sa namiji, shiyasa annoba bazata rabu damu ba saboda aduk lokacin da akasumu saukar annoba to sabon Allah ne yai yawa akasa, kuma duk masu wannan dabiar a wuta zasu dauwama.
STORY CONTINUES BELOW
wa’iya zu billah.
* * * * * * * *
Yunwar da ta fara kwakular ciki nane ta tashe ni daga nannauyen baccin daya dauke ni na manta a mota nike saboda haka nai mika gami da yin juyi, ai kuwa cikin rashin sa’a na fada sakon mota inda ake saka kafafu, ihu na fara ina kiran sunan yaya da duk ya bi ya gaji sai mita yake wai Farooq baya gudu “. Shi kuma Farooq na cewa” in ba sama kake so na tashi ba ai wannan gudun ya isa “.
Ihu na ne ya katse musu firar su da sauri yaya ya juyo da kansa cikin motar yana fadin “subhanallah garin yaya haka ta faru maza tashi”. Ya karasa maganar yana zuro da hannayen sa da kyar na iya temaka masa ya daga ni, bayan na gyara zama na akan kujera nace “yaya wai har yanzu bamu kai ba ni na gaji yunwa nike ji”. Na karasa maganar cikin sigar shagwaba, nuna min Farooq yai yace “duk laifin shi ne kwata kwata baya sauri tafiya yake kamar wanda yake tsoran taka kwalta”.
Nace “to ni yaya yunwa nike ji”
Yace “to bari mu karasa can gurin ina kyauta ta zaton karamar kasuwa ce sai muje baza’a rasa abin tabawa ba”. Ya fad’a yana nuna min wani guri da nike hangan mutane
“To” Nace yayin da na hada kaina da gwuiwa ta
Ba mufi minti 7 ba muka karasa bakin gurin, kasuwa ce yar karama mata da maza sai zurga zurga sukeyi, yara da manya Farooq yace “banda abinka Sadeeq me zamu samu anan da zamu ci?”.
Yace “mu fita ahaka ba zamu gane ba kuma can ma kamar masallaci ne mayi sallar azahar gashi ma kamar ana kiran la’asar duka sai mu sauke nauyi,
Yah Sadeeq yace” ki zauna a mota bari mu fita mugani ko zamu samu abinci”.
Ban bashi amsa ba suka fita harda rufe motar
Basu wani jima ba sai ga Yah Farooq ya dawo da kwano a hannun shi da kwarya, bayan ya bude motar ya miko min na amsa, shi kuma ya juya
Koda na bude kwanon danbu ne na gani yaji gyada da zogale yayin da ita kuma kwaryar fura ce acikin ta me rai da lafiya
Ba tare da nayi bismillah ba na shiga cin danbun, duk da yawan danbun saida na kusan yin rabin shi saboda ina mutukar son danbu a rayuwa ta, bayan na koshi kuma na dauki kwaryar fura itama na fara sha saida naji na cika cikina dam, har inaneman gurin numfashi sannan na hakura ba don bakina ya koshi ba sai don cikina da ya koshi
Gyatsa nike so nayi kozan dan ji dadin ciki na amma taki zuwa saboda haka nai ta bude baki ina Jan iska
Can saiga su yaya nan sun dawo hannun Yah Sadeeq dauke da gorar ruwa bayan sun zauna yace “kin rage dan bun?”.
Nace “eh”.
“yauwa miko wa Farooq danni bazan ci ba furar zan sha ai itama kin rage?”
“eh nace yayin da na miko mai kwanon danbun dana furar
A mota suka ci bayan sun gama suka je suka mayar da kwanon da kwaryar
Daka bisani muka kuma daukar hanya
” Nace yaya amma dai mun kusa zuwa ko?”
” eh mun kusa bai fi sauran mu 30 minutes ba mu karasa, ya nuna min wata katan ga da muke ta shigewa yace “nan kinga duk makarantar ce, zaro ido nai nace” kai yaya gari guda haka “.
Yace” eh har tafi haka girma bari muje ki gani”.
Haka dai nai ta yiwa Sadeeq surutu yana biye min duk da fuskar sa babu wal-wala amma duk tambayar da nai masa yana bani amsa, a raina nike cewa “nasan yana tsoron nace na fasa ne shiyasa yake amsa min”.
* * * * * * * * * * *
Aban garen Zuby kuwa bayan sun gama sheke ayar su tashi sukai suka shiga wanka kamar kullum nan ma saida suka bata lokaci suna tsotse-tsotse kana suka fito fiskokin su dauke da nishadi suka shirya cikin wata doguwar riga me ruwan kwai tana da laushi matuka Lubancy tace “ina zamu yau?”
STORY CONTINUES BELOW
Zuby tace “gurin shakatawa man, yauwa naga baki hau online ba meyisa”.
Lubancy tace “banida data ne, wani abun ya faru ?”
Zuby tace “kwarai ma kuwa ina wannan yarinyar da kika sameni ni da ita jiya?”.
Tace “eh na tuna ta”.
Zuby tace “ashe yar lekan asiri ce yanzu haka tayi left a kungiya kuma ni fa cemin tai turai ce ta kawo ta ashe karya tai min”.
Lubancy tace “nifa shiyasa tun na kalli yarinyar naji batai min ba kwata-kwata kuma yanzu wani matakin aka dauka?”.
“Har yanzu dai ba’a samu mafita ba kasancewar wa’innan tsinannun dokokin kungiyar na aiki, ke nifa abun ya fara isa ta gashi yanzu wlh ina cikin damuwa” Zuby ta fada tana sauke ajiyar zuciya
Kusa da ita Lubancy ta matso ta ce “kawa ta me ke damun ki fada mun naji ko zan iya miki magani”.
Nan Zuby ta kwashe labarin komai yadda sukai da Abba ta fada mata hankalin Lubancy a mutukar tashe tace “da matsala gaskiya ya zama dole a fada wa yan kungiya saboda su taimaka mana da shawara kinsan a ka’ida ko aure kai baka daina wannan harkar da zaran ka bari kungiya zata tona maka asiri kuma kinga Maheer ba kalan mazan da zasu dauki raini bane”.
Gwauran numfashi Zuby ta sauke tace “wallahi kawa ta shiyasa duk na bi na damu amma dai mu dan jinkir ta kafin mukai maganar kungiya idan Abba ya dawo zan roke shi”.
Lubancy tace “to Allah yasa a dace”.
“Ameen” ta fada yayin da ta mike ta dauki katon hijab din ta gami da fiddo nikabin ta a jaka tace “kawa tashi ki shirya mu tafi”.
“To” Lubancy ta fada yayin da itama tai shiga kamar yadda Zubyn tai kana suka fito
Mama mama Zuby tai ta kwala mata kira daga can ciki Mama ta amsa
Zuby tace “kina ina ne Mama?”
tace “ina kitchen”
Shiga kitchen din sukai inda suka tarar da ita tana nuna ma mai aiki wani abun gasa kaza da aka siyo shi sabon yayi.
Fuskar Mama dauke da fara’a tace “sai ina kuma?”
Lubancy tace “wallahi Mama mun gaji da zaman gidan ne shine zamu fita ba jimawa zamuyi ba”.
Tace “to adawo lafiya”
“Allah yasa”.
* * * * * * * * * * *
Wangala-wangalan get yaya Farooq ya wuce guda biyu, kana yai tafiya marar tsayi a bakin wani guri yai farkin danaga an rubuta staff room, kasan cewar na iya karatu amma ban san ma’anar shi ba,
Shiru yadan ratsa mu kana yaya Sadeeq yace “mu sauka man”.
Yah Farooq ya fara fitowa sannan sai yaya Sadeeq, bayan ya fito yazo ya bude min kofa yace “fito mun kawo, bayan mun fito office-office mukai ta shigewa har muka isa wani office dan madai-daici, shiga mukai da sallama dauke abakin su yaya, inda muka sami wani malami a zaune da takardu a gaban shi yana ta dubawa, da alamar shine abokin yah Farooq ganin su yaya Sadeeq ya aje abinda yake, yah Sadeeq ya mika masa hannu, yana Murmushi ya amsa, hakama yah Farooq bayan sun gama gaisawa yai musu nuni da su zauna akan wasu kujeru da aka tanade su saboda baki,
Babu abinda nike sai zaz-zare ido ina kara shigewa yaya.take naji bazan iya zama a wannan dokar Dajin ba gaskiya to wai ma in banda abun mutane taya za azo dokar daji ayi gini ace wai makaranta, ni dai gaskiya bazan zauna ba.
Da turan ci malamin yai min magana, ban san me yake nufi ba yaya Sadeeq yace ” ya sunan ki yace?”
Nace “Siddeeqah Suleiman”.
STORY CONTINUES BELOW
Yace “suna mai dadi, ku tashi na raka ku ofishin shugabar makarantar”.
“to suka ce yayin da suka mike a tare, muka fito ina ta ganin dalibai na wucewa dai-dai haka, wani office din muka kuma shiga ba laifi ofishin babba ne kuma an dan kawata shi wata mata ce muka gani zaune akan kujera fuskar ta dauke da gilashi ba laifi matar ta dan manyan ta fara ce sosai kamar ka taba jini ya fito, dagani hutu ya zauna a jikin ta, tana da kyau dan irin doguwar fuskar nan gare ta tana da manyan idanu da dogan hanci ga dan karamin bakin ta, sanye take cikin kayan alfarma tana dan juya kan kujerar da take zaune, da Sallama muka shiga, fuskar ta dauke da fara’a ta amsa kana ta nuna mana kujeru tace mu zauna, tunda na kalli matar naji ina son ta ban taba haduwa da wanda naji ya kwanta mi arai lokaci daya kamar ta ba,
To aban garan Hajiya Aisha ma haka lamarin yake dan kuwa tana kallon Sadeeq da Siddeeqah taji gaban ta ya fadi, ga kuma kwarjinin da sukai mata har taji son su da kaunar su ya shiga ran ta.
Tana dariya tace “Malam Naseer suwaye wa’innan?”.
Yace “ai ranki shi dade sune wa’inda na miki maganar su wannan itace kanwar tasu da akai ma register”.
Tace “masha Allah” yan mata ya sunan ki?” Hajiya Aisha tai maganar tana kollon Siddeeqah
“Siddeeqerh” na bata amsa yayin da muka hada ido ta sakar min Murmushi tace “sunan ki babban suna ne kuma nima sunan yarinya ta babba ce”.
Nace “Ammi da gaske kema kina da yarinya me suna na?”.
Bani da na fadi sunan ba ita kanta Hajiya Aishan yanayin ta ya nuna taji dadin yadda na kira ta shi kuwa yah Sadeeq mamaki ne ya kama shi
Tace “da gaske nike yata amma a halin yanzu bama tare”.
Nace “to Ammi tana ina?”.
Idon Hajiya Aisha ne ya kawo kwalla ganin haka yasa yah Sadeeq yace “ke Siddeeqah ya isa haka kin cika tambaya”.
Jikina a mutukar sanyi nace “Ammi ki yakuri na daina”.
Handkerchief ta d’auka ta dan yi sama da glass din ta ta share kwallar data cika mata ido tace “babu komai yata”.
Ya Sadeeq ta kalla tace kai ya sunan ka?”. Nai sauri nace “Sunan shi Sadeeq yaya na ne kuma dashi Daddy ya daura min aure yace Wai alkawarin kanwar shi ne data…”.
“Ke!!!” Yah Sadeeq ya daka min tsawar da saida naji yayan cikina sun kada a tsorace na dago kai na kalle shi inda na hangi tsan tsar bacin ran sa ture ni yai daka kusa dashi ya tashi ya fita fuu kamar zai tashi sama.
Farooq yace “ranki ya dade ki yaquri haka yake zuciya gare sa”.
Hajiya Aisha da ke saka abubuwa bar katai a ranta tace “ba komai, amma abinda ta fada gaskiya ne dan ta tuna min da wani dana shima haka yake kamar wannan?”.
Farooq yace “eh gaskiya ne”.
Daga haka babu wanda ya kuma furta wata kalmar
Malam Naseer ta duba tace “Malam jeka dasu office din ka kaina ya fara min ciwo ka bata ajin da ya dace da ita”
“To” yace muka fito, yah Sadeeq na hanga acan jikin mota, harara ya wurga min nima na rama harda murguda baki, a zuciya ta nike cewa ba zai taba canzawa ba”.
Bayan mun zauna a office din
Malam Naseer yace “
“A jin ki nawa a makarantar da kika baro?”
Nace “Js 1”
“Shekarun ki fa?”
“sha hudu 14” na bashi amsa a takaice
Wata farar takadda ya dauko ya danyi rubuce-rubuce kana ya shiga yin magana da turanci yah Farooq na bashi amsa bayan sun gama ya miko min wata yar takadda yace “zan sa students su zo su tafi dake yanzu hostel din ku, dan yanzu dalibai suna aji ana karatu amma ke bazaki samu damar yin karatu yau ba saboda an kusa tashi “.
” to” nace bayan na amsa takaddar
Bayan mun fito da gudu na isa gurin yah Sadeeq na kan kame shi ina kuka nace “yaya yanzu tafiya zakai ka barni? saboda ba ka kauna ta, kalli fa kaga ni dai na fasa bazan iya rayuwa anan ba”.
Rage tsayin sa yai ya tsugunna yace “kowa da haka ya saba kema zaki saba karatu ne kuma ba’a samin sa a sauki saboda haka ki jure sannan banda rashin kunya dan akwai ban banci tsakanin makarantar kwana da ta jeka ka dawo, idan senior tace kiyi kiyi banda kin ji dan idan kika ce zaki rashin kunya wuya zaki ci”.
Hawaye ne masu zafi suka cigaba da wanke min fuska na kara rungume shi, yah Farooq yazo yace “sake shi Siddeeqah saki shi haka nan, ki hakuri ba wani jimawa zaki ba zaku tafi hutu”.
Ban sake shi ba na cigaba da kuka na “da kyar ya Sadeeq ya dago ni yana cewa” nace ya isa haka ki daina kuka muje na baki number na kuma insha Allah idan na samu lokaci zan zo na duba ki, kuma idan lokacin ziyara yai su Momy zasu zo”.
Nace “to yaushe ne ziyarar?”.
“an kusa”. Ya bani amsa yana Jan hannu na muka nufi gurin mota
Bayan motar ya bude ya fiddo wannan katon akwatin kana ya maida ya rufe
Yace “yauwa wannan shine akwatin ki duk abinda kike so akwai a ciki”.
Kanshi ya dan dafa yace “Farooq munyi mantuwa fa”
“ta me?”. Farooq ya tambaya
“Uniform din ta mana”.
yace “a haba na dauka ka dinka mata ne bari naje in karbo”.
Cikin office din da muka baro ya koma bai wani jima ba sai gashi ya dawo da leda a hannun sa
Wasu students ne guda uku suka zo inda muke da turan ci suka gaida su yaya suka ce Sir Nazeer ne yace muzo mu kaita hostel din ta, yah Farooq yace “to gata nan dan Allah amana ku kula mana da ita”.
“insha Allah suka ce”.
Kana ya Sadeeq ya ciro kudi ya bani nace “bana so yaya wanda Daddy ma ya bani suna gida na baro su”.
Yace “ki amsa ki nada bukatar su”.
Duk yadda yaso na amsa ki nai ba yadda ya iya wasu kudin ya ciro yabawa yan matan yace “wannan naku ne ku raba wannan kuma nata ne idan tanada bukatar wani abun sai ku bata”.
“To” suka ce yayin da suka shiga Jan akwati na
yah Sadeeq yace ce “to Siddeeq zo ki amsa number kada na manta mota ya shiga ya dauki memo da biro ya rubuta number ya miko min na amsa
yace” sai na dawo duba ki Allah ya bada sa’a”.
Ameen yah Farooq yace inda shima ya shiga mota hannu nai ta daga musu har saida naga sun Kule min sannan na daina na kalli wa’innan yan matan guda uku nace “ina zamu yanzu?”
Ba wanda ya tanka min suka cigaba da Jan akwatin da kamar na daina bin su sai dai nace bari naga gudun ruwan su
* * * * * * * *
_____Iska ce mai dadi take ta kadawa tako ina saboda yawan bishiyoyin gurin, dalibai sai zirga zirga sukeyi, can na hangi wasu dalibai su biyu durkushe akan gwuiwoyin su, wata budurwa ce mai Jan dan kwali ke ta zabgar su kamar ta samu bayi da alamar yaran da ake duka magiya suke a kyale su saboda naga sai daga hannu sukeyi alamun ban hakuri, sai da muka matso dab da wa’innan matan naga wata zabgegiyar bulala ce ta darbejiya a hannun mai dukan, take naji na tsane ta raina yai kuna zuciyata na yin radadi, yaran da ake duka duk sunyi laushi idan su ya furfuto waje, adai-dai inda mai dugan taje wa’innan yan matan da aka hadani dasu suka tsaya, ba shiri nima naci burki.+
Wannan firifet din tana ganin mu tayo kan mu tana dariya tace “sista Zamra daga ina haka”. bata lura dani ba, dan kuwa na dan boye a bayan daya daga cikin wa’inda aka hadani dasu
Wacce aka kira da Zamra tace “wallahi daga staff muke”
Daya daga cikin matan da muke tare tace “ke dai Jamlah kullum kina cikin duty ko gajiya bakyayi wallahi da akwai kanwar ki a makarantar nan sunan ta sorry dan ta gama kadewa”.
Wacce aka cewa Jamlah tace “hhhmmmm Saudat kenan ai shiyasa naki bari a kawo Sajida yanzu haka kano aka wullata”.
Wacce nike bayan ta ce ta goce sai alokacin Jamlah ta lura dani dago kai nayi muka hada ido take naji gaba na yai mummunan faduwa har saida na sa hannu na dafe kirji na saboda yadda yake buga min.
Ita ma a bangaren Jamlah kusan haka taji faduwar gaban, sai dai bai kai nawa bugawa ba kallon kallo mukayi har saida Wasilah tace “yaya dai Jamlah kin San ta ne?”.
Da sauri Jamlah ta dauke idon ta daga gareni tace “a a ban san ta ba naga dai tana kama da Wanda nasani ne”.
Zamra tace “koda naji dan new commer ce yanzu haka hostel zamu kai ta”.
Murmushi Jamlah tai daya kara fito da kyawun ta tace “yakamata ku han zarta kaita dan kuwa dole muyi mata welcome to……”. Bata gama karasawa ba Wasilah tace “wai ke Jamlah wace irin muguwa ce? na lura Sam bakya jin dadi idan baki ci zalin yayan mutane ba to wallahi wannan bazaki dake ta ba idan ko kika dake ta duk abun da ya faru dake ke kika ja ma kan ki”
Tana gama fada tajanyo hannu na muka fara tafiya ganin haka yasa senior Zamra da Saudat suka biyo bayan mu Jamlah taji zafin kalaman da Wasilah ta fada mata don haka ta kuduri aniyar ramawa tako wani hali ne dan ba’a yi yar da zata gaya mata magana ba, kuma saita daki bushashshiyar yarinyar taga uban waye ya tsaya mata da har suke taqama tasan indai kudi ne ba za’a fi uban ta ba, ranta bace ta wuce batare da ta kumu kallon wa’innan yaran da take duka ba.
Munyi tafiya mai nisa sannan muka zo bangaren hostel din wani dogon daki ne muka shiga ba laifi dakin yana da girma bashida wani fadi can amma akwai tsayi, gadaje ne ajajjeri ko wanne gado sama da kasa mun samu tsira run dalibai a ciki, mun danyi tafiya a cikin hostel din saida muka kusan zuwa karshen shi sannan muka tsaya a saitin wani gado hannu senior Zamrah ta dora a saman gadon ta taba tace “Alhamdu lillah wai me sunan ki ne?” nace “Siddeeqah”.
Sadaut na dariya tace “masha Allah sunan kanwata ne wacce take bina insha Allah zan kula dake kamar yadda zan kula da kanwa ta” sannan ta nuna min saman gadon tace “kin ga wannan gadon shine gadon ki” ta kuma nuna min kasan tace “wanna kuma na Fadila ne ita ce makociyar ki, wani dan soko ta nuna min dayake tsakanin gado da gado a gyare na ganshi tsaf kamar dakin amarya yaji ado da kyale kyale harda sif tace” nan kuma corner ce anan zaki aje akwatin ki naga baki zo da bokiti ba a kudin ki da yayan ki ya baki zan sa a siyo miki “.
STORY CONTINUES BELOW
To nace yayin da nafara taka matakalar da zan hau saman gadon ina dariya na dare abu na sai naji kamar mafarki nike saboda wannan sabuwar rayuwar.
Akwatin suka ajiye a cikin corner din sannan sukai min sallama suka wuce
Wata yarinya naga tazo ta zauna akan kasan gadon mu, hakan yasa naji ajiki na ita ce Fadila Saukkowa nai na mika mata hannun mukai musabaha tana dariya tace “sannu Sista ni sunana Fadeela kefa?” ta kare tambaya ta tana kama hannu na ta zaunar dani a bakin gadon ta
Bayan na zauna nace “nikam sunana ba na yayi bane ke nifa da ana canza suna da tuni na canza dan wallahi ji nike idan an kira ni kamar tsohuwa aka mai dani”
Fadeela na dariya tace “ba wani nan halan ma sunan ki yafi nawa fada min dai naji sai na yanke hukunci”
Nace “wai Siddeeqah fah”.
Rungumoni tai tace “sister sunan ki mai dadi wallahi sunan ya min sosai ina kuma son mai sunan, ke in takaice miki in Allah yasa nai aure na haihu sunan zan sama diya ta kin San ko saboda me?”
Girgiza mata kai nai alamar “a a”
Tace “saboda in faranta ma Ammi sunan babbar yarinyar ta ne data bata har yau mun kasa gano ta, ko dayike gaskiya ba wani bincike mukai ba, saboda ko maganar Ammi ba taso da anyi mata maganar duk annurin da yake a fuskar ta za kiga ya dauke, amma idan ka nutsu da kyau ka lura da yanayin ta zaka fahimci tana cikin damuwa lokuta da dama idan na kalli kwayar idon ta ina hango soyayyar diyar ta a tare da ita duk da kamin Daddyn mu ya rasu ta haihu dashi yan biyu mace da namiji yanzu haka zasu kai shekara bakwai kuma kasancewa ta marainiya gaba da baya yasa Ammi ta cigaba da kula dani, saboda mahaifiyata ta a gurin haihuwa ta Allah yai mata rasuwa, kafin Daddy na ya auri Ammi yar aiki ya barwa ragamar kula dani saboda ita kanta mahaifiyata marainiya ce bata da kowa sai Allah, ba karamar wuya nasha a gurin Atine yar aiki ba saboda Daddyn mu ba mazauni bane idan yana gari kar kiga yadda Atine ke kulawa dani tun ban da wayau har na fara wayau bayan wasu shekaru na saba da wuyar da Atine ke bani duka da zagi wanka da ruwan sanyi horo da yunwa saka ni aikin da yafi karfi na, kwatsam sai wata rana na kwanta rashin lafiyar da banyi tunanin zan kuma bude ido na na ganni a duniya ba, da farko Atine tayi banza da lamari na ta cigaba da da tsangwama ta, bayan kwana biyu tazo ta sameni a bayi na kwance ko numfashi bana yi ruwa ta dibo ta shiga kwara min, amma ko alamar farfadowa banyi ba, kusan sau uku tana kwara min amma ko motsi banyi ba hakan yasa ta kwarma ihu game da fadin waiyo ni Atine na shiga uku, takai ta kawo ta rasa mafita can dabara ta fado mata akan ta gudu ta barni tasan idan aka kama ta baza ta tsira ba, haka kuwa akai tuni ta shiga dakin ta bata dauki kaya ba sai jakar ratayawar ta kamar mara gaskiya ta fito ta danyi waige waigen ta kana ta fara tafiya cikin sanda koda ta fito harabar cikin gidan sai tai tozali da abinda yasa zuciyar ta ta buga, wato Daddy ne ta gani tare da escorts din shi da alamar yanzu ya shigo gidan, tana sosa kai ta karasa inda yake kamar yadda ya saba yi mata aduk sanda suka hadu haba haba duk da kasancewar shi babban attajiri amma Sam baya kyamatar talakawa hasali ma kullum cikin kyautata musu yake tare da marayu, bayan Atine ta gaishe shi yace “ina zaki ne haka Atine naga kamar shirin fita ne a tare da ke? keda tunda kike a gidan nan baki taba fita ba saida izini na gashi yanzu ma ba dan mun hadu ba sai dai naga ba kyanan to ina kika bar min er leleta? mummunan mafarki nai a kanta shiyasa na dawo nigeria duba lafiyar ta saboda na samu nutsuwa”
Tuni gumi ya fara karyo wa Atine kan kace me saman kan hijabin ta ya jike jagab kasancewar a tsakiyar rana suke alhaji bai kawo komai ba ganin Atine bata da amsoshin shi yasa yace “wai lafiyar ki ko mutuwa akai miki naga ba kamar yadda na saba ganin ki ba”.
Muryar Atine na rawa tace “eh ranka shidade Baba ta ce dama ta rasu to shine zan…..”
Bata karasa ba ya daga mata hannu gami da fadin “haba Atine Ince ba yau nike da ke ba, ai bai kamata ki tafi haka ba da kin sanar dani ko a waya ne sai nasa a kai ki, amma yanzu muje na sallame ki tunda ina gari sai ki bar min shalele ta”.
STORY CONTINUES BELOW
Gaban Atine na faduwa ta juyo cikin gidan tasan yanzu bata da halin fita tako ina masu tsaro ne gwara ta shigo in yaso ko bariki ne sai tai mishi da wannan shawarar ta samu nutsuwa, da karfin ta ta dawo gidan duk kuwa da karfin hali take kar ki tona kiji kasan zuciyar ta.
Akwai kofa ta musamman da Daddy yake bi saboda haka tanan yabi bai zarce ko ina ba sai ban garen sa inda ya gaji da kayatuwa dan zubin gidan sarauta akai mai kayan kawa kuwa da alatu ba’a magana saida yai wanka ya kintsa sannan ya fito dama ka’idar sa indai yana nan daukata yake mu tafi gurin cin abinci, aduk irin ranar sai najini sakayau kamar ina aljanna motsi kadan zanyi Daddy na zai ce me kike so saboda yana mutakar so na da kauna ta kuma tunda nike ban taba bude baki nace mashi ga abunda Atine take min na rashin kyautatawa ba
Koda fitowar sa sunana ya shiga kwala kira shalele shalele haka Daddy ke kirana, jin shiru yasa ya zauna akan daya daga cikin kujerun falo ya dauki rimot ya canza channel, sunan Atine ya shiga kira a karo na uku sai gata ta fito daga dakin ta da injin shara a hannun ta tana ja tace “Alhaji kira na kake dan na kunna inji kasan kara bazai bari inji ba”
“eh” Daddy yace mata
“shalele zaki kira min dan ina ta kiran ta naji shiru nasan yanzu ba lokacin baccin ta bane”
Duk da Atine taji mugun faduwar gaba amma sai ta dake tace mai “to”
TA shiga bangare na ko bayin da nike bata kalla ba ta danyi shawaginta ta dawo harda durkusawa akasa tace “Alhaji ban ga Fadeela ba na duba ko ina kuma da zan fita anan falo na barta tana kallo kuma nace karta je ko ina”
Da sauri Daddy ya mike yana fadadin “what? bazai yuyu ba Sam wannan ba mai yuyuwa bane”
Wani madanni yaje ya danna a jikin bangon falon , kan kace me saiga escorts dinsa nan sun shigo ce musu yai “Fadeela ce ta bata ku nemo min ita tana cikin gidan nan nima zan tayaku dubata”
Atine ya kalla yace “ina da ina kika duba?”
Bakin ta na rawa tace “ranka shidade iya bangaren ta kawai na duba”
Gyada kai yai alamun gamsuwa kana ya dubi daya acikin escort din yace “kai da ita ku tsaya anan ku kuma ku shiga ko ina ku duba banda bangare na”
Haka sukai ta binceka lungu da sakon gidan in takaice miki har farfajiya suka fito amma basu same ni ba, daya daga cikin su ne yai bangaren siminful shiga ciki yai wai ko zai sameni amma shiru, cikin rashin nasara duk suka hallara a falon idon dadi ya kada yai jawur saboda tsananin tashin hankali, iya kaduwa Atine kam tayi, dan kallo daya zakai mata ka fahimci rashin gaskiya atattare da ita
Komawa kan kujera Daddy yai jikin sa babu laka tagumi yai ya rasa ina zai sa rayuwar sa kadde ace mafarkin da yai ne ya tabbata idan kuwa hakane ya ci amanar Maryama wato mahaifiyata kenan gaban sa ya cigaba da tsanan ta bugu, can yai zunbur ya mike yana fadin “kun duba toilets kuwa?”
Gabad’ayan su suka bashi amsa da “a a”
Kafin yace suje su duba tuni kowa ya fad’a ciki duk inda suka san da bayi sai da suka buda kwatsam Daddy ya buda toilet din da ke daki na mai zai gani gudan jinin sa ce kwance a bandaki ko numfashi ba tayi, cikin jarumta ya qarasa ciki, zufa na keto mai dago ni yai kaina yai baya luu, cire mun jikakkun kayan jiki na yai kana ya fito dani durowa ta ya bude ya fiddo min wata doguwar riga fara kyal ya sanya min a kan gado ya shin fidar dani tsabar rudewa ya rasa me zaiyi, can ya tuna da wayar sa daya bari a falo, futowa yai ya dauka bai tankawa kowa ba ya dawo daki na, number Dr Tameem ya shiga laluba ringin biyu ya dauka Daddy bai wani tsaya amsa gaisuwar da Dr Tameem ke masa ba ya shiga shaida masa dalilin kiran nasa da cewa lallai-lallai yana son ganin sa yanzu.
To bayan Daddy ya kashe wayar zirga-zirga yashiga yi, yana cikin wannan yanayin Dr Tameem ya shigo ya iske sa, bayan Dr ya kalli fuskar Daddy ya dauke kai saboda kallo daya zakai wa daddy ya baka tausayi, inda nike kwance Dr ya nufo dama da akwatin gwaje-gwajen sa yazo nan take ya shiga dubani da bani kulawa ta musamman, cikin kwarewar aiki irin na Dr Tameem, da farko yaji tsoro sakamakon jin numfashi na baya harbawa, cikin ikon Allah da ambaton Allah da yake ya kara daukar hannu na ya kai kusan 4 minutes kana ya saki hannun yana mai godiya ga Allah jin bugun zuciya ta ya dawo, da sauri da sauri ya cigaba da dubani yana kuma fahimtar inda matsalar take kan kace me tuni yasa na fardado daga dogon suman da nai amma ban bude idanu na ba Daddy ne ya matso kusa dani yace “shalele ki yakuri kada ki tafi ki barni bani da kowa sai ke”.
STORY CONTINUES BELOW
Naji abunda Daddy ya fad’a amma bazan iya bashi amsa ba saboda baki na yayi nauyi
Dr Tameem ne yace “kar ka damu Daddy da ikon Allah zata warke harma tafi da lafiya yanzu baza ta iya magana ba saboda rashin kuzarin da yake tare da ita bari na gama duba ta saboda naga abunda yake damun ta”.
Nan gefe na Daddy ya zauna yanzu ya dan samu nutsuwa sai dan abunda ba’a rasa ba.
Atine kuwa tunda taga shigowar Dr take ta zagawa ban daki dan ta zaga yafi a irga, ta ruga ta san kashin ta ya bushe.
Bayan wasu awoyi da basu haura biyu ba Dr Tameem ne zaune akan sif din gefan gado na yayin da Daddy ke zaune a bakin gadon Dr yace “nayi mamaki da na sumu Fadeela na dauke da cutar ulcer da limoniya gashi ulsar har tana nema tazama kuronik”.
Shiru Daddy yai saboda ya rasa abunda zai ce ido ya kura min yana jin tausayi na har cikin ransa ledar ruwan da ake kara min ya kalla ko rabi bai yi ba ido na a limshe ina bacci saboda allurar baccin da akai min.
Kallon Dr Tameem yai yace “na dade ina zargin wannan nanny din bata ba Fadeela abunci, saboda aduk lokacin dana fita da ita restaurant karka ga yadda take cin abinci kamar wata mayunwaciya, amma saboda na kara tabbatar wa zanje na duba ctv camera na”.
Dr yace “yafi ma dan wallahi idan muka ga itace silar wannan ciwan sai na Illata ta, saboda wannan tsantsar rashin imani ne da butulci kaduba irin wannan ni’ima da take ciki komai fa yi mata kake Daddy”. Ya kare maganar cikin takaici
Numfasawa Daddy yai yace “Tameem kenan har yanzu kai yaro ne baka gama fahimtar macece duniya ba to acikin wannan duniyar da kake gani akwai mutane masu son zuciyar su, marasa godiya ga ubangijin su, acikin su akwai wanda da ubangiji zai bashi gabad’aya arzikin duniya, baza su taba gani bare su gode masa ba, da za su samu haram ci za suyi saboda zalinci da son kan su, shiyasa a kullum nike kara godewa Allah dayasa inada ga cikin bayin sa masu godiya saboda kaga duk wanda baya godewa mutane to baya godewa ubangijin sa”.
Dr Tameem yace “Hakane Daddy wallahi son zuciya yai wa mutane yawa ko a gurin aikin mu ina ganin masu mutukar son kansu”
Daddy yace “Allah ya ganar dasu damu baki daya”
“ameen” Dr ya fad’a
Kiraye kirayen sallar la’asar aka shiga yi saboda haka Daddy ya Kalli Dr yace “kaje kai sallah ni yau bazan samu damar zuwa masallaci ba, idan ka fita falo kace wa escorts din suma suje suyi sallar amma abar mutane uku su tsare Atine”.
“to” ya fad’a yayin da ya mike ya fice, kamar yadda Daddy yace mai haka ya sanar musu kana ya bar gidan.
In takaice miki labari koda Daddy ya idar da sallah bayan Dr ya dawo ya bar masa ni shi kuma ya tafi bangaren sa, da shigar sa inda yake aje computer dinsa ya nufa bayan ya dauko ta ya nemi gefen makeken gadon sa ya zauna, dayike komai na gidan asete yake da kwamfutar sa, ba tare da bata lokaci ba ya shiga dubawa bayan wasu a wanni saiga idon daddy na zubar da kwalla, cikin sauri ya rufe computer saboda annune inda Aitene tasa kafa ta shuta ni na bugu da gini sai ga kaina ya fashe yana jini hakan bai ishe ta ba sai da ta kara min da duka, har yanzu Daddy mamaki yake bai taba zaton Atine ba yar halak bace kan sa ya dafe yace “oh ke duniya ina zaki damu ace duk wanda ka bawa amana sai yaci babu masu tsoran Allah, a gidan ka kana tsoran iyalan ka a waje kana tsoran mutanen da kake mu’amula da su, saboda rashin amana da yadda.
Mikewa yai jiri na diban sa ya fito bai daki na ya dawo inda ya samu Dr na ta faman danna waya, da ganin Daddy ya aje wayar saboda yanayin Daddy ya nuna yana cikin damuwa.
Dr ya dade yana tambayar Daddy, amma Daddy ya gaza cewa komai.
Saida ya zauna ya samu nutsuwa kana yace “ka kira min Dpo Babawo kasanar dashi yar aiki tayi yunkurin kashe yarinyar da take kulawa da ita”.
STORY CONTINUES BELOW
Hannun Dr na rawa ya lalubi wayar shi, tuni shima idanuwansa sun kada sunyi jawur, number Dpo Babawo ya lalubo ya danna kira ta dade tana ringing sannan ya dauka, daga can bangaren yai magana da turanci, shima Dr cikin turancin ya mayar mishi.
To bayan ya kashe wayar ba’a wani bata lokaci ba sai ga motocin rundunar yan sanda tazo, da yike anguwar manya ce kullum cikin jin jiniya suke saboda haka mutanen unguwar basu kawo mai laifi aka zo kamawa ba.
Ita uwani tunda taji jiniya hanyar cikin ta ke kadawa sai muzurai take, bata gama sarewa ba sai da taga yan sanda sun shigo mata biyu maza uku, tana ganin su ta mike tana fadin “na tuba ku yafe min Alhaji Alhaji dan Allah kayi magana a kyale ni, a dai-dai lokacin Daddy ya fito daga daki na Dr na bayan sa kallon tsana Daddy yabi Atine dashi yace” tur da halin ki dama tsintacciyar mage bata mage, da izinin Allah sai kin girbi abinda kika shuka ku tafi da ita idan kun gama binciken ku ku mika ta koto dan sai na tabbatar da na kwatar ma yarinya ta yancin ta”.
Tuni yan sanda suka tasa keyar Atine zata tsaya mu gaddama suka tara mata gajiya tare da saka mata ankwa a hannu suka ce mata “indai ta kara magana sai sun harbe ta”. Da haka suka kashe bakin ta amma da sai ihu take tana ta fadin “ta tuba”
bayan yan sanda sun tafi da ita sunyi binkicen duk da yakamata kuma sun kama ta da laifi dumu duma, saboda haka suka mika ta koto inda aka yanke mata hukuncin shekara 25 agidan yari tare da horo mai tsanani kuma babu beli.
Tun daga nan Daddy shi ke kula dani duk wata dawainiya ta shine dan ya hakura da fita kasashen da yake shike kaini makaranta kuma ya dauko ni, bai yadda da kowa ba gani yake za’a kuma cutar dani.
Kafin kice me nayi kyau nayi bul-bul dani da kuwa kamar ki hure ni na fadin
Bayan wasu watanni Daddy ne a cikin masallaci bayan sun idar da sallah Ladan yace yana da magana, wasu aciki sun fita yayin da wasu kuma suka zauna, acikin wa’inda suka zauna harda Daddy na ladan ne ya fara jawabi kamar haka “sama da shekaru biyar da suka wuce na tsinci wata mara lafiya cikin ikon Allah nai ta nema mata magani saboda na lura sammu ne akai mata, to Alhamdu lillah yanzu ta samu sauki amma na tambaye ta ahlin ta tace bata da kowa to shine nike so naji ko akwai wanda zai iya cigaba da dawainiya da ita, saboda naga bata sakewa a gida na uwar daki na kullum cikin tsangwamar ta take, Duk da Daddy na tsoro bai hana shi cewa ba “ala gafarta malam babu damuwa zan dauki nauyin ta”. Kasancewar Ladan yasan Daddy yasa yace “ah Alhaji Hamza mai zai hana ka aure ta tunda naga baka da mata ga marainiyar diya kana tare da ita, duk da na ga abinda ya faru kwanakin baya a labarai da mai aikin ka ta kusa kashe ta, yanzu sai ka sama mata uwa ai”
Gabad’aya yan masallacin sunyi na’am da batun sukai ta bawa Daddy kwarin gwuiwa, “to ba’a kin ta mutane” daddy ya fad’a ya kuma dora da cewa “amma ni yanzu tsoran matan nike gani nike kamar duk daya suke”
Nasiha Liman yai mishi daga bisani aka daura auran Daddy da Ammi abisa sadaki mafi karanci, bai kuma dawo gida ba sai da amaryar sa wato Ammi.
Sanda Daddy ya shigo na gansa da Ammi tambayar sa nai wace ce? Yace “Ammin ki ce”. Da gudu naje na rungume ta ina jin son ta da kaunar ta har cikin raina, tunda ga ranar nima nai uwa farinciki na da wal-wala ta ya karu banda wata matsala saboda yadda Ammi ke bani kulawa ko mama ta na da rai iya abinda zatai min kenan, sosai nike jin dadin zama da ita kuma tana iya bakin kokarin ta akan tarbiya ta, har ta samu ciki, duk da itama wajen haihuwa taji jiki har nafara tunanin ko itama zan rasa ta ne, sai kuma Allah ya tashi kafadar ta, ta haifa min kyawawan kannai Wudat da Walid
Wannan shine takai-taccen tarihin Fadeela
Ci gaban labari
Kallo na fadeela tai tace “kin San wani abu kuwa?”
“a a”. Na bata amsa
Tace “kina kama da Ammi har muryar ku iri daya wallahi”
Zanyi magana kenan saiga firifet sun shigo da bulala a hannun su, daya daga cikin su tace “eh lallai kune ferarrun yan iska ko da ba zaku wuce kitchen ku karbi abinci ba tun dazu aka buga ringing”
Yo ni dai ban san ya abin yake ba hakuri Fadeela ta shiga basu, yayin da ni kuma sai zare ido nike,duk magiyar da Fadeela tai musu bai sa sun kyale mu ba
Wata gutunwa a cikin su tace “wallahi baku isa ba Kuje ku karbi abinci kuzo kuyi mana wanki dan baku isa ba”
Kallon fuskar ta nai kamar kai amai, ban san sanda dariya ta kwace min ba, harda rike ciki, ina cikin yi naji saukar bulala tsui-tsui ban san sanda na kwarma ihu ba ina kiran sunan yah Sadeeq.
Cikin bacin rai tace “idan ma uban Sadeeq zaki kira kin dade baki kira ba da ganin ki baki da tarbiya agidan ku ba’a koya miki ladabi ba kin ja ma kanku wallahi bayan wanki da zakuyi sai an muku wankan jego”.
Na bude baki na rama kenan Fadeela tai saurin toshe min baki, ta hanyar sa tafin hannun ta a baki na _____fita sukai suna huci, ni kam raina gabad’aya ya gama baci, Fadeelah nadafa ido na cike da kwalla nace “wai dan Allah a haka kuke rayuwa na fahimci da kiyi laifi da karkiyi duk daya, idan jinin ki bai hadu da su ba sai suyi ta jibgar mutum, ni gaskiya bazan iya dauka ba, haka kawai a gidan mu ba’a dake ni ba sai anan wasu katunan banza su rinka bugu na”.+
Fadeelah tace “uhm Siddeeqah kenan wannan ma kadan kika gani amma ahankali zaki cigaba da fahimta, kuma kamar yadda kika ce idan fa jinin ki bai hadu da su ba kin shiga uku, musamman ma suga kina da kyau to sai kin fi banuwa, tashi muje kar wasu su zo, su ganmu mu kara laifi”.
Mikewa nai zuciya ta babu dadi yau daya ko yinin arziki banyi a makarantar ba duk ta gundure ni.
Muna cikin tafiya muka ji ana kiran Fadeelah da sauri Fadeelah ta waiga dan ganin wacce take kiran ta, aikuwa tai sa’a dan batai mugun gani ba school Momy dinta ta gani, da sauri taja hannu na muka isa gurin ta rungume ta Fadeelah tai tace “Momy Halima wallahi tun jiya nike zuwa room din ku amma sai su senior Dijah su hana ni shiga”. Ta karasa maganar cikin yanayi na damuwa
“ke kada ki damu dama naji ajikina kin zo kin barin ki sukai saboda na tambaye su suka dunga yimin hanya-hanya” a cewar Momy Halima
Kallo na tai muka hada ido tace “Fadeelah kenan, ai dama na fada miki dole wataran zaki nemi kawa, gashi ba’a dau wani lokaci ba har kin gaji da yawo ke kadai, amma dai diyar firinciful ce ko dan ga kama nan?” Momy Halima ta kare maganar cikin sigar tambaya
Fadeelah na Murmushi tace “wannan fa sabuwar zuwa ce yau aka kawo ta kuma ba diyar Firinsifal bace amma dai hostel din mu daya kuma sai naji ta kwanta min a rai, yanzu haka kitchen zamu amsar abinci dan su senior Habiba sun rutsa mu a hostel” nai dai ta labarta mata abinda ya faru, cizan dan yatsa Momy Halima tai ta ce ” Allah ya saka mata amma ba wani wanki daza kuyi musu ku zo muje room din mu”
Binta mukai muna tafiya tana mana hira sai dariya muke
* * * * * * * * * *
Zaune suke cikin gurin shakatawar, Lubancy ce ta dubi Zuby ta ce “ni kam kawata kin yi waya da Sadeeq kuwa?”
Sai alokacin Zuby ta dago kanta daga danna wayar da take ta ce “a a wallahi nayi ta kiran sa bai dauka ba, banyi tunanin yana da bakar zuciya ba sai da wannan dan abin ya faru”.
“kada ki damu nasan bai huce bane amma tunda yana son ki dole idan ya huce zai daga miki kawai dai ki cigaba da kiran sa”
A cewar Lubancy
Kai Zuby ta daga alamun gamsuwa
Suna nan zaune wata matashiyar budurwa tazo wucewa, sanye take da dogon hijab amma bai kai kasa ba kuma fuskar ta sanye take da nikab, ga kuma bakin glass ta sanya, yanayin ta ya nuna kamar tana sauri, saida tazo gab da su Zuby wata leda dake hannun ta ta fad’i, ai kuwa takardun dake cikin ta suka watse, tsugunnawa tai ta fara kwashewa amma sai dai bata gama ba wayar ta ta fara ringing, daga wayar tai ta bar kwashe takar dun ta kuma yi tafiyar ta abun ta.
Gefan kafar Zuby Lubancy ta kalla tace “ke ga wata nan kusan kafar ki”.
Zuby ta ce “me?”
Lubancy ta ce “kardun waccan da suka watse dauko mu gani”
Hannu Zuby tasa ta dauko, har zata mikawa Lubancy sai taga kamar rubutu ne aciki sha’awar karantawa taji, saboda haka ta shiga karanta abinda ke ciki kamar haka
“tabbas ranar nadamar ki ta kusan zuwa bama ke ba da duk wasu masu aikata mummunan dabi’a irin taki na rubata wannan sakon ne saboda nasan zai iso gareki”.
STORY CONTINUES BELOW
Ras-ras gaban ta yai mummunan faduwa, mikewa tai cikin hanzari tana fadin ina take ina zan ganta, hanyar da taga wannan matashiyar tabi ta shiga bi, da ganin haka Lubancy itama ta mike ta biyo bayan Zuby tana tambayar ta lafiya? Menene? me yafaru? Haka ta jero mata tambayoyin ajere, Amma Sam Zuby ta kasa bawa Lubancy Amsa har bakin titi suka fito amma ko alamar ta babu,
Mai keke nafef ne yazo wucewa, Lubancy ce ta daga mai hannu yai faking, shiga sukai kana Lubancy ta fada mai unguwar da zai kai su.
* * * * * * * * *
Su Sadeeq ne a hanya sai sharara gudu yake duk da sun shigo garin kaduna amma bai daina gudu ba, saboda yaga Farooq bai gudu shiyasa tun acan, ya amshi tukin motar, kuma gashi sunyi sauri sosai daka kalli Sadeeq zaka san baya cikin damuwa
Farooq ne ya dube shi ya ce “kai mutumi na yanayin ka ya nuna kana cikin wal-wala fa, wai maye sirrin a bani? A sammini nima in tafi ina nishadi” ya fad’a yana duban abokin nasa
Saida ya kara gyara zama ya ce “Farooq kenan bai kamata ka tambayi sirrin farin ciki naba saboda nasan ka sani duk da nayi mata alkawarin ba zanyi aure ba har sai ta gama makarantar ta na saketa, amma wallahi kar ka tona zuciya ta kaji tayi fari kal kamar auduga, dan gani nike kamar yau ne zan rabu da kaya,
Sabalo Farooq yai yana kallon Sadeeq yama rasa mai ze cemai, wato sai yau ya kara tabbatar da Sadeeq gara ne number daya, tunda har karamar yarinya tafi shi wayau da hangen nesa,
Dariya Farooq ya shiga yi yana tafa hannayen sa
Ganin dariyar Farooq ta fara yawa yasa Sadeeq kuluwa, dan shi ya tsani rainin hankali, to inba rainin hankali ba maye na dan ya fadi abinda ke cikin ransa zai tsaya yin dariya.
Cikin kulawa ya ce “kai bansan iskanci, ka bude baki sai dariya kake kamar kaga wawan zama”
Saida Farooq yadai-daita kansa kana yace “wani hasashe nai shiyasa kaga ina wannan dariyar, amma ai har gwara naga wawan zama akan abinda na hango nan gaba kadan inda rayuwa”.
Kwafa Sadeeq yai bai kara tanka mishi ba, saboda ya gama lura da Farooq dan rainin hankali ne.
A haka suka isa masaukin Farooq dake nan cikin barnawa, bayan sun wuto gets, fakin Sadeeq ya nemi guri yai, a kusan tare suka fito daga motar kowa hannin sa a sama yana mika, saboda kowannensu ya gaji likis, ban garan shi suka nufa direct, basu zarce ko ina ba sai bedroom ko takalmi Sadeeq bai tsaya cirewa ba, ya fad’a kan lallausan gadon Farooq yana kiran sunan Allah.
Shima Farooq dan wannan tafiyar data taso mai ne amma da lafiyar gadon zai bi, yanzu kam ba yadda ya iya, takalman sa ya cire ya fad’a bayi bai wani jima ba ya fito, bayan ya gama kintsawa yashiga shirya kayan sa duk wani abu da yasan yana da bukata ko zai bukata saida ya dauka, bayan ya gama shirya komai ya zauna a bakin gadon ya dubi Sadeeq da idanuwan sa suke alumshe kamar mai bacci, ya ce “nifa zan tafi don nagama shiryawa, nabar maka mukullin ne?” Sadeeq kaman bazai kula sa ba, saboda har yanzu bai gama hucewa ba, har Farooq ya fidda ran amsa sai yaga bakin Sadeeq na motsi
” a a ka jirani bari na watsa ruwa sai mu fita tare ” wannan itace amsar da Sadeeq yabayar
Kan Sadeeq ya mike wayar Farooq ta fara ringing, ganin sunan abokin aikin su ne yasa ya dauka gami da karawa a kunne, adai dai lokacin shi kuma Sadeeq yashiga bayan gida
* * * * * * * * *
Ahanya muka ci karo da wannan gajerar firifet din, kasancewar bata magana da Momy Halima yasa ta bimu da kallon banza
Kallon Fadeelah nai nace “wai ya sunan waccan abar ne?”. Na fada ina nuna inda take
Fadeelah tace “Rafi’a sunan ta, amma Rafsy ake ce mata”
STORY CONTINUES BELOW
Ina dariya nace “ta ko ci sunan Rafcy din”
A haka muka karasa Room din Momy halima, gado ne guda hudu na gani aciki saboda karamin daki ne, kuma a gyare yake tsaf, ko ina a tsaftace
Har bakin gadon ta muka zauna ta ce” bari na dafa mana Indomie dannima yunwar nike ji”.
Wani dan karamin risho naga ta janyo daga karkashin gado, gami da dauko tukun ya, a wani bokiti naga ta dibi ruwa, inda ta bude loka ta dauko indomin, ba awani dauki lokaci ba indomin ta dawu, wani filet ta dauko ta juye mana gaba daya ta ce “Kuje ku wanko hannun ku kuzo muci” to muka ce muka dibi ruwa akofi muka fita, fitar mu keda wuya muka hangi, senior Jamlah inda muke take nufowa, cikin sauri na wanke hannun na dawo room, saboda yadda gabana ke faduwa.
Ko zama banyi ba sai ga Fadeelah tana dariya ta ce” kar dai har kin fahimci Senior Jamlah muguwa ce?”. Tai maganar cikin sigar tambaya
Bayan na zauna ita ma ta zauna nace “ba dole ba kin San irin mutanen nan halin su baya boyuwa, koda kuwa sun so boyewa” nan dai na kwashi labarin komai da nagani na fada mata,
Batai wani mamaki ba tace “indai Senior Jamlah ce tayi abinda yafi haka ma, ke wallahi ko ni na tsane ta tsana mai mutakar yawan gaske, kuma kar kiyi tunanin ta taba duka na fa, a a ko daya haka kawai na tsane ta, kuma yanzu haka na hangi kiyayyar ki atare da ita, dan har tambaya ta tai wai maye alakata da ke? Nace mata ba komai, shine ta wuce tai kwafa”.
Zanyi magana kenan Momy Halima tace “kubar firar haka ku bari sai munci abinci”
Sosai naci indomin dan dahuwar tai min dadi
Karrawa naji ana bugawa Fadeelah na kallah nace “ta maye kuma?”
Tace “ta bacci ce maza tashi mu tafi hostel, kuma kada idan munje ki saki jiki kiyi ta sharban bacci, dan wallahi idan lokaci tashi yai baki tashi ba kin kade”.
Nace “kai wannan wani irin bala’i ne haka makaranta sai kace wurin horan barayi da kangararru”.
Momy Halima tace “kuyi zaman ku anan ke Fadeelah ai kin san ba mai shigowa cikin su koda kuwa karan hauka ne ya cije su ku bari sai la’asar mu fita,
* * * * * * * * * *
Direct Gidan su Zuby mai nafef ya sauke su, ko kudin sa bata tsaya basa ba, Lubancy ce ta biya sa
Koda ta shiga falon gidan babu kowa sai TV da aka bari a kunne yana ta wake wake, zama tai tasa hannu ta dafe kanta, saboda azabar ciwan da yake mata,
Lubancy ce ta shigo, bayan ta nemi guri ta zauna tace “wai don Allah kawa ta meya faru? Ni kin barni a duhu tun dazun sai tambayar ki nike kinyi banza dani, bazan iya jure kallon ki a cikin wannan halin ba, saboda haka zan tafi idan kin shirya fada min kya neme ni, ko ta waya ce “
Ganin Lubancyn da gaske take tafiyan zatai yasa Zuby tai saurin cewa “dakata zan fada miki”. Nan dai Zuby ta kwashe labarin abunda ta gani ta fada mata, cike da mamaki da fargaba Lubancy tace “amma fa wannan lamarin akwai daure kai mutuka, nama rasa ta ina zan fara “
Gwauran numfashi Zuby ta sauke tace “nima tuntuni abin ke yawo a kwakwalwa ta kenan, na rasa me hakan yake nufi?”
Yar aikin su ce tazo shigewa bayan ta gaishe su zata tafi, Zuby tace “kawo mana abin korawa” bayan ta kawo musu Zuby ta dubeta, tace “ina Mama ne? Kota fita ne?”.
Rahamatu mai aiki tace ” tana ciki ko wata kila bacci take yi” daga haka ta bar gurin
* * * * * * * *
Bayan Sadeeq ya fito daga wanka, durowar Farooq ya bude ya dauki kananun kaya riga da wando na jins, rigar me ruwan blu ce amma lite sai wandon jins baki, yai matukar yi masa kyau daya saka abun ka da mai kyau, bayan ya gama kintsawa ya taya Farooq diban kaya suka sa a bayan mota, suka kuma daukar hanya, bayan sun fito a bakin titi Farooq ya sauke Sadeeq sukai wa juna sallama, saboda ba hanya daya zasu bi ba, Motar haya Sadeeq ya hau inda yace “musu Kawo zasu kai shi” bayan ya sauka a kawo ya kuma tarar motar buruku daga nan kuma bayan an sauke shi ya hau mashin din da yake kaisu cikin kauyen su Inna saboda mota bata shiga, har kofar gida mai mashin ya sauke Sadeeq, inda ya ciro kudin sa ya bashi, kana ya shiga gida bakin sa dauke da sallama, Inna dake tsakar gida na shan iska tana ganin sa tafara tafi tana cewa “maraba maraba lale-lale da yan birni” karasowa inda take yai, kana ya zauna akan wata kujera data gefan ta, yace “sannu Inna na same ki lafiya?”
Tace “ina lafiya lau mai gida ina yar rigama ta?”
Yace “Inna yar rigimar ki tana nan amma yau kwanan makaranta zatai”.
Ido Inna ta zaro waje tace “makarantar kwana ka kaita ne?”
Kai ya gyada alamun “eh”
Inna tace “ina karami? Kuma ya barka ka kai yarinyar nan inda za’a cutar da ita?”.
Sadeeq yaso yace “dama ai baiyi dan taji dadi ba” sai kuma ya tuna mitar Inna, dan kuwa ta dungi yi har labari ya koma kunnen Daddy, labari kwa na komawa kunnen Daddy ai ya bani
Kara gyara zama yai, yaita yiwa Inna bayini akan makarantar kwana gwargwadon yadda yaso ya shigar da ita, kuma ta shiga tsaf dan sosai ya tsara ta, ya kuma shaida mata yanzu sun daina fada sun shirya da juna, sosai Inna taji dadin wannan lamarin dan haka tace “akwai wata fura dana dama bari na shiga na dauko maka nasan kana mutukar so” mikewa tai takwaf-takwaf taje ta dauko mai kwarya ta kawo mai, karba yai yayi godiya yace “Inna ni a gajiye nike, bari na je dakina na dan huta”.
“to” Inna tace
Yayin da shi kuma yanufi hanyar soro
* * * * * * * * *
Hudu saura Momy Halima ta tasheni daga nannauyen baccin daya daukeni dan na gaji, da kyar na iya bude ido na, kallon gefe na nai Fadeelah na gani zaune idanun ta sunyi mishi-mishi sai hamma take famanyi, mikewa nai zaune nace “Ash dadin gida kenan wallahi”
Momy Halima tace “maza ku tashi yanzu ba lokacin fira bane”
Haka muka fito daga room din muka tafi hostel din mu, kiran sallah naji anayi nace “lah dama akwai massalaci anan ne”.
Fadeelah dake kokarin fiddo da sabon silifas a cikin akwatin ta tace “eh man ai nan da kike gani babu abin da babu don kinga har da islamiya ma, kuma har sauka ake yi”
Daga haka ban kuma cewa komai ba, Alwala muka je mukai muka tafi masallaci.
To da dare kuwa gaza bacci nai don kuwa banda juyi babu abunda nike, da yike bacci barawo ne ban san sanda ya kwasheni ba
Washe garin tun shida Fadeela ta tada ni, saboda nai wanka tace “idan banyi da wuri ba zan makara gurin zuwa class, to bayan nayo wanka nazo saka yunifom yace dauke ni inda kika barni, neman duniya ban ganshi ba, Fadeela na fadamawa tace” to ke a’ina kika barshi?” nace nan saman akwati na fa na dora shi”
Cikin takaici Fadeela tace “ai kuwa gwara ki daina wahalar nema dan an sace inada sabo bari na baki, amma kin San daya bazai isheki ba dole sai kinje office din shugabar majar kin karbo wani,
Cikin mamaki nace” ikon Allah mutum ba shi ya aje abu ba yazo ya dauka”.
Fadeela tace “wannan ba abun mamaki bane bari na fiddo miki kisa kada mu makara.
Bayan ta fiddo min na saka, kallo na tai tace” Siddeeqah kinga yadda yunifom din nan suka miki kyau?”
Ido na zaro waje nace” ke dai kin cika zolaya wallahi”
Tace “daga fadan gaskiya”.
Nace “ba wani gaskiya ke dai tashi mu tafi, tunda mun gama shiri,
” To” Fadeela tace min kana ta Mike muka fito, kitchen muka nufa, bayan mun karbi breakfast din guri muka nema, bayan mun gama ci muka tafi class.
Wannan kenan