HUTU CHAPTER 12

HUTU 





CHAPTER 12






Hydar na zaune yana lallaba Kausar akan ta taso suje su dawo da Binta amma taki, ba yanda beyi da ita ba ta kiya, wanyanshi ne ya fara ringing ya dauko yaga Ummi ce ke kira ya dauka tareda karawa a kunnenshi ya mata sallama ta amsa sannan tace “in kun samu lokaci kazo kaida Kausar inason ganinku”, “toh gamu nan zuwa”, ya amsa mata dashi sannan ya kashe wayan ya kalli Kausar yace “toh kinji, Ummi wai muzo”, badan taso ba ta tashi ta shirya Nawaf itama ta shirya sannan suka fito. Hydar da kanshi ya jasu a mota ko kadan Kausar bataso zuwa ba dan bataji dadin abinda Binta ta mata ba, ace duk zaman da sukayi akan maganan da be kai ya kawo ba rana daya ta tattara ta tafi ai bata kyauta mata ba. 

A compound din gidan Ummi sukayi parking suka fito Hydar ya karbi Nawaf suka karasa ciki, da sallama suka shiga Binta dake kallo a parlor ba karamin bugawa zuciyarta tayi ba jin sallamansu, da kyar ta iya amsawa tareda gaishesu amma Hydar kadai ne ya amsa dan Kausar koh kallon inda Binta take batayi ba, Binta tasan Kausar na fushi da ita amma ya ta iya, batada yanda ta iya, dolece ta sata barin gidan dan bataga zata iya zaman ba bayan antynta na neman ta hadata aure da mijinta.

“Ina Ummi?”, Hydar ya katse musu shirun da tambayan Binta, “tana daki”, take bashi amsa ya kalleta yace “meyasa kika bar gida ba da izinin mu ba”, shiru tayi yace “ke yanzu abinda kikayi kin kyauta kenan”, tace “a’a”, yace “good, idan zamu koma tareda ke zamu koma, kuma banson makamancin abinda ya faru yau ya sake faruwa”, shiru tayi dan ita harga Allah batajin zata iya komawa tinda Kausar taki ta sake mata fuska. Ummi ce ta sauko daga sama tace “ashe kunzo”, Hydar yace “eh Ummi”, sannan  Kausar ta sauka har kasa ta gaishe da Ummi ta amsa mata fuska a sake tareda daukan Nawaf daketa wasanshi inda yake kwance kan kujera wanda tin dazu Binta keson daukanshi amma ta kasa tashi dan ji take kaman ruwa ya cinye ta. 

Zama Ummi tayi tace “Kausar me ya hadaku da Binta?”, kan Kausar kasa tace “ba komai”, Ummi tayi murmushi tace “tacemin wai kinzo kince mata ta auri Hydar”, “anyi haka Ummi”, cewar Kausar da har yanzu kanta ke kasa Ummi ta kuma cewa “meyasa?”, shiru Kausar tayi na en dakiku sannan tace “saboda a ganina shi zefi kula da ita tinda ‘yar uwarshi ce kuma shi ai yana sonta”, Ummi murmushin su na manya tayi sannan tace “itama Binta tana sonshi ne”, Kausar ta girgiza kai alaman a’a, Ummi ta sake cewa “kuma bakya kishin mijinki ne”, shiru tayi dan idan tace bata kishinsa tayi karya amma indai akan Binta ne ai zata iya danne kishinta, “Kausar”, Ummi ta kirata, a hankali tace “ina kishinsa”, Ummi tayi murmushi tace “toh shikenan magana ta kare, idan basu ne suka sasanta kansu ba karki shiga maganan saboda gaba, kai kuma Hydar bance ka matsawa ‘yar mutane ba, ku barta ta zabi wanda takeso, tayi auren soyayya itama kaman yadda kuma kukayi ba tareda wani ya hadaku ba, sannan daga yanzu Binta ta dawo wurina kenan sedai ta dinga zuwa gaishe ku”, Kausar batace komai ba Hydar ne yayi karfin halin cewa “Ummi ki bari ta dawo gidanmu, Insha Allah bazamu kara takurata akan abinda bataso ba. 

Shiru Ummi tayi sannan ta kalli Kausar, ganin yanayin Kausar yasa Ummi cewa “shikenan, ku tafi da ita amma banson ta kara kawomin korafinku”, “Insha Allah”, cewar Hydar a yayinda yake murza hannun Kausar dan ko ba’a fada mishi ba yasan ranta a bace yake. Se yamma lis suka bar gidan tin a mota har suka kai gida Kausar bata yarda tawa Binta magana ba, sosai rashin yi mata maganan ke damun Binta amma ya ta iya tinda ita ta jawo, koda suka shiga gida kowa dakinshi yayi. Tana zaune kan gado Anwar ya kirata ta dauka suka gaisa har take bashi lbrn ta dawo gida, ranshi beso ba amma se yayi addu’an Allah yasa hakan shi yafi alkhairi, sosai sukasha hira yake fada mata yama mahaifinshi magana tace “Allah ya tabbatar da alkhairi”,

Washegari ya kama Sunday kaman yanda Dad yama Anwar alkawari haka koh akayi, sun shirya shida Uncle Hamza sukaje sukaga Abba kuma alhmdllh Abba ya amince dukda besan Anwar din ba amma tinda ance sun sasanta da Binta toh shima ya amince, sosai su Dad sukaji dadin  karamci irin na Abba, a nan take suka biya sadakin Anwar kaman yadda sukayi na Khaleel, wannan karon ma seda Abba ya rage yace yayi yawa ya karba 50k. Sanda Anwar yaji lbrn ji yayi kaman ya zuba ruwa a kasa yasha dan murna, bayan su Dad sun wuce Abba ya dau waya ya kira Hydar yace yanason ganinsu gabadaya, da toh Hydar ya amsa mishi sannan ya kashe wayan, kallon Kausar dake sawa Nawaf pampers yayi yace “Abba na neman mu, ki fadawa Binta”, ya fada yana mikawa dan ya canza kaya, “ka fada mata da kanka ai tana daki”, se a lokacin ya tuna ashe har yanzu Kausar batawa Binta magana dan koh data gaishe ta da safe ciki ciki ta amsa mata, girgiza kai yayi a zuciyarshi yace “mata kenan”, sannan ya sauka ya fadawa Binta da kanshi sannan ya koma sama. 





Koda sukaje gidan anty Maryam tazo ziyara da yaranta tinda weekend ne, seda duk suka gaggaisa sannan suka wuce parlorn Abba inda yake zaune suka zazzauna Abba ya kalli Binta yace “kiramin mamanku”, tashi tayi ta fita ba jimawa ta dawo tareda Ummi duk suka zazzauna Abba ya dauko kudin da su Dad suka bayar yace “ga sadakin Binta nan an kawo”, ba Hydar ba har Kausar seda taji wani iri amma tayi shiru a yayinda Binta taji dadi ya ziyarce ta dan ko ba’a fada mata ba tasan Anwar ne, Hydar ne yayi karfin halin cewa “waye ya fito”, kallonshi Abba yayi yace “wai sunanshi Anwar kanin Khaleel abokin ka, mijin Zeena” shiru Hydar yayi dan yasan waye Anwar da rashin jinshi kap lbrn Anwar ba wanda Khaleel baya fada mishi har zuwanshi India da dawowan shi duka Hydar ya sani amma baya ganin ze iya hana Anwar Binta kodan abokantakan dake tsakanin iyayensu da wanda ke tsakanin shi da Khaleel amma kuma yasan idan yayi hakan toh beyi ma Binta adalci ba tinda kila ita batasan haka halin Anwar din yake ba, ‘toh yanzu me abinyi?’ ya tambayi kanshi amma ba amsa. 


Dagowa yayi ya kalli Abba yace “Abba ita tana sonshi ne”, kallonta Abba yayi yace “iyayenshi sunce wai yace musu kun sasanta kanku haka ne, kina sonshi?”, cike da jin kunya tace “eh hakane Abba, ina sonshi”, runtse ido Khaleel yayi yayinda Abba yace “toh kaji”, kada kai yayi yace “Allah yasa hakan shi yafi alkhairi”, Ummi da anty Maryam suka amsa da “ameen”, banda Kausar da tayi kicin kicin da fuska tana hararan Binta, kafin wani ya sake magana ta kalli Binta tace “Binta fada min gaskiya wannan Anwar din shine wanda kika fadamin tin haduwar mu dake”, gaban Binta na faduwa ta kada kai alaman “eh”, Kausar tace “toh bazaki aureshi ba”, da sauri Binta ta dago tana kallon Kausar tareda cewa “anty”, wanda batama san sanda ta kira Kausar din ba, Kausar ta maka mata harara sannan ta juya wurin Abba tace “Abba yaron da ake magananshi beda kamun kai”, runtse ido Binta tayi jin ance Anwar beda kamun kai, Kausar taci gaba da cewa “wannan yaron shine wanda ake nema wanda ya dauketa daga gidan Hajiya be mayar da ita ba har ta fada hannunmu”, hawaye Binta keyi yayin da parlorn yayi tsit kowa na digesting maganan da Kausar tayi.




Anty Maryam ce ta kalli Binta tace “Binta wannan yaron shine wanda ya daukeki har ya kaiki hospital sanda baki da lfy da dawowan ki kuma abokinshi ya nemi ya bataki amma be samu dama ba kika gudu”, kada kai Binta tayi tana kuka dan tasan an kusa a rabata da Anwar dinta, anty Maryam da batada hakuri cikin daga murya tace “ba magana ake miki ba kike dagawa mutane kai kaman wata kadangare”, cikin kuka Binta tace “anty shine”, ta fada tana saukowa daga kan kujera ta zauna kasa ta dunkule wuri daya tana kuka dan harga Allah batasan inda zatasa ranta ba idan aka rabata da Anwar, shiru Hydar yayi dan besan me zaice ba, shi dama yasan Anwar bejin magana amma be taba tunanin rashin jinshi ya kaishi har gidan karuwai ba, amma kuma ta wani bangaren zuwanshi gidan ya kubutar da Binta tinda d’ace bai je ba da kila yanzu rayuwar Binta ta gama tabarbarewa, shikuma Abba shiru yayi dan beyi tunanin irin yaron da Binta zataso ba kenan tinda tanada kamun kai, amma indai har yayi confirming cewar haka yaron yake toh tabbas baze bari Binta ta aureshi ba, Ummi kuwa shiru tayi dan tama rasa wani irin tunani zatayi ga tausayin Binta nan duk ya kamata saboda kukan da takeyi, anty Maryam dake zaune tana kallon Binta tace “tashi ki bamu wuri shashashar banza kawai, kikasan yaran mutane nawa ya lalata zaki kawo mana shi gidan mu gidan mutunci zakisa sunanmu ya lalace a gari, toh wlh baki isa ba, wawiya kawai, kuma kema se nazo na dubaki na tabbatar ba’a tabaki ba dan ban yarda da yaron nan ba, Allah dai yasa be miki komai ba”, da kuka sosai Binta ta tashi ta wuce dakin Zeena tasa makulli ta kulle kanta, Abba ya kalli Hydar yace “kamin bincike akan yaron nan zuwa gobe”, Hydar ya amsa da “toh”, dukda ya riga ya gama sanin halin Anwar, rashin ji, shaye shaye, zuwa club, rashin bin maganan iyaye ba wanda be sani ba akan Anwar amma baya ganin ze iya kawowa Abba wannan hujjojin amatsayin binciken da yayi dan yasan muddin ya fada to ba Binta ba Anwar har abada, shikuma son da yakema Binta baze barshi ya rabata da abinda takeso ba, tinda tace Anwar takeso ze kira Anwar din suyi magana man to man kodan farin cikin Binta, yayinda Kausar taji wani sanyi a ranta dan tasan idan Binta bata samu Anwar ba dole Hydar zesa kai tinda yana sonta kuma a lokacin tana ganin da wuya Binta taki yarda.





Tinda Binta ta kulle kanta a daki ba abunda takeyi banda kuka, gabadaya tunaninta ya karkata kan Anwar dan gani take za’a rabasu tinda ko ita tasan kadan daga halin Anwar na zuwa club da shaye shaye bayan haka kuma ai ko ita a gidan karuwai ya daukota, sedai fah dukda haka bata ganin zata iya rabuwa dashi, sedai akai ruwa rana amma bazata yarda a rabata da Anwar ba. Sosai taji kanta ya fara sarawa alamun ciwon kai amma wannan besa take daina kukan ba, tanaji su Kausar na bubbuga mata kofa ta fito su wuce gida amma ta sharesu, tanajin sanda Ummi tace su tafi su barta tinda bata bude ba. 

A nan dakin tayi sallah ta kwanta har bacci ya dauketa, koda ta tashi ana kiran magrib saboda haka tayi sallah ta zauna harseda akayi isha tayi sannan ta koma ta kwanta ba tareda tunanin fita ba, so take ta kira Anwar amma kuma wayanta na cikin jakanta kuma ta barshi a parlorn Abba, ta bangaren Anwar tinda mahaifinshi ya fada mishi an gama magana yake neman layin Binta yana ringing amma ba’a dauka, seda ya mata kusan 20missed calls sannan ya hakura badan ranshi yaso ba, har zuciyarshi yanajin ba lfy tinda Binta bata dau wayanshi ba, haka yayita juyawa kan gado ko masallaci ya kasa zuwa a gida yayi sallah dan Mom kanta ma kasa gane kanshi tayi dan duk a tunaninta ze nuna farin cikinshi tinda an nemo mishi auren wacce yake so amma setaga sabanin haka dan farin cikin da ya nuna na lokaci kadan ne, shima haka ya kwana zuciyarshi ba dadi kaman yadda zuciyar masoyiyarshi ke cikin kunci dukda besan meya sameta ba. 

Hydar da Kausar gida suka kuma kowannensu jiki a sanyaye ba kaman Kausar da take gani kaman batawa Binta adalci ba tinda Anwar din shine farin cikin Binta sedai kuma bata ganin zata iya zama ta zuba ido Binta ta auri Anwar bayan tasan bashida halin kirki, kallon Hydar tayi dake kokarin bude kofan bedroom dinsu tace “she will hate me right?”, kallonta yayi fuskarshi dauke da murmushi yace “no, she won’t, saboda abinda kikayi daidai kenan”, shiru tayi kafin daga bisani tace “I don’t think so, ina gani kaman na rabata da farin cikinta for my selfish interest”, Hydar dake zaune kan gado ya kalleta yace “bangane ba, me kike nufi”, shimfidar da Nawaf daketa baccinshi tayi sannan ta koma kusa da Hydar ta zauna tace “gani nayi idan ba’a bari ta auri Anwar ba maybe ka yarda ka aureta kodan ka share mata hawayenta, wannan dalilin yasa naki rufa mata asiri”, shiru Hydar yayi yana kallon Kausar not believing what she’s saying, wato duka abinda tayi da manufa biyu tayishi, ta samu ya raba Binta da Anwar saboda shi ya samu ya auri Binta, kallon Kausar yayi yana girgiza kai tareda cewa “I’m disappointed in you”, zatayi magana ya tashi ya bar mata dakin ya koma dakin da ke kusa da nata ya kwanta yana tunanin meyasa Kausar ta dage dole seya auri Binta dukda ita yarinyar ta nuna bataso.

Daukan wayanshi yayi ya kira Khaleel, ringing biyu Khaleel ya dauka tareda cewa “soja mazan fama ai nayi tunanin ka manta dani ne”, tsaki Hydar yaja yace “gwara kai duniya tama dadi tinda kana tareda Zeena”, murmushi Khaleel yayi ya kalli Zeena da ta riga tayi bacci a gefenshi sannan yace “toh ya son raina, tinda ina tareda Zeena ai komai ma dadi yakemun ba duniya kadai ba”, hararan wayan Hydar yayi kaman Khaleel din na ganinshi sannan yaja tsaki yace “an kawo sadakin Binta”, Khaleel daya riga yasan dama kiran kenan yace “nasani, kuma the worst part of it is brother dina ne ke sonta”, Hydar ya sauke ajiyar zuciya sannan yace “that’s not even the worst part”, shiru Khaleel yayi yana nazari dan ya tabbata ba lfy ba, “meya faru?”, ya tambayi Hydar, Hydar dake kwance ya tashi zaune tareda labarta mishi abinda ya faru tin daga lokacin da Kausar tace lallai lallai seya auri Binta har zuwa abubuwan da suka faru yau, shiru Khaleel yayi dan besan me zaice ba saboda ya tabbata Abba baze ba Anwar auren Binta ba da wannan halayen nashi wanda ba daya na gari a ciki. Ajiyar zuciya Khaleel ya sauke sannan yace “bari gobe da safe zamuyi magana sannan mu nemi Anwar din muyi mishi magana ta fahimta, koma menene we will resolve it by tomorrow”, kada kai Hydar yayi yace “Allah ya kaimu”, sannan sukayi sallama suka kashe wayan kowa da abinda yake tunani. 

Story continues below

Washegari tinda asuba Ummi ke kwankwasawa Binta kofa amma shiru Binta bata bude ba, tin abin baya damun Ummi hardai taje ta kira Abba ganin gari ya waye amma Binta batada niyar fitowa gashi tin jiya rabonta da abinci, Abba na zuwa ya shiga kwankwasa kofan amma shiru, kallon Ummi yayi yace “baza’a rasa spare key ba, bari na duba ina zuwa”, kada mishi kai tayi ya nufi sashenshi ba dadewa ya dawo da keys dayawa a hannunshi nan suka dinga gwada hardai Allah yasa suka samu wanda ya bude kofan, kwance suka ganta kan gado cikin blanket babu ma alamun ta tashi tayi sallan asuba, da sauri Ummi ta karasa tana tashinta amma shiru Binta ko motsawa batayi ba, Abba ne ya dora hannunshi kan wuyan Binta aikuwa yaji zafi radau, kallon Ummi yayi yace “shiryata muje asibiti, da alama suma tayi kuma batada lfy”, kallon Binta Ummi tayi tausayinta na kara shiganta, Abba fita yayi ya basu wuri Ummi ta samu ya cire jallabiyan da Binta ta kwana dashi sannan ta dauko mata dogon riga mara nauyi tasa mata da taimakon ‘yar aikinta suka kai Binta mota inda Abba ke jiransu, koda sukaje hospital emergency akayi da ita, Khaleel yayi mamakin ganin an kawo Binta da sassafen nan dan shima wata mata akazo da ita emergency akayi kiranshi, seda ya kira Hydar ya fada mishi Binta ba lfy sannan ya shiga ya soma dubata, basu dauki dogon lokaci ba aka fito da ita, aka bata daki a lokacin har Hydar da Kausar sun karaso, kallonsu Khaleel yayi sannan yace “karku damu, ba wani abin tada hankali bane ya sameta illata kukan da tayi jiya ne ya tasar mata da ciwon kai da fever, se kuma rashin abinci amma bayan wannan ba abinda ya sameta sakamakon tana shan magungunanta yadda ya dace, nan da anjima kadan zata tashi, asamo mata abinda zataci”, cikin sanyin murya Kausar tace “bari naje na kawo abincin”, kallonta Hydar yayi tareda yi mata alama kan ta tafi sannan Ummi da Abba suka shiga dakin da aka kwantar da Binta, yayinda Khaleel da Hydar suka fita zuwa haraban hospital din dan su tautauna kan maganan Anwar da Binta. 

Kallon Hydar Khaleel yayi bayan sun jingina jikin mota Khaleel yace “Hydar kai yanzu ya kake gani zamu bullowa maganan nan dan gaskiya Kausar ta mugun bata Anwar gabansu Abba”, ajiyar zuciya Hydar ya sauke sannan yace “kira mana Anwar muyi magana dashi man to man, if he’s ready to change toh ni me iya rufa mishi asiri ne dan farin cikin Binta is all that matters to me, kuma koh ba’a fada ba kaima kasan Anwar ne farin cikinta, akwai shakuwa tsakaninsu tinda ta dade da saninshi, kuma ya taimaketa tinda badan shi ba kila da har yanzu bamusan wacece Binta ba kuma kila da yanzu rayuwarta ta gama tagayyara”, “hakane”, cewar Khaleel dake kokarin ciro wayanshi daga aljihu saboda ya kira Anwar, sannan ya kalli Hydar yace “na tabbata idan Anwar son Binta yake tsakani da Allah ze shiryu kodan kar ya rasata”, kada kai Hydar yayi yace “kira mana shi, aimu masu iya nutsar dashi ne tinda yayyenshi muke”, kiran Anwar Khaleel yayi ya dauka cikin magagin bacci dan besamu bacci a daren jiya ba seda yayi sallan asuba sannan ya samu bacci ya daukeshi, ba bata lokaci Khaleel ya shaida mishi yanason ganinshi a hospital yanzu, dukda baccin dake idonshi wannan be hanashi son zuwa ba, dan haka kurum yaji yanason zuwa asibitin, tashi yayi ko wanka beyi ba illa brush da yayi ya wanke fuska sannan yasa kaya ya fesa turare se kamshi yake, idan ka ganshi bazaka taba cewa beyi wanka ba ya fito, ko breakfast beyi ba ya fice daga gidan. 
Koda yayi parking hango Khaleel yayi yana hira da Hydar, seda gabanshi yayi mugun faduwa ganin Hydar a wurin dan ko kadan bayason ganinshi, a hankali ya karasa inda suke tsaye suka gaggaisa sannan ya kalli Khaleel yace “Yaya ka kirani”, Khaleel ya kada kai yace “kwarai mun kiraka ne dan muyi magana ta fahimta dakai”, seda yaji faduwan gaba jin abinda Khaleel yace, Hydar ya kalleshi yace “jiya anzo an nema ma auren Binta harda sadaki aka bayar amma se bayan tafiyan mahaifinka aka fara kwankwato kan a baka ko kar a baka saboda gashi gashi….. “, nan Hydar duk ya koro mishi halin da ake ciki, sosai idanun Anwar ya kada yayi ja tsabar bacin rai dan a iya saninshi tinda yake a rayuwa so daya yaje gidan karuwai da sunan samun mace dan yayi lalata da ita amma kuma tinda ya hadu da Binta se sha’awan yin lalata da mata ya fita ranshi dan bega amfaninshi ba kuma zuwanshi na farko ma Mahmoud ne ya turashi, shaye shaye ne dai yasan wannan baze musa ba amma tinda ya dawo daga India bikin Khaleel ya hadu da Binta a ranar da yaje bar da sunan shan giya Binta ta kirashi a waya tinda yabar bar din be taba waiwayan wani abu waishi giya ba, sosai su Khaleel sukayi mamakin ganin hawaye na zuba a idonshi dan baze manta ranar da Dad yama Anwar duka ba amma ko digon hawaye se yau ne akan mace yake zubar d’a hawayeshi, lallai ya yarda Anwar nason Binta son da baya ganin nan gaba Anwar zema wata mace irinshi.


Kallon Hydar Anwar yayi cikin muryan dake nuna tsantsar bacin rai yace “zan iya rantse maka da alqur’an ban taba lalata da mace ba, amma shaye shaye bazan musa maka ba sedai kuma na dade da dainawa tin zuwana bikin Ya Khaleel kaga kuwa an shari watanni, I know I’m not perfect sannan kuma kowa nada nashi past din saboda haka na bar maka zabi idan kaga na dace kanwarka ta aureni falillahil hamd, idan kuma bakaga dacewar mu ba shikenan, zan rungume kaddara amma kuma inaso kasan abu daya we don’t judge people with their past”, yana fadan haka yabar wurin ranshi na kuna, duk kiran da Khaleel ke mishi be ko juyo ba balle ya saurari cewarsu. 


Hydar rashin sannin abinyi kan abinda Anwar yace mishi yasa ya kalli Khaleel yace “mu shiga ciki”, jiki a sanyaye duk suka juya suka koma hospital din Khaleel ya wuce office dinshi Hydar kuma ya shiga ward dinda Binta take a lokacin har Kausar ta dawo da abinci ya zauna shima kaman yadda yaga ko wannensu zazzaune kowa da abinda yake tunani, ba su wani dade ba Binta ta tashi, duk da ido ta bisu amma ba wanda tawa magana dan gani take kaman duk basason farin cikin ta, Ummi ce tayi karfin halin cewa “tashi ki wanke baki kici abinci”, bata musa ba dan ita kanta yunwa takeji, da taimakon Ummi tayi brush taci abinci, duk wanda ya tambayeta ya jiki sedai tace “da sauki”, amma ko kadan bata sake musu fuska ba, Abba da Hydar sun hango abinda yasa taki sake musu fuska, Khaleel ne ya shigo ya bata magunguna tareda discharge dinta.


Sanda suka koma gida parlorn Abba ta shiga ta dau jakanta wanda tasan wayanta na ciki ta koma dakin Zeena wanda ta mayar nata yanzu, kwanciya tayi ta shiga kiran wayan Anwar wanda be bata lokaci ba ya dauka, salama ta mishi ya amsa mata tareda tambayarta inda ta ajiye waya, nan ta fada mishi inda ta bar wayan tareda koro mishi jawabin abinda ke shirin faruwa dasu, murmushin takaici yayi tareda cewa “da alama anty dinki bata sona”, ajiyar zuciya Binta ta sauke sannan tace “ba haka bane, amma don’t worry I won’t let them separate us no matter what”, murmushi yayi yace “karkice haka, idan sukace bazaki aureni ba kema kinsan babu yadda zamuyi, saboda haka karki bani hope bayan ni kaina a yanzu bansan a wani aya nake ba, se abinda family dinki suka yanke ne se tabbatar mun dako zan samu aurenki ko bazan samu ba”, hawaye takeyi dan a ganinta ko za’a hada sama da kasa Abba baze bari ta auri Anwar ba, jin kaman tana kuka yasa Anwar cewa “karki yimin asarar hawayenki, let’s keep praying kinji”, kada kai tayi kaman yana gabanta sannan tace “indai basu bari na aureka ba, toh nima bazan auri kowa ba”, dariya yayi saboda ganin tsantsan yarinta tattare da ita sannan yace “shikenan my baby girl, Allah ya shige mana gaba”, tace “ameen”  sannan suka dauko wani hiran kaman basu da matsala tattare dasu. 



A WEEK LATER

Har sati daya yaje shude amma Anwar da Binta kaman wa’anda basu da damuwa tattare dasu, ta koma school abinta amma bata yarda ta koma gidan Kausar ba, Kausar ba karamin missing din Binta takeyi saboda yadda takejin gidan ba dadi idan ba Binta. Yau weekend Abba ya tarasu gabadaya saboda su tautauna kan maganan Binta dan Binta ta musu kaura, tana gidan ne bata gidan dan bata shiga harkan kowa, sosai ta nuna musu bacin ranta saboda haka Abba ya hada meeting kodan asan abinyi Binta ta daina wannan zaman kadaicin da takeyi a daki ita kadai kullum. Duk suna zazzaune a parlorn Abba harda ita Binta kanta Abba yayi gyaran murya sannan ya kalli Hydar yace “nace kamin bincike akan yaron nan amma har yanzu na jika shiru”, sunkuyar da kai kasa yayi yace “Abba an gama binciken”, Abba yace “toh ina jinka”, Binta kallon Hydar tayi dan taji me zaice shima kallonta yayi ya sakar mata murmushi sannan ya juya kan Abba yace “Abba nayi bincike kan yaron kuma gaskiyan magana shine wannan yaron da farko dai ba mazinaci bane kaman yadda ake zato dan shi kanshi tsautsayi da abokai ne suka sashi zuwa gidan karuwai amma koda yaje babu wani daya aikata na alfasha”, kada kai Abba yayi sannan yace “toh maganan shaye shaye fah?”, nan ne Hydar ya sunkuyar da kai Binta kam har yanzu bata dauke kai daga kallonshi ba dan idanunta har sun ciko da kwalla saboda ta tabbata idan Abba yaji Anwar na shaye shaye shikenan tata ta kare, kai a sunkuye Hydar yace “Abba yana shaye shaye a da amma yanzu ya bari kusan watanni shida da suka wuce”, shiru Abba yayi sannan yace “kanaso kacemin a halin ya daina shaye shaye”, Hydar yace “kwarai kuwa Abba”, Abba ya kalli Binta yaga ta sunkuyar da kanta kasa, da alama kukan zuci takeyi, kukan da yafi ko wani kuka kuna da ciwo. 



Murmushi Abba yayi yace “naji bayaninka, kuma a bisa bayanin da kayi a halin yanzu zamu iya cewa yaron beda wani aibu sedai ban tashi bashi Binta ba dan bamusani ba ko tuban mazuru yayi, na bashi nan da shekara daya yayi proving kanshi, ban yanke mishi zuwa wurin Binta ba, ze dinga zuwa suna ganin juna suna zantawa amma idan naga ko naji wani abu tattare dashi wanda be kwanta min ba dole ke Binta ki rabu dashi, idan kuwa har shekara ta zagayo banji wani aibu tattare dashi ba zan aura mishi ke tinda a lokacin zaki gama karatun secondary dinki dan Hydar yace min a ss2 yakeso ki rubuta waec, sannan inaso ki riki kanki da mutuncin kinji”, cike da murna ta kada mishi kai yace “Allah ya miki albarka”, duk suka da “ameen”, Binta dadi takeji sosai at least ko ba komai yanzu tanada hope kan Anwar dinta. Abba ne ya kalli Hydar sannan yace “inason ka gana da yaron akan maganan da mukayi dan ya fahimta”, kada kai Hydar yayi yace “Insha Allah Abba”, Kausar dake zaune kusa da Ummi ta kalli Abba tace “Abba dan Allah inaso mu tafi da Binta idan zamu wuce gida”, murmushi Abba da Ummi sukayi Abba yace “gaki gata seku sasanta kanku”, murmushi Binta tayi dan ita a yanzu ai kowama tana shiri dashi tinda ba’a rabata da Anwar dinta ba. 



Tana zaune daki tana hada kan kayanta Kausar ta shigo dauke da Nawaf a hannu, a hankali ta karasa ta zauna kan gadon tana kallon Binta dake kokarin daukan Nawaf Kausar tace “Binta nasan na miki ba daidai ba, kiyi hakuri ki yafemin ki dawo gida, wlh gidan ba dadi idan babu ke, kinga Nawaf ma kanshi yayi missing dinki”, murmushi Binta tayi tana kallon Nawaf dake mata wasa tace “anty karki damu tareda ku zan koma, kingama hada kayana nakeyi”, ajiyar zuciya Kausar ta sauke sannan tace “thank you Binta”, murmushi kawai Binta amma batace komai ba dan yanzu batada burin da ya wuce taga Anwar ya ganta saboda ta fada mishi ita din tashi ce, se gab magrib suka bar gidan harda Binta suka koma gida, Binta tayi mamakin ganin dakinta a gyare, a wanke mata toilet dinta, sannan kayan wankin da ta bari ma an wanke mata, kuma tasan babu wanda zeyi wannan aikin se antynta, zama tayi kan gado tareda ciro wayanta ta kira Anwar amma be dauka ba saboda yana sallah saboda haka ta ajiye wayan itama ta tashi ta shiga bathroom dan ta samu ta kimtsa saboda tayi sallah. Da shiganta bathroom ta cire kaya zatayi wanka taga abinda ya mugun razanata, batasan time dinda ta saki wani razanannen ihu ba wanda seda gidan ya amsa, Kausar da sauri ta fito daga daki Hydar na biye da ita a baya har suka karasa dakin Binta, ganin a bathroom take ihu yasa Hydar jan birki yayinda Kausar ta karasa har cikin bathroom din, turus Kausar tayi ganin Binta tsaye ba kaya tana kallon pant dinta a kyamace tana hawaye sosai, “Binta”, Kausar ta kirata, da sauri ta dago tana kallon Kausar dan bataji shigowarta ba, batasan sanda taja towel ta rufe jikinta ba Kausar da batama nuna ta damu da yanayin da taga Binta na rashin kaya ba tace “Binta lfy”, hannun Binta tasa tana nunawa Kausar pant dinta dake kwance kasa, ido Kausar takai wurin wanda tana kallon abinda Binta kema kuka, kiris ya rage Kausar batayi dariya dan sosai dariyan ke cinta amma ta danne sannan tace “Binta wannan ai ba komai bane, alamun balaga ne, yi wanka zan miki bayani, bari na dauko miki pad na dawo”, da haka Kausar ta fita tana dariya Hydar dake tsaye yace “meya sameta?”, Kausar dake dariya tace “nothing serious”, ganin Kausar na dariya yasa Hydar daga kafada sannan ya fita, Kausar pack din pad ta daukowa Binta sannan ta dawo dakin, tana zaune Binta ta fito har tayi wankan, nan Kausar ta nuna mata yanda akesa pad jikin pant, bayan Binta ta shirya tasa kaya Kausar ta zaunar da ita ta mata bayani dallah dallah kan jinin da ta gani, kunya ne ya kama Binta dan se a lokacin ta tuna malaminta ya karantar da ita akai, ganin alamun tanajin kunya yasa Kausar fara tsokananta tana cewa “ahh lallai bari naje na fadawa Abba Binta ta shirya aure dan abinda takeso kenan tinda har take daddage ta fara haila”, hannu Binta tasa ta rufe fuskarta tana murmushi Kausar kuwa zama tayi tana mata dariya tareda cewa “ashe sister dina matsoraciya ce, bari na kira Zeena na fada mata bestie dinta matsoraciya ce”, dariya Binta tayi amma batace komai ba haka suka zauna Kausar na zolayan Binta hardai wayan Binta ya fara ringing sanin me kiran yasa Kausar fita ta koma dakinta inda ta tarar Hydar ya fice zuwa masallaci Nawaf kuma yayi bacci. 

Binta daga wayan tayi tareda sallama Anwar ya amsa mata tareda tambayarta ya take tace tana lfy, hira sukayi sosai har ta bashi lbrn hukuncin da Abba ya yanke wanda shima Anwar sosai hakan ya mishi dadi saboda ya samu ya gama youth service dinshi kafin lokacin, wanda an dade da yin posting dinshi zuwa FAAN dake Abuja, basu sukayi sallama ba seda sukaji kiran sallahn Isha sannan ya mata sallama tareda mata alkawarin ze kira idan ya idar da sallah, kwanciya Binta tayi bayan ta gama wayan ta shiga tunanin wai yau itace ta balaga tinda ta fara haila, toh meyasa nata bezo da sauri ba har seda ta shiga 15yrs going to 16, bayan ta tina koh a school dinsu cewa akayi mostly girls at the age of 12 suke balaga, haka tayita tunanin da beda kai balle kafa hardai Kausar tazo ta kirata dan taci abinci.

Komai ya koma normal tsakanin Kausar da Binta kaman basu taba samun wani sabani ba, suna zaune lfy yayinda suke ba Nawaf kulawar da ta dace a tare inda Hydar ya maida hankali kan ganin ya bama iyalinshi farin cikin da suke nema, yana zuwa aikinshi ba tareda sa wasa ba, ya samu yawa Anwar magana kuma alhmdllh sun fahimci juna, Kausar tayi enrolling kanta a catering school wanda Hydar ya bata full support dari bisa dari, yayinda ko kadan bata kiwan yin aikin gida, tana shara tayi mopping tayi dusting ta kuma wanke toilet ba tareda ta nuna gajiyawarta ba yayinda Binta ke taimaka mata da wanke wanke da sauran ayyukan da baza’a rasa ba, Binta ta maida hankali kan karatunta saboda waec din da ke approaching dinta. 

Agurguje

A YEAR LATER

Lokaci tafiya yakeyi a yayinda kwana daya ke zama sati, sati ya zama wata, wata ta zama shekara, a yayinda lokacin mutane ke tafiya kaman kyaftawan ido (Allah yasa mu cika da imani). Alhmdllh yau Binta ke graduation din gama secondary school, Hydar, Kausar da Nawaf, Khaleel, Zeena da ‘yarta Ibtisam , Ummi, Abba, Anwar, Anty maryam da yaranta ba wanda be hallaci graduation dinta ba, she felt loved, har hawaye seda tayi saboda murna, bata taba kawowa a ranta akwai ranan da zata wayi gari taga ta gama makarantar boko ba, kowa congratulating dinta sukayi, they felt proud of her, it’s not easy ace ka fara karatu daga sama ba tareda kasan komai ba amma in a short period of time harka gama wanda ba komai bane yasa take gane karatun har tayi saurin gamawa ba illa sa kanta da tayi da naci, Kausar couldn’t ask for more, yau ga Binta ta gama secondary abinda take burin gani yau gashi Allah ya nuna mata. 

Se yamma lis duk suka koma gida a gajiya, suna dawowa Binta ta shiga dakinta wanda a halin yanzu dakinta ya koma sama kusa dana Nawaf, wanka tayi sauri sauri saboda Anwar yace mata zezo, riga da wando tasa sannan ta dau hijabi har kasa tayi sallolin da ake Binta ta hada magrib sannan ta tashi ta gyara fuskarta ta dora after dress kan kayanta, tana gamawa Anwar na kira, murmushi kwance a fuskanta ta dau wayan tareda sallama, amsawa yayi sannan ya shaida mata yazo tace gatanan zuwa, seda taje ta fadawa Kausar sannan ta sauka kasa, tayi mamakin ganin Anwar a compound dan tasan idan yazo parlorn baki yake shiga tazo su sha hiransu, karasawa tayi wurinshi tace “meyasa baka shiga ba?”, yayi murmushi tareda mika mata ledan hannunshi yace “sauri nakeyi, yanzu zan wuce, ga abinda nazo kawo miki”, shagwabe fuska tayi tareda cewa “haba Ya Anwar daga zuwa kuma se kace zaka tafi akan wani dalili”, murmushi yayi dan shi a rayuwa idan akwai abinda ke matukar burgeshi tattare da Binta toh shagwabanta ne, cikin sanyin murya yace “idan bakyaso na tafi toh bazan tafi ba”, da sauri tace “Yauwa karka tafi dan ban gaji da ganinka ba”, dan murmushi yayi yarse da hakwaranshi suka nuna sannan yace “toh mu shiga ciki”, da murnarta ta juya suka shiga ciki Anwar a ranshi yace “Binta badai yarinta ba”.


Jama’a ya lbrn Zinaru da antyn Birni da Hajiya me gidan dadi, Hajiya da Antyn Birni sun dade da fitowa daga prison yayinda Hajiya tana fitowa ta nemi gida ta kama da dan abinda ta tsira dashi sannan ta nemi islamiyyan matan aure dake unguwar ta shiga, kullum cikin istigfari take ba dare ba rana dan tasan ta salwantar da rayuwar yaran mata dayawa, wanda a sanadiyan ta suka shiga barikanci, tasan cewa akwai hakkin mata dayawa a kanta dan ko a yanzu wata tayi zina wacce ke karkashinta toh tasan itama tanada kaso a cikin zunubin da za’a rubuta mata. Antyn Birni kuwa tana fitowa ta koma aikin barikancin ta ba tareda tayi nadaman wani abu tattare da ita ba dan kuwa duniyancin ta takeci hankalinta kwance.



Yau wa’adin da aka dibarwa Zinaru ya cika, saboda haka yau aka fito da ita daga prison, wani hamdala ta sake data ganta a waje wani iska mai ni’ima na ratsa duk wata sassa na jikinta, daga prison bata tsaya ko ina ba se inda tasan zataga antyn Birni, cikin sa’a kuwa ta sameta tana shirin fita, da mamaki antyn Birni ke kallonta tace “wai Zinaru har an sakoki?”, Zinaru da batada wani buri daya wuce taga tayi wanka taci abinci tace “gashi kina gani, ni ban ruwa nayi wanka”, da mamaki Antyn Birni ta zuba mata ruwa a bokiti ta kai mata dan kewayen ta sannan ta dauko mata soso da sabulu, kafin Zinaru ta fito Antyn Birni ta fito mata da kaya sannan ta fita dan ta siyowa kanwarta abinci saboda koh ba’a fada mata ba tasan Zinaru najin yunwa, Zinaru na fitowa ta shirya cikin kayan da Antyn Birni ta dauko mata tasa  sannan ta zauna tana jiran dawowan Antyn Birni ba tareda tayi tunanin sallah ba balle salati ba, ba dadewa Antyn Birni ta dawo da jollof rice cikin kwano ta ajiyewa Zinaru sannan ta zauna gefe tana kallon yadda Zinaru ke cin abinci kaman wacce ta shekara bataci abinci ba.  Tana gamawa batayi wata wata ba tace “Anty abinda yasa kikaga na biyo tanan saboda banda ko sisi a tattare dani ne, yanzu kudi nakeso ki bani inyi kudin mota zuwa kauye dan naga malam saboda wlh nawa kaina alkawarin muddin ina numfashi toh yarinyar nan Bintoto ba ita ba zaman lfy. 

Toh fah readers kunji wata sabowa, ga Zinaru ta fito kuma tana tunanin komawa kauye dan taga malaminta saboda kar Binta ta samu zaman lfy, da alama Zinaru bata horu sosai ba. 
Kaman yadda Zinaru ta bukata haka Antyn Birni ta dauki kudi ta bata ba tareda ta mata fada koh wani abu ba, da kanta ta raka Zinaru har tasha ta shiga motan Adamawa amma zata sauka a kauyensu, seda Antyn Birni taga tashin motansu sannan ta juya ta kama harkan dake gabanta. Zinaru a mota duk ta kasa zama wuri daya, ta juya nan ta juya chan duk ta takurawa na gefenta dan Allah Allah kawai take ta ganta a kauyensu, ji take dama ta zama tsuntsuwa dan kawai ta ganta gaban malam, tsaki taja sanda motansu ya lallace a hanya akace su fito a gyara, banda masifa ba abinda take zazzagawa driver wai dama yasan motarshi batada lfy ya kwashe su aciki, banza yayi da ita yayinda wasu sukayi kokarin fahimtar da ita ai irin haka na faruwa, nan ma ta hada dasu ta zaga.



Seda taga tashin mota sannan hankalinta ya kwanta, nan duk suka shiga ta damesu cikin mota har aka kai inda zata sauka ta sauka, gabadaya en cikin motan seda suka bita da “Allah ya wadar hali irin nata”, tana sauka ta dauki dan achaba ya kaita har cikin kauyensu sannan ta biyashi ya kara gaba.




Tindaga inda aka sauketa ta fara ganin canji, ganin yara kanana cikin uniform suna dawowa daga makarantar yamma dauke da littatafansu na islamiyya wanda ba kowane yayi wannan kokarin ba illa Hydar, haka tayita kusawa cikin gari har ta kawo gidanta data siyarwa mai gari, tayi mamakin ganin gidan ya koma masallaci ga islamiyya a gefe wanda ake both Arabic da boko a ciki, ba komai yasa ta gane gidan ba sedan gidan makocinsu mallam Mamman dake nan gefe har yanzu, tin ba’aje ko ina ba gari ya dauka cewar ga Zinaru ta dawo, har gidan mai gari seda sukaji lbrn. 




Cike da mamaki ta karasa gidan Malam dake chan karshen kauyen, tayi mamakin ganin an kewaye gidanshi da kara, sallama ta dinga makawa amma shiru ba amsa, daga karshe kutsa kai tayi cikin gidan inda tin daga waje takejin wani irin wari na bugota, tushe hanci tayi da mayafinta sannan ta karasa ta daga dan zanin da yayi labule dashi wanda ya gaji da kodewa, kutsa kai tayi cikin dakin inda taga malam yashe a kasa kaman kayan wanki tsutsotsi na bin jikinshi, duk kashi ya bushi a jikinshi gashi ya jika wurin da fitsari, a rikice tace “malam kaine?”, da kyar ya iya bude ido ya kalleta dakyar magananshi baya fita sosai yace “Zinaru ashe zan sake ganinki?”, matsawa baya Zinaru tayi malam yayi murmushi takaici yace “idan kowa ya gujeni aike be kamata ki gujeni ba”, kara toshe hancinta tayi saboda the scent is unbearable sannan tace “malam meya sameka haka, mutanen gari sunsan kana cikin wannan halin kuwa?”, da kyar ya kalleta yace “hakkin mutane Zinaru, hakkin mutane, hakkin mutane be bari na zauna lfy ba, kuma kema nasan baze bari ki zauna lfy ba sannan kowa a garin nan yasan halin da nake ciki hatta mai gari wanda shine yace a katange gidana da kara sannan kuma ya hana kowa zuwa wurina balle su bani taimako”.




Shiru Zinaru tayi tana tunanin maganan malam kafin daga baya itama ta juya ta fita duk kiran da ya mata ko waiwayowa batayi ba dan tasan a halin nan da yake ciki ba shida wani taimako daze iya bata, tana fita yaran gari dake jiranta chan nisa da gidan malam suka fara jifanta da dutse suna kiranta mayya, harda mata wakan ta bar musu gari kar ta jawo musu annoba, sosai tayi nadaman zuwa kauyen nan, ita gashi batasamu abinda tazo nema ba, gashi yara kanana wa’anda ada kallo daya zata musu suji tsoronta sune yau suke jifanta da dutse suna binta da waka suna kiranta mayya, batasan kuka takeyi ba seda taji hawaye a fuskarta, koda suka kai ta wurin gidan mai gari duk suna zazzaune amma ba wanda yayi yunkurin hana yaran a haka har suka rakata wajen kauyen sannan suka juya suna tsalle suna murna sun kori annoba, wuri ta samu ta zauna tana kuka, duk jikinta jini ne saboda ciwukan da taji yayinda ake jifanta, gashi ba tada kudin motan komawa dan ta yar da jakanta a hanya.





✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴



Wasa wasa gashi Binta na nema ta zama na Anwar dan kuwa a yau akasa rananta nan da wata biyar saboda ta samu tayi saukan alqur’aninta, sannan shima Anwar ya samu ya gama youth service dinshi, murna a wurinsu ba magana, kowa ya musu murna dan hatta Kausar ta sauko kuma sosai ta nuna farin cikinta, Kausar tayi enrolling din Binta catering school dinda take zuwa kuma sosai ta maida hankali tana koya dan idan aka koya musu abu idan ta dawo gida se ta kara gwadawa, Kausar tace ta dauki nauyin kayan furnitures din Binta, Hydar kuma yace ya dauki nauyin suturunta, anty Maryam tace ta dauki nauyin kayan fitanta na biki, Zeenah kuma tace ta dau nauyin kayan da zatasa idan sun shirya wani event din, kowa bayaso a barshi a baya, Ummi da Abba kam ba bakin magana ganin yaransu sun dauke musu duk wani nauyi daya rataya a wuyansu amma duk da haka sunce bazasu zauna su nade hannu haka kawai ba, saboda haka Ummi tace ta dau nauyin dauko me gyaran jiki da lalle da makeup inda Abba kuma ya dau nauyin en uwa daza suzo biki da kuma abincin da za’aci, duka wannan shirin Binta batasan dashi ba.




Ta bangaren Anwar suma shiri sukeyi sosai, Abba ya bashi tangamemen gida duplex me parlour biyu da dakuna shida, biyar a sama se daya a katsa, se kitchen da store da balcony, a matsayin nashi gudunmawan, Anwar yana saving kudi wurin Mom na lefe kafin lokaci yazo, ba wanda ya kai Meenah burin ganin wannan rana da yayanta zeyi aure, Khaleel ma ba’a barshi a baya ba shima ya bada nashi gudunmawan na daukan nauyin kayan abinci da kuma akwatin lefe da inda en uwansu baki maza zasu sauka, Mom ma ba’a barta a baya ba dan ta riga ta hada kusan rabin lefen ba tareda sanin kowa ba, Anwar ya kira abokanshi MK da Jamil ya shaida musu ansa rananshi sosai suka tayashi murna bayan sun gama mishi tsiya sannan suka shaida mishi se sun gama hada yadda bikin ze kasance sannan zeji daga garesu wanda wannan ko kadan be dameshi ba dan yasan they won’t let him down.




Kuyi hakuri baku jini kwana biyu ba kuma dana tashi typing se nayishi kadan, wlh banjin dadi ne shiyasa kuka jini shiru, kuma yauma karfin haline yasa nayi typing saboda karkuga kaman ina ja muku rai, nvl din ya fara zuwa karshe da yardar Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *