AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 13 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
ya feshe jikinsa da turaren da yazame masa jiki sannan ya dauko duk abin da zai bukata ya fito. Gidan ya rufe gabadaya maigadinsa Dan fulani ya bude mishi kofa ya fita.
Duk mutanen gidan ba su fito ba sanda ya isa, a
falon farko ya jira Daddyn ya sauko ya karbi jakar hannunsa. Bai wani sake masa fuska ba ya wuce shi yayi gaba, mukullin babbar motarsa kawai ya ba shi yana nufin shi zai tuka su. Ya soma gaishe shi da safiya wadda a da baya irin ta duk don ya samu Daddyn ya sake masa ne, maimakon haka sai Daddy ya harzuko. A fusace yace “Ba za ka rabu da ni ba Abdul’azeez? Na ce ina bukatar gaisuwarka? Gaisuwar dole ce? Nace dole ce?”
Www.bankinhausanovels.com.ng
“A yi hakuri Daddy”. Ya ce yana shafa kai.
Sai da maigadi ya rufe gate bayan fitarsu suka hau titi sosai, sannan Daddy ya ce a gajarce, “Ka biya mu dauki Kakanka’”’O.k Daddy”. Hararsa ya yi, Abdul’azeez na hangowa ta madubi ya nutsu ya kara shiga taitayinsa. Da alama yau a Ambasadansa yake baya son wargi. A ma’adanar motocin sa suka tadda shi(tsohon Minista Abdulkarim Dakata) ana goge masa motar da ya yi niyyar yin tafiyar a ciki. Aka wangale musu tafkeken (gate) din suka shigo. Ya iso motar tun kafin Abdul’azeez ya gama parking ya mikawa dan sa Hamza hannu, Abdul’azeez ya gaishe shi, shi ma ba sakin fuska ya amsa masa. Daddy ya ce, ya hutar da direbansa kawai ya zo su hadu su yi maneji a mota daya tunda a yau za su dawo. Ya amince da hakan. Tafiyar nutsuwa da kwarewar tuki ta awanni hudu cur ta kawo su Kanon Dabo. Tushensu, usulinsu. Yaro ko da me ka zo an fi ka. Suka shigo cikin birni, sannan sannu a hankali Abdul’azeez ya karya kan motar suka shiga un guwarsu mai tsohon tarihi a Kanon Dabo, wato Dakata. Adda Hafsatu na aikin abincin ranar gidan sanda suka iso. Yau gidan akwai rangwamen mutane kasancewar ranar aiki ce, kuma ranar makaranta ga jikoki. Sun samu Baffa Atiku na baccin rana don haka dakin Adda suka yada zango, ta cika su da ruwa da lemuka kasancewar ba ta gama abinci ba. Sai da ta ji lafiyar jikokinta na Daddy da ‘ya’yan kaninta Abdulkarim su ma suka ji lafiyar ‘yan uwa, sannan suka shiga hira, tana tsokanar Www.bankinhausanovels.com.ng Abdul’azeez wai ko takwararta ba ta iya tuwo ba ne ta ga duk ya yi dan wuya bayan da ma can ba shi da tsoka? Sunkuyar da kai ya yi gabansa ya soma faduwa da ya ji sallamar Baffa a kansu. Farin dattijo mai farar aniya da nisan kwana. Mai son jikokinsa fiyeda Hamzah da ya haifa. Sai dai fa in aka yi ba daidai ba, ba’a jinta da dadi daga gare shi. Sai dai a Sshirye yake da ya dauki komai da kowanne irin hukunci daga gare su in dai a karshe zasu hakura su dawo mai da Hafsah! Zaunawa Baffa ya yi a kusa da shi ya bugi kafadunsa. “Lauyan duniya, idonka kenan? Dama kuwa ina nemanka”. Su Daddy suka duka suna gaida Baffan nasu. Amsawa yake yana sa albarka kamar yadda ya saba in ana gaishe shi. Sai dai ya lura duka da damuwa a fuskokinsu kada Abdul’azeez ya ji
labari. Baffa ya dubi Abdul’ azeez ya ce. “Neman duniya da harkallar cikinta ta sanya a yanzu ba kwa damuwa da addu’a, ba kwa kiyaye
yin azkar din da kullum nake nusassheku daga ku har iyayenku, boko kawai ku ka sa a gaba. A kwanakin baya na yi ta mafarke-mafarke a kanka masu nuni dakana cikin sarkakiya da dabaibayi, na yi kwanaki ukku ina istikhara a kanka na kuma samu wani duhu cikin rayuwarka da ke bibiyarka ba tare da saninka ba. Na ga wata mace na farautar zuciyarka da tsafi . Abdul’azeez ina sallolin darenka? Ina addu’o’in da kullum nake tura maka? Ina ka bar zam-zam da na ce ka ke alwala da shi akai-akai in za ka shiga kotu?” Shiru suka yi bakidaya, zuciyar kowanne da waswasi, a zuciyar Abdulkarim ya ce, “Ko dai wannan ‘yar Yarbawan ce?” Daddy kuwa bai kawo komai a ransa ba ban da harkar aiki. Shi kuwa mai gayya mai aiki maganganun kakansa a tunani suka jefa shi. Tunda ya fara jin son Mu’ azatu bayan a haduwarsu ta farko ya san ba sonta yake ba, daga baya zuciyarsa ba ta taba hutawa da azabtar da shi a kanta ba sai ranar da ya saki Hafsat! Ranar ne ya ji kamar sakin ya tafi har Mu’azatun, ranar ne ya ji shi sakayau ( free from all worries and tortures) , shin ko ita ce ta tsafe zuciyar tasa? Www.bankinhausanovels.com.ng
Jin shirun ya yi yawa Baffa ya muskuta, “Ko ma dai mene ne ya wuce, sai a tari gaba a yi wa jiki Kariya, a kuma kula da abubuwan da na ambaci cewa ana wasarere da su. Ba kai kadai ba har sauran ‘yan uwanka. Akwai rubutu da na sa aka yi muku dukkanku yanzu za ka sha naka ku tafi musu da sauran har su Farhan. Yanzu dai na ganku da damuwoyi, me ya faru?” Abdulkarim ya yi gyaran murya, ya ce, “Baffa ai Abdul’azeez ya warware duk shirin nan da ku
ke yi kai da shi, tunda ya saki matarsa!Ashe duk tsawon lokacinnan zaman yarjejeniya yake yi da aurensu ba da sanin kowa ba, wai zai sake ta sanda yaga dama ya auri wata, sai da komai ya damalmale masa yadda ba zai iya gyarawa shi kadai ba sannan muka sani”. Salati Baffa da Adda Hafsatu suka saki a tare, Addah ta ce, “Yar amanar ya saki marainiyar Allah? Abdul’azeez din ne ya maida auren nasu na mut’ayana sane ko yaya abin yake?” Baffa ya ce “Auren da muka daura ta tsabtatacciyar hanya yaushe ya koma na mut’a? Abdul’azeez ba zai yi haka da gangan ba. A sanina har a Saudiyyah ya yi islamiyyah, yayi haddar Alqur’ani ya kuma san hukunce-hukuncen addini balle ya yi aikin batan Www.bankinhausanovels.com.ng hikima irin haka”’Wannan karon Abdul’azeez ya kasa jurewa, kuka ne ya kwace wa idanunsa. A sanda yake tsarawa Hafsat su yi ‘contract marriage’ ya san ba abin kirki yake shirya musu ba, amma bai zaci hakan yana da wani babban effect ga addini ba, duk karatun islamiyyarsa bai taba karanto wannan shafin ba, bai zaci abin zaiyi girma a gaba yadda yayi a yanzu hannun iyayensa ba, shi kawai hanyar auren Mu’azatu yake nema… He is desperate to have her … Shi a wurinsa dabara ya kulla wadda za ta kai shi ga cikar burinsa. Bai taba jin wannan kalmar wai mut’a da suke ambata ba, shi ba malamin addini ba ne, amma yana da sani daidai nasa, kuma babban gibinsa bai tsawaita bincike a kai ba. Ya yi nadama yadda ba zai iya bayyanawa ba. Ga wani irin tsoro da ya zo ya baibaye shi; tsoronsa na farko kada Baffa ya
ce aure ya haramta tsakaninsa da Hafsat har abada. Tsoronsa na biyu kada ya ce mayarwa da ya yi mata bata yiwu ba. In hakan ta faru shi da aure har abada! Hawayen da yake zubarwa akaiakai ya tada hankalin Baffah, ya kashe kuzarin duk wani batanci da ya yi niyyar yi masa. Cewa ya yi da Uncle Abdulkarim ya yi masa bayanin komai yadda zai gane kan matsalar. Nan ya warware masa yadda Abdul’azeez ya fada masa. Adda Hafsatu sai tafa hannuwa ta ke tana fadin, “Kurucci dangin hauka!”’.
Daddy da tun bayan fara maganar bai ce komai ba ya dubi Addah Hafsatuya ce. “A sanda ya shirya Www.bankinhausanovels.com.ng kwangilar sa shekarunsa sunfi talatin da daya ya girmi kuruciya, zan fi yarda in ya ce ba ya zuwa islamiyyar da nake tura shi, ko babu islamiyya ai akwai abinda da ka ji shi ka san daidai ne ko ba daidai ba ne. Na san dai ba ya son Suhaanar aka yi auren nan, amma ya yaudare mu daga baya ya ce ya amince bayan ya gama boreborensa. Daga ni har Maryama a lokacin mun sa a ranmu in kwanakin da muka diba masa yayi shawara suka cika yazo da gamsashshiyar amsa ta rashin amincewa da auren Hafsat zamu hakura ya auri zabinsa. Amma ya yaudaremu yayi wasa da hankalinmu a karshe ya bige da sabawa Ubangijinsa. Shi ya sa ko na so ganin laifin Maryama kan kafewarta kada a maida aurennan sai in mata uzri’”. Gabadaya suka dauki idanu suka zuba masa har Baffa cike da al’ajabi da takaici.Abdul’azeez ya gurfana gaban Baffa ya ce, “Ku yi hakuri Baffa don Allah, wallahi na yarda na yi ba daidai ba, ba tun yau ba. Na yarda Allah ke hukunta ni da zunubin saba ma dokar aure da na yi da kaunar Hafsat a yanzu. Baffa ban Www.bankinhausanovels.com.ng
taba sanin hakan haramun ba ne, na san dai kawai ba abinda kirki nayi ba, kuma tun kafin na yi sakin na soma kaunarta. Na yi don in kubuta daga dafin alkawarin da na yi wa Mu azatu…”.
Baffa ya kara harzuka,da kakkausar murya ya ce “Wace ce haka? Ashe cika alkawarin da ba na bin Allah da Manzon sa ba wani abin kiyayewa ne? Ashe akwai biyayya ga wata halitta wajen sabawa Mahalicci?”
Abdul’azeez ya sake rikicewa, “Astagfirullah! Astagfirullah!!Astagfirullah!!!”. Ya jera ta har sau uku a lokaci guda ba tare da shan numfashi ba. Ya rike tafin kafar Baffan. “Don Allah Baffa ku maida min ita. Na yi alkawarin zaman aure na hakika da ita datsabtatacciyar niyya har karshen rayuwarmu, ba zan kuma maimaita kuskure makamancinsa ba, ko kusa dashi bazan kara zuwa ba, zan baiwa Mammah hakuri za ta huce ta sa mana albarka, musamman idan na maida ita. Babban burin ta shine ni da Hafsat mu rayu tare karkashin inuwar aure, Baffa zan yi zama na soyayya da amana da Hafsah har karewar numfashinmu ba don Mammah ba, sai don zuciyata da ke son ta da kaunarta”’. Www.bankinhausanovels.com.ng
Babu wanda cikinsu da jikinsa bai yi sanyi ba. Abin da zai sa Abdul’azeez kuka tabbas ba karami ba ne sun sani. Tun fil’azal shi jarumi ne tun yana karami, wanda bai jingina a jikin kowa don ya rayu. Yau ga shi a gabansu yana kuka don ya rayu da Hafsat. Hannunsa Baffa ya kama, ya dago shi ya ja shi ya zaunar a gefensa.
“Abdul’azeez!” Ya kira sunansa.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG