HIKIMA CHAPTER 4

HIKIMA






CHAPTER 4






Kwanaki a hankali suke tafiya har Allah ya kawo ranar daurin auren Anty Fadila da Hamma Mussadiq, gaba daya gidan a cike yake Tun ranar alhamis har yau asabar abin yafi tsamari, ko ina ka gifta Yan Uwa ne da abokan Arziki kowa ka gani cikeda farin ciki yake.

Dama baa raba bikin ba dukkan dangi from both sides dukkansu gidanmu sukazo aka hade gaba daya dan Baffa yace hakan zaifi sauki. Kayana da aka kawo dazun daga gurin dinki saboda Yayi min yawa dole se an rage, wani lace ne me bala’in kyau, Yayi kyau har ya gaji ni da Mama ne tayi mana anko. Ina gamawa na fito bayan na bobbeye abinda ya dace. Ina fitowa Angwaye suna shigowa, tunda nake ban taba ganin Hamma Mussadiq Yayi irin wannan kyau din ba, Yayi kyau har ya gaji ga wata haiba da cikar zati da ta kara kamashi. Idanunshi a Kaina Inata Murmushi Kamar bakina zai yage. Alama yayi min akan nazo, kafada ta na make Ina girgiza Kai, turo baki yayi tareda nuna kanshi irin ni ko? Kaina na gyada alamar Eh, wata cousin dita Amira dake gefena taga Inata dariya tace

“Wai dariyar me kikeyi ne? ”

Juyowa nayi nace

“Hmm! ”

Matsawa nayi na nufi gurinsu dan tuntuni an fito da Anty Fadila se hotuna take, dukkansu Murmushi kawai suke me tsayawa a rai, Ina zuwa aka matsa min na shiga tsakaninsu tareda riko hannayensu akai mana hotuna, karkatowa Yayi saitin kunnena ya rada min

“Kinyi kyau Mashaaa Allah!”

Da sauri na saki hannunshi na kalla Anty Fadila wadda kwatakwata hankalinta baya kanmu Tana magana da kawarta ne. A Haka photo session ya Kare aka cigaba da biki.

Da yamma akaje Luncheon nanma munyi kyau sosae abinka da Fulani kusan dukkansu kowa fari ne, se kadan ne daga cikinmu Wanda skin dinmu Yayi duhu, munyi ankon Silver material mu sisters, friends dinta sun saka cream lace, iyaye kuma golden, ita dashi gaba dayansu fari suka saka all through. Luncheon yayi kyau babu karya, I enjoyed every minute of it.

Da wuri aka tashi saboda Kai Amerya dakinta, tunda aka tashi take kuka ta kama hannuna ta kankame Kamar ni zan hana a kaita, ni Kaina wani irin yanayi nakeji na fargabar rabuwa dukda bawai tayi nisa bane still a anguwan take, tazarar ba mai yawa bace sosae.

A dakin Mama muka shiga, kanwar Mama Anty Hadiza ta kalleni tace

“Hikma jeki ta shirya to”

Kokarin tafiya nake amma Anty Fadila ta damke hannuna haka babu yadda zaayi se hakura akai na zauna, kuma duk nasihar da ake mata da fada a gabana akai aka gama, hannunta cikin nawa aka kaita gurin Mamanta, Ummiey, Tana zaune cikin yan uwanta aka kaita tayi mata nasiha sosae sannan ta dubeni tareda yimin Murmushi tace

“To ko ke Zaa basu yar zaman daki? ”

Dariya nayi nida mutanen gurin Wasu na fadin

“Wayaga shirme!”

Da haka muka Je gurin Mama wadda rungumeta kawai Tayi tace 

“Allah Ya baki hakuri, Allah Ya Baku zaman lafiya” 

Daga nan se Mota lokacin anata kiran Sallar ishai, a Haka mukaje, ina zaune a gefenta mutane se sambatun haduwar gidan suke, Dan babu karya gida yayi kyau an kuma Kawata shi da furniture masu kyau kana kallonsu kaga gidan yar gata. Haka mutane suka Fara bajewa seda ya rage Yan kadan Wanda zasu kara tsaftace gidan, suma suna gamawa na mike dan na bisu mu tafi amma fir Anty Fadila ta Hana, seda aka Kira Ango saboda wani irin kuka da take har seda ya karya min zuciya na Fara, yana daukar wayar yace a barni idan ya shigo zaisa a maidani, Haka suka tafi ya rage daga ni se ita, lullubinta ta yaye fuskarta ta bayyana wadda seda gabana ya fadi saboda yadda tayi wani irin pink tsabar kuka, gashi kwaliyya da akai mata ta luncheon bata wanke ba. Ai kwanciya nayi gefenta na dinga dariya ina nuna ta da yatsa, ai se ta kuma bata rai ba tareda tace min komai ba, seda nayi me isata kafin na janyo hannunta na kaita gaban rantsatsan dressing mirror dinta, Wanda ya kawatu da cosmetics iri iri, itama Tana ganin fuskarta se ta fashe da dariya Tana zaro ido. 

“I’m sure idan Hamma ya ganki a Haka, koraki gurin Mama Zaiyi. ” 

Harara ta sakar min, sannan ta wuce toilet don wanko fuskar ta, Tana fitowa muka cigaba da zama muna taba hira nake ce mata 

“Anty Fadila, Dan Allah kada Ki Bari ki zama koma baya wajen Hammana” 

Harara ta tayi tareda hura hanci tace 

“Auren Hadin? Shi da ba sona yake ba” 

Tsaki na dan yi kadan nace 

“Lallai ma, zaman da zakiyi kenan?” 

Bata Kai ga bani amsa ba mukaji sallama a parlor, da sauri na dakko veil dinta na yafa mata har Kai sannan na gyara zaman nawa na fita parlon daidai shigowar Hamma Har seda mukai gware, nayi baya da sauri ina shafa goshi na tareda turo bakina nace

“Ka buge ni” 

Murmushi yayi yana zare glasses din idanunshi Murmushi fal fuskarshi, Yayi kyau me sanyi Har ya gaji a cikin manyan kayanshi na farar dayyar shadda se sheki take Tana daukar ido. 

“Hamma is apologizingl” 

Ya fada yana hade hannayesnshi guri guda alamun ban hakuri yace 

“Ina Addar taki? Kuzo” 

Matsa mishi nayi don ya shiga ciki, ya gane manufata hakan yasa ya shige ciki, parlour na wuce muna gaisawa da friends dinsa harda cousins dinmu Wanda suke saani da Hamma, se tsokanata suke Wai kanwar Ango ta gaban goshi. Nidai sae Murmushi kawai nakeyi. Daki na koma seda suka gama barkwancin su da nasihohinsu sannan ya shigo yace 

“Fito Zaa kaiki gida” 

Immediately na mike na bi bayanshi, inajin sheshekar kukan Anty Fadila Hakanan naji zuciyata ta karye nasan ba karamar kewa zanyi ba. 

Karfe Tara da Arbain tamkar rana haka gidan Yayi saboda Wasu irin guda dake tashi from every angle na gidan, Aminu ne dalilin gudar don tunda aka daura aure bai shigo ba se wannan lokacin. Banda Murmushi babu abinda ke tashi daga kyakywar farar fuskarshi, yanata gaisawa da mutane ana tayi mishi Allah Ya sanya alkhairi, straight parlon Alhajin shi ya nufa, yana zaune shi daya yana kallon tashar CNN, yana jin sallamar Aminu Ya dago within a blink of an eye Ya kare mishi kallo, Sanye yake da Wagambari yar ciki da wando coffee se babbar rigar milk, hular kanshi Zanna Bukar ce wadda mafi yawan zaren da akai amfani dashi milk ne, agogon hannunshi na kamfanin Invicta yayi masa das se kyallin angonci yake. Zama yayi fuskarshi da wannan kayataccen Murmushi na tunda akai zancen kome yake yi. 

“Yaushe zaku tafi kaida hafsa?” 

Kanshi Ya Sosa yace 

“Eleven pm ne flight time din namu” 

Kai Alhaji Ya gyada yace 

“Allah Ya bada zaman lafiya se a kara kula a kuma kiyaye” 

“Inshaaa Allah Alhaji” 

Addua doguwa Alhaji yaja sannan ya sallami Aminu daga nan Straight dakin Dada ya nufa yasan nan kadai zai iske Hafsa, ile kuwa tana can kurya ta gama cakarewa cikin wata tattausar Lafaya me kyau Tasha sequence a jiki matsayin adon lafayar, tamkar an mata barin turare saboda yadda take kamshi. Yana shigowa aka soma sowa, bai bi takan kowa ba don lokacin tashinsu ya kusa, don Haka hannunta kawai ya kamo hakan yasa ta dago fuskarta pleadingly, yana jin Dada na gyara murya ammma haka ya janye Hafsa Salima se iskanci take mishi.

Karfe goma da ashirin suka isa airport ana gama screening suka shiga jirgi kuma har lokacin daidai da single word bai fita a bakinsu ba sede kana kallonsu kaga Wanda feelings da soyayya me azabtarwa ke dawainiya da junansu, amma yatsa sun kasa kaiwa junansu, kowanne zuciyarshi banda bugawa babu abinda takeyi. A Abuja wani friend dinshi yazo Ya daukesu yana ta tsokanarsu se Aminu ke mayarwa Haka Har suka isa Gwarimfa inda anan sabon gidan Aminu yake. Tundaga gate zakasan gidan ba karamin Haduwa Yayi ba, ko ina bulbs sun haska tamkar gidan rawa, suna parking Aminu Ya riko hannun Hafsa wadda yasa dukkansu jin wani effect na radiating jikinsu…………. 

Tsabar gajiyar dana Tarawa kaina koda asuba kasa tashi nayi sallah, inda Allah Ya taimaka ina period da idan na tashi I won’t forgive myself, saboda duk duniya babu abinda na dauka da muhimmanci Kamar sallah, I hate it idan nayi delaying sallah Ko Yaya ne, shiyasa nake mamakin yadda musulmi zai tashi kuma yanada tsarki amma yaki tashi Yayi sallah, rabuwar tayi yawa saboda munsan cewar sallah ita ce shugabar ayyuka. 

Har Karfe goma sha daya ina kwance cikin Duvet cover me laushin gaske Kamar fur din mage, dama sanyi ake it’s winter bacci dadi. Cikin bacci naji muryar Mama tana fadin 

“AI har Yanzun bacci take? ” 

Cikin fullanci, Aneeysa cousin dinmu ta mayar mata itama cikin fullancin 

“Tun dazun takeyi ko Sallar asuba ba tayi ba” 

Kusan Uwa tafi kowa sanin halin danta, tasan bana wasa da sallah hakan yasa ta shigo ciki sosae tana bubbuga min gefen gado, a hankali na yi juyi sannan na fito da kaina daga Duvet din ina mitsika idanuna nace 

“Mama Yalli jam? ” 

“Jam kalau Hikma, akace bakiyi sallah ba? ” 

Kaina na gyada nace 

“Period nake fa” 

Kanta ta gyada sannan tace 

“To tashi kiyi wanka, ki gyara jikinki an hada breakfast din gidan Hammanki” 

Kaina na gyada nace 

“Inshaaa Allah zan fito” 

Tana fita na Mike Ina zabgawa Aneeysa harara nace 

“Shi ne kika ce Banyi sallah ba” 

Harara ta wurgo min itama tace 

“Kinyi? Bakiyi ba ai ba karya na fada ba” 

Bama shiri da ita kwatakwata, a haukan ta Hamma Mus’ab take so ganin takun sakar da muke dashi tayi tunanin may be zai ce yana sona shiyasa Bama ga maciji da ita. Wani mugun kallo Nayi mata nace 

“Dadin abin ni bana skipping Sallah, idan kinga banyi ba period nake

Ai se ta mike tana huci saboda tasan gaskiya na fada, Nana itama cousin dinmu ce ta mike tareda riko hannunta tana fadin 

“Aneeysa Meye Haka wai, Hikma Yaddiko ba wanka tace kiyi ba?…..” 

“Maimaita abinda kika fada,…..” 

Da sauri Hikma ta katse ta da fadin 

“Baki bukatar hakan Dan Kinji me nace, ni bana skipping sallah sede period” 

Wani wancakalarwa tayiwa Nana Har seda ta fada gadon da na tashi a Kaina tayo Kaina Tana zage zage, yadda ta taho I thought dukana zatayi shiyasa na tsaya still inason ganin gudun ruwanta. Ganin ta tsaya Nesa Dani yasa nayi Murmushi kawai na wuce toilet, Ina tura kofar naji tace 

“Da baasan asalin balbela ba se tace daga Misra take” 

Wani bugu naji a kirjina amma Se ban fito ba Wanda nima bansan dalilin hakan ba. Aminu Hafsa ya dinga ringing cikin kunnuwana, a Haka na fito na samu babu kowa a dakin, a tsanake na shirya cikin wata coffee abaya Anyi adonta da stones masu tsananin haske, milk veil na yafa sannan na fito, Inata gaida mutane Har na dauki abincin dake cikin basket na nufi waje Se nayi wani tunanin hakan yasa na karasa parking lot na bawa driver nace ya Kai ni kuma na juya gida, ina shigowa nayi karo da Zaki da Aneeysa, ta wani bata fuska tana ta shagwaba Kamar zata narke, cikin sauri na rufe fuakata da veil din don Naga basu lura Dani ba, kafin ya tsinka ni cikin mutane. Dakin Mama na iske ta itada sisters dinta suna ta shirin tafiya gidajensu, Amarya ta tashi zaman me zaayi?

Story continues below


Baki bude Mama tace 

“Ya kika dawo Hikma? Me ya faru” 

Seda na zauna sannan nace 

“kinga gani nayi idan naje Anty Fadila bazata Bari na taho ba shiyasa na bawa Bara’u driver” 

Cikeda gamsuwa tace 

“Kinyi kyan kai” 

Daga Haka na fice ina dariyar jin Anty Raziqa Tana fadin 

“Biki se na auta Kare nono” 

Kwanaki hudu gidanmu ya koma daidai daga mu Se mu amma wannan lokacin nasan some part of me is missing, nayi missing Anty Fadila sosae yadda baki bazai iya fada ba, kullum dare Se nayi kukan rashinta har wani dare tsabar kuka seda na samu attack aka kaini asibiti sannan na dawo normal. Kullum tana cikin kiran wayar Mama akan Bazan zo ba. Se ranar Friday tana kwanaki biyar a gidanta Mama tace naje na yini, wayaga dauki? Tun seven nayi wanka amma Mamaa ta taja min rai Har se 10am na samu na tafi, dake a hankali yanmatanci Ya fara bayyana kanshi a Kaina musamman kuguna well figured, kana kallina Kasan makerin budurci has started his work danma babu laifi Inada tsayi shi ke shanye dukkan wani shape da ya Fara bayyana amma ni nasan akwai shi. 

A bayan mu suke hakan yasa na zabi tafiya da kafata, ina tafe ina rangaji tamkar bishiya iska na kada ta, nayi kyau me sanyi ga wani murmushi daya kwanta akan fuskata saboda Murnar ganin Anty Fadila. Daidai zan sha kwana naji muryar da ta sani saurin Juyawa, wato muryar Abdallah, yana tsaye ya harde hannayesnshi a kirji Se Murmushi yake min hakan yasa na sakar mishi sannan na dan rankwaba nace 

“Ina yini” 

Harara ta yayi yace 

“Bazan amsa ba, for how many days ban ganki ba do you know how hurt I’m? ” 

Idanuna na dan ware cikeda mamaki sannan nayi Murmushi Bance komai ba, ganin nayi Shiru se ya shafa kanshi yace 

“Ooops yadda kikai kyau dinnan ya zanyi fushi dake, amma Kinsan me? ” 

Kaina na girgiza a hankali, I’ve started liking the new thing 

“know that you have an admirer daga gefe, banyi tunanin zan fada miki da sauri har Haka ba amma I can’t do that. Actually Zainab Ina sonki” 

Wannan karan sosae na bude mishi manyan idanuna suka haske shi, Se ya lumshe idonshi sannan ya dubeni idanuna a kasa ina kokarin tafiya, da sauri ya kara shan gabana yace

“Ina zakije? ” 

“Gidan budurwarka” 

Tsira min idanu yayi yace 

“who’s that?” 

kaina na rausayar nace 

“Me letter” 

Dariya yayi sosae sannan yace 

“Anyi mata aure? Ayya kinga ke rabona ce” 

Dariya na danyi na cigaba da tafiya shima yana gefena muna tafe bawai magana muke ba don ni ina tuno kalamansa ne da suke saka gabana faduwa ina jin wani yanayi na daban a tattare Dani. Har kofar gidan Hamma mukaje sannan Yayi min sallama. 

Ina shiga na Tarar da Anty Fadila a parlor Tana mopping, Tana jin sallama Ta, ta sake mop din ta taho da sauri ta Rungume ni, Nima kyakyawa hug na bata cikeda farin ciki, seda na sake ta sannan na Fara dudduba jikinta Se ji nayi Hamma Mussadiq yace 

“Babu abinda na gutsira daga jikinta, Tana nan Kamar yadda kika kawota gidan nan” 

A take dukkanmu muka sake dariya ina rufe fuska sannan nace 

“Ayya Hammana, Kai Ko? ” 

Harara ta yayi yace 

“Fadila Munyi fushi Ko tunda se yau ta Nemo mu” 

Kai Anty Fadila ta gyada wadda ke ta Murmushi amma batace komai ba, ni ce nace 

“Kai ku kuwa, ba haka bane” 

Zama yayi ya maida hankalinshi Kan kallon da aka kunna, mu kuwa aiki muka cigaba dayi Har breakfast tare mukai, a can kitchen nake bata labarin yadda mukai ni da Aneeysa. Tsaki tayi tace 

“AI kin birgeni, Shegiya bushashiya kashi da rai kawai, ita tunaninta kowa sakarai ne irinta, Meye abin so a Mus’ab” 

Dariya na dinga yi sosae har seda na Fara tari sannan Anty Fadila tace 

“Ke rufamin asiri Kinsan condition dinki dai” 

Ruwa na Tara a sink cikin tumbler na kurba sannan nace

“Kece abin dariya Wai kashi da rai” 

Itama dariyar tayi sannan muka dakko abincin muka nufo parlour, suna ci ni kuwa Inata game cikin wayar Anty Fadila. Yinin ranar was awesome. 

Bayan kwanaki uku akai resuming makaranta new session, new term, new class. Na shiga SS1 Ina science class, Hamma ya kawo min sabuwar waya dalleliya, ranar nasha murna Har Rungume Hammana nayi Dan murna anan Mama ta fito tana fadin 

“Meye Haka, Mussadiq saketa mana” 

Da sauri na sakeshi Ina dariya sannan na nufeta ina nuna mata wayar, wani kallon banza tamini tace 

“Ja can, wadda bata girma, Kinje kina wani kakkama shi” 

Bakina na zunbura ina buga kafa na tafi gurin Baffa Ina nuna mishi wayar, karba Yayi yace 

“A’a Uwata waya tayi kyau se a kula banda abubuwan da basu dace ba” 

Kaina na gyada nace 

“Inshaaa Allah Baffa” 

Chaji na saka kafin lokacin islamiyya yayi naje na ciro wayar na saka a jakata nayiwa Mama sallama Se banka min harara take ni kuwa dariya nayi nace 

“Allah Ya barmin Mama ta” 

Daga Haka nayi Ficewa ta ina dariyar Mama da fushinta akan hugging dinmu. Ana tashi a islamiyya na jira Abdallah yazo Kamar kullum mukai hirar mu sannan na bashi wayar, yana ta jin dadi yasa digits dinsa sannan ya rakoni gida, ya Fara zama wani bangare na jikina, ko da yaushe zuciyata tunaninshi take, na yarda da din yarinta nayi ta bakin Najaatu Yanzun nasan Meye so kuma. 
Wayarshi da ko cirota daga Jakar system dinshi bai yi ba ce ta Fara ringing, idanunshi Ya bude Wanda tuntuni har sunyi jawur, it’s normal inhar zaiyi tunanin Lulu to Se jikinshi yayi matukar sanyi, most times idan ya Kalli hotonta na ranar da zaa saceta, her first birthday and that fateful day, ranar da bai taba Mantawa ba, bai taba shiga shock da ya shiga na wannan ranar ba, kukan da Har yau bai Kara yin irinshi ba, baya kuma tunanin Zaiyi irinshi. Indai zai kalleta yana kissima Yanzun da tayi shekaru sha biyar ko ya ta koma, yasan Baka ce amma Yaya wannan daradaran idanun irin Ma, ya pointed hancinta irin nashi? Wannan bakin zarazaran eyelashes din, da dogon gashi? Yasan duk inda take anata rubibunta, shidai adduarshi Allah Ya bayyana ta, yasa wannan dakon jiran da yake ita matarshi ce ba lokacin shi yake batawa ba.

Yana ciro wayar tana katsewa hakan yasa ya maida ya aje don he’s not calling back , Fainusa ce yarinyar ta nace mishi yadda baki bazai fada ba, Mamanta classmate din Ammishi ce, Ya rakata gidan suka samu Fainusan Tana Menstrual cramps, Ammiey tasa Yayi mata prescribing pills shi kenan Tasha ya tafi, da months Ya zagayo ta Nemo numbers dinshi akan ya kara fada mata shi kenan ta tsiri kiranshi, har lokacin bata fada mishi ko sonshi take ba amma dukkan Wasu signs sun bayyana dan tana tsoron yadda zai dauki Maganar shi yasa bata masa barobaro ba. 

Kara kiran da tayi yasa babu yadda Maina Zaiyi face Yayi picking call din idan ba Haka ba bazata hakura ba. 

“Doctor!”

Shi ne abinda ta Fara ambata yana dagawa, gyara zamanshi Yayi yace

“Hajiya Fainusa ya mutan gidan? “

Cikeda yanga, murya a can Kasa tace

“Duk muna lafiya, Ashe ka samu aiki a Kano amma ko ka fadamin Ko? “

Ta tambaya a shagwabe Kamar me shirin kuka, duk yadda yakai da kin yarinyar seda yaji wani mugun electric shocking jikinsa, wayace mishi Borno gabas take? Yana Cikakken Namiji yace don baya sonta He will feel normal? Ajiyar zuciya ya sauke yace 

“Fainusa aiki nake, muyi magana some other time”

Da sauri dan tasan kadan daga cikin aikinshi Ya katse wayar tace 

“Haba Doctor, Kasan me yasa na kiraka? Abba yace na fitar da miji ne fa “

Da sauri ya bude idanunshi a wahalce yace 

“Then, Meye nawa a ciki? Ki fitar da miji mana”

Muryar ta na rawa tace 

“Nace mishi Kai na…… “

“You must be very stupid amma! Ni a me? Na taba ce miki ina sonki? “

Cikin kuka Fainusa tace

“Baka fada ba amma ni ina sonka! “

A zafafe yace

“Who cares?….. “

Kawai se ya katse wayar saboda tsabar bacin rai, take Ya fara neman layin Ammiey wadda tana gidan Ma a lokacin, seda ta kalli Hafsa sannan tace 

“Danki ke kira”

Harara ta wurga mata tace

“Malama ki samu damar daukar wayar”

Dariya Salima tayi sannan ta Kara wayar a kunnenta

“Ammiey Ki rabani da wannan yarinyar”

Cikin rashin fahimta tace 

“Wacce yarinya Likita? “

“That useless Fainusa mana, ta cewa Babanta wai ni take so, ni kinga Ko wayarta se ta kira sau biyar ban dauka ba, amma tace ni zata aura

“Maina take it easy, duk abin ba na Haka bane, waye ya fada maka? “

Zuwa lokacin muryarshi ta sauka hakan nada nasaba da Maganar Ammishi da yayi.

“Ammiey kirana tayi ta fada min, Ki Kira gidansu ki fada musu sannan ki ja mata warning”

Salima Shiru tayi ta kasa furta komai, ita Batayi tunanin hakan ba, hakan yasa kawai ta mikawa Hafsa wayar wadda ta zuba mata idanu tana jiran Karin bayani, 

“Son ya akai? “

Shi ne abinda Hafsa ta Fara furtawa Tana karbar wayar, cikin sanyin murya ya gaisheta sannan Yayi mata bayanin komai, Idanunta ta Dan runtse tana tunanin Anya kuwa basu cutar yaron nan sun zuba mishi ido yana jiran gawon shanu, jiran abinda Baa da tabbacin zata dawo, ta mutu Ko ta mayi aure, a hannun wa take? Allah kadai yasan amsar 

“Son, babu Wanda yasan ina Lulu take, babu Wanda Ya sani se Allah badai mutum ba. Ina ganin Kamar wannan jiran da kakeyi tamkar kana zaman jiran gawon shanu ne, Allah shi yasan daidai amma ni Kaina wannan zaman naka babu mata at this age Ya fara damuna, you need to settle, kana bukatar kayi aure Man, ka gane”

Wani gumi ya sharce jikinshi gaba daya Ya mutu, Ya rasa Yaya Maganar Ma take nufi ne, yayi aure ya hakura da Lulu ko me? Ranshi a jagule yace 

“Ma Baki yadda Dani bane? “

Da sauri Hafsa ta girgiza Kai tace

“Not at all Son, na yadda da kai saboda nasan tarbiyar ka, jiki da jini, yau da gobe ita ce rayuwa ka gane, give her a chance ai nasan Fainusa na yadda da tarbiyarta Maina, kayi tunani”

Bata jira abinda zai fada ba ta kashe wayar, da sauri Salima tace

“Ya zaki fada mishi haka? “

Idanunta ta bude tayi Murmushi me ciwo tace 

“In-law baki ganin Kamar muna yaudarar kanmu da tunanin watarana Lulu zata dawo garemu? “

Girgiza Kai Salima tayi tace 

“Ashe rahamar ubangiji me yankewa ce, jikina yana bani Lulu is some where and she’ll definitely return to us. In-law mu cigaba da addua, as for Maina Ina bayan Ya cigaba da jiran isowar ZAINAB, saboda duk wadda Maina Ya aura to zaluntar ta Zaiyi tunda babu so balle kauna! “

Cikin lokaci da bai cika watanni uku ba mukai wata irin shakuwa tsakanina da Abdallah, kullum se mun hadu dashi dukda sun tashi a anguwar mu amma Haka yake sammako yazo se ya wuce school kuma, da safe da yake wani junction nake zuwa nabi school bus zuwa school, to kusan Ina fitowa yana jirana muyi trekking tare, kullum tafiyar cikin farin ciki da annashuwa muke muna planning yadda rayuwar mu zata kasance, yadda muke tare dashi babu abinda na ke hangowa Kamar Munyi aure ni dashi. Shima kuma hakan take Dan bai taba missing fada min yadda yake sona ba, Tun Ina nokewa Ina jin kuka Har na ware na Fara maida martani, some times ma na fishi zakewa. Haka idan na dawo to tare zamu tako Har gida, sannan idan weekends ne to Har makaranta zai raka ni sannan mu dawo tare. Abin mamakin koda wasa ban taba Haduwa da wani ba, babu Wanda Ya taba ganinmu. 

A kwana a tashi babu wuya wajen ubangiji, na shiga SS2, ranar wata Thursday ina kitchen da yake Baffa da Mama dukkansu suna routine Monday and Thursday fasting , ina kitchen ina hada musu abin shan ruwa. Doll man nake son yi musu saboda Mama tayi min complain Tana constipation( kasa yin bayan gida). Shikafa na Fara parboiling, na aje ta a gefe, fridge na dakko Minced meat na hada da parboiled rice din, nayi seasoning sosae sannan na rufe. Wani fresh cabbage na dakko, cikin nutsuwa na dinga bare shi ina sawa cikin tukunya wadda already na zuba mata ruwa, seda na bare Wanda zai isheni sannan na rufe na daura a gas. Irish na Fere a guda guda nayi parboiling, na samu fresh tomatoes da garlic nayi blending shima na daura a wuta nasa Mai ya zama Kamar sauce, da yayi yadda nake so se na dakko Irish dina na jefa a ciki. Wannan cabbage din already yayi laushi saboda tafasar da yayi, shinkafar na dinga zubawa Ina nadewa ina sawa cikin sauce, na dakko fresh sweet pepper da ball pepper na cire hancin da yayan ciki na cika taf da shinkafar suma nasa cikin tomato sauce din na rufe don a samu penetration na komai. Ina kammalawa nayi kunu da juice saboda indai girkina mun hori a hannun Mama, Tun shekaru shida take samu grinding, bare, juya, zuba, wanke. Haka dai abubuwa shiyasa na tashi da son abin a raina. Ina gamawa na zuzzuba a inda ya dace sannan na koma daki inda na samu Missed calls din Abdallah kusan bakwai, wani irin muguwar faduwar gaba ta kama ni saboda tunanin abinda zaisa yayi min 7 missed calls. Jikina na rawa nayi returning masa call din, bugu daya Ya dauka yana fadin

“Haba my life, ina kika shiga haka. Inata kiranki” 

Ajiyar zuciya na sauke jin he sounds normal and good kawai ya Kira Dan Ya tsoratar Dani ne, bata rai nayi tamkar yana ganina nace 

“Dama lafiyar ka kalau ka kirani sau bakwai ka tayar min da hankali” 

Murmushi yayi Har seda naji sautinshi a kunnena yace 

“I badly wanted to hear your voice, shi ne kawai” 

Murmushi nayi nace 

“God, you scared every part of my being wallahi” 

Dariya yayi wadda jinta kawai ke tsuma zuciya da gangar jikina, Abdallah is surely the death of me saboda ina mishi so me zafin zafi, kowanne bangare na jikina yana begenshi. Daga nan muka cigaba da hirar mu Har aka Kira Sallar Maghrib shi ne mukai sallama Se dare kuma a daura, haka yake routine a rayuwarmu. Amma duk wannan shakuwar tamu bata hanamu fada, idan muka tashi fada Se kuyi tunanin bamu taba shiri ba, kuma fadan on the silliest thing. Kamar ranarj Ya kirani da weekend da daddare nayi bala’in gajiya saboda naje gidan Anty Fadila wadda ciki yake bata wahala, komai ni nayi a gidan Se bayan Sallar ishai Hamma Mustapha yazo muka tafi. Ina shiga gida Ko parlor ban zauna ba nayiwa Mama seda safe na wuce dakina nayi wanka sannan na kwanta, cikin kamkanin lokaci kuwa bacci ya daukeni, har baccin Yayi nauyin da duk kiran da Abdallah yayi min Banji ba, seda asuba na bi call din yaki picking, banmasan kin picking Yayi ba, tunanina may be yaje massallaci Ashe shi fushi yake. Wasawasa seda mukai kwana uku bai kira ba, ban kira ba. Iya jigita Munyi donni har seda Mama ta tambayeni ko akwai abinda ke damuna nace mata babu komai, amma Hatta yadda nake activities dina duk na rage, na zama very moody Hakanan. Se a Rana na hudu na dauki wayata don na kirashi amma Ego da pride suka hanani, zuciyata tana nuna min abinda take so ne fa kada nayi kuskuren katse call din, Haka mind dina ke fadamin shi ne marar gaskiya, tunda ni na kira karshe amma baiyi calling back ba, wannan battle din yasa na jefar da wayar tareda dafe Kaina, inajin wani irin abu yana taso min daga zuciyata zuwa wuyana. Nasan is nothing but missing, nasan Yau na kai limit din da idan Banji muryar Abdallah ba akwai damuwa ta gaske kuwa, amma ego da pride Ya hanani. Har dare ina kwance sukuku duk inda na samu na kwanta Kamar ruwa. Can wajen isha naji Abu tamkar ya tokare min makoshina, cikin sauri na mike don Nemo inhaler ta amma na tuna ta Kare jiya kuma ba Wanda na fadawa, take kuwa ta tashi Inata fuzgar numfashin Har na fito parlor, a gigice Mama ta yo Kaina Tana fadin 

“Yanzun nake tunanin zaman me kike a daki Tun safe Ashe bakida lafiya! “

Hamma Mus’ab yana zaune, Ya kalleni lokacinda na fito amma daga Haka ya cigaba da pressing phone dinsa as if baisan meke faruwa ba, Mama cikeda damuwa ta dubeshi ganin Har idanuna suna lumshewa, numfashin da kyar nake fuzgar shi tace

“Mus’ab Anya Kai kuwa kana da imanin musulinci? Kana kallon yar uwarka amma babu alamar zaka taimaka? “

A zuciyarshi yace 

“Yar Uwa kuma? Ina Laifin yar tsintuwa”

Hawaye na zuba idanuna, se lokacin ya mike tareda daukar key daidai shigowar Hamma Musbahu, hannunsa rikeda na Nusaiba se matarshi Adda Asiya na bayanshi da tsohon ciki Se hannun Nabila da ta riko, a rude suka yo kanmu Dan basu taba ganin nayi ba tunda ba a gari suke ba balle ace sun taba gani, Mama dai ta sanar dashi akan idan akwai Traditional herbs Ya kawomin, to wannan ne yasa ya samu. 

Juyawa Yayi yayinda Mama ta zura hijabinta da tayi sallah dashi, dama ni nawa yana jikina da Haka muka wuce asibiti, kafin muje dukkan wahala na wahala se Sannu suke zuba min Nikam ni kadai nasan abinda nakeji, kafin muje har numfashina Ya dauke kawai farkawa nayi naga ansamin Abu Kamar oxygen da wani hayaki yana fitowa ina Shaka Har ta lafa. Allurai akamin sannan sukai discharging dina Har na rame. Rules din na kullum aka kara nanatawa Wanda na haddace, most mutane suna ganin having asthmatic attack Kamar sakaci ne amma akwai abubuwan da dole ne su faru they’re inevitable!

Kamar Abdallah yasan abinda ya faru da daddare ya kirani Har na kwanta Amma banyi bacci ba, AI ranar har haki na dinga yi saboda masifa, karshe muka shirya muka kara dinkewa. To Haka fadanmu yake silly thing to a big fight, amma na yadda da wani abu a soyayya, matsawar zaa dinga fada to Kamar kuna Kara understanding Kanku ne kuma kuna Kara kusantar juna.

Ranar ta kama jumaa, jumaatu babbar rana, ta bawa ranar samu kamar yadda taken ranar yake. Na gama shan plain Tea, na shiga daki na karasa shiryawa sannan na fito na wuce dakin Baffa, yana tsaye da alamun da wurwuri zai fita, Tsugunnawa nayi na gaisheshi cikin fullanci, shima ya amsa min sannan yace

“Muje na kaiki tunda na shirya”

Har raina naji babu dadi saboda zamu hadu da Abdallah amma wace ni na Musa, haka jikina a sanyaye na bishi muka fito Mama na bayanmu Har Mota ta rakamu, sannan ne tace 

“Zaki je gidan Fadilan? “

Kaina na gyada mata ban furta komai ba saboda bacin rai. Muna tafiya Baffa yana fadin 

“Uwata saura kiris Ki gama secondary Ko?”

Wannan yasa nayi Murmushi nace

“Eh Baffa, baifi 9 months ba”

Kanshi Ya gyada yace 

“Nace miki aure zanyi miki Ko? “

Da sauri na kalleshi bakina yana rawa nace 

“Baffa karatun fa?”

Dan Murmushi yayi sannan yace

“Ko a gidan mijinki zakiyi shi Hikma, wannan burina ne yata mace tana gama secondary zanyi mata aure, bakiga yadda nayiwa Fadila ba?”

Hawaye idanuna suka cicciko, a hankali na cije Dan bansan na zama second victim shekaru biyu da auren su Hamma Mussadiq, gashi ita bata Fara Karatu ba ita bata haihu ba, se ciki da take samu on and off, kuma ya azabtar da ita amma ko 3 months bai rufawa zakiga cikin ya zube, abin Har abin tausayi. Sati biyu da sukaje asibitin Malam Aminu Kano aka daura ta akan ta Dan huta na dan lokaci, da zarar taji alamun tayi conceiving se ta taho asibiti. To shikenan ni nayi aure kuma Nazo at a very tender age na haihu, Kai duk ba wannan ba tsorona rasa Abdallah Dan nasan bazaayi mishi aure Yanzun ba don ko first degree bai hada ba, balle a fara neman aiki Wanda Ya zama Tashin hankali tunda karatun yi akeyi amma kwatakwata gwamnati ta bar millions of graduate unemployed, kuma kullum thousands of student are graduating without future.

“Ya akai Uwata, akwai lokaci Kinji? “

Kaina kawai na gyada ina share hawayen idanuna, dama yadda muka tsara nida shi, idan na gama secondary nayi joining college ko Uni, kafinnan shi kuma yayi settling to wannan Maganar ko ya zaayi da ita? 

Tunda na shiga class nake kuka, kukan da ban taba irinshi ba a duniyata a wannan lokacin, ina hango Tashin hankali me girma dake tunkaro mu, Abdallah a level 3 yake, kuma 5 years course yake, service na jiranshi, fafutukar aiki da komai. Kafin a tashi zazzabi me zafi Ya rufeni, hakan yasa straight kawai na wuce gida ban ma tafi gidan Hamma ba Kamar yadda nayi niyya. Naje na samu Mama bata nan ta tafi Unguwa, Haka na kara fitowa na koma gidan Hamma, lokacin zazzabin ya danyi sauki amma fuskata ta kumbura especially idanuna. 

Anty Fadila kadai na samu, ta tareni duk a rude musamman da tasan abu Babba yake sani kuka, haka ta dakko min magani da pepper soup na kifi, bana kincin Abinci idan Ina jinya, kome aka bani ci nake, na cinye sannan nasha nagani na kwanta zuwa laasar nai garau, nayi wanka nayi sallah sannan na fito na sameta Tana waya, tana gamawa ta dubeni tareda zama gefena tace 

“Tell me autar Mama, me ya faru? “

Ai se idona suka saki hawaye, hannuna ta kama tace 

“Menene? Me ya faru? “

Dauke Kaina nayi nace

“Kinsan yadda kika rasa Abdallah Nima rasa shi zanyi”

Na fada Ina sheshekar kuka, Shiru tayi Dan tuntuni tasan tsakanina da Abdallah, most of the time a gidanta muke hira idan mijinta baya nan, kullum ita ke karfafa mana gwiwa, Wasu lokutan musha dariyar haukan da tayi na sonshi wanda zallar kuruciya ce kawai. 

Wajen Karfe biyar Abdallah ya kirani yana kofar gida, da sauri na shiga daki na saka khol a idona Dan Ya boye kodewar da yayi, hijabi na saka na fita. Yana zaune akan machine dinsa yayi kyau Kamar kullum, yana ganina ya duro daga Kai ya taho yana sakar min Murmushi Wanda Ya wargaza duk intention dina na fada masa wani Maganar. Yadda muke kallon kallo zaka rantse that was the first time muka taba haduwa dashi, kullum haka abin yake indai zamu hadu dashi. Ni na Fara dauke idanuna nace

“Yau baka da lectures? “

Harara ta yayi yace 

“Ko Inada lectures dole nayi skipping nazo Naga wannan dazzling eyes din. It looks like Kamar Kinyi kuka kuma”

Ya fada yana Kara kura min ido, da sauri na dauke kaina saboda nasan halinshi tsaf zai iya ganewa, wasa na dinga yi da fingers dina sannan nace 

“Babu komai, Dan zazzabi ne nayi a class”

Se ya shagwabe fuska yana fadin 

“Shiyasa naji nawa temperature yana running”

Wata sassanyar dariya na saki ta jin dadi, wannan caring din shi ke kasheni, shi ke sani ina jin babu wata budurwa da tayi saa kamata. Muna ta hira Dan gaba dayanmu gwanayen surutu ne daga ni Har shi, har Banji isowar Hamma Mussadiq ba se kawai kamshin turarenshi Yayi min sallama , wani irin juyowa nayi seda gabana Yayi mugun faduwa, idanuna a waje bakina na rawa nace

“Ha.. M…. Hamma! “

Baice dani uffan se ba se hannunshi da ya nuna min alamar na shiga ciki, Ko takan Abdallah ban bi ba, na wuce Abuna guje Har ina tuntube!!! 
Ban Kai ga karasawa ba naji sallamar Hamma Mussadiq, seda cikina ya kada, nayi sauri zan bar parlon naji yace

“Kina Matsawa daga inda kike, se na tattakaki, useless girl kawai”

Mama ce ta kalleni ta kalleshi sannan tace 

“Meye Haka?”

“Mama yarinyar nan Ashe yar iska ce, maza take tarawa bamu sani ba”

Mama ai se ta mike, ni kuwa banda kuka babu abinda nakeyi, inason magana amma Hamma Mussadiq yace ko bakina na bude se ya mareni 

“Wanne irin Tara maza babu dadin ji? Ke Hikma me hammanki yake fada? “

Idanuna na hawaye nace

“Wallahi Mama, mutum daya ne kuma Anty Fadila ta sani. Allah Mama”

Kamar wani zaki ya yo Kaina zai jibga, a guje nayi bayan Mama na kankameta, se sallamar Baffa Wanda Ya jima a tsaye amma bamu lura dashi ba. Karasa shigowa yayi yace 

“An Kira sallah”

Wannan Yayi saving dina, daki na koma nayi sallah amma na kasa fitowa har akai Sallar ishai, se na Fara gyaran wardrobe, Inayi ina tunanin Dan kawai an ganni da saurayi shi ne wannan commotion din, saurayi kawai? To idan banyi saurayi ba ta Yaya zaayi min auren da ake fadar zaayi min. 

“Kizo inji Baffanki”

Haka kawai Mama ta fada min ta fita. Lace din da nake ninkewa na yar tareda daura hannuna a kai sabon hawaye na kokarin zuba daga idanuna. Na kusan Minti biyar sannan Kamar munafuka nayi waje, suna zaune Hamma Mussadiq, Mama da Baffa. Gefen kafar Mama naje na takure nace

“Baffa gani”

Ya jima yana kallona sannan yace

“Zainab waye kuke waya dashi? Waye kika kai gidan Hammanki?”

Idanuna na lumshe sannan na bude tareda kallon inda Hamma yake, wata harara da ya banka min yasa nayi saurin dauke idanuna nace

“Sunan shi Abdallah Baffa”

Kanshi Ya gyada yace 

“Kice ina son ganinshi, tashi kije”

Mikewa nayi a sanyaye na koma daki, seda suka tabbatar na kulle dakin Sannunku Baffa ya dubi Hamma Mussadiq yace

“Kasan Mussadiq na fada maka ban raini Zainab a hannuna Dan na aurawa da na ba, is not my motive. Koda Zainab zata shekara talatin babu aure to daya daga cikinku bazai aureta ba, saboda nayi alkawarin Bazan taba yin abinda Hikma zata san cewar mu ba iyayenta bane, zanfi kowa farin cikin Hikma ta cigaba da zama damu amma Bazan iya hakan ba. Kai da kunya kace kana sonta bayan Kasan tsakanin ta da matarka. Ana barin halak Dan kunya. “

Seda yayi Shiru sannan Mama tace

“Mussadiq bana son ka raba zumuncin da Allah Ya hada, banson Haka. Baka San irin kyautar da Allah Yayi maka ba, da ya baka Fadila? Baka gode ba? “

Da sauri ya girgiza kanshi yace

“Haba Mama me yasa kuke haramta halal ne? “

Baffa ko saurareshi baiyi ba ya wucewarshi daki, ni kuwa ranar na kasa tantance me yake faruwa dani, farin cikin Ance Abdallah yazo ko kuma fargabar yadda abubuwa zasu kasance nake. Shiru nayi Inata tunanin, na kulla wancam na kince wancan har bacci ya daukeni. 

Misalan goma na safe Abdallah ya kirani ya sanar Dani yana kofar gida, Kamar munafuka haka na tafi dakin Mama na fada mata, cemin tayi na shigo dashi zata fadawa Baffa. Na fita se gamu tare, Yasha manyan Kanya shi da abokinshi amma dukda manyan kayan kana iya hango tsabar yarintar shi. Ban wani bata lokaci wajen gaishesu ba na kaisu gurin Baffa sannan na koma daki.

“Kaine Abdallah?”

Kanshi Ya gyada yace 

“Ni ne Baffa “

Shiru Baffa yayi, jikinshi a sanyaye Dan baya hango yiwuwar hakan kasancewar Ko Baa fada ba yasan Mahaifin Abdallah bazai yi mishi aure ba. 

“Inason ka turon mahaifinka muyi magana dashi, kaje kayi musu bayani duk yadda ake ciki ina jiranka”

Tashin hankali Haka Abdallah ya ayyana a ranshi, nufar Baba da wannan zancen ai…. Shi bazai fara ba ma. Ko lemu da Mama ta basu basu sha ba balle Abinci, suka tattara suka tafi. Bayan awa Daya na kirashi nace

“Ya kukai da Baffa”

Wata dariya ya saki ta shakiyanci yace

“Wai cewa Yayi na turo Abba suyi magana”

A hankali na saki Ajiyar zuciya dukda naji haushin dariyar amma ba lokacin fushi bane Yanzun, 

“ka fada masa kenan?”

Wata dariyar ya kara saki kafin yace

“Ashe ni mahaukaci ne, ta Yaya Hikma zan doshi Abba da zancen aure Yanzun, se yayi tunanin Ina shan weed ne”

Zuwa lokacin raina Ya fara baci hakan yasa nace

“Abdallah will you please explain abinda Kake nifi”

A hasale yace

“Na hakura!!! “

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *