HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 19 KARSHE BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}
…………Bayan kowa ya zazzauna Abba yay sallama San nan ya Fara Magana kamar haka Kun dad’e kuna shirya yadda zakuyi kuga bayanmu ga maza jenku Azaune d’azu sunmin waya kuma dukkansu mun fahimci juna dasu Rahanatu Babu Abinda zance Miki duk Abinda kikaimin nabarki da Allah Dan haka mutane ku shaida na saketa saki 3 San nan yaran Shuriem da matarsa ta Haifa Masa zamuje Ayi gwaji na D.N.A kitabbatar dayara na waye, San nan kince se Munyi bara Atiti yanzu da fari kowacce taciro wayarta ta nuna Mana kud’inta na Account cikin rawar jiki da kid’ima kowa ya D’auko ya nuna Suma mazajen sunyi mamaki bak’aramin kud’i suka taraba.
Atake suka Basu wani Account suka juye kud’in Aciki nanfa suka Shiga koke koke domin su yan’ Atarene basa siyan wata kadara Mijin Hajiya Amina ne ya daka musu tsawa sannan ya kalleta yace” kin Rabani da Ahalina gaba d’aya kin raba Ni da uwata data kawoni Duniya kin mallakeni Sai Abinda kikacemin kije Allah zai sakamin Dan haka kije kema nasakeki saki
Itama saita rushe da kuka Baban Meerah ne yay gyaran Murya Shima yafara jawabi kamar haka kin cuceni Laila tsakani dake Allah ya Isa ban yafeba kin rabani da kowa nawa San nan kin D’auko yar’ wani kin hauro da ita gidana kinsa Naci da ita na shayar da ita na tu fa tar da ita, Allah ya Isa tsaka Nina dake..
Abba ne ya mik’e yace” Ina Heedaya? tana d’aki tana barci cewar Anty Saudat, kuma dubanta Yayi yace” Aje Atasota ta sako hijab d’inta dukkanmu yanzu zamu Asibiti, Amsawa tayi sannan tayi d’akin Momy, Ina kwance cikin bargo Ina Shan barci naji Ana tashine Mitstsike Ido nashigayi San nan nawaresu don ganin Wanda ya tasheni Anty Saudat nayi Arba da ita da murnata nace” Anty yaushe kuka dawo, Bata bani Amsata ba Tace” Heedaya kizo Abba nakiranki yace” kitaho hijab d’inki domin Akwai inda zamuje cikin Murna nace” Abba yadawo yaushe ya samu lafiya yanzu Kai Alhamdulillah.
Anty ce takatseni da cewa Heedaya yanzu ba lokacin wad’annan tambayoyin bane kitashi mutafi kawai saukowa nayi dama doguwar rigace ta Material Ajikina Toilet na Shiga na sake kintsa jikina San nan na fito mukayi falo Mutane nagani Azazzaune wasu ma bansan suba.
ABBA ne yay gyaran Murya San nan yace” Heedaya wan Nan baban Meerah ne wannan kuma Mijin Haj. Amina Nan yay min bayani Atak’aice San nan ya d’ora da cewa” yanzu Asibiti za muje domin yin gwaji Kallo inda Yaya yake nayi, na kalli Yaya Taufiq, da saurinta nayi gurin Yaya Taufiq nace Masa muje kawai, su Abba ne suka fita Sai yan’sanda suka tasa su ummy Agaba sannan Mukabi bayansu, inasane nak’i Shiga Motar Yaya nashiga ta Yaya Taufiq domin Akwai k’arin bayanin Dana keso yay min.
Dukka gidan Muka tafi Aka rufe gidan Bayan mun Fara tafiya yashiga Yi min bayani dallah_dallah Abinda ya faru dani A egypt gaskiya na Jin Masa Yaya Taufiq D’an uwane na k’warai Amma Allah yasaka Masa da Alkairi.
Bayan mun isane Abba yasamu babban likita kuma k’wararre Yay Masa bayanin Abinda ke tafe Damu Nan take yasa Akai Mana gwaji, muka Zauna jiran result.
Bayan wasu Awanni Aka kawo Mana saka mako bud’e wa likitan Yayi San nan yace” wace ce Merah San nan wace ce Heedaya dukkanmu mik’ewa Mukayi lokaci guda, cigaba Yayi da maganarsa wan Nan sakamakon gwaji ya nuna Yara na Heedaya ne, bana Meerah ba kamar Yanda kuke zato ba. Farin ciki me ya mamaye Raina da zuciyata.
Ummy muka gani ta Fara zabure zabure Ai kuwa kallo yakoma kanta nan ta ringa tonawa kanta Asirin duk Abinda tayi harda kisan Babar su Shuriem Sai data fad’a.
Maman Meerah kuwa fad’uwa tayi Nan take b’arin jikinta ya shanye Hajiya Amina ma itama bazama tayi Nan ta yadda D’an kwali da mayafi ta yanki titi. Abun tsautsayi tana fitowa Mota ta kwasheta Ai Sai gawarta.
Nan fa Mutane sukai tayi mata tofin Alatsine, Meerah dataga Daddyn ta zai tafi yabarsu Agurin kuka tasa tar’iko rigarsa da sauri ya bige Han nunta yace” kije can kinemi ubanki ko ki tambayi uwarki tagaya Miki inda yake Amma ba dai Niba, haka muka bar Asibitin kowa ransa badad’i, Abba ji yay Mutuwar Mamansu Shuriem ta dawo Mai sabuwar, Haj. Safiya mace Mai hak’uri da juriya, Allah kajik’anta Kai Mata gafara, gefen rigarsa yasa goge hawayen Daya silalo mai, Sai yanzu ya tabbatar Rahanatu Shai d’aniyace ko ya Akaina ya Aureta.
Koda zamu dawo ma Motar Yaya Taufiq na biyo Nan take fad’amin maganar Badd’o Aikuwa nashiga tashin hankali ba kad’anba kuma nace yabarni dashi.
Ranar da Akayi suna gaskiiya Ansha shagali Ankashe kud’i ba kad’anba Hasan sunan Abba Hussain. Kuma sunan Baban Momy Ranar kuma Aka d’aura Auran Sadiya da Yaya Taufiq gaskiya banji dad’in Yanda Akai bikin Ina cikin jegoba haka Akakai Amarya gidanta lafiya.
Bayan nayi Arba in Yaya yatashi hankali Sai na koma Ni kuma na cije nace” wallahi Sai ya sakeni yaje ya Auro Badd’o dayaga bayanda zeyi dani Momy yaje yagayawa itama Awannan Karan cewa tayi yaje yararrashi matarsa su dai daita Shuriem fa ya Shiga tsaka me wuya Dan yanzu yatabbatar Soyayyar Heedaya Tai Masa babban kamu yanzu yazaiyi da ita kowa yakyalesu ya zuba musu Ido da yaga dai ba Mafita gurin Abba yaje yace” shidai yayiwa Malam Mai farin gemu magana gashi yazo ya firgita Masa Mata dak’uwa Abba yay Masa San nan yace” badan halinkaba Sai Dan kasadar da Heedaya ta d’auka Akan rayuwarmu gaba d’aya, haka Akayi kuwa Abba yaywa Malam magana, Malam kuma ya Amince dama Akwai Wanda yana cewa ita badd’on.
Heedaya sun koma gidansu da Shuriem cikin K’aunar juna da kulawa Ayanzu rayuwa Tai musu dad’i Dan har sun zaga k’asashe 3 don cin Amarcin da basuyiba.
Tammat bihamdillah