TATTALINTA
CHAPTER 7
*B*alqees kuwa da kyar ta samu ta iya kaiwa safiya sabida kukan da tashi. k’arfe 5 da rabi ta mik’e da kyar tayi alwala tayi sallah tana addu’ar neman sassauci a gurin ubangiji sannan ne ta fara samun sauk’in zuciyarta sama-sama.
Wajan k’arfe 7 Aamanee ta matsa kusa da ita har lokacin tana zaune kan sallaya tayi shiru idanuwanta a lumshe Aamanee ta janyo hannunta still bata bud’e idon ba Aamanee tace.
“Wai har yanzu baki dena son guy d’in nan bane duk da yayi aure?!”
Numfashi Balqees ta sauke tare da zare hannunta daga rik’o da tayi mata. bud’e ido tayi ta watsa su akan na Aamanee cikin razana tace,
“Kuka kika yi Balqees?why?!”
Bata bata amsa ba sai tambaya data wurga mata.
“Yayya Aamanee yaushe zaku koma gida?!”
“Bin mu zaki yi ne?”
Ta kuma yi mata tambayar itama tana faman kallonta zuciyarta nayi mata sak’e-sak’e da yawa. Balqees ta share kwallar da ta zubo mata akan kuncinta sannan tace.
“Eh..”
Aamanee ta gyara zama tare da sake kamo hannun Balqees tace,
“Gobe zamu wuce amma kafin sannan sai naje na samu Sultan na gaya mishi abinda ke ranki dan wallahi wannan abun ya isheni kuma baki isa ki hanani fad’a ba, sai kinje kin kashe kanki a banza a wofi…”
“Dan Allah karki min haka yayya Aamanee, idan kika fad’a mai duk abinda ya faru dani kece sila dan haka ki rabu dashi ni dai kiyiwa uncle Bashir magana cewar nima zan biku.”
“Toh naji bazan sanar da Sultan abinda yake damunki ba, haka zalika kuma bazan gayawa uncle cewar kina san komawa ba, kina da waya ai sannan kina da number’n shi zaki iya kiran shi ki sanar mai.”
“Kiyi hakuri ni ba da wani abun nace karki gaya mai ba ina da dalilina..”
“Toh ai nace bazan fad’a ba nima, kije kiyi tayi dakwan so dai ba abubane me billewa, mtww.”
Daga haka Aamanee ta mik’e tabar gurin, shirin kayansu ta farayi ita kuma Balqees ta kife kanta a k’asan gurin tana kuka k’asa-k’asa daga haka bacci mai nauyi yayi awan gaba da ita a wajan.
Su Aamanee na kammala shirin su suka yiwa su Umma sallama sannan suka wuce ba tare da sun tashi Balqees sunyi mata sallama ba. sai wajan k’afe 9:45am sannan Balqees ta farka,tayi mamaki ganin babu kowa a d’akin sannan babu jakunkunan kayan su Aamanee dasu Afrah,ta mik’e da kyar tana jin jiri dan wata muguwar yinwa take ji kirjinta sai zafi yake ta fito zuwa parlor shima mutane ne tsilla-tsilla ta koma cikin d’akin ta d’auki wayarta tare da kunnawa ta fara neman layin Afrah dan tasan har lokacin yayya Aamanee haushinta take ji dan haka ma bata nemeta ba, sai kawai taji na’uarar computer na cewa wayar a kashe take nan tayi kundun balan kiran Aamanee itama a kashe ta fara tunanin inda suka tafi basu gaya mata sai kawai ta kira Bilkisu cikin sa’a taji ta shiga tana d’auka tace.
“Billy kin san inda su yayya Aamanee suka shiga?na tashi bangan su ba.”
Bilkisu tace mata.
“Sun tafi ai, sunce zasu je Adamawa daga can zasu wuce ethopoeia gobe kenan.”
Story continues below

Kit Balqees ta kashe kiran tare da fad’awa kan gado tana kuka, sai da tayi mai isarta sannan ta dena yi gabaki d’aya ta zuge har ta d’an fara k’ashin wuya. sai wajan k’arfe 1:00pm sannan ta fito lokacin babu kowa a parlour’n ta samu ta shiga kitchen da kyar, ruwan Lipton ta had’a tun a cikin kitchen d’in ta fara sha sabida rad’ad’in da taji kirjinta nayi mata. sai da tayi kur6a d’aya biyu kawai ta saki cup d’in tayi k’asa tana zille-zille lokacin inna me aikin gidan ta shigo kawai taganta sai tayi saurin juyawa tana kiran Umman Sultan suka dawo dare da ragowar ‘yan biki wad’anda basu tafi ba.
Da sauri Umma tace a d’auki mota a kaita asibiti, suna tafiya tayiwa abba waya ta gaya mishi shima daga can office ya wuce asibitin dan jin abinda ya sameta.
Suna zuwa asibitin Dr gadanya aka bata gado nan suka samu Dr Khalid ya kirasu ya sanar dasu cewar olser ce ta kuma yi chronic sosai dan haka sai ta d’an kwana biyu a asibitin dan kula da ita.
Kwance abba ya shiga ya ganta sai faman bacci take yi duk tayi wani iri tamkar wadda ta dad’e tana jinya. haka da hajiya kaka tazo ta dinga fad’a tare da nuna yadda bata cin abinci musamman a cikin datsin bikin nan haka dai abba ya dinga bata hakuri yana kare Balqees d’in da yake shi besan abinda hajiya kaka ta sani ba akan Balqees d’in ba dan haka tayi mai banza.
Shi kuwa Sultan ina an samu amarya gabaki d’aya hankalinshi da tunaninshi yana kan Nadiya, da baki sunzo sun fita zai jata bedroom ya hau shashshafata domin ta riga ta rud’ashi tun daran jiya dama wayoyinshi be kunna suba sabida kar a dame shi hakan yasa besan lalurar da ta samu Balqees ba,yayin da Nadiya ke mamakin shi dan ko kama beyi da irin wanda za’a ce zai yi irin wannan nacin ba dan yadda ka ganshi sai kace ma baxai iya cire d’ankwalin mace ba.
Sai washe gari sannan Sultan yaji labarin cewar Balqees na asibiti amma a ranar za’a sallame su dan haka da yayi wanka yayi breakfast sai ya tafi gidan hajiya kaka dan abba yace mishi tana can gidan.
Yana shiga ya ganta kwance a parlour sai bacci take gefe guda kuma kufin madara ne tasha ta rage ya tsuguna a saitin fuskarta yana kallonta. muryar hajiya kaka yaji daga bayan shi tana cewa.
“Sai yau zaka zo dubiyar Muhammadu?”
“Afuwan hajiya ta wallahi bani da labari sai d’azu abba ya buga yake gaya min, ya jikin nata?”
“Gata nan dai, yarinya duk tasa damuwa a cikin zuciyarta ga shegen fad’in ran tsiya ana mata magana tana kallon mutane a d’age.”
Mamaki ya kama Sultan jin yau hajiya kaka da kanta take fad’ar haka akan baby, duk yadda aka yi ta kaita bango ya kalleta bayan ya zauna sosai yace.
“Hajiya wai me yake had’aki da baby ne kwanan nan?!”
“Oho kawai ni bana son wannan halin da take ciki, nace ta gaya maka tak’i toh bansan uban wa zataje ta sanarwa da damuwarta ba sakarya kawai…”
“Sorry hajiyata zan kuma tambayar ta amma nima nayi iya yina akan ta sanar dani damuwarta tak’i, sai dai zan kuma tuntub’arta inji..”
Guri ya samu ya zauna a kusa da ita zuciyar shi cike da tsananin tausayin ta,sama-sama suke d’an ta6a hira da hajiya kafin ta mik’e ta shiga cikin d’akinta,shi kuwa yana ganin tabar gurin tamkar jira yake yi ya ciro wayar shi tare da nemo sunan Nadiya ya kirata suka hau hira tamkar sun dad’e basu ga junansu ba.
Ya shagala da zazzak’ulo kalaman k’auna masu ratsa zuciya bema san cewar Balqees ta farka ba sai faman girgiza kafafuwa yake kanshi ya d’ora a gefen kujerar da take kwance da alamun kuma yana jin dad’in yin hirar.
“Uhm..uhm, ni dai kawai kin barni da kewarki ko dai nasa axo’a d’aukeki kema kiyi dubiyar sai mu dawo tare kinga dai ak’alla ina tare dake face to face…?!”
Batajin abinda Nadiyar ke cewa sai dai taji yayi murmushi mai sauti yace.
“Uhmm nak’i wayon yanzu zan taho me kika tanadar min idan na dawo….?”
Story continues below

“Kai ban yadda ba bana son shi sake wani…no..a’a shima…tunda kin rasa me zaki bani toh ki tanadar min kanki.”
Balqees najin haka ta kuma rufe idanuwa,ta kuma jin yayi murmushi ya gyara zama,
“Eh ni ke nake so dan haka sai ki shirya irin na d’azu zamu yi..”
K’irjin Balqees ya kuma bugawa jikinta ya hau rawa tamkar an jona mata shock ya kuma cewa.
“Ok tom sai na dawo a shafa min boobs d’ina ace musu nace I miss them..”
Ita kanta Nadiya kashe kiran tayi sabida nauyin maganar tashi bare Balqees da take jin maganar a gabanta, nan da nan jikin ya kuma tsananta yin rawa ta fara rasa nutsuwarta hakan yasa shi janyo hankalin shi fuskar shi fal murmushi ya waigo yana kallon Balqees da mamaki ya rankwafo kanta ganin jikinta na faman rawa yasa hannu tare da rik’o nata yace.
“Baby kin tashi, sannu ya jikin naki…?!”
Kasa cewa komai tayi sabida tsananin shiga rud’ani, ya kuma matsa hannunta cikin nashi ta zame tare da gyara kwanciyar ta tana lumshe ido cikin tattausar murya yace.
“Tashi kici abinci hajiya ta sanar dani cewar olsa d’inki tayi tsanani sosai.”
“Yaya na koshi bana jin yinwa.”
Ta fad’a cikin sanyin murya,
“Me kika ci da zaki ce min kin koshi bayan yanzu aka kawo abincin?ki tashi nace kafin ranki ya 6aci.”
Cikin ranta ta fara mamakin shi,
_”Wato ita da take rashin lafiya yana yi mata fad’a, amma yanzun nan ya gama waya da mai lafiya ras yana lalla6ata tare da gaya mata kalamai na sanyaya zuciya shine ita zai yi mata fad’a dan ita baya sonta.”_
“Ba magana nake miki ba baby.”
Taji ya fad’a idanunshi cikin nata amma sam tak’i sanya natan cikin nashi, ya kuma had’e rai tare da mik’ewa tsaye ya d’agota daga kwancen da take ya zaunar da ita sai faman turo mai baki take yi.
Abincin ya zubo cikin plate ya kuma saka cokali sannan ya koma kusa da ita ya zauna, faten dankali ne daya sha busashen kifi da alaiyahu sai kamshi yake yi ya zauna tare da d’ebowa ya kai bakinta yace.
“Oya ha..!”
Balqees ta kauda kai alamar baza taci ba ya sanya hannu tare da juyo da fuskar tata ya tura mata a cikin bakinta taci tare da had’iyewa da kyar dan ji take yi tamkar zata yi amai. haka ya dinga tura mata har taci kusan spoon biyar yana k’ok’arin Kai mata na shida ne yaji kawai ta kwararo mai amai, gabaki d’aya sai da ta zubar da abin da taci nan hajiya kaka ta fito tagani gaba d’aya ta 6atashi shi kuma ya rik’eta kam sabida yadda yaga tana kokarin amayar da kayan cikinta.
“Sannu baby…”
Ya fad’a yana k’ok’arin kwantar da ita akan kujerar sannan ya tashi ya shiga toilet d’in dake cikin parlour’n yana kwanke jikinshi hajiya kaka kuma tasa me share mata gida yazo ya gyara gurin ita kuma Balqees tana kwance jikinta duk yayi sanyi tamkar bata da laka idanunta a lumshe har ya dawo parlour yana gyara farar vest d’in jikin shi sabida ya cire shit d’in jikinshi sai dai wandon shi wanke gurin kawai yayi dan bazai iya zama da trunks ba a gidan,ya koma kusa da ita yana mata sannu.
Magungunan ta ya 6allo ya bata, da kyar ya samu tasha sannan ta koma ta kwanta sabida sam jikinta babu kwari ya zauna yana shafar kanta a haka ta kuma komawa wani baccin sannan shi kuma ya tashi ya koma gida da nufin sai anjima zai dawo ya sake ganin yadda jikin nata yake.
Tunda ya koma gida be sake fitowa ba sai washe gari, nan fa hankalin Balqees ya kuma tashi ta kuma tabbatar da lallai Yaya Sultan yanzu baya kaunarta yayi aure sam ya dena kulawa da ita tayi kuka har ta godewa Allah.
****
Sati biyu da bikin su Sultan amma be zo yace Balqees ta shirya ta koma can gidan shi ba kamar yadda ya alkwauranta mata sai dai ya shigo gidan hajiya kaka yayi mata zancen fara zuwa skull d’inta ya fita amma sam beyi mata zancen komawa gidan shiba itama kuma tayi shiru taga iya gudun ruwan shi kuma da alama bashi da niyar cewa ta koma d’in.
“Daddy ya kamata kaje kuyi maganar nan da kaka gaskiya na gaji domin ina son yarinyar nan.”
“Oh common my boy, na gaya maka cewar munyi zancen da hajiyan amma tace wai ita dole sai kaje kun dai-dai ta idan ta yadda shi kenan na rasa yadda zan 6ullowa wannan al’amarin.”
“Amma dai daddy ai tana yiwa wasu na dolen, baga broth Al-eemin (Shaheed) nan ba ai baya son Feedoh kuma aka yi auran ba gashi yanzu har da rabo a tsakaninsu ba. Toh nima daddy kasa a aura min ita nasan zata soni nan gaba, tunda ga broth Heemu nan shima shida Jamila ai suna zaune kuma karkaga yadda yanzu yake sonta gaskiya daddy kayi wani abun.”
Alhaji Abduljalal ya kalli sweet son d’in nashi cikin lallashi yace,
“Shikenan karka damu daga yanzu ka fara shirye-shirye domin kamar ka auri Maryam ne zance na sanar da ita da kuma hajiyan zan kuma nuna mata example da yadda tayi wa na baya.”
“Yauwa daddy shi yasa nake sanka sabida kaima kana son farin cikina.”
Alhaji Abduljalal yayi murmushi cike da jin dad’i sannan suka ci gaba da tattaunawa akan yadda zasu 6ullowa lamarin akan gadan Balqees koda sunyi aure.
Yau kimanin sati hud’u kenan da yin auran sai a lokacin ne Sultan yaxo ya sami hajiya kaka akan cewar yana son ya tafi da Balqees can gidan shi sai dai Hajiya kaka ta kalleshi tace…..
*”T*oh ita yanzu tace ta fasa zuwa gidanka, anan gurina zata ci gaba da zama ta dinga zuwa makarantar daga nan ai zata iya nan dai da north west tace min zata tafi da kanta sai kayi hakuri kuma.”
Zaro idanuwa yayi cikin tsananin mamaki yana kallon hajiya kaka, mirgina Kai yayi tare da dafe goshin shi yace.
“Haba hajiya kaka, ke yanzu sai kika yadda da abinda tace? gaskiya ba zai yiwu ba can zata koma ni zan dinga kaita ita da Nadi, ita yanzu har ta kai munzalin da zata ce wai a barta tayi abu da kanta za ta iya?!”
“Kai! Wai me ka mayar da yarinyar nan ne? Yan zufa idan baka manta ba tana cikin shekaru na sha tara sauran ‘yan wattani dan dai kawai bata da tsawo ne duka-duka da shekaru nawa matar taka zata girmeta amma duk kabi sai maida yarinya kake ‘yar kankanuwa…”
“Haba kaka ai baza ki ma had’a Nadi da baby ba, Nadi fa 23 ita kuma ko 19 d’in ma bata cika ba kinga akwai tazara me yawa a tsakaninsu. dan Allah ki barta mu koma.”
“Baza taba nace..!”
Yaji ta kuma fad’a cikin fad’a da had’e rai sai ya fara tunanin ko wani abun yayi mata ba tare da ya sani ba, tashi yayi ya nufi bedroom d’in Balqees d’in sai faman sake-sake yake yi har yayi norking amma bata bud’e ba kawai yayi kundun balan bud’ewa ya shiga.
Tararwa yayi bata ciki da alama tana cikin toilet kasan cewar yaji motsin zubar ruwa daga ciki hakan yasa shi juyawa yafita. Compound ya fita ya zauna saman motar Nadiya kasan cewar da motar yazo, mintuna kad’an ya d’auka sannan ya sake komawa cikin d’akin, tsaye ya ganta a gaban madubi tana sanye cikin wando blue jeans da ‘yar k’aramar riga gefe kuma wayar tace ta sanya wakar India kasaam-kisaam tana tsaye tana shafa lotion tana rawa har wani d’aga gashi take yi daga keyar ta sam baganshi ba dan haka hankalinta kwance take yin rawar.
“Ke..!”
Balqees tayi saurin waigowa suka yi ido hud’u da Sultan kafin yayi magana ya jiyo muryar Yusif da daddyn shi sun shigo daddy ya wuce gurin hajiya kaka shi kuma Yusif yayo d’akin Balqees d’in dan yaga Sultan a tsaye a bakin k’ofar.
“Yaya zulkallain ina yini..?!”
“Hi guy..”
Yusif ya fad’a kafin Sultan ya amsa gaisuwar da Balqees d’in take mai, kallon juna suka yi ita kuma ta d’auki hula ta sanya a kanta gashi rigar jikinta k’aramin hannu gare ta dan haka Sultan yake ta faman hararar ta amma bata gane ba ta zauna bakin gado tana k’ok’arin kashe wak’ar da ta kunna, cikin gadara Yusif ya ratsa ta gefen Sultan ya shiga ciki yana mata wani shu’umin kallo.
“Wifey nah…!”
Balqees tayi mai banza tamkar bataji abinda yake fad’a ba dan abun da yayi mata ya kasa goguwa daga zuciyar ta, cikin halin ko’in kula Sultan ya kalleta shekeke yace.
“Ki sanya hijjab d’inki sannan ki d’ebo kayanki ina jiranki a waje..”
Yana kaiwa nan yabar d’akin yayin da ita kuma ta zaro ido tabi bayan shi da kallo cike da mamakin shi.ji tayi Yusif na shafar gefen kuncinta tayi saurin mik’ewa tsaye cikin 6acin rai tace,
“Wai Yaya Sufee mekake nufi akaina ne? wallahi ka uzzara min wannan wane irin d’abi’ace kake zuwar min da ita? kodan kaga ba a gaban iyayena nake ba shi yasa kake son 6atamin rayuwa…?”
Story continues below

Gyara zamansa yayi bayan ya d’an matsa kad’an daga jikinta, kallonta yayi idanuwanshi kal-kal tamkar ana samusu Klin dan tsananin haske hancin nan zuwit tamkar ya d’orashi.
Saurin Kawar da kai tayi gefe dan zuciyarta zata iya sanyata yin abinda bada so.
“Zaki aure ni.?”
Taji ya fad’a sai ta tsuke fuska tace,
“Nidai Yaya Sufee kayi hakuri kaga by know karatu zan fara.”
“Ok na gane nufinki qees-qees, I love you you love him ko? na gano hakan ni ai tuntuni.”
Saurin kallonshi tayi tana faman zare ido cikin tsananin mamaki bakinta na rawa tana son yin magana amma ta kasa Yusif yayi murmushi na gefen baki sannan ya mik’e tsaye tare da furzar da iskar bakin shi ya cusa hannunshi cikin aljihunan wandon shi ya tsaya a gabanta kamar zai rungumeta cikin k’asa-k’asa da murya yace.
“Kiyi tunani wannan guy d’in ba auran ki zai yi tunda har kikaga yayi aure dan haka ki saki ganye ki kama reshe nan bada wani lokaci ba zan mallakeki kyayi karatun a d’akin ki.”
Yana kaiwa nan yayi parlour ta biyo bayan shi tana cewa.
“Ni dai Yaya Sufee ka rabu dani babu wani auran da zanyi ai ance ra’ayi riga dan haka ka rabu dani babu lallai ba dole tunda nace a’a…”
Sam bata san akwai daddy a parlour’n ba suka had’a ido tayi saurin yin k’asa da kai tare da cewa.
“Daddy ina yini..?!”
Ba tare da ya amsa mata ba ya juyar da kanshi tare da kiranta alamar taje kusa dashi, shi kunyar ma nemarwa Yusif d’in auranta yake yi sabida k’ank’antar ta da yake gani. K’arasawa tayi ta zauna duk tanajin kunya sai faman sunkuyar da kai take yi tana kuma yin wasa da yatsunta yan kubul-kubul dasu.
“Balqees dama abinda yasa muka zo gidan nan yanzu so muke muji ta bakinki domin a fita hakk’inki, shin zaki auri yayan ki Yusif ko kuma kina da wanda kike so..?!”
Taji daddy ya watso mata wannan tambayar,shiru tayi kafin ta kalli inda hajiya kaka take wadda ta had’e rai sannan ta kalli inda Sultan yake gani tayi babu komai a fuskar shi sai ma matsar wata ‘yar bear yake yi tayi shiru tana neman abin fad’a.
“Ke muke sauraro domin kinsan muma mahaifanki ne muna da right d’in kula dake haka kuma mune zamu aurar dake ina son jin ta bakinki.”
Da kyar ta samu damar yi mishi magana cikin rawar murya tace.
“Daddy ni yanzu karartu zan fara, bana jin son yin aure kurkusa ba wai kuma dan bana son Yaya Sufee bane.”
“Ai Balqees aure baya hana yin karatu, haka ma karatu baya hana aure, so muke muji ta bakinki in yaso sai ayi komai a sanya rana.”
Shiru tayi ba amsa kirjinta sai dukan d’ari-d’ari yake gashi ya kafeta da ido yana jiran jin ta bakinta.
“Ke nake saurara sauri nake yi akwai inda zani.”
“Daddy akwai wanda zuciya ta take so, kuma shi nake son aura.”
Da sauri daddy yace,
“Yauwa toh a ina yake dan kinsan bawai haka kurum zamu aura miki wanda kike so ba dole sai anyi bincike dan sanin nagartarshi.”
Kanta a k’asa yayin da hajiya kaka ta kafeta da idanuwa tana jiran jin abinda zatace, shi kuma Sultan murmushi yayi dan yasan Yazid ne sabida yasan shine yake kan star d’in manemanta, yana can yana shafar kwantaccen quarter million d’in fuskar shi yaji tace.
“Daddy shima nagartacce ne kuma nasan zaku zaku yaba da za6ina domin Yaya Sultan Ahmad ne…!”
A razane Sultan ya d’ago yana kallonta bakin shi bud’e jikinshi sai rawa yake tamkar ba namiji ba Yusif ya buga hannunshi a akan kujerar da yake kai yace.
“Daddy kaji ko? Dama na gaya maka mutanan nan sun riga sun san juna, wallahi toh baku isa ba ni naji na yadda zan aureta a haka dan shi yaudararta kawai yake yi sabida gashi ya sami abinda yake so a jikinta har ma ya auri wadda yake son yayi zaman aure da ita..”
“Ya isheka haka Yusif tunda kai baka da hankali baka san me kake yi ba, ke baby….”
Hajiya kaka tayi saurin katse shi dan ba k’aramin burgeta Balqees tayi ba yau ganin zai kwafsa mata yasa ta dakatar dashi ta hanyar cewa.
“Kai Muhammadu yi min shiru Karna sake naji bakinka a gurin nan, kuma duk abinda Yusif yace nasan karya yake yi tunda yarinya ta riga tayi magana shikenan.”
Zaro ido ya kuma yi yana kallon hajiya kaka, Yusif ya kalli daddyn shi yana wani kumbura fuska yace,
“Dad kaji fa!kaji abinda kaka ke cewa, hmm dama ai akan idonta suke duk iskancin da suke yi tayi shiru sabida sune na gaban goshinta, toh wallahi baza ta sa6u ba gara ma asan abin yi ni na yadda zan zauna da ita a haka zan kula da ita sabida maraicinta.”
“Innalillahi wa’innailaihir raji’un…”
Sultan yake ta maimaitawa a fili sai uban gumi yake yi tamkar ba iska a cikin parlour’n, jijiyoyin jikin shi duk sun mik’e tamkar wanda yake excesses idanuwan shi sun kad’a sunyi jawur dasu yaji daddy na cewa.
“Karka damu Yusif zanje na samu Yaya (abban sultan) zamu yi maganar dashi zaka auri Balqees domin bata da miji sai kai ka kwantar da hankalinka.”
A hankali Sultan ya mik’e tsaye zai fita hajiya kaka tayi saurin cewa,
“Karka tafi ka bari ku tafi tare kamar yadda kazo d’aukarta, idan kuma ka fita baka tsaya kun tafi tare ba a bakin ubanka….”
Jin haka yasa shi tsayawa cak ba tare da ya waigo ba sannan ta kalli Balqees tace,
“Baby tashi kije ki d’akko kayanki ki bishi Allah ya bada sa’ar karatu.”
A sanyaye ta mik’e jikinta duk yayi sanyi dan ganin yadda ran Sultan d’in ya 6aci da alama ma ko san ganinta baya yi _anya zata iya binshi kuwa kar fa taje tasha wulakanci tana tsoron faruwar hakan amma ba yadda zata yi dole ta bishi dan gujewa Yusif da abinda ya kudurta akanta_.
Katuwar trolley ta fito da ita tana janta da kyar taje ta wuce zata fita sultan yayi saurin k’arasawa ya kar6a ganin sai uban nishi take yi. fita yayi da ita yayin da Balqees tabi shi da kallo tana tunanin ko ya hakura ta jiyo su daddy na yiwa hajiya kaka magana tare da cewa,
“Sai munzo hajiya akan d’aurin auran.”
“Jalal kenan me d’ah.”
Haka kurum ta fad’a tana binsu da kallo har suka fita sannan ta kira Balqees ta k’arasa wajan ta hajiyan tace.
“Kiga yaron nan yaji haushi wannan yaron bada soyayyar aure yake miki duk wad’annan abubuwan ba dan haka sai nasa baki a cikin al’amarin nan amma zaki sha wahala baby domin idan aka yi aure miji baya sanka toh bazaka ta6a jin dad’in zaman ba gashi yana da wata kuma yana sonta bazai iya 6oye kaunarta a gaban idonki ba ke kuma macace ba zaki iya daurewa ba ya kamata kije kiyi shawara sannan ki dinga bawa samari damarki dan wata k’ila Muhammadu ba mijinki bane, wannan wawan kuma ki barni dasu daga shi har sakaran mahaifin nashi.”
Balqees na hawaye ta d’agawa hajiya kaka kai sannan ta mik’e ta fita jin sai zabga musu horn yake yi. Tana zuwa ta bud’e ta shiga jikinta duk yayi sanyi, ba tare da yace mata komai ba yaja motar suka bar cikin gidan.
Ganin bashi da niyar yi mata magana yasa ta tace.
“Yaya Sultan kayi hakuri ban fad’i hakan ba sai dan na ceto rayuwa ta daga fad’awa tarkon Yaya Sufee, na fad’i hakan ne dan a rufe babin Yaya Yusif ganin cewar kaine kawai zan iya fakewa a inuwar ka na ji dad’i kamar yadda kake cewa zaka zamo mai share min hawaye a duk sanda zasu zubo, sai gashi ka gaza, shi yasa aka ce duk wanda ya rasa iyayansa hakika yayi mugun rashi, kayi hakuri ka gafar ce ni ba nufina na 6ata maka rai ba..”
Da k’arfi ya ja wani uban….
*D*a k’arfi yaja wani uban birki a tsakiyar titi wanda hakan yasa Balqees kwallara k’ara tare da rintsa ido dan duk a tunaninta sunyi accident ne.
Kallonta yayi idanunshi sun kad’a sunyi jawur sannan ya gangara motar gefe duk suka yi shiru kowa da abinda yake sak’awa, kusan awa d’aya suna zaman shiru can dai Sultan yace,
“Baby! Kiyi hakuri bawai haka nake nufi ba, kinga maganar aure ba’ayi mata wasa why kike yin haka? Shin har yanzu kina nufin babu wanda kika tsayar? kin san kuwa halin daddy kuwa? Hmmm daddy mutum ne wanda ya fiye son kai, yana matuk’ar nuna cewar nashi shine nashi babu ruwanshi da yadda suke da mutum kuma nasan indai yaje gurin abba toh babu shakka auranki da Yusif sai dai wani ikon Allahn amma sai anyi shi ni kuma bana son ki aure shi. me yasa baza ki bawa Yazid damarki ba? abokina ne gurin aikin mu d’aya kuma nutsatse ne yana da ilimi ki gaya min ko auran ne baza kiyi ba?!”
A hankali cikin hawaye Balqees tace mai,
“Zanyi Yaya zulkallain, ina son dai kawai ka taya ni da addu’a Allah ya za6a min mafi alkairi.”
“Amin.”
Ya fad’a sannan ya tada motar suka k’arasa gidan shi, lokacin Nadiya na kitchen ita da mai yi mata moping tana taya ta aiki. Tana jin sallamar shi ta d’aurayo hannunta ta fito tana fad’in.
“Oyo-yo be mine..,ahhh lallai kace yau za ayi mana ruwa da manyan k’ank’arori tunda yau ga daughter a gidan mu.”
Tayi maganar tana k’ok’arin k’arasawa wajan Balqees Sultan yayi saurin tare ta ya kama hannunta yana kashe mata ido d’aya tare da mirgina mata kai yace,
“Ni baza ki min sannu da zuwa ba zaki tafi gurin baby?!”
Murmushi tayi ganin yadda yayi kalar tausayi sannan ta sanya d’ayan hannun da be rik’e ba ta rik’e kunnanta tace.
“Sorry mijina amma ba haka nake nufi ba.”
Sakin hannun yayi ya wuce bedroom yana cewa,
“Ban hakura ba sai kisan yadda zaki yi dani.”
Kai ta girgiza tare da k’arasawa wajan Balqees wadda take ta yin yak’en dole amma zuciyar tafarfasa kawai take yi Nadiya tace.
“Sannu da zuwa muje ki huta kici abinci.”
Jan hannunta tayi, cikin wani d’aki ta kaita wanda aka k’awata shi da kayan wasan yara komai na ciki kalar lemon green ne da white daga gani aikin Yaya sultan ne domin yasan best colors d’inta sai dai ya mugun raina mata hankali ganin irin kayan wasannin da ta gani a cikin d’akin sai kawai ta yi murmushi tare da kallon Nadiya tace,
“Nagode sosai.”
“Shhhhh karki kuma yin godiya yanzu kiyi wanka sai ki fito parlour.”
Balqees tace “Toh nagode.”
Sannan Nadiya ta fita, bedroom d’in shi ta bishi tsaye ta ganshi d’ure da towel da alama wanka zai shiga ta k’ara inda yake kamar jira yake dama yayi saurin janyota jikin shi ya had’e kirjinta da nashi kafin ya jata zuwa kan gado sai dariya suke yi.
“Wanka zanyi amma ba zanyi a banza ba sai nayi.”
Yayi maganar yana wasa da dukiyar kirjinta fuskar shi sai zagaye sassan jikinta yake yi tana dariya tace.
Story continues below

“Dama ana yin wankan banza ne?!”
Ya shafa kitson kanta yana mata wani irin kallo yace,
“Sosai ma kuwa musamman idan mutum yana da mata kuma lafiyarta kalau ba mensuration take ba kamar dai yanzu ni dake.”
“Uhmm ni ban ta6a jin haka ba sai yau.”
“Eh ai gashi yanzu kinji dan haka…”
Yana fad’a ya hau jujjuya ta itama tana taya shi daga haka har suka raya lokacin sannan suka yi wanka lokacin Balqees har ta gaji da zaman jiran fitowar su ta koma d’akin da aka bata tana ta tunanin abinda ya dad’ar dasu a cikin d’aki.
Sai da suka shirya sannan suka fito mak’ale da juna dai-dai sannan ita kuma Balqees tazo fitowa sai tayi saurin komawa cikin d’akin da sauri ba tare da sun ganta ba ta dafe k’irjinta da hannu tare da lumshe ido tana tunanin an kawo tane gidan kawai a halakata.
“Baby..!”
Tajiyo muryar shi yana kiranta tayi saurin mik’ewa ta gyara zaman skirt d’inta sannan ta fita tana murmushin yak’e.
“Kin wani shige cikin d’aki sai kace wata bakuwa, zo nan ki zauna..”
Sultan ya fad’a yana nuna mata kan kujera wa’inda aka k’awata parlour’n dasu, k’arasawa tayi ta zauna fuskarta a sake yayin da Nadiya ta kawo musu drink’s da snack’s d’in da tayi sannan ta zauna kusa dashi suka fara hira ita dai Balqees daga eh sai a’a sai oh shi kenan abinda take ce musu sabida iya kuluwa ta kulu da yadda taga sun ware ta suna ciyar da junansu cike da tattalin juna da nuna kauna basu san lokacin da tabar wajan ba sai da Sultan d’in yace zai je gidan Umman shi sannan yaga bata gurin, d’akinta ya nufa kwance ya tarar da ita tana daddanna waya ta d’ago ta kalleshi ya sakar mata murmushi tare da shiga ciki ya zauna kusa da kafafuwanta yana kallon yanayin d’akin yace.
“Baby ya kika ga d’akin hope dai komai yayi miki yadda kike so.?”
“Komai yayi Yaya na gode kasan duk abinda nake so.”
Ta fad’a tana ‘yar dariya amma a ranta cewa take.
_”sai dai ka kasa gano halin da nake ciki game da kai Yaya nag.”_
“Ol-right baby you’re free kiyi komai a cikin gidan nan amma banda yiwa Nadiya rashin kunya kinga tana sonki karkiji yadda take murnar zuwanki gidan nan dan Allah ku zauna lafiya kinji baby?!”
“Toh Yaya insha Allah…”
Janta yayi da ‘yar hira kafin ya tashi ya tafi gidan Umma.
****
Kwanan Balqees uku da zuwa gidan abban Sultan yace taje yana nemanta dan haka Sultan ya shirya ya d’auke ta ya kaita. A zaune suka tarar su Umma,Mommyn Yusif,abba da shi kanshi Yusif d’in suka k’arasa suma suka zauna sannan suka gaisa jikin Balqees duk yayi sanyi tunda ta sunkuyar da kai kuwa bata d’ago ba har abba ya fara magana.
“Akan abinda ya taramu anan nasan kowa ya sani dan haka ‘yata dawo nan kusa dani zan miki magana.”
Da rarrafe Balqees ta k’arasa wajan abba dan baza ta iya mik’ewa ba kafafuwanta duk sunyi mata sanyi taje ta zauna a gefenshi ya shafa kanta sannan yace.
“Allah ya gafartawa su Abdul-raheem yasa aljanna makoma ce a gare su muma ya ji k’an mu idan mun koma gareshi.”
“Amin..amin.”
Duk suka fad’a baki d’aya sannan abba yaci gaba da bayani har tsawon lokaci kafin ya kalli Balqees yace,
“Mun yanke shawara nida daddyn ki dan cikawa d’an uwanmu ga6ar da ya bari a duniya dominki wato aure, mun yanke shawarar cewa zamu had’aki dake da yayanki Yusif da fatan zaki abince da za6in mu.”
Story continues below

“Sam bata yadda ba ahe, munafincin banza dana wofi ni zaku gulmata? Karku manta duk cikin ku babu wanda ban haifa ba bare ko raina min hankali, da kune kuke had’in auran? Idan kun manta bari na tuna muku, ni da Bilkisu matawalle da kaina na had’a auran Jamal da jawaheer sannan na had’a Aminullahi da Fiddausi, haka kuma na had’a Ibrahim da Jamila duk suka yi biyayya a gareni, amma kai..!
Ta nuna Yusif cikin 6acin rai sannan taci gaba,
“Kaine ka fara watsa min k’asa a ido ubanka kuma ya goyi da bayanka kace baza ka auri bilkisu ba, sai me binka a baya Muhd da shima ya watsa min k’asa a ido yace baxai auri Aishatu ba sai yanzu zaku yi maganar banza, au kun d’auka nayi tsufan da zan dinga manta abinda ya faru ko? Toh ras nake in gaya muku kuma baby baza ta auri Yusif ba domin itama tana da wanda take so a’h’e.”
Gabaki d’ayan su tabisu da kallo su kuma tsananin mamakin ganinta yasa suka kasa cewa komai, alamar hakan ta gani akan fuskar su dan haka tace.
“Duk wani shirye-shiryan ku na sani, shi yasa kuka ganni. Kai Muhd tashi ka maida ita gida baza ta aure shin ba, ai duk cikin ku babu wanda ya kaini iko akanta dan haka nice uwarta ni kuma ce ubanta tashi nace maka.”
Cike da murna sultan ya mik’a sannan itama Balqees d’in ta mik’e suka fita. Nan fa Yusif ya fara rashin kunyar tashi musaman yanzu da yake son yin aure yana da ‘yan matan kwalisa na bugawa a jarida amma yafi son ya auri Balqees sabida yanzu itace a cikin zuciyar shi.
Sim-sim ta mik’e tabi bayan sultan suka fita, abba kuwa duk kunya ta kama shi ganin lallai yayi ragwan azanci wajan yin wannan abun dan haka ya k’arasa wajan hajiya kaka tayi saurin d’aga mai hannu tare da juyawa tabar gidan dama a napep tazo dan haka anan ta koma dan lokacin su sultan sun bar compound d’in.
“Daddy rabu dasu ai ba ita kad’ai bace ‘ya mace a duniya ba na hakura da ita har abada.”
Yusif ya fad’a cikin zafin rai tare da fita daga parlour’n yana wurgi da duk abinda ya gani a hanyar shi ta wucewa.
Shima daddy ya kalli matar shi sannan yace,
“Muje ko..?!”
Tayi sallama da Umma sannan suka fita har suka je gida suna tattauna zancen a mota tare da mamakin yadda hajiya kaka ta kafa ta tare akan Balqees d’in.
****
Tun daga lokacin Balqees ta samu sake takurawar Yusif da fargabar me zaiyi mata duk babu, karatun ta yanzu take yi hankali kwance hatta Yaya sultan yanzu tayi watsi da al’amran soyayyar shi ba wai kuma dan ta dena sonshi ba kawai dai tsananin yin addu’a ne yasa Allah ya sassauta mata.
A 6angaran zaman su da Nadiya kuwa sai son barka domin suna zaune lafiya idan suka dawo kowa ya dawo daga school tare suke yin girki sannan kuma tare suke ci sam Nadiya bata nuna bak’in cikinta akan yadda taga sultan yana kulawa da ita tamkar zai maida ita ciki dan tasan duk kulawar shi baxai iya bata kanshi ba.
Lokacin da waheeda ta haihu matar Yaya Jamal Nadiya da kanta ta siya kayan barka masu yawa da tsada ta aikawa da Umma nan ta dinga godiya sannan ta kuma siyan wasu ta samu Balqees zaune a d’akinta tana browsen ta kalleta tayi murmushi tare da cewa,
“Sannu da zuwa Maman baby na.”
Nadiya ta zaro ido jin abinda Balqees tace, zama tayi tare da kura mata ido tace mata.
“Ya aka yi kika sani?!”
“Hahaha wallahi ni yanzu na k’agara ki haihu Allah yasa macace tare zamu dinga kwana ina yi mata kitso…”
“Naji duk abinda kika ce amma ya akai kika san akwai?!”
“Ta hanyar ganin test trip d’in da kika yar a cikin dosbin.”
Nadiya ta dafe goshi tare da rufe ido tace.
“Daughter dan Allah ya zama secret tsakanin mu karki gaya mai kinji ko?!”
“Sabida mene? Gaskiya a gaya mai yaji shima ya godewa Allah.”
“Ni dai kiyi min alk’awari dan Allah.”
“Toh na fasa bazan gaya mishi ba Maman baby.”
Nadiya tayi murmushi tare da kawar da zancen ta hanyar d’ora mata ledar hannunta tana cewa.
“Ga wannan kayan ki kai naki ne na barka da zaki bawa yayya waheeda ni nakai nawa.”
Da sauri Balqees ta rungume Nadiya tana mata godiya, tana fita ta bud’e kayan ta gani sannan ta kifa kai tana tunanin _gaskiya be dace tayiwa Nadiya haka ba sai dai ya zata yi?ta kamu da soyayyar Sultan tun kafin tasan meye ake nufi da so amma zata ci gaba da dannewa har Allah ya kawo Mata za6inta._
_#yanzu za’a fara_
*A* gajiye ta dawo yau daga makaranta duk tayi wujiga-wujiga da ita domin har wata juwa takeji sabida tsabar jin yinwa, dan haka a gaggauce ta shiga cikin parlour’n karaf ta hange su a zaune akan kujera yayin da Nadiya ke zaune a saman cinyar shi sai zabga shagwa6a take shi kuma yana tarairayar ta kamar k’aramar yarinya.
Yana shafar cikin ta yana magana,
“Wai baza ki gaya min ba how many months…?!”
“Months kuma? ka ta6a ganin ance wa te6a wata nawa?ni bani da abinda kake nufi garama ka kyaleni..”
Ganin sai musu suke yi yasa Balqees dake mak’ale bakin k’ofa tayi kundun balan shiga ciki ba tare da ta kallesu ba tace.
“Sannunku da gida Yaya.”
Sultan yace,
“Yauwa baby zo dan Allah ki gani dan Allah wannan tudun cikin na meye…?!”
Balqees ta kalleshi cikin mamaki da alama tana tunanin ko be san yayi mata tambayar ba tayi shiru ya kuma kallonta tare da maimaita mata abinda ya tambayeta nan da nan suka had’a ido da Nadiya wadda ke ta faman girgiza mata kai alamar karta fad’a mishi dan haka ta ta6e baki tana gyara suwaga bag d’inta tace.
“Yoni Yaya taya za’ayi na gane kumburin meye nida ba ma’aikaciyar lafiya, sai dai kakaita asibiti a gano maka matsalar ni kam ban sani ba..”
Ta fad’a tana yatsina fuska ji take tamkar ta makeshi ganin yadda duk ya kanainaye Nadiyan sannan tayi hanyar d’akinta tana jiyo shi yana cewa.
“Kona rantse bazan yi kaffara ba akwai ajiya ta a ciki har tama fara girma, no wonder naji kin k’ara dad….”
Nadiya tayi saurin toshe mai baki dan lokacin Balqees bata k’arasa shiga cikin d’aki ba Sultan ya d’auke ta suka nufi d’akin kwanansu yayin da Balqees ta shiga d’akin tare da fad’awa kan gado tana sauke ajiyar zuciya, jin k’irjinta na zafi yasa ta had’a black tea ta zuba kal-tufa tasha sabida olsar ta sannan ta d’auki waya ta kira k’awarta wadda tayi a makaranta mai suna Sadiya tana d’agawa tace.
“Sdy na shiga uku wad’annan mutanan zasu kashe ni.”
“Tofa yau kuma me suka yi miki Balqees?!”
“Kin san kuwa yana gida amma beje ya d’auke ni ba, dana dawo ma ya ganni amma ko yace min ga dalilin daya hanashi zuwa d’auka taba, koda yake na gani yana tare ne da Nadiya ne.”
“Toh shine me? Kina nufin karya kula da matar shi bayan kince min tana da juna biyu a yanzu? Ke kinga idan zaki barsu ki barsu kizo kema kiyi kokarin yadda zai gano irin soyayyar da kike mishi zaki wani tsaya kisawa kanki tension.”
“Toh sdy anya zan iya kuwa, wallahi idan ya gano ban san yadda zanyi ba.”
“Kinga idan zaki bi hanyar dana gaya miki kiyi idan kuma bazaki yi ba karki k’ara gayan matsalarki sai anjima.”
Tana kaiwa nan ta yanke kiran yayin da Balqees ta kifa kanta a kan pillow tana tuna nin tayi abinda sdy ta gaya mata kokuwa dai ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido.. da wannan tunanin bacci ya d’auke ta ba tare da ta yanke shawara guda d’aya ba.
***
Kwana ki suna ta tafiya har dai cikin Nadiya ya fito ta yadda kowa yake iya ganewa domin har yakai watanni bakwai. Sultan, Balqees da Umman shi suna matuk’ar kaunar cikin ji suke tamkar su maida su cikunan su hakan yasa Nadiya ke shan gata dan babu abinda suke bari tayi komai na gidan yanzu Balqees ce da Sultan suke yi wanka kuwa indai yana gida shi yake mata dan yashe sokewa students d’in shi lectures yace suyi hakuri bazai samu damar zuwa ba.
Story continues below

Lokacin da cikin Nadiya ya shiga watan haihuwa dama suna cikin hutu dukan su dan haka sai abin yazo musu da sauki wanda har lokacin Balqees bata samu damar yin abinda sdy tace tayi ba.
Cikin dare Nadiya ta tashi da nakuda hankalin Sultan ya tashi nan ya kira Balqees suka had’u suka kaita asibiti suna zuwa aka shiga da ita labour room, tun wajan 3:15am har k’arfe 6:30am gaba d’aya ta wahala har an fara tunanin yi mata c.s Allah ya temaketa ta haifi ‘yarta budurwa tabarakallah.
Kwananta biyu a asibiti aka sallame su drictly aka wuce da ita gidan su cewar Umma duk kuwa da cewar shi Sultan ba haka yaso ba amma ba yadda ya iya dole yana ji yana gani aka kaita sannan aka d’ibi kayanta, kullum yana hanyar zuwa gida ba dare ba rana har washe garin suna da yaje suna zaune a sitting room tayi wani kyau kamar ba jego take yi ba an yi mata kunshin ja da bak’i kanta yasha gyara duk da cewar dama kusan kullum haka yake amma na yau na musamman ne ya jata jikin shi yana shak’ar k’amshin jikinta yace.
“Kamar bake kika haihu ba, kinyi wani fresh alhalin ko suna ba’ayi ba.”
“Uhmm a haka ba amma ni kad’ai nasan yadda nake ji wallahi, wannan d’inkin duk ya takura min da kyar fa nake iya tafiya..”
Ya kuma matseta a jikinshi kafin ya d’agota ya kalleta yace.
“Tashi na gani yadda yayi idan da matsala mu koma asibiti.”
‘Yar hararar shi tayi cikin shagwa6a tare da d’an turo shi ganin yana niyar d’aga mata zani tace.
“A’ah babu abinda zaka gani ko ka manta a tushe gurin yake da pad, kuma ma ance is normal wai sai na d’an kwana biyu ina shiga ruwan zafi sannan zan denaji.”
Cikin kalar tausayi Sultan ya shafa kanta tare da kissing d’in saman lab6anta yace,
“Sorry kinji wai ina baby d’ina ne ko Ummi ta 6oye ta dan taga sabuwar kishiya?!”
Dariya suka yi tana manne a jikin shi sai jin sallamar Balqees suka yi domin itama tun ranar da aka taho da Nadiya itama kullum tana gidan sai yaje tukunna yake taho da ita da kyar sabida bata son barin baby.
K’arasawa tayi ciki dan tasan ba sakin Nadiyan zai yi ba dan ta gansu hakan yasa itama taje tare da mik’a mai yarinyar ya sa hannu ya kar6e ta.
“My sweet dreams, my Aishat Allah ya raya min ke yasa ki gaji halin mai sunan.”
Gabaki d’ayan su suka kalleshi dan sai yanzu ya fad’i sunan da zai sanya mata, ai kafin Nadiya tayi magana tuni Balqees ta k’arasa jikin shi tare da rungume su shida baby d’in tana kuka, baki bud’e Nadiya ta bita da kallo jin irin kukan da takeyi kafin taji ta d’ora da cewa.
“Na gode Yaya Sultan hakika kai d’in me tsananin kulawa ne a gareni, kabani farin ciki baka son ganin duk wani bakin ciki nawa, yauma gashi ka k’aramin ta hanyar sanyawa ‘yarka jininka sunan mahaifiyata na gode Yaya bani da abinda zan iya biyan ka, kullum a gurinka nake neman alfarma nake kuma cinta Allah ya kara maka bud’i ya baku ikon tarbiyantar da itah.”
Hawaye Nadiya ta share sannan ta kalli Balqees tace,
“Karki kuma yin godiya daughter akan duk abinda kika san yayanki zai yi miki, Allah ya raya mana ita.”
“Amin..”
Balqees ta fad’a can k’asan makoshinta.
Ranar suna yarinya taci sunan Aisha, anyi shagali sosai kamar noman kud’in ake yi su Balqees ankasa an tsare da kyar take barin ‘yan suna su d’auki babyn a haka har taro ya watse ranar a gidan su Nadiya ta kwana.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya daga makaranta Balqees take cewa ya kaita gidan su Nadiya gurin Aisha, shima da yake da kishirruwarta yake kwana ya tashi be ta6a musawa yace a’a ba dan haka ma a can gidan suke dinner da lunch sannan su tafi har Nadiya tayi arba’in ta dawo gidan sultan. Sabuwar soyayya suka bud’e yayin da rainon humaira ya koma hannun Balqees hatta bacci tare suke yi tana jin kaunar yarinyar kamar yadda takejin kaunar mahaifinta a cikin jini da tsokarta.
Lokacin da humaira tayi watanni shida wata rana Balqees tana kwance humaira na saman cikinta tana yi mata wasa da waka kawai ta kurawa yarinyar ido hawaye na bin kuncinta a hankali take cewa.
“Ummi yazan yi da raina da rayuwata akan soyayyar mahaifinki? Ina son shi tun kafin na mallaki hankalin kaina amma na kasa gaya mai shi kuma ya gasa fahimtar inda zuciya ta take akansa baby na me zanyi ya gane ya soni har ya aure ni…?!”
“Ummi nah kice wani abun please.”
Cewar Balqees tana faman girgiza humaira ita kuma sai 6al6alla dariya take irin ta yara, daga bayan ta taji ana bata amsa,
“Ta6d’i jam, ya za’ayi kuwa tayi miki magana tunda dai yarinya bata san abinda kike cewa ba…”
A razane Balqees ta mik’e har da sakin wata ‘yar guntuwar tusa suttt! tsabar kad’uwa da shiga tashin hankali ta waiga wajan k’ofar tana zare idanuwa kafin ta dafe kirjinta da hannu tare da sauke ajiyar zuciya mai tsananin k’arfi ganin ko wacece tayi maganar. Ita kuma ta kwashe da dariya sannan ta rufe k’ofar tare da sanya jamlock ta k’arasa wajan gadon cikin dariyar da tak’i tsayawa Sdy tace.
“Kambala’i Balqees duk tsananin rud’ani ne kin d’auka matar gidan ce yasa ki sakin tu….?!”
“Allah ya isah wallahi domin kin tsoratar da musulma.”
“Muchh malama kika tsoratar da kanki dai, wallahi hakan ma zata iya faruwa inda zaki dinga tisa ‘yar yarinya a gabanki kina sakin sirrin dake ranki, wata rana a kunnan Nadiyan zaki fad’a.”
“Hakan ma baza ta faruba Sdy, na yanke shawarar kawai zanyi abinda kika ce komai fanjama-fanjam, daga gobe za’a fara.”
“Koke fa yanzu kika zama mutum.”
Daga nan hira suka d’an ta6a har kusan magriba sannan Sdy ta tafi gida yayin da Balqees ta koma d’aki ita da Humaira suka ci gaba da zaman su.
Washe gari da yamma bayan ta dawo daga makaranta suna zaune dukan su a parlour Balqees tana yiwa humaira kalba yayin da Sultan keta faman aiki a cikin laptop d’inshi ita kuma Nadiya tana gyara mai farcen k’afar shi baba meh gadi ya kwankwasa k’ofar Sultan yace,
“Waye..”
Mai gadin daga bakin k’ofa yace,
“Bak’o ne yazo wai yana son ganin Maryam.”
Sultan ya wurgawa Balqees wani banzan kallo fuskar shi a mutukar 6ace, ita kuma tayi saurin mik’ewa tsaye ba tare da ta kalleshi ba tace.
“Gani nan zuwa…”
Sultan kuma ya zare kafarshi daga hannun Nadiya yace.
“Ina zuwa naga uban waye yazo min gida…”
Daga haka ya fita fuuuu..
Yana fita kuwa yaga wani yaro a shekaru bazai wuce 22-23 ba duk kusan age mate d’inta ne sultan ya k’arasa wajan shi yaron yana ganin shi ya tsugunna har k’asa yana faman sosa keya yace.
“Good evening sir?!”
Ko kula gaisuwar beyi ba ya kalli yaron tundaga sama har k’asa sannan yace,
“Daga ina haka…?!”
Saurayin yana daga tsugunne yana sosa kai yace.
“Amm sir dama…dama gurin Balqees nazo department namu d’aya da ita.”
“Uhmm ina jin ka.”
Yace,
“Sunana Adam musa kuma..kuma…dama…uhmm.”
Ya kasa k’arasawa sultan yace,
“Tashi tsaye ina sauraronka me kazo yi gidan su?!”
Kafin ya bashi amsa wani arnan kamshi ya turare compound d’in gidan nan da nan kirjin Sultan ya fara bugawa a da sauri ya waiga dan ganin me sanye dashi kawai idanunshi suka sauka akan Balqees tana tahowa sanye cikin wata had’ad’iyar atamfa d’inkin riga da skirt bata d’aura d’an kwali ba sai wani jililin mayafi da ta mak’aloshi daga kanta zuwa wuyanta. Harta k’arasa sultan kallonta yake baki bud’e tana zuwa ta kalleshi tace.
“Yaya ga…..”
TATTALIN MACE – TATTALIN MACE:- Page 30 – Page 3
*🎪🎪 TATTALIN MACE….*🎪🎪
NA
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER’S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer’s)
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
DEDICATED TO:- *AUNTY MAIJIDDA MUSA*🤝
Page *30*
Wata uwar harara yake dank’ara mata amma sam tak’i kallon shi sai da ta fad’i abinda zata fad’a tace,
“Yaya ga Adam.”
Ta fad’a tana kallon Adam d’in tare da sakar mishi tattausan murmushi har k’ananun hakoranta suka bayyana Sultan ya kalleta yace.
“Idan baki koma ciki ba sai na faffalla miki mari wallahi tallahi.”
Ya k’arasa fad’a a daddak’ire, da gudu ta juya ta koma ciki tana kuka shi kuma ya kalli Adam wanda jikin shi yayi sanyi sannan yace.
Adam ya zaro ido tare da girgiza kai bakin shi na rawa yace.
“Dan Allah sir kayi hakuri wallahi bana so.”
Sultan ya kad’a kai sannan ya nuna mai hanyar get yace.
“Toh yi nan karna sake ganin kazo gidan nan, kai ko a school karna sake gani ko jin kayi mata kallon soyayya ko zancen soyayya karatu na kaita tayi kana jina ko…?!”
“Insha Allahu sir a huta lafiya.”
Adam ya fad’a tare da saurin barin gidan shi kuma Sultan ya koma ciki a fusace, rungume ya ganta a jikin Nadiya tana faman kuka ita kuma sai lallashinta take ya kalli Nadiya sannan ya kwashe da dariya yace.
“My Nadi kinga irin yaran da baby take kulawa? Oh my God! wallahi yarinyar nan wawuya ce.”
Wani haushi da takaici ya kuma kama Balqees jin ya kirata da wawuya ta mik’e fuskarta sharkaf da hawaye tace.
“Toni Yaya shi nake so shine za6in raina kuma ya kwanta min a zuciya ta.”
“Are you serious baby?!”
“Eh Yaya.”
Ta bashi amsa tana share hawaye Nadiya kam ta kasa magana ya ja tsaki mai k’afi tare da cewa.
“Wannan yana tabbatar min da cewar ke yarinya ce har yanzu, toh na rabaku dashi bake ba shi kinaji na.”
Cikin kuka Balqees tace,
“Toh Yaya wa kake son na kawo? Nifa ina sonshi.”
“Baby ki samu babba mana mai hankali wanda idan kika kawoshi zamu yadda cewar auranki zaiyi, amma kin kawo wannan duka-duka yaushe aka yaye shi, har yanzu be dena kwana a d’akin Mom d’inshi ba amma ya wanko wando yazo wai ke yaki jira mtww.”
“Yaya ni dai ina sonshi tunda shima yana so…”
“Shirt up stupid girl.”
Ya fad’a ranshi a 6ace yana harararta. Da sauri Balqees ta nufi hanyar d’akinta tana buga kafafuwa tana cewa.
“Ni wallahi bazan yadda ba nace shi nake so ya za’ayi a ce baza a bani ba wallahi sai na gayawa hajiya kaka.”
Koda Balqees ta shiga cikin d’aki tsalle ta farayi kamin ta fad’a kan gado tana mirga-mirgina ta janyo wayarta dake karkashin pillow ta kira kawarta Sdy cikin zumud’i tana d’agawa tace,
Story continues below

“K’awas an gama day 1 Adam yazo ammafa ko bari beyi mun gaisa ba ya wani korani wai na d’akko yaro.”
“Oh haka ma yace? Toh ki rabu dashi the next day sai kiyi inviting d’in saurayi babba ai kinyi sa’a ma kina dasu kala-kala dan be sani bane.”
“Ai wallahi sdy yanzu zai sani har wad’anda bana kulawa sai nace yazo gidan nan har sai naga iya gudun ruwan Yaya sultan.”
Daga nan hira suka ci gaba dayi har aka kira sallar magriba Balqees tayi sannan ta sad’ad’a zuwa kitchen ta d’ebo abinci dama Humaira na gurinta dan haka ta kulle d’akin taci ta koshi ta had’awa Humaira priso suka yi dam, sai da tayi sallan isha’i sannan ta nemi gado tare da rungumo Humaira suka yi bacci.
Wajan k’arfe tara da rabi ya dawo daga gidan hajiya kaka, yayi mamaki ganin Nadiya ce kawai a parlour’n take zaman jiran shi ba kamar daba dazai zo ya tarar dasu dukansu suna jiranshi. Tashi Nadiya tayi taje ta rungume shi tashi makeup bayan tayi addu da wani bak’in material anyi mata doguwar riga shape d’inta duk ya fito ya kalleta tare da makale kanshi a jikin wuyanta yace.
“Ya akayi yau na ganki ke d’aya a nan ina sauran?!”
Nadiya ta sauke numfashi tare da shafo kanshi tace,
“Wallahi tun fad’an da kayi mata ta shiga d’aki bata fito ba, naje nayi magiyar amma tak’i ta bud’e ni tazo taci abinci ma wallahi tak’i bud’ewa.”
Hannunta yaja suka k’arasa wajan k’ofar d’akin Balqees d’in Sultan ya fara bubbuga wa amma fur tak’i zuwa ta bud’e, ganin haka yasa shi cewa.
“Idan ke bazaki fito ba baby ki kawo min ‘yata…”
Shiru babu alamun zata bud’e gashi bashi da wani extra key duk suna hannunta ya kalli Nadiya da tayi shiru duk ta shiga damuwa yaja hannunta suka bar gurin, toh suma kasa cin abincin suka yi suka tafi bedroom d’inshi sai faman mita yake yi cikin dabara da kware tare da sanin halin mijin nata tayi kokari har ta kawar da duk wani 6acin ranshi da haushin Balqees da yake ji suka kwana cikin farin ciki. Tunda ya dawo daga sallan asuba ya wuce ta d’akin ya sake bugawa cikin sa’a Balqees taje ta bud’e mai tana sanye da hijjabi har k’asa da alama ta idar da sallah hannunta rik’e da humaira kanta a k’asa ta mik’a mishi ita yak’i k’ar6ar ta sai ma shiga d’akin da yayi tare da tura kofar ya tsaya a gabanta yace.
“Wato baby ke baxa ayi miki fad’a bako? Kinfi son a barki kiyi ta abubuwa ba tare da an tsawatar miki ba, toh ba’a gidan nan ba dan inaji ina gani bazan bari kije kina kula wad’annan yaran ba, duk-duk da nawa yafiki? Shine harda k’in cin abinci ko?!”
Ko kula zancen da yake mata bata yi ba ta kuma mik’e mai humaira hawaye na zuba cikin idanunta murya na rawa tace mai.
“Yaya ga ‘yarka nan, dama nasan akwai lokacin da zanji anyi min irin wannan gorin, na san nan gaba na zamana a cikin gidan za’a min ina son kafin lokacin yazo na koma inda aka d’akko ni.”
Ta fad’a tare da rushewa da kuka still tana mik’a mai humaira, ji tayi ya janyo su dukan su ya rungume a jikin shi yana k’ok’arin d’ago da idanta tayi saurin rufewa dan kar ya karya mata tsarinta a hankali yace.
“Kiyi hakuri baby ba nufina haka ba, ina son dai ki ringa gane irin mazan da zaki dinga kulawa, sannan batun humaira kuma ba wai gori nayi miki ba haba baby bakiga yarinyar itama kanta tafi shakuwa dake ba?kiyi hakuri kinji, yanzu muje parlour ko ruwan shayi ne kisha kinsan dai matsalarki.”
Hannunta ya kamo suka fito zuwa parlour lokacin Nadiya ma ta fito har tayi wanka tayi kwalliya ta kalli Balqees d’in tace.
“Lallai daughter irin wannan fushi haka harda horan yinwa? Please dan Allah ki dena ni wallahi bana son ciwon ki ya tashi.”
“Na dena aunty Nadi kiyi hakuri.”
“Yauwa daughter.”
Daga nan tea Sultan ya had’o mata tana nan zaune ta sha sannan ta koma d’aki dan yin shirin makaranta. Wajan k’arfe 7:25am ta kammala tana fitowa tatarar Nadiya ta kammala musu breakfast ta zauna ta d’an k’ara sannan ta mik’e taje parlour tana jiran fitowar su.
*****
Bayan sati biyu babu wani tashin hankali daya k’ara faruwa domin sosai sultan ya sanyawa Balqees ido akan harkokinta na waje sai dai ance duk sa idonka wata rana sai ka gaza hakan ne ya faru tsakanin sultan dan Balqees domin da yaga tana bin duk wani dokokinsa sai ya dena bibiyarta sosai hakan ya kuma bata damar yin saurayi dama ya dad’e yana bin ta baya samun dama dan haka dama jira take yi ta bashi address d’in gidan yayi mata alk’awarin zuwa washe gari.
Haka akayi kuwa ranar Saturday yazo da yamma lokacin Sultan baya nan yaje d’akko abba a airport, mai gadi ne yazo yace ana sallama da ita Balqees tace yace tana zuwa duk da taji haushi yazo lokacin da Sultan d’in baya nan amma bata nuna ba ta tashi zataje ta shirya Nadiya ta kalleta tace.
“Yauma daughter wani kika kawo gidan nan? bakya tsoran yayan naki ya shigo ya ganki..?!”
Balqees ta had’e rai tace,
“Toh aunty Nadi idan ban kula su ba ya kuke son nayi? Zama zanyi kuyi ta kallona harna tsofa na mutu banyi aure ba? Ni wallahi na gaji…nagaji ina son nima nayi aure na samu yancin kaina.”
“Amma daughter ai…”
“Kiyi shiru kawai aunty Nadi, indai bazaki goyi da baya na ba wajan nunawa Yaya Sultan illar abinda yake son janyo min ba toh kawai kuyi shiru ku rabu dani.”
Tana kaiwa nan tayi cikin d’aki tana kunkuni, sosai ta ca6a kwaliya cikin riga da wando sannan ta d’ora wata shara-sharan after dress wadda kusan duk irinsu gareta kala-kala sannan ta feshe jikinta da turaruka ta d’auki mayafin after d’in ta sanya tare da sanya takalmi mai d’ankaran tudu ta sanya ta fita. A can ta hange shi zaune cikin kujerun dake cikin wata kyakyawar rumfa tayi murmushi tare da k’arasawa wajan, zama tayi sai faman kallonta yake zuciyar shi na bugawa sabida ganin tsantsar kyawunta da ya fito ya matsa sosai kusa da ita tad’an kalleshi ganin yadda yake kasheta da wani kallo murya k’asa-k’asa yace.
“Beautiful girl! Gaskiya kina da kyau.”
“Nagode.”
Kawai ta fad’a sannan ya kalleta cikin kashe ido yace,
“Zan aiko gaskiya manya su shiga cikin maganar nan, ban ta6a jin zanyi aure nan kurkusa ba sai da na had’u dake duk da cewar nasha wahala kafin na samu wannan damar ta zuwa gidan ku da kuma kulani.”
“Uhmm…”
Balqees ta yi kawai sannan ta tashi taje ciki ta kawo mishi abin motsa baki ta dawo ta zauna suna d’an hira jefi-jefi, sun d’an jima a zaune taji horn d’in mashin d’inshi me gadi ya bud’e sannan ya shigo, tunda ya shigo yaga wata rantsatsiyar mota a kusa da ta Nadiya ya fara tunanin ko su waye suka zo, tun kafin ya gama tantancewa ya hango Balqees zaune da wani sai 6a66aka dariya take yi shi kuma bakon ya kafeta da ido tamkar zai copying d’in kamaninta.
Kamar ya wuce su sai dai zuciyar shi tak’i yadda da hakan, k’arasawa yayi inda suke kirjin Balqees ya buga ta kalleshi ya zabga mata harara tamkar kwayar idonshi zata fad’o k’asa tayi saurin kawar da kanta yayin da bakon nata ya mik’e tsaye yana bawa Sultan hannu ya mik’a mai da kyar bayan ya kai zuciyar shi can nesa sannan cikin rawar murya Balqees tace,
“Yaya zulkallain ga Imran nan.”
“Uhmm na ganshi Ai baby, shige gida zamuyi magana dashi.”
Ta turo mai baki kamar zata yi kuka tace,
“Amma Yaya dan….”
Yayi saurin katseta tare da tsuke fuska dama Imran ba kallonsu yake yi ba yace,
“Nace ki wuce ciki zamu yi magana dashi ko…!”
Wucewa Balqees tayi fuskarta a matuk’ar 6ace kamar haka zuciyar ta take, k’arasawa yayi sosai kusa da Imran ya kalleshi tare da cewa,
“Malam a tunani na idan har son auran baby kakeyi da gaske kamata yayi ka fara tambaya a gidan su shine tsarin gaskiya kasan ita d’in marainiya ce bana son ace ta samu wani wanda zai yaudare ta.”
Imran yayi murmushi saurayi ne wanda a shekaru zai yi 28–30 hakan yasa sultan beyi mai irin ta Adam ba sannan yaga alamar yana da ilimi kuma daga gani ya fito daga hannun masu arziki, imran yace.
“Karka damu yayan Mu sannan kayi hakuri kuskure ne aka samu, kuma ni da auran gaskiya nake son Maryam yanzu ma zancen da nake mata kenan na cewar zan turo manya na su shiga zancen dan gaskiya yayan mu ina son ta har cikin zuciya ta..”
Haka kurum Sultan yaji wani kudum a cikin ranshi wanda ya rasa dalilin jinshi, kallon shi ya kuma yi sannan yace,
“Toh amma yanzu dai ina son kad’an bata lokaci har zuwa lokacin da zata kammala school.”
Imran ya shafa circle d’in bakin shi sannan yace,
“Toh yayan mu amma dai zan dinga zuwa sabida mu k’ara fahimtar juna, ina sonta bana son na dinga d’aukar kwanaki ba tare da mun gaisa ba yayan mu ayi min wannan alfarmar dan Allah.”
“Kayi hakuri kaima Imran, nayi wa mahaifina alkawarin baxan bari ta had’a soyayya da karatunta ba akan wannan sharad’in ne yasa kake ganinta a cikin gidan nan, dan haka kayi min afuwa ka tayani cika wannan alkawarin.”
Shiru imran yayi domin ba haka yaso ba sai dai yace,
“Toh shikenan yayan mu yanzu a d’an turo min ita muyi sallama na gode.”
Juyawa kawai Sultan yayi zuciyar shi na zafi wanda ya rasa dalili ya shiga ciki, shiru-shiru be fito ba sannan kuma Balqees ma bata fito ba ganin yana 6ata lokacin shine yasa shi k’arasawa mota ya fito da kayan da ya kawo mata a leda katuwa ya bawa mai gadi yace ya mik’a mata. Sai da imran ya tafi mai gadi ya rufe get d’in sannan ya shiga yayi norking Sultan yazo ya bud’e ganin shi da kaya yasa shi cewa,
“Wannan fa daga ina?!”
Meh gadi yace,