HEEDAYA CHAPTER 7 BY By Khaleesat Haiydar
Www.bankinhausanovels.com.ng
Abba ne xaune main parlor bayan isha, lkci lkci yake kallon agogon dake manne bangon parlon, Mami ta fito daga
part dinta sanye da hijab har kasa ta karaso cikin parlon tace “Good evening Barrister” yana kallonta yace “Good
evening Rahinah” xaunawa tayi one sitter dake parlon tace “Gani” Abba yace “Me ya sa kika dau lkci baki fito” tace
“Putting things in other” Bai ce komai ba, ya kalli hanyar kitchen don Mumy na ciki, tun daxu take kai wa take
komowa ko gaisuwa bai hadata da shi ba tun shigowarsa, shi kuma hakan bai hanasa ce mata yana da magana a
parlor da ita da Mami ba, xata sake komawa kitchen daga bangarenta yace “Maryam” juyowa tayi fuska daure tana
kallonsa bata ce komai ba, yace “Ke muke jira” Tana masa wani kallo ta karaso cikin parlon tace “Ni ku ke jira? in
maku me? A kan me ma xa ku jira ni? Nace maku ina da wnn lokacin ne? Plss I have more important things to do
then sitting and staring at you both, bani da wannan lokacin barrister….” Ta juya xata bar wajen, rai bace yace “Ina
magana xa ki wuce?” Juyowa ta sake yi tace “Bbu tasirin da maganganun ka xa su min barrister, in xauna kace xaka
mana nasiha ko me? Did I tell you I need that, ita dai xaka xaunar ka ja ma kunne ta tsaya iya matsayinta a gidan
nan kar ta ce xata yi karambanin xuwa kusa da nawa matsayin, matsayina daban nata daban, ni uwar gidanka ce
kuma uwar ‘ya yanka, ita kuma uwar rainon yar tsintuwar ka ce, wa enda xaka dinga ciyarwa, kaga banbancin kuwa
ba karami bane, idan tace xata yi gigin matsowa lane dina ita xata kwana a ciki, so bbu wani xaunawa da xan yi ka
hada mu kayi magana, bata kai matsayin ba, ga most important maganganun nan duk nayi, sai dai kawai tayi taking
caution, ka kara mata da wanda xaka kara mata” Tunda ta fara Abba ke kallonta, Mami tayi yar dariya tace “To ai da
sauki tunda kamar yanda xa a kira ki matarsa haka nima xa a kirani ynxu, kuma tunda baki isa korar yar tsintuwa ba
balle ni Alhmdllh, muna nan sai mun xame maki kadangaren bakin tulu, xa ki gane matsayina da naki bai kai
banbancin da xa ki dinga bragging ba….” A fusace Mumy ta karaso kusa da ita tana huci tace “Karya kike wllh, nace
karya kike…” Tsawa Abba yyi mata yace “Kina da hankali Maryam??” Mami ta mike tace “Ina fa, sai dai in koya
mata cikin yan kwanakin nan….” Daga haka ta bar masu parlon ta wuce bangarenta, Mumy ta fashe da kuka tace
“Ka cuceni barrister, ka ci amanata, ka rasa warce xaka auro ka kawo mana gida sai yar bariki….” Mikewa Abba yyi
ya dakatar da ita in few seconds ta hanyar nuna ta da yatsa strictly yace “Don’t you ever try that again Maryam….”
Bai jira cewarta ba ya bar parlon. Mami ce xaune that same night tana kallon Heedayah tace “Ina jin ki…” Heedayah
ta marairaice tace “Tea kawai….” Mami tace “Kece kike cewa kina son tea din kenan” Heedayah ta girgixa kai tace
“Ammi na ce take bani in sha da daddare” Mami tace “To da safe fa?” Tace “Tea and bread and egg” Mami tace “Da
rana?” Heedayah tace “Indomie” Mami tace “Sai kuma da daddare ki sha tea” Kai Heedayah ta gyada mata, Mami
tace “Toh after this night baxa ki sake shan shayi ba duk abinda aka dafa aka baki shi xa ki ci is that clear?” A
hankali Heedayah ta gyada mata kai, Mami ta mike ta dauke fried rice da chicken dake cikin plate da Heedayah ta ki ci wai sai tea ta nufi kofa ta fita, hanyar kitchen ta nufa ta bude kofar kitchen din, tsaye ta ga Shuraim gaban kettle
din ruwa alamar tea xai hada don ga kayan shayin a ajiye gefe, ta kasan tiles yake kallon wanda xai shigo kitchen
din, yana ganin wacece kuma ya kauda kai ya ci gaba da abinda yake, Mami ta ajiye abincin hannunta ta nufi inda
cups suke ta dau daya da cokali, ko kafin ta juyo har ya fice daga kitchen din, karasawa tayi gun kettle din ta juye
ruwan ciki a cup din ta bude kayan shayin ta hada tea sannan ta fita kitchen din, Khadijah ta gani parlor ta shigo
daukan takardunta, tana ganin Mami ta kwashi takardun ta wuce bangarensu da sauri, Mami dama tun da ta kalleta
sau daya bata sake kallonta ba har ta wuce nata bangaren, sai da shayin ya huce sannan Heedayah ta sha Mami ta sa
ta kwanta nan da nan bacci ya dauke ta. Washegari Saturday tun kafin yan gidan su tashi bacci Mami ta hada ma ita
da Heedayah breakfast, da yake abinda Heedayah take so ne tsaf ta cinye komai, Mami dai sai kallonta take, sannan
tace “Kin koshi ae?” Heedayah ta gyada kai, Mami ta mike tace “To mu je ki gaida Abba” har parlon Abba Mami ta
kai ta, Abba dake aiki system ya daga kai yana kallonsu, Mami tace “Weldone” yace “Har ina tunanin kawo maki ki
karasa” tace “Noo nima ga nawa can” yyi murmushi yace “Akwai maganan da nake son xa mu yi Rahinah” tace
“Alright, but before then nima ina da magana da kai” yace “Yanxu?” Tace “Later…” Abba ya xaunar da Heedayah
gefensa yace “How are you my dear” tana washe hakora tace “I’m fine” Mami tace “Baki yi gaisuwa ba” tace “Abba
ina kwana” yace “Lafiya lau daughter” Mami tace “Let me freshen up” daga haka ta fita parlon, yana kallon
Heedayah yace “Wa ke koya maki English” tace “My teacher” ya d’an bude ido yace “Really?” Tace “Ehh” Abba
yace “Me da me yake koya maki kuma a ina yake koya maki?” Heedayah tace “Ammi tace min she’s a Female, tana
koya min komai da komai a gidanmu” yace “Wani sura kike?” Da sauri tace “Jinnnn” Abba na gyada kai so
impressed yace “Kullum take xuwa koya maki?” Heedayah ta gyada masa kai, Abba xai yi magana aka bude kofar,
Shuraim ne ya shigo parlon da sallama yana sanye da jallabiya, Abba ya amsa, xaunawa yyi nan kasa gefen Abbansa
yace “Ina kwana Abba” Abba yace “Lafiya lau” Heedayah tace “Abba har da boko take koya min ma….” Satan
kallonta Shuraim yyi ya kara hade rai, Abba na kallonta yace “Toh xan kawo maki warce xata dinga koya maki a nan
gida” Heedayah ta wara manyan idonta tace “Thank you Abba, but…” Yace “But what?” Tace “Yaushe xaka kai ni
wajen Ammina? Kila tana ta nemana” a sanyaye tayi maganan, Abba ya shafa kanta yace “Ina sha Allah xan kai ki,
har yanxu ana neman Ammin taki” Tace “Abba ai gidan Yakumbo take” Abba yace “Eh ban manta ba xa mu je can”
Mikewa Shuraim yyi ya nufi kofa yace “Sai anjima Abba” Abba yace “Da yaushe kake yi ma su Khadijah karatun
qur’ani” Juyowa yyi yana kallon Abban nasa, ganin kallonsa Abban ma yake yace “Da asuba” Abba yace “Ohk,
Heedayah will join also, sai ka dinga masu gaba daya” dawowa yyi ba tare da ya shirya ba ya durkusa inda ya tashi
yace “Abba ai na kwana biyu ban koya masu ba” Abba yace “Eh to sai ka dinga yi mata ita kadai tunda ba Islamiyya
xata je ba, su kuma dama suna xuwa islamiyya” Kasa cewa komai yyi yana kallon Abban nasa, Heedayah tace
“Abba a suratul jinn nake” Abba yace “Eh daga nan xa ku ci gaba” Shuraim yyi karfin halin satan kallonta, Abba
yace “That’s all xaka iya tafiya, idan ya so sai in samar mata lesson teacher na boko kawai” Mikewa Shuraim yyi bai
ce komai ba ya fice daga parlon ya kulle kofar, fuzar da iska yyi bayan ya fita ya juya yana kallon kofar da
idanuwansa da suka sauya kala. Mumy ce xaune dakinta tayi tagumi, da ka ganta kasan tana cikin tashin hankali,
kanwarta Salima ce xaune dakin, tace “Allah kuwa nake gaya maki Yaya, duk wannan tunane tunanen da saka kai a
damuwa ba shi bane, just swing into action, dubi fa yanda take ta harkar gabanta a gidan kamar warce tayi wata da
watanni ke kuma kina nan xaune kina ta wani kishi da damuwa, wllh tuwo da lafiyayyen miyan agushi tayi ynxu a
kitchen, makauniyar kuwa na can ta kafa mata kujera a kitchen din tana xaune….” Mumy ta fashe da kukan takaici
tace “Wllh Salima har ynxu na kasa yrda cewar kishiya barrister yyi min, gani nake kamar bakuwa nayi xata wuce,
baki ji ynda xuciya ta ke min xafi ba, Kuma fa tun jiyan ko lekowa dakin nan bai yi ba, ita kuwa ta shiga bangarensa
ina lura yau yafi a kirga, wllh ji nake kamar in banka ma gidan nan wuta kowa ya huta” Salima tace “Ba wani banka
wuta Yaya, gashi kin fara bata chance ta kwace maki miji ta xama ita ce kan komai a gidan….” Mumy tace “Duk ba
wannan ba nata bai tsaya min kamar yanda na makauniyar ya tsaya min a rai ba, ki bani shawara ta ina xan fara, me
kike ga xan ma wnn yarinyar in huce takaici, ni dai baxan kasheta ba amma ina son abinda xan mata kissa ya fi mata
alkhairi da shi, wllh na tsaneta, na tsani duk wani me son ya ganta kusa da shi ma, wllh sai na tarwatsa rayuwarta”
Salima tayi dariya tace “Ni fa ban wani jin yarinyar nan Yaya, minti nawa ne xa a kada ta ta bar gidan ma gaba daya,
ita dai wnn yar bokon ya kamata ki fara tunanin ynda xa ayi da ita ba yar yarinya ba” Mumy tace “To ni ta yarinyar
nake tukun” Salima ta mike tace “Toh ki kwantar da hankalin ki Yaya, wnn me sauki ne, mu da muka san kan komai,
yanxu dai ana jirana tun daxu a waje, xan dawo ko xuwa jibi” Mumy tace “Ba wani nan, ke din ce xan gani kwana
kusa, idan kika tafi gantalin ki ba sai an gan ki ba” Salima tayi dariya tace “Ai ynxu na daina kwana a waje….”
Mumy tace “Toh ni dai gobe xan taho gida kar ki fita don Allah” Salima tace “In sha Allah yaya, sai mun hadu
goben” Daga haka ta fice daga dakin….. Bakin gate Salima ta kusa cin karo da Junaid xai shiga cikin compound din,
ja baya tayi tana kallonsa, yace “Sorry” bata iya ta amsa ba har dai ya wuce ta, ta juya ta bi shi da kallo ko kiftawa
babu, underneath her breath tace “Waow….” Tana tsaye tana kallonsa har ya isa entrance din shiga main parlor, ya
kwankwasa kofar, Mami da ta san yana hanya ta fito daga kitchen ta bude kofar tana kallonsa tace “Har ka iso?”
Yace “Ehh ina yini Mami” ta basa hanya tace “Lafiya lau” daga haka ta koma cikin parlon ya bi bayanta, saman
kujera ya xauna tace “Ya su Uncle din naka” yace “Alhmdllh…” Kitchen ta nufa tace “I have been waiting for you
since xaka dauko min sako a gida” Kafin ta shiga kitchen yace “Mami ina…” Mami ta juyo jin yyi shiru, tace “Wa?”
Yace “Wannan babyn” dariya tayi tace “Sunanta Heedayah” yace “Oh ohk, Heedayah” Mami tace “Tana can tana
bacci, let me get you water” Drink ta kawo masa parlon, duk suka kalli direction din da suka ji footstep, Mumy ce ta
fito rike da makullin motarta fuskarta a murtuke, Mami ta nufi bangarenta don tado Heedayah, Junaid yyi kasa da
kai cike da ladabi ya gaida Mumy, kallonsa ta kara yi snn ta amsa a dakile tayi ficewarta xuwa gidan Hajiya Sadiya
ta ji ita kuma nata shawaran. Ba a dau lkci ba Mami ta fito rike da Heedayah dake sanye da doguwar riga iya gwiwa,
duk gashin kanta a bude, kana ganinta kasan daga bacci ta tashi, Mami ta xaunar da ita nan kusa da shi tace “Ga
Yaya ki gaishesa” daga haka ta koma kitchen don karasa abinda take, hannu Heedayah ta kai a hankali tana ta6a sa,
har ta kai hannunta fuskarsa, ya kama hannun yana kallonta yace “Ina maki wasa ne?” Turo baki tayi tace “Nasan kai
ne ai” hancinta ya ja yace “Sai na…..” Ganin ynda ta 6ata fuska xata yi kuka ya jawota kusa da shi yace “Ohk sorry,
let me pour you juice, xa ki sha?” Ta turo baki sai kuma ta gyada masa kai, ya bude drink din da Mami ta kawo masa
ya diba, tace “Baka kawo Farida ba?” Bai ce komai ba ya kai glass din bakinta yace “Bude bakin” bude bakin tayi ya
fara bata juice din a hankali, Mami ta fito kitchen din tana kallonsu tace “Da baka bata ba, bbu wani abincin da take
ci sai kayan xaki” Heedayah na jin haka ta karasa shanye lemon da saurinta, murmushi yyi ya ajiye cup din, Mami
tace “System dina xaka dauko min a gida yanxu” Junaid yace “Ohk…” Heedayah tana ta6a sa tace “Xaka je da ni??”Mikewa Junaid yyi ya da makullin sa yace “Sai na dawo Mami” Mami tace “Alright” a hankali Heedayah tace
“Mami ki ce in rakasa plss” Mami ta kalleta sannan tace “Ki rakasa ina?” Tace “Inda xai tafi” Shi dai Junaid bai ce
komai ba ya nufi kofa har xai fita sai kuma ya juyo yace “Mu je da ita Mami?” Mami ta hade rai tace “Ku je da ita
ina” Yace “A’a na ji tace xata je ne” Mami tace “To baxa ta je ba, kayi wucewar ka malam” Heedayah ta tashi tsaye
kamar xata yi kuka tace “Mami nooo, pls ina son in je, I want to meet with farida, ki ce in bi sa” Mami ta kamo
hannunta tace “Farida na Abuja Heedayah, she is not back yet, idan ta dawo you will see her” Shiru Heedayah tayi
kamar xata yi kuka, Mami ta kalli kofa ta ga har Junaid ya fita, bangarenta ta tafi ta dauko ma Heedayah hularta da
takalmi sannan ta dawo ta sa mata, ta kama hannunta suka nufi kofa, Mami na kallon Mai gadi tace ya leka yace ma
wanda ya fita yanxu ya tsaya, hakan Mai gadin yyi, Heedayah ta ji dadi jin fresh air ta gane sun fito waje, sai da
suka kusa gate Heedayah tace “Mami kin san me?” Mami ta kalleta tace “Aa my dear, what?” tace “Ina jin kamshin
ruwa….” Da mamaki Mami tace “Kamshin ruwa ku ma daughter?” Heedayah tace “Ehh” Mami tayi yar dariya ta
leka gate, ganin Junaid tsaye jikin motarsa tace “To ga ta ku tafi amma kar ku dade plss ka ga yamma yyi” ya karaso
ya kama hannunta yace “Toh Mami” daga haka ya wuce mota da ita, Mami na tsaye har taga ya nufi mota da ita
sannan ta koma ciki, front seat junaid ya bude, kawai ya ga ta fara kokarin shiga, ya dagata ya sa ta cikin motar ya
rufe sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar suka bar layin. Heedayah ta juya Inda take tunanin
yake tace “Ya sunan ka? Sai in dinga kiran ka” Bai kalleta ba idonsa na kan titi yace “Ke ya sunan ki” Tace “Sunana
Heedayah Ahmad….” Yace “Heedayah is not a real name” Ta wara ido tace “Ohk, Ammina tace min sunana Fatima”
Sai a sannan ya kalleta, ya dai ci gaba da tukin da yake, tace “To ka gaya min naka sunan” Yace “Sunana Fatima
nima” ta xaro ido kamar tana ganinsa tace “To ai kai ba na mace bane” yace “To ni na menene?” Tace “Kai namiji ne
mana” Ya d’an yi murmushi yace “Ya aka yi kika sa ni namiji ne? ni ma mace ne kamar ki” Ta kyalkyale da dariya
har da kyakyatawa, juyawa yyi da sauri yana kallonta, murmushi kawai yake ya ci gaba da tukinsa, tayi dariyarta
mai isarta sannan tace “Toh ai naji muryarka kato ne, ba irin na mata ba, kuma…..” Matsawa tayi kusa da shi ta fara
tattaba sa tun daga saman kansa, Bai san sanda ya samu waje yyi parking ba da sauri yana kallonta, ta sakko da
hannunta har fuskarsa ta fara jan dogon hancinsa sannan ta shafa beard dinsa ta sakko da hannunta har chest dinsa,
dariya ta kyalkyale da tace “Namiji ne wllh” kasa daina kallonta yyi, can yayi murmushinsa me kyau yace “How did
you know?” Tace “Gashi naji gashin kan ka d’an kadan ne ba irin nawa ba, kuma kana da beard a fuskar ka, kuma
you don’t have breast” He couldn’t help it but laugh out loud jin maganar ta na karshe, ita ma ta fashe da dariya tana
taya sa, sosai Heedayah ta basa dariya, lkci daya ya daina dariyan yana kallonta yace “To ai ke ma baki da shi balle
ni” ta tsuke fuska tace “Teacher na tace grown up people ne kawai suke da breast ni yar yarinya ce ai” Murmushi yyi
yace “Ashe kema namiji ne kamar ni” Lkci daya ta 6ata fuska tace “Ni ba namiji bane, ni na mace ne…” tana fadin haka ta cire hularta dogon gashinta ya xubo kasa tace “Ka kalla ka ga” Ya fi second ashirin yana kallon gashin nata
sannan ya motarsa after watching and making sure there is no car coming, sai da ya d’an yi nisa yace “Ke ma dai
namiji ne bbu ruwana da gashin ki” rungume hannunta tayi ta jingina da motar ta ki cewa komai wai tayi fushi, bai
kuma ce mata komai ba har suka isa gida, Mai gadi ya bude masa gate ya shiga yyi parking, fitowa yyi ya xaga ya
bude side dinta yace “To na ji ke mace ce, sakko” ta turo baki xata sakko ya dagata ya fito da ita, tace “It is going to
rain” kallon sky yyi yace “How did you know?” Tace “Ina jin kamshi” ya kalleta da kyau ya sake kallon sama, da
hadari amma ba sosai ba, ya kama hannunta suka nufi cikin gidan, tare ya tafi dakin Mami da ita ya dau system din
ya kamo hannunta suka fita, tana bin sa a hankali tace “I want to take tea” Yace “Me yasa baki gaya ma Mami a can
gida ba” tace “Tace baxata sake bani tea ba” downstairs ya sakko da ita ya xaunar da ita saman kujera yace “Wait for
me” ya ajiye system din hannunsa ya wuce kitchen ya kunna gas ya sa mata ruwan tea, Yana tsaye kitchen din yana
jiran ruwan shayin ya tafasa aka fara iska sosai, muryar Heedayah ya ji with all her strength tace “Where are youuu”
ya kashe gas din ya fito, tsaye ya ganta duk a tsorace, ya karasa inda take yace “I’m here” ta kamo hannunsa tace
“Kar ka bar ni, ina jin tsoro” tana rike da shi ya tafi ya kulle duk windows din gidan har upstairs, lkci daya aka fara
ruwa sosai, ya duka dai dai fuskarta jin kamar magana take yi yace “What?” Tace “I told you I smelt rain” d’an
murmushi kawai yyi yana tunanin baiwa ne kilan nata, downstairs suka koma ya xaunar da ita saman kujera yace
“Let me make the tea for you” da sauri tace “Noo, kar ka bar ni, ka tafi da ni plss” tare ya koma kitchen din da ita,
tana makale jikinsa har ya hada mata shayin sannan suka dawo parlor, ya ajiye shayin saman center table yace “Ki
jira ya huce” bata yarda ta xauna ba sai da ta tabbatar kusa da shi ne, ta jinginar da kanta shoulder dinsa tayi shiru,
ya dau wayarsa ya haske fitila don tuni aka dauke wuta da ake iska, missed calls na Mami ya gani guda hudu, yayi
dialing number ya kai kunne, yana fara ring ta dauka, a fusace tace “Junaid da ku ke tafiya baka ga hadari bane, me
yasa baka dawo min da yarinyar ba??” Yace “Mami ni ban lura ba sai da muka iso nan gida” Mami tace “Where is
she now?” Ya haska fuskar Heedayah ya ga idonta a lumshe, ya mayar da wayar kunnensa yace “She’s sleeping”
Mami tace “I don’t care ko kana tuki cikin ruwa ko baka yi, just in the next 20 mins ina son ka dawo min da ita, I
don’t want to call you back after this” daga haka ta katse wayarta, kallon Heedayah ya sake yi xai kwantar da ita ya
duba karfin ruwan da ake a waje ta bude ido da sauri ta rikesa cikin muryar kuka tace “Noo where are you going”
yace “Ba Inda xanje kiyi baccin ki” kin sakesa tayi, ya koma ya xauna, ta kwanta jikinsa, Yana ta xaune parlon ita
kuma tana ta bacci, har kusan karfe shidda, har sannan kuma ruwan ko raguwa bai yi ba sai ma karuwa, idan akwai
abinda bai iya ba a rayuwa to driving ne cikin ruwa, sarai kuma Mami ta san hakan, duk motsin da xai yi Heedayah
sai ta kara makale masa, bayan wani lkci ya haska fitilar wayarsa a fuskarta yaga fararen idonta a bude, duk
tunaninsa bacci take, yace “Kin tashi?” A hankali tace “Idan nayi bacci xaka wuce ka bar ni ni kadai” Ya kwantar da
ita jikinsa sosai yace “Noo baxan tafi in bar ki ba yi baccin ki” sai bayan Magrib ruwan ya tsagaita yana son yaje yyi
sllh Heedayah ta ki sake sa duk da har sannan bata koma bacci ba, haka ya wuce dakinsa da ita yyi alwalan a can
sannan yayi sllh suka fito tare, tace “Where is my tea?” Gaba daya ya manta da shayin dake kan center table, yace
“let me make another one, wannan yyi sanyi” cikin few minutes ya hada mata wani shayin amma ba mai xafi ba,
suka koma parlon ya xaunar da ita ya kai mata cup din baki, ta rike ta fara sha…. Tana gama shan shayin ya dau
makullin motarsa yana rike da ita da system din Mami suka fita gidan, ya kulle gidan sannan ya nufi motarsa, sosai
garin yyi sanyi, ya bude front seat ya xaunar da ita bayan ya ajiye system din a baya, ya xaga ya shiga motar suka
bar gidan, dai dai kofar gidan Abba yyi parking, nan gabansa ya fara faduwa don yasan Mami won’t take it likely
with him this night, ya dai fito ya xaga ya bude ma Heedayah side dinta, ta laluba ta kamo hannunsa kamar xata yi
kuka tace “Ina jin sanyi” ya saukar da ita yace “We are home” dai dai bakin gate suka hadu da Shuraim xai fito,
Junaid na kallonsa ya sake hannun Heedayah ya basa hannu, Shuraim ya amsa yana kallon Heedayah daga sama har
kasa, suka gaisa da Junaid, Shuraim xai fita Junaid yace “Ehm naga it’s late already, pls can you go in with her, ina
d’an sauri ne” Shuraim ya sake kallon Heedayah sannan ya kalli Junaid yace “Alright” Junaid yace “Thanks” daga
haka yyi patting kan Heedayah ya sa hannunta cikin na shuraim yace “Ki gaida Mami, xan kawo mata laptop din
gobe” juyawa yyi ya fita gate din ya nufi motarsa, Heedayah ta 6ata fuska xata yi kuka jin Junaid ya wuce ya bar ta,
Shuraim dake ta tsaye Heedayah na rike da hannunsa gam, ya saci kallon motar Junaid ganin har yyi reverse ya
xame hannunsa daga nata yayi wucewarsa masallaci, Heedayah dai na ta tsaye ga sanyi da take ji sosai sai juye
juyen idonta take gwanin tausayi, Mai gadi ne ya fito daga dakinsa alamar shi ma xai wuce masallaci don yin Isha
ganinta yace “Me kike yi a nan yarinya, ki shiga ciki mana” Cikin rawar murya tace “Bana gani ai” yace “Bakya
gani kuma?” Ta gyada masa kai, lkci daya hawaye ya cika idonta, kama hannunta Mai gadin yyi ya fara tafiya xuwa
entrance din shiga gidan yaga tana bin sa a hankali, lkci daya jikinsa yyi sanyi, yace “To wa ya ajiye ki bakin kofa?”
Tace “Sake ni yyi ya wuce ya bar ni” dai dai kofa suka hadu da Abba, Abba na kallonsu yace “Wa ya dawo da ke
Heedayah?” Tace “Ban san sunansa ba” Kama hannunta Abba yyi ya wuce part din Mami da ita, Mami ta mike
ganinsu, Bai ce ma Mami komai ba ya sake hannunta ya juya ya fita, kana ganinsa kasan he is angry and don’t want
to talk. Mami ta kamo hannun Heedayah tace “Ina Junaid din?” Heedayah tace “Ya wuce” Mami bata ce komai ba ta
wuce daki da ita. Sai kusan sha daya na daren Mami ta tafi bangaren Abba bayan Heedayah tayi bacci, xaunawa tayi kusa da kujeran da yake xaune tace “I’m truly sorry barrister, hakan baxai kara faruwa ba in sha Allah, nasan you are
not happy” Yace “It’s okay, but pls ki sa ido a kan wnn yarinya fisabilillah, don’t expose her much to anybody, let her
be home all through, kin san condition dinta, tana bukatan kulawa sosai Rahinah, ina jin yarinyar nan tamkar jinina
bana fatan wani abu ya sameta…..” Mami tace “In sha Allah” yace “Yaushe Farida xata dawo?” Tace “Ranan laraba”
yace “Alright, na sa a nema ma Heedayah lesson teacher soon, Shuraim kuma xai dinga mata karatun qur’ani da
asuba na gaya masa, so after prayer kar ki bari ta koma bacci….” Mami ta kallesa sai dai bata ce komai ba… Dai dai
wnn lokacin kuma Mumy na dakinta ta shige can cikin bathroom tana ta waya kasa kasa, Mumy tace “Kai ni har na
gaji da bayani har yanxu baka fahimta ba, ce maka nayi makauniya ce fa yarinyar, kuma dududu Rabi’ah ta ma ta
girmeta ina ga, yar yarinya ce fa sosai, bata wuce sha biyu ba ma kila….” Dariya sosai wanda take wayan da yyi yace
“Haba Hajiya, to meye kuma xaki daga hankali kan yar yarinya? Ni wllh na xata ma kishiyar ce kike….” A fusace
Mumy tace “To kai ina ruwanka? ba dai kudin ka kawai ka sani ba, ni fa na riga da na gama magana da kusan
mutane uku, kawai raba kafa nake ta yi ta ko ina shi sa na kira ka ba wai wani abu ba don kai ka fiye shiririta, ina
ruwanka da kankantan yarinyar?? kaga…. idan har ka shirya kaga xaka iya sai ka kirani gobe da safe ni kwanciya
xan je inyi…” Tana kai wa nan ta kashe wayar ta fice daga bandakin ta kwanta kan gadonta tana fata ta samu bacci
ko xata ji saukin xafin da ranta ke mata, rabonta da baccin kirki tun ranan da ta dawo kaduna. Da asuba Shuraim na
dawowa masallaci ya shiga parlon Abbansa don gaishesa don kusan tare suka dawo masallacin, Abba dake hada
wasu files ya amsa ba tare da ya kallesa ba yace “Yau xa ku fara karatun da Heedayah koh?” Shiru Shuraim yyi da
farko, yana mamakin why all of a sudden Abba xai fi karkata hankalinsa gaba daya kan makauniyar nan, Bai ma ce
suyi har da su Rabi’ah ba wai Heedayah, jin shiru Abba ya juya ya kallesa, Shuraim yace “Sure in sha Allah” Abba
yace “Good, a can parlon Aunt dinka xaku dinga yin karatun” shiru ya kuma yi na kusan second goma sannan yace
“I prefer mu yi a inda nake yi ma su Rabi’ah” Abba yace “Ina kenan?” Yyi kasa da kai yace “Balcony” Abba yace
“Noo, akwai sanyi waje, you look for another alternative” mikewa Shuraim yyi ya nufi kofa ya fita, gaba daya ji
yyi ya kara tsanar Heedayah har ransa, WTF, ba don he can’t look into his father’s eyes and tell him baxai yi ba da
bbu abinda xai hanasa yin hakan, ya fi minti biyar tsaye a parlor kafin ya nufi part din Mami ya tsaya ya kwankwasa
kofar fuskarsa daure.