HUTU
CHAPTER 13 KARSHE
Wasa wasa shirye shirye ya kankama saboda kusantowan lokaci, Binta ta dade da komawa gidan Ummi saboda gyaran da ake mata, kayan yayi ready aka inda zata zauna ma, komai anyi shi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, yau su Hydar suke da niyyan zuwa kauye dan kai musu katin gayyata na auren Binta, duk sun shirya shida Abba se Khaleel da yace ze rakasu, mota daya suka dauka Hydar da Khaleel na gaba Abba na zaune baya aka musu Allah ya kiyaye hanya suka dau hanyar kauye, hira sukasha a hanya har suka isa dan ba karamin gudu Hydar ke sharara wa ba dan kawai su samu su shiga da wuri su fito da wuri.
Tin daga nisa Hydar yaga kwance a bakin titi guda da sauro duk sun zagaye ta, banda sushe sushe ba abinda takeyi, a hankali Hydar yayi slow down tareda cewa “Abba ga wata chan kwance a kasa, koh zamu duba kila tana bukatan taimako, kada kai Abba yayi ai kuwa sukayi parking suka fito Zinaru da ta dade da ganesu dan ko a gadon mutuwan ta take bazata manta fuskar Hydar ba, da sauri ta tashi taja baya gudan na kara binta Hydar dake karasawa ya tsaya cak yana kallonta kafin daga baya ta nunata da yatsa yace “dama kece a nan”, ya fada disgustingly, shiru ta mishi Khaleel da Abba suka hada baki wurin cewa “ya ya”, kallon Abba yayi yace “Abba matar da ta rike Binta ce, har taso ya salwantar mana da rayuwarta a gidan karuwai”, se a lokacin Abba ya gane ta yarda girgiza tareda cewa “yaushe ta fito”, Hydar ya daga kafada yace “nima ban sani ba, mu wuce kawai, kila ishara ne Allah ke nuna mata tin yanzu”, girgiza kai Abba yayi yace “a’a baza’ayi haka ba, bazeyu mu barta a nan ba”, daga sama sukaji tace “ai kawai ku wuce ku barni a nan din, dan an kauyen mu ma basa sona shiyasa suka koreni”, kallon kallo sukawa junan su sannan Abba yace “muje mu gana da mai garin”, juyawa sukayi suka shiga mota suka kara gaba ta bisu da kallo.
A gaban gidan mai gari sukayi parking aka tarbesu da mutunci suka samu wuri kan tabarma suka zazzauna, bayan sun gaggaisa Abba ya kalli mai gari yace ” munzo baku katin gayyata ne, ‘Yata Binta zatayi aure nan da sati biyu rana ita yau kenan”, gabadayansu seda sukasa albarka tareda nuna farin cikin su karara suka karbi katin Hydar ya shaida musu ze bari azo a dauki wa’anda zasuje idan ana gobe daurin aure sannan Abba ya gyara zama yace “munga matar mahaifin Binta a wajen gari bakin titi nace koh lfy”, mai gari ya gyara zama tareda cewa “ai kawai ku barta inda kuka ganta dan Zinaru annoba ce, ga malaminta chan shima Allah ya saukar mishi da bala’i, itama gwara kawai ku kyaleta dan ba alkhairi bace”, Abba beson yaja magana dan haka yace “Allah shi kyauta”, duk suka amsa da “Ameen”, seda sukayi sallan zuhr sannan suka bar kauyen.
A nan inda sukaga Zinaru suka sake ganin masu wucewa suna bata sadaka tana karba, suma kowannensu seda ya bata kudi ta karba cike da jin kunyar su, Abba be bar wurin ba seda ya shaida mata bikin Binta wanda taji kaman ta mutu dan bakin ciki da takaici, suna wucewa take miki ta hau tsakiyan titi tana tsayar da motocin dake wucewa saboda ta samu ta shiga birni dan tawa kanta alkawarin indai tana da rai toh Binta bazatayi aure ba.
Wani babban motane yazo wucewa da gudu, tin daga yake mata horn amma ina Zinaru se daga mishi hannu takeyi ita ala dole seya tsaya, ashe nan motan beda break shiyasa yake ta danna mata horn, da gudu motan yayi kan Zinaru wacce tin kan motan ya bigeta taga mutuwanta (Allah kasa mu cika da imani, Ameen) motan na bigeta ya kara gaba abinshi, ya barta wurin kwance gefen titi duk kwanyar kanta ya fito waje haka ma en hanjin cikinta, (yau Zinaru taga karshenta ba tareda ta nemi yafiya ko gafarar wa’anda take zalunta ba, ni bazan yanke mata hukunci ba tinda bamusan tsakanin bawa da Allahnshi ba, sedai muce Zinaru Allah ya jikanki).
A gajiya su Hydar suka koma gida batare da sanin abinda ya faru da Zinaru ba, Binta, zaune a dakinta tareda Afeefah da Zeenah suna tsara yanda bikin ze kasance wayan Afeefah ya soma ringing, tana dubawa taga MK ne dan dama ya musu alkawarin kira, dauka tayi tasa a speaker sannan suka gaisa yake tambayarta ko sun gama tsara events din tace mishi sun gama, “nawa kuke bukata yanzu?”, ya tambayeta, kallonsu Zeena tayi sannan tace “200k will be enough”, murmushi yayi sannan yace “ba matsala, anything else?”, tace “se maganan hall”, yace “muna sane dashi, any other thing”, ta girgiza kai tareda cewa “no”, yace “ok, turo min account number da za’asa muku kudin ciki”, sallama sukayi suka kashe sannan ta tura mishi account din Zeena, suna zaune suna hira Binta na musu mitan events din sunyi yawa sukaji alert, Zeena na dubawa taga 250k ta kalli Afeefah tace “Amma abokan angon nan sunyi a rayuwa, kalli harda karin 50k akai”, Afeefah tayi dariya tace “Abu na masu kudi”, itadai Binta shiru kawai ta musu tana kallonsu, bata taba tunanin zatayi irin wannan wedding din da ake tsara mata ba, not even in her wildest dream.
Shirye shirye ake na biki ba kama hannun yaro, dangi na nesa da na kusa duk sun fara halartowa, maza da mata har ma da abokan arziki, yau ya kama laraba kuma yaune dangin amare kesa ran za’a kawo lefe, yayin da amarya da kawayenta suka shirya Tea Party a gidan Zeena, basu wani cika sosai ba, daga kawayenta wa’anda sukayi school tare se en uwa da sukazo biki se Zeena kirjin biki, inda amarya ta shirya cikin simple long gown wine, ba wani make up din azo a gani tayi ba, simple make up tayi, inda kawayenta ma duk suka shirya cikin gown kowa nashi daban, sedai akwai specific color da sukayi which is peach.
Shirye shirye ake na biki ba kama hannun yaro, dangi na nesa da na kusa duk sun fara halartowa, maza da mata har ma da abokan arziki, yau ya kama laraba kuma yaune dangin amare kesa ran za’a kawo lefe, yayin da amarya da kawayenta suka shirya Tea …
Karfe hudu aka kai lefen Binta akwati takwas, amma kayan dake cikin akwatin sunfi karfin Akwatin kanshi, kaya ne na azo a gani dan kuwa bana banza aciki, sosai mom tayi kokari wurin hada lefen dan kuwa kowa ya yaba kyan kayan.
Akwatin lefe👆
Su Binta basu suka dawo gida ba se dare, sun ga lefe kuma sun yaba dan Binta harda hawayenta dan bata taba tunanin zatayi irin wannan wedding din ba, angwanai basuje Tea Party ba amma sunga hotuna, Anwar duk yadda yaso yaga Binta ta hanashi zuwa gidansu kusan sati biyu kenan amma taki yarda ya ganta se dai suyi waya.
Washegari Thursday sukayi bridal shower wanda ya hadu sosai, sunyi komansu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ba tareda hayaniya ba, inda amarya ta shirya cikin white bathrub me touches din peach da black, ta dora karamin crown a kanta, sosai tayi kyau kaman a sace ta a gudu, gabadaya kawayenta kuma black vest sukasa an musu customize din sunansu da white ink suka hada da black pencil jeans se takalmi trekkers shima white, sosai sukayi kyau komai sunyi shi ne with maturity da civilization.
Washegari Thursday sukayi bridal shower wanda ya hadu sosai, sunyi komansu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ba tareda hayaniya ba, inda amarya ta shirya cikin white bathrub me touches din peach da black, ta dora karamin crown a kanta, sosai tayi..
Washergari Friday akasa amarya a lalle, tin safe se wuraren goma aka bari tayi wanka sannan aka fara mata bakin lalle a hannu da kafa, basu suka gama ba se sha biyu sannan ta samu ta sake wani wankan, sosai lallen ya karbeta ya mata kyau, karfe biyu aka fara kamu a cikin compound din gidan wanda akama decoration da kayan kumbo, gabadayansu atampha sukasa yayi daga manyan har yaran har kawayen gwanin sha’awa, hatta Nawaf little baby boy dinta yasa yayin, amarya kuwa shiryawa tayi cikin blue lace da sarka silver kayanta dikin buba da zani, sosai tayi kyau abinta se shan hotuna takeyi, angwanai sunzo sunyi kamu da misalin karfe hudu aka fara watsewa aka bar en uwa zasuyi fulani day.
Karfe biyar aka fara Fulani day, gabadayansu sun shirya cikin kayan Fulani, amma na amarya ya dan banbanta da nasu, sosai Fulani din ya kayatar banda wakan Fulani ba abinda ake bugawa a wurin, Binta da kanta seda tayi rawa sosai harseda ta hada gumi sannan taje ta zauna dan ta huta. Se da duhu ya shiga sosai sannan DJ ya kashe aka watse.
Se da duhu ya shiga sosai sannan DJ ya kashe aka watse
Duka wannan events da bidirin da akeyi ba’a bar Kausar a baya ba dan kuwa itace uwar amarya, su mai gari, abokan Abba, abokan Dad, abokan Hydar da Khaleel, abokan ango na nesa dana kusa duk sun karaso saboda gobe asabar daurin aure wanda za’ayishi da karfe 10 na safe, tinda Binta tayi wanka ta kwanta ta shiga tunanin iyayenta da rayuwarta ta baya, wai yau itace ta samu wannan gatan kaman ba marainiya ba, dan kuwa ita kanta tana manta cewar ita marainiya ce ba kaman sanda take tareda Zinaru ba da a kullum seta tuna mata da cewar ita marainiya ce wacce batada wani gata sena aikin bauta, batasan sanda ta fara hawaye ba seda taji kumatunta a jiki, goge hawayenta tayi sannan tayiwa iyayenta addu’a, tayi addu’a ta kwanta, tana kwanciya text ya shigo wayanta, dauka tayi ta duba taga Anwar ne, murmushi tayi dan tasan fushi yakeyi da ita saboda taki fitowa ya ganta, tana bude text din taga an rubuta “from tomorrow onwards u will b mine, I can’t wait to have u in my arms baby mama💕💓”, so uku tana karanta text din tana murmushi sannan tayi reply dinshi da “same here”, text din na shiga ta kashe wayan saboda karya kirata dan wani kunyarshi takeji wanda ada batajin wannan kunyar.
Washegari tin da safe gida ya fara cika, se shirye shirye zuwa daurin aure akeyi, Hydar ne tsaye a dakinshi dake gidan Ummi, Kausar na tsaye gabanshi tana tayashi shiryawa Nawaf kuma na zaune kan gado shima yasa kaya iri daya dana babanshi zeje daurin aure, turare ta fesa mishi sannan ta kalleshi tace “kayi kyau”, yayi murmushi yace “amma ai duk kyau na ban kaiki ba”, hararanshi tayi sannan tace “yanzu da gaske kaine waliyyin ta”, ya kada kai yana murmushi yace “haka Abba yace”, cikin zolaya tace “iye, su Abban Nawaf an zama manya har ana waliyanci”, dariya ce ta kubce mai ya kalleta yace “idan na biye miki sena makara, akwai mutanen da zanje na dauko a hotel yanzu, se bayan daurin aure zaki ganni”, kada mishi kai tayi yayi kissing dinta sannan ta mishi Allah ya kiyaye hanya ya amsa da Ameen yana daukan Nawaf suka fita, Kausar kuma tayi cikin gida.
Kafin goma an cika a masallacin unguwan, chan na hango Anwar sanye da farin shadda dinki babban riga da jumpa, yasa hula zanna bukar gold kaman yadda aikin kayanshi yake gold, haka ma takalminshi da agogonshi, gefenshi MK ne da Jamil tsaye, a hankali suka taka zuwa cikin masallaci inda suna shiga bada dadewa ba aka daura aure akan sadaki naira dubu hamsin lakadan ba ajalan ba, Anwar gabadaya bakinshi yaki rufuwa, se murmushi yakeyi yana gaisawa da mutane wanda mostly abokan Dad da Abba ne, Allah Allah yake ya bar cikin masallacin amma jama’a sunki karewa, chan cikin gida kuwa ana daura aure Kausar ce first person data gaya musu an daura saboda tin kan a daura Hydar ya kirata yasa wayan a speaker duk abinda akeyi tanaji, Binta kuka ta fashe musu dashi saboda tunowa da mahaifanta datayi, koda aka kira Ummi tazo ta lallasheta itama kuka tasa bame lallashin wani, da kyar Anty Maryam da Kausar suka samu suka lallashe su, a lokacin har maroka sun shigo compound sun fara buga kalangunsu sunawa amarya waka, ba jimawa sega angwanai sunzo gaida iyayen amarya, suna gama gaisuwa aka fara daukan hotuna, Anwar beji dadin ganin yadda idanun Binta ya kumbura ba saboda kuka amma seya basar ya rungumo abarshi jiki sunata hotuna, a kunne ya rada mata “karkiyi kuka idan za’a kawoki gidana saboda banaso ciwon kai ya kamaki”, murmushi kawai ta iya tayi shikuma ya mata sallama suka wuce tareda abokanshi dan aje a shiryawa dinner.
Karfe shida aka fara shirin zuwa wurina dinner, gabadayansu less sukasa, ba wani takamammen outfit, kowa abinda yake dashi yasa, amarya ta shirya cikin white gown wanda aka jera gold sequence a jiki da mayafi white, sosai kayan ya haskata tayi kyau kaman ba ita ba, shima ango white shadda yasa amma aikin jiki silver ne.
Karfe shida aka fara shirin zuwa wurina dinner, gabadayansu less sukasa, ba wani takamammen outfit, kowa abinda yake dashi yasa, amarya ta shirya cikin white gown wanda aka jera gold sequence a jiki da mayafi white, sosai kayan ya haskata tayi kya…
Kausar ma ta shirya cikin cordless ash da head ash an jera wine stone a jiki tasa bead a wuyanta sosai tayi kyau sannan ta shirya Nawaf cikin sky blue shadda irin na babbanshi hadda hulan yarbawa blue.
Sosai dinner din ya kayatar an bada lbrn ango da lbrn amarya sannan akayi rawa akaci aka sha aka watse misalin sha daya na dare, ganin dare yayi akace ango ya bari washegari za’a kawo mishi amaryarshi amma ina ango ya rufe ido yace shi besan zancen ba, seda aka bashi hakuri aka lallabashi sannan ya yarda badan ranshi yaso ba sedan idon mutane, haka aka watse Hydar ya mayar da amarya da Kausar da Nawaf gida dan ta samu hutu in yaso gobe se’a kaita dakin mijinta.
Washegari da misalin karfe biyu na rana Binta ta shirya cikin farin lace sannan tasa white veil daya rufe ta tin daga saman ta har kasa, dakin Abba su anty Maryam da Kausar suka kaita bayan sun gama mata wanka da humra, a kasa ta zauna kusa da kafan Abba, kanta kasa bame ganin fuskanta balle yasan ga halin da take ciki.
Cike da murna Abba ya shafa kanta idonshi cike da hawaye yace “ban samu daman ganin auren kanwata ba wacce bayan ita banda wata amma cikin ikon Allah se gashi naga auren ‘yar cikinta wanda wannan yasa nakeji kaman Aisha nake aurarwa”, hawayen da B…
Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
Cike da murna Abba ya shafa kanta idonshi cike da hawaye yace “ban samu daman ganin auren kanwata ba wacce bayan ita banda wata amma cikin ikon Allah se gashi naga auren ‘yar cikinta wanda wannan yasa nakeji kaman Aisha nake aurarwa”, hawayen da Binta ke rikewa ne yayi nasarar zubowa haka zalika Abba, Anty Maryam da Ummi ma hawaye sukeyi, ba komai yasa Anty Maryam hawaye ba se ganin Abba na hawaye abinda tin yarintarta bata taba gani na, Kausar kuwa barin parlorn ma tayi dan bazata iya zama ba.
“Binta nasanki da hakuri da rashin son magana, shi aure ba zaman jin dadi kadai bane, zamane na hakuri, komai zakiyi se kin hada da juriya da hakuri, kiji, ki ki ji, ki gani, ki ki gani, yi kiyi, bari ki bari, yanzu zaman aure zakije kiyi, kinada miji yanzu, wanda cikin kashi dari na halayenshi kashi goma kika sani yanzu sauran kashi tamanin din zasu fara bullowa, haka shima akwai halayenki da be sani ba, saboda haka hakuri zakiyi da duk abinda zaki gani kinji”, Kai kawai ta iya dagawa, sannan ya yace “Allah ya miki albarka”, duk aka amsa da “Ameen”, sannan ya kalli Ummi yace “da maganan da zaki mata”, Ummi ta girgiza kai tace “ai ka gama magana”.
Dan nasihan da baza’a rasa ba sauran mutane suka mata sannan aka sata mota, Kausar kin binsu tayi saboda kukan da sukeyi ita da Binta, dakyar aka rabasu kaman basu rabu ba, gidan iyayen Anwar aka kaita tareda damka amanarta a hannunsu, sosai suka nuna farin cikinsu ba kaman Mom da yau take gani kaman tafi kowa farin ciki yau ga Anwar dinta da mata, basu bata lokaci ba suka kaita gidanta wanda already su Zeena na gidan suna jira a kawo amarya, da misalin karfe hudu ne, saboda haka suna zuwa duk sukayi sallah hadda ita amaryan kanta sannan suka tsaya ganin yadda gidan ya hadu, se wuraren shida aka watse aka bar amarya se tilon kawarta Afeefah se babban ‘Yar anty Maryam dan Zeena kin zama tayi wai bazeyu ta zauna tarban kanin mijinta, a wurinta zubar da girma ne. Ana sallahn isha su Afeefah suka kara gyara amarya suka gyara mata daki saka mata wanka da turare suka sawa dakin ma turare sannan suka zauna zaman jiran Ango.
Ango kuwa yana chan ya hadawa abokanshi zafi akan idan basuyi sauri ba shi zeyi tafiyanshi ba dole bane rakiyan ba, banda dariya ba abinda suke mishi dan tinda suke basu taba ganin ango me zumudi irin Anwar ba, run rasa dalilinshi na wannan saurin, shi kuwa ba komai yasa yake sauri ba se dan gani yake kaman idan ba ya ganshi gashi ga Binta a karkashin inuwa daya ba zata iya zama yanzu wani at any given time tinda aurenta ma ba’a bashi cikin sauki ba, haka abokan suka gama shirinsu suka fito daga hotel dinda suke kowa ya shiga motanshi sukasa Anwar tsakiya sukayi convoy zuwa kai ango, Anwar hankalinshi be kwanta ba seda yaga an shiga unguwar, horn sukayi aka bude gate motoci uku suka shiga gidan sauran kuma suka parka a waje, duk fitowa sukayi sukasa Anwar a tsakiya se jin kanshi yake saboda tsabar murna.
Binta tinda taji shigowar motansu ta rasa nutsuwarta dan tin dazu ba abinda Afeefah keyi se tsorata ta, gabadaya se taji auren ma ya fita ranta, indai se taji ciwo sannan zataji dadi daga baya toh ta yafe jin dadin dan bata ganin zata yarda Anwar ya ji mata ciwo da sunan nuna soyyaya, Afeefah kuwa banda dariya ba abinda take mata har sukaji sallaman angwanai, amsawa sukayi banda Binta da kanta ke kasa tana wasa da yatsun hannunta, zama Anwar yayi gefenta yayinda sauran suka tsastsaya Anwar ze bude fuska Afeefah tace bata yarda ba, ya fara bada kudin buda baki sannan, magiya ya fara mata tace batasan zancen ba har seda ya ba Binta dariya, abokanshi ya kalla da idon tausayi su kawo mai doki amma kowa ya sunne kai kasa, suka lokacin da zasu rama masifan da ya dinga musu kenan, a hankali yace “baby mama sun hanani ganinki”, Binta dake lullube cikin mayafi tace “mijina ai basu suke da daman bari ka ganni ba, nike da dama, idan kanaso gaka fuskata umarni kawai zaka bani ni kuma zan aikata”, kowa baki sake yake kallonta dan babu wanda yayi tunanin zatayi magana mussaman ma a gabansu, shi kuwa Anwar murmushi yayi yace “haka akeso mata ta gari ta kasance, yake tauraruwata kuma kyakyawata inaso ki bude min wannan kyakyawan fuskar taki dan a halin yanzu babu abinda nake muradin gani se wannan fuskar taki”, jin haka yasa a hankali ta daga mayafin kanta tareda kallonshi fuskarta dauke da murmushi, shima murmushin ya mayar mata sannan a hankali yayi pecking din goshinta, en dakin kuwa kowa kallonsu yakeyi dan da alama sun manta da mutane a wurin.
Jamil dake tsaye bakin kofa saboda daga nan airport ze wuce zuwa Niger yayi gyaran murya Anwar ya dago tareda hararanshi yace “kunki biyan kudin siyan baki se gashi amarya da kanta ta bude min fuskarta na gani shine kuma zaka tsaya bakin kofa kanamin gyaran murya”, murmushi Jamil yayi cikin hausanshi na nijar yace “malam ka biya kudi kawai a wuce wurin”, “in ka biya ma ai ba lefi bane”, cewar Anwar da a halin yanzu yana rungume da Binta ajikinshi, Jamil kallon Afeefah yayi dan tinda ya shigo dakin ta dauke hankalinshi, hannu yasa a aljihu ya zaro kudi wannan shi kanshi besan ko nawa bane sannan ya ciro card dinshi ya hada da kudin ya mika mata MK dake kallonshi yace “maza kenan”, Jamil ya musu murmushi tareda musu sallama da fatan alkhairi sannan ya wuce tareda MK wanda ze saukeshi a airport, sauran ma addu’an suka musu suma suka wuce daya cikinsu yace ze ajiye Afeefah da ‘Yar anty Maryam gida, har waje Anwar ya raka su sannan ya dawo ciki zuwaga amaryarshi.
Yanda ya barta zaune haka yazo ya sameta, da murmushi ya karasa ya zauna kusa da ita tareda rungumota a jikinshi, a tare suka sauke ajiyar zuciya sannan ya “alhmdllh”, ya kai so uku kafin ya tashi yace “muyi alwallah muyi sallah”, a hankali tace “nayi sallah”, yayi murmushi yace “wanne kikayi?”, tace “magrib da Isha, da kuma shafa’i da wutri”, ya sake yin wani murmushin yace “ai nima nayi amma wannan da zamuyi daban ne, zamuyi shi ne dan nuna godiya ga ubangijinmu daya nuna mana wannan ranan”, kada kai tayi alaman ta gamsu sannan ya mike tareda kama hannunta, a tare sukayi alwallahn suka fito ya shimfida musu sallaya tareda tada kabbara, raka’a biyu sukayi suka sallame ya musu addu’a tareda kama kanta ya mata addu’a sannan ya mata tambayoyi kuma ta bashi amsa, sosai yaji hankalinshi ya kwanta da Allah ya bashi mata nutsastsiya, kamilalliya kuma ilimin Arabi a kanta, babu abinda ya iya yi a lokacin se sake godewa Allah.
Babban rigan jikinshi ya cire ya ajiye sannan yace mata “ina zuwa”, fita yayi ba dadewa ya dawo da cups da plate, kazan da ya shigo dashi ya juye a plate din ya zuba mata fresh milk a cup ya tura gabanta tareda cewa “bismillah”, Kallon kazan takeyi tana hadiyan miyau dan harga Allah yunwa takeji, rabonta da abinci tin kafin tayi wanka a kaita parlon Abba, amma da ta tuna Afeefah tace mata intaci kazan taci bashi yasa takici,(ni kuwa nace ai gwara kici kayanki dan da kici da kar kici duk daya). Kallonta Anwar yayi ganin bataci yace “kici abinci mu kwanta, ko bakyajin yunwa ne?”, shiru ta mishi tareda sunkuyar da kai kasa, hakan yasa ya gane kunya takeji, taci yayi ya dawo kusa da ita ya zauna sannan ya dauki nama ya kai bakinta amma taki karba, ajiyewa yayi sannan yace “meyasa bazakici ba?”, a hankali tace “na koshi ne”, yace “ban yarda ba, kici ko kadan ne ko kuma nayi fushi dake, kisan ance ba kyau mata ta bari miji yayi fushi da ita koh”, kada kai tayi yace “toh kici kinji”, da haka ya samu ya mata yawo ta soma karba yana bata harse da tace ta koshi sannan ya bata fresh milk din ta shanye sannan yace “kiji kiyi wanka kiyi shirin kwanciya, nima wankan zanje nayi”, tace “toh”, tashi yayi ya fito da plate din duk a tunaninta ya tafi kenan shiyasa ta tashi ta shiga closet dinta ta cire kayan jikinta sannan ta daura towel ta shige bathroom.
Wanka tayi tayi brush sannan ta fito ta zauna kan dressing mirror tashafa man humranta sannan ta shiga closet dinta tasa rigar baccinta me hannun shimi wanda ya kwanta a jikinta, daki ta koma tayi addu’anta ta kwanta tareda jan duvet ta lullube jikinta, nan da nan bacci ya dauketa saboda gajiya. Da sallama Anwar ya shiga dakin tareda kulle kofan, yayi mamakin ganin har tayi bacci, fitilan dakin ya kashe ya bar dim light da bed side lamp sannan ya karasa kan gadon tareda yaye bargon da ta lulluba dashi yana karewa surar jikinta kallo, a hankali ya “she’s still young”, kwanciya yayi gefenta tareda janyota jikinshi sannan yaja musu bargo, kaman wanda aka tsikarawa allura ya tashi zaune harseda Binta ta dan motsa, kallonta yayi idonshi jajir a ranshi yace “me zan jira when she’s not a virgin”, kallonta ya sakeyi yaga baze iya hakura ba, ganin tinda a wurinshi ba virgin bace ai ba wani tausayi kawai gwara yayi abinda ya dace a wuce wurin, da wannan tunanin ya jawota jikinshi tareda fara aika mata sakwanni wanda kwakwalar mutum kaman Binta baze iya dauka ba, cikin bacci taji ana tabata, bude ido tayi taga Anwar amma ba Anwar dinda ta sani ba dan wannan gabadaya ya canza mata, idonshi yayi jajir gashi duk wani abinda yake mata cikin zafin nama takeyinshi dan babu abinda ke yawo a kwakwalar kanshi se Mahmoud na rapping din Binta, wannan tunanin yasa bemasan yana mata da zafi ba, hannu tasa tana turashi tareda wage baki zata saka mishi kuka ya hade bakinshi da nata, fita nayi naja musu kofa ganin abin yafi karfina.
Ina zaune waje bakin kofa amma duk kukan Binta inaji, kiran sallahn farko na farka daga baccin da ya daukeni a bakin kofan, “baby mama! Baby mama!!”, abinda naji Anwar na kira kenan yasa nadan bude kofan na leka, kwance Binta take kan gado amma a sume tsabar ta wahala, (su Binta anji maza😂🙊), jijjigata yakeyi sosai amma bata tashi ba, bathroom ya shiga ya debo ruwa yazo ya yayyafa mata bata tashi ba, seda ya kara yayyafa mata sannan taja wani dogon numfashi, ajiyar zuciya ya sauke tareda rungumota jikinshi, dukda batada karfi amma wannan be hanata turashi daga jikinta ba, se yanzu ta gasgata maganan Afeefah, duk kokarinta na son ganin ta turashi ta kasa saboda yanda ya riketa gam, shi kuka ita kuka ni kuwa na tsaya kallon ikon Allah, cikin sheshekan kuka tace “ni ka sakeni mugu kawai, azzulumi”, kara sautin kukanshi yayi ya kara kankameta a jiki ba abinda yake iya furta se “I’m sorry”, be taba tunanin she’s a virgin ba shiyasa ko kadan be bi da ita a hankali ba, amma sosai kanshi ya daure dan Mahmoud ya tabbatar mishi da yayiwa Binta fyade amma ze tambayi Binta yaji gaskiyar maganan. Jin tayi shiru se sauke ajiyar zuciya takeyi yasa ya gane tayi bacci, kwantar da ita yayi yaja duvet ya lullube sannan ya tashi ya shiga bathroom, wanka yayi yayi alwallah ya fito a hankali ya wuce dakinshi saboda kar ya tasheta, seda yayi sallah yayi addu’o’in shi sannan ya dau waya ya kira Khaleel, Khaleel dake zaune yana lazumi yaga wayanshi na ringing, Zeena ta miko mishi yana ganin Anwar ne ya girgiza kai sannan ya kalli Zeena yace “da alama anyi barna”, dariya tayi kawai tana girgiza kai Khaleel ya dauka ai kuwa koh gaisuwa Anwar beyi ba yace “Yaya I need ur help”, bashi da wanda ze kira daya wuce yayanshi shiyasa ya kirashi, Khaleel na jin muryarshi yasan yayi kuka, girgiza kai yayi yana mamakin halin Anwar na rawar kai da rashin bin komai sannu a hankali, “ka kawota hospital by 8 zan bari a dubata, amma for now ka hada ruwan dumi ka bari ta zauna ciki, kayi repeating dinshi so uku”, godiya Anwar yayi sannan ya kashe wayan Zeena ta kalli Khaleel tace “Allah yasa be baro aiki ba”, Khaleel ya amsa da “I hope so”.
Story continues below
Dakinta Anwar ya koma ya sameta kwance har yanzu bacci takeyi, bathroom ya shiga ya hada mata ruwan dumin sannan ya fito ya dauketa, bude ido tayi dan gabadaya jikinta zafi yake mata saboda haka da an tabata takeji, dukan kirjinshi takeyi akan ya sauketa amma be kulata ba haka ya jata har cikin bathroom, cikin bathtub din ya sakata ai kuwa tana saka mishi ihu, yanda take kuka take kokarin fita daga ciki yasa tausayinta ya kamashi, sosai take fighting dinshi dan gata ta fita amma yaki sakinta, seda ya maimaita so uku kaman yadda Khaleel ya umarce shi sannan ya fito ya barta tayi na sarki, bed sheet ya cire ya canza wani sannan zauna zaman jiranta, yana zaune ta fito tana tafiya kafanta na rawa, yanaso yaje ya taimaka mata amma kuma bayaso ta mishi kuka, yana nan zaune ta shirya tayi sallah a zaune dan kafafunta bazasu dauketa ba duk yana kallonta, tana idarwa ta kwanta wurin, zuwa yayi ya tsugunna gabanta yace “baby mama koma kan gado ki kwanta zan bar miki dakin”, ko kallonshi batayi ba ya sake maimaita abinda ya fada nan ma bata kulashi ba, tashi yayi ya kinkimeta duk turjewan da takeyi a banza dan seda ya kaita kan gado ya kwantar ya tabbata she’s comfortable sannan ya fito ya bar mata dakin, yana fita tasa kuka saboda takaici, wai ace Mahmoud beci nasarar yi mata fyade ba amma se gashi mijinta na sunna ne ya mata fyade, me ya kai wannan takaici da ban haushi, dakyar ta samu bacci ya dauketa saboda yadda kanta ke mata wani irin ciwo.
Tashinta taji anayi tana bude taga Anwar zaune gefenshi kuma tea ne da soyayyan kwai da bread, kau da kanta tayi gefe yayi murmushi dan yasan fushin da takeyi, kamo hannunta yayi ta fizge a hankali yace “tashi kiyi brush kiyi breakfast a dubamin lafiyarki”, ita kanta tanaso taje asibitin dan she can feel it a kasanta something is not right, dole ta mike duk dauriyarta na son ganin tayi tafiya daidai ya gagara dan karshe ma zubowa tayi a kasa dan gabadaya jin kafafunta takeyi kaman jelly fish, ko kadan basuda kwari, kuka tasa Anwar dake zaune yana kallonta ya tashi yazo ya zauna kusa da ita tareda rungumeta yana furta “I’m sorry”, bata turashi ba dan dukda shine yasaka a wannan halin amma she needs comfort and for now he is her only comfort zone, kara kankameshi tayi tayi kukanta bil hakki, shikuwa hakuri kawai yake bata kissing her head from time to time, shi ya taimaka mata ta gyara kanta tayi brush sannan tayi breakfast, ba komai yasa ta kyaleshi yake taimaka mata ba sedan ganin she needs help kuma bayan shi babu wanda ze iya taimaka mata, dogon riga ya dauko mata tasa yasa mata hijab da takalmi sannan ya dauketa a hannu suka fito, be tabajin ya tsani gida duplex ba se yanzu da yake sauri ya kai matarshi hospital amma gani yake kaman stairs din sunki karewa, a nan yawa kanshi alkawarin in ze sake gini bungalow ze gina, mota ya sata yayi buckling dinta da seatbelt ya koma drivers side ya zauna yaja mota gateman ya bude musu gate, duk sanda suka hada ido seta harareshi shikuma duk hararan da zata mishi baya bata mishi rai sema ya mayar mata da murmushi.
Parking sukayi ya fito ze dauke ta harareshi tareda cewa “ni ka kyaleni, karka daukeni cikin mutane”, murmushi yayi yace “baby mama let me help u, kinga ba’a cika ba yanzu, ko kinaso kiyi tafiya ne kowa ya gane halin da kike ciki”, shiru tayi dan batasan me zatace ba, ciro wayanshi yayi ya kira Khaleel ringing biyu ya dauka tareda cewa “kun iso ne?”, yace “eh yaya”, “ok”, kawai Khaleel yace ya yanke wayan, suna nan wata doctor ta fito ta karaso gabansu tace “kaine Anwar kanin Khaleel”, yace “eh nine”, tace “ok, be karaso ba tukun, yanzu ya kirani wai za’a duba matarka, tana ina?”, nuna mata Binta dake zaune cikin mota yayi tace “bazata fito bane?”, sosa keya yayi sannan yace “tafiyan ne ke bata wahala, ta bari na dauketa kuma taki”, murmushi tayi sannan ta leka cikin motan tace “sannu koh”, Binta ta kalleta tareda cewa “ina kwana”, ta amsa da “Lfy lau”, sannan ta kara da cewa “dan Allah ki bari mijinki ya daukeki in samu in dubaki dan wannan jinkirin ze iya janyo miki wani aikin”, shiru Binta tayi sannan ta kalli Anwar dake kallonta ya mata fuskar tausayi sannan ta kada musu kai tana fitowa da kafafunta waje, matsawa doctor din tayi sannan Anwar ya dauki Binta ya kulle motan doctor din tayi murmushi dan sun bata sha’awa, so young and adorable, bayanta suka bi reception dinma ba mutane se nurses, patients din daya daya ne, kowa kallon wannan young couple din akeyi, in ka gansu koh ba’a fada maka ba kasan newly wed ne, wani daki suka shiga sannan ta nuna mishi gado ya shimfida Binta, doctor tace “cire hijab kar ya takura miki, ki cire pant dinki ma”, tana maganane tana sa gloves a hannunta, Binta kaman zatayi kuka ta cire hijab ta mikawa Anwar amma taki cire pant din, doctor na karasawa ready to work taga Binta na hawaye sannan kuma bata cire pant din ba, murmushi tayi tace “don’t worry it won’t hurt, cire wandon”, a shagwabe Binta tace “toh kice ya fita”, murmushi doctor tayi dan dariya ma suke bata sannan ta kalli Anwar tace “dan Allah in bazaka damu ba dan bamu wuri”, kada kai kawai yayi sannan pecking lips dinta ya fita waje ya zauna bakin kofa kan bench, doctor tasha mamaki ganin barnar da Anwar yayi, tana mishi kallon yaro ashe dai ba yaro bane, “dole a miki dinki”, ta fadawa Binta dake hawaye dan duk inda aka taba azaba takeji, seda ta mata alluran kashe zafi sannan ta mata dinkin, tana gamawa ta mata alluran bacci dan taga alamun Binta na bukatar hutun, tana gamawa tawa Anwar magana ya shigo, wajen Binta ya karasa yana goge mata hawayen da takeyi doctor ta rubuta mishi magunguna tace “yaje ya siyo”, yana fita ta kalli Binta tace “fadamin gaskiya Binta, kinyiwa mijinki gardama ne”, kada kai tayi alaman “eh”, “meyasa?”, doctor ta tambayeta nan tace mata Afeefah ce tace mata akwai ciwo shiyasa taki yarda shikuma yayi mata fyade, dariya tayi jin wai Anwar ya mata fyade, ba shakka kuwa fyaden ya mata amma kuma bata laifinshi ba tafi ganin wautan Binta, magana ta mata ta fahimtar da ita abubuwa dayawa daya kama ta fahimta sannan ta tabbatar mata da cewar next time karta mishi gardama saboda baze mata zafi ba kuma shima Anwar din zata mishi magana, da “toh”, Binta ta bita saboda baccin dake fizgarta, koda Anwar ya dawo tayi bacci, shima sosai doctor ta mishi fada kuma yace mata ze gyara wannan ma akasi aka samu, sallamansu tayi ba tareda ta rubuta musu bill ba dan Khaleel yace kar a karba.
TWO WEEK LATER
Anwar da Binta an shirya kaman babu abinda ya taba hadasu, ya tambayeta dalilin da yasa ya sameta virgin kuma ta shaida mishi Mahmoud be mata komai ba dan Allah be bashi nasara ba, ya nemi yafiyarta kuma ta yafe mishi, suna zaune lfy banda soyayya da tarairaya ba abinda yake nuna mata, yana tayata duk wani aikin da takeyi koh kadan bayaso yana barinta ita kadai, ya fara zuwa aiki a company din Dad dinshi as general manager while Dad da kanshi ne CEO, Binta bata neman abu wurin Anwar ta rasa, cikin lokaci kankani ya dasa mata wata irin muguwar shakuwa dashi, inya fita duk se taji ba dadi, kullum tana waya da Kausar da Nawaf wanda yake mata magana cikin gwarancinshi, idan tace a kawoshi se Kausar tace seta gama cin amarci za’a kawo matashi, tana waya da Zeena da Ummi ma, kowa na bata kulawa kaman itace autar mata, hutu da jin dadi sun zauna a jikinta tayi kyau tayi bulbul ta cicciko sedai har yanzu jikin ne ba kiba da alama dai ita bame kiba bace.
Yau tana kitchen tana hada dinner saboda Anwar ya kusa dawowa, white rice ta dafa da stew wanda yaji nama da kayan ciki, sannan ta soya plantain, salad ya yanke ta jera komai kan dinning ta wanke kwanukan da ta bata sannan ta koma dakinta tayi wanka, jan mini gown tasa wanda gabadaya tsayinshi a contact ya tsaya sannan ta gyara gashinta tayi parking dinshi, tana cikin sa turare taji horn jin motarshi, da sauri ta dauko hijabi ta zura dan yau farkon ranan da ta fara irin wannan kayan shima kuma Kausar ce ta aiko mata dashi kuma tace dole se tashi, jan parlorn slippers ta dauko tasa sannan ta sauka kasa, tana sauka yana shigowa, kallonta ya tsayayi dan hijab din me kama jiki ne wanda wannan yasa ya gane komeke karkashin ba rigan arziki bane, murmushi yayi ya karasa ya rungumeta tareda cewa “ya akamin kwaliyya kuma aka buyeshi karkashin hijabi”, sunkuyar da kanta tayi kasa tareda cewa “ba komai”, bece komai ba yaja hannunta suka koma sama a zaunar da ita kan gado, tana kallonshi ya rage jikinshi ya shiga wanka ya fito ya shirya cikin riga da wando jeans sannan ya kalleta yace “baby mama a cire hijabi a sha iska mana”, cikin zolaya yayi maganan ta sunkuyar da kanta kasa yace “I have a surprise for you, amma sekin cire hijab zan nuna miki surprise dinki”, kallonshi tayi tace “me surprise din”, ya kashe mata ido daya tareda cewa “ai ba’a fadan surprise, if you are eager to know toh ki cire hijab”, curiosity yasa ta cire hijab din ta ajiye gefe tareda sunkuyar da kanta kasa dan duk setaji ta a takure, “wow”, shine abinda Anwar ya furta tareda janyota ya dorata kan cinyarshi yace “u look extremely beautiful”, murmushi tayi tace “thank you”, zeyi wani maganan ta katseshi da cewa “my surprise”, “oh ok”, yace sannan ya tashi bayan ya zaunar da ita kan gado ya dauko tickets biyu tareda da dawowa ya dora kan cinyarshi ta dauka sannan ya rungumota yace “two tickets for me & u to London to study at Cambridge University United Kingdom, zanyi masters dina ke kuma zakiyi degree and guess what again”, girgiza mishi kai tayi dan dadi ma ya hanata magana yace “I was able to get you admission to study medicine”, tsalle tayi tareda ihu ta kankameshi kaman bazata sake ba tace “thank you so much Ya Anwar, I love you to the moon and back”, dariya yayi yace “I love u more”, dadi sosai taji ganin batada niyyan bashi abinci ya kalleta yace “I’m starving”, murmushi tayi tace “let’s go, dinner is ready”.
Nnamdi Azikwe International airport
Gabadaya family din Anwar da Binta sun zo musu rakiya, babu wanda aka bari a gida, ba’a bata lokaci ba aka kiransu duk sukawa kowa sallama Binta kaman zata tafi da Nawaf amma dole ta hakura ta tafi ta barshi, Kausar harda hawayenta saboda zatasha kewa, cikin jirgi shiru Binta tayi dan duk a tsorace take, this is her first time na shiga jirgi, dariya ne kawai Anwar be mata ba, basu bata lokaci ba suka daga zuwa UK, koda suka sauka already an san da zuwan su, wanda ke jiran karasowansu shi ya dau bags dinsu sannan yayi leading dinsu zuwa mota, Binta kallon garin kawai take saboda yanda ya bata sha’awa, wani mini flat aka saukesu wanda wannan ne masaukinsu, godiya sukawa mutumin sannan Anwar yasa key ya bude kofan suka shiga, daki biyu ne kowanne da bathroom se parlor da kitchen da visitors toilet, seda sukayi wanka suka huta sannan suka fita dan neman abinda zasu sawa cikinsu.
A MONTH LATER
Sun gama process din admission har sun fara attending classes, school din har anyi marking dinsu as youngest couple, tare suke zuwa school su dawo tare, lectures ne kawai ke rabasu, cafeteria tare suke zuwa, in zashi buga ball da ita yake zuwa ko ina zashi yana tafiya da ita saboda bayaso ya barta ita kadai a wannan foreign country din dukda tace ai da haka zata saba. Yau tin safe da Binta ta tashi take jinta wani iri, duk abu da takeyi karfin hali kawai takeyi, Anwar yana lura da yanayin ta amma idan ya mata magana se tace kawai batajin dadi ne, yana gama shiryawa ya kalleta yace “ni zan wuce”, ta mike daga kwancen da take tana daukan jakanta tace “muje”, kallon yanayinta yayi yace “zaki iya zuwa”, tayi murmushi tareda riko hannunshi ta shiga janshi tana cewa “why not”.
A school karfin hali kawai takeyi, koda suka dawo gida kwanciya tayi a parlor Anwar ya debo mata ruwa tasha sannan yace “let’s freshen up se muje hospital”, girgiza kai tayi tace “a’a bacci nakeji”, ganin kasala ya mata yawa yasa ya dagata tareda kaita daki. Washegari da safe Zazzabi yasata gaba, suje hospital kuma taki, dole Anwar ya kyaleta saboda bayaso ya takurata, beso zuwa school ba amma tace yaje ya dawo ba abinda ze sameta, haka ya hakura ya tafi badan ranshi yaso ba, ga mamakinshi koda ya dawo gida taji sauki se ciye ciye kawai da takeyi. Washegari same thing ya sake faruwa, haka suka jera sati Binta na fama da morning sickness, Anwar ganin baze iya biye mata ba yasa dole ya kaita hospital dukda batason zuwa, gwajin farko aka shaida musu tana dauke da cikin wata daya da sati biyu, dadi wurin Anwar ba’a magana, Binta kuwa dora hannunta tayi kan cikinta hawaye na yawo kan fuskarta saboda murna wai yau itace ke dauke da ciki, zata haifa nata babyn itama, Anwar ya kira kowa ya shaida musu Binta nada ciki kuma sosai suka tayata murna ba kaman Kausar, haka Anwar da Binta suka dinga tarairayan cikin dukda cikin me shegen laulayi ne amma haka take daurewa.
ELEVEN MONTHS LATER
“Wayyo Anwar bayana, the baby is coming, do something!!”, a rikice Anwar ya rikota ganin yadda ta rikice, tinda suke bata taba kiranshi Anwar ba se yau, da gani tana cikin matsanancin azaba, ba karamin kokari yayi ba wurin kaita hospital dan duk arikice yake, bata dau lokaci ba ta santalo baby dinta mace kyakyawa da ita, Anwar yayi murna har hospital staffs din sukasan an mishi haihuwa, kira yayi gida ya shaidawa kowa Binta ta haihu sannan ya shiga dakin da aka kwantar da ita da babynta, yana shiga ta fara hararanshi shikuma da murmushi ya karasa wurinta tareda rungumota jikinshi yayi pecking din goshinta sannan yace “thanks baby mama, kin biyani, kinyi gama mun komai a rayuwa, hararanshi tayi tareda cewa “amma daga wannan mun gama haihuwa koh?”, dariya yayi saboda jin abinda ta fada sannan yace “a’a baby mama bamu gama ba, yanzu akayi daya saura sha daya dan dozen zamuyi”, da sauri tace “kaida wa?”, yace “ni dake”, girgiza kai tayi tareda cewa “bada ni ba”, haka sukata hira har kukan baby yayi distract dinsu sannan suka shafawa kansu lfy. Washegari akayi discharge dinsu suka koma gida, da yammacin ranan suka wuce airport saboda dawowa naija tinda haihuwan fari ne.
A gidan Ummi Binta ta sauka, kowa zuwa ganin ita da baby dinta akeyi, Nawaf na ganinta ya gane dan kullum suna video call ta Skype yayi wayo sosai yanzu going to three years harya fara zuwa school, Kausar ma sosai tayi murnan ganin baby itama tanada wani cikin yanzu wanda haihuwa yau koh gobe, ranan suna yarinya taci sunan mahaifiyar Anwar suna kiranta da Benazir. Yarinya tayi kaya haka ma mahaifiyarta, sanda Binta tayi arba’in Ummi ta musu jagora zuwa Adamawa tareda Hydar da Kausar zuwa asalin garinsu inda danginsu suke, sosai Binta taji dadin ganin gida, da sati daya suka dawo ta koma gidanta inda suka bude sabon shafin soyayya ita da Anwar dinta, seda Kausar ta haifi mace akayi suna yarinya taci sannan Ummi suna kiranta da Nabila sannan Zeena ma ta haifi namiji sukasa mishi sunan Abba ana kiranshi junior da sati Binta da Anwar suka koma bakin karatunsu tareda Benazir inda suna zuwa suka samo mata nanny.
TWELVE YEARS LATER
Abubuwa dayawa sun faru cikin shekara goma sha biyu nan, Binta da Anwar sun dawo naija sakamakon gama karatunsu, Meena tayi aure haka ma Afeefah ta auri Jamil haka Seema ma tayi aure, Hydar da Kausar suna zaman lfy da yaransu hudu Nawaf wanda yanzu ya zama saurayi se Nabila se twins Ummul Khairi da Ummu kalthum, Khaleel da Zeena suna zaune lfy, Zeena ta gama karatunta inda ta zama cikakkiyar barista da yaransu shida Ibtisam, Junior, Abul khair, Abul Abbas, Laila se auta Amnah, Anwar da Binta soyayya se abinda ya karu, Binta ta zama cikakkiyar likita tana aiki a hospital din Khaleel as a junior doctor, yaransu biyu kacal, mace daya namiji daya, Benazir se Shaheed. Abba da Ummi sun tsufah dan a halin yanzu ma Abba yau ciwo gobe lfy, Dad Allah ya mishi rasuwa shekara shida da suka wuce sakamakon ciwon koda daya kamashi wanda kafin a gane kuma ciwo ya riga ya cishi, sunyi kukan rashinshi sosai sannan suka barwa Allah komai, Mom ta koma gidan Khaleel da zama dan bazata iya zama ita kadai ba tinda Meena tayi aure.
Yau gabadaya an taru a gidan Hydar saboda tayashi murnan karin girma daya samu wurin aiki, yanzu ya zama babba wanda bayanshi ba wani a samanshi, an bashi rank din field marshal, gabadaya gidan cike yake da yara da iyayensu da kakanninsu, kowa na harkan gabanshi, wasu na wasa, wasu na ciye ciye, wasu na surutu, chan na hango en mata uku wa’anda bazasu wuce 14, 13 ba suna kallon wani dan saurayi wanda a kalla zeyi 16, ta tsakiyan cikinsu wacce da gani tafi tsiwa tace “Ya Nawaf bayawa mutane magana, shi kullum yana game ko kuma yanajin waka”, wacce ke gefenta tace “ke Benazir bakya jin magana, inya kamaki ba ruwana”, murguda baki Benazir tayi sannan tace “dadina dake Ibti akwai tsoro, dan Allah zo muje mu tsokaneshi”, zaro ido Ibti tayi tace “ni rufamin asiri kije keda Nabila”, Nabila da tin dazu batayi magana ba se wasa da gashinta takeyi tace “ban shirya mutuwa ba, gwanda ku anjima gida zaku, nikuma ina nan da Yaya kuma na tabbata kuka wuce seya kusa kasheni”, tsaki Benazir taja sannan tace “toh zanje tinda ku bazaku ba”, ai kuwa tana gama magana bata jira cewarsu Benazir ta ruga a guje se bayan kujeran da Nawaf ke zaune, tsugunnawa tayi sannan a hankali ta mike ta zare headphone dinda ke kunnenshi ta ruga a guje, yasan babu wanda ze mishi haka se Bena saboda haka ya mike tareda binta aikuwa duk gudunta taku biyar yayi ya kamota, ihu tasa mishi dan parlorn ihunta kawai akeji seda taja hankali kowa sannan tayi shiru tana zaro ido yace “ni sa’an wasanki ne?”, ta girgiza kai yace “zaki kara?”, a shagwabe tace “bazan kara ba”, sakinta yayi sannan yace “in kin isa ki kara”, kallonshi tayi tace “sena kara”, sannan ta figa a guje yabi bayanta danya kamota. Tamat billah.
Alhamdulillah a nan na kawo karshen littafina mai suna ‘Yar hutu, kuskuren dake ciki Allah ya yafe mana sannan sakon dake ciki Allah yasa ya isa inda nakeso ya kai.