CONEL AHMARD CHAPTER 3

CONEL AHMAD






CHAPTER 3







Tin a airport Madina tasauka daga kan keken marasa lfyn da take akai, cool susi tace “au..bazamaki bari har mu isa kenan” tafad’a cikin murmushi itakwa tace “inafa zan iya, ai wlh namatsu mudawo dan nagaji da xama akansa ssi” nan suka kyalkyale da dariya.

Driver d’in su chuchu ne yazo d’aukansu danhaka ana fito da kayansu suka d’auka sannan suka fice izowa gida,

RAHA suka fara sauka inda Madina taje tama tsofaffin k’auyen su gdy sannan tamasu daddad’an albishir amma tace sujira harta sake dawowa, Saida suka kwana d’aya anan Raha sannan suka fice izowa birnin kebbi.

Around 2pm dot suka isa birnin kebbi d’in, dik agajiye suke dan can Raha dinma basu samu sunhuta ba, danhaka suna isowa sukai wonka suka canja kaya taredacin abinci saisuka bi lafiyan gado, jawahir kam batajin bacci, data gaji da wasa itakad’ai saita tafi gun momy abunta.

…….Washe gari around 6pm Dr. Isma’il yazo, koda yazo basanan sun fita unguwa nan yashiga yagaisa da momy sannan yafice.

Around 8pm bayan sundawo saiya sake dawowa, saida tasakeyin wonka tasauya kaya izowa sket da riga na atampa green and white color, tasha make-up sannan tai daurin ture kaga tsiya, bayan tagama dika tasaka d’an tirare mara k’amshi sannan tayafa mayafinta green color tasaka takalma sannan tad’auki phone dinta tafita.

A inda suka saba zama koyaushe idan yazo yanzuma acan yazauna danhaka tana hangosa can itama taje,

Tinda takamo hanya yakafeta da ido hana kallon yanda take tafiya cikin nutsuwa, dakuma yanda tasha ado kamar wocca zata woni babban biki, kallonta yake yana murmushi zuciyarsa cike da farinciki da gdy ga Allah daya bashi mata kyakkyawa mai hankali da tarbiya dakuma nutsuwa, komai nata a natse takeyinsa hatta tafiyar ma a natse takeyinta,

Harta kariso bai daina kallonta ba yana murmushi, tana isowa tamasa sallama tareda zaunawa kan carpet d’inda yake shimfide a wojen sannan tace “irin wonnan kallo haka my noor, ai saikasa nafadi ka kafeni Kanata kallo kamar yau kafara ganina”

Woni irin murmushin yai wonda yake k’ara masa kyau sannan yace “ai ke a kullum sabuwa kike k’ara dawoman, dik sadda naganki sainaga kamar lkcn ne nafara ganinki, kinada tsabar kyau gimbiyata, komai naki is accurate nd u look so beautiful so cutie,

To barekuma kinyi ado da kwolliya, saiki kara rikitani, shys kike ganin nake kasa controlling idanuwana idan naganki, musamman idan kina tinkaroni kina wonnan tafiyarki taki wocca take k’ara rikitani”.

Murmushi tai sannan tacemasa “wonnan kod’awor tayi yowa my noor, karka saka kaina yafashe, dan nidai nasan bankan matsayinda kake dorani akaiba dan nasan dik kyawona bankai na madam ba” tafad’a cikin yanayin tsokana.

Hararanta tareda Shan kunu sannan yace “Kinga mubar wonnan zancen dan Allah, karkisaka muna cikin farincikinmu yanzu raina yabaci” murmushi tai tace “Allah yabaka hak’uri my noor”.

Gyara zamansa yai yafuskantota cikin fara’a sannan yace “ya..ina muka kwana da maganarmu, tinda kindawo kuma kincika burinki, so inasan nanda 1week nakawoki gidana, maana muzama ma’aurata” d’an sadda kanta tai kasa tana wasa da yatsunta sannan tace,

“Nasan kayiman uzuri, kuma nasan halinda kake ciki, amma dan Allah har yanzu ina rokonka dakayi hkr akai bikin nan zowa next month, bcoz I have many thing danakeso nayi kamin auren, so plss and plss ka k’ara hak’uri dan Allah”.

Sam Isma’il baiso hakaba amma ina bayanda ya’iya sbd Madina tafi k’arfin komai agaresa, kallonta yai sannan yace “Ok…bdmwa, Allah yakaimu, but inasan aje asaka mana rana kuma ayi sadaki yazama na lkc kawoi muke jira yazo”.

Story continues below

Murmushi tai tace “badamuwa, Allah yanunamana lkcn” yace “ameeeen… gimbiyata” yafad’a dasauri, aikwa me Madina zatayi inba dariya ba,

Shima d’in dariyar yai yace “karkiga laifina, banida maraba da gwauro, yanzune zansan nayi aure, ammafa saikinyi hak’uri dani, dan inacikin sahun maza masu jaraba” yafad’a tareda kashe mata ido d’aya, dasauri tarufe fuskarta cikin yanayin kunya tareda fad’in,

“Haba my noor, meya kawo wonnan zancen kuma” dariya yai sannan yace “ai gwonda nafad’a maki sbd kizama cikin shirin zama jaruma domin biyawa mijinki buk’atar sa”.

Kunya dikta mamayeta takasa bud’e fuskarta sai Yar murmushi takeyi, kallonta yai yace “a,a..to bud’e fuskar mana, ai bazan sake fad’a ba, kuma naga ai taimakonki nai, dana barki acikin duhufa saikinzo kidinga Shan wahal…” kukan shagwab’a tafara masa tana fad’in,

“Nidai kabari wlh, bawoni taimakona dakai, tsoratani ne kawoi kakeyi” tafad’a tareda hararansa, dariya ya kyalkyale daita sannan yace “gsky shagwabar nan tamaki kyau, plss karki dainaman ita, Kinga saina hada baby biyu, ke dakuma jawahir” dariya tai tareda gyara zamanta.

Sunjima ssi sunashan soyayyarsu kamin daga bisani yamata sallama yafice,

Koda takoma saita tadda su chuchu a parlon momy sunacin abinci tuwon shinkafa da miyar kuka, nan itama tazauna tasaka hanu sukacigaba da ci atare, jawahir tini tai bacci tana rungume ajikin chuchu, Madina tacemata “tai bacci kije ki kwontarda ita mana, amma haka ai bazakiji dad’in cin abincin ba”.

Chuchu tace “waya fad’amaki haka inajin dad’in ci kowa” saita tabe baki sannan tagyara zamanta tace “am guyz..dama inasan zanfada maku woni abu, idan kunada wota shawara saiku bani” Nan sukace “Ok…muna jinki Ormme jawahir” saitai murmushi sbd sunanda suka kirata dashi, yamata d’adi.

Cigaba tai da fad’in “kud’inda aka banine nace, zan gina makarantan islamiya da boko dasu zankuma gina rijiya najanyo pampo a k’auyen mu, zanginasune wa y’ar uwata da mahaifiyata, inasan ladan yadinga zowamasu acikin kabarburansu, zankuma gina asibiti kyauta a kayenmu, kud’in jawahir kuma inaso nakaita k’asar MADINA domin tai karatu inaso tazama abar koyi wa mata sauran kudinta kuma zan adana mata a account d’inta harta lkcnda tagirma zatai aure, amma mekukace wonnan shawararda nai ce”.

Numfashi suka sauke a tare sannan cool susi tace “wonnan shawarace Mai kyau, kinga koba komai y’ar uworki da mahaifiyarki zasuyi farinciki kuma zasuji d’adi dan mamaci ba abunda yake nema kamar addu’ah dakuma lada mai tsabta” chuchu kuma tace “kuma Kinga yarki zata tashi acikin San addininta, zatai rayuwa Mai tsabta, zata kuma samu background Mai kyau insha Allah wonda harmu zamuyi alfahari da’ita, ke harma wonnan mugun uban nata shima zaiyi alfahari da’ita wota rana”.

Murmushin jin Madina tai sannan tace “to Alhmdllh, saikuma munyi magana da Isma’il yace magabatansa zasuje Raha ayi sadaki sannan asaka lkc, so yake zowa next month ayi bikin insha Allah” dariyar farinciki sukai cool susi harda mikewa tsaye tadinga rowar murna, chuchu tace “Alhmdllh, rayuwa mai d’adi, Allah kasadamu da dad’in lahira” suka amsa da ameen.
________________________

Acikin k’ank’anen lkc kowa aka fara ginin makarantar boko tareda islamiya, sannan aka gina rijiya aka ja pampo mutanen k’auyen suka fara diban ruwa, saikuma wota katafariyar hospital itama da’aka fara ginawa dik acikin kauyen na Raha,

Madina kuma tasaka aka fashe gidansu gaba d’aya aka sake masa sabon gini Mai dauke da 3bedrooms 2palors da kitchen, dakuma woni parlor na Abban ta wonda yake had’e da bedroom da toilet d’insa, saikuma harabar gida da makeken gate d’insa,

Acikin k’ank’anen lkc aka kammala ginin aka zubamasa kayan furniture’s komai da komai sannan tasaka aka nemowa Abban ta mata akai auren, bayan auren sannan taginamasa katuwar plaza mai d’auke da sunan jawahir,

Story continues below

Hakama sauran gine ginenda akeyi komai ankammala kayan aiki naciki kawoi yarage, hospital d’in akamata suna MUNAWARAH GENERAL HOSPITAL yayinda school d’in kuma aka sakamata suna JAB’BO INTERNATIONAL SCHOOL tana d’auke da nursery, primary and secondary School,

Islamiyar kuma jab’bo malja’ussunnah Raha, dika ko sisi baabiya sai only PTA money kawoi suma kuma d’ari biyu ne kacal sai uniforms dazaka dinkawa yaronka da sauran tarkace.

A gab da islamiyar kuma akwoi kaaton masjid wonda dik acikin ginin.

Bayan angama ginin sannan aka saka kaya, school din akasaka mujeru da white board da dai sauran tarkace, office d’in malamai ma komai ansaka, hakama hospital d’in koina ansaka kaya komai da komai da ake buk’ata,
Acikin k’ank’anen lkc akafara aiki acikin hospital d’in hakama school d’in a karon farko dalibai dari da shida aka d’auka, yan nursery da primary, uniforms dinsu mata sket da riga da hijab maza kuma wondo da riga da hula, wando green color riga kuma light green hakama hijab light green, maza kuma hula green, hakama islamiya uniforms dinsu blue color.

“Alhmdllh burina yacika, ya Allah ka kai ladan wonnan aikin ixowa ga mahaifiyata da y’ar uwata” Madina tafada lkcnda sukazo ganin aikin ita dasu chuchu,

“Ameeen….” sukuma suka amsa dashi.

On 10th January 2020 ne zaa d’aura auren Madina da noor d’inta Dr ismail, yau kuma sati biyu kacal yarage afara gudanarda shagalin bikin, danhaka tini suka shirya domin tafiya k’asar Dubai su siyo kayan d’aki.

Ranar wota Saturday around 2pm dot jirginsu yad’aga izowa k’asar Dubai, wonnan tafiyar ma da y’ar lelensu sukayita, 

To su Madina asauka lfy, mudai muna nan sai andawo.

  ________________________

Tin ranarda aka yanke masa hukunci ya zubda makamansa na yaki, sbd yanzu baisan kuma akan me zai sakeyin yakin ba, abarda tafi komai k’ask’anci agaresa, tafi komai wulakanta agaresa, abarda yamayar mafi k’ask’anci agaresa yau itace taci galaba akansa, to kuma wone yakin zai sakeyi,

A yanzu yafahimci cewa d’an hakinda ka raina shike tsole maka ido, yau Wai mace ce tai galaba akansa, hmm tabbas ikon ubangiji da girma yake,
  ……………

Yau kusan wata d’aya da sati biyu kenan dagama shari’ah, shikuma watansa d’aya kenan da dawowa gida Nigeria, komai na rayuworsa ya canja, gaba d’aya bodyguards d’insa ya sallamesu hakama saif yamaidasa garinsu tareda bashi makudan kudi yace yaja jari dasu,

Shikowa yanzu koina baya zowa sbd gani yake kamar inya fita mutane kallonsa zasu dingayi su rika nunasa, hakan yasa yanzu kullum yana gida kusada iyayensa.

Tini momy tanema masa woni malama dake karantarwa a islamiyar su meehash, sbd taga yanzu gaba d’aya yasauya yai nadama, Saida tai kamar tanayi sannan fa yafara zowa yana d’aukan karatu, dan gani take harda jahilci yana damunsa, meehash da d’an uwanta bak’aramin farinciki sukaiba da shiriyar d’an uwonsu, yanzu kullum atare suke tafiya islamiyar idan sundawo gida kuma atare suke tilawa.

Dawood ne dai har yanxu baidaina abunda yakeba, DEEDART kowa kallonsa kawoi yake koyagansa tareda y’ammata komai baya cemasa saidaima yajuya yafice abunsa.

Gaba d’aya rayuwar DEEDART yanzu tasanja kamar ba Mr. AHMARD DEEDART ba, mai ji da kansa ba yana kuma takama da naira, tabbas ikon ubangiji da girma yake.

Dik kamfanoninsa yabayar sadaka, hakama dik wosu sabgogi nasa yanzu yadaina, yanxu ba abunda yake yi sai zama gida atareda mahaifiyar sa.

Saidaifa wota sabuwa inji y’an caca, har yanzu yakasa mantawa da Madina a rayuworsa, dikda kowa cin mutuncinda tamasa wonda wota zuciyar take d’aukansa as cinmutunci, wota zuciyar kuma take d’aukansa as gyaran rayuworsa ne tayi, dan gashi yanxu Allah yataimakesa asanadinta yashiryu daga mummunar tirbanda yake akai, 

Tinanin hakan yasa yad’auki abunda dayar zuciyar take masa tinani akai, nacewa taimakon rayuworsa ne tayi, to sai yace mezai hana shikuma yasakamata da abunda tamasa, to saidai yakasa sanin tawonne hanya ne zai sakankamata d’in.

Saidai zuciyarsa tana nan tanamsa woni aikinda shi kansa baisanshiba, kawoi yanajinsa ne a gangar jikinsa.

Izowa yanzu yakasa controlling na zuciyarsa akan tadaina sak’amsa abunda takeyi, amma yakasa, saidai har yanzu kuma bai gasgata abunda take sakamasa dinba, hakan yasa yake shareta batareda yabiyemata ba sbd Sam bamayasan tinawa da hakan,

A kullum cikin tinani yake gakuma mafarkai barkatai woenda sune suke kara ingiza zuciyarsa akan abunda take sakamasa, a dik sadda momy tagansa yai shuu shikad’ai to tinanin abunda zuciyarsa take sakamasa yake, wonda kuma yake gani a mafalkinsa,

Yawan tinane tinanen ne yasa dikya rame yai baki gashi yanzu baya fita koina bayasan yawon magana damakuma gashi miskili abun dika yaharde masa 
Rayuwa tasauyawa DEEDART fiye da yanda baiyi tinaniba, a yanzu idan yakalli halinda yake ciki yakan tsinci kansa acikin tarin mamaki dakuma gdy wa ubangiji.

Izowa yanzu yanayinda zuciyarsa take sakasa aciki yana nema yafi k’arfin tinaninsa koma nace yafi k’arfinsa dan yanzu shikansa yafara gasgata abunda take sakamasa d’in.

Yanzu yafisan zaman kad’aici kokad’an bayasan zama acikin mutane kuma bayasan hayaniya, dama kuma gashi miskili,

         …….Kamar kullum yauma zaune yake acikin makeken parlonsa shikad’ai, Qur’an ne a hanunsa hizifi biyar yana tilawa amma tinda yafara tinaninda yake a yanzu ya ajiye tilawa yai tagumi yai shuu yana tinani,

Bakomai yake tinaniba face MADINAH wocca tatsayamasa a zuciya, tinanin Madina yana nema yazautarda tinaninsa, yarasa meyasa zuciyarsa takasa mantawa da ita, take kuma k’ara kusanto masa ita a fuska da zuciya, tinda yake baitab’a tsintar kansa acikin yanayinda ya tsinci kansa aciki ba yanzu kuma akan mace, hakan yasa yake kwokwonta akan abun,

Tinaninta yake lkcnda yafara ganinta a shataletale, yana tinawa ne da yanda take magana acikin dakiya da rashin tsoro had’e da tsiwa, d’an murmushi yai wonda ya bayyanarda wishiryarsa sbd tino da Madina lkcnda tamatso dab dashi tana nunasa da yatsa tana fad’in,

      “Waye kai..? dahar zakazo ka tare mana hanya kahana kowa ficewa, waye Kai, bacin kuma hanyar ba tsohuwar taka bace kuma ba gadarta kayiba agun tsohonka”.

A dik lkcnda yake tinatinta yakan tsinci kansa acikin farinciki da nishadi musamman idan yana tino yanayinta da tsarinta, komai nata a tsare yake gashi ita jaruma ce abunda yafi jan hankalinsa kenan, gata kuma da tsarin sura mai kyau, amma shidai dik yanayinta yafi birgeshi,

D’an dago da kansa yai saiya tino da sadda yasaka aka d’akko masa ita a Cyprus, gaba d’aya yarinyar tana nema ta tafi da tinaninsa batareda yasaniba.

Bai ankaraba yaji ana knocking on the door, hakan ne yadawo dashi daga duniyar tinaninda yaje, d’aga kansa yai saiyaga 2:30pm har tayi, aikwa dasauri yamik’e tsaye yaje domin bud’e kofar, Saida yasaka password kamar yanda yasaba sannan kofar tabude,

Momyn sace yagani a tsaye tana sanye acikin atampa rer, black and white color d’inkin zani da riga, tai daurin d’ankwali ture kaga tsiya, idan kaganta Sam bazakace itace ta haifi DEEDART ba, sbd yanayin jikinta da fuskarta Sam ba alamar tsufa ko woni yanayi Mai kamada hakan.

Cikin murya mara sauti yace “momy na…” ahankali ta amsa sannan tace “DEEDART…wai meyasa bakajin maganane eh” shafa sumarsa yai yana d’an murmushi batareda yace komaiba, saita cigaba da fad’in,

   “Haba DEEDART, yakamata kamanta wonnan abun, kaciresa acikin ranka, komai yariga yawuce amantasa, nifa ko wlh wonnan yarinyar abunda tayi tamatukar birgeni kuma ta taimakeni takuma taimaki rayuworka, dan gashi yanzu yadawo mutumin kirki bakar tirbanda kake akai dakuma k’azamar hanyarda kake akai yanzu dik kasauka kuma kadaina kakuma rungumi  kaddara, sbd haka kamanta komai yafara tsara rayuworka dazakayi anan gaba”.

Shuru yai yana sauraron abunda mahaifiyar tasa ke fadamasa, sab’anin da dako lkcnta bashida bare har yatsaya suyi magana kamar haka,

Nannauyan numfashi yasauke sannan yace “Ohk…momy, insha Allah zanyi k’okari naga nacire komai daga raina” sai tai murmushi sannan tajuya tareda fad’in “dakyau my son, yanzu kafito muyi launch dadyn ku yadawo yana sama kamin lkcn tafiya islamiya yayi”.

“Ohk….” yafad’a sannan tafice shikoma yadawo ciki domin yai sallah sbd tinanin Madina dayake yasa baimasan lkcn yatafi har hakaba”.

Toilet yafice yai wonka tareda dauro alwola sannan yafito, bayan yafito yashirya acikin jallabiya bak’a da hula sannan yafeshe jikinsa da dad’add’an tiraruka masu sanyin k’amshi kamar yanda yasaba, bayan yagama sannan yaduki woyarsa yafita,

Story continues below

          Kai tsaye masjid d’in cikin unguwar tasu yaje domin yai sallah, bayan yagama sannan yadawo gida.

Koda yadawo sai baiga momy da dady a parlon samaba saisu Neehash ce kawoi yagani, cikin girmamawa suka gaidashi shima ya amsa cikin fara’a sannan ya tambayesu su momy, nan suka fadamasu suna sama har yanzu basu sakkoba, shima d’in saman yahaura shima domin yacimmasu acan d’in.

A bedroom d’in Abba yataddasu, Koda yashiga saiya tadda momy da dady a zaune kan gado suna kuka, dasauri yakarisa a ciki tareda fad’in,

  “Subhanallah…momy meke faruwa ne” yafad’a cikin damuwa, share kwolla tai momy sannan tace “DEEDART….muna cikin damuwa da tashin hankali” cikin damuwa DEEDART yace “meke faruwa ne momy?”.

   Sake share kwolla tai sannan tacigaba da fad’in “kayan mahaifinka da aka kwoce akan boda sune suka janyowa mahaifinka masifa da balai, a yanzu haka kayan suna hanun hukuma bayan angama bincikensu, y’ammatan dake cikin sauran motocin sunyi bayani akan cewa, ana d’aukansu ne ana kaisu k’asashen woje domin yin aikatau, bacin kuma idan ankaisu d’in badan aikatau ake kaisuba, siyardasu akeyi,

Hakan yasa hukumar tai kwakwaran bincike wonda allura ta tono galma, a yanzu dai andakatarda mahaifinka daga kan mukaminda yake akai, sannan dik wosu gidajen man fetir d’inda yakeda ankwace, ankuma kwace manyan motocinsa da’ake masa safarar miyagun kwayoyi daga waje dakuma woenda ake d’aukan y’ammatan ana fite dasu woje,

Komai nasa ankwace kuma andakatarda gidajen mansa dama dik wosu kadarorinsa, sannan anmakasa kotu”.

Kafafuwonsa nema suke sugaza d’aukansa  sbd woni juyawa da kansa kemasa, hakan yasa yai saurin dafe bango tareda dafe kan nasa yana ambaton “innalillahi wa’inna ilaihi rajiun” tsoro yakama momy sbd ganin halinda yashiga a yanzu,

Kwollah ne suka fata bin kuncensa masu tsananin zafi, cikin murya mara sauti yafara magana “hakika Allah yana arawa bawa lkc domin yabauta masa, saidai mafi yowan bayi sunayin amfani da wonnan lkc dakuma damar da ubangiji yabasu domin su sab’amasa, kamar mu kenan,

Duniya ta rud’emu, dad’in duniya yasa munmanta da lahirarmu dakuma ranar nadama wocca take zowa batareda neman iziniba, a yanzu ina matukar nadama da halinda natsinci kaina a baya, ina kumayin farinciki da halinda nake ciki a yanzu wonda bantab’a tinanin zan tsinci kaina aciki ba,

Kaima kuma dady yakamata fahimci cewa Allah yanasanka ne tinda yatoni b’arnarda kakeyi batareda sanin kowa ba, danhaka yakamata yanzu ka tuba dady tinkan lkc yakure maka” dasauri momy tace,

   “Hmm…. DEEDART kenan, ai lkc kam yariga daya kure masa, dan yanzu haka sunce yazamana cikin shiri sunanan tafe sutafi dashi domin atsaresa acan kamin afara shiga kotu”.

Shuruu DEEDART yai yakasa sake cewa komai, dady kowa gaba d’aya yarikice hankalinsa yatashi matuka, yarasa miye mafita a yanzu, dik inda yalalibo shuru bawota mafita,

Can dai wosu manyan abokanansa suka fara kiransa, sannanfa hankalinsa yafara kwontawa domin sunce ya kwontarda hankalinsa zasuyi iya kokarinsu domin ganin komai yatafi cikin sauki batareda antozartarda shiba, tinda dai Nigeria ce, kud’i kadai zasumasu dik abunda sukeso insha Allah.

Jin hakan yasa hankalinsa yak’ara kwonciya, nan yamike dasauri yashuri hularsa da phone d’insa yafita a hargitse.
  ________________________

Kamar kullum zaune yake acikin office d’insa yana duba wosu file’s, sanye yake acikin suit black color, irin dai shigarsu ta manyan likitoci, kan table d’in can daga gefe phone d’insa ce da wota y’ar ball wocca akai zanen duniya ajikinta tana kan woni d’an abu tana juyawa, gefe d’aya kuma cup din black coffee ne sai kuma tarin file files na mutane marasa lfy dayake dubawa,

Yana cikin rubuce rubucensa kawoi saiyaji anbude kofa dak’arfi bako knocking bare kuma neman izinin shigowa, dasauri yad’ago domin ganin mai shigowa,

Story continues below

Hmm….wazai gani banda bahijja fuskarta tamkar wocca akama sakon mutuwa, a murtuke kamar bata tab’a sanin miye dariya ba a duniyar nan, sanye take da riga da sket na leshi sunmatseta ssi dan rabin kirjinta ma a woje yake, hakama kanta d’an kwalinda ta d’aura sumarta kusan rabi dik a woje take, mayafin kowa dorasa kawoi akan shoulder wonda dashi gondama babu.

Dakaga yanayinta kasan bakaramar gogaggiya bace, sbd Sam babu kalar raini a tattare da’ita, tanada kyau matuka gakuma haduwa da gayu, wonnan wonkan ma datai yamatuk’ar yimata kyau, tahadu ainun, ba masoka agareta, dan zan iyacemaku koda Madina tafita to dakad’an ne, saidai da tsayi, hasken fata, dakuma kyau, dan Madina ba bayaba wojen kyau, daace zataje gasar kyau ta duniya to tabbas dazata lashe gasar tazamo ta d’aya, 
Ita kyanta nadaban ne, amma dai dikda haka bahijja tamata zarra a cikar halitta ta mata, duda itama tanada tata.

 “Uhm…nikam ma danaga bahijja Saida nace, namiji akwoi ruwan ido, wonda yakeda wonnan santaleliya mexaiyi da Karin aure, ga kyau ga gayu ga had’uwa gakuma cikar halitta irinta mata, dan komai tahada, gaba dakuma baya”…….


Yana ganinta dakuma yanayinda tashigo dashi yasa gabansa faduwa, kirjinsa yashiga dukan tara tara sbd yafi kowa sanin wacece bahijja, dasauri yamike tsaye tareda furta,

    “Bahijja….lfy kowa…? naganki acikin wonnan yanayin?” dak’arfi cikin kakkausar murya tace “aikafi kowa sanin abunda ke faruwa, mugu macuci, mayaudari, azzalimi, wlh Dr. kabani mamaki, wato ni inacan inafaman riritaka acikin kawayena, Kai zakine wojen kare kanka daga mata, bazaka tab’a kawoman wota acikin gidaba dasunan kishiya ba, ashe dik irin soyayyarda nake nunama baka ganinta, shine zakaje kaci amanata woi harka nemi mata harkai engage da sadaki harda saka rana harma ana shirin afara shagalin biki batareda nasaniba”.

Dasauri yazo danufin yarikota saita cemasa “dakata..! dakata Ismail, karka tab’a ni wlh, macuci kawoi” kofar yaje yarufe dasauri sannan yadawo yafara mata magana cikin tattausar murya,

     “Kingane my Love, dan Allah kitsaya namaki bayani mana, wlh bans…” dasauri tadakatardashi cikin kakkausar murya da fad’in “dakatah…!!! banasan jin komai daga bakinka, saidai inasan kasani, wlh katsokanowa kanka masifa da bala’inda baka ima, kadakkowa kanka ruwan dafa kanka da kanka, dan kasani, wlh…wlh…wlh sainaga bayan dik macenda ka kawo acikin gidana dasunan woi kishiya, Kai barama kagani ai nasan yarinyar kuma nasan gidan ubanta” tana gama fadar haka kawoi tajuya,

Dasauri yasha gabanta tareda riko hanun ta, cikin magiya yafara fad’in “haba bahijja, dan Allah kitsaya kisaurareni mana namaki bayani” cikin zazzaro ido tamkar mahaukaciya sabon kamu tace,

“Mezaka fadaman Ismail, bayan kagama cin amanata, wlh saina kashe wonnan yarinyar, sainaga bayanta wlh” tana fadar haka taturesa dak’arfi tabude kofa tafice abunta.

Idan hankalin Ismail yai dubu toya tashi, sbd yasan halin bahijja sarai, zata iya aikata komai akansa, dik macenda tace zata rabesa to tabbas zata fuskanci kalu bale mai tarin yowa, tino da hakan yasa dasauri yashuri key car d’insa da phone d’insa yafice dasauri.

    
       ……Yana fita yafara dialing number din Madina, tashiga kam amma hartagama ringing bata dagaba, saiya sake Kira again ma baadagaba, hakadai yacigaba da Kira harya isa gun motarsa yashiga yatada yafigeta dak’arfi yafice.
   _______________________

Da taimakon Allah, da taimakon abokanan dady suka samu aka kashe zancen kama dady izowa kotu, dakuma zancen yin shari’ah, bayanda suka zube mak’udan kud’i wa hukumarda case d’in yake a hanunta, saidai Sam sunki bada motocin dasuka kama sannan sunsaka anmaida y’ammatan gidajensu suka kuma sakasu Saida suka basu kud’i domin suyi sana’a tareda kuma sakasu a makaranta domin su sami ilimi,

Sannan sumasa kashedi akan karya kuskura yabari susake kamasa da irin wonnan lefin, idan suka sake kamasa tabbas saisun makasa kotu sannan dole zairasa muk’aminda yake akai yanzu.

       …..Dady dikya amince da sharud’ansu sannan yai alk’awarin bama zai cigaba da yin sana’ar ba bare har susake kamasa, insha Allah daga yanzu yadaina, dukiya dai iya dukiya yatarata kuma yanada ita wocca har jikokinsa bazasu iya cinyeta ba, bare kuma yayansa,

Daganan aka Kashe maganar, mutane sun kashe kunne suna jiran afara shari’ah domin jin irin hukuncinda kotu zata yankewa chief justice amma shuru kamar anshuka dusa, daga karshe ma sai lbrn yazama tarihi.

Hmm….! nikwa nace Najeriyar kenan, cin hanci da rashawa, dakuma rufe kaifin masu laifi musamman idan manyan k’asa ne, kokuma kin aiwotarda hukunci wa manyan k’asa, Allah dai yakyauta kawoi yadawo da masu bata akan hanya ameen.


       …..Zaune suke acikin k’ayataccen lambun dake cikin makeken gidansu, wonda yake d’auke da shuke shuke kala kala masu kayatarwa.

Acikin jikinsa take a zaune, kanta yana kan kirjinsa yayinda hanunta d’aya yake sakad’e da nasa yana murzasa, tufa takeci tana dariya tana bashi lbr wonda yakasa fahimtarsa amma dai yana binta kuma Yana mata murmushin nan nasa wonda yake k’ara bayyanarda kyansa a fili.


Dikansu sanye suke acikin fararen kaya wando da riga dika iri d’aya, d’ayan hanunsa yana kan lallausar sumarta yana shafata, akai akai kuma yana sumbatar goshinta.


D’agowa tai takallesa cikin murmushi tareda Kai masa tufar abaki alamar yaci batareda tamasa magana ba, ahankali kowa yakai bakinsa tareda janye tufarda tamiko masa danufin yakai bakinsa akan nata yai kissing, kawoi saiyaji yawun bacci sunfara zubowa akan d’ayan hanunsa daya dafe kuncensa yana sharan bacci.

Aikwa yanajin sanyin yawun dasauri yafarka daga nannauyan baccinda yake, ahankali yatashi a zaune yajingina bayansa da kan gadon sannan yajanyo pillow yarungume a kirjinsa yana murmushi, fara’a fal a fuskarsa.

A zuciyarsa yake fad’in “woi meke Shirin faruwa danine, zuciyata mekike nufi ne, kardai ace son yarinyar nan ne yakamani, Kai ina bahaka bane wlh….!” haka yaita zancen zuci shikad’ai bamai basa amsar tambayoyinsa, har  kusan 2:30am baisake komawa bacci ba, sbd gaba d’aya tinanin Madina ne yadawo masa sabo,

Dayaga abundai baya karewa saiya tashi yashiga bathroom yadauro alwola yafito, bayan yafito yasaka jallabiyarsa tareda shimfida sallaya yatada sallah.

    Raka’a shida yai sannan yasallame, nan kuma yad’akko Qur’an d’insa yafara tilawa..
Bahijja nafita Kai tsaye gidan wota k’awarta Mai irin halinta tanufa, tana zowa talabarta mata abunda ke faruwa, nan fa sadik’a tashiga ziga bahijja akan lallai tad’auki kwakwaran mataki akan Ismail, kada ta kuskura tabari a d’aura wonnan auren na Madina da Ismail.

Zigar da saddik’a tadinga mata yasa zuciyarta tak’ara harzuk’a tak’ara tafasa da tono da mugwayen dabarori woenda zata aiwotar domin tarwotsa wonnan auren.

Nan tad’auki saddik’a suka fice atare, inda taje tasiyi sabuwar wuk’a dan ji take gwondama takashe Madina data aurar mata miji, tana siya Kai tsaye suka kama hanyar k’auyen Raha.

         Dr. kowa yana fita kai tsaye yafice izowa garin Raha, tinda yahau hanya yacigaba da kiran layin Madina amma haryamata kusan 9miss call’s bata dagaba, hakan ne yak’ara tada hankalinsa ainun,

Yana cikin tafiya saiga Madina takirasa, aikwa dasauri hanunsa har yana rowa yadauki Kiran, baiko jira tace komaiba yafara magana “Madina kina inane naketa faman kiranki baki d’aga wa?” cikin tattausar murya mai cike da tsintsar so dakuma k’auna tafara magana,

    “Wlh my noor naje gidansu kaka ne, woyar kuma nabarta a gida nasaka charge sai yanzu nadawo” dasauri yacemata “Madina kikoma gidansu kaka dan Allah yanzi yanzinnan, kiyi sauri dan Allah, ga bahijja nan tafe kada tacutarman dake tamaki illa, bansan waya fad’amata zanyi aure ba, wlh bansaniba, dan Allah kitafi Madina….” 

Cikin mamaki tacemasa “Dr….dama baka sanarda matarka zaka k’ara aure ba…?” cikin daburcewa yace “Look Madina, ba lkcn yin wonnan zancen, please…! kid’auki jawahir kutafi, wlh bahijja batada imani, batada hankali zata iya cutardaku, please…..! Please….!!! Madina”.

Irin magiyarda yakemata yasa takatse Kiran sannan tafadawa su cool susi abunda ke faruwa,
Cikin masifa chuchu tace “kan uban can, ai wlh tayi kad’an tahanamu zama a gidannan woi sbd tsoronta, tazo d’in, dik abunda take takama dashi wlh nafitashi, dik abunda take taunawa nikuma zan iya had’iyemata shi, wlh dik masifarta y’ar k’arama ce” cool susi tace,

      …..”Yanzu shi Dr. har zaiyi aure batareda matarsa tasaniba, gsky bai kyautaba indan kyaitawa kam, sbd dik abunda bakaso amaka to kaimafa kada kayiwa woni, dik irin kishinda bahijja tai kada kuga laifinta wlh, dan nima zan iyayinsa” wota muguwar harara chuchu ta wurgamata kamin tace,

“To uwar iyayi, munji d’in, dan kawoi baifada’amata zaiyi aureba shine zatazo ta sauke fushin akan Madina, bacin kuma baitace tamata lefi ba, taje gun mijinta tasauke akansa man tinda dai shine yamata lefin, wlh dikta kurkura tazo garin nan dasunan masifa, wlh saita gane kurenta dansaita nemi ceto dakanta”.

Itadai Madina tai shuu tana saurarensu, tai tagumi tana nemawa kanta mafita.


      ……Suna a zaune saiga Abban Madina yashigo yafad’a mata ga Dr nan yazo, hijab dinta kawoi tasaka tafita izowa gunsa.

Ajingine tahangosa kan motarsa yai shuu alamar yana tinani, tab’e baki tai sannan tak’arisa gunsa ahankali,
Sallama tamasa kamar yanda tasaba, ahankali yad’ago tareda sauke nannauyan ajiyan zuciya sannan kuma ya amsa sallamar.

Tsayuwa tai agabansa tana fuskantar sa, ahankali kuma takallesa sannan tace “Isma’il….meyasa kak’i fadawa matarka zakayi aure ba? meyasa kak’i sanarda ita tinda wuri sai yanzu dataji a woje, kenan nima zaka iyaman haka kenan wota rana radda kahango wota a woje…?”.

Gyara tsayuworsa yai sannan yafara magana “haba Madina, ba wonnan maganar yadace muyiba a yanzu, mafita akan bahijja itace abunda yadace kiman magana ba wonnan ba, tabbas nasan nayi kuskure danaki sanarda ita, amma kuma nayi hakan ne domin gujewa fitina domin gujewa masifarta”
Kallonsa take harya gama magana sannan tace “To yanzu miye mafit…” batako k’arisa rufe bakintaba saiga motar bahijja ta’iso wojen,

Story continues below

Dr. naganinta hankalinsa yak’ara tashi, cikin tashin hankali yace “Madina kinga shige gida ga bahijja nan ta’iso kada ta cutar man dake” juyawa tai domin ganin wonnan bahijjar d’in, saikwa tahangota tafito daga mota hanunta rike da wuk’a sabuwa gal tana kyalli,

Waro ido tai tareda ja da baya cikin tsintsar tashin hankali, “wuk’a…” tafad’a batareda tamasan tafad’a dinba wonda hakan yasa shima duba bahijja d’in, waro ido yai cikin tashin hankali,

Tana rufe motar tafito saddik’a ma tafito, tana hangosu a tsaye suna kallonta kawoi itama tayo kansu dasauri hadda d’an gudunta tamkar zararriya, fuskarta babu alamar fara’a a tattare da’ita saima tsintsar mugunta dakake hangowa k’arara a fuskar tata,

Kai tsaye ta tinkarosu hanunta rike da wuk’ar tana huci tamkar kumurcin maciji, dasauri Dr yamaido da Madina bayansa yana fad’in “Madina shige gida, shige gida karta illataki” ganin tatinkarosu gadan gadan yasa dasauri Madina tafice tashige gida, bahijja naganin hakan saita bita dagudu nan shima Dr yabi bayansu yanaso yadamko bahijjar amma Inna dagudun tsiya takebin Madina,

Koda Madina taisa cikin gida cool susi nawoje tareda jawahir da Abba dawosu yara maza guda hud’u kannen Madina yayan kanen Abban ta, suna ganin halinda Madina tashigo aciki nantake hankalinsu yatashi, cool susi tace “Madina lfy…? meke faruwa ne…?” cikin shesheka tafara fad’in,

     “Bahijja….bahijja ce tazo da wuk’a woi saita kashen….” batako rufe bakintaba saiga bahijjar tashigo dagudu Dr nabayanta sadik’a ma tanabin bayansu, dasauri cikin masifa cool susi tace “wlh karki kuskura ki k’ariso nan, idan kika kariso wlh sai ankwasheki matacciya” cikin zazzaro ido cike da masifa da balai tace,

   “Wlh yau saina kashe wonnan bak’ar magen, saina kasheta inyaso idan tajecan lahira ta auri mazan dakecan, amma ba mijina ba” tana cikin magana bata ankaraba Ismail yafizge wuk’ar daga hanunta sannan yawonka mata kyakkyawan marika har biyu, dasauri tadafe gunda yamareta har kwollah tazubo, ahankali kuma tadago takallesa tareda fad’in “Isma’il…ni zaka mara?” cikin b’acin rai yacemata,

“Ke woce irin mahaukaciya ce mara tinani, kawoi dan zanyi aure shine kike nema ki tozartani a idon duniya, agaban sirikaina, haba…haba bahijja” cikin tab’e baki tace “hmm…wlh indai akanka ne zan iya aikata komai”.

Sadik’a ce tazo tariko hanun bahijja cikin masifa takalli Dr tace “lallai kowa Ismail, wlh kabani mamaki, yau bahijja ce ta cancanci kadaga hanu kamareta akan wota banza karya, wocca batako shigo gidankaba, to wlh bara kaji, wonnan masifar yanzu aka fara, matukar baka janye batun auren nanba, to saikaga abunda baka tab’a tinaniba” bahijja tai murmushin mugunta sannan tace “barshi…barshi kawoi sadik’a, dani yake zancen”.

Chuchu tafito daga bedroom d’in madinah jin hayaniya a tsakar gidan, kwatsam saitaga Dr da wosu mata guda biyu, ganinsu ya tabbatar mata dasu bahijja ne, jin abunda sadik’a kefad’a yasa ta tabbatarda ba alkhairi bane yakawosu,

Dagacan nesa tafara takowa tana fad’in “kuyi gaugawor fita daga cikin gidannan, if not…kuma wlh kusha mamaki, shashashun banza mara hankali da tarbiya, sai yanzu na tabbatarda gskyr abunda mukeji a woje ashe gaskiya ne, cewa ke bahijja cikekkiyar mahaukaciya ce” tak’arisa fad’a tana isowa gunsu,

Cikin masifa bahijjar tai kanta danufin kaimata duka tana fad’in “bara kuwa na nunamaki ni cikekkiyar mahaukaciya ce yanzu” nanfa tacakumo rigar chuchu, ganin haka yasa cool susi itama tai kan bahijja nanfa itama sadik’a tai kan cool susi,

Nanfa komai yakacame, hankalin Madina gaba d’aya yagama tashi sai zubda kwollah take tana janyo cool susi tana fad’in “kukakyalesu mana chuchu, ku kyalesu, meyasa zaku biyemasu wojen habbaka barna da tasoda fitina”.

Dakyar da sud’an goshi Dr dasu Abba tareda taimakon makotansu Madina aka raba wonnan  fad’an, dakyar Isma’il yaja bahijja yafita woje da’ita, sai fad’ar take “wlh saina nunamaku ruwa ba sa’an kwando bane, sainayi maganinku wlh, mijina yamaki zarra, mallakinane nikad’ai dan ni kadai aka haliccesa, k’arya kike kice zakishigoman gida wlh” haka dai Dr yasamu yafice da’ita itama sadik’a su baba mairoje suka samu suka fita da’ita.

Story continues below

Suna fita bahijja tafizge  daga rikonda Dr yamata tareda galla masa harara sannan taje tabude motarta tashiga sadik’a ma tashiga nan tafizgi motar dak’arfi suka fice.

Bayan sun fice sannan yadawo cikin gida, gun Madina yaje danufin yafara bata hak’uri saitai saurin dakatarda shi da fad’in “dakata…! dakata Ismail, dama haka halayyar matarka take shine baka sanardani ba, meyasa kak’i fadaman halayyarta tin farko, domin nashirya zama da’ita, tabbas inasanka kuma zan iya zama dakai a kowanne hali, halayyar matarka bazasu tab’a razanardani ba sbd bata gabana, amma yakamata kasanardani tin farko,

Anyway…yanzin ma baka makaraba, tinda tazo dakanta kuma tanunaman halin nata, kaga sainamata shiri na musamman domin tarbanta a dik yanayinda ta karbeni, kasa a ranka dik wonnan hargowar tata bazata tab’a razanardani ba, bakuma zata hanani aurenka ba tinda kanasona ina sonka, bakuma akanta zanyi zaman aureba”.

Murmushin farinciki Dr yai sbd a zatonsa zata d’auki woni hukunci ne sab’anin wonda tayanke a yanzu, saiya kalli Abba yace “dan Allah Abba kuyi hkr da abunda yafaru” Abba kam ransa yabaci da abunda bahijja tai, cikin b’acin rai yace,
“Nidai wlh da anfasa wonnan auren, sbd wonnan yarinyar babu alamar imani a tattare da zuciyarta, kartaje ta hallakaman yarinya kokuma tamata illa, a yanzu itakad’ai ce nake gani naji farinciki, itakad’ai ce jinina wocca nake gani naji tarin farinciki, bakincikin da yake tasoman wonda aka cusaman tsawon shekaru yakau, sbd haka kawoi a fasa wonnan auren”.

      ….Abunda Abba yafad’a yamatuk’ar ratsa Madina, hakama Dr danhaka yace “kayi hkr abba, kakuma kwontarda hankalinki, namaka alk’awari insha Allah ba abunda zai faru sai alkhairi acikin auren mu, ba abunda bahijja taisa tayiwa Madina matukar ina numfashi” Abba kam Sam baigamsu da maganarsa ba, dandai yanace ne amma shikam idan ta tasane kawoi afasa auren, bayanda yaiya sbd ganin Dr yanace danhaka yace,

    “Shikenan, amma dan Allah Ismail kakulaman Madina, kariketa amana, kada kabari wani ko wata kokuma Kai yacutarda ita, wlh bazan tab’a yafewa dik wonda yacutarman da y’a ba” numfashi Dr yasauke kamin yace “insha Allah abba, namak wonnan alk’awarin” sai Abba yajuya yakoma woje kan dakali gunda suke zama tareda tsofaffi abokanansa.

Madina kowa rakiya tayiwa Dr a bakin mota sannan sukai sallama yafice itakoma tadawo ciki.
  ________________________

Kwonce yake akan bed d’in momyn sa yadafe bayan kansa da d’ayan hanunsa fuskarsa na kallon sama yakafe idanuwonsa gu d’aya taredayin shuruu alamar yafad’a duniyar tinani.

Momy kowa salla take akai akai kuma tana kallon yanayinda yake aciki,

Hartai sallar farillah raka’ah uku takuma yi nafila dik hankalinsa na gu d’aya, bayan tagama taja charbi dadik y’an abubuwonda take bayan tagama sallah sannan tazauna kan bed d’in tana fuskantar sa, ahankali takira sunansa,

    “DEEDART…..” amma bai d’agoba bare ya amsa, hakan ya tabbatar mata da yayi nisa ssi acikin duniyar tinani, sake Kiran sunan nasa tai akaro na biyu saiya dawo hayyacinsa dak’arfi yawaigo saiyaganta zaune kusa dashi tana kallonsa,

Shafa fuskarsa yai sannan yatashi a zaune tareda fad’in “momy, harkin gama sallar ne” tace eh sannan tacigaba da fad’in “DEEDART, bazance har yanzu baka cire woccan damuwor aranka ba, amma dai natabbatar a yanzu baitace take damunka ba, DEEDART kaduba yanda dik ka lallace, ka rame, Kai baki kak’ara tsayi sbd damuworda kake ciki a yanzu, haba DEEDART be a man mana eh, Ohk…now tell me what’s wrong with u eh…tell me now now….inajinka” sosar kansa yashigayi yana d’an murmushi sannan yace “bakomai fa momy, kawoi canjin rayuwane dana samu, wonda kuma bantab’a tsintar kaina acikinsa ba, shine kawoi”.

K’uresa tai da ido sbd tasan abunda yafad’a ba gsky bane, yadai fad’a ne domin yakare kansa, amma tasan na gsky bane dan DEEDART akwoi zurfin ciki gashi shu’umin mutum ne, sai kuma tace masa “are u Sure…bawota damuwa” cikin murmushi yace “yes Mom, am hundred percent sure”.

Story continues below

Saita sauke numfashi sannan tace “Ohk…shikenan, kaje kafara shiri gobe zamu tafi gwondu ( kebbi state), zaayi bikin Abbas” daalamar tambaya a fuskarsa yace “waye kuma abbas momy?” juyowa tai takallesa sannan tai d’an murmushi tace,

     …..”DEEDART kenan, bazanyi mamakiba dankace bakasan abbas ba, sbd abaya nikaina danake mahaifiyar ka bakada lkcna bare kuma woni dangina Koda yake shima Abbas d’in dik halayyar ku iri d’aya ce, shima sa’ankane 35yrs amma sai yanzu zaiyi auren fari shima kuma Saida muka sakasa agaba muka zabo masa matar dakanmu acikin yay’an y’an uwa sannan zaiyi auren, 
Kaima kakiyaye kafito da mata kokuma amaka yanda akamasa.

 Abbas d’an d’an’uwana ne, yayana wonda nake bi, yayansa shida mata hud’u maza biyu, Abbas kuma shine first born, gobene zaafara gudanarda bikin sbd haka inaso mutafi gobe gaba d’aya tinda dama su Neehash sunyi hutu”.

Maganar momyn sa tashigesa ssi hakan yasa yafarajin yanaso yasan danginsa dakyau, “Ohk momy, bara naje nafara shiri to kamin dady yadawo nafito” to tacemasa sannan yafice.

A side d’insa dayaje, bawoni abunda yai sbd yakasa tsara kayan nasa acikin akwati, sbd yariga daya saba a da komai yimasa akeyi wonka da cin abinci ne kawoi yakema kansa, ganin yakasa aikata komai kawoi saiya dawo palor yakunna TV yafara kallon News, kallon News din yake amma gaba d’aya hankalinsa baya kan TV d’in,

Gaba d’aya hankalinsa nacan ya lula a duniyar tinani, wonda kuma bakomai yake tinanin ba face Madina, mafi yowan abunda yake tinawa akanta shine rigimarda sukai a shataletale, idan yana tina hakan yakan tsinci kansa acikin nishadi da farinciki, saiyaita murmushi shikad’ai musamman idan yana tino yanda take masifa tana magana, d’an bakinnan nata yana juyawa kamar yakamosa yatsotse.


Hmm….shifa DEEDART har yanzu yakasa sanin dalilinda yasa tinanin Madina yazamemasa abun yi a Koda yaushe, kuma abunda yake sakasa nishadi da farinciki, to kodon baitab’a tsintar kansa acikin soyayya bane shys yakasa fassara hakan da so, maana sonta ne yakamu dashi, oho dai gamu gani reader’s.

Yajima ssi acikin wonnan yanayin har Saida momy ta aiko Deen yakirasa sannan yatashi suka fice izuwa cikin gida.
  

            …… Around 2pm dot jirginsu yasauka k’asar kebbi state a katafaren filin jirgin nan mai suna Ahmadu bello international airport dake cikin birnin kebbi L/gvmnt, jirgin nasu na sauka driver’s d’insu sukazo suka d’auke su izuwa garin gwondu L/gvmnt.

Saikusan 2:50pm sannan suka isa, Kai tsaye family house d’insu momy suka fice, gidan babban gidane wonda yake d’auke da uwa uba yaya dakuma jikoku hadda kamakunne,

Suna isowa Kai tsaye aka budemasu gate driver’s d’in suka shiga da motocin, bayan sunyi parking sannan suka fito akafara fito da kayansu aka shiga dasu ciki kamin su sushigo, atare da momy sudika suka shiga ciki, momy da DEEDART suna a gaba su Deen kuma suna bin bayansu kasancewor baatare da dady sukazo ba, su DEEDART dik ainahin shigar hausa sukai, shadda galila da hula dakuma takalma, wonda yak’ara bayyanarda kyansa a fili dan bakadan ba shigar kemasa kyau.

Kai tsaye babban palorn hajiya mahaifiyar momy suka fice wonda yake acike da mutanen gidan ana jiran isowarsu, suna isa kowa aka taryesu cikin farinciki su Neehash aka rungume fadila kanwar abbas, 

DEEDART kam tsaye yai yana kallonsu danshi bayan hajiya da baffansa  sai kadan daga cikin mutanen gidan bawonda yasani, haka suma abun mamaki yazamemasu dan rabonsu dasuga DEEDART yazo gidan tin yana farkon fara business d’insa,

Momy talura dayanda yanayinsa yacanja sbd ganin irin kallonda mutanen gidan kemasa, amma bata damuba sbd tasan shine yajawa kansa.

K’arisa wa sukai ciki suka zauna, ahankali yafara gaishe dasu hajiyar, cikin mamaki suke amsa masa, hajiya dai bata boye mamakinta ba Saida tacemasa “Hmm…tbd jam amadu, yau kaine a gidannan, lallai kowa yau zaamana ruwa hadda k’ank’ara” d’an murmushi yai tareda shafa kansa,

Ummi mahaifiyar su Abbas tace “yo banda abunki hjy, namiji ai bashida isasshen lkcn kansama bare haryasami lkcn yawo, musamman yanda yanayin aikin d’an nawa yake” tab’e baki hajiya tai tace “hmm…bawoni, kedai kare dan naki kawoi kike” sai sukai dariya,

Daganan aka shiga gaggaisawa ana tambayar bayan rabuwa, suna anan sai Abbas yazo yaja DEEDART suka fita, cikin garin na gwondu suka shiga inda suka zazzaga gari DEEDART yaga garin dakyau, sai dare suka dawo bayan sunje woni restaurant sunci abinci,


Da dare ma sunjima ssi a palorn hajiya ana fira hadda baffansa dasu momy dasu neehash dika, sai kusan 10pm sannan akai sallama kowa yafice izowa bacci.

  Washe gari itace ranarda zaafara gudanarda shagalin biki, itace ranarda zaayi kamu, tin 9am DEEDART yaja abbas suka fita, hmm abun mamaki yau DEEDART shike driving dakansa, abunda yakwashe shekaru masu tarin yowa baiyiba, Kai tsaye hanyar garin kangiwa suka nufa wonda yake acikin birnin kebbi L/gvmnt wonda kuma yake garinsu Saif, babban yaron DEEDART kuma amininsa..


Tafiyar kusan 35mnts sukai kamin su iso garin kangiwa, bayan sun iso kuma suka d’auki hanyar gidansu Saif, dakyar da tambaya yagane gidan bcoz komai yasauya yanxu, ansamu cigaba ssi bakamar da ba, wosu gidajen na ginin k’asa dik an sauyadu, gidansu Saif ma ancanja masa gini daga na k’asa ixowa na sement, bayan sun iso yai parking sannan suka fito,

      ….Suna fitowa Kai tsaye suka shiga cikin gidansu Saif cikin sallama, mahaifiyar sa suka fara cin karo da’ita zata shiga palorn ta, tanajin sallama saita dakata tareda amsa sallamar cikin tsintsar mamaki, bawoi zowan DEEDART agidan bane yafi bata mamaki ba, aa kayanda ke jikinsa ne dakuma yanayinda tagansa aciki wonda baitab’a zowa da irinsaba gidan,

Ahankali suka k’ariso gunta sannan yadurk’usa cikin fara’a da sakin fuska yace “Umma barka da kwana…yah gida..yah aiki?” cike da mamakin yau DEEDART ne yadurk’usa yana gaidata tace “hmm…! barka dai AHMARD, gida Alhmdllh, yh can d’in yakuma iyayenka da k’annenka” yace “dik suna lfy suncema agaidaku” saitace “to Masha Allah, kushigo ciki mana”.

Nan suka shiga cikin parlon takawo masu ruwa da fura da kindirmo kasancewor su fulanine ssi, aikwa DEEDART ansamu abunda ake so nanfa yazage yasha abarsa Saida ya koshi, hakama Abbas yasha amma ba ssi ba, sbd shi fura bata acikin tsarinsa,

Bayan sungama sannan DEEDART yace mata “am… Umma, nace Saif fa, ko yana nan” cikin fara’a tacemasa “Ehh…yana can sabuwar plaza d’insa daya buda a bakin titi, bara nasaka akaiku” yace to sannan tafita,

Batafi 15mnts dafitaba saigata tadawo tareda woni yaro wonda bazaifi 14yrs ba, saitace “AHMARD…gashinan, shizai kaiku gun Saif” cikin fara’a DEEDART suka mike a tsaye sannan sukamata gdy sannan sukai sallama suka fice,
Suna fita kai tsaye suka fice izowa gun Saif, yaron yadinga nunamasu hanya har suka iso a bakin plaza d’in sannan yai parking suka fito, yaron ne yaje yafadawa Saif yayi baki, bayan yafad’a masa sannan yadawo DEEDART yabashi y’an kud’i ya karb’a yai gdy sannan yafice.

Saif nafitowa yahango su a jingine kan mota, dasauri yaje cikin fara’a da tsintsar farinciki yana murmushi, DEEDART ma yana ganinsa yafara fara’a nantake kewar aminin nasa tadawo masa sabuwa, dasauri Saif yazo yarungume DEEDART cikin tsintsar fara’a haryana zubda kwollan farinciki.

Nandai yajasa suka shiga cikin mota sannan suka shiga gaisawa, Saif yace “Sir. bakada lfy ne hala, naga kayi wota iriyar muguwar rama kamar wonda yai jinya” murmushi yai sannan yace “lafiyana k’alau Saif, saidai wlh inacikin wani hali wonda nakasa fahimtarsa, nakasa gane abunda ke shirin faruwa dani, nasani Saif kafi kowa sanin waye ni, kuma kafi kowa sanin halayyata, Saif kasani tinda nake bantab’a saka wota y’a mace a rainaba, sannan macema Sam bata a gabana, bata acikin abunda zansaka agabana harya dameni, amma wonnan karon tasauya zani,

Saif nakasa mantawa da wonnan yarinyar a raina, nakasa cireta a raina, a kullum itace take tayani fira, itace abunda nake tinawa najini acikin farinciki, sannan a zuciyata inajin woni abu akanta wonda nakasa fahimtar menene, nakasa gane meke Shirin faruwa dani” yana kawo nan saiyai shuru tareda sauke numfashi,

    “Hmm….!, shine nazo gunka Saif domin kasamaman mafita sbd Kai kanka kasan banida woni aboki ko amini wonda nake fadawa damuwata sai Kai, Kaine babban yarona kuma aminina” dariya Abbas ya kyalkyale daita saif kuma yai d’an murmushi Abbas yace,

“Malama, kawoi kace kashigo hanu kawoi, amma kawoni tsaya kana mana woni kwana kwana” hararansa yai sannan yace “dalla malama kama mutane shuru dan Allah, nashigo hanu kuma kamarya?”.

Saif yadafa shoulder d’insa sannan yace “Sir. inagafa abunda abbas yafad’a yayi gsky, tabbas ka kamu da son wonnan yarinyar ne batareda kasaniba” dasauri yawaro idonsa cikin tsintsar mamaki tareda fad’in “what….!!!, me kake fad’a haka Saif, are you mad, yarinyar da tatozartani a gaban idon duniya, tanemi taga bayan rayuwata, itace zakace woi zuciyata takamu da sonta, haba…haba Saif think before you talk mana” murmushi saif yai Abbas kowa har yanzu dariya yake kyalkyalawa.


     Saif yacigaba da fad’in “Sir. dik woennan alamomin daka fad’a kanaji gameda wonnan yarinyar sune alamomin so woenda mace ko namiji keji idan takamu da son woni ko yamaku da son wota, yawon tinani musamman irin na soyayya yafi komai saka mutum yadinga ramewa tamkar wonda yai jinya, wonda kuma ga alamun hakan nan sun bayyana a tattare dakai, sannan yawon tinaninta dakake ya nuna cewa tabbas ka kamu da sonta ne, Sir kada ka k’aryata hakan, kamar yanda kafada nafi kowa sanin waye Kai, sanin hakan yasa nafahimci tabbas ka kamu da son wonnan yarinyar tabbas”.

Shuruu DEEDART yai nawosu y’an dak’iku, Saif yadafasa tareda fad’in “kawoi muje ka bayyana mata soyayyarka agareta, kaga saikuyi aurenku kucigaba da tarbiyyar yarku dakuma sauran yay’an da zaku haifa, wlh Sir kunyi matukar dacewa da juna, had’in ku zaiyi kyau kuma tabbas mutane zasuyi farinciki da wonnan had’in naku” yakarisa cikin fara’a,

Abbas yace “perfect match kenan, dikda dai bansan wonnan pretty d’in ba, ammadai natabbata itama kyakkyawace kamar broz dina” shidai har yanzu yakasa furta komai, al’ajabi yacikasa, a zuciyarsa kowa fad’ar yake “Kai…Kai…Kai, ina haba zuciyata idan kikaman haka kowa bakimin adalci ba, baki kyautaman ba wlh, kirasa wocca zaki kamu da sonta sai wonnan yarinyar wocca tanemi taga bayan rayuwata, wocca ta tozartani a idon duniya, haba…haba” yana cikin tinani Abbas yadafashi tareda fad’in,

    “Yadai broz…” numfashi yasauke nannauya sannan yace “ina tinanine dakuma mamakin kasancewor wonnan al’amarin” Abbas yace “uhm…ai al’amarin ubangiji ba abun mamaki bane, Allah yana aikata abunda yaga dama kuma a lkcnda yaga dama, danhaka wonnan ba abun mamaki bane, sannan kuma idan zai aikata baya neman shawarar kowa” sai yai murmushi wonda har ya bayyanarda fararan hakoransa.

Saif yace “Sir. kawoi kabari muje kabayyana mata soyayyarka, sbd abari ya huce shike kawo rabon woni, kada Kai sanya kaje lkc yakure maka” Abbas yace “lallai kam, gwonda kacire girmankai dadik woni abunda kakeji sbd karkaje kuma daga baya kadawo dana sani, inafatar kagane abunda muke nufi”.

Nannauyan numfashi yasauke “hmm…..!” tareda gyara zamansa sannan yace “shikenan, zanyi shawara akai” sukai murmushi kawoi.

Sunjima ssi anan suna fira kamin daga bisani sukama Saif sallama suka fice.
  
      …..Koda suka isa gida anata shirye shiryen tafiyar kamu danhaka suka fice izowa gun abokanan ango, dik yanda Abbas DEEDART yashirya sutafi kamun atare baiyiwuba, dan DEEDART cemasa yai kansa ke ciwo yana bukatar yahuta, suje kawoi gobe yaje dinner, badan yasoba dole yabarsa suka tafi,

Bayan sunfice yarage saura shikad’ai acikin d’akin, nan yatsunduma acikin kogin tinanin mafita akan halinda zuciyarsa take ciki, yajima ssi yana tinani can daga karshe yasamo mafita.

Da dare bayan andawo daga kamu d’in yasami momy itakadai a d’akin hajiyarta yamata magana cikin fahimta,
“am….momy, dama inaso nafad’a maki wota magana” saita gyara zamanta kowa tareda fad’in “inajinka” saiya cigaba da fad’in “inasone naje naga yarinyar nan sbd inasone tasaba dani ahankali domin zan karb’otane daga hanun mahaifiyar ta namaidata gida” murmushi momy tai sannan tace “DEEDART kenan, bazan hanaka kaga yarka ba, ammadai kuma bazan baka goyon bayan karbe yarinyar nan ba karabata da mahaifiyarta sbd y’a mace ta uwa mace ce, sbd haka kabarta a hanunta inyaso dik abunda kasamu ka’iya kaje kakaimata, sannan kad’auki nauyin karatinta, ka karb’i nauyin daga hanun mahaifiyar tata kakuma dinga kula da’ita iya k’arfinka”.

Hakika maganar mahaifiyar sa gsky ce shikansa yasan hakan, amma yanaso yayi amfani da wonnan damarce ta karb’an yarinyar domin cimma wota manufa tasa agun mahaifiyar tata, d’agowa yai yace “ok momy, zanyi yanda kikace insha Allah” saitace,

    “DEEDART, bawoifa nahanaka d’aukan yarka bane, aa shawarace nabaka” murmushi kawoi yai batareda yasake cewa komaiba yatashi yamata sallama yafice abunsa, batasake ce dashi komaiba tacigaba ca sabgarta dan idan dasabo tariga data saba da halin d’an nata.


         …..Washe gari around 2pm bayan sundawo daga masjid yasake wonka yacanja kaya izowa wota tsadajjiyar shadda gizna mai tsadar gaske dakuma kyau, White color mai kyan gaske, saikuma hula da takalma suma masu kyau, 

Nantake ainahin kyansa ya bayyana k’arara, tsintsar kyansa ya bayyana a fili sai haske yake yana kyalli tamkar hasken farin wata a sararin samaniya, bayan yagama shirinsa saiya feshe jikinsa da dad’add’an tirarukan sa masu sanyin k’amshi, bayan yagama sannan yatsaya a mirror yana kallon kansa, d’an murmushi yai sannan yashuri key car din abbas yafice..

Yana fita yaje parking lot yad’auki motar yafice, kai tsaye wota Central market yafice inda yafitarda kud’i yai tarin siyayya wa y’ar sa gudan jininsa, dik woni abu na bukatar yara Saida yasiyeshi, kamar kayan sakawa sitiru, abinci mak’u lashe, kayan wasa, takalma da dai sauran su.

Yakashi kud’i ssi dan idan kaga kayan kaikace shagone ma yad’akko gaba d’aya, sbd tarin yawonsu gakuma kyau da tsada, hatta Teddy’s woenda yasiya sunfi a k’irga,

Bayan yagama siya aka sakamasa a mota yabiya kud’in sannan yashiga motarsa yafice,
Daganan Kai tsaye k’auyen Raha yadosa.

Tafiyar 30mnts yai kamin ya’isa garin na Raha, tin a hanyar shiga garin yafara cika da mamaki, sbd ganin yanda komai yacanja, gine gine nazamani gakuma shaguna akan titi manya masu girman gaske, ciki hadda k’atuwar plaza mai kyan gaske wocca kuma tak’ayatarda shi ainun.

Can daga gefen titin kuma wota k’atuwar hospital ce mai suna “munawara general hospital” ganin tambarin sunan ne yasa yatino da abunda yafaru a baya, nantake abun yadawomasa a zuciya.

Cigaba yai datafiya ahankali yana tafiya acikin k’auyen wonda ya canjamasa gaba d’aya, ta tafiya yake amma yakasa gane ma inane yakebi kasancewor damacan baisan gidansu Madina ba,
Can yahango wota katafariyar makarantan boko wocce take had’e da islamiyya mai suna jab’bo international School da islamiya mai suna jab’bo malja’ussunah Raha dakuma masjid a gefensu, ko bai fad’a ba a baki tabbas a fuska school d’in guda biyu sun birgeshi dan sai kallonsu yake, ya kalli nan ya kalli can, yara y’an makarantar sunfito breakfast sai wasa suke wosunsu kuma sunashan ruwa agun pampo wosunsu kuma tsaye suke kawoi suna magana.

Can yamatsa kusa da wosu tsofaffi dake zaune kan dakali yai parking sannan yafito, bayan yafito sannan yaje gunsu yamasu sallama suka amsa cikin sakin fuska sannan yacemasu “dan Allah ina tambayar gidan mallam ja’ey ne?” nan take suka kwatantamasa, amma saidai baigane kwatancen nasuba danhaka suka hadasa da woni yaro domin ya kaisa har gidan.

Nan yamasu gdy sannan yamasu alkhairin kud’i sannan yamasu sallama yafice, acikin y’an sakonni suka isa gidan, abun mamaki, katafaren gida ne DEEDART yaga yaron yatsayardashi alamar nanne gidan, wonda gidan yabashi mamaki matuka ace akwoi irinsa a wonnan k’auyen, bayan sun iso kuma yasaka yaron yaje yamasa sallama da Madina,

Yana zaune yaron yadawo yace ance woi waye Madina batanan, baifadi sunansaba saiyace da yaron “je kace zowa yaushe zata dawo?” nan yaron yasake komawa Jim kadan yadawo yacemasa “ance zatakai azahar”.

D’an jimm yai nawosu y’an seconni can sannan yad’ago tareda saka hanunsa acikin aljihu yaciro kud’i yabama yaron sannan yamasa sallama da gdy shima yaron yamasa gdy sannan yafice.

Gyara parking d’in motarsa yai sannan yakwontarda sit yai kwonciyarsa tareda d’akko woyarsa yafara chart.

         …….Madina kowa sunacan wojen lalle da saloon acan cikin garin bunza, ita dakuma su chuchu da shauran kawayensu dakuma jawahir,

Sunjima ssi acan dan saida akai sallar la’asar sannan aka gama masu itadai Madina komai angama mata kasancewor gobe ne za’a fara gudanarda shagalin, gobe zaai kamu, hmm reader’s naso kuga yanda tauraruwor tamu tahaska, tasha jan lalle da bak’i gakuma gyaran Kai daaka mata, gakuma kalolin gyaran jiki daakamata na dilka da kurkur da halawa, gaba d’aya sai kyalli take tana woni shining tamkar tauraruwo zarah idan tafito tareda wota suna haske da kyalli.

Gakuma woni fitinannen k’amshi fatake na had’addun tirarukan tsuguno dana jiki irin na mutan kebbi da maiduguri woenda ake tsumata dasu, gakuma wota y’ar kiba datai sbd kularda ake bata acikin satin bikin dayashigo,

Gaba d’aya tafara canzawa sai kyalli take, dik inda ta gifta saitabar k’amshin dad’add’an tirarukan jiki.

Saida aka gamawa kowa kusan 4:30pm sannan dank’ara dank’aran motocin abokanan ango Dr ismail sukazo suka d’auke su izuwa gida.

Story continues below

DEEDART kowa dayaji shuru saiyai parking na motarsa gaba d’aya sannan yafitarda woni prayer mart babba yashimfida yai kwonciyarsa, idan akai sallah saiya tashi yaje masjid yayi sannan yasake dawowa, hakama woyarsa daga karshe kasheta yai, yau dai ya kud’iri aniyar fara tinkarar Madina domin isar mata da manufarsa.

Daya gaji da zama a k’asa saiya koma cikin motarsa, cikin ikon Allah kowa saigasu sun iso yana zaune acikin motarsa, cikin fara’a da dariya suka fiffito jawahir na hanun chuchu suka fito tana rike da hanunta, itama tasha lallen, amma ita ja akamata, saikuma woni kitso mai shegen kyau da’aka mata.

Dik sauran kawayen sunshiga gida amma ciki kowa hadda chuchu da cool susi amma baiga Madina tafito ba, hakan yasa yafarajin b’acin rai a zuciyarsa nantake yanayin fuskarsa ya canja daga fara’a zowa damuwa.

Can kwatsam saigata tafito daga gaban motarda ke gaban sauran motocin wocca glasses dinta suke black, fuskarta d’auke da dariya da fara’a, fararan hakoranta sai kyalli suke, tana dariya dimples d’in ta sai lotsawa suke gwanin birgewa,

Sanye take acikin hijab har k’asa kasancewor tinda akafara mata gyaran jiki akahanata fita Koda atsakar gidane batareda k’aton hijab ba, hijab d’in blue color ne abunka da farar mace saiyamata kyau kamar damacan danta aka dinkasa.

Kallonta yake yanda take fara’a tana dariya sai shima yatsinci kansa acikin fara’ar, fitowa yai daga cikin motarsa yai tsaye, y’ar tazararda ke tsakaninsa da ita batada woni nisa hakan yabashi damar Kiran sunanta ahankali a lkcnda tai sallama da wonda take mgn dashi zata fice,

    “MADINAH…..” tsayawa tai cak sbd jin muryarda Koda a mafalki tajita bazata tab’a mantawa da mamallakinta ba, nantake yanayin fuskarta ya sauya, annurinda ke d’auke a fuskarta yakawor, ahankali kuma tajuyo.

Tabbas kowa shid’in ne, mamakin dake zuciyartane yakasa b’oyuwa harsaida ya fito k’arara a fuskarta, shima kuma yaga hakan.

Ahankali yamatso kusa da’ita kasancewor motocin dake gurin dik sun fice bakowa saisu kadai, tsaye yai agabanta yana tinanin taina ma zai fara mata magana,

Woni irin sabon tsana da takaici ne suka tasomata, batasan lkcnda tacemasa “Kai….! malam lafiya, meya kawoka a kofar gidanmu?” tai maganar tana watsa masa wota muguwar harara, dikda k’arfin hali irin nasa a da amma yanzu saiya tsinci kansa da in ina woi kuma agaban mace “am…am…dama..daman” dasauri takatsesa da fad’in,

     “Kaga malam, wlh kayi gaugawor barin kofar gidannan tinkan nasaka amaka wulak’anci da cin mutuncinda ba’atab’a maka irinsaba a rayuworka, wato kazone kacigaba da aiwotarda tarin wulak’anci da cin amanarda kamana, bayan wocca kamana a baya, to kasani yanzu bakamar da bace, nafi k’arfin tinaninka wlh, kayi gaugawor barin kofar gidannan”.

Kallonta kawoi yake yarasa mezaice mata, ganin hakan bashine mafita agaresaba yasa ya yanke hukunci fadamata sak’on zuciyarsa, ahankali yabude bakinsa danufin yai magana kawoi saiga jawahir tafito tareda cool susi, murmushi yai sannan yace,

“Nazone naga y’ata, banazo bane don wota manufa kamar yanda kike tinani, Madina inaso kiyi hkr kimanta da abunda yafaru abaya kodon feature d’in y’ar mu, kiyi hkr dan Allah, dama nazone domin inbaki hkrn abunda yafaru a baya, saikuma nazone naga y’ata idanda halima harna d’auke ta natafi gida da’ita domin y’an uwonta susanta itama tasans….” ai baiko k’arisaba Cool susi tai saurin katsesa da fad’in,

       ….”Hey…hey…Mr. man, dakata dakata dan Allah, y’ar ka, tin da can bakasan yarka bace sai yanzu woi har kake fad’in abaka ita katafi da’ita, hmm kaga malam, kayi gaugawor barin kofar gidannan wlh tinkan mumaka rashin mutuncinda yafi wonda muka maka a Cyprus” kallon Madina yai saiyaga tana watso masa mugun kallo da muguwar harara wocca tasakashi d’imaucewa.

  Dak’arfi Madina tace “zakabar kofar gidannan kosaina saka anman k’asa k’asa dakai, kadaisan irin yanda mutanen k’auyen nan ke takaicinka, to wlh yanzinnan zansanardasu suxo sumaka d’an banxan duka wonda harsaisun sauya maka kamanni”.

Story continues below

Ahankali yake kallonta yana murmushi, shisam abunda take fad’a baya bata masa rai, hasalima woni irin farinciki yakeji yana ratsa zuciyarsa dama gangar jikinsa gaba d’aya, leb’banta yake kallo yanda take sarrafasu wojen fitarda magana, Saida tagama sannan yace “hmm…! Madina kenan, ai dai nasan Koda nai laifi tinda nabaki hak’uri to yakamata ki hak’ura d’in, kodon darajar y’ata” cool susi tace “ai wlh bakada wota sauran daraja a idanmu, dan natabbatarda ko ita y’ar taka taji lbrn abunda kayi bazata tab’a yafemaba bare kuma ita wocca ka aikatawa zalincin, kaga DEEDART kabar kofar gidannan wlh tin kanada kyan gani” murmushi kawoi yai sannan yakoma agun motarsa,

Sukowa shigewa cikin gidan sukai tareda rufo kofar.

Shikowa yara yasamu yabasu kayanda yasiyowa jawahir yace sukai cikin gidan, yaran nashiga dasu saiga Madina dasu chuchu sunfito a fusace cikin tsintsar masifa da bala’i, Madina ko hijab babu d’an woni d’ankwaline kawoi tayafo akanta,

   Jikinta kuma tana sanye da sket da riga na material light blue mai ratsin fari a jikinsa, d’inkin yamatuk’ar karb’anta yazauna daram a jikinta, matasan zamanta dik sun fito, hakama dukiyar fulanin ta sunfito sbd cikarda sukeda shi yasa har suka rinjayi rigar.

Cikin masifa takarbi kayanda ke hanun d’ayan yara tana fitowa tawatsa masa su a jikinsa sannan tanunasa da yatsa tareda zazzaro ido ta firfito dasu woje hancinta sai budewa yake yana rufewa sbd tsabar b’acin rai, yatsanta kamar zai tab’o hancinsa dikda kowa tsayinsa yafi nata amma sbd masifa da b’acin rai saitakejin inbata nunasa da yatsan haryatabo hancinsaba bazataji d’adi ba, hakan yasa tamatsa gab dashi tana fad’in,

“This is the first and last dazaka sake d’akko tarkacen shararka ka kawo acikin gidanmu, kasani y’ata naginatane akan tubalin gsky, y’ata bazata tab’a cin haram ba, bazata tab’a shan haram ba sannan bazata tab’a saka sitirar Haram ba matukar ina raye kowa,

   DEEDART…. y’ata bata bukatar komai naka sbd awadace take da dikwoni abu dazaka d’akko ka kawo mata, Koda ka d’akko shi ka kawo ni bazan tab’a barinta tayi amfani dashiba, be

Woi shin DEEDART me kake nufine, so kake y’ata taci abincinda aka siya da kud’inda aka bak’anta rayukan mutane bila adadin, so kake tasaka sitirarda aka siya da kud’inda aka samu tahanyar cin zarafin woni bawon Allah wonda yake neman abinci da abin sha, to kasani matukar ina raye jawahir bazata tab’a saka komai daya fito daga hanunkaba, kokuma taci abinda yafito daga gunkaba, Koda kowa tanajin yunworda zata iya sanadin barinta duniyane, matukar saitaci abinda yafito daga hanunka zata rayu to gwonda tamutu wlh,

DEEDART daga yanzu   karka sake nasake ganin kafarka a kofar gidannan, wlh wlh idan nasake ganinka a kofar gidannan hmm…” saitai kwafa sannan tak’arisa da fad’in “zakasha mamaki ne” sannan tajuya tana wurga masa wota muguwar harara, 

Hakama su chuchu mugun kallo suke watsa masa wonda yake d’auke da tsintsar tsana a fili, hakika ransa yabaci matuka da kalaman Madina izowa garesa,

Baisan lkcnda kwollah suka cikamasa idoba saikuma yai murmushi wonda yafi kuka ciwo, bud’e motarsa yai yashiga yatada yafice yabar kayan anan batareda yadauka ba.

Tafiya yake yana driving lkc zowa lkc kuma yana sharan kwollah, a zuciyarsa yake fad’ar “woi yau nine wota mace take fadawa woennan mugwayen kalaman batareda yamata komaiba, tabbas kalaman Madina sun matukar tab’a zuciyarsa amma kuma tsananin so da k’aunarta dake azalzalar zuciyarsa yasa yake mantawa da kalaman nata.

Gudu yake ssi nantake kowa cikin y’an mintina ya’isa gida, Koda ya’isa kowa yana wojenyin sallar magrib danhaka shima yai alwola sannan yafice izowa masjid,

Bayan sungama sallar yadawo gida yashige d’akin su yai kwonciyarsa, yau itace ranarda zaayi party danhaka angwaye dik sunacan wojenda akewa ango shiri, su momy kowa suna cikin gida ana shirye shiryen tafiya party d’in, kasancewor yau ranar ta y’ammata ce da samari shys su momy kam sukace bazasuje ba.

Story continues below

Tinda yabaro garin Raha yakashe wayoyinsa gaba d’aya, Abbas sai kiransa yake amma bata shiga baya samunsa, gashi jiya akai kamu kuma baijeba, yaukuma gashi anyi party again baizoba,

Layin momy yashiga kira, saidai yana shiga Kiran amma ba’ad’agawa, dan woyar tanacan a bedroom d’in hajiya tayar.

Ganin bata dagaba yasa yakira layin Deen yace yakaiwa momy woyar yanaso yai magana da’ita, nankwa dasauri Deen yaje yakaiwa momy woyar tanacan acikin babban parlor tareda bak’inda sukazo biki, nanyamika mata woyar tareda fad’in “Yaya Abbas yakira yanaso zaiyi magana dake, yaita Kiran layinki amma ba’ad’agawa” karb’a tai tareda k’ara woyar a kunne, ahankali Abbas yafara magana kamar haka,

      ….”Ammu na, dan Allah ki kira brother kimasa fad’a, ammu na kiduba kiga yanda brother yake nema yasaka kansa acikin woni mawuyacin hali, jiyafa baije kamu ba yauma kuma baije party ba, gaba d’aya ya hargitse, yana cikin damuwa ssi amma yaki yafad’awa kowa damuwor sa, dan Allah ammu na kimasa magana wotak’il ke zai gayamaki” numfashi momy tasauke sannan tace “shikenan Abbas, barni dashi kawoi, zansan yanda zanyi dashi insha Allah” saiyace,

     “To ammu na” nan sukai sallama sannan yakatse Kiran, tana katse kiran Kai tsaye tafice izowa side d’insu na maza.

A kwonce ta taddasa kan kujera yad’ora kansa akan hanun kujerar tareda d’ora hanunsa d’aya akan goshinsa d’ayan kuma kan cikinsa fuskarsa tana kallon sama alamar yai zurfi acikin duniyar tinani.

Tin a kofar shigowa tai sallama takuma sakeyin wota lkcnda tak’ariso kusa dashi amma shuru kakeji, yai nisa ssi acikin duniyar tinani,

Ahankali momy ta tab’asa tareda Kiran sunansa “DEEDART…” sai a lkcn yai furgigit yadawo hayyacinsa, ganin momy tsaye agabansa yasa yamike a zaune dasauri sannan yashafa fuskarsa da dika hannayensa,

Zama momy tai a kusa dashi tana fuskantar sa, ahankali kuma tafara masa magana “Ahmard, tin bayan lkcnda woncan al’amarin yafaru dakai nafahimci akwoi damuwa a tattare dakai, ahmard ni mahaifiyar kace nafi kowa sanin woni motsi naka dikda kowa baka fad’aman damuworka, nasani tabbas kanada damuwa amma kak’i kafadaman kakuma ki kafadawa kowa,

Ahmard dikda zirfin cikinka kake dashi yau kakaiga damuworka hatta bayyana a jikinka, ahmard dik karame Kai bak’i Kai muguwar rama Ahmard, dik wonda yasanka abaya idan yaganka a yanzu tabbas zaice karame,

A kwanan baya idan baka mantaba nataba tambayarka akan abunda ke damunka kaceman bakomai, yau ahmard inaso nasan abunda ke damunka, meke damunka ne DEEDART…?” tajefa masa tambayar Kai tsaye kuma cikin d’aurewor fuska da Shan kunu.

Ganin babu alamar fara’a a fuskarta yasa dole yadawo hayyacinsa tareda gyara zamansa, saikuma yashafa fuskarsa sannan yafara magana cikin nutsuwa.

“Hak’ika momy tabbas inada damuwa kuma inacikin damuwa wocca nakasa magancewa kaina ita, dikda dafarko band’auketa wota babbar damuwa ba amma yanzu tana nema tafi k’arfina,

Sanin kankine momy tinda kika haifeni bantab’a yin soyayya ba bankuma tab’a afkawa acikin tarkon so ba, hasalima ni mace bata a gabana bata acikin abunda zansaka agabana harya dameni, saidai wonnan karon kam tasauya zani momy,

Na afka acikin kogin so, na tsunduma tsundum acikinsa wonda kuma nakasa fitarda kaina” saikuma yai shuru tareda sadda kansa a k’asa.

Momy tace “son wacece ka kamu dashi, wacece ita, suwaye iyayenta a fad’in jihar nan?” gyara zamansa yai sannan yacigaba “bakowa bace momy face wonnan yarinyar damuka samu matsala da’ita a kwanan baya wato Madina, momy zuciyata takamu da so da k’aunar wonnan yarinyar a lkcnda baidace ba, momy bansan lkcnda zuciyata ta afka acikin wonnan yanayin ba, danasani wlh danayi k’okarin hanata, yanxu gashi nakasa controlling nata, nema take ma tasakani acikin woni mawuyacin hali konace ma tasakani d’in,

Story continues below

Woni irin sonta nakejin yana azalzalar zuciyata momy, dafarko ban yarda da abunda nakejin zuciyar tawa take sak’amanba shys naki fadawa kowa, saigashi yanzu abun yafara fin k’arfi na, dikda irin k’okarin danne abun danakeyi amma Saida bayyana kowa yasani, 

Momy naje gidansu Madina domin nafad’a mata sak’on zuciyata amma taki ta saurareni, daga karshema tace karna sake zowa kofar gidansu, hakama y’ata tahanani naganta hatta kayanda nasiyamata taki karb’a daga karshe ma anan tabarsu yashe ak’asa tafice, momy nakasa samun mafita, wlh inasonta ina matukar k’aunar ta, nikad’ai nasan irin azalzalar da sonta yakeman acikin zuciya” yak’arisa maganar tareda shafa fuskarsa yashafe zufanda yake keto masa.

        ….. Nannauyan numfashi momy tasauke tareda gyara zamanta sannan tace “tabbas wonnan al’amarin dagirma yake, wlh ni nama kasa taina zan b’ullowa lamarin, DEEDART bakada wota hanya wocca zaka sami soyayyar yarinyar nan, sbd wlh konice kayiwa abunda kamata bazan tab’a aurenka ba, Kai koma ganin fara’a ta bazakayiba barema har akaiga batun aure, zahirin gsky katafka babban kuskure, amma dudahaka baza’arasa abunyi ba, yanzu dai firstly kafara neman soyayyarta tahanyar yarka, maana kajefi tsuntsu biyu da dutse d’aya, nima kuma zantayaka neman yafiya agunta domin kasami saukin samun soyayyarta”.

Murmushin jin d’adi yai harsaida fararan hakoransa na gaba suka bayyana sannan yace “Okh…momy, tnx u allot, kuma kitayani da addu’ah dan Allah momy na, Allah yasaukaka zuciyar Madina ta yafeman abunda namata sannan ta amince da tayin soyayya ta” momy tace,

    “Insha Allah, zan tayaka, kaima kuma kadingayi” yace insha Allah, 
bayan sungama magana momy tamike a tsaye tareda fad’in “katashi ka dauro alwola kazo Kai nafila” yace to tareda mikewa a tsayen itakuma tafice,

Yana kan sallaya yana addu’oi bayan yagama sallar saigasu Abbas sundawo, su hud’u ne kowanne yasha wonka tsadajje nagaske, Abbas ko kallonsa baiyiba woi fushi yake dashi, bayan yagama yaje yarungume shi yashiga bashi hkr,

Dakyar Abbas yahak’ura sannan suka dawo normal akacigaba da tsare tsaren yanda fulanis day nagobe zai kasance, shidai sauraronsu kawoi yake amma hankalinsa dama zuciyarsa gaba d’aya tanacan gun masoyiyarsa Madina.

      ……..Kwonce yake akan bed d’insu yayinda Abbas da Dr ilyas abokin Abbas ke gefensa suna sharan bacci, a yanzu kusan 2am kenan, kowa yai bacci amma bandashi, bacci ya k’auracewa idonsa gaba d’aya banda tinanin Madina ba abunda yakeyi, sai faman juyi yake akan gadon.

Dik ya rintse idanuwonsa ba abunda yake gani sai kyakkyawor fuskar Madina wocca take d’auke da murmushi da fara’a, mostly abunda yafi tinawa dashi nata shine, 

      Yanda take sarrafasa leb’banta idan tana magana, skin color d’inta ma nadaban ne Madina bare kuma kyanta, babban abunda kuma yake k’ara masa sonta shine, zazzak’ar zumarda ya d’andana ta y’ar uworta wocca ta gigitasa ta jagula masa lissafi, tinda yake baitab’a jin mace mai cikekkiyar ni’ima kamarta ba, hakan ya tabbatar masa da tabbas itama Madina tanada wonnan ni’imar tinda dai munawara da Madina dik abu d’aya ne, maana twins,

Wonnan abun ne yake k’ara hargitsa masa lissafi, sbd yana matukar San mace mai ni’ima musamman yanda yake da yawan buk’ata.

Tabbas idan yarasa Madina yayi babbar asarar rayuwa wocca bazai tab’a samun kamarta ba, Koda yasamu to bazatakai kamar Madina ba,

Yanacikin tinane tinane baisan lkcnda bacci b’arawo ya d’aukesa ba, nikwa nace mallam DEEDART asuba tagari.
  ________________________

A b’angaren amare su Madina kowa, a daren jiya da’akayi mother’s night bahijja ta’ebi k’awayenta suka cika mota har biyu sukaje suka rikita wojen suka hana ayi event d’in,

Wojen masifa harta yankawa Isma’il wuk’a a hanu, taje tayankawa Madina ne shikuma saiya kare Madina wuk’ar tayankesa, Kai daga karshe dai Saida aka Kira police sukazo sannan aka d’auki su bahijja akaje dasu station, Dr yace asakasu a sell kar a fito dasu har sai angama biki and’aura auren.

A daren dai haka aka watse ba’acikin farinciki ba.
  ________________________

Washe gari bayanda ya’iya dole yabi su Abbas wojen shirye shiryen event d’inda zaayi a yau, saidai dik abunda ake jiki a sanyaye yakeyinsa sbd yawon tinane tinane dayakeyi akan Madina,

Sai kusan 3pm sannan suka dawo gida, haryai wonka ya kwonta suna y’ar fira tareda su Abbas saikuma yamik’e tsaye yashiga ciki,

Sabon shiri yai inda yasaka kaya English wears wandon jeans da white t-shirt, sai takalma cover shues masu kyau, bayan yashirya sannan yafeshe jikinsa da dad’add’an tiraruka masu sanyin k’amshi, daganan yafito yacewa Abbas,

      “Brother bani key car d’inka inaso zan fita amma bazan jimaba zan dawo, sbd yau kasan ranarmu ce fulani, so dole nayi attending nata, kodon gujewa gorinka” yak’arisa cikin murmushi, shima Abbas d’in murmushi yai sannan yaciro key car din yabashi tareda fad’in “Allah yabada sa’a, yasa adace, yakuma kiyaye hanya” cikin mamaki DEEDART yakallesa dan yai mamakin yanda Abbas yagane inda zashi.

Abbas yalura da mamakinda DEEDART yake saiya kaimasa dukan wasa irin nasu na gayu yana dariya tareda fad’in “Oh.. come on broz, tafi mana” sai yai murmushi sannan yafice tareda kashe masa ido d’aya, Abbas yai dariya danyaga yanzu ya fahimci inda yadosa.

Yana fita kai tsaye yafice izowa garin Raha, acikin d’an k’ank’anen lkc ya’isa garin, yana isa Kai tsaye yafice izowa gidansu Madina, 

Koda ya’isa bakowa a kofar gidan danhaka Saida yajira yasamu yaro ya aikesa yace yaje yace ana sallama da Madina, nan yaron yashiga Jim kadan yadawo yace “ance tana zowa” saiya masa gdy sannan yabashi 1k yaron yakarba yana murna yana gdy yafice abunsa,

Har kusan 15mnts bata fitoba, danhaka yasake aika woni yaron akaro na biyu, nanma Saida takwashe kusan 5mnts sannan tafito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *