HIKIMA
CHAPTER 9
A wannan lokacin ji nayi kamar na kashe Kaina saboda wani irin bakin ciki da ya turnuke min zuciyata, da ace an barni na kadaice wallahi ko ban kashe Kaina ba se nayi attempting suicide. Gaba daya rayuwar baya Hamma Mus’ab yayi ta ne akan cutar dani amma wannan abin da yayi min shi ya wanke dukkan laifufukansa.
Baffa dasu Hamma Sunyi iya bakin kokarinsu ganin sun bani baki, jinsu kawai nakeyi Dan jikina na fada min bayin kan Abdallah bane, no way Abdallah yana hayyacinsa zai ce bazai aureni ba, wannan Maganar hankalina bazai dauka ba. Naso ace da Abdallah yace ya Fasa Baffa baimin auren dole ba Naso ace kyaleni yayi na samu wani amma tunanin yadda zanyi coping da zama da Wanda bana so shike kara sani kuka.
Kowa ya tafi ya rage daga ni se Nanah se Aneeysa wadda mijinta ya dawo da ita se kuma Najaatu. Tun tuni na cire kayan ina zaune kan sallaya na idar da Sallar ishai, kaina cikin cinyoyina ni ba kuka nake ba amma gwara ace kukan nake. Gashi a lokacin nasan tuni BP na ya hau sboda dukkan Wasu signs sun bayyana. Wayata dake hannun Nanah ce ta Fara ringing,
_Nothing is gonna change my love for you, you ought to know by now how much I love you, one thing ……._
Ko bata miko min ba nasan Abdallah ne kadai yakeda wannan ringtone a cikin contact dina. Katse kiran Nanah tayi hakan yasa na dago da sauri, dukkansu kallona suke nace cikin dasashiyar murya
“Nanah, Ya kika katse?”
“Me zai ce miki kuma, bakuda alakar da ta rage”
Kaina na girgiza hawaye na sauka a hankali nace
“We have Nanah, baimin bayani ba, bansan dalilinshi ba. Nima kukan nan da nakeyi ba so nakeyi ba, na gaji dashi…..”
Ban karasa ba naji Ya sake kira, cikin sauri na karba nayi swiping tareda amsawa
” _Farin cikina_ Ban cika alkawarin da na dauka miki ba, I failed you, I didn’t fulfilled promises din da nayi miki. Da nasan Haka zamu kare da ban kulaki ba, da banyi breaking miki zuciyarki ba, duk yadda bansan ganin kukanki amma Ni ne sanadin kukan….. ”
Tuni na fashe da wani irin kuka, zuciyata gaba daya ta narke, bai hanani ba seda nayi me isata sannan nace
“Just tell, from the start dama abinda Kake nufi Dani? Dama duk alkawarrikan daka dauka ba Har zuciya suke ba? Abdallah why will you do this, why will you?….. ”
Ban karasa ba wani kukan ya Kara kubce min, nayi kuka sosae shima bai hanani ba, seda nayi me isata kafin yace min
“Kiyi hakuri Hikmah, nasan a gurinki I’m a monster, nasan na cancanci dukkan Wasu sunaye da zaki kirani dashi, amma abu daya nake so dake Dan Allah ki saurareni”
“Bayan mun gama waya, nace miki na dawo daga massallaci. Straight hotel din da muka sauka da Abbu nan mukaje, tuntuni shi ya shirya nima dakina na shiga na shirya. Abinda zan tuna Abbu yace min muje kada mu makara, daga nan na yanke jiki na fadi, Nidai consciousness dina bai dawo ba seda akai Sallar Maghrib daf da ishai. A gigice na mike ganin duhu Ya shiga, na kalla mutanen gurin, Abbu, Ummiey, kannen Abbu biyu da kannen Ummiey, Idanunta Sunyi jawur alamar Tasha kuka, hannunta na kama ina kuka nace, Ummiey An daura auren? Na aura hikman? Gaba daya Shiru sukai suna kallona se Abbu ne ya cemin, Abdallah cewa kayi Baka sonta ka fasa aurenta, cewa kayi daka aureta gwara ka mutu, I wanted to force you aurenta amma yadda kayi baimin dadi ba, Abdallah haka na kira mahaifinta nace a aura mata wani, a take kuwa Yayi mata miji, ka dauka haka Allah Ya tsara maka. Hikmah kuka kawai nake Dan nasan I was possessed, bayin kaina bane…… ”
Gaba daya seda tsikar jikina ta tashi saboda yadda yake kuka, Nima Haka na shiga yin nawa bazance asiri bane kai tsaye amma abin da mugun mamaki, all of a sudden.
“Ki yafe min, ki sani ina sonki Bazan taba Mantawa dake ba. Ashe we’re not meant to be, dama wani baya aurar matar wani. Inasonki Ina kaunar ki Hikmah, Naso aurenki na rayu dake amma Allah bai nufa ba, ke matar wani ce. ”
Munjima muna hira dukda inner self dina na fadamin babu kyau hakan amma naji hankalina ya kwanta sosae, at least naji sanyi saboda nasan ba yin kanshi bane, na yadda dashi Haka nan naji hankalina ya kwanta. Seda na daina kuka Har ina Murmushi sannan Yayi min adduoi tareda fatan alkhairi, Naso sosae na Tambayeshi Mupheeyda amma nasan ba hurumina bane.
Ina aje wayar naji wata irin nutsuwa da dangana Ya shiga zuciyata ban taba tunanin hankalina zai kwanta ba Kamar haka. Mikewa nayi daidai shigowar Hamma Mus’ab, Da murnarshi yace
“Hikmah, Alhamdulillah! ”
Dan Murmushi nayi ya miko min Leda hannunshi yace
“Zauna kici”
Komawa nayi na zauna dukda banida appetite amma Haka na bude ledar, shawarma ce da yoghurt, kallonshi nayi Ina Murmushi na tuna Marin da nasha akan wannan abin. Kaina na girgiza Ina tuna rayuwa, Surely no condition is permanent in life! Seda naci sannan nace
“Hamma waye aka aura min? ”
Zamanshi ya gyara yace
“Bansanshi ba amma nasan yanada nasaba me kyau, sunanshi Ibrahim, Likita ne. Asalinsu Yan maiduguri ne. Shine kawai abinda na sani game dashi. Kinyi saa shi ne abinda kawai zance miki, Inshaaa Allah bazakiyi regretting ba. ”
Lumshe idona nayi bance komai ba, se can yace
“Jiya Bakiyi bacci ba, kije Ki kwanta ko. ”
Kaina na gyada na mike nace
“Hamma thank you for everything”
Kanshi Ya gyada yana min Murmushi na wuce dakin da aka bani, Nanah tuni tayi bacci Nima alwala nayi na kwanta gefenta, tunanin kullum ne a raina ko waye mijin? Ko ya kamarshi take, a Haka bacci yayi gaba Dani. Mafarkin Abdallah Munyi reuniting shi ne komai.
Washegari shi ne birthday Dina, nayi bacci bayan Sallar asuba bani na tashi ba se goma shima saboda Nanah zata tafi ne, Har mamakin yadda na dangana nake babu attack balle BP rise. Seda muka kaita har Tasha sannan na dawo nayi wanka, doguwar riga Aneeysa ta bani na saka, muna parlour dukkanmu muna hira, ga cake Hamma ya siyomin, yana aje ko yankawa banyi ba se wayata dake hannuna Inata replying messages na jaje da fatan alkhairi hade da birthday wishes.
Twitter na shiga ina dudduba abubuwa kawai naga tweet din IBmaina, ciki sauri na bude hoto ne amma yana loading bakai ga budewa ba, a caption yasa *Today marks 21 years, since you were kidnapped, we love you so much and we missed you, I….. ”
Ban gama karantawa ba picture Ya bude, gabana yanata faduwa na bude picture, bansan lokacinda na zabura na mike ba, Inata kallon hoton, ni ce wallahi babu tantama ni ce, so CBN governor is my father, lumshe idona nayi, dukkansu basu kula dani ba seda na fito rikeda veil, sannan Hamma yace
“Hikmah ina zakije? ”
Gyara yanayina nayi nace
“Yanzun zan dawo, gurin Mama zanje”
Ban jira abinda zasuce ba nayi gaba, Inata wulla kafa Kamar zan hantsila, kwanya ta ta cushe. Ina zuwa Naga Baffa yana nan I’m sure suna tare, hakan yasa na lallaba na shiga dakinta, trolley nan da Naga kayan nan da hand tag tana nan saman wardrobe, Hawa kan gado nayi na sakko da ita, kayan ne kawai a ciki snapping nayi daya bayan daya sannan na rufe na mayar na fita babu Wanda yasan da shigowata. Gidan Najaatu na wuce na shiga dakinta na Fara mawa IBmaina DM da pictures din a kasa nace
_I might be the missing baby!”
Ina turawa da wannan caption din na aje wayar tareda kwanciya na runtse idona, addua nake Allah yasa yayi responding sharp sharp. Amma nafi mintina goma a zaune babu reply kuma twitter shi ne kadai access dina dashi. Cikin sauri na mike na koma gidan saboda bana son kowa Yayi tunanin wani abu, amma tabbas inajina banfi an inch away from them ba. Ina zuwa gidan Hamma Mus’ab, na samesu yadda na barsu, zama nayi Aneeysa tace
“Har Kinje, na zata bazaki dawo ba”
Kaina na girgiza nace
“Banje ba, gidan Hamma Mustapha na leka. Haba dai”
Cake din na yanka na cira slice daya nasa a plate hade da fork, Sauran fridge na mayar na wuce daki, favorite dina ne chocolate cake with Italian frosting and strawberry topping. Duk yadda nake son shi baifi sau biyu naci ba kawai na ture plate din tareda neman wayata na koma tweeter amma still babu reply. Kifar da wayar nayi na kulle Idanu na inajin wani zafi a raina. A cikin mintina goma na duba notifications dina yafi sau ashirin, waiting really sucks.
Aneeysa ce tayi saving dina daga zaman da nake tace min Aiman yana parlour yana jirana. Allah Sarki Hammana, na ayyana hakan a raina. Cikin sauri na sakko a gadon na dauki hijab sannan na sameshi shi da Hamma Mus’ab zaune suna hira. Gefe daya na samu na zauna ina gaisheshi, Hamma Mus’ab ya mike ya fita dukda Hamma Aiman yace yayi zamanshi amma yasan tabbas we need privacy.
“Naji dadi sosae da naga condition dinki yayi improving, Dama inata adduar Allah yasa kada hakan yasa ki samu matsala. “
Kaina na gyada nace
“Nima I’m happy da hakan, amma ka gani komai a rayuwar Dan Adam Allah Ya ke yinshi, naji idan nayi kukan Kamar ban yadda da hukuncin Allah ba. And Abdallah explained everything”
Kanshi Ya gyada yace
“Yeah, Ya kirani jiya. Abin sede addua Dan itama Mupheeydar bai aureta ba…. “
Idanuna na zaro nace
“Kai Hamma”
“Wallahi Hikmah, Kinsan Friday naki, Saturday nata, da mamanshi taga abinda ya faru a aurenki tace indai ita ta haifeshi he’ll not marry that bitch, coincidentally akwai Naeeyla yayar budurwata Afaf, Tana sonshi kuma cousins suke da Babansu Afaf da mamanshi, so madadin auren Mupheeyda se aka aura mishi ita. “
A hankali hawaye ya saukar min kuncina, am so happy for Abdallah da bai auri wannan daughter of a bitch dinnan ba.
“Allah Sarki Abdallah, dama Haka rayuwar take, since from the beginning we are not meant to be. Hamma Aiman I think na samu iyayena”
Da sauri ya kalleni yace
“How comes? A Ina? Su waye? “
Murmushi nayi nace
“Relax! Kasan CBN Governor?
Shiru yayi yace
“Aminu Bukar Maina Ko?”
Kaina na girgiza nace
“I dunno his full name, ina tunanin shi ne Mahaifina”
Shiru yayi tamkar me son tuna abu, kafin can ya ciro wayarsa yana Kira, da sauri na karba wayar na kashe nace
“A’a, Hamma baayi confirming ba fa kada ka daga maganar”
Ajewa yayi yace
“Amma Hikma ta Ina tunanin Anya ba familynsu akai miki aure ba. Wait angon Ya kiraki? “
Kaina na girgiza nace
“Ko daya, bai kira ba”
Kanshi Ya gyada yace
STORY CONTINUES BELOW
“Shi ne waliyin Ango, so ina tunanin cousin dinki kika aura”
For the first time naji hankalina ya kwanta akan auren, naji as far as Dan uwana ne zanyi hakuri na zauna dashi.
A hankali Hafsa dake zaune hannunta rikeda wayarta tana order kayan lefen Maina, shima yana zaune suna dan hira, Tana kara kwantar masa da hankali. Can Sega Pop din message din Afaf ta Whatsapp, Murmushi Hafsa tayi tayi minimizing Dan duba sakon Afaf, hotuna ta turo mata wajen guda goma, cikin sauri Hafsa ta Fara budawa haka kurum taji gabanta yana wani irin bugawa, network Kamar yasan she’s eager yaki budewa, seda ta shafa fin mintina biyar duk Maganar da Maina ke mata bata ji ba, gaba daya hankalinta yana kan pictures din da suke bata tough time ne, da sauri tace
“Maina bude min hot-spot da wayarka “
Bai Ko ce komai ba ya bude mata, tamkar yana jira hotunan sukai downloading gaba daya at a time, a hankali Hafsa tasa hannunta ta bude na farko, Hikmah ce, idanu ta tsira mata gaba daya tsikar jikinta ta Mike, ta bude wani a Haka seda ta kai karshe sannan tayi Shiru gabanta na faduwa ga wani abu Kamar zazzabi dake neman rufeta lokaci daya, cikin sauri ta dauki wayar bata jira komai ba ta danna kiran Afaf, Dama Tana zaune jiran wayar take, hakan yasa Hafsa na kira Afaf ta dauka tace
“Ma kinga hotunan Ko? Wallahi ban taba ganin two people in this world that looks alike kamar ke da ita ba”
A hankali Hafsa tace
“A ina kika Santa? Ya sunanta “
“Sunanta Zainab amma HIKMAH ake ce mata, kin tuna Aiman dina, to cousin dinta ne. “
Lumshe ido Hafsa tayi tace
“I’ll call you back”
Daga Haka ta katse kiran ta Mike, ko kadan ta manta abinda take balle wani Maina Wanda hankalinshi baya parlon balle yasan halin da Uwar tashi take ciki ba. Straight parlon Alhaji Bukar tayi, tamkar an jefata Haka ta shiga hakan yasa yace
“Hafsa lafiya”
Bata amsa shi ba se zama da tayi tace
“Abba is like Lulu tanada rai”
Glasses din idanunshi ya zare yace 1
“Hafsa sure? A Ina? “
Se kuka ya kwace mata, wayarta ta Mika masa a hankali ya dinga bin hotunan da kallo yana fadin
“Sure Hafsa wannan jininmu ce, wannan Zainab ce”
Kafin tayi magana Aminu Ya kira hakan yasa Abba Mika mata wayar yace
“Ki nutsu”
“Hello! “
Ta fada tana kara wayar a kunnenta
“Anga Lulu tana kano”
Mikewa Hafsa tayi jikinta na kyarma tace
“Yaushe? “
“Hafsa be calm, ki zauna na shigo maiduguri Yanzu zan karaso gidan”
Komawa Hafsa tayi ta zauna tareda toshe bakinta saboda kuka da ya kubce mata, oh Ashe zataga wannan ranar, yau shekaru ashirin da daya da batanta gashi Allah Ya nuna ikonsa, a hankali cikin kuka tayiwa Abba bayanin yadda sukai da Aminu. Wata doguwar sujadda yayiwa ubangiji sannan ya fita, ko jimawa baiyi ba se gashi da Alhajin sama sun dawo, gaba dayansu fuskokinsu cike suke da madaukakin farin ciki marar misaltuwa, Hafsa kam bazaka gane wani yanayin take ciki ba, Tsoro ne fal zuciyarta, ko Yaya yarinyar take? Ko ya zata karbe ta, Allah kadai ya sani. Suna cikin wannan yanayin Sega Aminu Ya dawo, straight dakin Abba ya wuto bisa umarnin Alhajin sama, yana shiga wayarshi Ya mikawa Alhaji na abinda Hikma ta tura masa.
STORY CONTINUES BELOW
Zama Duka sukai kowanne yana Kara gasgata Ikon Allah, waye Zaiyi Haka idan ba Allah ba, waye Zaiyi wannan ikon banda Allah.
“Meye abinyi? Ya zaayi? “
Alhaji ya tambaya yana directing tambayar ga dukkansu, Aminu ne yace
“Alhaji na rasa ta Ina zan Fara, saboda bana son muje gidan mutane kai tsaye kawai da sunan neman ya, it feel some how”
Dariya Abba yayi yace
“Ido zamu zuba, Aini tuntuni nasa ayimana booking flight zuwa Kano, Yanzun gari ya waye, Karfe daya. Muje mu samesu ciki da gaskiya wuka bata fasa shi. Amma kayi retweeting ma yarinyar ne?”
Kanshi Ya girgiza yace
“I don’t feel ok retweeting, bansani ba Ko setup ne, though nasan account dinta ta dade Tana following dina tana liking abubuwa na, so bansani ba”
Se lokacin Hafsa tace
“It can’t be Setup, komai is real, yarinyar mu ce”
Kai Alhaji ya gyada ya Kalli Hafsa yace
“An turo miki address din? “
Kanta ta gyada tace
“Ta turo”
Daga Haka Hafsa ta fice zuwa dakinta ta Fara shiri, anan Alhajin sama yake sanar dasu Dada da Mom dasu Ummiey latest development ,gaba dayansu banda hamdala babu abinda suke, Alhaji yace Mom da Dada suzo suje tare da Hafsa, shikam Maina baisan abinda ke faruwa ba Dan fitar Hafsa shima ya fice hakan yasa babu Wanda yabi ta kanshi suka tafi. Tunda Hafsa take bata taba shiga nervousness da uneasiness irin wannan ba, gaba daya gumi take tamkar Baa jirgi take ba. A Haka suka iso Aminu Kano airport inda suka gama komai wani friend din Alhaji Bukar yazo Ya daukesu se gidansu Hikma.
Tamkar a mafarki, Mama Tana parlour tana yiwa Mus’ab wayar Anjima Ya dawo da Hikmah tunda an watse Dama saboda gulmar mutane suka maida ita can, sannan dan ta sake yasa suka kaita can. Tana aje wayar taji sallama hakan yasa ta Mike ta bude musu kofar tareda binsu da kallo na tambaya, fuskarta a sake Har ta musu iso sannan taje ta dakko musu ruwa da lemuka, anan Dada tace mata
“Bamu kadai bane, tare muke da maza a waje, ko maigidan yana nan? “
Da Murmushi Mama dukda ta kasa ganesu amma wani abu daya tsoratar da ita shi ne fuskar Mom data Hafsa, tamkar wadda aka cira ta Hikma aka saka musu, her older version, Tana ta kallonsu taje ta samu Baffa ya fito daga toilet yana gyara hannun rigarshi na jallabiyya, bata zauna ba tace
“Kayi baki”
“Su waye?”
Ya tambaya yana zura wayarshi a aljihu, kanta ta girgiza tace
“Banda masaniya amma akwai Babban alamari a tare dasu, ina zaton iyayen Hikmah ne”
“Iyayen Hikma kuma? Haba dai Rukayya “
Bai jira abinda zatace ba yayi gaba ta take mishi baya, sede suna hada idanu da Mom ya Kara bude idanunshi Ya tsira mata ido, bai Maji gaisuwar da suke mishi ba seda Mama ta taba shi sannan yace
“LA… Lafiya, Sannunkul”
Tun anan suka sha jinin jikinsu, Mom ce ta mishi bayanin su Alhaji suna waje, kanshi Ya gyada zai fita Sega Hamma Mussadiq ya shigo yana fadin
“Surukan Hikmah ne sukazo, Baffa nace su shigo”
Zama Baffa yayi yana cewa Mama
“To, kinga sunzo ban mayi musu Maganar ba”
Bata bashi amsa ba Alhajin sama a gaba Sauran na biye dashi, mikewa Baffa yayi yana ta Murmushi tareda musu tayin zama cikin kujerun parlon, kafin wani lokaci Mama ta cika gabansu da kayan Motsa baki. zama tayi lokacin Baffa na cewa
“Kunjini Shiru ko, abubuwan sukai yawa shiyasa ban neme Ku ba, Dan Allah kuyi hakuri”
Su matan da basu gane abinda ke faruwa ba kansu dukka ya kulle ganin mazan sun San junansu, Alhajin sama ne yace
“What a beautiful coincidence, a blessed day. Malam Muhammad a gaskiya koda muka taso a maiduguri ba nan mukai niyyar zuwa ba amma gidannan ne, se da naga Mussadiq sannan na fahimci inda muke. Wani alamari ne ya kawo mu, bansan yadda zaku fahimci Maganar ba amma ina fatan zakuyi mana kyakyawar fahimta. Wannan…. “
Ya fada yana nuna Aminu da Hafsa sannan ya cigaba da fadin
“…..Shekaru ashirin da uku da suka wuce sun haifi yarsu Zainab, bayan shekara daya aka saceta, mun nema, munyi cigiyar Allah bai sa zamu ganta ba. Se yau Aminu yasa hotonta a twitter na ranar da aka mata hoton kawai se yarinyar tayi retweeting da itace yarinyar data bata”
Mama da Baffa, Hamma Mussadiq da Hamma Musbahu da ya shigo babu jimawa se kallon kallo suke, nan Aminu Ya mika musu hoton, take kuwa wannan ranar ta dawowa dukkansu, Allahu Akbar shi ne abinda Baffa ya furta kafin yace
“Lallai Allah shi shi ne Allah, shi ke yin komai lokacinda yaso. Tabbas Zainab Hikma da na aurawa danku ita yar kuce, jininku ce, ko wannan matar kadai ta isa fadar hakan. Allah Nagode maka, na sauke nauyi”
Mama ce ta shigo da trolley da kayan Hikma ke ciki ta aje musu, kowannensu banda kabbara da kirari babu abinda bakinsu ke furtawa. A take aka tabbatar da komai Se kuma hira bayan Baffa ya basu labarin yadda ya samu Hikma da yadda ta rayu hannunsu, Hafsa se kuka take dukda Mama Tana ta lallashinta.
“Maman Hikma, bata nan ne? “
Hafsa ta tambaya kasa kasa hawaye na bin kuncin. Kai Mama ta girgiza tace
“Yanzun zasu karaso….. “
Se sallamarta kawai sukaji tana fadin
“Mamata! “
A guje kamar yadda ta saba, amma kafin ta rungumeta Idanunta ya sauka akan na Hafsa, wani irin abu taji yana fizgarta tareda muguwar faduwa gaba, Hafsa da Aminu lokaci daya suka mike, tabbas wannan Lulu ce!
Kamar an watsa min kankara ko irin nayi freezing dinnan haka na tsaya, Inata kallonta itama Tana ta kallona, ni Tsoro ne akan fuskata saboda ban taba ganin photocopy na mutum irin yadda naga fuskata a fuskarta ba, Haka na kasa dauke idanuna zuciyata se bugawa take Kamar zata balla kirjina ta fito, Ina kallo naga hawaye ya Fara gangaro mata ga kuma wani genuine smile da takeyi min shi. +
“Go to her Hikmah, she’s your mother, ita ta haifeki”
Haka na tsinkayi muryar Baffa yana fadamin, Juyawa nayi na kalleshi Se naga ya Gyada min kai, na kalla Mama hawaye ne taf Idanunta Tana kallona tana gyada min kai, irin hug her mana, da sauri na tafi na fada jikin matar dake tsaye. Wallahi naji wata nutsuwa da soyayya da ban taba jin irin ta ba, se kawai na fashe da kuka ina sake kankameta, a raina banda Subhanallah! Babu abinda nake maimaitawa, I was so and super excited, bayana ta dinga bubbugawa a hankali itama kukan take, munfi mintina biyar sannan na saketa amma na kankame hannunta saboda gani nake kamar guduwa zatayi, kamar Ina bude idona zanga mafarki ne da na saba yinshi a kwanakin nan. Amma dana bude I was still standing next to that woman, next to Loml💕 tana ta min Murmushi da babu Wanda ya taba min irinshi a rayuwata,
“Ni bazata zo na ganta ba, duk kin kankameta”
Wanda nake tunanin shi ne Mahaifina the CBN governor Ya fada yana hararmu, kowa a parlon seda yayi dariya, sakin hannunta nayi na nufi inda yake ban jira wani abu ba na rungumeshi, shima rungumeni yayi yana fadin
“Blessed you my child! Allah Yayi miki albarka Kinji, Daddy is sorry baby”
A hankali Wasu hawayen farin ciki suka sauka min daga idanu na, I’m so happy, ban taba jin farin cikin da nake ciki a wannan ranar ba. Seda na zauna gefen Daddy sannan Hamma Musbahu yace
“Nikam Hikmah for how long kika san Baffa da Mama ba iyayenki bane? Naga Bakiyi mamaki da akace ga real parents dinki ba”
Baffa da Alhaji suka hada bakin cewa
“Gaskiya kam Musbahu”
Hannuna Daddy ya rike, ina Murmushi nace
“Haba Hamma, ai Bazan taba canja Baffa da Mama ba, iyayena ne. Yanzun daka fadi haka se naji kunya, nake ganin Kamar ban kyauta ba. Babu Wanda ya fada min (seda na Kalli Hamma Mussadiq, Wanda ya tsura min idanun shi, nasan bazai so na fadi sunanshi ba) kawai na dade ina ayyana Baa gidanmu nake ba, naga wannan kayan sannan bana kama ban dakko halin kowa ba, to jiya birthday Dina, I was going through twitter se naga post din Daddy na missing daughter dinshi, dama na dade inajin Anya bashi bane Babana ba, so anan na tabbatar da zargina shi ne nayi maka tweeting kuma bakai retweeting ba Har na hakura”
Kowa farin ciki yake sannan Daddy yace
“Ga Grandparents dinki”
Kowanne seda ya nuna minsu, Ina binsu da hannu muna musabaha, naji dadi sosae wannan ranar seda nayi recording dinta a diary dina. Kafin wani lokaci duk su Aneeysa dasu Hamma sun taru a gidan, tamkar ana yin biki, se girke girke ake, babu Dama na mike Mama zata balla min harara Wai ina Zanje na bar Mamata.
Daga karshe dakina muka wuce nida ita, Tana ta bugawa mutane waya muna gaisawa, inajin yadda suke murna nasan nayi Saar dangi. Ina tason nace mata waye na aura amma Se naji kunyarta, se can tace min
“Azizaty, Kinada saurayi Ko? “
Wani kallo nayi mata irin saurayi kuma? Kaina na girgiza nace
“Inada aure fa”
Gyara zamanta tayi, Ina karanto disappointment din a fuskarta, Dan har seda ta runtse idanunt kafin tce
“Aure, Tun yaushe? “
Shigowar Mama yasa ban bata amsa ba, tare muka fita saboda tace mana Abinci is ready. A parlor duka muka zauna ina nanike jikinta kamar zata maidani ciki, duk inda nayi tana biye Dani da idonta, Haka dana tsaya sauraren Abu zatace
STORY CONTINUES BELOW
“Azizaty bakya ci”
Duk duniya babu abinda ya kai Uwa, wannan tsaftaciyar soyayyar daga Allah ce. Daga karshe karbar spoon din tayi daga hannuna tana bani, oh Nikam naga Ikon Allah, babu Wanda ya hanata se dariya dake mana, Nikam kunya nakeji saboda ban saba ba amma a Haka Har na ware inajin dadin concern dinsu. Ana Sallar Maghrib suka Fara shirin tafiya saboda dama basuda niyyar kwana, MA ce kawai zata zauna. Mun fito zamu raka su kowa yanata tambayata ko akwai matsala ko wani abu, Daddy ya riko hannuna ya samin kudi a ciki yace
“Take care of yourself Child”
Ina Murmushi nace
“Daddy….. “
Kanshi Ya girgiza yace
“Naaa, babu godiya tsakaninmu”
Murmushi nayi na isa gurin Mom da ko Baa fada min ba nasan cewar ba yar Nigeria bace, kuma kamnninta muke dashi, cemin tayi
“ki daina wannan beautiful smile din, mijina Ya rufe kofa bazaiyi aure ba”
Dariya nayi na nuna Abba nace
“Nima mijinki yayi min tsufa, mijin Dada nake so”
Dakuwa Dada tayi min tace
“Ja’ira Baka kawai, can dai babu abinda Zaiyi dake”
Alhajin sama yace
“Ni Ina son ta “
Dariya akai suka shiga Hamma Mussadiq zai kaisu airport, muna dawowa muka hadu aka gyara gidan Mama da Ma sunata hira abinsu Kamar ba yau bane first meeting dinsu ba. Muna zaune Mami tace
“Ashe Anyi auren Hikmah? Me takeyi a gida to? “
Mama tace
“A’a Hikmah kuma? Ita ce fa wadda Ibrahim yake aure”
Wani irin zabura Mami tayi tace
“Ita ce? Subhanallah! “
Ai se ta sakko kasa tayi Sujadda ta dago ta rungumeni tana fadin
“Allah me iko! Allah abin godiya”
Nan ta zauna Tana bamu labarin komai na rayuwar Ibrahim, da tsawon jirana da yayi without knowing zan bayyana Ko Bazan yarda ba. Tana gama fada ta juyo Kaina tace
“Azizaty, ina fatan bazaki bani kunya ba, Ina fatan zaki jure zama dashi Har lokacin da zakiji kina sonshi. Idan kikai min haka kin gama min komai”
Hawayena na goge a raina Ina fadin, Allah Sarki Abdallah yayi min alkawarin Inshaaa Allah zai zama sanadin haduwata da iyayena, surely Allah is wonderful, Shikadai yasan yadda alamura ke tafiya. Abdallah ya furta hakan baisan yadda zai Nemo min su ba, ashe Allah Yayi fasa aurenmu shi zaisa na hadu da iyayena sannan na hadu da sadaukin Masoyi, Wanda ya soni batareda sanin ina ina na, baisan wacce duniyar nake baisan looks dina ba. Tabbas da nasan da zamanshi da ban Bari Abdallah ya fasa min zuciyata ba, da ban bata lokacina na zuwa event din bikin Abdallah Ahmad ba. Aamma Allah shi shi ne Allah, shi yasan gobe. Hannunta na kama nace
“Mami, Inshaaa Allah zan zame miki sanyin idaniya, zan zame miki Ya daya tamkar da dubu, bazaki kara rashin kukan da ba. Yaya Ibrahim kuwa Banji sonshi a zuciyata ba amma zuciyata ta bashi Babban matsayi Wanda babu meshi, Inshaaa Allah Se na saka yaji worth din jirana “
“Blessed you child”
Ta fada tana shafa kaina, wayarta ta ciro ganin mu kadai muka rage Dan tunda ta Fara magana suka baje suka bamu guri, babu jimawa naji tana fadin
“Son, albishirinka!”
Banji me yace ba, tace
“1million cash! “
Se tayi dariya tareda matsoni jikinta tace
“Ga Lulu! “
Mika min wayar tayi, a hankali na karba na kara kunnena Inaji tana fadin
“Amma naji dadi da wayarka ta mutu da tuni an rigani Baka Daddan labari”
“Yaya Ibrahim Ina yini”
Muryarshi a tausashe kanaji Kasan me ita maabocin nutsuwa ne amma dukda hakan, kana jiyo excitement da amazement a muryar
“Baby are you there? Kece da gaske? Dama nace musu Kinada rai zaki dawo I was right nasan Zaki jirani. Alhamdulillah! Alhamdulillah!! “
Gaba daya a cikin seconds baifi goma ba yayi maganar har seda naji tsoron kada fa Yaya kware, tausayinshi sosae Ya lullubeni nace
“Ni ce Yaya Ibrahim, Inada rai kuma na jiraka. “
“Bakiyi aure ba? “
Ya tambaya sounding nervous, Murmushi nayi nace
“Anyi min aure amma Kaine mijin…. “
Shiru yayi tamkar ruwa ya cinyeshi I’m sure so yake yayi comprehending abinda na fada masa, se can yace
“Ban fahimta ba “
Dariya nayi na kashe wayar, na mike na kashe komai na parlor nabi bayan Ma wadda tunda ta bani wayar ta koma dakin, wani sabon yanayi naji, bawai so ba amma Se na samu Kaina da matsanancin tausayinshi hade da ganin girmanshi. Ina shiga yana Kara kira, wayar na mika mata na wuce toilet dan yin alwala. Bansan me sukace ba na fito na sameta har ta kwanta, jikinta na shige ina jin wani irin nishadi da soyayya. A wannan Daren Munyi bacci me dadi, seda muka kai 2am muna hira sannan mukai bacci, da asuba mukai sallah sannan muka koma Har 8am sannan na shiga na hada mata ruwan wanka na fita gaida Mama, Tana zaune naje na rungumeta ina gaisheta, sosae ta amsa sannan tace
“Baffanki yace Anjima zaki bi Maminki ku tafi can Maidugurin”
Kallonta nayi nace
“Kai Mama! Na bita kuma. Ni gaskiya A’a “
Wata harara ta sakarmin daidai shigowar Mami tana zama tace
“Maman Hikma Ina kwana “
Murmushi nayi naji dadin karar da Mami takeyiwa Mama, gaisawa sukai, tare mukai breakfast sannan na wuce nayi wanka, anan Baffa ke cewa Mami ta tafi Dani, da farko tace
“A’a Baffan Hikmah, karka damu idan kuka gama shiri a kawota kawai gaba daya”
Kai Ya girgiza Yana Jinjina karar dangina yace
“A’a Kuje kawai, idan ta kwana biu akai fixing date Se ta dawo”
Godiya sosae Mami tayi musu, ina fitowa tace
“Kira min Hamma Mus’ab dinki zai kaini Unguwa zaki rakani”
Wayata na dakko na kira Hamma Aiman Dan jiya baya nan yaje Abuja akan visa dinsu, se na kira Hamma Mus’ab a tare suka iso. Yadda yayiwa Mami tamkar yasanta ko sun dade tare, itama she’s free kuma Tun dare nayi mata bayanin kowa da role dinsa a rayuwata Dan Haka sallama mukaiwa Mama muka tafi ta bani wayar ta mukai waya da Mummy tace min ita ce Maman Yaya Ibrahim.
A Beauty Gaze muka tsaya, daga ni se ita muka shiga, gurin mayuka ne da sabulai iri iri, wani Hot chocolate ta siya min set, itama Haka Dan skin color, se Wasu Acne set. Daga nan muka wuce mukai siyayya sosae.
Karfe Tara na dare aka rakamu airport, I’m feeling a new me, tamkar Ni din wata sabuwar halitta ce, iyaye Rahama ne! Karo na farko da na Fara shiga jirgi, Inada height phobia amma gani ga Mami se naji duk tsorona Ya tafi. A Haka mukai landing maiduguri, first time of I been there, se kalle kalle nake, inajin yadda Mami ke ta barbarci da mutane abin se birgeni yake.
Babu Wanda yasan da zuwanmu banda Daddy shi kuma ya riga da ya koma Abuja saboda aiki, amma Mami babu Wanda ta fadawa zamu zo, shiyasa babu Wanda yazo daukarmu daga airport se cab ta samar mana drop muka tafi. Muna tafe Tana yimin bayanin guri guri, immediately I fell in love with Maiduguri over and over, saboda dama tuntuni ni inason garin. Se Misalin goma da wani abun muka isa gidan, Tun daga kofar gidan nasan Babban gida ne na masu hannu da shuni, ginin kadai ya isa fada maka masu mallakin gidan ba abun wasa bane, Alhajin sama Yayi deputy governor, Abba Yanzun shi ne chief of staff na Borno, Alhaji Bulama da bangani ba Mami tace min shi kuma Babban Dan kasuwa ne a garin. To iyaye kenan baazo kan ‘ya’yansu ba balle kuma su jikoki irinsu Yaya Ibrahim, ai sede a rufe baki da Sam barka.
Gidan Ya danyi Shiru, saboda mafi yawancin mutanen gidan sun kwanta, muna shiga wata matashiyar budurwa ta fito daga can part din gefe, kunnenta da ear piece a makale, Tana hangomu ta zare tareda ihun
“Ma! Oyoyo”
Kai Mami ta girgiza tace
“To town Crier, Announcer, dare ne yanzun”
Dariya ta saki amma ganina takure jikin Uwata yasa ta Kalli Mami sannan ta kalleni tace
“Ma, Lulun ce? “
Kafin Mami ta bata amsa tamin wata irin runguma da banda Ni Babba ce da se na samu fracture. Rungumeta nayi nima inajin dadi, sakina tayi ta Mika min hannu tace
“Nima cousin dinki ce, sunana Labiba amma zaki iya cemin Milk!”
Idanuna na dan bude da mamakin sunan, se kuma nayi Murmushi nace
“Hikmah!”
Shaking hands muka kara Har lokacin Mami na tsaye, seda muka gama tace
“Muje parlour nasan kin gaji”
Dukkanmu muka shiga wani tangamemen parlour, yayi kyau Kamar kada na fita a ciki, babu kowa se wata budurwa itama da batafi saa ta ba tana ta jerking, kafafunta cikin ruwa, hakan ya bani dariya, Dan idan Tun Yanzun sha daya batai ba Anyi tsome tabbas zuwa sha biyu tayi bacci kenan. Mami ce tace
“Nikam Nasiba bana hanaki tsoma kafa cikin ruwa ba, idan bacci kikeji ki tafi ki kwanta ki saita alarm. Amma you can’t cheat nature”
Tayi abinda aka ce mata, amma wani ihu da ta buga Tazo ta rungumeni Ni kaina seda na firgita, there and then na fahimci inda na gado hayaniya, ashe a maiduguri na dakko. Kafin wani lokaci mutane sun firfito Dan ganin lafiya, da yake ba bacci sukai ba sun kwanta ne kawai. Da fuskokin dana hadu dasu jiya da Wanda basu nan Haka na dinga binsu da kallo, hug kuwa seda na gaji. Ga gajiyar hanya banda burin da ya wuce naji na kwanta amma ina haka muka zauna anata hira, Yan mata wajen shida, duk jikoki sun nanike ni. Har wajen sha daya sannan Dada tace aje a kwanta ko Dan na huta. Se naji duk na wartsake koda zaa kwana a Haka Bazan gajiya ba.
“Ma, zamu tafi da ita dakinmu mu kwana”
Nabila ta fada tana kallona, Kai Mami ta girgiza tace
“Yanzun an samu canji daga Ma, na koma Mami. So kowa Yayi cancelling Ma a ranshi. “
Murmushi nayi Dan nasan saboda na Fara kiranta da Mami shi yasa. Binta nayi na canja kayana zuwa kayan bacci sannan na kwanta gefenta Kamar jiya. A Haka bacci me dadin gaske yayi gaba Dani. Duk da naso Naga Mijina kafin na kwanta amma ganin babu Wanda Yayi zancenshi yasa nima na share kawai.
Washegari, bayan Munyi Sallar asuba Mami ta daukeni dakunan kakkanni na naje muka gaisa, a karshe dakin Ummiey ta barni ta koma nata. Munata hira da ita dukda tayi tayi na kwanta amma naki. Can Sega Yan matan gidan sunzo muka hadu dasu munata hira, ka rantse da Allah mun dade da sanin juna. Hirar Har ta gangaro kan Maina, babu Wadda ta kusheshi banda shawarwari da suke bani akanshi tareda gwada min son da yake min, se naji na kagu mu hadu na ganshi.
STORY CONTINUES BELOW
Se wajen takwas sannan na fito na kuma wajen Mami, Tana cikin bargo tana bacci na shiga nayi wanka sannan na fito na shirya cikin wani lace maroon da pattern design na milk. Yamin kyau sosae nima nasan da hakan. Ina cikin daurin dankwali naji sallama, aje dankwalin nayi na fita Dan duba sallamar, na bar Kaina Wanda tun gyaran da akai mishi na wancan auren nawa, Allah Ya taimaka Yanzun na taje na kamashi da band, da bansan Kunyar da zanji ba. Ina fatan baku manta ni a kazantar gashi ba.
Yana tsaye da jallabiyya Fara tas me karamin sleeve, hade da hula, idanunshi Sunyi haske Ya kafesu akan kofar da dukkan alamu jiran a bude yake, ina budewa idanunshi suka koma kaina, Kamar yadda Nima na tsareshi da nawa idon, sede gabana da bansan dalili ba, bugu yake, irin bugawar da bai taba yin irinshi ba. Shiyasa na duburburce na kasa bude baki balle nayi mishi magana, shikam bansan nashi dalilin ba. Wannan ne Karo na farko da naga namiji bayan su Alhaji, na dauka matan ne kawai sukeda kyau Ashe mazan ma Mashaaa Allah.
“Hikmah, ke da waye ne?”
Naji muryar Mami ta katse min tunanina, cikin sauri na dauke idanuna Ina tuna Ashe ni matar aure ce. Matsawa nayi daga kofar ina fadin
“Mami nemanki ake”
Tuni tasan waye, Maina ne shi daya ke zuwa gaisheta da wurwuri, kuma tace masa zata dawo amma Jiyan baisan ta dawo ba, kilan wani ya fada masa. Sakkowa tayi ta nufo inda muke, yana tsaye har lokacin bai Motsa ba bai kuma yimin magana ba, so I started asking Ko dai shi kurma ne? To amma ai sallamar shi tasa najiyo shi. Ban gama tunanin ba naji yace
“Ma, Ina kwana? “
Da sauri na kalleshi, muryar da naji a waya ita ce wannan, wato shi ne Yaya Ibrahim kenan. Cikin sauri na shige ciki, sun dade da Mami sunata barbarci Har na gama shiryawa, na gyara gadon na hada mata ruwan wanka sannan ta shigo tace
“Oya! Aje wannan mayafin, kije ga mijinki can ku gaisa. “
Baki na turo cikeda shagwaba nace
“Mami ba mayafi kuma”
“Ungo nan “
Tayi min dakuwa, dariya nayi na aje veil din nayi hanyar parlon, inajin wani race da akeyi a cikin kirjina. Seriously Mijina, kawai se nayi Murmushi. Yana zaune ya tsirawa kofar idanu, ina fitowa wani murmushi me kyau da ya haska fuskarshi ya kubce daga bakinshi, se na samu Kaina da mayar masa martani sannan na zauna cushion din da yafi kusa dashi, na dan zamo kadan nace
“Yaya Ibrahim Ina kwana? “
Kallona kawai yake bai amsa min ba, se na gyara zamana kawai ina wasa da yatsun hannuna, na sani Abdallah ya iya kallo amma Ibrahim kallonshi daban ne, inajin nervousness idan Abdallah na kallona amma na Maina ji nake tamkar na zura a guje na bar mishi gurin. Seda muka shafe fin mintina goma, ina tunanin lokacin ya dawo hayyacinsa yace
“Baby, yimin magana naji muryarki”
Bakina na zunbura nace
“Ba na gaisheka ba, kuma Baka amsa min ba”
Rufe bakinshi Yayi yana dariya kasakasa, God irin wannan dariyar haka zata iya sawa naji duk duniya komai ya tsaya min.
“Sorry Baby, kin tashi lafiya? Ya sabon guri. Ina fatan you find us loving? “
Murmushi nayi nace
“I’m fine, kunada kirki! “
Kanshi Ya girgiza yace
“Ina Mama da Baffanki? “
Take naji wani dadi ya Kara ratsa ni saboda bana son naji an manta dasu, they surely deserves a medal.
“Suna kano”
Kanshi Ya gyada, se kuma mukai Shiru kowanne na sake sake cikin zuciyarshi, can na mike nace
“Zanje gurin Mami”
Shima Se ya Mike yace
“Tohm Bari nayi wanka, ki jirani se muyi breakfast tare “
Kaina na gyada na jira Har ya fita sannan na shiga dakin, ta gama shiryawa, tana zaune Tana waya, naje na zauna gefenta tareda kwantar da kaina a kafadarta, ganin bata gama wayar ba yasa naje na dakko tawa na kirasu Baffa munata fullanci, Mami se kallo na take seda na gama tace
“Fulani, ba zaki iya barbarci ba”
“Kai Mami bazaki koya min ba, inaso fa”
Murmushi tayi tace
“Maina zai koya miki, Ehen! Ya Naga kin dawo? “
Langwabar da kaina nayi nace
“Mami baya magana sede yayi shiru”
Dariya tayi tace
“Ke zaki sakashi ya dinga yi, kina yi mishi hira. “
Zama nayi kamar wata sokuwa nace
“Mami ta Yaya? Nifa bamu saba dashi ba kwatakwata”
Hannuna ta rike tace
“Tashi muje kitchen, mu hada abinci”
Tashi nayi nabi bayanta, a tare da ita inajin tamkar babu wata marar damuwa Irina, inajin rahamar Allah shi ne ya bani Mami matsayin Uwata. Stool taja ta zauna ta sani na cicciro abinda Zamui amfanin dasu, Ko hannu bata saka ba tana bani umarni har muka kammalla hada breakfast din. Warmers na dakko da flask din tea na zuba komai sannan muka koma daki na canja kaya, zuwa wani material doguwar riga silk yana ta rawa a jikina. Turare Kamar zaayi barinsu haka ta feshe ni dasu, humra masu sanyi ta saka min sannan ta bani hijab, ta kira Rukayya ta rakani dakinshi. A kofa muka rabu da ita, yayinda na dade rikeda basket din ina ayyana yadda zaayi na shiga kai abincin nan, gaba daya Tsoro nakeji da kuma kunya. Nafi mintina goma a tsaye bansan yadda zan Nemo wannan courage din ba , ban ankare ba naji an bude kofar, da sauri Nayi baya, cikin rashin saa nayi tuntube zan hantsila yayi saurin riko ni, se jina nayi a kwance jikinshi. Na tsorata sosae hakan yasa na dinga sauke Ajiyar zuciya, seda na nutsu sannan ya sakeni, Haka na dauki kayan ya tayani muka shiga. Dakin Babba ne sede kallo daya Kasan dakin maza ne, a hargitse komai yana zaune inda yake. Muna aje kayan ya Fara kokarin fara tattara dakin, tashi nayi na karbi system din na aje kan study table dinshi nace
“Bari nayi”
Mika min Yayi in surrender Ya bani sannan ya zauna ya jiran na gama. Ban wani jima ba na gyara sannan muka zauna cin Abinci, gaba daya atmosphere is tensed saboda Shiru babu me magana. Haka yasa muna gamawa na mike dan tafiya yasa hannunshi ya kamo nawa Ya zaunar Dani gefe, gaba daya jikina Se goosebumps, na Fara blushing shi kuma Murmushi yake yace
“Me yasa da mun zauna Seki tafi, ko ina baki haushi ne.”
Da sauri na girgiza kaina tareda kwace hannun nawa nace
“Kaine se ka dinga yin Shiru”
Dariya yayi yace
“Oooo! Tohm Yanzun muyi hira. Bari na Fara Baki labari”
A hankali ya Fara bani labarinshi, karatun da yayi da kuma ayyukan da yayi, Inata kallonshi ina gyada Kaina, seda ya kammalla nace
“To kuma me yasa Bakayi aure ba, kanata karatu”
Shiru yayi Kamar me tunani, hakan yasa na shiririce ina kallonshi kawai se naji bakinshi a nawa, God! First kiss which was passionate and affectionate. Ko hanashi banyi ba, dukda akwai rashin Sabo amma I enjoyed it. Seda ya sakeni sannan naji wata kunyarshi ta lullubeni, shima kawar da kanshi Yayi yace
“I was waiting for you, only you baby. Gimme a chance na nuna miki yadda nake jinki a jikina. Forget about your past, just embrace the present. Inshaaa Allah bazakiyi dana sani ba”
Wata Ajiyar zuciya na sauke tareda gyada mishi Kaina, ganin da gaske kunya nakeji yasa yace na fada mishi rayuwata, abinka da me surutu tuni na balle, wani yayi dariya, wani yace banida Wayo. Karshe I was embraced in his chest a Haka muka gama hirar!
Tsabar yadda hirar tayi dadi, bamusan lokaci ya tafi har Haka ba, kawai se kiran Sallar azahar mukaji, kallona Yayi ya lakuce min hanci yace +
“kin gani Ko? “
Kauda kaina nayi nace
“Me nayi?”
Dagani Yayi sannan ya mike tareda fadin
“Shiga kiyi alwala”
Kaina na gyada na shiga, babu laifi bayin is neat sede laundry bin din ya cika da kayan wanki Wanda duk inners dinsa ne. Ni Kaina ina mamakin karfin halin da nake, ban taba kawowa zan zauna da mijin da ban taba gani ba, balle har na sake jiki dashi Haka ba. Amma gashi nan har Ina iya zama mu shafe awanni tare. To meke faruwa dani, Kodai Dama tun can bana son Abdallah? How can my heart open up for someone so quick? Wannan miracle ne, Allah kadai Zaiyi Haka.
Alwala nayi na fito sannan ya shiga, kafin ya fito na tattara kayan da mukai amfani dashi na fice. Amma ina fita na juyo, daidai shi kuma ya fito zaije massallaci mukai karo. Baya ya dan ja sannan yace
“Ya akai Baby?”
Turo baki nayi nace
“Kunya nakeji fa”
Dariya yayi yace
“Naga hira kawai mukai, babu abinda mukai ai”
Da sauri na rufe fuskata nace
“Se kayi ta bani kunya”
Dariya ya kuma yi, sannan ya miko min hannunshi yace
“Oya! Bani abata “
Kallonshi nayi nace
“Me fa? “
“Kunyar mana”
Ya fada sounding naughty, dauke kaina nayi daidai lokacin aka Fara iqamah Hakan yasa yace
“Baby shiga kiyi sallar idan na dawo se na rakaki”
Cikeda jin dadi nace
“Yawwa, Allah Ya dawo da kai lafiya”
“Amin My Purkinje fibres “
Wani irin farin ciki marar misaltuwa ya kamani, nasan Meye Purkinje fibres, zarririka ne a cikin zuciya dake taimaka mata wajen bugawa. Ni ce tashi kenan! Dan squealing nayi sannan na wuce dakinshi nayi sallah, na dade a zaune inayiwa Allah godiyar ni’imominsa a rayuwata, yadda lokaci daya tayi wani 360 turn, yadda komai within a blink of an eye, komai ya canja, a Yanzun jina nake tamkar ban taba yin kuka ba tamkar dama a cikin farin ciki nake. Na yadda Allah shi ne Allah, shike maida baki ya zama fari a lokacinda yayi niyya. Subhanallah!
Ina nan zaune ya dawo, cikin hanzari na bishi muka fito, gaba daya ji nake kamar kasa ta tsage na shige. Amma shi Ko a jikinshi, banda Murmushi babu abinda yake yana min magana kasakasa, Nikam ko kulashi ma banayi saboda gani nake duk shi ya shashantar Dani. Muna shiga parlon Dada naji Mami tana fadin
“Nafisa dauki basket din can lunch din su Maina ne, jeki Ki kai. Kinga har kya ga Lulun”
Idanuna na runtse na ja na tsaya, hannuna Ya janyo ai se gani kawai a parlon, Tana zaune itada wata mata da bata wuce sa’arta ba amma kana kallonta kaga Daddy kaga kuma Yaya Ibrahim, da Rukayya data rakani gurinta. Suna zaune Dadar ma bata parlon. Kaina a kasa na tsuggunna nace mata
“Ina yini! “
Bata amsa ba se wata runguma da tayi min tace
“‘Yata barka da dawowa, sannunki”
Murmushi nayi bance komai ba, seda muka zauna sannan suka gaisa da Maina dake can gefe hankalinsa akan Mami dake min bayanin matsayin Mummy Salima. Zamewa nayi daga jikinta tunda naji Ance surika ce. Dariya tayi tace
STORY CONTINUES BELOW
“Rainon Fulani, ni Mamanki ce, waccan ita ce sirikar ki kinji”
Kaina na gyada dan na fahimci har tafi Mami barkwanci, muna nan zaune sunata hira, na sulale na koma parlon Mom inda nan naji hirar Yan matan. Tare mukai lunch sannan muka daura hira. Can har uku Mami Bata shigo ba, na mike, Nafisa tace
“Matar Yaya Ina zakije”
Dan Murmushi nayi da dan kunya nace
“Gurin Mami zani”
Gaba daya seda sukai dariya, ban kulasu ba nayi gaba abina, Tana zaune itada Dada, Mummy na parlon Ummiey, jikinta naje na kwanta nace
“Mami!”
Aje Tab din hannunta tayi tareda bani dukkan attention dinta tace
“Hikmah yaya? Kinci Abinci? “
Kaina na gyada, Dada Tana ta min fullanci ina amsa mata a Haka bacci ya daukeni kaina cinyar Mami.
Washegari da wurwuri Mami ta tashe ni, naje na hadawa Yaya Ibrahim breakfast saboda zasuje Kano gaisuwar surukai. Ina gamawa nayi wanka sannan na zura wata simple morning gown na daura Hijab na tafi dakinshi. Yadda fito a wanka ya saka kayanshi yana zaune na iske shi. Seda na gaida shi sannan na hada masa tea, ya karba sannan na zuba mishi plantain chips da cinnamon rolls. Ina nan zaune Har ya gama sannan muka fito tare. Ciki ya shiga ni kuma na koma gurin Mami na kwanta, nanma cemin tayi na tafi dakin Mummy na gaidata. Babu musu na tafi can, Tana zaune Tana waya na sameta, ina shiga ta nuna min gefenta na zauna dukda inajin kunya Har ta gama muka gaisa tace
“Hikmah bana jin dadin yadda kike min fa, Ki saki jikinki Dani kinji”
Kaina na gyada na gyara zama, yadda Mami tace tayi min haka taimin, tambayoyi ta dinga min ina bata amsa a Haka har na ware abinda bata tambaya bama fada mata ba. Itada Mami su kadai suka tambayeni Abdallah, ban boye mata komai ba na fada mata. Muna haka Maina Ya shigo yayi kyau sosae, wata bugaggiyar Ash shadda ce Anyi mata dinki da bakin zare. Harda babbar riga Ango sak. Gefen Mummy Ya zauna, suka gaisa, sosae ta yi mana nasiha tareda fatan alkhairi. Mikewa yayi yace
“Mummy Dr Dalhat yazo, Bari na wuce”
“To Allah Ya tsare a gaida su kafin muje”
Kallona Yayi yace
“Babu sako wajen Mama? “
Murmushi nayi nace
“A gaida su”
A hankali rayuwa ta cigaba da tafiya, duk Wasu wanda ya kamata na gansu na gansu, na hadu dasu. Seda nayi kwana goma lokacin Har an Kai Lefe Kano. Satimu daya a maiduguri muka koma Abuja. Iya shakuwar da ya kamata muyi da Yaya Ibrahim Munyi, duk dana taho seda naji kewar shi. Anyi fixing date din bikin da tarewa ta nan da sati daya, da Ance Kano zaayi amma Baffa yace lallai a maiduguri zaayi, su Sunyi nasu amma zasu zo. Iya shiri na sha a gurin Mami da Sauran mutane, lectures kuwa Wasu lokutan da Dama idan aka gama bana iya kallon Mom, Sam bata jin kunyata.
Sati yazo mukai Maiduguri da shirin biki, ranar murna sosae saboda zanga Maina, ni Kaina mamakin hakan nake, tunda na taho kullum se Munyi waya, shiyasa muka saba sosae. An gama shirya ni na wushewushe Anty yana ta cemin Yan Kano sunzo, a guje na fita se inda aka saukesu, jikin Mama na fada Ina fadin 1
“Mamatal”
Rungumeni tayi tana fadin
“Hikmata, Mashaaa Allah, Yata tayi kyau “
Murmushi nayi se lokacin muka gaggaisa, akayi wushewushe aka tashi lafiya, kawayen Mami kamar kasa. Washegari Zakayi Dinner, Tun safe ake shiri, bamu haduwarsu da Maina ba tun jiya. Wajen azahar na gama cin Abinci akace naje Maina yana kirana, Rukayya naja itada Nusaiba saboda tamu tafi zuwa daya mukaje. Dakin nashi a cike yake da abokanshi, yana tsaye a bakin kofa dake dama jirana yake, Ina zuwa ya riko hannuna yace
“Baby Kinyi kyau sosae, Abokaina zasu ganki”
Kaina na gyada nace
“Muje “
Tare muka shiga hannunmu cikin na juna muka shiga, gaisawa mukai dasu suna ta fadin
“So duk shekarunnan Kece kika tsayar mana da Abokinmu”
Dan Murmushi nayi na kalleshi, Murmushi yayi min sannan sukai mana addua, na fito. Karfe Tara aka Fara dinner tsabar yadda mukai kyau se lumshe idanuna nakeyi, Ina kallon kowa, I was so happy kamar nayi me, shima murmushin yakeyi. Washegari akai yini da laasar akai shirin kaini, mutane goma, biyar dangina na Kano, Kawata daya, cousin daya se uku daga nan Maiduguri. Abuja ne kuma ta jirgi zamu tafi hakan yasa baa tafi da yawa ba. Nasha kuka Kamar zanyi me, na Rungume Mami itama Har seda na sakata kuka a Haka aka banbareni na Rungume Mama muka tafi ,inajin tamkar Zaa kaini wata duniyar ne.