HOD’IJAM CHAPTER 3 BY NOORIEEYAH
Www.bankinhausanovels.com.ng
Tun a kallon farko ta kwanta mata a rai,a kallo na biyu kuma ta yarda da ita,a kallo na uku ta sanyata cikin mutane ma’abota gaskia,a kallo na hudu kuwa take yanke taimata shigar burtu cikin zuciyarta,a kallo na k’arshe,wanda kuma shine kallon da take binta da shi,take kuma da yaqinin cewa zata cigaba da binta dashi,shine kasantuwarta uwar jikanta,a lokaci guda kuma matar d’iyanta.
Kasantuwarta uwar jikan da samsam bata maraba da zuwanshi duniya a da!amma a yanzu ganin mahaifiyarsa ya sanya ta shure wancan lamarin,ai tanajin babu ta yanda Allah baya lamarin sa koh?tanajin ai qaddarar su kenan,eh sosai kuwa qaddarar su kenan,qaddararsu kenan samar da Fawad ba ta hanyar aure ba,duk da haka sai takejin zata iya yafe musu,zata kuma sake jadaddda masu neman yafiyar ubangiji,mussaman don sanin tabbacin shi din Allah gafurur rahimun ne.
Ta sake d’aga ido tana kallon Fadwan a karo na barkatai tun bayyanuwar ta a gidan,a can k’asan zuciyarta kuma tana sake jinjina girman son d’anta da ta ke hangowa kwance male male a idanuwan Fadwan,tabbas irin Fadwah ce ta dace da zama suruka a gareta,ita din ce daidai dashi,ko banza zasu taru su gyara kuskurensu,su kuma sanya hannu bibbiyu wajen fatali da duk wani qalubale daka iya kawo wa rayuwar yaron su cikas,ai tana ganin tamkar hakanne daidai koh?
Shigowar Ni’imah dakin na Mammy ya sanyata fasa maganar da tayi niyyah,lokaci guda ta sake fadada fara’arta,sosai take jin duniyarta na tafiyar mata yanda take so a yanzu,mussaman don tabbaci da take dashi game da lamarin Niiman da Mukhtar din,ashe da gangan take zargin bawan Allah,ashe ashe da wacce yake so a zuciyar shi,wacce kuma take ganin cewa ita din er asali ce kuma er dangi,haka zalika er babban gida masu tutiya da zallar ilimi da dimbin dukiya,kenan babu laifi don ta sota kuma ta yarje mata zama suruka a gareta.
“Mammy sannunku.”
Niiman tai kokarin furtawa,mussaman yanda tun shigowarta ta fahimci irin kallon uku saura kwatan da baquwa ko kuma tace mai iqirarin cewa ita din mahaifiyar d’iyan da ta jera watanni kusan goma daukedashi amahaifarta,hakika tun jia bayan zuwan Fadwar duniyarta ke cikin halin ha’ula’i,mussaman don mulkin mallakar da ake neman yi mata akan danta.
“Af Niimah,kin shigo?kema halan kinfara kewar Fawad dinne?tun jia yayi maki balaguro ko?kinsan uwa dadi gareta,kinganshi nan Kwance a kirjin mamanshi yana jin duminta,kwana takwas ai ba wasa ba.”
Ta ida maganar tana dariya,kallo guda zakai mata ka hango zallar farin cikin dake tattare da muryarta,hakan yasa bata lura da wasu qarin canjujjjuka daga Niiman ba.
Murmushin yake Niiman tayi,yayin da kirjin ta ke sake yi mata nauyi,har yanzu takasa gane ainihin menene manufar wannan mata da ta kira kanta da mahaifiyar nata yaron,shin Mukhtar ta wannan hanyar zai bullo mata,?domin sosai take da tabbacin hakan duk plan din shi ne,mussaman domin tsira daga threat din Mammyn.
“Eh nagani ai Mammy,dama naga tun jiya ne banga Fawad ba,shine nazo dubashi.”
Ta ida zancen tana kokarin dauke idonta daga kallon Fadwan da tai mata kane kane da yaro,ga kuma wani irin kallo da har yanzu takasa gane wane mataki yakama ta aje shi.
Murya cikin nishadi Mammyn ta dan kyalkyale da dariya,lokaci guda tana mai aje kallonta a kan Fadwan dake kwance kan tamfatsetsen gadon ta naniqe da Fawad din,wanda wanka ma kawaici kawai takeyi tana yarda ta badashi,ba’a maganar nono dama,domin tuni ta nunawa Mammyn cewa bata da ruwan nono,kila tana daga cikin irin jinsin matan da ke da qarancin ruwan nono ne,a tunanin Mammyn kenan,hakan yasa bata wani damu ba,mussaman ganin cewa dama yaron bai san nonon ba dama tun farko,dadin dadawa kuma lafiya lau yanzu yake amsar madarar da ake bashi kanshi tsaye.
STORY CONTINUES BELOW
“Inafa zaki ga Fawad Niimah,ai kinganshi can wajen Mamanshi,ni kaina na hakura na kyaleshi,tunda ta qarfen ta bayyana.”
Ta ida zancen tana er dariya,al’amarin da ya sanya Niiman yin qasa da kanta,lokaci guda tana jin wani gagarumin tashin hankali na sake riskarta,duk kuwa da kashedin da take wa kanta,ai da ta dauka tana iya rayuwa ne babu shi,ta dauka zata iya jure rashin shi,ta dauka kuma abun qarami ne ta wannan fannin,ba tai tunanin Mukhtar din zai iya reaching up to this limit ba,hakan na nufin kalmar da yake jifanta da shi kullum ke nan?
“Ki bini a hankali Hayatiey,decision dina nan gaba ba llallai bane yai maki dadi ba.”
Ta sake tuna maganar shi ta karshe a tsakanin su,har ga Allah batai tunanin abu makamancin wannan ba,kuma tanajin tamkar yaqara wa kanshi baqin fenti ne a wajen ta,kwarai dagaske yana daga cikin mutane ma’abota son kan su matuqar gaya,dama ta dade da sanyashi a wannan ajin!
Dakyar ta daure tace
“Please ko zan iya ganin shi?”
Ba tare da ta d’ago ba,ballantana ta dubi Niiman ba tace a yangace
“Ayyah bacci yake,may be in yatashi zuwa anjima sai kizo kiganshi,that is in daddyn shi bai rigaki shigowa ba.”
Maimakon kalmomin nata su zama ababe masu dan girma a kunnuwanta sai aka samu akasani hakan,domin kuwa da gudun gaske kalaamen suka dad’ad’a mata,itafa yanzu ta san Mukhtar yasamu mata,matar ma ta nunawa sa’ah.
“Ok toh ba damuwa,nagode.”
Tai qoqarin danne bacin ranta,kana batare da wani second thought ba ta yarje wa zuciyyarta abinda ta dade tana kitsa mata,yau ba sai gobe ba zata aiwatar da abinda take da tabbacin shine tsira a gareta da yaron ta,ko da hakan na nufin ta so kanga da yawa,ai tanajin son son kaine ko?amma kuma ai son kai yafi.
Kafin ta idasa ficewa Muryar Mammy ta dakatar da ita.
“Niimah,inkina fita ki biya kitchen,kicewa Mama Ladi takawo mani kunun gyda,and daga nan ki kira mani Addanku a waya,kice nace su shiryo dukkan su su zo,domin gobe goben nan nakeson a daura auren Mukhy da Fadwah,gara ai auren kawai,inyaso su koma american su rubuta final exams din su,daga nan ma in sungadama suna iya yin zamansu a can,mussaman don gujewa tsugudidi da yamadidi irin na dangin nan naku,dama jama’ar gari baki d’aya.”
Ji tai tashin haankalinta ya ninku,ya sake ninkuwa,yakuma sake girmama,bata san kuma ainihin menene sanadin hakan ba,ita dai abinda take iya tunawa a lokacin shine yaronta,shin menene makomar yaronta kenan?bata so ta yarje wa kanta amsoshin da d’ayan sashen zuciyarta ke bata,hakan yasa da sauri ta dawo baya tace,
“Mammy toh shikuma Fawad fa?ina zaa kaishi?”
“Ikon Allah,wai ni kuwa Niimah yaushe zakiy hankali ne,inbanda abinki duk wannan haqilon da nakeyi akan wa nake yinshi?ai duk don samun rufewar asirinshi ne,yin hakan naa nufin Fawad rayuwa cikin mahaifan sa tamkar ko wane yaron,dukkan wannan alfarmar tashi ce,ko da akwai wata to qalilan ce akan tashi din.”
Sake hadiye wani miyau quuuut tayi,yayin da takejin wata zufa na bin bayanta tamkar ansheqa mata ruwa,sosai takejin hantar ta na kadawa,kenan hakan na nufin nan da wasu kyawawan awoyi masu gajeran tsayi ba zata sake sanya yaron ta a idanunta ba?ba zata sake ganin shi ba?ba zata sake jin dumin shi ba?ba zata sake rungumeshi bisa qirjinta ba,ba zata sake jin kukan shi ba?zai tafi yafara rayuwa da wata sabuwar uwa. da ba itaba?zai rayu da wata can daban da ba ita ba?
“No,No,this has to stop!”
“Niimah?ke Niimah,Niimah na jina kuwa?”
Firgigit ta dawo hayyacinta,yayin da idanuwan Mammy dana Fadwan ke bin ta da kallo,mussaman kallon Fadwan kallo ne da yasha banbam da na Mammyn.
“Toh toh shikenan Mammy zan sanar da su.”
Daga haka ta juya a sukwane zata fice,hakan yayi daidai da sanyo kan Mukhtar dakin,wani irin kallo tai mashi,kallon da zai iya rantsewa da Allah bai taba ganin ta da shi ba,kallon da ko bayan da ta fahimci abinda yai mata watanni tara da suka wuce batai mashi irin shi ba,wannan kallon hade yake da tsanaa mai tsananin muni,tattare yake da ni da kai mu zuba,tattare yakeda zallar tuhuma da zargi.
Meyasa yake jin tamkar wani gagarumin al’amari na shirin samun shi?
***
Assalamu alaikum dearies,dafarko zanfara da baku hakuri bisa jina shiru da kuka yi,dama banyi alqawarin update kullum ba,amma zanyi matuqar ganin na aje chapter daya a duk lokacin da samuwar damar hakan ya samu,in sha Allah.5
Nagode da dimbin qaunarku a gareni,inakuma bada hkrin rashin replyn messages da bana samun yi kwana biyu,fatana dai shine ku cigaba da jurewa wajen bina domin ganin inda alqalamina zai ajemu,tafiyar ba kadan bace,tafiya ce mai tarin nisa,ai inajin tamkar zaku jure wa duk wasu qalubale daka iya gifto mana koh?then mucigaba da tafiya domin ganin qarshen lamarin.Duk wani kyaftawar agogo,yana tafiyane daidai da bugawar zuciyarta,har yanzu takasa samun mafita guda d’aya,har yanzu ta rasa matakan da zata d’auka,infact ta ina ma zata fara?bata da wannan masaniyar,meyasa bata da wannan masaniyar?eh toh kila hakan nada nasaba da k’arancin shekarun ta,a inda karancin shekarun nata suka taka muhimmiyar rawa wajen alaqa da sassanyan halin ta,hakan yaqara taimakawa wajen fito da ainhin rashin wayon ta,bata da wayoh kam,ga kuma k’arin rashin sanin madafa,rashin gurin zuwa,rashin sanin taqamaimai halin da duniya ka iya wurgata,mussamman in ta tuno da k’udirin ta.
Kamar kukan shi take ji?sai tai tsam da ranta,ta maida dukkan sauran hankalin ta zuwa ga inda take tunanin jiyo sautin kukan nashi,dagaske shi dinne ke kuka,wani sabon faduwar gaba ne ya sake ziyartar ta,awanni kusan ashirin da tara kenan rabon da ta ji dumin danta,rabon da ta shayar dashi abincin sa,a hankali ta maida kallon ta bisa qirjinta da tuni sun cigaba da bulbular ruwa kamar yanda suka saba,bata damu da ta tare ba,ba wannan ne a gaban ta ba,abinda ke gabanta guda d’aya ne,abinda ke gabanta shine samun tudun dafawa,abinda ke gabanta shine tsira da sauran adadin kwanakin da Allah ya dibar mata a ban k’asa,domin tanaji a jikin ta,in batayi da gaske ba,in bata yi da gaske ba,toh sosai duniyar zatai mata juyin waina,juyin da bata jin nan kusa zata farfado daga azabobin ta.
Ta sake jiyo hayaniyar muryoyin mutanen da ke sanya zuciyarta tsalleh,sai kumata mike a hankali ta fito,su dinne tsaitsaye a tsakiyar falon gidan suna ta fama da Fawad din da ya cika gidan da ihun kuka,ta sani,ta sani kwarai meke damun shi,sosai yafison nonon akan madarar da ake bashi,amma ta yaya zata amshe shi yanzu?a lokacin sai tai fatan inama Mukhtar din na kusa,tabbas da ta san ko da me suke taqama sai Fawad din yazo hannunta,ai yafi kowa sanin abinda yaron nashi yafi so.
“Mammy me ya sameshi haka yake ta kuka?”
Ita kanta bata san ta isa wajen su ba,sai dai kasai ta tsinceta a gaban su.
“Niimah mun rasa meke damun yaron nan,kinganshi tun dazu ya hanamu sukuni,kuma ni nasan yunwa e ke damun shi,tunda tun wajen awanni biyar kenan yaqi amsar madararshi,kuma nabi duk wasu alternatives danasani wai ko wani abu ke damun shi,amma kinga yaron nan lafiyarshi kalau.”
Ta ida maganar cike da bayyananniyar damuwah,yayin da Niiman ke sake jinjina lamarin a zuciyarta,awanni sama da biyar yaron ta baici abinci ba?tumbin shi babu komi cikin shi duk iyya tsawon awannin nan?shin alhakin yaron nan ba zai kamata ba kuwa?
Fuskantar Fadwan tayi dake faman kai kawo tana aikin jijjiga Fawad din da kamar sake zugashi ake,wannan karon har wani mimmiqewa yake kamar me shirin shidewa.
“Don Allah kibani shi in gwada lallashin shi,qila ayi sa’ah yai shiru.”
A fusace Fadwan ta maido da hankalinta kanta tace,
“Keh wai bahaguwar wace qasa ce for Goodness sake?kinfini son shi ne ni mahaifiyar shi?ko kuwa kin fini sanin abinda ya dace neh?inata kokarin ganin nayi maki uzuri,kasantuwar yarinta dake dawainiya dake,but still na lura baki cika gane wannan kawaicin nawa ba,like i have to split fire on you,inajin sannan ne zaki shiga taitayinki,for your information, banson shishhigi,kin gane ai?”
Batai mamaki ba,ganin yanda tun a kallo na farkoda matar taimata ta hango tsantsar tsanarta a idaniyanta,harmata riqa mamakin me tai wa matar har haka da bata iya boye fishin ta.
Batai mamakin jin abinda Mammyn ta ce ba,domin tuni ta sanya alamar tambaya akan alaqar dake tsakaninta da Mammyn,a da ta tunanin ko alabarkacin kasancewar ta diyar qanin miji da kuma aminiyarta yakamata ta riqa samun sassauci a wasu abubuwan,amma sai ta rika ganin akasin hakan,al’amarin dake matuqar daure mata kai.
STORY CONTINUES BELOW
“Niimah inace dazun nan da safe nake fada maki ki saurara da wannan shishishigin naki,tunda mai d’a ta buqaci kibarta da d’anta why can’t you just abide by it?ki hakura haka nan,nasan kina son Fawad,amma ai sonki cikon cikoli ne akan ita da ta kawoshi duniya koh?”
Wani abune ya wuce mata ta maqoshi,a hankali ta furta,
“Hakane Mammy,kuyi hakuri nayi shishhigi,hakan ba zai sake faruwa ba.”
Daga haka ta juya a hankali yayin da hawayen da take ta faman riqewa samun ikon zubowa,hawaye ne masu zafin gaske,hawayene da take da tabbacin babu ranar tsayawar su har sai randa takoma ga mahalliccin ta,meyasa duniyar nan ke da tsaurine?abubuwan sun mata yawa,ga duka ga tsinka jaka.
Ba ta lura ba,ba ta tsammaci ganin shi ba,domin ba ta dauka tana da wannan nutsuwar ba,abinda tasanj shine kawai jin hannu mai kama da na namiji cikin nata,da hanzari tai kokarin samawa kanta nutsuwa don fahimtar ko waye,tasan dama bai wuce shi din,amma me yakeyi tsaye a corridor din?
Bai bata ikon yin magana ba,mussaman yanda yai nuni da hannayenshi saman labbanshi a alamun tai mashi shiru,ba kuma tare da ya damu da komi ba yacigaba da jan hannunta dake cikin nata zuwa falon da ta baro,zuwa yanzu sun zauna,amma har yanzu Fawad din bai fasa burari ba,ita kanta Mammyn kallo guda zakai mata ka hango zallar gajiyawa da tashin hankali.
Ganin su a haka ya sanya Mammyn da Fadwa miqewa,Mammy tsabar rudewa ma bata lura da hannun Niiman ba dake sargafe da na Mukhtar din ba,ita dai ganin Mukhtar din take tamkar wani magani da zai kawo qarshen wannan shegen kukan na Fawad din.
“Madallah dan halaak,yanzu nake shirin kiranka,ko dai asibiti za akai yaron nan ne?kaji uban kukan da yake tayi mana tun bayan fitar ka daga gidan,ke Fadwa miqa masa shi.”
Hankalin Fadwa gaba daya baya kan kowa sai hannayen su dake a sargafe,bata dauka zata iya jure ganin Mukhtar din a irin yanayin nan ba tai shiru,haqiqa ita din mace ce mai zafin kishi,mussaman akan Mukhtar da take da yaqinin cewa zata iya komi akan shi.
Ba tare da ta sauke idanuwan ta daga garesu ba ta maida wa Mammyn amsa.
“Mammy ko zan iya ganinki ke kadai minti biyu?”
“Me zai hana Fadwah,amma before then baiwa Mukhy yaron nan ko kunnuwan mu sa huta.”
“No Mammy,Mukhy ba zai sake tab’a man yaro ba,matuqar bai koyi kebance kanshi daga taba hannun ko wace sakarya da ka iya zuwa gabanshi ba.”
Sai a lokacin Mammyn ta lura,takuma lura da yanda Niiman ke kuka tana faman son raba hannunta da na Mukhtar din amma hakan yaqi samuwa,asalima sake damqe hannun nata yai qam qam,yanajin kukan nata na bi cikin saqo da lungu na zuciyarta,how could he be this selfish?duk selfishness din shi ne yai leading to all this tantrums, amma duk da haka baya danasanin faruuwar wasu ababe masu tarin muhimmaci da suka faru da shi sanadiyar nashi son kan,ko banza son kan nashi ya haifar mmashi da d’a mai ido!eh mana d’a mai ido,tunda selfishness din nashi ne sanadin samuwar Fawad din shi,kuma daga matar dayafi so kaf duniya bayan mahaifiyar shi.
Bai bi takan bambamin da Mammyn take ba,hasalima maida hankalin shi yayi kan Niiman dake faman kuka a hankali.
“Oya look at me”
Ya fada a hankali,domin ita kadai taji me yacedi,amma duk da haka qin dagowa tayi,sosai yau take da yaqinin musiba babbba da Mukhtar din ke shirin sanyata a karo na biyu.
“I said look at me,else i will makes sure i break your promise right now, kinsanni kinsan abinda zan iya aikatawa Hayatiey.”
Da sauri ta dago tana kallon shi,yayin da shima yai qoqarin sanya idanuwanshi masu kama da na mashaya yana sake k’are mata kallo,he needs to look at those eyes to his own satisfaction, yanajin tamkar nan da wasu lokuta yakusan yin nesa da su,nisan da bayajin nan kusa zai sake samun damar hakan,thank God for his undying love towards this pretty innocent woman!
“Go and get him.”
Ya furta mata daga kasan makoshin shi,sosai ta hango tausayinta male male a can cikin idanun shi,sai kuma ta sake hango wani abu mai girma da qarancin hankalinta ba zai bata ikon fahimtar menene ba,abu guda tasani a lokacin shine,yabata wata dama a duniyarta a karo na farko,damar da bata jin zata dena ganin daraja da girman ta,he is just like a saviour to her right now.
“Go get him,feed him,bath him,and make him fall asleep in your arms,for tomorrow you might, you might……”
Sai kuma yakasa karasawa,ai yanajin kamar ita din uwace koh?uwa ce ,uwa da bata cancancin wadannan kalar kalamen ba,amma sai kuma yake ganin kamar ta cancanci ta san gaskia ko?duk da sanin cewar wannan gaskiar me daci ce,mai zafi ce,yin shirun nashi shine mafi a’alah,mussaman don farin cikin a yanzu.
Sake hannunga yayi daidai da juyawarta ta fuskanci Fadwan,sai ta riqa jin wani kwarin guiwa na shigarta,ta rika jin sabon qarfi,eh ko banza she need to be strong,for her baby and ofcourse for herself,ai tanajin hakan ba laifi bane ko?
Wannan karon bata nemi izinin ta ba,bata jin kuma zata nema,hakan yasa tana isa gaban ta ta sanya duka hannayen ta biyu ta amshe yaronta,daga nan saita rungume shi,ta sunsuna shi,ba kuma tare da ta saurari duk wasu burarida Fadwan ke shirin yimata ba ta juya domin ficewa daga falon,fitar da ta gama tabbatar wa kanta cewar fita ce ta har abada,fita ce daga rayukan da suka taka muhimmiyar rawa wajen maida zamantowarta abinda tazama,take shirin zama nan gaba.
“All thanks to them!!!”
Bata fasa kallon shi ba har tazo kusa dashi,kafin ta fita sai ta tsaya a gefen shi tace.
“Zanyi dukkan abinda kace kamar yanda nasaba bin dukkan cewar ka,sai dai wannan karon harda abinda baka ce ba ma zanyi.”
“I will take care of our Baby Ya Mukhyy,i promise.”3
Tasan be fahimci me take nufi ba,domin da ya fahimci me take nufin,da bai jefeta da murmushin jin dadi ba,wannan shine kuskuren shi da zai fara girba!
***Har yanzu da yadawo dakin shi ya kintsa domin samun hutu ya gaza samun hutun,bai san menene ainihin abinda ya hanashi samun sukuni ba,sai dai yana ta’allaka hakan da auren da Mammy ke son qaqaba mashi a goben,auren da baya da hurumin daga ko da idone ya nuna tawayen shi,duk saboda mene?duk sabida girman alkawarin Ni’imah,alqawarin ta mai tarin girma ne a gareshi,kuma yanajin zai iya jure komi domin ganin bai sab’a mata ba,ko da hakan na nufin nashi b’atancin ne.1
Har yanzu bai nunawa Fadwan komi ba,since she can go to this extent, thinking she can get him,then yanajin sanya mata idanu din kadai zai wadatar,duk da cewa har yanzu mamakin yanda ma akai tasan da zancen dukkan lamarin bai sake shi ba,al’amarin da ya sanya shi sanya alamar tambaya kan abokin shi Ra’is!because idan aka cire Doctor Frank,toh hakika Ra’is ne kadai mutum na biyu dake da sanayya akan wannan sirrin nashi,but how could he betrayed him?tambaya ce har yanzu da bashi da amsar ta.
Ya sake juyi akaro na biyu,lokaci guda yana mai kokarin latse bedside lamp din dake zaune kan bedside drawer din shi,sai kuma yafasa,lokaci guda yana mai yin tsam da ranshi,awanni kusan biyu kenan da Ni’iman ta tafi da Fawad din,and tun bayan haihuwar Fawad din babu rana ta Allah da baya zuwa yai mashi addu’oin bacci tare da bashi duk wata kulawa har yai nisa cikin bacci,abu ne da ya riga ya sabar wa kanshi.
Toh amma yau d’in sai yake ganin tamkar ya cancanci ya bar yaro da uwa suyi kwanan bankwana,coz yana da yaqinin cewa daga rana kamar ta gobe ba zata sake sanyashi a idanunta nan kusa ba,he has that feelings,hakan yasa ya hakura ya latse ragowar hasken d’akin,k’asan zuciyar shi yanajin wadannan abubuwan dake faruwa duk na d’an lokaci ne,abinda yasani shine komi lokaci ne,a yanzu zai hakura yaga ina wannan qaddarar zata aje su.
Ya rufe idanuwan shi bayan ya dauko hoton Ni’iman da Fawad din a zuciyar shi,rayukan da yakejin duk numfashin shi na bugawa ne da soyayyar su!tabbas sun cancanci soyayyar shi,they are the only reasons yake fatan Allah ya ara mashi tsawon rai domin ya dad’ad’a masu,ya faranta masu,ya sanya farin ciki da annushuwa cikin rayukan su,ya kuma tabbatar ma duniya how precious they are to him,despite yanda aka samar da su kuwa,they deserve it.
Kafin bacci yai nasarar d’auke shi,sai da yaji wani irin kuka mai sauti,baccin da yaci k’arfin shi bai bashi ikon tantance sautin waye ba,ballantana kuma ya fahimci daga ina sautin kukan ke fitowa.
***
A hankali take yin baya baya daga jikin k’ofar dakin da ta kasance ta Mammyn,yayi n da bugun zuciyar ta ke qaruwa,lokaci guda ta rika nadama,nadamar wannan rana,nadamar lokaci irin wannan da bata bar gidan ba tun lokacin da tasamu ikon yin hakan,menene ma ya kawota dakin Mammyn?
Her credentials and all her belongings da suka danganci tarkacen E-passports dinta da Visan ta,sune manyan dalilan da suka hanata tafiya tun dazu,a yanzu kuma sun zama sanadin yayewar duk wani sauran farin cikin da yai wa rayuwar ta saura,wannan wace iriyar muguwar rana ce a gareta?
Ta riqa tariyo kalamen da sukai nasarar tarwatsa ta,lokaci guda kuma sukai nasarar fahimtar da ita ko ita din wacece.
“Fadwah ki kwantar da hankalinki,kamar yanda nafada maki ne Mukhy baida wata mata a duniya in bake ba,ko ba don komi ba don wannan albarkar dake tsakanin ku,Ni’imah kuwa ina tabbatar maki ko bayan babu raina na haramta zamowarta wata bangare na rayuwar Mukhy,alkawari ne da naa sanya Mukhtar din ya daukar mani ba tun yau ba,in banda ma dai sakarci irin na Mukhtar har zama nayi fa na gaya mashi asalin wacece Ni’imah,Ni’iman da duk duniya daga Allah,sai ni sai mahaifiyarta,sai kuma likitan da yai mana aikin samuwar Niiman,mu kadai muka san cewa ba diyar sunna ba ce!”
“What?Mammy?”
Ta tsinkayo muryar Fadwan na fadi cike da tashin hankali.
“Mammy i thought Niiman cousin din su Mukhtar ce?”
STORY CONTINUES BELOW
Dariya Mammyn tayi
“Yes a idanun duniya cousin din su ce,amma a bad’ini kuma gaskiyar lamari babu abinda ya danganci blood line tsakanin su,alaqar dai bata wuce kasantuwar ta diyar aminiyata,aminiyar da bani da kamar ta ba,amma duk da haka ba zan zura ido jininta ta gurb’ata man nawa jinin ba,ba zan yadda ba,ba zan taba yadda in bari Mukhtar ya auri yarinyar da ni na raka uwarta sperm bank,muka samu donor akai implanting din ta a mahaifar ta ba tare da sanin mijin ta na sunna ba,wanda yakasance qani a gurin baban su Mukhy,kuma ina tabbatar maki da cewar har yakoma ga mahallicin shi baida masaniya akan diyar da yake kira ‘yar shi ba ta shi bace,diya ce da muka je muka yo farautaar ta a cryos USA international sperm and egg bank,yes,banajin zan iya manta sunan gurin,aikin ya daukemu kimanin sati biyar zuwa shidda.”
“Mammy kina nufin sperm bank kuka je kuka samu sperm donor akai mata amfani da shi ta hanyar IVF?if im not mistaking kenan?”
“Kwarai dagaske,i know i shouldn’t be talking to you about this Fadwah,but here i am!meyasa nake gaya maki all this?sabida na yarda dake,kuma dadin dadawa inason tabbatar maki da cewa Mukhtar bashi da wata mata in ba ke ba,Niimah ba ta dace da shi ba,duk da ba zina akai aka samar da ita ba,kai tsaye kuma ba zaa kirata da diyar sunna ba,duk da cewar wannan din sirri ne daga ni sai mahaifiyarta muka san dashi,sai ko Mukhtar a wasu watannin baya,sai kuma ke din a yanzu.”
Har zuwa lokacin da kunnuwanta suka kasa cigaba da jure mata maganganun dake fitowa daga bakin Mammyn,lokacin da kuka yaci qarfin ta,lokacin da kunnuwanta suka gama jiye mata ainihin wacece ita,har a lokacin tambayoyi ne maqare a zuciyarta.
“Sperm bank?sperm donor?IVF?”
In vitro fertilization(IVF),wata kalmace da ta dade da shiga tarihin rayuwarta,sabida ta wannan hanyar aka samar da nata d’an,ta hanyar aka bi wajen taimakawa samuwar Fawad,duk da anyi mata hakan ta bayan gida ne ba tare da sanin ta ba,amma duk da haka bai dauke ma’anar cewa ta sanadi guda kuma hanya d’aya aka samar da ita da kuma nata d’an ba.
Innalillahi wa’inna ilaihirraju’ooun ta rik’a maimaitawa a tsakankanin numfashinta,aa yayin da take toshe bakinta wajen fitowar kukan ta da iya k’arfin ta,kalmar k’arshe da tafi d’aga mata hankali a dukkan zantuttukan na Mammy shine.
“Ba zaki gane abinda yafi cimani tuwo a qwarya ba akan yarinyar nan,asalin donor din da yabada sperm din ma fa a wancan lokacin inyamuri ne mazaunin america,kinsan su basa boye identity din donors din su,asalima sai ka zaba ka darje,tsautsayi ya sanya mu d’aukar nashi ba tare da mun damu da mu duba tribe din shi ba,kawai dai munsan musulmi ne,sai daga baya a pappers din da muke signing muka lura da cewa inyamuri ne.”
“Hakan ke nunida cewa ita din asalin tsatson inyamurai ce!!!”
Bata jirayi qarasa jin dariyar da Fadwan take ba,ttasani,tasan me take wa dariya,sai kuma bataji haushin ta ba,ba ta ga laifin ta ba,a al’ada ko kuma ince hali irin na malam bahaushe idan akwai yaren da baigani da gashi ko sauran mutunci toh malam inyamuri ne,asalima shi malam bahaushe bai cika yadda ba in aka nuna wancan inyamuri ne kuma a ce musulmi ne,toh nan fa zaka ga kallon mamaki da kuma kokwanta akan kalmar ta musulunci da aka danganta inyamurin da shi.
Ikon Allah ya qarasa da ita d’akin ta,zama tayi bayan qofar ta riqa wani irin kuka,kukane da tun da uwarta ta kawota duniya batajin ta taba yin irin shi,kuka take cike da sarewa,kuka take cike da rashin sanin madafa,kuka take cike da tausayin kanta da d’anta,a lokacin ta maida kallon ta side din da gadon ta yake yana bacci cikin nutsuwa,kallon shi take tana mai tausaya musu,tana tausayawa yadda tasu qaddarar tazo,meyasa Mukhtar yazabi da yai mata haka?yasan da labarinta amma still he went ahead wajen sake maimaita same mistake da mahaifiyarta ta aikata akan ta,ta cigaba da kallon Fawad din tanajin girman zaluncin da mahaifin sa yai mashi,haka kuma tacigaba da tuna zaluncin da tata mahaifiyar tai mata,tambayar ta anan itace,shin meyasa mahaifiyarta ta zabi abinda tayi din?Abbu na,ta tuna fuskar mahaifin ta mai qaunarta fiye da duk abinda ya mallaka a dunia,ta rika tuna girman sonta a zuciyar shi,ashe ita din bba jinin shi bace?
Ta runtse idanunta yayin da tausayin wanda take kira mahaifi ke sake mamayeta,godia daya zatai wa Aallah da baiyi tsawon rayuwar da zai gane wannan mugun sirrin ba,amma shin mahaifiyarta ta cancanci yafiya ko afuuwa daga gareta?tana jin ta cancanci ta yafemata,ko banza mahaifiyarta ce,mahaifiyar da ta sota ta gatanta ta da dukkan iko da iyawarta,ta sota ta kuma dage wajen bata tarbiya mai kyau,despite da irin kasar da suke zaune a ciki kuwa.
“I will learn how to forgive you Ammy,but kafin nan ina buqatar sanin dalilin da yasa kika ci amanar mahaifina,dalilin da ga sanya kika zabi ki samar dani ta wannan hanyar,duk kuwada igiyoyin aure dake rataye a kanki.”
Daga haka ta kalli agogo taga qarfe biyu da minti arb’ain da bakawai na dare,ba tare da wani dogon tunani ba ta mike tsaye ta shiga bayi ta wanke fuskarta gami da dauro alwala,nafila ta gabatar raka’ah biyu,ta dade a sujjada tana kai kukan ta wajen Allah madaukakin sarki,fiye da mintuna talatin ta kwashe tana zabga addu’o’i,bayan ta idar ta mike ta dauko fawad din ta sanya mashi nono a baki,bayan ta tabbatar da ya koshi ta sabashi a bayanta ta goya shi tsam,hijabin sallarta har kasa ta zumbula,bata dauki komi ba face wallet dinta,daga haka ta sanya kkai a haankali ta fito,bayan ta tabbatar da babu mai kallo ko jin motsinta tabi ta qofar balcony ta baya ta fice,bata jin baba maigadi,saabida ta sanshi gwani ne wajen kafirin baccin tsiya.
Bayan ta fita ne ta juyo tana yi wa gidan kallon karshe,gidan da mafi yawa daga cikin qaddarorinta sun fara ne daga nan.
“Sai watarana.”1
Ta furta hakan a bayyane,yayin da hawayen fuskar ta suka cigaba da gangarowa.
***