HIKIMA CHAPTER 10 THEND KARSHE

HIKIMA 





CHAPTER 10 THEND KARSHE






Tunda naga sun gama komai zasu tafi na kankame Mama Ina kuka, gaba daya ji nake tamkar an daura min wani Babban nauyi a kaina, tunda naji kowa yana cemin HIKMAH kiyi hakuri, to nasan tabbas aure ba karamin Abu bane. Haka ina kallo gaba daya suka tafi ko Nafisar Baa barmin ba. Da gudu na koma daki na fada gado na saki wani irin kuka, Ni bansan me yasa nake kukan ba amma na kasa lallashin kaina. A hankali naji numfashina pattern dinsa ya Fara canjawa, hakan yasa na mike na zaune, cikin raina na Fara bawa kaina hakuri, tareda tunawa kaina, Ni kadai ce fa, babu wani Dazai kawo min dauki gwara na daina kukan. A hankali shima ya dauke dif, se Ajiyar zuciya da nake ta yi. 

Nafi awa daya a zaune, kafin na mike na yaye lafayar da aka Nada min, na tafi gaban dressing mirror, fuskata na kalla, Haba se kawai na kwashe da dariya, kwaliyyar da Nafisa ta yimin, gaba daya ta jagule, Dama da kyar na yadda akai min saboda nasan chances inyi kuka, 95% ne to gashi kuwa. Kara kallon kaina nayi a take ranar da aka kai Anty Fadila ta fado min, yadda tayi kuka make up dinta ya bata mata fuska, nayi ta dariya. Kawai se nayi Murmushi na wuce zuwa kofar da nafi tunanin ta bayi ce. Face wash nasa na wanke fuskata tsaf, nayi alwala saboda daf ake da ishai. Sannan na fito na dan shafa powder, na maida lafayar da naxo da ita. Kafin na zauna kiran Sallar yasa na daidaita kaina nayi sallah Harda shafa’i amma banyi wutiri ba. Ban jima da idarwa ba naji shigowar shi, da farko na tsorata Dan Banji motsi ba se turo kofa kawai naji, a firgice na juya, na ganshi a tsaye yaci wani soft yadi fari tas, Babbar riga. Yayi kyau sosae. Idanuna suka cicikko da kwalla, a hankali suka Fara zuba saman kuncina, shigowa yayi sosae yana girgiza min kai yace 

“Sorry Baby, ni ne na barki ke kadai ko? ” 

Kaina na gyada ina Hararashi, ban ankare ba naji ya rungumeni gaba daya, tareda miko min hannunshi daidai saitin bakina yace 

“Oya, Tofo a rama” 

I couldn’t resist, seda nayi dariya sannan na kwanbala mishi yawu a tafin hannun, sakina yayi ya kalla hannun sannan ya kalleni yace 

“Tab, Baby a hannuna? Kin taro match!” 

Inata dariya Naga ya yiyo kaina da hannun alamun zai goga min, kofar na bude fice a guje ina fadin 

“Zan fadawa Mami fa ” 

Kawai gani na nayi tsakiyar Parlor, ga maza a zazzaune, Kai naji kunya kkĺĺk]lol*gJr Jr NHL da sosae, it escaped my mind ranar farko Ango da Abokanshi yake zuwa. Kamar ruwa ya cinye ni hakan na tsaya, na kasa motsi, su kuma se tsokanata suke Wai Haka nake son Abokinsu dama. Ina nan tsaye se gashi ya fito yana dariya da dukkan alamu hannunshi ya wanko, Dan naga ruwa a gaban malumalin dinshi. Tunda ya shigo suke mishi tsiya, Babu Wanda ya kula seda yazo gefena, ya Dan riko hannuna yace 

“Zauna, Karki kulasu” 

Zama nayi gefenshi sannan sukai mana addua sosae, da abinda ke fadar min gaba wato muyi hakuri. Daga nan suka gabatar da kansu sannan suka tafi. 

Aure abune dake canja maka rayuwarka entirely. Idan kana cewa kai bazakiyi kaza ba, ba kya son kaza to bata kama Ki ba. Maza sunada wani Hali na wannan abin nawa ne, I’ve every right over it, se kiga Wasu abubuwan da gayya akeyinsu. Nafi tunanin shiyasa ake cewa muyi hakuri. 

Yana dawowa daga rakiyar Abokanshi, ina nan zaune inda ya barni, nayi zurfi sosae cikin tunani, Inata ayyana yadda zaayi wannan zaman, abinda na sani akanshi kalilan ne Haka zalika shima. Zama yayi gefena yace 

“Tunani da yawa is Bad, anan gurin ke kadai kike da iko da ita. So zamanmu Inshaaa Allah zan zame miki adali tunda ni ne shugaba, zanyi miki dukkan abinda ya dace gwargwadon iyawata, zan sauke nauyin da Allah Ya daura min, idan da Hali I’ll go extra miles. Zamannan bazai tafi daidai ba seda Hadin Kanki, Abu daya zan rokeki, Dan Allah Hikmah kada Ki boye min zuciyarki, open up to me, hakan Zansan yadda nakeyi, amma idan kika rufeni, I might think wannan abin is right bayan kuma ke cutarki ne. Kinsan aure a ganina abu uku ne, building blocks dinsa, Trust, Communication and perseverance. Idan muka rike wannan ina ganin se munfi Wanda suka shekara dari suna soyayya. ” 

Bance komai ba amma naji shi, komai ya shiga Kaina, kuma alkawari na dauka Inshaaa Allah komai zai tafi daidai. Hannunshi ya bani na kama se daki, mukai sallah, mukaci Nama. Gani ga Nama babu sassauci, text ne ya shigo wayata, dake wayar na gefenshi, shi ya miko min, Nanah ce 

_Zuwa Ynzun nasan an kawo kaza, kamar yadda kika roka, na sako miki yajin garlic, jikin bedside drawer, akwai pain killers hade da box of tissue, se pepper soup a kitchen. Thank me later!_ 

Kawai se na saki dariya na mike tsaye, bina yayi da kallo har na dakko yajin, bai cemin komai ba seda na Fara dangwalawa sannan yace 

“Tuna miki akai” 

Murmushi nayi na bashi text din ya karanta. Kanshi Ya shafa yace 

“Muna godiya, tunda Kinada pain killers tashi na baki gajiya” 

Ture Naman nayi nace 

“Na koshi” 

Dariya yayi yace 

“Ci abinki Babyta” 

Daga Haka ya shige toilet, gaba daya se naji tsoronshi nake amma ya zanyi duk daga baya ne wannan. Tare muka kwanta bayan Munyi demacating gadon saboda Tsoro. Yana ta dariya yace 

“Kiyi kwanciyarki, ni aiki zanyi na 30mins” 

Cikin jin dadi na haye gadon kafin mintina shida bacci me nauyin gaske ya daukeni saboda gajiyar dana kwasa. Bansan lokacinda yazo Ya kwanta ba, amma ya jima yana kallona imagining nayi ruining plan dinsa, saboda yadda ya sawa ranshi duk ranar da yayi aure, ranar zaa yita ta Kare, hakanne kadai zaisa yaji completely ni din tashi ce. Amma yadda nake baccinan bazai iya tashi na ba, balle ya rigada yace bazai min komai ba, idan Yayi ya saba alkawarin. 

Kwanciya yayi ya rungumeni, nima bansani ba na rungume shi Nima. A Haka mukai bacci so peaceful and so lovely. Bayan Munyi Sallar asuba, Har seda gari ya fara haske Ya bani wayata yace 

“Kira duk Wanda ya kamata, kiyi musu bangajiya” 

Yana Gama fada ya fita, su Mama na Fara kira, mun danyi hira ta Kara min nasiha sosae sannan mukai sallama ina sharar kwalla. Sannan na kira Mami, 

“Hikmata kin tashi lafiya” 

“Lafiya lau Mamita, ya gajiya? ” 

Nan ta tambayeni Maina nace Yanzun yaje parlor, nan ta farfada min abubuwan Wanda duk tuni ne sannan mukai sallama. Wasawasa na kira mutane da yawa, wajen mintina talatin da fitar shi, hakan yasa na mike nabi bayanshi, se na tarar yana waya a parlor, kitchen na wuce, Inata kallon yadda ya hadu kamar a mafarki, na taba wannan na Danna wancan, na bude can na rufe Haka nayi tayi. Se can na daura Tea, ina tunanin me zan dafa na breakfast, naji gyaran muryarshi. Kashe Gas din yayi yace 

“Zo muje bacci bai isheki ba. ” 

Banyi musu ba Dan nasan Inada taurin Kai amma banida musu ko kadan, ranar da Mami ta Kara jaddadda min Aljannata tana karkashin kafarshi, da yazo nace zai daga min. A take ya daga ta yace 

“Baby na daga miki, shiga kawai zakiyi as far as kin bani Hadin Kai. Banida damuwa. ” 

Har daki mukaje, gadon yana nan yadda muka barshi, seda nayi stretching sheets din, na gyara sannan na kwanta, shima kwanciya yayi, nayi tunanin bacci Zamui amma se naga an fara wani abu daban. God nayi kuka, nayi cizo, nayi yakushi, majina amma ina Maina bai saurara ba seda ya maidani tashi, seda ya tabbatar na zama mallakinshi sannan ya dinga rarrashina, I was pissed off amma a Haka bacci ya daukeni. 

Na jima ina bacci se daf da Zuhr sannan na tashi, Dama ya lafiyar kura balle tayi zawo. Normally Ni me son bacci ce balle kuma sanadi yazo, ai se inda Mai ya Kare min. Da na tashi baya nan, ni daya ce a dakin, cikin takatsantsan na shiga toilet na Tara ruwa cikin katon bath, Allah yasa akwai heater toilet din kuma ya tafasa. Duk zafin da nake ji haka na daure nayi sitbath din sosae Dan nasan shi zaisa naji dadi. Daga nan nayi wanka nayi alwala sannan na fito. Wani sabon yanayi naji a jikina tamkar wata sabuwar halitta, naijini so empty, kamar an canja ni. 

Ina hango kofar kitchen naji wata azabbabiyar Yunwa, zama nayi ina tunanin ta inda zan Fara, Dan yunwar nan bazata jira nayi girki ba, emergency ce. Sallamar Maina yasa na dubi kofar da sauri, shi ne din ya shigo tareda Zama gefena, yace 

“Kin tashi? Ya jikin? Akwai inda yake miki ciwo? ” 

Kaina a kasa na girgiza Kai ina dan Murmushi, inajin dadin concern dinshi a Kaina, ina fatan farin cikinmu Ya daure. Hannunshi yasa ya dago fuskata amma duk yadda yaso nayi magana Ko na hada ido dashi naki, gaba daya wata irin kunyarshi nakeji, ji nake inama kasa ta bude na fada. Kanshi Ya gyada duk ya damu yace 

“Kiyi min magana mana, Haba Baby, daga abu daya se ki ta jin kunyata kuma? ” 

Juyar da kaina nayi Ina wasa da yatsuna, a raina Ina fadin Ni kawai ka bani Abinci shi ne abinda nake bukata. Kamar yaji se cewa Yayi 

“You must be hungry I know, taso muje kici abinci” 

Wata Ajiyar zuciya na sauke, kafin ya Mike tuni na mike, Nidai a parlon banga dining area ba Ashe hade suke a kitchen, dazun da na shiga da safe ban lura ba Sam. Dining din yana extreme na kitchen din, ya hadu iya Haduwa, kujera ya jamin na zauna sannan ya zauna shima. Tea Ya hadamin me kauri, yana aje min na Fara sha, amma ko rabi banyi ba na aje saboda abinda na gani cikin plate, Noodles ce, Irish da kwai fried. Kallo daya zakayi kaji ka koshi, saboda yadda noodles din ta sankare, Irish din yayi deep brown, Kwan kuwa rabi a kone yake. Idanuna na lumshe dan Bazan iya cewa Bazan ci ba, nasan it takes a lot of effort kafin yayi wannan girkin, kuma nasan saboda Ni ne. 

“Bar tea din haka, muci abinci” 

Kallonshi nayi nace 

“Bakai breakfast ba Kaima? ” 

Kanshi Ya girgiza yace 

“Inata jiranki ki tashi” 

Se naji babu dadi, hakan yasa na saka masa fork a gabanshi nima nasa daya, a tare muka kai bakinmu, na farko noodles din Anyi overcooking dinta, Irish ya kone amma ko laushi baiyi ba, Kwan kuwa daci yake saboda yadda yasha wuta. Muka Kalli juna mukai Murmushi sannan muka hadiye da kyar, da yayi Loma ta biyu kwace fork dina Yayi yace 

“Baby, kiyi hakuri ban iya girki ba, gashi duk na bata abincin” 

Murmushi nayi nace 

“Kayi kokari kuma naji dadi amma Bari a daura sabo” 

Kanshi Ya girgiza yace 

“A’a bazaki shiga kitchen ba, shiyasa nace su Mummy su dawo Ko Dan abinci” 

Dariya nayi nace 

“Sooner or later zanyi girki, so Bari na Fara yau” 

Kafada ya dage yace 

“Naki wayon, tashi muje mu ci a waje” 

Story continues below


Ya zanyi Haka nabi bayanshi muka fita. Wani dadi na dinga ji Kamar irin Anyi uncaging dina. Wani hadadden eatery mukaje, shi yayi mana order, naci sosae se petting dina yake, da nayi Nan zaace Baby ya akayi? Haka dai Yayi ta yawo dani bansan na ware na daina jin kunyarshi ba. Se bayan Maghrib muka je gida. 

Seda nayi sati daya ban kara fita ba, shima bai koma office ba, so kullum muna tare dashi manne da juna, rayuwar gaba daya tayi yadda nake mafarkin samunta. Ranar da Nayi sati daya Tun dare muka shirya akan zai kaini gurin Mummy (Salima). Da wurwuri muka tafi ko breakfast bamuyi ba, shima doki yake tunda shekaranjiya suka dawo daga maiduguri. Muna zuwa an gama breakfast hakan yasa nan muka fara sauka, seda muka gama sannan aka dawo parlor sabuwar hira. Babu wani zancen Sabo Dama tuntuni mun saba, se wajen daya da nayi sallah dakin Mummy na bingure a gurin na kama bacci, bani na farka ba se laasar nayi sallah naci Abinci, Mummy nata fadan bana cin Abinci, Wai ni ce. Maina kam idan ta fada Se ya kalleni ya kwashe da dariya. Bayan Sallar ishai muka tafi gidanmu. 

“Anyi resuming school fa” 

Na fada mishi ina ninke sleeping wears dinmu, yana zaune da short da vest saman gado yace 

“So soon? ” 

Juyowa nayi na Dan Harareshi na wasa nace 

“Tun last week aka koma fa, dama nayi 3 weeks a kano” 

Kanshi Ya gyada yace 

“To amma shi ne baki fada min ba, salon Yan gidanku suce na hanaki Karatu Ko? ” 

Dariya nayi Dan nasan su Baffa yake nufi idan yace Yan gidanmu, seda na karasa sannan na dawo gefenshi na kwanta nace 

“Ai tuntuni, Ido kawai ya zuba maka” 

“Da gaske kike? ” 

Dariya nayi na mike zan fita, ya janyo ni na fado jikinshi kaina ya buge da kirjinshi, kan na shafa ina yatsina fuska nace 

“Allah kana cin zalina fa, kasa na bige kaina” 

Ai bai bani amsa ba muka tafi wani gurin, he’s very romantic. Washegari gidanmu Ya kaini, ko shiga baiyi ba ya juya saboda zaije wani conference acan Garki. 

“Kice Mami tayi min favorite dina, Zanzo nayi lunch” 

Fuska na bata nace 

“Mami kuma? Bama ni ba” 

Murmushi yayi yace 

“Tohm kiyi min, Baby kinajin something about me? ” 

Idanuna na kyafta sannan nace 

“Kamar me fa? ” 

Kanshi Ya girgiza tareda riko hannuna yace 

“Is ok, ki gaida Mami da Daddy” 

Kallonshi nayi Dan na fahimci me yake son cewa, wato Ko na Fara sonshi. Bansani ba amma nasan ban taba kinshi ba, kuma Yanzun da zaace mu rabu inaga da bomb din da zan tayar se ya tada duniyar nan gaba daya. Babu inda bana jinshi a jikina, ina jinshi mutum me amfani da kuma muhimmanci cikin rayuwata. 

Hure min idanu yayi yace 

“Kije, zan makara” 

Kaina na gyada tareda kissing ganinshi dake cikin nawa sannan na dauki handbag dita nayi cikin gidan. Tara daidai na shiga parlon, Mami se kai kawo take daga parlor zuwa kitchen. Daddy yana zaune bansan ya akai baije office ba, sallamata yasa ya dago fuskarshi cikeda Murmushi yana fadin 

“Oyoyo Daughter! ” 

Gefenshi na tsuggunna na gaisheshi dan nafi sakin jiki da Mami akan Daddy, hannuna Ya kama yace 

Story continues below


“Zauna anan, ina Ibrahim din? ” 

“Yaje NMC Conference, yace na gaisheku” 

A lokacin Mami ta fito, tayi gayu sosae , Nikam idan ban koyi gayu da kwaliyya ba, ba Mami ta haifeni ba. Mikewa nayi na tafi da gudu na rungume ta Ina fadin 

“Mamita!” 

Kaina ta shafa fuskarta fal murna tace 

“Azizaty, surprise ne hakan? ” 

Kaina na gyada, Daddy dake kallonmu cikeda shaawa yace 

“People I’m jealous fa” 

Dariya duka mukai, Daddy yace 

“Wannan partiality ne duk tafi sonki Hafsa, har Yanzun kunyata takeji.” 

Gefenshi na zauna nace 

“Daddy, nafi sonka fa” 

Daddy yayiwa Mami gwalo, Itakuma tace 

“A Ko makaho ya shafa yasan daidai.” 

Dariya nayi anan mukai breakfast, Daddy Yayi canji akan yanada meeting da senators a chamber dinsu. Har Mota muka rakashi ya tafi sannan muka dawo. Mun jima munata hira da Mami sannan muka tafi kitchen tace min Baki zatayi. 

“Azizaty, yaushe zaki koma school ne, kada ki saki jiki fa. ” 

“An koma ai tun last week” 

Da Mamaki Mami tace 

“Shi ne baki fada min ba, Kai ni na rasa irinki” 

Murmushi nayi Ina tsane cabbage din cikin collander nace 

“Mami kunata shiri, shi yasa amma dazun na fada masa ai” 

Kanta ta gyada muka cigaba da hira, tana ta nuna min muhimmancin su Mama, kada na yardasu. Suma iyayena ne. Mami ta Fara fitowa bayan Munyi sallah ni na zauna amsa call din Maina. 

“Baby, na gaji Kamar na gudo” 

Dariya nayi wadda Yanzun hardly nayi mintina banyi ba, to duk mutanen da nake tare dasu are funny, 

“A’a ka rufa asirina , ka zauna. Zakazo lunch din? ” 

“No, babu wannan chance din. Se dinner Zamui Inshaaa Allah ” 

Kaina na gyada nace 

“Allah Ya yarda. Take care of you kaji” 

“I’ll Baby. Ina sonki” 

Can Kasan raina nace I feel like, amma a zahiri Murmushi nayi, daga Haka mukai sallama na aje wayar na fito da alamun Mami bakinta sunzo Dan na Fara jiyo muryoyin mata. Su uku ne suna zaune cikin sofa, sun Juyawa kofar bedroom din baya, se bayansu kawai nake gani. Da sallama na shigo Ina fadin 

“Sannunku da zuwa” 

Gaba dayansu kallona suka bini dashi Har na zauna gefen Mami, 

“Anty Hafsa, Lulu ce? OMG kuna kama kamar ke wallahi” 

Daya daga cikinsu ta fada, Murmushi nayi, Mami tace 

“Hikmah, ga Zahra, Naeeyla da Afaf. Na miki bayaninsu ko? ” 

Kaina na gyada nace 

“Eh, nice to meet you Sisters” 

Dukkansu suka zo suka rungumeni. Ai se hira Kamar mun saba, anan mukai lunch. Zahra dake da tsohon ciki suka shiga daki da Mami, Naeeyla ta kwanta tana waya da mijinta tace kwana daya ne tsakanin aurenmu da nata. Se nida Afaf muke hirar, dake ita ce sa’ata, Can Afaf tace 

“Nifa kamar na taba ganinki somewhere” 

Nima kallonta nake tayi, fuskarta looks familiar, can nace 

“Budurwar Hamma Aiman right?” 

“Aikuwa dai, Kinsan da nayi tunanin sonki yake. Idan Yayi min maganarki kamar na mutu Haka nakeji” 

Dariya nayi nace 

“Kowa haka yake gani, amma mu munsan ba soyayya muke ba” 

Wasawasa munata hira Har dare, kowacce mijinta zai zo daukarta, Afaf driver zai zo daukarta. Kowacce seda Mami tasa ta tayi wanka, muka ci gayu muna jiran mazajenmu. Daddy ya Fara dawowa se Maina. Tare sukai sallar maghariba da ishai, mukai a gida sannan muka shirya dining. Daki na koma, bansan dalili ba se naji gabana yanata faduwa. Nafi mintina goma a kwance sannan Afaf ta shigo tace Nazo, kowa ya dawo. Tare muka fito, idanuna karaf cikin na Abdallah dake kokarin karbar juice daga hannun Naeeyla, jikina Har wata irin rawa yake nace da Afaf 

“shi ne mijin Naeeyla Dama ” 

Tabe bakinta tayi tace 

“Destined couples kenan! ” 

I was numbed entirely, ji nayi wani abu ya tokare min makoshina, na kasa Matsawa dake Daddy da Mami basu rigada sun fito ba, se ji nayi an rungumeni, wannan hug din ya sassauta min zuciya ta, hannuna yaja muka isa dining din muka zauna, mijin Zahra na Fara gaidarwa sannan muryata na dan karkarwa na gaida Abdallah, shima gaba daya yanayinshi Ya canja yace 

“Sannunki Amarya” 

Wani irin tukukin takaici ya kama ni so Sannu Amarya yace. Gaba daya hankalina se na tattara na mayar kan mijina, dukda abincin cakalkala kawai nake har seda yace 

“Mami, ‘Yarki bata cin Abinci fa” 

A tare Daddy da Mami suka kalleni, Daddy yace 

“Me kike son ci? ” 

Kaina na girgiza nace 

“Kawai kaina ke ciwo” 

Mami tace na gama nasha magani. A daddafe na karasa na gudu dakin Mami Inata kuka, bansan kukan Meye ba amma zuciyata Kamar zata fashe Haka nake ji. A Haka Mami ta sameni, gaba daya hankalinta ya tashi, tambayar duniya aman naki fada mata komai. Se ta kyaleni tace na shirya mijina na jirana. Fuskata na wanke na shafa powder da lip balm, nasa khol se idon nawa Ya washe. Ina gyara zaman Dan Kunne na Mami tace 

“Mijin Naeeyla shi ne Abdallah saurayinki? ” 

Da sauri na juyo muryata na rawa zanyi magana ta karaso inda nake tsaye tace 

“Shhhh!!! Shi ne? ” 

Rungumeta kawai nayi Ina kuka, cireni tayi daga jikinta tace 

“Kukan me kikeyi? Har Yanzun kina sonshi ne? Baki karba Maina matsayin miji ba?” 

Kaina na girgiza nace 

“Mami zuciyata Kamar zata fashe, ce min yayi Wai Sannu Amarya” 

Ina kallon fuskar ta naga bacin rai akai, Tsaki tayi tace 

“Uban me kike son yace miki? Sannu me? Bana son shashanci da wauta. He’s happy been with her, ke bazaki iya moving ba kenan?” 

“Mami zuciyata….. ” 

“Tashi ki fita min a daki, kije can ki karata. ” 

Mikewa nayi handbag, veil Duka a hannuna, hawaye ya bata min fuska. Yana zaune shida Daddy na fito, dukkansu kallona sukai, Daddy yace 

“To me ya faru? ” 

“Seda safe” 

Daga Haka nayi waje, cikin sauri ya biyo bayana, duk rarrashina da yake kasa daina kuka nayi saboda na batawa Mami rai. 

Ban iya abu kadan ba, Ko damuwa nasa a raina bansan in cireta lokaci daya ba, bansan abinda mutane suke cewa overlooking ba. A’a yadda nake da naci da taurin Kai Haka nan zuciyata take idan ta takura min. Wannan abin da Abdallah yayi min yasa nayi kuka Har mukaje gida ban daina ba, shi kuma bawan Allah Maina duk tunaninshi saboda naga Mami ne, baisan ba haka bane. Seda muka je gida sannan nayi Shiru amma fuskata babu alamar walwala a tare da ita. Shima se ya kyaleni kawai ya cigaba da alamuranshi. Seda safe tukun na wartsake, ranar ma zai koma wannan conference din, so tunda nayi Sallar asuba na wuce kitchen na shirya masa breakfast. Na hada mishi ruwan wanka, sannan na Nemo masa kayan sawa. Ina kwance na dunkule cikin blanket ya fito daga toilet, kan stool Ya zauna tareda kallona yace

“Madam, taso ki shafa min Mai” 

Fitowa Nayi a Blanket din, Nazo na dauka lotion din, munata hira Har na gama. Yace 

“Awnnnnnn, Thank you Baby. Gobe zamu Je Kano, daga can mu wuce Zaria. So idan na dawo se muje shopping Ko? ” 

Kaina na gyada ina Murmushi nace 

“Allah Ya kaimu” 

Kaina ya shafa, ni kuma na fita na kawo mishi breakfast din. Tea kadai yasha yace nayi packaging Sauran, jiya ya makara, so yau baya son Yayi latti kuma. Har Mota na Kai shi ya tafi sannan na dawo, straight daki na koma bayan na kulle ko ina, nayi setting alarm na Fara bacci. Ban tashi ba se Karfe goma da rabi. Dakin na gyara, na dawo parlor na gyada, haka kitchen ma sannan na daura noodles na ci. Nayi wanka nayi sallah sannan na dawo parlor na kirashi 

“Baby! Ya gidan ” 

Kallon gidan nayi nace 

“Lafiya lau, ya conference din? ” 

Dan Tsaki yayi sannan yace 

“Ki Bari kawai, Se ynzun zamuyi breakfast fa ” 

Idanuna na dan zare nace 

“Kai suna wahalar min da kai fa, kenan Se yamma zaka dawo” 

Yadda yayi Murmushi nasan dadi yaji nace zasu wahalar min da kai. 

“To ya zanyi. Kiyi kallo kada kiyi tunani, I love you! Se na dawo” 

Kaina na gyada Kamar yana kallona nace 

“Take care” 

Daga Haka mukai hanging, na kunna kallo, da can ni ba fan din kallo bace, shiyasa gaba daya na kasa concentrating Se wayata da nake ta dannawa, na duba Mami ko tayi min reply amma babu, duk se naji babu dadi, Dan tun ina hada masa breakfast na mata text amma babu reply. Shi Daddy dama ya kirani tun sassafe. Ina nan zaune muna chatting da Nanah da Najaatu, dukkansu tambayata suke ko Inada ciki, banda dariya babu abinda nake, nace kowacce Tazo Abuja ta duba da kanta. 

Se naji knocking, mikewa nayi na leka ta door hole, anan na hango Nafisa tana waya, da murnata na bude tareda rungumeta nace 

“Ashe zakizo da gaske?” 

Se lokacin naga mutanen dake bayanta, tare muka shigo, daga kamannin su nasan suma cousins dinmu ne, 

“Nafi wai bazaki aje wayar ba ne? ” 

Na fada ganin Har lokacin wayar take, kuma so nake tayi ta gama tamin introducing mutanen. Mikewa nayi na Fara entertaining dinsu, seda ta gama sannan tace 

“Wannan Amaly ce, Uncle huzaifa na Edo state shi ne Babanta, wannan Munnira yar Anty Amina ce” 

Kaina na gyada nace 

“Sannunku da zuwa” 

Ina tunanin familynmu babu Shiru Shiru sede idan Baa saba ba, kafin wani lokaci mun dinke Se hira muke. Suka tayani na hada dinner sannan suka tafi. Ina idar da Maghrib nayi wanka nayi kwaliyya sosae, na dinga tunanin abinda zan saka ma, nasa Atamfa, nasa lace, Haka shadda, material komai. Kawai na dakko wani Jeans na saka, ya kamani sosae tamkar shi ne skin dina na biyu, wata off shoulder top white silk ce sosae. Ko hula ban saka ba, na dakko Sarka nasa sannan na koma parlour. Ina zama ya turo kofar, Juyawa nayi cikin daukar hankali ina kallonshi, he looked so tired and exhausted. Babu necktie ya cire, suit din a kafadarshi, waya a hannu, briefcase dayan hannun. Inata kallonshi a raina Ina ayyana Meye Laifin wannan Mutumin dake gabana, ko sau daya bai taba nuna min komai ba banda zallar kulawa da soyayya. He loved me and he still loves me. Bai taba ganina ba, baisan yadda looks dina yake ba amma duk da Haka, he waited for me. Bai taba kallona yace min ya kafata take ba. Tunda na aureshi ban kara kunci ba, banni da farin ciki da kullum yake sani ba. To me yasa Dan naga Abdallah naji ina kuka, ina nufin Allah zanyiwa butulci akan duk daukaka ni da yayi, duk yadda ya juya alamurana. 

Story continues below


Tafiya nayi cikin hanzari na rungume shi, Kamar Ina masa rada nace 

“I love you! ” 

My Friend kankameni yayi, dama tuntuni kayan hannunshi sun samu matsuguni akan sofa, cikin Kunne na yace 

“Baby kina sona? ” 

Kaina na gyada masa in confirmation, sannan nace 

“I love you! So much….you’re my world my everything, my knight in shining armor!”

Wani passionate, sensitive and seductive kiss yayimin da seda na shide, ji nayi tamkar kafafuna bazasu iya daukar jikina ba, Yayi kasa da kanshi daidai yadda zan iya mishi magana, nace 

“Hold me zan fadi” 

Sosae Ya rikeni seda na dawo nutsuwata sannan yace 

“Kinyi kyau, da alamun Baki son komawa makaranta”

_*Nobody sees, nobody knows, we’re a secret can’t be exposed, that’s how we reach, that’s how it goes, far from the others, close to each other! In the daylight when the sun is shining, in the late night when the moon is blinding, plain sight like stars they hifing*_

Dariya nayi, ina kallonshi nace 

“Haba! Bari naje na canja kayan toĺ” 

Kwace hannuna nayi na nufi dakin, ai se naji Ya biyoni yana fadin 

“Haba Hikmata wasa nake fa” 

Sarai na jishi kuma I’m not changing, wardrobe na bude kamar me neman kaya, anan ya taddani. Nace muku Maina Ya iya wasan banza? God har ya koya min, indai muna mu biyu to babu zancen zaman lafiya Har wasan doki muke. Yana shigowa ya tunkude ni daga gurin, Allah yasa gado ne a kusa na fada, ya danne ni. Inata ihun kiran dauki yace 

“Zaki Kara? ” 

“A’a wallahi, ka Dagani to ” 

Daga ni yayi munata dariya sannan Yayi wanka mukaje muka ci Abinci sannan na gyara shigata muka tafi shopping, maimakon ayi na school se akai na gida, Bance komai ba Har mukaje gida. 

Washegari nasan zamuje Kano, so Tun hudu na tashi na harhada abinda zanyi amfani dashi, kaya kadan na dauka tunda duk suna can Zaria din. Se asuba ya tafi massallaci Ni kuma nayi a gida sannan na tafi hada breakfast. Ya dawo ya miko min wayarshi Wai Baffa ya kirani amma wayar tawa bata shiga ba. Haka kurum naji gabana ya fadi, me zaisa a kirani da sassafiyar nan. Zama nayi kan stool nayi dialing wayar, yana dauka muka gaisa yace 

“Anata shirin komawa makaranta ko? ” 

Kaina na gyada nace 

“Eh Baffa, amma zamu Fara zuwa nan ma kafin mu wuce” 

“Yayi kyau hakan. Amma Kinsan jiya na kira Daddynki akan Maganar karatunki. Munyi shawara dukkanmu. Kinga da da Yanzun ba daya bane, Yanzun Kinada aure, Zaiyi wani iri kina can, mijinki na wani gurin. Se nake ganin ki manta da can din kawai ki Fara a fresh……” 

Hannuna nasa na dafe stool din da nake Kai, saboda ji nayi jiri zai fadar Dani, kaina nake gyadawa, zuciyata na wani irin bugawa, amma kwakwalwar Kaina fada min take all is well. Namiji Dan Gata! Saboda shi zan bar karatuna level 3 na koma 1. Baffa da Daddy sunfi karfin komai, hakan yasa bayan Ya gama dogon sharhi nace 

“Baffa babu komai, Allah yasa hakan ne mafi alkhairin” 

“Yanzun nake shirin binki, naga me kikeyi, time na tafiya” 

Kwantar da kaina nayi nace 

“Baffa yace wai na Bari ba sai na koma ba, Zaa samo min wata school…..” 

Da sauri ya katse ni yace 

“Saboda me? Haba dai ” 

Gyara zaman Kaina nayi nace 

“Seriously wai saboda zan bakka Kai daya, gwara na hakura” 

Shiru yayi kafin can yace 

“Amma an shiga hakkinki ai, idan na Bari kamar I’m selfish ne” 

Dan Murmushi nayi nace 

“Kai Baka San zancen ba, fada maka akai Bakada laifi. Su kuma sun isa dani shi ne dalili. Mami tace min aure is sacrifice, you can sacrifice every of your happiness for your partner. So don’t feel bad kaji Mine! ” 

Rungumeni yayi, se naji sanyi ya Kara ratsa min zuciyata, nasan Mami ita ta kawo wannan shawarar, tana ganin Kamar idan na koma zan damu Ko kuma na kula Abdallah, not knowing na rigada na wuce gurin. 

Ranar babu inda mukaje, se dare ya tafi gidansu sannan na kira Mami, Tana daukar wayar nace 

“Mami Kinyi fushi Dani ne? Mami kiyi hakuri dan Allah” 

Murmushi tayi tace 

“Hikmata, Mamanki tayi kokarin miki tarbiyya wadda ko ni ce na raineki se hakan. Sede you lack Abu daya, tawakalli. A zamana na gane Baki daukan Abu cikin sauki. Komai a gurinki me zafi ne. Ki daina zaki sha wuya. Supposing jiya Maina yasan kukan da kike ya zaiji? He’ll be heartbroken. Dan Allah Hikmah Ki manta komai Ki rike mijinki Kinji? Ibrahim shi ne kadai gatan da zan miki, Ko banida rai nasan I’ll rest kina hannu na gari” 

Hawayena na share nace 

“Mami Inshaaa Allah. Kuma Allah Ina sonshi” 

Fadar Haka naji muryarta ta canja, ta dinga shimin albarka sannan ta kwantar min da hankali tareda min alkawarin school very soon. 

Seda nayi sati biyar, Nanah Har ta gaji da tambayar yaushe zan dawo. Ranar da weekend muka tafi Kano, Kamar a cinye mu Dan kauna. Kawo wannan kawo wancan. Anan muka kwana, da zan tafi duk naji kewarsu. Daga nan muka wuce Zaria na kwashe kayana. Nanah Har da kukanta. Abinda Nasan ba amfani zanyi dashi ba haka na bayar, na dauki na dauka. Muka juya Abuja. 

Thank you for always standing next to me! 

_My silent is in your arms, when the worn gives, I can bear sometime, on your shoulder I can reach endless sky, feels like paradise. Put two and together forever will never change_

Bayan Watanni Hudu 

Tunda na farka Sallar asuba nake jin wani irin Kwadayi, kuma na cheese abin mamaki ni ba fan din cheese bace Mussaman cheddar cheese, bana sonshi. Amma Yanzun tunashi idan nayi se naji wani salivation a bakina. tare mukai alwala Ya wuce massallaci, ni kuma nayi rakaatanul fajr sannan na tafi kitchen. Freezer na bude na ciro wata bowl da froze chicken breast yake, Allah Yasa shekaranjiya muje shopping na siyo Harda cheese din. Fito dasu nayi daga fridge na aje dan su sake jikinsu. Ball of yellow pepper, da green da red na yayyanka Manya Manya. Sannan na dakko baking tray, nayi greesing dinshi, na jera chicken breast din akai, peppers dinnan na zuba akai, nayi seasoning sannan na yaryada Mai nasa a oven. Flour, Mai, gishiri na kwaba da ruwa, kamar kwabin meat pie na barshi ya saki jikinshi. Daki na koma nayi sallah. Inata mamakin kaina, duk yadda nake da ci bantaba jin inason abu wuta wuta ba irin Haka ba. Mamaki sosae nake. Ina idarwa ko adduar Arziki banyi ba na koma kitchen. Ina zuwa na Barbada flour kan working surface na dakko pin ina fadada ta in a round shape, wani round cutter na dakko na yanka ya fitar da shape din sosae. Seda nayi goma sannan na dakko nonstick frying pan na daura akan cooker, low heat, nayi greesing da mai sannan na dakko round shaped flour ina sawa, idan Yayi na juya. Har na gama. Na aje ya huce na Fara hadawa Armor abincinshi, ya koma aiki, yana nan a National hospital nan yake. Yanzun consultancy dinshi yake a cikin asibitin. 

Kunun gyada na hada masa da farfesun kifi Wanda tun jiya nayi yau warming kadai nayi. A gefe nayi setting na dawo kan nawa abincin. Sliced mozerella cheese, na saka cikin wannan pita bread din dana gasa, pita bread a kasa, sliced mozerella cheese guda biyu se na rufa wani pita bread a sama. Na jera akan baking tray bayan nayi greesing. Wannan Chicken Breast din na dakko, Yayi laushi sosae, fork nayi using na farfasa shi, na zuba tsakiyar pita breads dinnan, na grating cheddar cheese na watsa akai na rufa Wasu bread din masu cheese akai na maida oven. Zama nayi na hada plain black tea, Inasha. 

Daki na koma, ga mamakina Har ya fito a wanka, taya shi nayi ya shirya ina ce masa 

“Amma Armor ka shigo Baka nemeni ba” 

Shafan Kai yayi yace 

“Naga Yau Kwadayi ya tashi, tun asuba ana kitchen kinga gwara na barki kafin Anjima Kice na dameki” 

Bakina na turo Ina fadin 

“Dama Haka mukai dakai? Are we not team? ” 

Hannuna yaja muka fita zuwa kitchen yace 

“Ai munfi team, mu squad ne, so kinga ni dake babu me jin kanmu” 

Hannuna na dunkule shima ya dunkule muka buga sannan nayi ihu tareda rungumeshi, nasan mijina baifi mijin kowa ba amma a gurina, Ina ganin babu kamarshi, babu Macen da zata zo tayi min bragging akan mijinta. Na yadda akwai matsaloli sosae cikin aure kuma ko Yaya kuke son Kanku dole ne Ku fuskanci hakan amma ranar da aka kawoni gidannan, yace min aure consist of 3 building blocks, Trust, communication and perseverance. Hakane su Muka rike shiyasa muke ganin daidai. A Yanzun Ina ganin munfi Wasu Wanda sukai shekaru goma in curtship Sannan sukai aure, to munfi su son juna da tattalin junanmu, shi nawa ne nima tashi ce. Kullum ina Kara shiwa Hajiya Talatu adduar shiriya at least tayi kokarin wajen kara kusanto ni nida abin kaunata. 

Story continues below


Tare mukai breakfast kowa yana cin nashi, God idan na yanka na ciro naga wannan cheese din se naji Kamar nafi kowa dace. Muna gamawa na aje Sauran sannan na fito na rakashi. 

Yana tafiya nayi yadda na saba, gyaran gida Se bacci amma ranar banda juyi babu abinda nakeyi, daga karshe wani mugun ciwon Kai ya taso min, idanuna a lumshe Ko iya budeshi ma banayi, abin se mamaki yake bani, saboda bana rashin lafiya, Ko annual malaria da ake se nyi shekara hudu banyi ba, banda wannan Asthmar babu wata cuta da take damuna Kamar ita. A hakan nayi ta kwance har azahar tayi, Anma na tashi nayi na kasa, ko idona bana iya budewa balle nayi sallah, Haka na ayyana ina Sallar tunda addini bai daukemin ba, dole a kowanne Hali nake matsawar Inada tsarki dole se nayi ta, if not? 

Zuwa laasar, zazzabi me zafi Ya rufeni, Ko numfashi naja to wani huci me zafi ne yake fita, idona se hawaye yake, tsorona daya kada na mutu Ni daya, azo ace Baa San me ya sameni ba, wannan kukan yasa zazzabin da ciwon kan suka karu, zafin zazzabin da yadda nake jan numfashi da kyar yasa na samu attack, ai na fitar da rai, mutuwa zanyi ma kawai. Ganin abin Yayi yawa yasa na daddage na mike na amma wani mugun jiri Ya kwasheni na koma gadon. 

Da karfi aka turo kofar, wata Ajiyar zuciya na saki dan nasan anzo rescuing dina. Muryar Mummy naji tana fadin 

“Na shiga uku ni Salima! Me zan gani Haka? ” 

Daga nan bazance ga abinda ya faru ba, na farka kawai na ganni a asibiti, Mami se kuka take a kusa dani, kallonta nayi da jajayen idona na riko hannunta nace 

“Mamina, Ki daina kuka gashi na farka” 

Se lokacin ta fahimci hakan, cikin sauri ta rungumeni tana fadin 

“Hikmah, Ina ke miki ciwo, me yasa baki fada masa bakida lafiya ba?” 

Dan Murmushi nayi Dan garau nake jina, tamkar bani bace dazun kamar zan mutu ba, hannunta na riko nace 

“Mami babu abinda ke min ciwo, ki daina kuka” 

Sakina tayi na zauna, se kuma ta fita can se gata ta dawo da nurse din, tana zuwa ta ciremin oxygen din dake hancina, ta kashe. Tayi rubuce rubuce sannan tace 

“Sannu Doctor zai zo dubaki Yanzun ” 

Kaina na gyada ina Murmushi, fita Tayi na Kalli Mami nace 

“Zanyi sallah” 

Ita ta rakani toilet nayi alwala nayi laasar da maghariba, dama su kadai suka wuceni, Inayi nace 

“Mami ke kadai kikazo ne? Ina Yaya ” 

Zama tayi gefena tace 

“Sunje gida su dawo, Yayanki bai sani ba, ya kirani yace zai shiga surgery, tunda ya fita baki kirashi ba, kuma shi yayi kiran bai sameki ba, yasan dole babu lafiya shi ne mukazo da mummynki, dama Kinada Asthma? ” 

Se lokacin na tuna ban taba yi ba tunda nayi aure, kuma Ashe ban fada musu ba, Haka na fada mata lokacinda akai diagnosing dinta. 

“Mami, inason naci burger da cheese ” 

“Burger kuma? Inace Baki son cheese ” 

Shiru nayi sannan nace 

“Nima yau ina tashi naji shi nake so” 

Idanunta ta tsira min tace 

“Yaushe rabonki da kiyi period? ” 

To fa anzo gurin, ni inaga tunda nayi aure twice period dina yazo a wata biyar, oh am I that careless kenan? To shi me yasa bai gane ba shima. 

“Mami sau biyu nayi, month din farko, na tsallake daya, ana uku nayi. Se wannan fourth and fifth dinne banyi ba. Mami…. ” 

Rungumeni tayi tace 

“Alhamdulillah! I was so scared zakiyi gadon rashin haihuwa amma Allah Yayi reversing abin.” 

Ban bata amsa ba mukaji sallamar Yaya da Doctor da zai dubani, ban sani ba Ko ya manta Mami tana gurin ne, yana shigowa ya rungumeni yana fadin 

“You gave me a heart attack baby, Dama Kinada asthma Baki Taba fadawa kowa ba, Sannu akwai wani abu kuma? ” 

Murmushi nayi Dan Mami da Doctor sun fita nace 

“I’m fine Alhmdllh, ya aikin, ka gaji Ko? Kaci Abinci” 

Hancina Ya lakuce yace 

“See you, waye ya damu da Abinci, da gajiya, idan rayuwata Tana kwance babu lafiya” 

Dadi naji, lokacin ya fita yazo da Doctor, nan ya daura ni akan drugs, yayimin tambayoyi kafin nayi PT serum, mukaje scanning nan akai confirming Inada ciki wata biyu babu sati daya. God! Murna Har na rasa waye yafi wani. 

Washegari akai discharging dina, Tundaga ranar nake laulayi amma ba wani sosae ba, bana girki, Mummy ke aiko mana , Harda yar aiki saboda cikin da yakai 3 months Se na Fara bleeding, akai scanning ya nuna cikin na rawa, so I was on bedrest for almost a month daga nan muka cigaba da rainonshi. tunda muka kai 7 months muke shiri, kowa shirin tarbon baby yake, Har Yan Kano, Mama Tazo ta ganni tayi kwana daya ta koma. 

Wasawasa a hankali rayuwa take tafiya, cikina yakai watanni Tara, kullum cikin shiri muke amma har nayi 38weeks ban Fara labor ba, idan nayi masa complain se yace ai, 40weeks ne se a dauki action, kamar yayi min Baki kuwa se da nayi 40weeks din amma babu ciwo. Babu shiri muka tafi asibiti, nan akai scanning Twins Wanda mun rigada mun sani, amma leading din kwanciyar shi oblique , se CS. 

Babies din Mace da namiji ne, da na farka aka kawo minsu yace nayi musu huduba, ajesu nayi na Kalli mazauna parlon nace 

Kowa yaga hankalina, yaga kaifin tunanina. 

OXFORD UNIVERSITY, ENGLAND. 

20years leap 

Cikin makeken conference hall na medics dake cikin university, manyan likitoci, Wanda suke daga mabanbantan kasashe across the world. Wani workshop ne hade da conference aka hada anan akan Head transplant da ake son a gwada. 

Dr. Ibrahim Maina yana daya daga cikin mutanen da suka samu privileged din zuwa wannan conference din, kasancewar duk Nigeria babu wani Neurosurgeon da yayi fice yasan aikinshi Kamar shi. 

Karfe hudu Dr. Canavaro wanda shi ne leader na wannan head transplant din, yayi akan monkey which was proved to be successful, har monkey yayi surviving for 20hours sede unconscious. Shi ya bada closing remark, da lokacinda Zaa Kara Haduwa ranar Monday. 

A gajiye tikis Maina Ya fito daga dakin taron, shekaru sunja kana kallonshi Kasan Ya manyanta, amma jin dadi da kiyayewa yasa hakan bai nuna sosae ba. Cab ya samu ta kaishi har flat din da ya sauka. Hannunshi yasa ya kada door bell din sannan ya tsaya yana jiran a bude. ya kusan mintina uku sannan aka bude kofar, wata kyakyawar mace ce a tsaye wadda shekarunta suka Dan ja amma ba can, Har Yanzun kamanninta yana nan babu wani abu da ya canja, Illa cika da ta kuma, da nutsuwa hade da alamun kwanciyar hankali. 

Briefcase dinshi Ta karba, fuskarta dauke da Murmushi tace 

“Masoyi, Barka da zuwa. You look tired” 

Murmushi yayi yace 

“Ganinki ya warware komai gimbiyata. ” 

Hannunshi yasa ya sakalo na Hikmah wadda fuskarta babu komai banda Murmushi madaukaki. Tare suka shiga, cikin cushion Ya zauna yana fadin 

“Gidan Yayi Shiru, Ina Sauran Yaran da Hamida? ” 

Aje glass cup me cikeda ruwa tayi tace 

“Sun fita yin shopping, sannan akwai wata kawarta zata biya” 

Kanshi Ya gyada yace 

“Muje Yau a tayani nayi wanka, kafin su dawo a bani excuse” 

Dariya tayi tace 

“Kai Ko? ” 

Hannunshi ya Mika mata ta kama, suka wuce bedroom dake can gefe, gidan babu laifi yanada girma, katon parlor ne, me kunshe da bedrooms biyar, akwai na Hikman daya, Hamida daya, yaransu mata biyu se dayan na mazansu. 

Seda ta tayashi yayi wanka sannan suka fito, sukaci Abinci aka koma daki aka baje soyayya, wadda bata taba tsufa ba, sudai masoyan ne suka kwana biu. 

Karfe Tara na dare gaba daya gidan ya karade da sautin Door bell, hannu Hikmah ta goge jikin apron din jikinta ta nufi kofar, tana budewa gaba daya suna tsaye sunyi matukar gajiya, ran Afeeyya a hade saboda ta tsani yawo, ita Bata fiya shiga cikin mutane ba, amma Anty Hamida ta daukesu Tun safe se dare Yanzun zasu dawo. 

Mimi suka gaidar Kamar yadda suke kiran Hikma, Tana ta musu ban gajiya suka shigo ciki sannan suka baje cikin kujerun parlon, fitowa Yaya Kamar yadda suke kiran Maina Yayi daga bedroom din Mimi. Gefen Hamida ya zauna, Yaran suka gaisheshi, cikeda kulawa Ya amsa sannan ya dubi Hamida yace 

“Ya hanya? ” 

Kanta ta Dan kwantar Kan kafadarshi tace 

“Tiring, ga Afeeyya nata fushi” 

Dariya yayi daidai zaman Mimi gefen Afeeyya yace 

“Kin gajiyar da ita ai dole” 

Take Afeeyya tayi tace 

“Mimi abincin kin gama” 

Kanta ta gyada, sannan suka mike dukkansu suka isa dining din, Tuwon shinkafa miyar egusi, shredded beef, se white rice hade da stew da salad. Se strawberry monk. Duk sunfi farin ciki da ganin Tuwon musamman Hamida fadi take 

Story continues below


“kai Doctor, abincinki is always the best. Allah I envy yadda kike girki” 

Dariya sukai, Hamida matar Maina ce ta biyu. Ya aureta shekara goma baya, shekaru goma bayan aurensu da Hikma. Yaranta biyu dukkansu mata ne. Maryam da Salma, Maryam shekararta bakwai, Salma hudu. Yaran Hikma biyar, twins dinta na farko Afeeyya da Akram, seda tayi shekara bakwai bata Kara haihuwa ba, ranar da ta haifi Al’amin ranar Akrma ya rasu, ya rage Se Afeeyya ita daya. Bayan Al’amin yayi shekara hudu ta haifi me sunan Nafi’u ana ce masa, Munsif, se Hafsa da Salima suma twins ne, Ammi da Mami. 

Hikmah tayi MBBS a Germany, Yanzun Haka gynaecologist ce wadda ake ji da ita a fadin Abuja. Suna gama cin Abinci, suka dawo parlor aka Fara hira, Afeeyya tace 

“Yaya yaushe zakuyi head transplant din ne? So nake naji yadda possibility hakan zai zama” 

Dariya Maina Yayi yace 

“Curiosity ko, Kinsan Bazan iya yin wannan aikin ba. Saboda akwai opposition sosae” 

Kanta ta gyada, gidan Yan Boko kafin wani lokaci gurin Ya kaure da hira, banda hirar Karatu babu abinda suke, se wajen sha daya sannan suka tafi bacci. Afeeyya tana shiga tayi saurin karasawa bedside drawer ta dauki wayarta, missed call din Noafal ta tarar, an hour ago. Kanta ta dafe sannan tayi Shirin bacci ta kwanta ta dauki wayar ta kirashi. 

“Loml, ina kika shiga? ” 

Babu abinda Afeeyya take jin farin ciki akai irin taji Noafal yace Loml, wani nishadi take yi, tana jin idan babu shi ya rayuwa zata kasance? 

“Muna taredasu Mimi, se Yanzun na shigo. Ya aiki? ” 

Daga dayan bangaren yace 

“Tiring, amma nan da sati hudu dukkan Gajiyata zata warware ko?” 

Dan Murmushi tayi saboda wata daya ya rage ayi aurenta itada Noafal, Babban Dan Hamma Mussadiq, soyayya ba karya bace, abinda babanshi ya kasa samu shi kuma gashi Zaiyi pursuing, dama Haka rabo yake. 

Sunfi awa suna hira sannan Yayi mata sallama shima Baa son ransu ba, Haka suka kwanta tamkar su janyo ranar. Da sassafe bayan tayi sallah ta koma bacci, Maryam Tazo wai Anty na kiranta, Dan Tsaki tayi ta nufi dakin Hamida, seda suka gaisa sannan Hanifa tace 

“Afeey zaki rakani wani mall anjima” 

Idanu ta zaro tace 

“Anty yauma fita zamuyi? ” 

“Eh” 

Ta bata amsa ba tareda ta kalleta ba, Kai Afeeyya ta gyada tace 

“Allah Ya kaimu ” 

Se Hamida tayi dariya tace 

“Ko ke fa, Kinsan nafi son kafin mu bar London ace mun rage siyayyarki, jiya mun gama magana da Doctor.” 

Kanta ta gyada saboda Yanzun har ta Fara rama, wannan shirin bikin kamar zatayi hauka, har ji take dama gidan Mami tayi zamanta da hakan bai faru ba, Yanzun Dubai zasu tafi itada Mimi jibi, daga can Nigeria zasu wuce a fara biki. 

Daga dakin Hamida, kitchen ta wuce, gwara ta hada breakfast tunda ta rigada ta tashi, wayarta ta dauka ta turawa Noafal text, sannan ta Fara aiki, ta kusa gamawa Mimi ta shigo. Gaisawa sukai sannan ta zauna Tana fadin 

“Afeey, ta kusa barina ta tafi wani gidan daban, ta kusa zama cikin wani family sede ta kawo mana ziyara. Nasan duk inda kike zanyi alfahari dake, saboda na miki tarbiyar zama da kowa, Dan Allah Afeeyya kada Ki bani kunya, kada ki barar da tarbiyar da nayi miki, Ki zauna da mijinki lafiya kamar yadda kika tashi kika gani, Dan idan kikai wani abun bani bace wani abun kika gani. Ina miki fatan alkhairi tareda jaddadda miki hakuri, amma hakurin Bance ki kashe Kanki ba, idan Kinji bazaki iya ba,  am always available, I’ll give you my shoulders whenever you need them. Rayuwata ban taba tunanin Haka zata kasance ba, yarinyar da aka dasa cikinta, aka saceta, ta rayu a baren hannu, Tasha wahalar soyayya. Amma Allah a kiftawar idanu ya juya dukkan lamarin. Ki sani iyayena ban taba ganin me kishiya ba amma inada ita, kinga da gado ne bazaayi min ba, ba yana nufin kishiya gazawa bane A’a rabo ne. Ina miki fatan alkhairi! I’ll miss you ” 

Rungumeta Afeeyya tayi tareda sakin kuka, tabbas Miminta is a role model, sosae take son Noafal amma bata son barin gida kwatakwata ba. Haka suka jima a tsaye Rungume da juna itama Hikma ji take Badan karta kara karya mata zuciya ba da kukan zatayi. Hakanan Yaya ya shigo yana fadin 

“Is like I missed something ” 

Juyawa sukai a tare, Afeey tayi Murmushi ta basu guri shi kuma ya matso ya rungumeta tareda fadin 

“I love you!”



Wannan shi ne karshen labarin HIKMAH, ina fatan Allah Ya saka muku da alkhairi, I hope message dina ya isa inda nake son zuwanshi, nasan bazakuji dadin yadda nace HIKMAH Anyi mata kishiya ba? Yeah I always say my novels aren’t fictional or delusional, Aniyah! It’s based on real life, so kunsan kishiya is inevitable sede idan babu shi cikin kaddarar Mumini. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *