ABBAS
CHAPTER 19
Haka a gida ma da yawan mutane na farin ciki da wannan aure sai faman sanya albarka akeyi.
An shirya Teemah cikin wata doguwar riga mai kyan gaske kalar touqoise blue da ratsin golden, rigar ta kama ta sosai daga ‘kirji ‘kasan rigar kuwa abu’de yake ba ‘karamin fito da kyaunta rigar tayi ba.
Hannah kam yau ba ta jin gari, tunda aka ‘daura auren ta fara ‘kiran Teemah da suna _amaryar_ _Yayah_ , Teemah tun tana mitar bata so har ta ha’kura tayi shiru balle da taji kanta yafara sara mata ai tuni sai ta nemi ‘dakin da aka sau’kar da Mummy ta shiga da niyyan hutawa.
Mummy kam korota tayi tace maza taje cikin ‘yan uwanta ta zauna bata son zama shirun nan.
Fuskar shagwa6a tayi tace
” _Allah Mummy kaina ke ciwo ne shi yasa_ “
Mummy tace taje yanzu ta ‘dau maganinta tasha ba jiya an siya miki magunguna ba, hayaniya ne ke saki ciwon kan ba komai ba.
Fita tayi taje ‘dakin su nan ta samu Hannah da ‘kawayenta sai ihu sukeyi, haka ta zauna agefensu tayi shiru bata kula su amma duk yadda Hannah tasan zata takalo ta tasata magana sai tayi.
‘Karfe uku nayi duk suka wuce gidajensu da sunan zasu je kowa ta yo shirin walima su dawo.
Hannah ma kasuwa ta shiga aka bar Teemah ita ka’dai.
Taji da’din raguwar hayaniyan amma kuma sai ta ringa jin zazza6i na son taso mata.
Zama tayi a’dakin nasu ta’ki zuwa ko’ina kuma ta’ki shan maganin ma .
Kafin yamma kuwa zazza6in Teemah sabo fil ya dawo ga jiri dake faman ‘diban ta har bata iya tsayuwa da kanta sai ta kama abu, gaba ‘daya ta fita a hayyacinta.
Anty ne tazo neman ta dan afara shirin yi mata kwalliyar yamma ta zuwa walima, gagarumin walima ne da Daddy da kansa ya shirya shi.
Sosai Anty ma tayi ‘ko’kari dan kuwa duk wasu kaya da Fateemah tayi anfani dasu da ma wa’dan da zata sa agaba duk Anty ne ta ‘dau nauyin yinsu tare da ‘dauko wata shahararriyar mata wacce ta ‘kware a fannin kwalliya na zamani domin ta ringa yiwa Teemah make’up har biki ya ‘kare.
Ko yanzun ma da kanta ta shiga duba Teemah sai ta tarar da ita kwance ta du’kun’kunu a cikin blanket.
Da sauri ta ‘karaso tazo gareta tana tambayar ta “me ya faru?
Tayi saurin fahimtar abinda ke faruwa ne sanadin zafin da taji jikinta yayi ga kuma ha’duwan da ha’koranta keyi.
Fita tayi da sauri da niyyan ‘kiran Mummy sai kuma tariga ha’duwa da Ummah tun kafin ta kai ga Mummyn.
Ummah kam ganin hankalin Anty atashe yasa tayi saurin barin maganar da takeyi ta taho ta tareta da tambayar meke faruwa ne?
Bayani Anty tayi mata atakaice tun kafin tadasa aya kuwa Ummah ta furta ” _subhanallah_ ” sai tayi gaba, tare suka ‘dunguma zuwa ‘dakin su Teemahn da Anty da wasu mata guda biyu.
Story continues below

Ganin yanayin Teemah yasa Ummah fa’din ” Fateemah sannu ko, sannu Allah ya sauwa ‘ka!
Juyawa tayi ta kalli ‘dakin tace “wai ni har yanzu Hannah bata dawo bane?
Wata Antyn su da suka zo daga Gombe ce ta bata amsa da fa’din ” inaga de bata dawon bane ‘kila”
Ummah dialling no. tayi ta ‘kira shiru tsawon seconds bakwai sannan ta furta
“Ameen wa alaikassalam”
“Jama’ah Alhamdulillah”
“Fateemah ba ta jin da’di ne nace ko zaka aiko doctor adubata “
“Ok, toh shikenan”
tafa’da tare da yanke wayar.
Iya abinda kowa yaji kenan kuma babu wanda yasan da waye tayi magana.
Sai da ta cire wayar a kunnanta kafin tayi musu bayanin cewa ” Abbas zaizo yanzu ‘kila ya taho da likita ko kuma ya kaita asibiti ban san wanne zaiyi ba”
Fita tayi tace “bari tana zuwa yanzu kafin ya iso”
15mins be cika ba sai gashi ya bayyana a’dakin cikin wata arniyar shadda sky blue mai kyan gaske wanda ya dace da yanayin jikinsa.
Da sallamar sa ya shigo tare da gaida wa’danda yagani a’dakin.
Sake tambayar Anty yayi abinda ke damun Teemah Antyn sai tace dashi ” _inajin zazza6in ne ya dawo dan jikinta ya dau zafi gaskiya sosai_ “
Tayi maganar tare da kaiwa hannunta zuwa jikin Teemah.
Abbas kam tana gama bayani sai ya kallo inda yaga maganin ta jiya, aikuwa sai yagansa still agurin, zuwa yayi a hankali ya isa inda yake ajiyen ya duba sai ya ga tun wanda ya 6alla mata jiya ne bata ‘kara shan wani ba.
Sai yanzun yakai dubansa kan Fateemah da tun safiyar yau yake mararin ganinta amma be ganta ba sai yanzun.
Jikinta arufe ruf illah kanta ne yake iya kallo dan fuskarta yana ‘daya bangaren ne ta juya musu baya.
Tuni ‘daurin da aka mata ya zame ya koma gefe ya bar iya gashinta dake kwance gwanin sha’awah awaje yana ta she’ki.
Takawa yayi a hankali zuwa bakin gadon yasa hannu ya ta6o fuskar tata sai yaji zafi gau be ‘dauke hannun ba sai da ya shafi gashin kanta da ya ‘dau hankalinsa yanda babu wanda zai lura cewa dagan gan yayi.
Juyawa yayi ya fara tafiya yace da su akaita motansa zai same su acan, yace gara muje hospital adubata yafi”
Yana gama fa’din haka ya bar ‘dakin.
Wasu su biyu ne suka kama kafa ‘dunta zuwa inda ya fa’da ‘din Anty na binsu abaya.
Anan ya same su ri’ke da ita an lullu6a mata mayafi akanta wanda yarufe jikinta da kyau, hakan kuwa ba ‘karamin da’di yaji aransa ba, sai daya iso ya bu’de motan kafin ta shiga da taimakon Anty sannan shima yashiga tare da furta _bismillah_
don zatonsa ko da ‘dayansu za’a.
“Sai kun dawo, Allah ya tsare ya bada lafiya in gantacciya”
Anty ne tafa’di haka kafin ya amsa kuwa har sun juya masa baya.
Ganin sun juya kuwa yasashi sakin hamdala azuciyarsa dama shi ba son rakiyar yake ba dan sai ya cire babbar rigar dake jikinsa ya wulla ta baya dama duk ta takurasa ha’kuri kawai yakeyi da ita na yau ka’dai.
Jan motar yayi suka bar haraban gidan, sai da ya hau titi kafin ya juya ya kalleta sai yaga ta kwantar da kanta ajikin cinyoyinta ta takura guri guda ga dukkan alamu sanyi takeji sosai.
Be yi mata magana ba hannu yasa kawai ya kashe AC gaba ‘daya sannan yaci gaba da tu’kinsa.
Koda aka gwada ta ma ba komai ke damunta ba zazza6in ne kawai sai stress daya mata yawa amma bakomai, kuma ciwon na ‘kara ‘karfi ne sanadin rashin cin ishshen abinci da batayi.
Story continues below

Yau kam cewa yayi ayi mata allura dan bata son shan magani ma yace ko najiya ma ‘kin sha tayi.
Kuka tafara tare da ro’konsa akan dan Allah yayi ha’kuri bazata sake ‘kin shan magani ba.
Kau da kai yayi yace da nurse ‘din ta ha’da injections ‘din yace kuma bata son cin abinci ma doctor.
” _Yayah plz kace ta bari Allah zan rin’ka shan magani kullun_ “!
Yi yayi kamar beji ta ba sai ma yace da doctor ta hanzarta please.
” _Wallahi ni bana son alluran nan, kuma sai na gayawa Ummah da Anty da Daddy ma_ “.
Murmushi doctor tayi aranta take mamakin irin dramar wa’dannan Yayah da ‘kan wan suna matu’kar birgeta ita kam.
Dakansa ya ri’ke ta tana fiffisgewa amma sai da aka mata har biyu sannan ya saketa.
Zamewa tayi ta ‘dora kanta ajikin ‘kafafunsa taci gaba da kukanta daya ga haka sai yace ta koma kan sofa ‘din dake office ‘din ta kwanta, itama sai tayi kamar bata jishi ba, murmushi yayi ka’dan yasan haushinsa takeji yanzu dagangan sai yace da nurse ‘din ” _doctor inajin fah alluran be isheta_ _ba_ “
Tana jin haka ta mi’ke ta koma inda ya fa’din ta kwanta shiru tana sau’ke ajiyan zuciya, dayaga kamar zatayi bacci ne sai yace su tafi gara taje ta huta gaba ‘daya a gida.
*****
Can gida kuwa already shirye-shiryen walima ya kankama kowa nata faman shiri, lokacin da suka iso gidan ma ‘dakinsu yayi niyyan kaita amma jin hayaniyar Hannah da ‘kawayenta a ‘dakin dole sai ya maida ta 6angarensa dan so ya ke ta huta sosai zuwa lokacin kuwa bacci yariga yaci ‘karfinta gaba daya.
Suna isa tazame ta ta ‘dora jikinta akan gadonsa sai kuwa bacci ya ‘dauke ta ahakan sai sakin ajiyar zuciya take yi na kukan da tayi ‘dazu.
Abbas kam tsayuwa yayi akanta yana ‘kare mata kallo ba ‘karamin kyau ta masa ayadda take ‘din ba, ahankali yadawo da idanunsa saman la66anta da suka ‘karayin ja sosai.
Da sauri ya kawar da mugun tunanin da yazo ransa tare da fa’din ” a _uzubillah_ “
Gani yayi kamar kayan da ke jikinta sun mata nauyi dan haka sai ya ‘dauki wayarsa yakoma parlour, layin Hannah ya’kira amma bata ‘daga ba, daya sake ‘kira kuwa sai ta ‘daga amma bata jin sa tsaban hayaniyan daya yi yawa agurin da take.
Take yayi tsaki ka’dan tare da yanke ‘kiran.
Dama so yake ya sanar da ita ta kawo wa Fateema kaya marasa nauyi amma hakan be samu ba ganin bajinsa zatayi ba, sai kawai yafara tunanin wata mafitar daban.
Baifi 5mins a parlour ba sai ya tashi ya koma bedroom ‘din tare da ‘daukan stool yakoma gaban gadon ya zauna ya zuba mata idanu.
Ahankali yakai hannunsa zuwa bayanta ya zuge zip ‘din doguwar rigan da ke jikinta wanda yakamata ‘dam ya zauna sosai.
Ahankali ya zare rigar zuwa ‘kasa har ya cire ta gaba ‘daya.
Abbas kam suman zaune ne yaso kama shi dan be ta6a tsintan kansa acikin irin wannan yanayin ba, be ta6a kallon surar mace azahiri irin hakan ba, macen ma kuma Fateema, idanunsa be ta6a cin karo da abu makamancin hakan ba, ‘kirjin ta ya kura wa idanu dake sanye cikin jan bra mai kyan gaske, ajiyan zuciya ya sauke tare da kawar da idanunsa gefe itama Teemah adai -dai lokacin sai ta motsa ka’dan dan sosai taji alamun sauyi atattare da jikinta iska taji na hura ta amma saboda ‘karfin alluran dake yawo ajininta yasa bata wani yi motsin na kirki ba ta cigaba da baccinta.
Tashi yayi yaje cikin kayan sa ya ‘dauko rigar polo ba’ka na aikinsa ya dawo inda take, yanzun kam hawowa gadon yayi gaba ‘daya yafara ‘ko’karin saka mata rigar, a hankali, idan yaga kamar zata motsa sai ya dakata da abinda yakeyi sai ta kuma yin luf sannan yake cigaba da sawa kamar me dressing wa jinjirin da ba’a so ya tashi a bacci da haka har yagama mata, shi kansa mamakin kansa yakeyi yanda har ya iya tsayawa ya 6ata lokacinsa wurin sanya mata kaya duk kuwa da cewa hakan ba’kon lamari ne agurinsa amma a hakan sai da ya sa mata.
Shida kansa ya san Fateemah dabance a rayuwarsa, bata da me kama koka’dan azuciyarsa.
Story continues below

Yana gamawa kuwa aransa ya furta ” _tubarkallah-masha_ _Allah_ ” tare da shafa gashin kanta ahankali,
Dan yadda rigar ta matu’kar amsan jikinta ya kuma ‘kara fito mata da asalin kyaunta da haskenta kamar ace nata ne, baran ma da ya ha’du da ba’kin skinny trouser ‘din dake jikinta ai ba magana, sosai Abbas yaga ‘karin hasken ta ya zarce na baya.
Abbas kam shashancewa da kallon ta yayi ya mori wanda suka wuce shi ma abaya, shi kansa yasan Fateemah mace ce, mace ce da kowa ni ‘da namiji zaiyi sha’awar kasance wa da ita.
Ya godewa Allah aransa yafi sau a ‘kirga saboda kawai mallaka masa ita da yayi amatsayin mata.
Abbas ‘dinku kam kasa jurewa yayi lokacin da idanunsa suka sau’ka akan bakinta, sai ji yayi kamar an fizgeshi ya ran’kwafo da kansa zuwa dai-dai fuskarta, bakinsa ya ha’da da nata ya bata light kiss asaman la66an ta.
Yana cire bakinsa kuwa yaga ta turo bakinta gaba tare da juyi zuwa ‘dayan 6angaren.
Sai da ya lullu6eta kafin ya tashi yana murmushi ya koma kan stool ‘dinsa ya zauna.
Tsawon mintina talatin yana zaune wurin agabanta kamar mai gadin ta, sannan ya koma parlour anan ya tarar da tarin missed calls awayarsa har da na Daddy, Ummah da sauran abokansa.
Abokansa kam dama yasan dole zasu neme shi dan be yi sallama da su ba ya taho abinsa, amma be bi ta kansu ba, sai yabi bayan ‘kiran Daddy, shima na Daddyn be shiga ba wanda hakan yasa ya gane cewa tafiyar su zuwa Lagos tayi nisa kenan.
Sai da ya ‘kira Ummah yace da ita yana bu’katar ruwan tea ta amsa masa da toh sannan ta tambaye shi jikin Fateemah yace da sau’ki yasanar da ita cewa sun dawo ma already suna gida.
Godiya wa Allah Ummah tayi tare da fa’din tana zuwa anjima toh tadibo ta.
A silent ya saka wayar bayan sun gama magana da Ummah tare da ajiyeta agefensa, sam be yi niyyan zuwa ko’ina ba dan haka yayi zamansa a parlourn yana gadin farkawar ta.
Daga shi Abbas har ita babu wanda ya halacci taron walimar, inda kuwa babu laifi walima ta ‘kayatar fiye da zaton mai karatu, gurin ma ka’dai abin kallo ne dan idan kaga yanda aka tsara gurin dole sai ya birgeka komai fari akayi decoration ‘din wajen gwanin birgewa, ga wasu shahararrun malaman musulunci da aka gayyato maza da mata inda suka ja hankalin mutane akan ha’kuri da zaman takewar aure, ga ‘dumbin jama’ar al’ummar musulmai da suka halatta suma ba ‘a cewa komai, Ga Hannah ma da tawagar ta agefe guda suma ba laifi yawa ne da su, zakayi mamaki idan ka kalli ayarin ‘yan CAPTAIN ABBAS FANS 1&2 suma agurin suna ta rawar kai abin su afa’dar su wai bikin nasu ne,’dai-‘dai kun cikin su ne ke zaune aguri ‘daya, wasu ko fuskar nan babu walwala, musamman ma masoyan CAPATIN na ha’ki’ka da suke jin cewa za’a musu kishiya, su kam har banson ganin fuskar su dan ko ka’dan babu walwala, sunzo ne da niyyar ganin kalar amaryar Abbas ‘din amma basu samu dama ba dan Cpt. abbas ya 6oye amaryarsa ya hana su ganinta, basu sami ganinta ba kuwa har taro ya watse gaba ‘daya.
Ummah da kanta ta kawo masa Tea ‘din inda tasame shi zaune a parlour, taso ganin Teemah amma Abbas yace bacci takeyi dan haka sai kawai ta tambayi yanayin jikin ya sanar da ita cewa ba laifi jikin da sauki, tace “toh Allah ya sauwa’ka” daga nan ta tafi da zummar sake dawowa ta dubata idan ta tashi.
Mummy naso taga ‘yarta taga halin datake ciki dan rabon su da ganin juna tun da rana data hanata 6uya a’daki, zazzabin nata ma labarin sa tazo taji bayan sun wuce asibiti ta kira layin Teemahn kuma ba’a ‘daga ba, tana so taganta amma nauyin ganinta tare da Abbas ‘din sai ya rinjayi ‘kudurinta dole ta sanyawa ranta ha’kuri zuwa gobe idan Allah ya kaimu.
Bayan sallar maghrib Hannah tazo da sallamar ta ta gaida shi tare da fa’din ” ‘dazu ka kirani Yayah?
Yana kishingi’de cikin kujera be ko kalleta ba yace
Story continues below

” meyasa toh sai yanzu zaki zo?
“Ayyah Yayah muna wajen walima ne fah alokacin shiyasa”
Sarai yasan ‘karyane dan haka sai ya jijjiga kansa ya kauda kan daga barin kallon ta yace ki ‘dauko wa yarinyar nan kayan baccinta inajin zata bu’kace su”
Taso ta tambaye shi wacce yarinyar amma tsoron yanayin dayake ciki ya sanya ta ta ja bakinta kawai tayi shiru ta fita.
*****
Teemah kam bata tashi ba sai ‘karfe tara kusan da quarter ma sannan ta farka, ahankali ta bu’de idanunta sai kuwa taga duhu, bata tashi ba sai ta fara lalu6en Hannah a gadon hannu da ‘kafa amma bata jita ba, ” Hannah!
” Hannah!!
ta kira sunan ta har sau biyu, jin shiru yasata ta janye bargon dake jikinta ta sau’ko daga gadon tamkar zatayi kuka, tana shirin barin ‘dakin sai taga haske ya gauraye ilahirin ‘dakin gaba ‘daya.
Juyawa tayi sai caraf suka ha’da idanu dashi, zaro ido tayi waje tare da rufe bakinta da hannayenta duka biyu wanda sai alokacin kuma ta fahimci a inda take.
Be kulata ba sai ya kawar da kansa gefe duk kuwa da cewa yaji da’din yanda yaga ta tashi garau da ita, amma be nuna hakan afili ba, sai ya wuce ta ya nufi bayi ya dan watso ruwa sai alokacin ne yaji nutsuwar yin wankan ya shige shi, tun ‘dazu yake so yayi amma ya kasa sallah ka’dai ke sashi barin inda take yana idarwa kuwa baya 6ata lokaci ako’ina yake dawowa yaci gaba da gadinta, dama burinsa be wuce ya ganta ta warware ba.
Yana shiga bathroom ‘din kuwa sai itama ta wuce parlour da hanzarin ta da niyyar barin ‘dakin, amma sai ta tarar da ‘kofan arufe da lock, mamakinta kuwa be wuce na yanda akayi tazo nan ‘din ba ga kuma wata riga ajikin ta dabata san daga ina ta sameta ba.
Kan stool ‘din dake wajen dressing mirror ta koma.ta zauna tana jiran fitowarsa domin ya bu’de mata ‘kofa ta tafi.
Abbas ma yaso ya 6ata lokaci a gurin wankan amma daya tuna cewa bataci komai ba sai kawai ya hanzarta ya fito in less than 15mins.
Shima yana fitowa direct gaban dressing mirror ya nufa dan ganin yanayin jikinsa yi yayi tamkar be ganta ba sai ma murmushin mugunta daya sake yi tare da kwar da kansa.
Dama yasan zata nemi hanyar fita shiyasa ya sakawa ‘kofan lock kafin ya baro parlourn tun da wuri.
Towel ‘dinsa ‘daure a ‘kugun sa ya fito, da farko Teemah rintse idanu tayi data ga ya nufo inda take ahaka, amma daga baya data gaji da rufe idanun sai ta bu’de su ahankali ta sau’ke su akansa.
Abbas duk yana lura da ita amma be tanka ta ba.
Ita kuwa akan cikinsa ta sau’ke idanun ta, ta kuwa ‘kurawa jikin nasa idanu ta na kallo har zuwa ‘kirjin sa.
Tasaba ganin Yaya Mahmud ahaka amma yau da taga Abbas sai ta ga tsarin halittarsa ba iri daya ‘daya data Mahmud ba, sosai yanayin jikinsa ya birgeta yanda jikin ya wani mummur’de ga wasu parks da ya ajiye sai take jin sha’awar ta6awa, amma bazata iya ba dan tasan halinsa idan ta ta6a shi 6a66allata zai yi wannan Yayan kam, kan ta ‘daga zuwa fusakarsa, suna hada idanu sai ya ‘dage mata gira tare da fa’din ” _ya dai_?
Kau da kai tayi gefe da sauri tace ” _ni ina so in tafi ne”_
” _Zuwa ina kenan_ ?
Ya tambaya batare da ya kalle ta ba.
Amsa ta bashi da fa’din
” _D’akin mu, gurin Hannah…_ “
Taranta yayi da fa’din ” _can ‘din yafi nan ne_ ?
Bata bashi amsa ba sai kawai ta tura baki gaba tayi fuskar kuka.
Ko kallan inda take Abbas bai sake yi ba yaci gaba da sha’anin gabansa.
Story continues below

Teemah kan kukan shagwa6a tafara yimasa ka’dan-ka’dan, Abbas still ‘kin kulata yayi sai daya ga kukan na shirin yin yawa ne sannan ya waigo azafafe ya dubeta yace ” _for god sake ni na hana ki tafiya ne? Kije abinki mana ko na ‘daure ki ne.._ ?
Da turarren baki cikin shagwa6a ta furta ” ‘ _kofan fa arufe da lock ai na duba ‘dazu_ “
Goshi ya dafe kamar ehh dagaske ya manta ne sai yace ” _muje in bu’de miki_ “
Gaba yayi aransa ya furta ” _zanyi maganinki ai_ ”
Itama sai ta bishi abaya har zuwa parlourn, yana budewa kuwa ko magana bata sake yi ba ta fice abinta.
Tura ‘kofan kawai yayi da gangan ya barta abu’de dan ya san zata dawo.
Ai kuwa ko bedroom ‘din be gama shiga ba yaji ta dawo da saurin ta har tana shirin wuce shi.
Murmushin gefen baki yayi yana tafiya yace ” _ya kin dawo kuma_ ?
Tana ha’ki ta bashi amsa da fa’din ” _Ni…ni tsoro nakeji, Yayah gidan fah shiru kamar ba kowa ga shi_ _hasken…ma ya ragu sosai bazan iya tafiya a…haka ba_ ”
Cigaba da tafiyar sa yayi, itama take tabi bayansa tana fa’din ” _please Yayah toh ka rakani mana!!_
Bai waigo ba yace da ita.
” _Saboda me kenan_ ?
” _Ayyah plz Yayah, wanka…. nake so naje nayi kuma inajin….tsoro_ “
Ta sake ro’konsa cikin jan magana sanadin ha’kin da ke damunta har yanzu.
Sai cewa yayi da ita” _toh ni ina ruwana da wankan ki_ “
Abayan sa ta tsaya lokacin yana cuming kansa, sai tayi fuskar tausayi tare da ran ‘kwafar da kai gefe gashi dama ‘dan gudun datayi yafara sata jin jiri daya ke ya ha’du da yunwa ga rashin ‘karfin jiki ga maganan da takeyi yanzun sai yasa zuciyarta ya riga harbawa faster than d normal duk gaba ‘daya sai suka ha’du suka canja reaction ‘din ta atake sai ta fara ganin dishi-dishi, tuni hawaye ya gangaro mata asaman kuncin ta.
Abbas sam be lura da yanayin da ta shiga ba dan ya riga ya juya mata baya, har ya isa wurin mirror ya ‘dauko man dayake shafawa a’kafar sa ya zauna akan stool tare da fa’din ” _zo nan inkina son in rakaki zo kimin wani aiki_ “
Duk da yanayin da ta shiga amma
tana jin ya fa’di haka ta taho a hankali zuwa inda yaken kamar yanda ya bu’kata.
Shi kuwa ‘kafar sa ‘daya ya ‘dago mata sannan ya mi’ka mata mai ‘din tare da furta ” _take this_ “!
Teemah bata yi wani musu ba kanta a ‘kasa tasa hannu ta kar6a dan ta riga ta fahimci manufarsa dan haka sai ta tsugunna tafara shafawa a hankali.
Aranta take fa’din dole zatayi masa a yanzun kodan ya rakata ma, dan bata da wani bu’katan da ya wuce ta fita daga ‘dakin nasa abubuwa dayawa take so taje tayi .
Abbas kam yanda take shafawan slowly ba ‘karamin birgeshi yayi ba, hakan kuwa yasa shi ‘kura mata idanu yana kallon fuskarta, anan ya hango hawayen datake fitarwa, take kuwa ya janye ‘kafar sa da sauri.
Faruwar hakan kuwa ke da wuya sai ta ‘daga kanta ta kalleshi, ha’da ido sukayi dashi kafin ta ‘dauke nata idanun sai ya jefa mata tambayar ” _me ya faru kuma ? Ba nace zan raka ki ba_ ?.
Bata bashi amsa ba sai ta kauda kanta gefe tare da yun’kurin mi’kewa tsaye.
Jiri ne ya ‘debeta tana ‘ko’karin fa’duwa sai yayi saurin tarota ta dawo jikinsa.
Kan gado ya maida ita ya kwantar inda hawayen ta yaci gaba da gangara ta gefen idanuwan ta.
Abbas be yi mamakin hakan ba dan yasan jirin nata harda yunwa ma musamman daya san cewa da kansa yasa an mata alluarar cin abinci.
Story continues below

Dan haka da hanzari yafara ‘ko’karin rabata da kayan dake jikinta da nufin idan ta watsa ruwa sai ya bata abinci zatafi jin ta normal sosai.
Amma sai Teemah ta ri’ke masa hannu tana hanashi aiwatar da abinda yayi niyya tana mai ‘kara sautin kukan ta.
Hannun yabi da kallo ba tare da ya kulata ba sai ya cire hannunsa daga cikin nata ahankali tare da kamo hannayen nata duka biyu ya ri’ke cikin hannunsa guda ‘daya, yasan idan yabiyeta zata ta 6ata masa lokaci ne abanza shiyasa gara yayi mata hakan.
Skinny ‘din dake jikinta ya janye shi gaba ‘daya zuwa ‘kasa tana mutsu-mutsu amma be ‘kyale ta ba sai daya ga ya raba sa da jikinta sannan ya sake mata hannuwan ta.
Take kuwa tafara ‘ko’karin kare jikin ta dasu wanda hakan sai ya bashi dama ya cire rigar ma cikin sau’ki.
Tana ganin haka kuwa ta juya ta kifu da cikinta a ‘ko’karinta na ganin takare jikinta tana gunjin wani wahalallan kuka.
Abbas ko ‘kala be ce da ita ba sai da yaga ta kifun sai ya ‘kara samun daman kai wa hannu yayi unhooking bra ‘din dake jikinta sannan ya mi’ke tsaye.
Wani ‘dan ‘karamin sabon towel ya ‘dauko mata ya lallu6a mata daga bayanta.
Tana jin haka kuwa ta kai hannu takama shi tare da ‘ko’karin cusa shi a’kar’kashin ta sai da taga tarufe jikinta sannan ta tashi ta zauna tana ‘ku’k’kuni.
Abbas kam ko kula ‘kala be ce da ita ba sai ma ya wuce bathroom ya ha’da mata ruwan wanka da kansa, wanda itama Teemah sai alokacin ta zare bra ‘din ganin baya ‘dakin sai tayi saurin cusa shi a ‘kar’kashin pillow ta 6oyeshi.
Tana ganin ya fito kuwa sai tayi saurin mi’kewa tsaye tana rarraba idanu tamkar mara gaskiya, wani sabon jiri taji na ‘diban ta sanadin tashi da tayi a fizge sai ta kai hannu ta dafe goshin ta dashi tare da komawa ta zauna abakin gadon.
Abbas ma da sauri ya ‘karaso gabanta ya sa hannu da niyyan ‘daukan ta amma sai tafara yi masa rigima, hakan kuwa yasa ya barta yace toh maza taje tayi wanka tafito yanzun nan.
Teemah kamar gaske ta tashi tafara tafiya dan ji take data bar shi ya ‘daga ta gara taje da kanta koma a yaya ne, taku biyar mai kyau batayi ba sai taji idanuwanta sunyi luuu, take taga duhu ya cika mata idanun.
‘Kasa tayi da sauri ta zauna dirshan akan tiles tana maida numfashin wahala har yun’kurin amai tafara ji sai kuwa ta saki kuka tare da ‘kiran sunan Mummy..
Da hanzari Abbas ya taho gareta shikan sa a’kage yake yaga tasa wani abu acikinta dan haka haka be yi wata-wata ba kawai ya cicci6e ta, take kuwa tafara yi mai rigiman bataso ya kaita gurin Antyn ta amma shi ko bi ta kanta ma bai yi ba, be direta ako ina ba sai cikin bathroom.
Yana shirin sata a bathtub tayi saurin ‘kan’kame shi da ‘karfi sai ya kalleta ganin ta’kiyin magana yasa dole sai da ya sau’ke ta batare da ya saka ta acikin ba.
Sai daya ajiyeta kafin ya tambayeta ” _me ya faru_ ?
” _Ni…da kaina zanyi_ “
Ta bashi amsa da fa’din haka cikin wata shagwa6a66iyar muryarta.
Da ‘dan tsawa yace ” _ba fah nason taurin kai ni, Allah sassa6a miki zanyi idan kika dameni_ !
Tana so ta bubbuga ‘kafafu amma motsin kirki ma yanzu tsoron yinsa take yi saboda tsoron jiri ko ha’ki dan ha ka sai ta juya masa baya tana ‘ku’k’kuni.
‘Kwafa Abbas yayi yana kallon ta tsawon da’ki’ku, kawai sai ya juya ya fita daga bayin bata sani ba sai ji tayi ya rufo mata ‘kofan da ‘karfi.
Sanadin haka kuwa yasa ta juyowa sai taga baya nan, gurin ‘kofan ta isa tasaka lock sannan tazo tayi wankan ta anatse, sosai kuwa taji da’din ruwan daya ha’da mata data gama wankan nata sai ta sake ha’da wani me ‘dumin tayi tsarkin ta dashi mai kyau sannan tayi niyyan fitowa tare da ‘daura towel ‘dinta.
Story continues below

Rarraba idanu ta hau yi a bayin ko zata samu abinda zata rufa wa jikinta amma bata ga komai ba, tsaki taja ka’dan sannan ta ‘dan le’ko da kanta tare da fa’din “Yayah!
Yana bedroom ‘din lokacin data ‘kira shin yana ‘ko’karin saka pyjamas.
Hankali kwance kuwa ya amsa ta da fa’din ” _uhmm_ ” haka kawai yace da ita
Sai ta kuma fa’din _Yayah na gama wankan_ “
Yace ” _toh me kike jira da ba zaki fito ba?_
Cewa tayi
” _Ayyah Yayah towel ne fah kawai ajikina dashi zan fito ahaka_ ?
Tsayawa yayi da abinda yakeyi yace ” _da ‘din aya ya kika shiga bathroom ‘din_ ?
Rage murya tayi ‘kasa-‘kasa tace ” _ni gaskiya kunya nakeji_ !”
Sai ji tayi yace ” _kunyar wa kenan_ ?
Shiru tayi ta’kiyin magana sai hararo hanyar ‘dakin da tayi tana tura baki.
Abbas kam jin tayi shiru yasa shi fa’din ” _Look, Allah 30seconds kika ‘kara abayin nan ni da ke ne yau agidan nan zakiga abinda zan miki, ba ‘dazu an miki allura biyu ba, toh yanzu hu’du zan sa a miki try me kiga abin_ _mamaki_ “!
Zaro idanu tayi waje tare da rufe bakinta kamar wacce tayi ‘karya jin abinda ya ce ‘din.
Sarai ta tuna muguntar da yayi mata ‘dazu har yanzu ma zafin allurar be daina ba ballan tana har guda kam ai mutuwa zata yi.
Tunowa tayi da 30 seconds ‘din da ya ce mata, wuf ta bu’de bathrum ‘din ta fito tana wani sunkuyar da kai ‘kasa.
Abbas ma yi yayi tamkar be ganta ba kawai ya wuce parlour yabarta a’dakin.
Kayan ta ta gani na bacci riga da wando da kuma packet ‘din pad akan gado sai dai babu pant ita kuma ta wanke na jikinta.
Bata tsaya mamaki ba kawai ta ‘diba kayan ta koma bayi ta saka su ajikinta, dama yau bata da bu’katan pad sai de ko gobe dan period ‘din ta yana bata hutun kwana da wuni ‘daya akowani wata, so ko yanzun ma rashin pant ‘din be dame ta sosai ba tun da kam tasamu kaya.
Kayan kuwa light pink ne mai laushi , gaban rigar kuma bottles dark pink ne ajere da wani ‘dan ‘karamin flower daga gefen ‘kirjin rigar, wandon kuwa yana da ‘dan fa’di ka’dan, kayan basu da nawi, dama tana son kayan sosai musamman ma saboda laushinsu.
Harta fito sai kuma taga rigar na fidda mata shape ‘din ‘kirjin ta sosai, haka ta saba sawa amma yanzun sai taga bazata iya fita gurinsa ahaka ba tunda ko mayafi bata da shi.
Bra ‘din ta ta ‘dauko ta sake komawa bayin ta saka.
Rashin kaurin kayan ma yaso ya hana ta sakewa, amma bata wani 6ata lokaci ba dan cikin ta har ‘kugi yake yi mata saboda yunwa, tunanin ta ma inda zata samo abincin dazata ci a wannan daren.
Yanke shawara tayi akan zata ro’ki Yayah ya rakata kitchen tasamu abinda zataci in yaso ko daga nan ma ya barta zata iya komawa ‘dakinsu ita ka’dai.
Tana fitowa kuwa sai ta ganshi tsaye ransa duk a6ace, a hankali ta ‘karasa ta ‘karasa bakin gado zata zauna, kafin ma ta zauna sai taji ya kama hannun ta kafin ta yun’kura kuwa taji yaja hannun dole tabi bayansa.
A parlour kan dinning ‘dinsa na marowatan nan in jita ya ajiyeta, ganin warmers da plates harma da spoons akan table ‘din sai ta ‘daga kanta ta ta dube shi , ” Oyah eat” yayi maganan tare da nuna mata warmers.
Abinci ne kala biyu tagani harda pepper soup ‘din kayan ciki, ita kuwa duk basu mata ba sai ta bu’de ledan data gani a ajiye shima, fruits ne a ledan tana ganin haka kuwa ta kauda warmers ‘din ta janyo fruits ‘din ta tafara sha, dama bata jin da’din bakin ta sosai hakan yasa abu me mai ‘ ko sam bata sha’awar sa.
Fruits ‘din taringa ci tana za6an masu ‘dan tsami tana sha, haka duk ta bi ta lalata kusan rabinsu dan in dai ta ta6a taji ba tsami toh ajiyewa take yi ta ‘dauki wani.
Tana cikin hakan sai ta ganshi tsaye akantsa hannun sa ri’ke da tea cup.
Sosai ta tsorata dan ta zaci ze yi mata masifan 6arnar da tayi ne amma ga mamakin ta sai ta ga ya mi’ka mata ‘daya hannunsa, kar6a tayi sai taga magunguna ya 6allo mata kafin tayi wani yun’kuri sai ya mi’ka mata tea cup ‘din.
‘Kamshin da tea ‘din keyi ne yasa ta sha’awar shan sa, aikuwa taringa sha a hankali tare da maganin da ‘da’d’aya har ta shanye su.
Abbas kam beyi mamaki ba dan yasan halin ta dama da jarabar son fruits shiyasa ma ya sa aka kawo, yazaci ma zata ‘danyi sha’awar peper soup ‘din amma sai yaga bata ko kula shi ba.
Yana ganin ta gama da maganin ya juya ya abinsa koma bedroom.
Data ga ya juya ne sai tayi saurin dakatar dashi da fa’din ” _Yayah toh tsaya ka rakani mana, na gama fah_ !
Ko kulata Abbas beyi ba yayi shigewar sa ciki.
Teemah kam bata tashi ba sai da ta gama da shayin ta dire cup ‘din, tayi zaman jiran sa na mintina, 5, 10 zuwa 16 mins zaton ta ko zai fito ne, ganin shiru har yanzu sai kawai ta mi’ke itama.
‘Kofan taje ta duba sai taga ya kuma sake saka lock, inda taga ya ‘dau key ‘dazu nan taje ta duba amma bata ga komai ba dan haka itama sai ta koma bedroom ‘din ta same shi.
Ganin sa tayi kwance yayi ‘da’d’daya agado, haushi yasa ta isa gabansa da sauri kamar wacce zata ‘dau wani mataki amma tana isa kansa sai taja ta tsaya tace ” _Yayah_ !
_Yayah dan Allah ka tashi ka rakani mana, su Ummah fah zasu_ ta _nema na, haka ma Hannah”!_
Shiru yayi tamkar beji ta ba sai tafara bubbuga ‘kafafu a’kasa.
Tashi yayi ya zauna, da taga haka sai ta sake fa’din ” _Nifah Yayah bacci nakeji kuma ka’ki ka rakani ni atsaye zan kwana_ _ne toh_ ?
” _in zaki iya kwana atsayen bismillah ai ban hanaki ba_ “
Hawaye tafara tana ‘ku’k’kuni ‘kasa-‘kasa.
” _banji ba_ ” yace da ita yana kallon ta.
Kauda kai tayi gefe tace ” _Allah Ummah fah da su Anty zasuyi ta nemana_ “
‘Dan ‘karamin tsaki yaja dan harga Allah rigimartan yafara isan shi sai ya fara
‘Ko’karin sake kwanciya tare da fa’din
” _Idan bazaki kwanta ba ki kama hanya kiyi tafiyar ki dan ni babu inda zani_ “
Yana gama fa’din haka ya koma yayi kwanciyar sa tare da juya mata baya.
Tsayuwan mintina sun kai ishirin tayi ahaka sannan a hankali ta shiga bayi, wani sabon brush data gani ba’a bu’de ba ta ‘dauka tayi amfani dashi sannan ta fito.
‘Dayan 6angaren gadon ta kwanta nesa dashi sosai tawani ‘dosa na jikin ta kamar ace fita ta zura da gudu.
Abbas kuwa be kula ta ba ko da yaga ta kwanta ‘din ma sai da ya bata tazarar kusan rabin hour kafin ya tashi bayan yaji ta sauke ajiyan zuciya .
Kakkashe dukkan hasken yayi sannan ya dawo gaban gadon, ganin har ta fara birgima yasa shi fa’din ” _fitinanniya kawai_ “
Space sosai yabada atsakanin su sannan ya kwanta.
Abbas kam ko daya kwanta ‘din ma bacci kasa ‘daukan sa yayi har kusan ‘karfe 12:00 na dare.
Tashi yai yayi alwala ya dinga jero nafilfili tare da addu’o’i sosai sannan ya kwanta.
‘Bangaren Teemah kuwa bacci ya mata da’di sosai har bata san lokacin da ta gangaro jikin captain ta shige jikinsa ba.
Har alokacin kuwa baccin be ‘dauke shi ba, ganin ta dawo jikinsa ne yasa shi sakin ajiyan zuciya, kanta akan hannun sa ta ‘dora, sai hakan ya bashi dama yake sha’kan dadda’dan ‘kamshin da jikin ta ke fitarwa da kuma gashinta, a haka bacci yayi awon gaba dasu gaba ‘daya.
Da asuba Abbas ne ya rigata farkawa ganin bata motsa ba sai ya sau’kar da kanta dake kan hannun sa ahankali ya mayar mata kan ‘karamin sweet design pillow dake kan gadon madadin hannun nasa sannan ya tashi.
Alwala yayi ya wuche masallaci domin gabatar da sallar asubah.
‘Karfe biyar da rabi ( 5:30am) Teemah ma ta farka.
A hankali ta bude idanun ta sai taga ita ‘daya ce a ‘dakin, tashi tayi da sauri ta nufi bayi ta ‘dan kintsa kanta a gaggauce sannan ta fito da sauri ko mayafi bata tsaya nema ba ta fice abinta.
Allah ya taimake ta kuwa daya fita abu’de ya bar ‘kofan hakan sai ya bata daman fita cikin sau’ki.
Har a lokacin gari be gama yin haske ba amma a hakan da duru-duru ta nufi ‘dakin su.
Hannah na kan sallaya bayan ta idar da sallan asubah sai taji an turo kofa an shigo, waigawa tayi sai taci karo da ita
kamar an koro ta ta shigo kanta ko ‘dan kwali ma babu.
Tashi Hannah tayi da sauri ta tareta tana murmushi tare da zaro idanu tace ” _Ah’ah amaryar Yayah ya haka da sassafen nan kuma kamar an koro ki_?
Teemah ko kula Hannah batayi ba ta wuce kan gado ta kwanta tare da jan blanket ta rufe jikin ta dashi, tana shirin juya wa Hannah baya sai Hannah ta dakatar da ita da fa’din ” _Haba Amarya har da nine a fa’dan amarcin_ ?
Sai yanzu Teemah ta bu’di baki tace
” _Hannah plz ni ki ‘kyale ni, Allah bansan damuwa ki barni nayi bacci na, ina kam jiya ‘kin_ _zuwa nema na kika yi dagangan kika barni na kwana acan bayan sarai kin san halin Yayah da masifa ba rakoni zaiyi ba_ “!
” _Yanzu dana barki kika kwana acan din me yasame ki? Baga shi kin ‘debo lada ba, ke dama zaku tafi tare da shi toh miye abin fushi dan kin kwana ‘daya awurin sa_ ?
Hannah tace tana kallon ta.
“Bazaki gane ba ne ai Hannah dan ba ke bace”
” _oh o o’oh barni da Bilalu na ni kam kuje can ku ‘karata keda wannan dodon mijin naki_ “!
Hannah tayi maganar tana kokarin tashi tsaye.
” _ai naje amma Yayah ya hana ni ganinki sai ma ya wani ce dani bacci kike yi irin ke ga me mijin nan…..nima ai barina kika_ _yi anan ‘din na kwana ni ka’dai bayan kinsan su Rauda ba kwana zasu yi anan ba_ _amma kika tafi, in hakane nima nayi fushin mana_ “
Story continues below

‘Kasa-‘kasa tace
” _Sai kije ai ki gaya masa wannan kuma, dan nima tsintar kaina kawai_ _nayi acan_ “
Juyawa Hannah tayi tana wa Teemahn murmushi irin na tura haushi tace ” _may be sace ki yayi babu wanda ya sani_ !”
” _Mtheww_ “
Teemah taja tsaki tare da gyara kwanciyar ta da kyau.
‘Karfe shida cif Abbas ya dawo sai ya tarar bata nan, amma be wani damu ba dan dama yasan matu’kar tasan cewa ‘kofa abu’de yake toh bazata zauna a dakin ba.
Kai ya jijjiga kawai lokacin da ya ga yanda ta tafi ta bar gadon batare da ko gyara shi tayi ba, yasan duk cikin saurin barin ‘dakin ne yasa ko tsayawa ta gyaran batayi ba.
” _Allah ya shirya_ ”
Yace a zuciyar sa, da kansa ya kintsa akin sannan ya koma parlour ya ‘dau ko wayar sa da tun jiya ya barta anan.
Ogansa ya ‘kira suka gaisa inda yayi masa murna tare da sanya masa albarka acikin auren da yayi.
Ya ‘kara da fa’din be samu ya halacci bikin ba lokacin yaje duba yaron sa ba lafiya ne shiyasa amma yayi ha’kuri. Godiya Abbas yayi masa dan ya tura masa sa’ko musamman yasa aka kawo mishi.
bayan haka ne suka yanke ‘kiran.
Daddy ya kuma ‘kira suka gaisa shima yayi musu ban gajiya tare da fatan alkhairi wa auren da suka je ‘daurawa.
Yana shirin ajiye wayar sai ga ‘kiran Saleem kamar yasan yana kusa waya a dai dai lokacin, domin tun jiya yake ‘kira amma Abbas ‘din be ‘dagawa.
Yanzun kuwa ‘dauka yayi ya kai kunnan sa tare da yin shiru dan yasan meze biyo baya, ai kuwa Saleem ‘din cewa yayi ” _Girman ka ne yalla6ai ,gaskiya najinjinawa zumuncin ka_ ”
Shi kansa Abbas yasan be kyauta ba amma sai ya basar yace dashi
” _Ya akayi ne Saleem ka 6uya fah?_
Ya fa’da a wani tsare.
” _Kai ka bari kawai maza sai a hankali wallahi, amma gaskiya ni banji da’din abinda kamin ba, ya za’a yi auran ka amma kawai sai de inji anyi ba wani labari_ !”
Shafo kansa yayi tare da fa’din
” _ohh sorry Saleem abin ne yazo unexpected in just 1 week Daddy ya yanke lokacin shiyasa, amma agafarce ni”_
Saleem cemasa yayi
” _Bakomai Cpt. yawuce girman kane ai, me ake shirya mana ne ina fatan za’a yi Sword_ _crossing kasan mu ta nan muka fi ‘karfi_ ”
Juya kai Abbas yayi yace ” _gaskiya bawani COS da za’a yi nima yaushe na nutsu Saleem, an shirya a Rivers amma inajin ba zai yiwu ba dan bazan samu zuwa ba. Amma may be ayi dinner yau in ya yiwu a nan Abuja inaga shi ka’dai ma ya isa nagaji da hayaniyan nan Allah gaba ‘daya Saleem_ “
” _Haba mana Captain……ko da yake bari sai na iso kawai nima da yaddar Allah yau_ _zan shigo_ “
Cewar Saleem.
Abbasa ma sai yace masa
” _okay, ba matsala, sai ka iso_ ”
Yana cire wayar a kunnen sa yaja tsaki aransa yace ” _bawani crossing na sword da za’a yi, haka kawai gardawa daku_ _ku saka yarinya atsakiya kuna faman ‘karewa halittar jikin ta kallo_ _a banza_ “
*****
Ba Teemah ta tashi daga baccin ba sai ‘karfe tara na safiya ta gota, tana tashi kuwa Anty kamar jira take tazo ta ha’da mata ruwan wanka na ha’din turare tace tayi dashi.
Zama tayi bayan shigan Teemah wurin wankan ta tallafi kanta da hannayen ta duk biyu tana tunani.
Anty na jin ‘kunci azuciyar ta fiye da zaton mutun musamman da tasan cewa yau Abbah zai yi aure abinda be ta6a ko kwatan ta zancen shi ba tun farkon rayuwar su har Allah ya kar6i ran Mahmud sai gashi Allah cikin ikon sa rana tsaka kamar wasa ana shirin ‘daura auren sa da wata daban.
Bazata ta6a fasa yi musu fatan alkhairi da zaman lafiya ba, dan koma menene yafaru laifin tane, she caused everything, dan haka ita a yanzu bata da wani buri illah taga ‘karshen rayuwar ta tayi kyau kawai fatan ta Allah ya fe mata kurakuran ta na baya.
Story continues below

Tana zaune tana tunani har Teemah ta fito daga wanka bata sani ba.
Teemah tayi mamaki sosai da taga ta ‘kira ta har sau biyu amma bata amsa ba hakan kuwa yasa ta matso dab da ita ta furta ” _Anty_ “!
Da ‘dan ‘karfi.
Firgigi tayi tare da sakin ajiyar zuciya kana tace
” _har kin gama wankan ne? Kinyi da kyau kuwa?_
Tayi maganar tare da ‘kwa’kulo murmushi ta sanyawa fuskar ta.
Cikin sanyin jiki Teemah ta amsa mata da fa’din “eh _h nayi mei kyau, Anty me yafaru ne naga kinyi shiru kina tunani?_
” _Hmm, bakomai Fatee na kawai ina tuna halin rayuwa ne yanda duniya ke juyawa damu, yau gashi Fateemah na ta sake zama matar wani karo na biyu”_
Anty ta tayi maganar tana mai sunkuyar da kanta kasa bata so Fateemah taga rauninta koka’dan musanman da yanzu ta tuna da marigayi gudan jininta Mahmud.
Teemah kam tsayawa kallon ta tayi kawai dan sam bata yarda hakan shine a zuciyan Anty ba, domin ‘karara damuwar ta ta nuna a fili kan fuskar ta.
Ganin da Anty tayi Teemah tayi shiru sai ta kamo hannun ta dawo da ita gaban mirror ta zaunar da ita kan stool tare da fa’din
” _Zo zauna in gyara miki gashin kin nan kafin mai kwalliyar ki tazo_ “
Teemah yanzun ma shiru tayi ba ta furta komai ba damuwar ta be wuci ganin sauyin yanayin Anty datayi ba, tana so tasan ainihin dalilin hakan amma tasan Anty idan ba tayi niyyah ba bazata ta6a sanar da ita ba, inda tayi niyya ne da tun ma kafin ta tambaya da da kanta zata sanar da ita.
Tsinkayar muryar Antyn ta tayi tana fa’din ” _Yarinta ta girma 4d second time, nauyin auren ya sake hawa kanki, amma kin san me nake so dake Mamana_ ?
Kai Teemah ta jijjiga mata ahankali alamar ” _ah ah_ “
Rage murya Anty tayi yanda bakowa ne zaiji su ba sai in kana kusa cikin natsuwa tace
” _Kinsan Yayanki Abbas shine mijinki ko?_
Ahankali Teemah ta bata amsa da fa’din ” _ehh nasani Anty_ ”
Anty cewa tayi
” _Yauwa uwata, ina fatan zuciyarki ta kar6i hakan baki ji cewa an takuraki_ _ko shiga hakkin ki ba ko_ ?
” _Ah ah banajin hakan koka’dan Anty_ “
Da sanyin muryarta ta bata amsa.
” _Alhamdulillah_ “
Anty ta fada harda lumshe idanu dan yanda taji da’di da kar6an auran da Fateemah tayi.
Afili kuwa Antyn cewa tayi.
” _naji dadi Fateemah, nayi farin ciki sosai, ni kaina na rigaki kar6an auren nan tun ma kafin a ha’da shi, da kaina Fateemah na hangi ‘kauna_ _da kishin ki tattare da Abbas kuma nasan da iznin Allah_ _rayuwar auren ku sai ta bada sha’awah watarana!, inaso koda kin koma gidan auren ki dan Allah Fateemah ki ri’ki_ _ibadar ki kinji, ki ro’ki Allah akan komai zai miki maganin koma menene, karki yadda ki kai kukan ki wurin kowa koda kuwa meze faru dake domin kuwa Allah kadai_ _ne mai taimakon da babu wanda ya isa ya miki makamancinsa_ _sai shi din nan dai Allah mabuwayi, Fateema rayuwa ta aya ce awurin_ _ki ai nasan kinsan duk abinda yafaru dani, ‘karshe wa gari ya_ _waya?_
_Niice da kaina nayi dana sani nayi Allah wadai da halina!Mijin ki mijinki ne Fateema kuma_ _sirrin kine, ‘yan uwan sa kema nakine dan ma kinga ai duk dangin_ _mijinki jininki ne dole ne ma ki so su koda babu aure a tsakanin ki da Abbas ballantana_ _kuma aure ya ‘kara ha’da ku, ki so su ki kauna ce su sosai, ki girmama ‘karfin_ _zumuncin dake tsakanin ku kar kiyi watsi da shi”._
” _Nasan auren ku auren ha’di ne na iyaye wanda za’a ce dukkan ku ba shiri yasame ku, amma dukkan ku kunyi_ _biyayya kuma na matukar jinjina muku, amma ki sani dole ne sai kinyi ha’kuri dan auren ha’di na tafe ne da wasu irin rikitattun abubuwa_ _wa’danda sai wanda ya ta6a faruwa dashi ne ka’dai zai gane su, ba zance bakwa son junanku_ _ba dan ban shiga zu’katan ku nagani ba amma nasan dole ne sai kin fuskanci wani ‘kalubale daga mijinki wanda ha’kuri ne ka’dai_ _zai iya magance miki su, Fateema kiyiwa mijinki biyayya, bansan taurin kai da rashin kunya banda_ _musu da jayayya dashi kinji? na tabbata idan kika ya’ki zuciyar ki kika kuma dogara ga_ _Allah komai zai zo miki da sau’ki amma sai kin daure sosai kinji?_
Story continues below

Ahankali ta ‘dagawa Anty kanta dan duk kalaman Antyn sun sa jikinta yayi sanyi matu’ka, duk abinda Anty ta fa’da gaskiya ne sai dai ita can ‘kasan zuciyarta take jin ta shiryawa zama da shi a kowani irin hali.
Anty cewa ta sakeyi ” _Yauwa uwata Allah ya miki albarka, yasa haske arayuwarku har illah masha Allah_ “
A saman la66a Teemah ta amsa da fa’din ” _Ameen_ “
” _Bansan me yasa nake jin da’din wannan auren naku ba har azuciya ta ba, inaji ajikina da iznin Allah auren ku akhairi ne,dan haka_ _ki bawa mijin ki kulawar data dace kinji_ ?
Kai ta ‘dagawa Antyn tana me sake sunkuyar da kanta.
Anty data fahimci taji kunya sai ta yi murmushi kafin tasake yin wata magana kuwa sai ga mai shirya Teemah ta iso da sallamar ta abakinta tare da wata mata abayan ta.
Amsawa sukayi dukkan su Anty sai ta mi’ke tare da gabatar musu da kayan da Teemah zatayi amfani dashi a yanzun sannan ta bar ‘dakin.
Abbas wanka yayi, ya shirya cikin wani shadda golden brown, ajikin babbar rigan kawai akayi aiki da coffee ‘din zare wanda ya ‘kara haska kayan sosai hakama a jikinsa sai annuri yake yi da sheki sosai kayan ya kar6i jikinsa, yana shirin fita kenan sai ga abokansa sun shigo, take kuwa suka fara yi masa tsiya akan tun jiya ya tafi ya ‘kyalesu ko dai amarya ce ta ri’ke shi.
Shiru yayi musu kawai har suka gama be kula su ba, dan shi be iya irin wasan nan ba be ma san me ze ce dasu ba.
Sai da sukayi suka gaji har sukayi shiru, daga baya suka fara hira normal sannan ne yasaka bakin sa aka ‘dan ta6a hirar da shi.
Anan aka kawo musu kayan break fast sukaci gaba ‘daya still suna masa tsiyan na gaba sai agidan amarya.
Wannan karan kam murmushi Abbas yayi dan indai akan girki ne bazata bashi kunya ba saboda yasan Mummy bata barta haka nan ba.
‘Daya daga cikin su ne mai suna Auwal ya tashi ya shiga ciki dan yana so yayi using bathroom, ai kuwa anan yaci karo da pant ‘din Teemah da ke shanye a bathroom ‘din,
har Allah-Allah yake kuwa ya fito dan ya baza kanu, aikuwa yana fitowa yaje gurin Abbas ya bashi hannu tare da fa’din ” _mazaah!!, ashe angon cewa kayi yau din shiyasa naga kana ta shan ‘kamshi!_ “
Kallon _me kake nufi_ yayi masa ha’de da harara yace ” _ban son iskanci Auwal toh haramun nayi? Me ma kaje yi min acikin ‘daki?_
Dariya duk sauran suka kwashe dashi suna nuna Abbas ‘din, sosai yaji haushin hakan duk dama abinda suke zato ‘din be faru ba amma ai wannan sirrin sa ne damuwar sa ma shine ya akayi har wannan tunanin yazo ran Auwal har haka, yariga yasan kayan ta data cire jiya ba’a fili yake ba sannan shi be ga wani abu a’dakin da zai sanya har mutun yayi masa wannan tunanin ba.
Basu wani da’de bama suka tafi, Abbas be bisu ba.
Suna tafiya kuwa yayi hanzarin shiga bedroom ‘din yafara investigating ‘dakin, still shi be ga komai ba dan hatta su bangles da earings ‘dinta da sauran su ma ba’a fili suke ba balle yace ko dan sune tunanin sa ya bashi cewa wani abu yafaru, sai dai ko in Auwal bincike yayi masa har yaga wani abin mace shiyasa yayi masa wancan tonon sililin…
Tunaninsa ya tsaya ne lokacin da ya bu’de ‘kofan bathrum idanunsa suka sau’ka cak akan jan pant ‘din ta dake shanye tun jiya abayin.
Wani ‘kululun ba’kin ciki, haushi da takaici hade da kishi ne ya tokare sa, sai yanzu ne ya fahimci asalin abinda Auwal ya gani da har tunanin can yazo masa.
Tsaki yaja tare da jan ‘kofan bayin ya koma parlour.
Waya ya ‘dauka ya ‘kira layinta ta kuwa ‘dauka dan lokacin already an gama yi mata kwalliya tana zaune da wayar a hannun ta.
Story continues below

” _Hello_ “
tace ahankali.
” _Me kike yi_ ?
Yace da ita a kausashe.
itama tace
” _Ba komai_ ”
” _maza ki zo yanzun nan karki 6ata min lokaci_ “
Be jira jin amsarta ba ya ending call din.
Teemah baki ta tura gaba ta kalli inda Hannah take tsaye tana rage kayan jikinta sai kuwa suka ha’da idanu, Hannah da bata gani tayi shiru sai tace
” _Ya daga amsa waya kuma kin fara fushi ince dai lafiya?_
Amsa ta bata da fa’din
” _Ba Yayah bane yace wai inje_ “!
Hannah sai cewa tayi
” _Dodo yayi kira kenan, sai ki tashi ki tafi ai kinsan angon naki sai ahankali inajin be gaji da ganin ki bane kika gudo”_
Kalan tausayi tayi tace
” _Dan Allah Hannah kije ko kuma ‘kira shi kice masa ‘kafata na ciwo….._
Tare ta Hannah tayi da fa’din
” _Ah ah sai de ince masa ‘kin zuwa kikayi…_
Sake marairaicewa Teemah tayi tace
” _Haba dan Allah Hannah_ “
” _ni baruwana kinga tsakanin ku ne, yanzu fah mijinki ne kun fi kusa, daina sani a shirgin ku please_ ”
Tana maganar ta nufi bathrum.
” _Hannah toh dan Allah tsaya ki raka ni mana_ ”
” _Daya ‘kira ‘din yace miki kije ke da Hannah ne, i thought amarya_ _ka’dai ya nema_ !
Tana gama fa’din haka tashige abinta tana dariyar mugun ta.
Teemah sharewa tayi kawai ta tashi ta wuce wurin Mummy dayake dama tun safe basu ha’du ba, Mummy da bata san me ake ciki ba sai ta zaunar da ita ta ringa yi mata nasiha kawai akan biyayyar aure.
Anan Hannah tazo ta same ta dan tana gama wankan ta taho ‘dakin da Mummy take anan take shiryawa tunda aka fara biki, sai kuwa taga Teemah tawani bararraje tana hira.
Hannah cewa tayi
” _har kinje ‘kiran Yayan kin dawo ne_ “
Da gangan ta tambaya dan tasan it’s hardly ace Teemah taje batare da tayi taurin kan nan nata ba.
Harara Teemah ta banka mata tare da ha’de ranta.
Muryar Mummy tajiyo tana fa din ” _na me kenan_ ?
‘Kasa Teemah tayi da kanta ta rasa me zatace dan tuni ta hango 6acin rai a fuska da muryar Mummy, gashi ita ba kowani lokaci ta iya shirya ‘karya ba ballan tana ta fidda kanta.
Mummy ne tasake fa’din
” _Teemah karki kuskura kice min Ya ‘kiraki ne baki je ba kika yo nan”_
“‘ _Karyan Hannah ne fah…Mummy naje ni… tun ‘dazu”!_
Tayi maganar kamar zatayi kuka.
Mummy juyawa tayi ta kalli Hannah ta ce ” _da gaske ne wai Hannah abinda ta fa’da_?
Hannah sai da ta kalle ta suka ha’da ido sai ta kawar da nata idanun tace
” _Bawani nan Mummy yanzun nan ne fa dazan shiga wanka ya ‘kiratan_ ”
Mummy dawo da kallon ta tayi wurin Teemah tace ” _na ‘kirashi na tambaye shi kin yarda_ ?
Da sauri ta jijjiga kanta alamar ” ah ah”ta ‘kara da fa’din ” _Allah Mummy Yayah allura yake sawa ayimin fah_ “
” _Bana son maganar banza Fateemah alluran saboda lafiyar waye akeyin ta?_
Shiru Teemah tayi ta sunkuyar da kanta ‘kasa tana ta juya hannayen ta cikin juna.
” _Ina tambayarki_ “!
Mummy ta daka mata tsawa.
Afirgice tace ” _saboda… nii….ne_ “
” _Toh 6ace min a’daki na tunda ke kullum kunnen ki bana jin magana bane kije kiyi tayi, kuma saura inji cewa baki jeba_ “
Tashi tayi sum-sum ta kama hanya tana bankawa Hannah uban harara kamar idanun ta zasu fito.
Hannah kam sai gwalo take yimata tana ‘karawa har suka daina ganin juna.
Aranta tace ” _kiyi ha’kuri ‘yar uwata ina sonki sosai kuma inason ganin kina farin ciki, amma nasan matu’kar kika ci gaba akan haka toh bazaku shirya da Yayah ba ni kuwa *BURINAH* inga kun gyara auran ku kun rayu kamar kowa”_.
Fitan Teemah kenan sai ta ha’du da Anty, take ta jefa mata tambayar ina zata kuma haka?
” _ba Yayah bane yace wai inje kuma fah Anty allura yake sawa ayi min_ “
Cikin shagwa6a tayi maganar tana turo baki.
Murmushi Anty tayi tace da ita
” _Habah kuma yarinyata da akeyi miki alluran bakiga kin fi samun sau’ki bane, maza kiyi_ _sauri kije kar ki 6ata masa lokaci_ “
Haka ta juya ta tafi tana ‘kun’kuni har ta isa.
Ciki-ciki tayi sallama haka kuma shima ya amsa mata ahankali.
‘Karasowa ciki tayi sai ta tarar dashi hakimce a kujera tamkar wani sarki, ba ‘karamin kyau yayi mata ba amma sai ta ta6e baki tare da kawar da kanta gefe.
Inda yake ta’karaso ta ce ” _ina kwana Yayah?_
Abbas kam wani yanayi na ‘kauna da shauki ne yayi nisan tafiya da shi hakan yasa be ma ji lokacin da ta gaishe shin ba, ita kuwa bata ‘kara ba sai ta ci gaba da tsayuwan ta.
Tunaninsa na dawowa sai ya kauda da kansa batare da ya sake kallon ta ba yace ” _kinyi breakfast ko_ ?
” _Uhmm_ ” tace dashi.
” _Me kika ci_ ?
” _Chips da…._
Kafin ta ‘karasa ma yatare ta da fa’din ” _D’auko maganin ki ki kawo ingani_ “
Wucewa tayi cikin bedroom ‘din nasa ta ‘dauko maganin saman drawer ta kawo masa.
Maganin ya 6alla ya bata ta kar6a tasha, har zata tafi ma ganin cewa dan maganin ne ya kirata kawai sai taji yace da ita ta wuce bathrum ta ‘dauke wannan abin nata da bari kuma karta kuskura ta sake amfani dashi, in kuwa ta ‘kijin magana shi da ita ne.
Zuwa tayi ta dudduba dan shaf ita ta manta da pant ‘din ta nan, tana gani kuwa ta hau gungunin ” _ina ruwansa da abuna toh, dama me yakai idonsa wurin da har ya gani._ ?
Haka tazo ta wuce shi tana tura baki.
Shima binta yayi da kallo harta fita, sai ya jijjiga kansa.
*****
‘Karfe 11:07am na ranar aka ‘daura auren Abbah da amaryar sa Halimatus Sadiya, ‘kanwa ga Hajiya Aisha matar abokin sa da tayi siyayyan kayan auren Mahmud.
Anty Sadiya ‘yar kimanin shekaru 31,kuma bazawara ce da mijin ta ya rasu ya barta da yaranta maza biyu, bayan rasuwar sa kuwa dangin sa sai suka kar6i yaran a hannun ta suka ri’ke agurin su.
Sam bata da matsala koka’dan, tana da hankali da nutsuwa, uwa uba ilimi ingantacce ya wadace ta boko da arabi, ga ta da son mutane da kuma yawan kyautata musu, wanda wannan dalilin ne yasa Abbah da kansa yayi sha’awan auren ta domin ya sa6unta rayuwar gidan shi da ya kafu shekaru da dama da suka shu’de.
Ahalin yanzu kuwa burin Abbah yariga yacika domin an ‘daura auren da Haleeman sa, bawai dan baya son Anty ba ah’ah sai dan kawai yana so shima rayuwar gidan shi ta canja.
*****
‘Kayataccen Dinner aka shirya wanda tsirarun mutane ne suka halatta saboda ba gaiya sosai akayi ba, shima ‘din Abbas be wani 6ata lokacin sa ya gaiyaci abokansa ba wa’dan da suke kusa dashi ne suka sani su ‘din ma yawanci friends ‘din sa na secondary school ne.
Daga wurin dinnern aka wuce da amarya zuwa sabon gidanta da ke…….
Daga wurin dinner sai aka wuce da Teemah zuwa sabon gidan ta dake Maitama.
Duk kushen mai kushe be isa ya kushe gidan Teemah ba, dolen sa sai ya bawa wannan gidan yabo ta musamman domin kuwa ko acikin ayari ba ze baka wahalar warewa ba, iya ha’duwa gidan ya ha’du matu’ka da duk wani abu da ‘dan Adam yasani na more rayuwa, Ba stairs bane gidan plat house ne dan’karere, sai dai ‘dakuna uku ne kacal agidan da kuma babban parlour ‘daya dake tsakiya, sai babban kitchen dake daga can hanyar wani corridor da zai fitar da mutun har bayan gidan inda wani ‘kayataccen lambu yake gwanin birgewa….
I can’t even describ ths house 4u clearly, but u urself should imagine it, koma yaya tunanin ku ya baku just take it as if daku aka shirya komai na gidan.
Abbas da kansa ya rakata har ‘dakin ta lokacin ‘karfe 7:30pm ne, ko tsayawa be ba ya barta ya fito ya shiga nashi ‘dakin dake nesa ka’dan da ita.
Itama binsa tayi da idanu har ya shige ciki.
Teemah kam Abbas na shigewa sai ta tura ‘kofar ta ta fara cire ‘kayatacciyar shigan da akayi mata na fitan dinner party ‘dazu.
Sosai irin wannan dressing ‘din auren suka isheta, dan kayan na takurata da nauyi, sai da ta cire gaba ‘daya kayan kafin ta nutsu kuma sai alokacin ne hankalin ta yadawo jikin ta, kawai sai ta saki baki tana ‘karewa ha’duwa, kyau da tsaruwan ‘dakin da Yayah Abbas ya ambace shi da suna nata ne.
Tashi tayi tana juyi tare da murmushi ” _wow_ ” tace tare da daka tsalle dan ganin dream bed design ‘din ta a’dakin kamar an shiga zuciyarta an gani, most especially colour ‘din bed ‘din fari ne tas sai akayi masa kwalliya da orange colour daya ‘kara haska shi, colourn paint ‘din entrance door dana bayi ma duk farare ne, hakama tiles ‘din dake ‘kasan ‘dakin shima fari tas, wani shegen ha’da’d’den labile aka sanya a’dakin orange colour mai matu’kar birgewa.
Sosai ‘dakin ya tafi da imanin ta haka tayi tsalle ta fa’da kan gadon tana murmushin farin ciki, ta zubawa farin ceiling fan ‘din dake saman ‘dakin idanu.
Mummy da Daddyn ta ne ka’dai suka san best colour ‘dinta akaf fa’din duniya sai ko Yayah Abbas dan ta ta6a fa’da masa da jimawa tun suna damaturu lokacin daya je hutun aikinsa acan, bayaga su ukun nan kuwa babu wanda yasan favourite colour ‘din ta har yau, hatta Hannah ma bata sani ba, amma acikin su ukun bata san waye ya yi mata wannan kyautar ba koma waye ita kam yasata farin ciki mara iyaka.
Shab tama manta da cewa ba kaya ajikin ta duk ta cire su, tana kwancen tana ci gaba da ‘karewa ‘dakin kallo kawai sai ta ji ‘karan sau’kan ruwan sama lokaci guda tamkar da bakin ‘kwarya.
Afirgice ta tashi ta zauna tana rarraba idanu sam bata san da akwai hadari har haka agarin m bama ita, sai sau’kan ruwan kawai taji.
Tashi tayi tafara duba abinda zata saka ajikin ta amma ta kasa samu sai masu nauyi ita kuma basu take so ba, da ‘kyar hannun ta ya jawo wata figigiyar riga ja mai sharara bata ma ko wuce mata gwiwa ba amma ahaka cikin hanzari ta saka shi ajikinta.
Story continues below

Tana gamawa saka wa sai ta fara duba wani ‘dan viel da zata rufe kanta dashi sai kawai taji ‘karan thunder mai ‘karfin gaske irin mai razanar wan nan ha’de da wal’kiya mai haske.
A 360 ta fito a’dakin tana toshe kunne ta nufi ‘dakin da taga ya shiga ‘dazu, duk taku ‘daya da takeyi tsoro ne yake sake kamata da haka har ta isa ‘dakin.
Tana zuwa kuwa dai-dai shima ya bu’de ‘kofan nasa sai sukaci karo dashi, jikin shi ta shige tana kakkarwan tsoro shima dayaga haka sai yasa hannun sa ya rungume ta ajikinsa sosai.
Tsawon mintina 8 tana faman sau’ke ajiyan zuciya sannan ya ‘dago ta ganin kamar ta ‘dan nutsu.
” _Me yafaru ne wai? Me yasa meki_ ?
Tambayar daya jefe mata kenan tare da jijjiga ta.
Cikin in in ta bashi amsa da fa’din ” _Yayah ni tsoro nake ji sosai_! “
” _Tsoron miye kuma? ke bazaki bar shirme ki girma ba ko_ ? _Ba gani nan agidan ba babu wani abin tsoro agidan nan da ze kamaki, ko kinga_ _wani abu ne_ ?
Kai ta jijjiga masa sai tace ” _thunder nake tsoro_ !
” _Toh ai baya kama mutun shi, oyah jeki ‘dakinki ki kwanta ki huta ko zaki ci abinci?_
” _Ah ah_ “
Tace dashi
sai yace ” _toh jeki ki huta kinga yau akwai sanyi kar ya shiga jikin ki!_ .
Teemah kam kuka ta sanya mishi tana bubbuga ‘kafafu a’kasa tace
” _ni wallahi tsoro nake ji ni ka’dai!_
” _Wai ya kike so in miki ne toh, umm_ ?
Ya fa’da yana kallon ta.
Shiru tayi bata ce komai ba, ganin haka yasa ya juya ya koma ciki dama dubota zeje yi dayaji ‘karan yasan sai ta tsorata sai kuma suka ha’du ashe be yi ‘karya ba.
Binshi itama tayi abaya tana tafiya tana waiwaye kamar irin wani abu na binta abaya ‘din nan.
Duk da tana cikin firgici amma hakan be hana ta ganin kyaun ‘dakin sa ba, compared to nata ma ai nata bakomai bane, hakama bed size ‘dinsa ba irin nata bane, ya zarce nata da girma, nashi komai fari tas aka sanya mishi, curtain ne ka’dai mint green da zanen fulawowi su kuma dark green ajiki.
Abbas yana zuwa ya wuce bathroom ya ‘dauro alwala, koda ya fito ma kallo ‘daya yayi mata ya kauda kansa ya wuce ga dadduma, sallah ya gabatar kusan raka’ah shida sannan ya ‘daga hannunsa ya dinga jero addu’o’i wa’dan da bata san iyakar su ba.
Teemah tun tana kallon sa har ta gaji ta lalla6a ahankali zuwa bakin gadon ta kwantar da kanta amma ‘kafafun ta na a’kasa ahaka bacci yayi awon gaba sa ita.
Abbas ne daya idar da sallahn yazo inda take ya tsaya akanta sai yanzu yaga tsantsan kyau da tayi cikin rigar dake jikinta, ahankali yakai hannu ya shafi gashin kanta har ya fara yawo da hannun nasa akan nata sai kuma wani abu ya ‘dar su aransa, da sauri ya cire hannun yana kallon hannunsa kamar wani sabon abu ne.
Tashi yayi ya tsaya akanta ya ‘kura mata idanu yana so ya kauda sa’kar haukan da zuciyarsa ke haska mishi amma ya kasa, ahankali ya gyara mata kwanciyan da kyau ya lullu6e ta sannan ya koma ‘dayan gefen ya kwanta shima.
Bacci kasa ‘daukan sa yayi ya zubawa fuskar ta ido yana ta sa’kar zuci, sam baya son hakan ya dinga zuwa ransa amma bazai iya ba, gashi yakasa kauda tunanin nan aransa.
Kishi ne ko shai’dan koma miye ke sarrafa zuciyarsa yakasa ganewa.
Ranar Abbas har makara yayi na zuwa masallaci, lokacin da ya tashin kuwa Teemah na jikinsa kamar de jiya haka yau ma tayi, sai ya ‘dan bata glance ka’dan dai-dai kuma itama ta bu’de idanun ta caraf sai sukayi 4eyes dashi, wanda motsin da yayi ne ya farkar da ita daga baccin da take yi.
Story continues below

Take ta diririce ta fara kalle-kalle ganin yanayin kusancin dake tsakanin su dashi yasa da sauri ta tashi zaune tana sussunkuyar da idanun ta ‘kasa dan ta fahimci itace, laifinta ne.
” _Mage ce ke ko_ ?
Taji ya ce da ita
Yayi maganar bayan ya tsareta da kallo.
Kai ta jijjiga masa tana ‘kif-‘kif da idanu, maganar tasa it’s clear that ita mai son jiki ce, haka yake nufi kuma ta fahimta amma sai ta’ki bawa kanta laifin ita ka’dai, asace take duba 6angaren daya kwanta itama ko zata ga space ‘din daya bari abaya ya matso amma sai bata ga komai ba.
Abbas be sake kulata ba dayake ma be fahimci me take yi ba gudun kar ya makara yasa ya mi’ke ya nufi bayi yana tunanin irin shegen son jikin datake da shi ga uban birgima kamar wata yarinya ‘karama.
Har ya shiga bayin ya gamo abinda zai yi ya fito tana nan zaune awurin kamar yanda ya barta ‘dazu.
I’kama ya tayar ya gabatar da Sallar sa cikin nutsuwa tare da yin addu’o’in azkar ‘din sa cikakke.
Al-qur’ani ya mi’ka hannu ya ‘dauko saman drwaer ya bu’de suratul A’araf ya fara karatun sa cikin sauti mai da’din sauraro tamkar bashi ne Abbas ba mai jin kai da rashin son maganan nan ba, qur’ani kenan, zancen Allah mai abin mamaki, duk wani girman kan ka ,miskilanci da ‘kafafan ka duk rashin iya hausan ka da ‘karfin da harshen ka keda shi akan yaren ka but when it’s comes to it (QUR’ANIL KAREEM) dole harshen mu ya dawo iri ‘daya.
Karatun nasa ba ‘karamin shigan ta yake yi ba, hakan yasa ta koma ta maida kanta akan pillow tana sauaraon sa tare da zuba masa idanu, wani ‘ka’k’karfan ala’ka take jin zuciyarta na ‘kulla mata game da Abbas ‘din sai take jin tamkar he is the only man in d entire universe take wani sabon babin ‘kaunar Yayan nata ya shige ta take jin shi ‘din na daban ne, kamar kar ya ‘kare karatun haka take ji.
Ko da ya ‘kare karatun kuwa sai ya sake bu’de wani page daga cikin ‘karshen Al’qur’anin yafara karanto addu’ar da ke rubuce a ciki wanda akeyi bayan an gama karanta Al’qur’ani mai girma ( Du’ah ‘u Khatmil Qur’an).
Yana shirin ajiye wa bayan ya kammala karatun sai suka ha’da idanu dashi kauda kanta tayi da sauri yayin da shi kuma ya kasa ‘dauke nasa idanun daga kanta, fuskar ta yake ‘karewa kallo har zuwa la66an ta, wani sabon salon ‘kaunar ta ke ‘kara nin kuwa masa a zuci, wanda har be san lokacin da ya mi’ke ya isa gaban gadon ahankali ba, ita kuwa tuni ta rintse idanun ta ganin ya nufo ta dan bata san me yake shirin aikata wa ba.
Abbas kam shai’dan mai masa muguwar sa’kan nan be zo masa ayanzun wata’kila sanadin karatun da yayi ne shiyasa, wannan karan shai’dan ‘din be yi masa mummunan sa’kar daya saba yi masa akanta ba, jiyayi kamar ana fizgansa zuwa gareta idanun sa na ‘kara haska masa asalin kyaun surar datake dashi……da ‘kyar ya dawo da tunanin sa dai-dai tare da jijjiga kansa ahankali.
Wani 6ari na zuciyarsa ne ya wurga masa tambayar ” _me kake shirin yi ne Abbas_?
Lumshe ido yayi yakuma bu’de su atake sai ya sau’ke su akan fuskarta dake ‘dauke da rintsetsten idanu har yanzun bata bu’de ba, ‘karfin gaske yake jin zuciyarsa na fizgarsa zuwa gare ta.
Dakewa yayi a tsayen sai dage ya harha’do wasu ‘kabilun kalaman da sam basu ne acikin ransa a wannan lokacin ba ” _yau ma bazaki… yi sallar ba…ne?_ “
Yayi maganar yana wani gyara tsayuwa.
Jin yanda yayi tambayar yasa Teema ta bu’de idanunta ta ‘dan waigo a karkace ta kalleshi dayake dama ta bayan ta yazo ya tsaya, goshi ta ha’da dan ji tayi tarasa me ma zata ce dashi, aranta tace ” _ina ruwansa toh da sallan ta_ ?
Jitayi yasake jefa mata wata tambayar inda yace
” _Ko har kinyine bansani ba_ ?
Kai ta jijjiga masa amamar ah ah tare da sau’ke idanun ta zuwa ‘kasa.
Story continues below

Abbas taran ta yayi da fa’din ” _amsani da baki i thought mun gama da wannan 6angaren tun ba yau ba_ ?
Ahankali ta bu’di baki tace
” _a’a banyi ba_ “
” _Sai yaushe kenan_ ?Ya sake tambayarta.
Cewa tayi
” _May be gobe_ “!
Tayi maganar kaman an matsi bakin ta ne an sata dole.
” _Okay_ “
Kawai yace da ita tare da
juyawa ya koma parlour dan kallon news ‘din safiya.
Teemah kam da idanu ta bishi har ya bar ‘dakin gaba ‘daya, sai kuma taji ta kasa ko da motsin kirki ma, haushin ta ‘daya yanda ya wani tsare ta da tambaya shi sam be san yaji kunyar abu ba, hakama ranar yawani cire mata kaya dan bata da lafiya ko kunya bayaji shi bayan yasan ita baso take ba, jiya ma haka yasa ta wai ta ‘dauke pant ‘din ta a bayin sa bayan ko be fa’da bama idan ta tuna zata ‘dauke abin ta da kanta, toh period ‘din da takeyi ma sai yaji dalili ne ko kuma ranar gamawar ta ?
Duk cikin ranta take wannan tunanin.
‘Dan karamin tsaki ta ja bayan ta ‘mare tunanin tace ” _mutum sai sa idon tsiya gashi kamar mumini amma san bahaka bane_”
Tare da juyawa ta gyara kwanciyar ta da kyau.
Caraf idanun ta suka sau’ka akan photo enlargement ‘din sa dake manne a bangon ‘dakin saitin ta, tun shigowan ta ‘dakin bata lura dashi ba sai yanzun sai taga kamar ita yake kallo shima.
Sanye yake da full dress na Uniform Karky ‘dinsa na sojoji, kansa babu hula ya ri’ke ta a hannun sa wanda ya ‘dago hannun sa dake ri’ke da hulan ya ‘dora akan ‘kirjinsa yana murmushi aka haska pix ‘din ba ‘karamin kyau yai ba ita kanta ya birgeta, daga dungun ‘kasan photon kuma wani ‘dan ‘karamine shima aka ha’da su, shima nasa ne kuma still da karky ajikinsa, ya ‘dan ‘daga hular dake kansa ka’dan kamar me shirin sarawa wani, bambamcin kawai wannan ‘din ya ‘dan sunkuyar da kai ne sa6anin sarawa da shi kai asama ake yinsa, wannan ma sai yafi yi mata kyau fiye da waccen babban dan shi ‘din yafi sake fuska aciki kuma yayi salo me birge duk wanda yagani yakuma fa’da’da fara’ar sa afili har ana ganin hasken hakoran sa.
Daga ‘kasa taga an rubuta *Cpt. M A AL-HASSAN* .
Sunan ta sake maimaitawa abakin ta sosai taji da’din fa’darsa abaki.
Ahankali ta sau’ka daga gadon ta koma gaban pix ‘din ta rin’ka shafawa tana kallon sa, ta6e baki tayi aranta tace a photo ka’dai ake ganin fara’a da murmushinsa shi, shiyasa ma yafi kyau anan ‘din fiye da ganin sa zahiri”
Tayi maganar tana wani shashshafa photon ahankali.
Ta shashance tana kallon sa har bata san cewa ta ‘dau tsawon lokaci ahakan ba.
Har Abbas ya shigo ma bata sani ba gyaran muryarsa kawai taji daga bayan ta sai kuwa tajiya da sauri.
Suna hada idanu yace da ita
” _Bana son rigima fah, idan kika kuskira kika yi min 6arna ni da ke ne_!”
Yana gama fa’din haka ya wuche bayi.
Ita ma binsa tayi da kallo tare da hararan bayan sa batare da tace uffan ba har ya shige cikin bathroom ‘din.
Teemah bata wani ‘kara ‘daukan dogon lokaci awurin ba ba ta wuce ‘dakin ta da rabon ta dashi tun jiya da dare.
Wanka tayi tafito ta sami wata atampa cikin jerin kayan data gani jere a ma’ajiyar kayan dake ‘dakin nata.
Riga ne da skirt kayan ‘din kin zamani, ko da tasa kuwa sai taga kamar kayan daga cikin kayan ta ne aka ‘dauko shi, domin ganin yanda ya zauna mata ajiki.
‘Bata lokaci tayi ta kashe ‘dauri bayan ta zizaro kwalliyar ta ta yayi gwanin birgewa sai dai bata cika fiskar ta da tarkace ba light make-up tayi kawai yau ‘din.
Maman Amal Teemah ta tuna da kalaman ta na baya da kuma Anty da nata maganganun basu da’de ba da ta fade su, wa’dan nan bayin Allahn sun bada ‘kyakykyawar gudum mawa arayuwarta ita kanta tasan hakan, sune suke cewa da ita taringa yin kwalliya sosai agidan mijin ta, Allah sarki Maman Amal ‘yar uwa mai ‘kauna saboda Allah kenan, lokacin auren ta na baya da Mahmud ba ‘karamin ‘ko’kari tayi ba na ganin ta gyara zaman takewar su, amma bai nifi tsawon rayuwa tsakanin ta da Yah Mahmud ba, Teemah da kanta tasan Maman Amal mai son tsakani da Allah ce kuma har yanzu darussan ta na nan bata manta ba, sosai Teemah tayi missing wannan baiwar Allahn.
Tana kammalawa da ‘daurin ta tashi tana ‘karewa jikinta kallo acikin dressing mirror, ‘karan door bell ne ya dakatar da ita sai ta tsaya shiru tana tunanin ko Yayan ta zai je ya bi’de , amma sai taji ‘karan ya kasa karewa kusan mintina uku ba’a daina ba hakan yasa ta fahimci cewa babu wanda ya bu’de ‘kofar, sai tayi tunanin ko har yanzu yana bathroom ne.
Saurin fita daga ‘dakin tayi ta nufi palour da niyyar bu’dewa sai kuma taci karo da shi wanda suka bu’de kofa atare suka fito, shima ‘din door bell ‘din ne yafito shi.
Sau ‘daya ya kalle ta sai ya ‘dauke kansa yaci gaba da tafiyar sa, Teemah daga inda ta ganshi bata ‘kara motsawa ba ganin ya fito kawai sai taja ta tsaya.
Hannah ce ta shigo hannun ta ri’ke da wasu ha’da’d’dun warmers guda biyu.
Tana ganin Teemah tasaki murmushi amma bata kula ta ba, sai da ta rissina cikin natsuwa ta gaida Abbas tukunna wanda yana amsawan yakoma ciki dan be gama shiryawa ba yafi to.
Yana shigewa Hannah ta danno da gudu ta rungume ta tana dariya ta ce ” _mrs Dodo kinyi kyau fah irin wanna show haka gaskiya kin yi wuta amarya, banzo da waya ba Allah da na miki photon mrs Yayah first day in her husband’s house_ “!
Ahankali take maganar dan kar Abbas ya jiyo ta.
Duka ta kai mata sai ta goce tana dariya.
Dariya sukayi dukkan su, hannun ta Teemah ta kamo tace ” _zo mu shiga ciki kiga wani abu_ “
Hannah da sauri ta ‘kwaci hannun ta tare da fact din ke barni ba yau ba, zan dawo watakila gobe yau din nana Ummah da babban warning ta ha’dani tace kar na yarda na wuce time din data bani wai in koma da wuri”
” _Ke de Hannah Allah ya shiryeki, idan baki son zama ai bazan tilastaki ba amma miye na buga wa Ummah_ _sharri har haka_ ?.
Teemah ta fa’da fuska ba yabo ba fallasa.
Tuni kuwa Hannah ta fahimci bata ji da’din hakan ba domin ta tabbatar mata sai tace
” _wai ke kina tunanin sharri ne” “ehh mana toh da menene? “Allah Teemah ba sharri nayi mata ba, can’t u see hannu na ko waya fah babu!_
Ta dago hannayen ta tare da waresu sannan taci gaba
” _Tasan i’m addicted 2 my phone shiyasa ma ta ‘karbe bayan ta ha’da ni da warning, dan tana tunanin ko dan wayar ma dole zan koma gida da wuri, ban gama kawo abincin bama fah bari in ‘dauko sauran_ “.
Hannah tana maganar tana nufan ‘kofa, Teemah ma sai ta bita abaya suka fita tare.
Sai da suka fitan ne Hannah tana murmushi tace da sigar tsokana
” _kin san yanzu ke amarya ce Ummah bata so a dame ku ne shiyasa…._
‘Kasa-kasa tayi da murya tace ” _ke inaga fa Ummah jika take so da wuri….._ “
Duka Teemah ta kai mata tana dariya itama da sauri Hannah ta goce itama tana dariyar da haka suka isa wurin motan batare da ta ‘karasa fa’dan abinda tayi niyyan fa’di ba.
Kar6an coolern Teemah tayi a hannun ta itama sai tace da Hannah
” _Bani zan tafi dashi ki je abin ki karki 6ata ran Ummah tun da bata so a dame mata ya’yah gara kiyi sauri ki_ _tafi_ ”
Dariya sosai Teemah ta bawa Hannah takuwa dara tare da fa’din
” _yarinya kenan!_ ”
matsowa tayi daf da kunnan Teemah tace ” _Darasin ki na gaba mrs dodo zaki gane kuren ki ai_ “!
Hannah na gama maganar ta shige cikin mota tana dariya, sai alokacin kuma Teemah ta gaida driver tare da ‘dagawa Hannah hannu.
Ashe har da driver Ummah ta ha’do ta ya kuwa jirata dan ma kar ta zauna ‘din dagaske.
Sai da taga sun bar gidan sannan takoma ciki, tana shiga sai ga Abbas ma ya sake fitowa cikin shigar suits ash colour, yana ganin ta yaja ya tsaya turus, take ya wani ha’de goshi tare da ‘kan’kance idanu yace ” _what nonsense!…. daga ina kike.._ ?
Hankalin ta kwance ta bashi amsa da fa’din ” _wannan na kar6o “_
Tayi maganar tare da ‘dago coolern ta nuna masa dan bata zaci laifi ta aikata ba.
Tsawa Abbas ya daka mata har sai da ta tsorata, yace
” _Shut up da Allah ni, ke aka aika ki kawo ne_ ?
_ko ita wacce aka aikon bata da hannu shigowa da shi sai ke? Wama yace miki ki rin’ka fita a haka da irin wannan shigan?_
Har yanayin fuskar ta ya canja zuwa yanayin kuka kamar yanda na shi ma canja ya koma yanayin 6acin rai, cewa tafara yi.
” _Yayah ni…._
Dakatar da ita yayi da fa’din
” _Yaya what_ ?
_did i send u_ ?
Shiru tayi ta sunkuyar da kanta ‘kasa ita masifar tasa mamaki yake bata ma.
Shi kuwa tsawa ya sake daka mata inda da ‘karfi yace ” _tamabayar ki nake_ _yi na aike kine_ ?
Sosai ta tsorata da tsawan nasa dan ita har ga Allah bata san irin hakan sam.
Kai ta jijjiga masa da sauri alamar ” _ah ah_ ”
Kwafah yayi yana kallon ta yace ” _so_ …!
tare da ‘dage gira ‘daya.
Baki tura gaba ta juya kai gefe a ranta tace ” _kai ka sani ai masifaffe mai hali biyu kawai_ ”
Afili kuwa ‘kun’kuni tafara tana wani ha’de rai itama.
Gani tayi ya fara tahowa inda take ai da sauri ta ajiye coolern ta yi ‘dakin ta da gudu, tana shiga kuwa ta datse ‘kofan ta tsaya maida nunmfashi.
Abbas kam binta yayi da kallo har ta shige ‘din sai ya saki guntun tsaki, har zuciyarsa yaji haushin fitan da tayi ahakan bayan yasan akwai maza a harabara gidan, batyan mai gadi yasan dole Hannah da driver zata zo amma shine an ta rai,a shi sai ta fita ahaka tana juya musu jiki, wama yasan irin yanda shigar tan ya birge su.
Wani tsakin ya ‘kara ja ya koma ‘dakin sa ya ‘dauko keyn mota ko ta kan abincin bai bi ba ya yi waje abinsa.
Teemah kam jikin ‘kofan ta mannu ta ringa sau’ke ajiyan zuciya, shab ta manta ma akan cewa ya tsani ‘kun’kuni shiyasa tayi, da badan haka ba da ba za tayi masa ba acikin irin yanayin da ta ganshi ‘dazun……
Afili ta ce ” _kai_ _wannan_ _mutumin ba dai mugun hali ba”_
Bata fito ba sai da ta ‘dau kusan 40 mins a’dakin sannan ta bu’de ‘kofan ahankali ta le’ko, sam bataga alamun mutum ba kamar yadda bata ji motsin kowa ba dan haka sai ta fito gaba ‘daya tana san’da ahankali.
Jin shiru a ko’ina ne yasa ta ‘dan saki jikin ta ganin kamar baya gidan.
Coolern data bari a hanya ‘dazu taje ta ‘dauke sannan tafara bubbu’de su tana ganin abincin.
Wainar shinkafan data gani ce ka’dai ya birge ta dan haka sai ta ‘diba tafara ci a hankali.
Sai da ta gama sannan ta koma ‘dakinsa ta gyara shi da kyau babu wani datti amma sanda ta share shi tas ta kunna burner sai ta ja ‘kofan ta rufe tare da komawa nata ‘dakin duk sai data bisu ta kintsa su inda cikin ‘kan’kanin lokaci ‘kamshin gidan ya canja, lungu da sa’ko sassanyan ‘kamshin turaren wuta ne kawai ke fitarwa.
Story continues below

Sai da ta gama da wannan sannan taji ta shiru, saboda babu wayar ta tare da ita, gashi kuma tana so tayi ‘kira amma bata san yadda zatayi ba, ta manta ‘dazu kuma bata ce da Hannah ta kawo mata ba.
Yana fita ko 1hr be kai ba yadawo sai gani tayi ana shigowa da drinks da snacks kala-kala ana ajiyewa.
Abinda kawai ya ha’da su cewa da yayi ta saka drnks ‘din a fridge da yawa, ya kuma tsaya sai da yaga ta sa ‘din ragowar kuma ta adana su kafin ya sake fita batare da yace da ita komai ba.
Zuwa 11am sai ba’ki suka rin’ka zuwa daga gida, ‘yan uwa da dangi kaca-kaca sun kuwa matu’kar ‘debe mata kewa dan kuwa hira auka rin’ka yi da su Hannah gashi da isheshshen abincin su suka taho wanda suka ci ya ishe su har da saura ma.
Abbas ma da yake yasan da zuwan ba’kin so bai ko le’ko gidan ba har sai bayan sallar maghrib, a lokacin kuwa dukkan ba’kin sun tafi saura ita ‘daya.
Gudun hayaniyar su nema yasa be zo dawuri ba sai da ya tabbatar duk sun tafi dan yasan mata duk inda suka ha’du akwai surutu.
Yana shigowa gidan ‘kamshi ya yi masa maraba, sosai da’din ‘kamshin ya ratsa masa zuciya, a parlour ya zauna ya wani lumshe idanu yana sha’kan dadda’dan ‘kamshin da ke tashi a parlourn.
Tsawon mintina goma sha yana zaune a parlourn, sai daga baya ne ya tashi ya kama hanyar ‘dakin sa, yaso ya duba ta kafin ya wuce amma kawai sai ya barta ya shige dan agajiye yake gaba ‘daya.
Teemah kam bata ma san ya dawo ba tana can kwance tayi zuru-zuru tsoro duk yabi ya cika mata zuciya, motsin kirki bata iya yi banda ‘dan ‘karan da fanka keyi babu abinda ke tashi a’dakin.
Tsoronta sake ninkuwa yakeyi aduk lokacin da idanunta ya kai ga kan agogon dake manne a bangon ‘dakin, ganin lokaci na ‘kara tafiya amma har yanzu shiru, tunanin inda Yayan ya tafi wannan lokacin ka’dai takeyi taso da ace wayarta na hannun ta da ta ‘kira shi ko kuma ta ‘kira Hannah ta sake ro’kon ta ko zata tausaya mata ta dawo dan taya ta zama.
Abbas kam yana shiga ‘dakin sa yatar da shi tsab a gyare ga wani sassanyan ‘kamshi na musamman daya ke fitarwa shima, duk dama ba’a birkice ya bar ‘dakin ba amma yanayin daya samo shi a yanzun ya matu’kar birgeshi.
Wanka yashiga inda ya kwashi kimanin mintina 20 kafin ya fito, shiryawa yayi cikin kayan baccinsa masu birgewa sannan yafito yaje ba’kin ‘kofar ta yayi mata knock, Teemah naji ta ‘dan firgita amma dataji an sake bugawa sai ta taso a ‘darare, da rawar murya tace ” _waye ne_ ?
Da ‘dan hanzari yace da ita
” _Open up pls, wa kike tunanin zaizo_ ?
Tana jin muryarsa ta yi saurin sa hannu ta bu’de ‘kofan, shima Abbas juyawa yayi ya koma parlour, itama Teemah sai ta fito ta biyo shi abaya tare da fa’din ” _sannu da zuwa Yayah_ ”
” _Yauwa matsoraciya_ “
Yace da ita batare da ya waigo ba.
Dai-dai lokacin da ze zauna yace ” _me kike yi a ‘dakin dama_ ”
Da ” *bakomai* ” tabashi amsa atakaice.
” _Tsoro ko_ ?
Yasake tambayar ta bayan ya daidai ta zamansa da kyau akan kujerar.
Tana tsaye bata zauna ba tace dashi ” _Ni ka’dai ce fah agidan tun ‘dazu, kuma nace Hannah ta zauna kar ta tafi amma_ _ta’ki yarda sai tayi tafiyarta kuma ni kuma tsoro nakeji_ ”
” _Kin fiya tsoro daya ne ke, bagashi na dawo ba idan ta zauna ma me zata kare miki_ “
Yayi maganar yana ‘ko’karin canja chanja channel ‘din T.V dake faman aiki.
” _Ai zamuyi hira da ita_ ”
” _Hmm_ “
Kawai yace batare da ya sake furta komai ba.
Shiru suka yi dukkan su na ‘dan wani lokaci banda ‘karan T.V babu komai.
Story continues below

Abbas ne ya yanke shirun da fa’din ” _bani ruwa plz_ ”
Tashi Teemah tayi a hankali ta nufi hanyar kitchen cikin cikin tafiyar ta me ‘daukan hankali wanda ita kanta bata ma san tana yi ba, Abbas binta da idanu yayi yana ‘kare mata kallo rigar dake jikinta roba ce, amma tabi duk jikinta ta kamata ta ko’ina, ilahirin shape ‘din jikinta babu wanda be bayyana ba, harta shige ya daina kallon ta amma be ‘dauke idanun sa daga wurin ba sai daya ga ta fito daga kitchen ‘din ne yayi saurin juyar da ‘kwayan ‘idanun sa ka’dai batare da ya motsa kansa ba, gudun karta kama shi yana kallon ta.
Ruwan ta zuba masa cikin wani farin glass cup ta mi’ka masa, Abbas kar6a yayi yana kallon fuskar ta ita kuwa idanunta nakan cup ‘din ne so bata san ma yana kallon ta ba, yana kar6a sai ya kai baki ya shanye ya sake mi’ka mata cup ‘din.
Tana zubawa yasake shayewa sai ya dire cup ‘din.
Teemah kai ta ‘daga ganin irin yawan ruwan da ya sha suna ha’de idanu sai ya ‘dage mata gira ‘daya.
Ita kam kauda kanta tayi gefe tare da ‘daukan cup ‘din ta mi’ke tsaye domin mai dasu muhallin su, Abbas kam harda kishin gi’da ya sake bin ta da wani sabon kallon har taje ta dawo.
Sai data dawo sannan ya sake maida ta ‘dakinsa ta ‘dauko magungunan ta, data kawo ya sake sata ta dauko ruwa, zuwa yanzun kam tafara gajiya da aikan nasa, meyasa dama ya barata ta maida ruwan bayan yasan ze ce tasha magani, sai ta fara ha’de ranta tana kwa6a fuska.
Abbas da ya lura da ita sai yayi murmushin gefen baki kawai ya jijjiga kansa, ri’ke take da ruwan ahannun ta, yayin da shi kuma yake 6allan maganin amma ya tsareta da idanu har se da ta maida nata idanun ‘kasa sannan shima ya kalli maganin dake hannunsa yace ” _Ni kam ina fatan Allah ya nuna min ranar da matata zatayi farin ciki da kasancewar mu, ranar da zan ce tayi min abu ta aikata min batare da ta 6ata ranta ba_ ”
Kanta ta ‘dago ta kalleshi dan bata san inda kalaman nashi suka dosa ba sai kuwa suka ha’da idanu dashi, ko a fuskar sa da cikin idanunsa Teemah bata fahimci yanayin sa ba dan shi kullun ahakan yake da wuya ka fassara ainahin yanayin da ka ganshi aciki.
Jitayi ya cigaba da magana inda yace
” _Ban sani ba ko sai ranar dana mallaki Zahra ta, may be ita zatafi faranta min bazata dinga gajiya_ _da min hidima ba_ ”
Shiru tayi tana tunanin _wacece kuma Zahra dayake magana akai haka_ ?
Maganin Abbas ya mika mata tare da fadin ” _Kar6i kisha_ !”
Ita tunanin Zahra ne ya tsaye mata arai koda ya mika mata maganin ma kar6a tayi kawai ta rike a hannu ta zuba ma hannun idanu, sai daya sake cewa da ita tasha sannan ahankali taringa sha da ‘dad’daya har ta shanye lokaci-lokaci takan ‘daga ido ta kalleshi zuciyarta cike taf da tambaya amma takasa furtawa.
Koma wa yayi jikin kujera ya jingina sannan yace da ita ” _ki ringa shan maganin ko bana gida kinga yau ma tun safe baki sha_ _ba_ ”
Ahankali tace da shi
” _ai na riga na warke yanzu ni lafiyata ‘kalau_ “!
” _Ban yarda ba, ban yarda da half treatment ‘din nan ba ki rin’ka sha_ _akan lokaci kinji_ ?
Kai ta ‘daga masa alamar taji, daga nan ta mike ta maida cup ‘din ruwan inda ta dauko.
Abbas lumshe idanu yayi yanajin zuciyarsa na harbawa sosai yake jin wani sabon yanayi yana ratsa shi.
Koda ta dawo kuwa sai bata zauna ba ta wuce ‘dakin ta inda ta watsa ruwa tare da canja shiga zuwa kayan bacci.
Zama tayi a bakin gadon ta tana tunanin wayarta sosai tayi missing wayarta a kwana biyun nan dan zama shirun yafara isan ta sosai, gashi ita ba gwanar zama ta kalli T.V ba da kuwa tasan zai ‘debe mata kewa.
Hisnul Muslim ta ‘dauka cikin takardun data gani a drawern ‘dakin tafara karanta azkar ‘din safiya da maraice bayan shi sai ta ‘kara dana kwanciya bacci kafin ta kammala ma sai bacci yaso yaci ‘karfin ta, a hankali ta mi’ke agadon ta kwanta take kuwa bacci ya dauke ta.
Lokacin da Abbas ya tashi ze daga parlourn har ya le’kata sai yaga baccin ta takeyi, hasken ‘dakin ya kashe mata ya bar dim light kawai tare da ja mata ‘kofar ya wuce nasa ‘dakin.
*10:30pm*
Ta farka daga baccin kamar an tsikare ta ta tashi ta zauna tabi ilahirin ‘dakin da idanu, tana gama fahimtar inda take wato a’dakinta kuma ita ka’dai ai sai ta tashi tafice da sauri ta bar da’kin, Allah sai ya taimake ta hasken parlour na nan be kashe ba.
Amma Teemah bata tsaya nan ba ta wuce ‘dakinsa, ‘kofan abu’de yake dan haka kawai sai ta tura ta shiga da ‘yar siriryar sallamar ta.
Zaune yake a bakin gado farar singlet ce ka’dai ajikinsa da dogon wando, system ‘dinsa na agabansa inda ya bada dukkan hankalin sa akai yana dubawa, ‘kafarsa ‘daya na tsaye yayin da ‘dayar kuma take tankwashe ya zauna akai.
Sallamarta ce ta sa shi ‘dagowa ya kalle ta da mamaki dan kuwa yasan tayi bacci tun tuni kawai sai ya ganta yanzun kamar an koro ta.
Hankalinsa da idanunsa ya mayar kanta ya tsaya ‘kare mata kallo, yau riga da wando ta sanya ajikin ta, yariga yasan zancen daya kawota amma duk da haka sai ya jefa mata tambayar
” _ya akayi_ ?
” _Babu komai_ ” itama tace masa atakaice.
Cewa yayi
” _Toh me ya hana ki bacci har yanzu? ko rigimar da saura ne bata ‘kare ba_ ?
Yasake jefa mata wata tambayar.
Goshi ta ha’de tawani yi kicin-kicin da fuska tace dashi
” Ni bana wani yin rigima…..kuma ma ai baccin nake ji ne yanzun shiyasa nazo dan inajin tsoron ‘dakin can ‘din”
Ido ya zaro waje akanta yace
” _Kullun ne wai ke kike jin tsoron_ ?
_Come on… go back to ur room kiyi addu’ah ki kwanta_ ”
‘Kafa ta fara bubbuga masa cikin shagwa6a take cewa ” _ni wlh tsoro nake ji ni ka’dai_ ….
Yatsan sa ‘daya ya ‘dago ya nuna ta dashi yace ” _bafa na son iskanci …da ‘din da wa kk kwana da zaki tsiro min da wannan iyayin yanzu_ ?
Kuka ta sanya mishi yanzun tana ‘kara maimaita ” _ni wallahi tsoro nake ji kuma ai ko da ma bani ka’dai nake kwana ba_ _da Hannah ne_ !
Kwafa yayi yana kallon ta kamar an matsi bakin sa sai ya sake fa’din ” _kafin itan kuma fah_ ?
Shi adole tsare ta zaiyi da fa’din hakan.
Teemah kuwa cikin kwanciyar hankali ta bashi amsa da fa’din
” _ni da Yayah Mahmud_ “!
Take Abbas yaji wani mugun bugu azuciyarsa, ransa gaba ‘daya yaji ya 6aci atake sai ya rintse idanun sa, wani mugun kishine yataso masa a zuciyarsa ga wani tunani na daban daya ‘dar su aransa, sai ma yake ganin kamar da gangan ta ambaci sunan Mahmud ‘din dan ta 6ata ransa.
Sam shi beyi tunanin zata ambaci Mahmud alamarin ba, he thought da can baya zata yi magana akai dan shima tunanin sa yatafi ne a lokacin datake gida a Damaturu, wancan lokacin kam yasan ita ‘dayan ta take kwana kuma dashi yaso kama ta.
Be iya jura ba sai da ya dafe kansa tsabar yanda yake sara masa, ‘kasa yayi da kansa ya sauke idanun sa akan system ‘din dake gaban sa, tamkar wanda yaga abin tsoro aciki ko kuma system ‘din ne yayi masa laifin sai ya rufe ta da ‘karfi.
Kamar an tsikare shi kuma sai ya mi’ke tsaye bai ko sake kallon inda Teemah take tsaye ba ya shige bathroom.
Teemah kam binsa tayi da idanu domin bata san me yasa shi canjin mood cikin ‘kan’kanin lokaci haka ba, amma ganin har ya shige be kula ta yasa ta tafi a hankali tayi kwanciyar ta.
Abbas haka da kayan jikin nasa bai ko rage ba yaje ya kunna shower akansa, zuciyarsa, nutsuwarsa da tunaninsa duk suka caku’de suka dagula masa lissafin sa gaba ‘daya.
Banda emergining rayuwarta da Mahmud babu abinda ke zuwa ransa alokacin, rayuwarta na baya agidan Mahmud yake tariyo wa har sai da ya kasance shine babban damuwar sa alokacin, shi kansa yasan ba dai-dai yake aikata wa ba amma zuciyarsa ta kasa yadda da cewa ‘kaddarar su kenan bayan yariga yasan hakan ne nd he can’t change it, he cant even erase d fact that ta ta6a zama gidan wani da sunan aure, kishin hakan ne ya hana zuciyarsa sakewa, shai’dan yariga ya yi masa mugun hu’dubar da ba za ta amfane shi da komai ba.
Story continues below

Shi kansa Abbas yasan kuskure ne hakan saboda babu amfani tuna irin wannan passed ‘din musamman ma daya kasance yanzu Mahmud is no more but ya kasa goge hakan azuciyar sa, muguwar sa’kan nan ta ri’ke mashi zuciya sosai tana kuma sake haifar masa da zazzafan kishin Fateemah aduk lokacin da hakan yazo ransa.
Shi kansa ya’ki yake da zuciyarsa akan hakan mafi yawancin lokuta yana burin ganin ya dai-dai ya tunanin sa, rayuwar auren su ta ‘dau hanya, amma kafin faruwar hakan sai gashi da bakin ta ta sake tuna mishi cewa wani ya mallake ta kafin shi, kenan wannan passed ‘din ba zai ta6a barin rayuwar su cikin sau’ki ba, rayuwar ta da Mahmud yasan azuciyar ta ne ba zai ta6a iya kankare mata ba amma me yasa sai ta furta masa da bakin ta?
Haka ya bar shower nata zuba akansa kusan 1hr yana tsaye guri guda batare da ya motsa ko da ‘dan yatsan sa ba, da ‘kyar ya samu ya saita tunanin sa da taimakon kalmar innalillahi wa innah ilaihi raji’un dayake maimaitawa ya samu har ya watso ruwa tare da ‘dauro alwala ya fito.
Lokacin da ya fito ma har tayi baccin ta Teemah kam cikin natsuwa batare da damuwar komai ba.
Kallo ‘daya yayi mata ya ‘dauke kansa, sai daya sa kaya kafin ya shimfi’da dadduma ya tada sallar nafila kamar yanda ya sabayi kullun, shafa’i da wuturi ya ‘kara a kai sannan yayi zaman ro’kon mahallici haka ya dinga jero addu’o’i akan Allah ya kawo masa sauki cikin al’amuransa ya daidai ta tsakanin zaman sa da iyalinsa in har hakan shine alkahirin dake cikin rayuwarsu gaba ‘daya, kuma ya jikan Mahmud yasa mutuwa hutunsa ce.
Bayan da ya idar ma be tashi akan dadduman da wuri ba, sai da yaji ya dan nutsu kafin ya tashi a awurin.
Ji yayi kamar yakoma parlour yayi baccinsa a acan, amma sai yaga rashin dacewar hakan kuma daga yanzun baya son yadinga bawa shai’dan ‘kofar da zai ringa gina musu katanga tsakaninsu dan haka sai ya tako zuwa gaban gadon ya tsaye nesa ka’dan da ita yana me sake koran shai’dan azuciyarsa.
Su hajiya Teemah sarkin birgima har ta juya tafara bararraje wa, jiyayi yana son ganinta sosai be yiwa idanunsa rowa ba kuwa ya ‘karaso ‘bangaren da taken tare da zama agefen ta yana me kusan ta kansa izuwa gareta, gashin ta dake tsefe ne duk ya baje mata afuska saboda fitan da ribbom ‘din dake kan wanda ta ‘daure dashi yayi.
Tunawa yayi da rigimar ta tun tana ‘yar karamar ta bata son kitso sam, yasan hakan ne sanadiyyan zuwa hutu daya keyi acan Damaturu, wasu lokutan idan yana can shine zai zauna ya tsefe mata kan da lallami wataran kuma har sai ya siyo mata tarin choculates kafin take zama, tun be iya tsifan ba har ya zo ya koya da kyau yana mata a weekend.
Idan za’a yi kitson ma sai an kai ruwa rana kafin asamu ayi, bayan haka kuwa idan taga kitson akanta sai tafi kowa iyayi da yanga dashi.
Har ta girma bata son kitso, kullum kanta atsefe, Mummy kanta tayi tagaji ‘karshen ta haka ta ha’kura ta ‘kyale ta har abin yabi jikinta. Hakan kuwa be sa gashin ya lalace ba, domin yana nan ne kamar mara zuciya tana dai yin saloon akan lokaci amma babu kitso, gashi ba’ki kullum yana shai’ki ban sani ba ko dan kasancewar ta tsakiyan fulani ne ko kuma nata halittan ne haka oho.
Hannu yasa a hankali ya tattara mata gashin gaba ‘daya zuwa tsakiyar kanta kusa da goshin ta anan yasa ribbom ‘din ya ‘daure mata gashin, dan yasan anan kam kowani irin bacci zatayi bazai ta6a takura ta ba.
Idanunsa ya tsayar akan fuskar ta ya tsaya ‘kare mata kallo musamman ‘dan ‘karamin bakinta na rashin kunyan nan.
Da yatsan sa ya shafo bakin a hankali sannan ya maida hannun nasa gaban goshin ta yana ‘dan shafa ‘kananun gashin dake gaban goshin a hankali ta yadda bazama tasan ana ta6a jikin ta.
Abbas ya kai kusan 15mins agaban ta sannan ya tashi ya koma ‘dayan gefen ya kwanta shima yasata agaba yana kallon ta a haka bacci yayi awon gaba dashi.
Story continues below

Washe gari da asubah daya tashi yau kam dabaibaye shi tayi, yajima da farkawa sai yajita ajikin sa amma beyi ko motsin kirki ba gudun karya tashe ta, ‘kiraye-‘kirayen sallah ne yasa shi motsawa tare da yun’kurin tashi wanda hakan yasa ta bu’de idanu.
Jin kamar tana jikin mutun yasa ta ‘dago idanu da sauri ta kalleshi sai ta kuma komar da kanta ‘kasa saboda ta ‘dan ji nauyin hakan dayafaru, shikuwa ganin alamar kamar bata da niyyan barin jikinsa sai ya ce da ita
” _Madam ‘dagani zanyi sallah ne, ko tashin ma sai na ‘daga ki kafin ki tashi dan na_ _ga alama naki son jikin na musamman ne_ ”
Jan jikin ta tayi ahankali ta bar jikinsa tare da juya masa baya tana ‘ku’kk’uni.
Sarai yajita amma be kulata ba saboda hanzarin karya makara yin sallah ,sai da ya mi’ke kafin yace ” _shine azhkar ‘dinki na tashi daga shimfi’da ko?_
Shiru tayi masa aranta tayi tsuka sai ayyana irin yanda ya takurata takeyi, kullum baya barinta tayi bacci mai kyau in badan ma tana jin tsoro ba da ina zai ganta ma balle ya dame ta.
‘Dan ‘karamin tsaki tasake ja tare da gyara kwanciyar ta da kyau dan taji da’din yin wani baccin.
Ita kanta tasan tana da birgima dan ko Hannah nayi mata complaint akan hakan watarana wasu lokuta idan suka tashi daga bacci amma ita baya damun ta kamar yadda bata kula Hannah koda tayi mata mitan dan kuwa ita bata san ta yadda zata daina ba.
Ko da datake gida ma gadon ta babban size daddy ya sai mata da mummy tagaya masa cewa tana da birgima, bata son taji ta takura idan zata kwanta shiyasa ma take birgimar ta son ranta, duk kuwa wanda yace zai kwanta gado daya da ita sai ya dasawa zuciyar sa ha’kuri sa6anin hakan kuwa sai de kai kayi ta annabawa ka bar mata gadon.
Tunanin ta tsayawa yayi cak lokacin data jiyo muryar sa yana rero karatun littafi mai tsarki cikin dadda’dan sautin sa me sa nutsuwa ga fidda dukkan ‘kal’kala da dokokin karatu, tana jin fitsari amma ta’ki tashi taje tayi dan kawai kar ta yanke jin karatun.
Har ya ‘kare karatun tana nan kwance, tana ji har ya gama gaba ‘daya ya mi’ke tsaye.
Tana ganin ya mi’ke agurin itama sai tayi hanzarin mi’kewa da saurin gaske ta shige bayi ko tura ‘kofan ma batayi ba dan yanda fitsarin ya matsata ta ke saurin sau’ke shi.
Abbas da idanu ya rakata har ta shige bayin sannan ya jijjiga kansa afili yace ” _Allah ya shirya_ ” sannan ya dawo da hankalin sa ga abinda ke gaban sa.
Yau ‘din bacci yakeji saboda baccin sa na daren jiya ka’dan ya samu yayi dan haka yau ko news ‘din safe ma be tsaya gani ba kishingi’da.
Teemah brush kawai tayo tafito dan tafi son tayi wanka a’dakin ta saboda zatafi sakewa acan kuma ma ko dan saboda kayan dazata saka ma.
Inda yake tazo ta tsaya har bacci ma ya ‘dan fara ‘daukan sa, sai yaji alamun ta akusa dashi, share ta yayi ya cigaba da baccin sa sama-sama sai ya jiyo ta tana ‘kiran sunan shi a hankali.
Idanun sa ya ‘dan bu’de sai ya sau’ke su akanta, suna ha’da idanu sai tayi saurin fa’din ” _ina_ _kwana Yayah_ “
” _Lafiya lau_ “
Yace da ita sai ya sake maida idanun sa ya rufe zaton sa ko dama gaisuwar ce.
Ganin haka sai tayi saurin sake furta ” _Yayah_ !
” _wai me zan miki ne_ ? Yayi maganr a’dan tsawace.
Teemah sai ta nutsar da muryarta cikin natsuwa tace ” _Yayah wayar ka zaka ‘dan ban aro in ‘kira su Mummy tun fa dana zo nan gidan ban ‘kara_ _waya dasu ba_ “!
idanun sa still arufe yace
” _Ina taki wayar_ ?
Ya sake tambayarta sai tace ” _ni bangani ba bansan ko tana gida ba_ “
Baya son dogon surutu dan haka sai ya nuna mata wayar tasa inda take.
Story continues below

Teemah ‘dauka tayi ta koma parlour ta ‘kira layin Mummy kamar yanda taga an rubuta awayar, bayan sun gaisa da ita sai ta ha’da ta da su Anty har ma da Ummah.
Inda duk suke ‘kara yi mata tuni akan biyayyar aure da bin dokar sa, Ummah ce ka’dai data kar6i wayar taringa ce da ita tayi ha’kurin zama da mijin ta.
Cikin farin ciki suka ‘kare wayar, bata maida masa wayar ba sai ma zaman ta data gyara zuwa kwanciya tayi pillow da hannun kujera.
Galleryn sa ta shige ta ringa bi tana kallon pictures ‘dinsa dama wa’danda ba nasa ba.
Cikin haka taci karo da pic ‘din wata mai kama da ita tana bacci, ganin kamar su da ita ne yasa ta tsaya ‘karewa pic ‘din kallo sai kuma tafara ganin kamar ita ce bawata daban ba, amma ta kasa tantance asalin gaskiyan waye ce a photon dan haka sai ta tashi tanufi wurinsa tana me ‘kara kallon fuskan wayar domin tabbatar wa.
Data kasa fahimta sai kawai ta bari akan wata daban ‘din ce ba ita ba, domin kuwa ita bata san lokacin da akayi pic ‘din ba, amma bari ta tambaye shi.
Tun kan ta ‘karasa cikin ‘dakin tafara ‘kiran sunan shi dolen sa ya yanke baccin ya sake bu’de idanun sa tare da fa’din ” _ya akayi_ ?
Kamar an korota tace dashi
” _Yayah kalli pic ‘din wata awayar ka me kama dani_ ?
Tayi maganar tana me sake kallon cikin wayar.
Beyi mamaki ba dan yasan yana da pix ‘dinta daya dauka da hannun sa wanda ita kanta bata ma san da zaman su ba.
Amma duk da haka
Abbas sai yace da ita
” _ingani_ “!
Dayake yana kusan tsakiyan gadon ne shiyasa sai da ta hau saman gadon ta zauna kafin ta nuna masa.
Abbas be kar6i wayar ba sai ya ‘dago kansa ya maida kan cinyar ta sannan ya kalli wayar sau ‘daya sai ya maida idanun sa ya sake lumshe wa sannan yace ” _kinsan ta ne_ ?
Amsa ta bashi da fa’din ” _ah’ah naga tana kama dani ne shiyasa….! a ina take Yayah?_ Tana maganar tana sake kallon cikin wayar ita dai abin na bata mamaki matuka.
Ce mata yayi ” _a_ _zuciya ta take_ “!
Teemah da mamaki ta kalleshi harda kwalalo idanu waje tace ” _Zuciya dai Yayah_ _saboda me kuma_ ?
” _Saboda ita Zahra ta ce, farin cikina kuma burin raina ina matu’kar sonta sosai……..inda kinsan yawan ‘kaunar da nake mata nasan har zaki tausaya wannan mijin naki, kusan hauka nayi abaya da_ ‘ _kaddara ya shiga tsakanina da ita ya sanya narasa ta sai daga baya kuma tadawo min alokacin da bana zato bayan har na yanke ‘kauna_ _da samun ta_ “
” _Ni kan ina so inganta Yayah plz ka kaini inganta even once_ “
Kai ya jijjiga mata alamar ” _ah ah_ ”
Sai t asake fa’din ” _pls Yayah mana nice fa_ “!
Yace
” _Ke wa_ ?
Itama sai bashi amsa da ” _Fateema Kabeer_ ”
Cewa yayi
” _Yes ai nasani_ ”
sai tace
” _Toh ka kaini in ganta mana kaji Yayah, Allah bazan ‘kara yima birgima ba daga yau ‘din nan_ “
Murmushi yayi dan kuwa maganar tata dariya taso sashi sai yace da ita ” _bazan kaiki ba ai yanzu ma damuna kikayi kika hana ni bacci dan haka nima sai ranar dana ga dama zan kaiki_
”
” _i’m sorry toh bazan sake ba Allah na daina daga yau_ “
Tayi maganar harda kama kunnuwan ta duka biyu.
Abbaskuwa ya jijjiga kansa.
Da sauri sai tace ” _Yayah toh sai yaushe kenan_ ?
Story continues below

” _Bayanzu ba akwai steps b4 aganta kinsan Zahra ta ta da bance_ “!
Teemah shiru tayi tana kallon fuskar sa dake kan cinyar ta yana murmushi har dimple ‘dinsa na lotsawa.
Ita kam abin na birgeta har ma bata san lokacin da ta kai hannu wurin ba.
Tuna waye ne yasa tayi saurin ‘dauke hannun ta tana sake kallon shi.
Ganin be motsa ba kuma be kulata ba yasa ta sake maida yatsan ahankali tana latsawa.
Abbas sai ya kai hannun sa ya ri’ke nata hannun dake masa yawo a fuska.
Yana cire hannun sai ya sake gyara kwanciyar sa akan cinyar tata.
Teemah sai ta tura bakin haushin ya hana ta ta6a dimple ‘dinsa bayan ya’ki amincewa ya kaita wurin Zahran sa.
Zuba masa idanu tayi cike da takaici, da ta rasa abin yi sai ta fara jan ‘kafar ta tare da fa’din ” _”daga min kafata nima tagaji Yayah_ “
Be ce da ita ko ‘kala ba sai ya maida kan nasa yayi matashi da pillow kamar yanda yake da farko tare da juya mata baya.
Teemah ma tashi tayi ta ajiye masa wayar a kan drawer sannan tafice zuwa ‘dakin ta fuska babu walwala, wanka tayi cikin sanyin jiki.
Yau ko kwalliya ma batayi ba powder kawai ta shafawa fuskarta, cikin rashin kuzari take yin komai dan tun barowar ta ‘dakin sa take jin 6acin rai nataso mata, ga tunanin Zahran sa daya tsaye mata a zuci, bata san me yasa take jin haushin ta ba, sai taji bata ‘kaunar ta ma sam, tasan wata’kila da Zahran ce ai da bazai hanata ta6a mai fuska ba.
Yau kam bata fita ba zaman ta tayi a ‘daki ko lokacin da door bell yayi ‘kara ma tanaji amma ta’ki fita, Abbas ne yaje ya bud’e ‘kofar wanda tun da ga jin yanayin gaisuwar su ma ka’dai yasa tagane ba Hannah bace yau takawo musu breakfast ‘din.
Sai lokacin ma ta tuna ashe yau monday ne Hannah nada lectures a makaranta.
Ashe kuwa ya taho mata da tarkacen wayoyin ta da sauran kayan ta na anfani ciki kuwa harda wayar Mahmud aka ha’do.
Dama ta sanar da Mummy cewa wayar ta na gida Hannah ta taho mata da wayar idan zata zo.
Abbas da kansa ya kawo mata har ‘dakin ta ko daya ga tana wani shan ‘Kamshi ma sai ya share ta shima ya fice abinsa dan yasan mecece matsalar ta.
Zuwan wayar ne ya ‘dan sanyaya mata rai ta ‘danji dama-dama sai duk ta bi ta sanya su a chaji gaba ‘daya.
*10:12am*
Abbas ya buga mata ‘kofa amma be jira ta bude ba kawai sai ya juya zuwa dinning.
Tana kwance tana faman chatn jin an buga mata ‘kofa yasa ta ajiye wayar ta fito sai ta hango shi zaune yawani hakimce yana amsa waya.
Tasan shine ya buga ‘kofar dan haka sai ta isa dinning ‘din itama.
Bata zauna ba sai ta koma kitchen ta ‘dauko su plates da cups ta dawo tayi serving nasu kana ta zauna bayan ta tura masa nashi gabansa.
Abbas na lura da ita amma be kulata ba dan yasan halinta sam magana be sata cin abin sai in har tayi niyyah sa6anin haka kuma sai de in kai ne zaka’dauki nauyin bata da hannunka dan haka be ma 6ata bakinsa ba, yasan idan taji yunwa zataci ne dolen ta ai tunda ita yunwa ba sabo ne da ita ba.
Har suka ‘kare cin abincin be ce da ita komai ba haka itama.
Ranar kam Abbas be fita ko’ina ba har aka ‘kira sallar azahar yana gida, sai de duk da agidan yake amma kowa na 6angaren sa babu wanda yaje wurin kowa.
Kafin azahar ‘din Teemah tayi wankan tsarki ganin cewa period ‘din ta ya ‘dauke, dama 4days takeyi.
Shi kuma lokacin da yayi alwala zai fita sai yabi ta wurin ta inda yazo dan sanar da ita fitar sa sai kuma ya tarar da ita tana sallah, be jira ta idar ba ya wuce kawai abinsa dan ba yaso jam’i ya wuce shi.
Story continues below

Bayan sun fito ne ya ‘kira ta awaya dayake yasan wayar natare da ita yace mata shi yafita kuma ba zai dawo yanzu ba, yace m za’a kawo mata abinci sai ta kula idan taji door bell taje ta anso kuma ta tabbatar ta rufe jikin ta da mayafi kafin ta fitan kuma bece ta fita ko da harabar gida bane.
Daga ‘karshe dan ya sake tunzura ta sai yace ” _zanje in dubo Zahra ta ne kwana biyu bana samun ta_ “!
Teemah ta6e baki tayi tare da fa’din
” _uhumm sai ka dawo_ ”
Koda ya yanke ‘kiran kuwa abin yaso ya dameta dan sosai ya tsaya mata azuci amma sai ta tambayi kanta dalilin damuwar sai ma taga laifin tane na shishshigin damuwar, miye ruwan ta toh da al’amarin sa ai yace itace farin cikinsa toh ita miye nata.
Tilastawa kanta tayi ‘karfi da yaji ta ya’ki zuciyar ta dole ta kawar da tunanin Zahran Yayah aranta sai de duk da haka lokaci zuwa lokaci tana sake tunawa.
Kamar yanda ya fa’da mata haka tayi domin tana jin ‘karan door bell tafita bayan ta zun6ula hijabin ta wadatacce babbah da take sallah dashi.
Driver ne yakawo sai ta kar6a bayan ta gaida shi tare da kawo masa coolers ‘din safe sannan tace da shi kar ya kuma kawo wa anjima wannan ma ya isa.
Ciki ta koma tana me jinjinawa ‘ko’karin Ummah sosai gashi kullun abincin yawa yake yi musu idan sunci ne ma sai Abbas yayiwa mai gadi magana yazo ya tafi da sauran gaba ‘daya ko ya yake yi dashi ma oho, ita dai nata kawai wanke warmers ‘din ne.
Zama tayi a parlour kawai tare da ‘kiran layin Ummah tayi mata godiya da kuma bayanin abincin sannan ta yanke ‘kiran.
Bata ko sake bi takan abincin ba taci gaba da duba wayar ta.
Abbas kuwa har se da yamma ya dawo gidan ya kuwa zo mata da fruits masu yawan gaske.
Daya duba abincin shima sai yaga ko ci batayi ba, yariga yasan hakan amma na yau ‘din sai yayi tunanin ko harda fushin Zahra ne, dan gudun kar ya shiga ha’k’kin ta da yawa daya watso ruwa bayan ya shirya sai ya fito yace tazo tayi serving nashi abinci.
Sai da ta wuche kitchen ta ‘dauko plates ‘daya da table spoon ‘daya sannan ta dawo ta zuba masa abincin dai-dai shi tare da ‘dauko masa lemonjuice da ruwa harda fruits ‘din da ta gama yanyan kawa tasa afridge ya ‘danyi sanyi domin kanta duk ta kawo masa ganin fried rice yau aka kawo kuma nada mai’ko sosai.
Tana shirin mi’kewa yadakar da ita inda yayi mata nuni da kujera.
Sam batada ra’ayin cin abincin musamman data ga ma cewa shinkafa ce wannan kuma bata cikin ra’ayin ta shiyasa koda zauna ‘din ma sai ta na’de hannu kawai tayi shiru tana tunanin ‘kila so yake ta taya shi zama.
Spoon ‘daya, biyu yakai bakin sa na ukun da ya ‘debo sai ya nufo bakinta dashi.
Teemah cikin idanunsa ta kallah sai yayi kamar be ganta ba hakan yasa ta dawo da idanun ta kan hannun sa dake ri’ke da spoon ‘din tare da bu’de bakinta ta kar6a.
Sai da yaga ta ha’diye sannan yace ” _bakya son cin abinci ko? Idan Zahra ta tazo raina ki zatayi dan kuwa ita_ ‘ _katuwa ce nikuma babu ruwa na_ “
Take tayi fushi ta tura baki harda ‘dan hararan sa ka’dan.
Murmushi Abbas yayi kawai amma na gefen baki be kulata ba yanzun dan so yake ta ‘dan ci abincin koma ka’dan ne shiyasa kawai ya shareta.
*****
Washegari da asubah da ya tashi sallah sai itama ya tashe ta ganin tafara yi, amma Teemah ta’ki ta tashi sai ta ringa juye-juye.
Har yaje yayo alwala ya fito bata tashi ba da yaga zata 6ata masa lokaci sai ya sa hannu ya ‘dago kafa’dun ta ya ta data zaune wanda hakan yasa dolen ta tashi tare da bu’de idon ta.
Sai yace ” _ki wuce kiyo alwala idan kika 6ata min lokaci Allah zan 6ata ranki kema_ “
Tanajin haka dolen ta ta mi’ke tana gunguni bata da’de abayin ba tafito bayan ta ‘dauro alwalan.
Abbas ne ya mi’ka mata hijab babbah daya ‘dauko a’dakin ta ta kar6a ta sanya tare da bin bayan sa yajasu sallar asubah tare da ‘daukan dogon lokaci yana addu’o’i tun kan su shafa Teemah take layin bacci suna shafewa kuwa ta koma gado ta du’kun’kuna cikin hijabin ko cire shi batayi ba sanadiyyan sanyin da ke tashi ka’dan-ka’dan da safiyar.
Abbas kam Al-qur’ani ya ‘dauko ya ‘dora da karatu tsawon lokaci sannan ya kammala.
Zuwa lokacin kuwa ruwan sama ya sa’k’ko sosai ganin hakan shima sai ya kishingi’da ya lumshe idanu yana me tasbihi ga mahallici.
‘Karfe takwas da ‘yan mintina Teemah ta farka daga bacci, jin ruwa na sau’ka yasa ta yin luf sosai take jin sha’awar shiga ruwan amma tarasa yanda zatayi dan tasan Abbas ba barinta zaiyi ba, juyawa tayi ta kalleshi sai taga kamar yana bacci ganin haka yasa da sauri ta fincike hijab ‘din dake kanta ta ajiye.
Cikin san’da ta ta kama hanyar barin ‘dakin dama Teemah gwana ce wurin son wasan ruwa Allah-Allah take tagan ta cikin ruwan nan musamman ma da yanzu ya ‘dan tsagai ta ka’dan.
Abbas idanunsa biyu babu baccin dayake yi duk kuma abinda take yi yana kallon ta sai da yaga ta kama hanyar barin ‘dakin ne yayi tunanin ko wani rashin ji zatayi dan haka sai ya dakatar da ita da fa’din
” *ZAHRA* !
Cak ta tsaya a inda take amma bata juyo ba shima kuma be sake magana ba idanunsa yasake lumshewa tamkar wanda ba shine yayi maganar ba.
Teemah kam jin be sake magana ba yasa ta waigowa sai taga still baccin sa yake yi sai tayi tunanin ‘kila ko cikin baccin ne yake ‘kiran Zahran sa amafarki murgu’da baki tayi.
Taso ta koma ta tashe shi a baccin kodan ya daina mafarkin Zahran ma dan ta ‘dan ji wani iri sanadin hakan amma jarabar son ta shiga ruwan sai ya fi rinjayar ta kawai ta juya.
Abbas ma sai ya ‘kyaleta kawai tatafi.
Cigaba tayi da tafiyar ta ta isa har kofan parlourn ganin a kule da security lock yasa ta koma tabi ta baya tafita ta ‘kofar kitchen.
Da farko hannayen ta tasa tana taran wanda ke sakkowa daga bakin roofing tana tara tana watsa shi afuskan ta tana murmushi, data ga hakan baze mata ba sai kawai tafara ‘ko’karin shiga gaba ‘daya.
Caraf taji an ri’ke mata hannu daga baya wanda ya matu’kar firgita ta domin bata ji zuwan mutun ba ita.
Arazane ta juyo sai taganshi take kuwa ya janyo ta zuwa jikin sa yana kallon cikin idanun ta yace ” _Kinyi ajiya aruwan ne_ ?
” _Umm- umm_ “
Tace da shi tana ‘kif-kif da idanu.
” _Toh me zakiyi_ ?
Yasake tambayarta.
In ina tafara tarasa me ma zata ce dashi sai yace ” _ina jinki_ “
Ahankali tace ” _wanka… zan..yi ne fah….Yayah_ “!
” _Shower ya lalace_ _ne_ ?
Ya tambayeta
Jijjiga mai kai Teemah tayi ranta har yasoma 6aci dan tasan ba barin ta zaiyi ta shiga ruwan ba tunda ya fito.
Sai ya sake fa’din.
” _bathtub fah_ ?
Da muryar shagwa6a tace
” _Yana nan_ ”
” _Bazakiyi ba toh, wuce muje bana son rashin ji_ ”
Kalar tausayi tayi tace ” _Ayyah Yayah ka’dan fah zanyi………._ “
Kafin ta rufe baki ma ya tare ta da fa’din ” _i said bazakiyi ba ko?…..ko ni sa’an ki ne dazan na magana kina jayayya dani_ ?