TANTIRIN NAMIJI CHAPTER 6

TANTIRIN NAMIJI






CHAPTER 6






“Haba Alhaji ai sai ka kashe ta daukar doka a hannunka bai kamata ba sam, ka bari ma asan wa yai mata cikin sai ku dau mataki” cewar Doctor Mahmud.


Ganin da gaske ya ke suka hadu suka bambareshi daga jikinta yana ihu kamar mahaukaci, gaba daya ya zauce saboda tashin hankali, “ku barni na kashe ta dan wallahi da naga wannan tashin hankalin gwara naga gawarta, kuma wallahi ba dai gidana ba ki sanja wani uban ba dai ni ba.”


“Ai bata da wani uba da ya fika kuma wallahi a gidanka zata zauna daram.” Umma ce ta fada tana kuka “tun sanda kuka taho na biyo bayanku dan duk maganarsa a kunnena yai muku, kuma dama na zargi wani abu a raina tun da naji shiru basu dawo ba.”


“Kika kara magana sai ranki ya baci dan ba wata yar iska da zata zauna min a gida, ta koma inda taje tayo iskancin nata har tayo cikin amma wallahi ba dai gidana ba, idan ko ba haka ba wallahi sai dai ki bita ku tafi gaba daya.”


“Wallahi ba inda zan bita kuma a gidanka zata zauna ko kaffara bazan ba, waya janyo wannan masifar kai ne da shegen kwadayin ka da san abun duniyarka, to wallahi anan zata zauna dan ko ka saken ba inda zani zama daram zan yi zaman yayana, dan kasan a yanzu dai wallahi sai dai kai ka barmun gida ba dai ni nabarma ba.”


“Baki da mutunci naga alamu ni kike gayawa haka? au ho to nagane komai ke kika dorata a wannan turbar kenan, tom yau Allah ya tona miki asiri wallahi sai kun girbi abunda kuka shuka gaba dayanku, ke kike turata iskanci wato ko? to wallahi sai kin yi nadama saboda kin gagara har fadi in fada kike dani saboda fitsara.”


“Kai dai zakai nadama wallahi Alhaji ai kafi kowa sanin cewa ba wata kalmar fadi in fada da zata ratsa tsakanina da kai, tun san da na aureka zuwa yau duk umarnin daka bani ina bi ban taba ketare dokarka ba, hasali duk umarnin daka ban sama da shekara talatin ban taba ketare ma ba.


Amma abun da nakeso ka sani hakuri na ya kare, bazan zuba ido kana zaluntar yata ba a banza ni da kai mukaje ta ce aure takeso amma kace baza kai mata ba karatu zatai, yanzu wace riba ka samu ita ba tai karatun ba kuma baka barta tayi auren ba saboda kulafucin san kudi irin naka, to wallahi bazan zuba ido ka salwantar mun da rayuwar yata ba.


Story continues below

Hakuri na ya kure saboda haka bazaka watsan yata ba wallahi, idan kai baka kaunarta ni ina kaunarta kara ce nake ma, abun da nakeso da kai shi ne ka fara tuntubarta waye yai mata kafin ka tafka abun kunya.”


Daddy ne ya ce “ya isa Hajiya! kamata ku samu waje ku zauna mu gama magana idan ma cire cikin ne sai ayi ba matsala, nayi alkawarin zan aureta na rufa mata asiri amma wallahi rai na yai gagarumin baci saboda na tsani harkar zina wallahi.”


Wata harara Umma ta doka masa ta nemi waje ta zauna ta jawo Maryam jikinta, duk da tsananin zafin da ta ke ji a kirjinta amma ta hadiye saboda ta kwatowa yarta yanci.


“Ke!” Abba ya daka mata tsawa “wallahi ko ki gayamun wanda yai miki ciki ko na kashe ki har lahira yanzu, dan wallahi ba wanda zai hanani nai miki yankan rago wallahi.”


Wani ihu ta saka “wallahi Abba zan gayama banaso na mutu yanzu ko dan na nai mi yafiyar ubangiji na” ta kara rushewa da wani kuka mai tsuma rai.


“Tabbas Abba da Umma na cancanci ko wane hukunci daga gareku wallahi tallahi bansan sanda ya nemeni ba, Abba kai kace komai ya ce nai masa nai masa da wannan damar ya ke samu ya ke duk abunda yaso dani.”


“Wai ubanwa kike magana akai? wa na ce kiwa biyayya a duniya? wannan wace masifa ce da jaraba zaki kwaso mun tsiya kuma ki nemi ki dora mun laifi? zaki fada ko sai na shake ki” ya mike a fusace.


“Wallahi Abba Yaya Arfan ne” “what?” Daddy ya furta da karfi, “wa kika ce yai miki ciki maimaita naji?” ta fashe da kuka “wallahi Daddy shi ne yai mun bantaba sanin wani namiji ba sai shi a rayuwata.”


Abba mikewa yai ya cakumota Umma ta bige masa hannu, “sakarmun yata karka lahantan ita” “Maryam banji wa kika ce ba maimaita naji?” “Wallahi Abba shi me yai mun yaya Arfan” “da gaske Arfan mijin yayarki Nafeesat shi yai miki wannan aika aikar?”


Daga masa kai kawai tayi tana kuka Umma ma kuka ta ke kamar zata shide saboda tashin hankali, ita dama jikinta ya bata tasan za a rina an saci zanin mahukaciya, kawai ji sukai luuuu Abba ya tafi ya zube ji kake tim kawai baki ya datse.


Ihu suka sa gaba dayansu saboda tsananin tashin hankalin da suke ciki da hanzari Doctor ya kira Nurse aka dauke shi akai emergency da shi hankalin kowa ya tashi.


Daddy ne yai dakin da Arfan ya ke yana kwance sambal kamar gawa har yanzu bai farfado ba, ya tura dakin Momy na gabansa tana ta hawaye wani mugun kallo ya jefeta da shi.


“Wallahi tallahi ko kaffara bazan ba sai na auri Maryam ko dan na dandanawa dan ki bakin cikin daya dandana mata ita da iyayenta da yan uwanta, kema kuma zaki dandaneshi kamar yadda nima nake dandana a yanzu.”


“Haba Alhaji da mai zanji kazo ka nai mun maganganun da suke barazana da kwakwalwata, ai na yarda ka aureta mai kuma yai saura yanzu? yaro na kwance rai a hannun Allah kasan me yake damunsa kasan me yake bukata?


To soyayya ce zata hallaka danka soyayya ce ta maida shi haka, san yarinyar da kai ma kake so.” Wani mari ya zabga mata da sai da ta kife.


“Na lura kema baki da hankali akwai abun da ke yawo a kwakwalwarki, bari kiji ko a zamanin jahilai na farko ba’a hada ya da kanwa a aura, sai dai idan baya tare da dayar ko mutuwa ko rabuwa ta har abada.


Ina so na sanar miki bisa san zuciya irin nasa da shedan ya kwadaita masa suffofinta, ya biyewa san ransa bisa yadda mahaifinta ya bashi goyon baya, ya yarda da shi da zuciya daya ya aminta da shi hakan yasa yaiwa Maryam kanwar matarsa Nafeesat ciki.”


“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Alhaji kasan mai kake fada kuwa, wayyo Allah na shi ga ukuna! ina zamu kai wannan abun kunyar, Ya ya Nafeesat baiwar Allah zata ji yarinyar da ta ke fama da lalurori ga ciki.”


“Shi ai bai san da haka ba yayi abun da yai masa kyau, saboda haka wallahi ko santa zai kashe shi ba zai aureta ba ni zan aureta wallahi.”


“Haba Alhaji waya ke ta zancen aure yanzu, tayaya zaka auri matar da danka ya shi ga gonarta har yai wasa a ciki, da wane ido zaka kalleta ka kalli dan naka? ana barin halal ai ko dan kunya Alhaji.”


Kwankwasa kofar ne ya katse ta ta bude Mama ce ta shigo suka gaisa cikin kunya irin ta surukai, “au Alhaji ashe kama warke ina ta zulumi naji shiru ina ta kiran wayoyin ku ba amsa, ta Hajiya kuma a kashe shi ne na biyo sahu tun safe naji shiru basu koma ba.”


*******************




“Haule akwai gagarumar matsala! yarki tana cikin gagarumin hatsari! tana tsakanin mutuwa da rayuwa, saboda cikin hatsarin da take kayan dubana sun kone.



Ba abun da zan ce dake a yanzu zan gaya miki magana ta gaskiya domin Allah, kije ki nemi manyan malamai masana Allah da sirrin alkur’ani su dage dayi miki addu’a akan wannan lamarin saboda warwarewar lamarin.”


Tana kuka ta ce “Malam ka taimakamun kai ma ai malami ne naga, ina zanje gaka? wallahi tun da aka kai yarinyar nan nake mugayen mafarkai akanta na rasa ya zanyi da raina.


Zancen kishiya ta nazo maka saboda ta mallake Malam amma raishe ya juye da mujiya wallahi ina cikin wani hali mai matukar muni.


Dama zaman kai na nake yanzu tun da mun rabu da Malam, kawai ya rufan asiri ne na rufawa kai na, dan Allah Malam ka taimakamun.”


“Ke! dakata, naga alamar baki da hankali, nagaya miki magana ta domin Allah amma kin ki ji, abun da nakeso da ke ki wuce ki ban waje tun da nagaya miki gaskiya naga baki yarda ba,karki janyon fushin aljanu yanzu.”


Zata kara magana ya daka mata tsawa dan dole ta fito tana sharar kwalla.


Indo na asibiti tana samun kulawa yadda ya kamata satin ta biyu, a yau su Maimuna suka zo mata sallama zasu daga Malaysia.


Malam yaji dadi ya dinga sa musu albarka sukai sallama da Umma suna kuka, haka Bello ya rukota sun burge Malam sosai sai da yaji daci a ransa, Nauwara ce ta fado masa ko a wane hali ta ke?


Dan yana yawan mafarki da ita yadda ta ke rokonsa gafara da yazo ya ceceta rabin jikinta na cin wuta, ya dan matse kwalla yana daga musu hannu har suka wuce, gaba daya ya zauna a wajen jagwaf ya nutsa kogin tunani.


Yana budewa Alhaji Ghali ne ya dawo a lokacin da bai taba tunani ba dan ya dawo da wuri sosai, yaga alamun rashin gaskiya daga gareshi karara amma bai kawo komai ba ya wuce ciki.


Ya fara leka dakunan kasan amma bai ga kowa ba, yaje bakin dakin ta har ya tura ko mai kuma ya tuna sai ya fasa ya wuce dakin su ya cire kayansa.


Sai da gabansa yai muguwar faduwa dan sunyi da wajewa ba wanda zai kara cin amanar kowa tsakaninsu, shi ya sa ya ke taka tsantsan yasan lokacin da ya ke kawo mazansa.


“Haba Alhaji wannan wane irin abu ne? wato zargina kake shi ya sa kake leka dakuna? to ka manta ai baka hau sama ba sai kai azama ka hau ka duba ko na boye wani a can.”


“Haba Baby mai yasa kake haka dan Allah! kawai dan na laika dakuna ba wani abu bane, na kwana biyu ban duba ba ne shi ya sa kuma sai na tuna ka hanani ganin yarinyar nan shi ne kawai nafi two weeks ban ga gilmawarta ba.


Wani tukukin kishi ne ya tasowa Baby Chakwai “eh lallai ka ce kana kewar ta kawai to sai ka je ai ka ganta ina ga hakan zai fi ma” fuuu ya wuce.


Da gudu ya bishi yana lallashi da lallabawa sannan ya dawo suka tsunduma duniyar masha’arsu wadda basa gajiya da ita.


Kwana uku a tsakani Alhaji Ghali na kewar Nauwara dan yana masifar sha’awarta a yanzu amma bai san ta ina zai fara ba da safe ya shirya yai wajen malaminsa.


Ya sanar masa bukatarsa yai binkice kawai ya gyada kai dan tabbas yasan yai wa Baby Chakwai aiki mai zafi akan sa amma zai ba shi dama shi ma dan ya dan dama.


Ya gyara zama “abun da zai faru shi ne zan baka wani magani wanda zaka din ga barbada masa a duk lokacin daka bukaci zuwa wajen ta shi kuma zai zube yai ta bacci har sai ka tashe shi.”


Yaji dadi yai farin ciki sosai ya zube masa kudade masu yawa ya taho yana murna da farin ciki.


Bokan nasu ne ya sheke da dariya dan ba’a kira shi Malam ba, “mahaukatan banza da wofi duk kan ku wajena kuke zuwa kowa bai san kowa na zuwa ba, kuma ina nan ina gwara kan ku dan ta kusa kare muku asirin ku ya kusa tonuwa.


Saboda haka gwara na tarkata ya nawa ya nawa na gudu kafin ta kwabe asirina ya tonu, hhhhhh! na samu abun da na samu kuma na dau fansa burina ya cika, gwara na bar nan naje nai sabuwar rayuwa dan na zama hamshakin mai kudi yanzu.”


Nan ya dinga wasu surutai yana karanta dalasimai sai ga wani narkeken aljani ya bayyana ya sheke da dariya mai tsanani, “hhhhhh! ya kai aljanu dan mulmuli inaso ka tarwatsa komai burina ya cika a yanzu.


Story continues below

Saboda wulakancin da Alhaji Ghali yai mun a duniya yanzu lokacin daukar fansa nai, hakika kai hadimi ne na gaske komai ya tafi yadda nakeso, na sa shi a hanyar da ba zai iya bullewa ba, ina so ka wargaza duk wani aiki da kai musu.”


“Hhhhhh! Ya sheke da dariya da muryarsa mara dadin amo, tabbas bukatar ka ta gama biya saura kadan ya girbi abun da ya shuka. Hhhhhh!”


Hhhhhhhhh! ya sheke da dariya “a yau burina ya gama cika a duniya, na dauki fansar jinin dana da matata da Alhaji Ghali yai silar salwantar su a duniya, sai kuma ya fashe da kuka ya mike ya sake komawa cikin bukkarsa yana hada kayansa.


_Waye wannan bokan wai?_


Ainihin sunansa Malam Habu, mutum ne mai ilimi sosai irin kararun kolawan nan na Maiduguri asalinsa dan Maiduguri ne, yakin Boko Haram ya sa suka gudo suka dawo Kano, suna wannan yawon Allah ya hadasu da Alhaji Ghali ya daukesu ya kai su gidan. Ya bawa Malam Habu aikin gadi ya basu boys quarters a gidan suke zaune, yaron Malam Habu sunan sa Khalil yaro ne fari kyakykyawa mai tsananin kyau, shekarunsa ba zasu wuce shekara goma sha biyu ba, zama suke cikin jin dadi dan Alhaji Ghali na wadatasu dama shi mutum nai mai tsananin kyauta, tun san da ya gamu dasu Allah ya dora masa kwadayin san Khalil duk da ba wani shi be masa ya ke ba, amma sai da Alhaji Ghali ya ja shi zuwa wajen sa har ta kai yana neman ya taya shi kwana, ana haka ya jashi don su kwana tare a daren yai masa fyade, wanda sanadin wannan fyaden Khalil ya rasa rayuwarsa abun da ya daga hankalin iyayensa musamman da suka ga gawarsa, anan suka shaida abun da ya faru, suka tuhume shi amma fafur yace baisan zancen ba, sunyi kokarin kai kara wajen yan sanda su kai musu bayanin yadda abun ya faru, tun da ficewa yai ya bar shi mahaifiyarsa taje taso shi taga gawarasa da danyen aikin da akaiwa Khalil, amma saboda kudi basu da wanda zai tsaya musu aka ce ba shi bane, kuma tabbas sunji ihunsa amma basu kawo shi bane a daren, kememe kudi su kai aiki aka rufe maganar,wannan bacin ran yasa Mahaifiyar Khalil ta hadiyi zuciya ta mutu, tashin hankalin daya shi ga ba kadan bane, a karshe ya rasa ta hanyar da zai dau fansa shi ne yai wannan tunanin, saboda yasan auren jisi kadai idan Alhaji Ghali yai shi zai tona masa asiri, wannan dalili yasa yai badda kama ya fara wuridi ya nemo aljani mulmuli, shi ne silar fara bokancin sa wanda ya samu kudi sosai daga garesu wannan shi ne silar bokancin sa kuma ya dau fansa wannan kena._





****************




Ba inda ya tsaya sai kofar gidan su Laila ya ai ka aka kirawo ta, sai da taja ajinta da kyar ta fito dan ta san jarabarsa ce ta motsa ya biyota, tana mota tana kallon ikon Allah ganin yadda ya ke lallabata wai ta shi ga mota ko wace yar iska ce wannan kuma?


Bakin ciki ya cika ta saboda sam bata gane Laila ba kishi ya rufe idon, “wallahi Lawan ba ka da mutunci na shi ga mota kai mun uban mai kuma? ka gama wulakantani a asibiti saboda ba ka sona kai mun sakin wulakanci yanzu kuma kazo ka daukeni kaje ka caccaka ko? to wallahi ba inda zanje inji ma da wahalar cikin da ke jikina da mai zanji?”


Habawa tana mota sam bata jin mai ta ke fada taga dai suna magana ana nuna mota, da zuciya ta debeta ta fito tana zuwa ba tai wata wata ba ta shake wuyan Laila ta gaura mata mari wanda sai da taga taurari, “dan uban ki wacece ke?”


Zata kuma magana ita ma taji saukar wani marin a kuncin ta, “uwar ki ce ita, matata ce ita mai yanci bake ba wawiya shashasha” ya kama Laila na ihu ya danna a mota ya sawa motar key.


Doctor Saudat duk ta haukace kamar ba wayayyi ba abun yai mata ciwo, bata san iskancin Lawan ya kai haka ba dole ta kara shiri, bakaken maganganu ta ke gaya masa bai ce mata uffan ba ya damkota har motar ta ya watsa, “ta kije zanzo na sameki wallahi sai kin raina kanki dan kan ki zaki tonawa asiri sakaryar banza kece kesan rufin asiri.”


Idan kika kuma bibiyata da matata wallahi sai kin raina kanki, matatace Laila mutu ka raba tsakanina da ita ba mai jure halina sai Laila ita kadai tasan waye ni, kin gane?”


Wani hawaye nai ya gangaro mata mai kuna, dama wadda taga yana kusanta a asibiti ce amma sam bata gane taba kodan kishi ya rufe mata ido, Allah yasa bata gane ta ba ita gudun tonuwar asirinta dan Doctor dan fillo ya matsa mata yanzu kuma bata so yasan tai aure.


Tabbas ta biyewa san ranta ga shi tun ba’a je ko ina ba ta fara nadama, zata jure komai ban da duka daga namiji dan wallahi ta tsani namiji mai duka, duk da tasan yana duka amma bata san abun ya kai haka ba, duk da ta aure shi dan san ranta da kuma niyyar daukar fansa, dan haka dole tai kokari ta dawo da shi hanya, dole shi ma tasa a tara masa gajiya dan bai mari banza ba, tana hawayen nadamar auren Lawan taja motar ta dan shi har ya bar wajen.


Kuka Laila ta ke yana rarrashin ta da ke yasan lagonta nan da nan ya shawo kanta, lafiya kalau suka isa Taheer dan yayi kewar ta anan suka wuni dan ya maida ta dakin ta, amma tai rantsuwa bazata koma gidan ba sai dai ya kama mata gida.


Ya ce bai da kudi shi sam, “to shi ke nan zan kama da kaina” farin ciki ya lullube shi ya samu inda zai sa Hajiyan sa hankali kwance, “shi ke nan Laila ta shi ya sa nake kara kaunarki tayaya zan rayu ba ke, na amince kiyi yadda kike so ai ni naki nai, sai dare ya maida ta gida ta sanarwa kawunta ya maida ta dakin ta cike da tsananin murna da zakwadi, dan gaba daya jinta ta ke kamar akan kaya wannan zaman.


Ransa bai so ba sam amma ba shi da yadda zai saboda an riga an kwashe albarkar auren tun a titi, dole aure yaki dadi ba ganin mutuncin juna baya san wannan auren ko kadan, musamman yadda yaron ya zauna ya kalli tsabar idonsa ya din ga gaya masa maganganu saboda bai dauke shi da mutunci ba, yanzu kuma ya sake ta ba biko ba komai kuma wai ya dawo ya ce ya maida ta.


Duk da ya fuskanci laifin na Laila nai, dan ita ta ba shi dama duk abun da yake, shi ya sa ba’asan kabar yarinya har ta wuce minzalin aure ba kai mata ba karshe sai kayi nadama mara amfani, gashi saboda san ranta da tausayinta na rashin iyaye ya bar ta tayi karatu mai zurfi har ta fara aiki, wanda shi nai silar lalacewar ta da haduwar ta da wanda baya ganin mutuncin kowa baya jin kunyar kowa a hankali ya ce.


“Wato Laila na fuskanci ke kike bawa Lawan damar wulakantamu a duk san da yaso, duk diban albarkar da kuke wallahi idon mutane na kan ku duk abun da kuke ana kallonku idon mutane na kan ku, tun da aka fara wannan auren naku ba kwanciyar hankali a cikinsa ba albarka sam.


Ta fashe da kuka “wallahi kawu ka tsani Lawan ni nasan baka kaunarsa ko kadan, dan anga iyayena sun rasu shi ya sa ba’asan farin ciki na, yanzu mai yai kuma? ya ce ya maidani ai abun farin ciki nai” kuka take duk jikin kawu yai sanyi da tsananin mamaki ya ke kallonta yanda lokaci daya ta ke furta masa haka saboda san namiji.


“Shi ke nan Laila kiyi shiru ke amanace a wajena, bazan ci amanar dan uwana ba shi ya sa nake kulawa da lamarinki, amma ina so ki sani wallahi sai kin yi nadamar auren Lawan ko da a gaba ne wallahi!” Ransa ya sosu ya mike ya fice ya bar gidan.



Jikin Mama yai sanyi ta rungumeta ita ma ta fara hawaye sannan ta ce “wai Hajiya mai ya ke faruwa dan Allah? ya kamata ki mun bayani kin zauna kinata kuka, dan Allah Hajiya ki mun bayani ga shi dai na sameku lafiya waye to a gadon ba lafiya?”


Nuna mata kawai tai da hannu da sauri ta riketa suka karasa bakin gadon salati tai ta sanar da ubangiji ganin Arfan kwance kamar gawa magashiyan yana jan numfashi da kyar.


Innalillahi wa’inna’ilaihir raji’un! lafiya Hajiya? Mai kuma ya same shi haka? Kuka ta kuma rushewa da shi dan bata san ta ina zata farai mata bayani ba.


Alhaji nai ya ce “ba wata matsala ba ce Hajiya zazzabi nai mai zafi ya kamashi shi nai ta ke ta kuka na rarrasheta amma ta daga hankalinta.”


“Haba Hajiya bai kamata ki daga hankalinki har haka ba, kiyi hakuri kiyi shiru haka dan Allah sai ki kara daga mana hankali, ai alhamdulillah tun da ke kin warke shi ma ya warke.” Kukan ta hadiye ganin Alhaji ya samo mata mafita, sai watso tambayar data gigita shi kansa Daddy “yanzu ina ita Umman yaran da Alhaji da Maryam din?”


Wata sarkewa yai dan muguwar kunya ce ta kamashi, ganin sun mata shiru ta ce “ko sun tafi nai?” da kyar Momy ta daga mata kai ta nai mi waje ta zauna Daddy ya ce “a’a Hajiya ta shi zaki nasa driver ya maida ki tun da yana nan.


Saboda yanzu kin ga kin baro Nafeesat ita kadai sai masu jinya kuma tana bukatar kulawarki sosai a halin yanzu daure muje.”


Baza ta iya musu da shi ba saboda sirikinta nai akwai kunya tsakaninsu “ba matsala Alhaji Allah ya ba shi lafiya idan na dubata zuwa dare zan dawo naga jikin nasa.”


“A’a ki zauna dan Allah nima zan yi kokari nazo na ganku bakwa bukatar komai dai ko?” “A a wallahi akwai komai mungode Allah ya saka da alkhairi” ya fito yasa driver ya maida ta.


Nafeesa ta gaza nutsuwa saboda sam tunanin kanwarta ta ke da mijinta tun da Mama ta fita ta kasa sukuni, Allah kadai yasan abun da ke damunta ba abun da ta ke so irin ganinsu amma bata san ta tambayi Mama tayi laifi.


Daddy nai ya karasa dakin, sun samu sun shawo kan matsalar hawan jini nai yai mugun kamashi wanda Allah nai ya takaita bai kamu da paralyse ba.


Daddy nai ya kira Umma “Hajiya inaso miyi magana da ke tun da cikin nan karami nai, kuma a kansa Alhaji ya ke neman shi ga wani hali hasali nayi tunani tarin abun kunya ya yiwa wannan cikin yawa.


Duk da har ga Allah banso haka ba amma dole ce, mai zai hana a zubar da cikin kowa ma ya huta ita ma yarinyar ta samu nutsuwa, wallahi Hajiya nayi alkawari tun da Allah bai haramta mun auren ta ba zan aureta.”


Story continues below

Wani kallo tai masa na baka da hankali ma amma ta share “haka nai Alhaji amma da hankalina da wayo na ba zan taba ba da goyon baya ba ai wannan abu, hasalima ba wanda ya isa ya taba wannan cikin sai ikon Allah.


Maganar aurenka kuma in dai kai alkawarin aurenta cikin wannan halin to ba fashi, tabbas ba ta da mijin da ya fika na yarda na amince fatana Allah ya sa albarka a lamarin, zan kai ta gidan kanwata idan ta haihu sai a daura auren a ranar.”


Duk da bai so maganganunta ba amma haka ya maze tun da sirikarsa ce ya ya iya, amma tarin kunya da abun kunyar da za’ai ya ke tunani musamman shi yadda ya ke a idon jama’a a ce dansa nai yai wannan katobarar kuma ya auri matar.


“Shi ke nan Hajiya yanzu meye abun yi yanzu abokiyar zamanki tazo kunyar sanar da ita mai ya faru yasa muka ce kun koma gida.”


“Ai Alhaji dole ta sani dan abokin kuka ba’a boye masa mutuwa, hasalima Maryam yar ta ce dan tafi shakuwa da ita a kaina, saboda haka dole na sanar mata komai musamman da mijinta ba lafiya dole ta ba shi kulawa dan yanzu haka tafiya zami sai na turota tai jinyarsa.”


Bari nasa driver ya kai ki Hajiya yanzu ya dawo daga kai Hajiyan dama” “a’a bar shi nagode wallahi zamu hau adaidaita bana bukata Alhaji. “


Gaba daya yai dana sanin gaya mata a zubar da cikin yadda ta ke fadar maganganu, lallai ya yarda mai hakuri bai iya fushi ba duk hakurin ta da ake fada tana da shi, gashi an kureta tayi abun da bai tunani ba, “shi ke nan Hajiya Allah ya sawake” ya juya ya tafi dan yaga bazata ta tankwaru ba a lokacin tayi fushi.


Kamo hannun Maryam tai “zo muje kema munafuka ina nan zuwa kan ki wallahi kema sai kin girbe abun da kika shuka, kuma aurenki da Alhaji Kamal ba fashi dan idan ba shi ba banga mai aurenki ba a yanzu.”


Tana kuka suna tafiya “dena mun kuka karki taran jama’a dan kan ki zaki tonawa asiri, kuma wallahi kan ki kika cuta shi namiji ba shi da abun kunya in gaya miki ke ya cuta kika cuci kan ki, kuma wallahi kin dima asara saboda ke karya ce ki rasa wa zaki bi sai mijin yayarki mai tsananin sanki.”


Fashewa tai da wani razannan kuka wani wawan mari Umma ta bata, “baki da hankali nai ko mai ni zakiwa wannan kukan, to wallahi baki ga komai ba ni da ke wallahi sai ido dan kin zubar da kimar da na ke kallon ki da ita a matsayina na mahaifiyarki.”


A haka suka samu napep suka hau haka ta din ga kuka har suka isa asibitin, “wallahi Maryam idan baki rufa mun baki ba sai na tara miki gajiya yanzu anan wajen, dan wallahi ban ga dalilin kuka ba bayan ke kika janyowa kan ki, tun da ba fyade yai miki ba da yardar ki akai, da fyade nai da tuni ai kowa ya sani an dau mataki, amma kin biye masa kun gama watsewa kun samo albarkar iskanci zaki tasani a gaba da kuka.


To wallahi kul ahir dinki ki rufe mun baki kafin ranki yai mummunan baci, hadiye kukan tai ta bita suka shi ga dakin suna zaune sun yi jugum jugum su kai sallama da fara’a suka amsa suka karasa ciki, Mama ce ta kurawa Maryam ido sai tai kuma zumbur ta mike.



**********************




Malam ya zurfafa tunani saboda kullum mafarki ya ke da Nauwara tana kuka tana naiman afuwarsa akan ya taimaka mata bari guda nata nata ci da wuta “ya Allah!” ya furta.


Tabbas akwai matsala ya kamata ya ajiye fushin da ya ke da diyar tasa zuwa yanzu tun da tana da cikakken hakki akansa, duk da ta bata masa amma da kuruciya akanta da kuma zugar mahaifiyarta.


Shi ya sa manzon Allah (s.a.w) ya ce ku zabawa yayayenku Uwa ta gari, domin Uwa ita ce aljannar duniya adduniya mata’un wa khari mata’uha Almar’attusalihatun amma sam ba’a duba da wannan.


Daga aurensa da Indo ko shekara basuyi ba amma har ya sanja saboda kwanciyar hankali da ladabi da biyayya, kowa sai yai mamakin yadda yai kiba tabbas Uwa wani bigirece a rayuwar iyalanta, duk yayin da ta kasance salaha sai iyalan su zama salahai ,yayin da ta kasance mai munananan hali haka iyalanta su ke koyi da shi.


Musamman yara mata photo copy nai na Uwa idan sun baci kece idan sun lalace kece, duk da yaran yanzu ka haifesu nai baka haifu halinsu ba amma tabbas Indo ita ta bada gudunmawa wajen lalacewar Nauwara.


Tabbas yayi sakaci tun farko amma ya ya iya dole yaje ya binkici halin da diyarsa ta ke ciki kodan ya samu tarbiyyarta ta gyaru, duk da yayi sake ice tun yana danye ake tankwara shi amma yasan har ga Allah yayi yadda zai iya yana tufka nai ana warwarewa.


Mikewa yai ya koma dakin da Indo ta ke dan yaga lafiyarta yana shi ga ya tarar har tayi bacci, dan an sanja mata daki yanzu ita kadaice a dakin da ta ke shi ya sa har ya samu ya ke zuwa wajenta tare suke kwana dan bai sanarwa yan uwanta ba.


A fujajan ta dumfari gidan Indo amma sai mai ba kowa sai Bilal da ya ke dakinsa na soro a kwance yana bacci, ta hau bugawa baji ba gani fitowa yai ya gaisheta “ai Inna basa nan suna asibiti da Ummata ba lafiya.”


Cikin kuka ta ce “ina Malam?” “ai Malam shi nai a wajenta ya hana kowa zama da ita, Yaya Maimuna ma tayi tayi amma yaki, gashi yanzu har sunnbar kasar ma da mijinta” wani kuka ta kuma fashewa da shi ta zube a wajen tana burgima.


“Wallahi na cuci kai na na cuci yata tun da ni na dorata a wannan turbar, gashi wata bakwai ko sawunta ban ganiba, duk wanda yaje an hanashi shi ga wai basa nan basa kasar bayan karya nai” ta rushe da kuka ta mike ta fice.


Tama rasa ina zata dumfara saboda tsananin tashin hankali, sai sannan Zuwaira ta fado mata a ranta dan tun da ta dawo daga wajen Malam sati biyu kenan ta ke zarya a hanyar gidan Nauwara amma da duka sojojin ke korota.


A yau nai ta labe a kofar wani gida kuma tana kallo Alhaji Ghali ya fita dan sai da ma ya tsaya yai hira da masu gadi sannan ya wuce ta gan shi sosai wannan shi nai abun da ya daga mata hankali.


Dan yana fita ba jimawa taga wasu maza sun shi ga gidan to mai hakan ke nufi ance musu ba kowa abun da ya kara daga hankalinta ke nan.


Gidan Zuwaira ta shi ga suna tsakar gida da mijinta da kishiyarta ko sallama batai ba ta afka, tana “Zuwaira! Zuwaira! fito wallahi yau dubunki ta cika wallahi, sai na fasa kwai kuma duk abun da kika dauka nawa wallahi sai kin dawon da shi.”


Da sauri ta mike “haba kawata ai ba ajin kan mu muje daki kiyi hakuri waya bato miki rai yau?” wata harara ta dalla mata “munafuka ai ba kawance tsakaninmu da ke kuma wallahi anan zan fada kowa yaji.”


Mijinta nai ya mike “lafiya Haule mai ya faru?” “Malam Mato Zubaida ta cuceni ta kai ni ta baro ni, kuma Allah sai yai mun hisabi da ita” jin haka ya ce “samu waje ki nutsu ki zauna miyi magana, kiyi hakuri komai zai zo karshe zan miki adalci.”


Cikin zubaida nai ya duri ruwa “dan girman Allah kiyi hakuri wallahi na tuba in dai sarkar dana sata ce gata” ta bazama daki mamaki nai ya kashe su a zaune ga ba dayansu.



Alhaji Ghali ya koma gida cike da farin ciki amma bai nuna masa ba ya cigaba da biye masa, duk sanda yai kokarin zuwa dakinta sai yaji shi gam ga shi ya rasa ina ragowar keys din su kai, bai san Baby Chakwai ya kwashe su ba.


Kullum yana zuwa ya dubata duk da ta tsaneshi tsana mai yawa, amma tana cin abincin da ya ke kawo mata, dan kullum sai ya kawo mata abinci mai rai da motsi da kaji da fresh milk, dan ta gama fuskantar ciki nai da ita shi ya sa ta ke karba tana cika cikinta.


Saboda rabonta da al’ada tun lokacin da Alhaji Ghali ya kusanceta bata kara ganin al’adarta ba, ga yadda take yawan amai da yawan jin yunwa tana cin abinci sosai shi ya sa ta ke cin abun da ya kawo mata.


Bayan sati uku ta warke sarai din kin ya warke dama bukatarsa ke nan shi ya sa ya ke kula da ita da kansa, saboda yadda Doctor din su yai masa takara 2 weeks ya ce a barta ta warke amma shi 3 weeks ya bata dan ya barje guminsa.


Dan sam baya jin dadin kowa da komai a yanzu ba abun da ya ke so sai ya wuni a kanta, shi ya sa ya tama mata yau ya bakantawa Alhaji Ghali rai yau dan ya dade bai dawo ba ya gwangwaje a jikinta.


_(Wa’iyazubillah! Allah ya Allah! kai mana tsari da wannan mummunan aikin, Allah ka karemu da san zuciya ka tsaremu ka tsare imanin mu, na tabbatar banda kwadayi da san zuciya tabbas da Nauwara bata fada wannan masifar ba, wallahi mata mu hankalta mu cire kwadayi da san zuciya da burin auren kudi, dan baka san tayaya namiji ma ya tara kudin ba, wallahi tallahi irin wannan tana faruwa life a gaske duk da na dan sanja wani abu na kara wani, amma wallahi yana faruwa, kuma san zuciya ke kai mu ga halaka, yanzu meye amfanin auren da tai mai ta tsinta a kudin, fatan mu miyi addu’a Allah ya bamu mai zuciya ba mai dukiya ba, dan wallahi namiji mai zuciya shi ne miji, ina kuke matan masu kudin naira dubu gagararsu ta ke, wayanda aka sakarwa kuma mijin gagarar ganinsa suke, daga haka shi ke nan mace ta fada lesbian ko neman maza, ya ilahil alamina ina zamu kai wannan, musamman yan matan yanzu masu dogon buri, wallahi ku cire ranku daga buri ku shi ga hankalinku, ku tsaya matsayin da Allah ya ajiye ku, dan wallahi idan ma kayi da ce ka samu yadda kake so to tabbas wulakancin danginsa ma ya isheka Allah ya tsaremu ya tsare imanin mu dan wannan rayuwar wallahi sai addu’a wata yar tunasarwa ce, musamman da ya kasance 80% cikin hundred na novel dina gaskiya nai Allah ka kiyayemu.)_


Ya siyo mata abinda yaga tafi ci chips da kwai sannan ya hado mata da fresh milk mai masifar sanyi, sai da taci ta ko shi ya bijiro mata da maganganu marasa dadi da rashin dadin sauraro masu barazanar tarwatsa zuciya.


“Kin ga Nauwara bafa zan miki dole ba ba zan takuraki ba amma abun da nakeso ki sani haka zaki ta rayuwa a wannan gidan a wannan halin dan ba mai cetonki.


Story continues below

Kuma abincin da nake kawo miki nadena ba ke ba ci ba sha a gidan nan haka zaki mutu ki rube ba wanda ya sani, kuma sai na sa an kashe iyayenki an batar dasu dan kin san cewa ina da duk wata alfarma a duniya.”


Kuka tasa mai tsuma rai “kayi hakuri dan Allah zan maka koma mene in dai zaka bar mun iyayena a raye, ina kaunar mahaifina ina so na ganshi na nemi yafiyarsa kafin rai na ya bar gangar jikina” ta rushe da kuka.


“Hhhhhh! kin wa kan ki gata kin ceto iyayenki, a yanzu abun da nakeso da ke shi ne zan din ga zuwa a duk san da na bukace ki a duk san da naga dama ina biyan bukatata, sannan bana san ihu ko musu ko nuna gajiyawa” daga masa kai kawai tai saboda tsananin kuka da ta ke.


Bai wata wata ba ya cire mata kaya tana kuka tana komai ya tsurawa kirjinta ido sun dau hankalinsa yan kanana a tsaye ya cafkesu ya din ga lailaya su ya tsotse tas cikin salon mugunta dan bala’in zafi ta ke ji hawaye kawai ta ke gaba daya jikin ta rawa ya ke.


Nan ya juyata ya hau kanta ya fara kokarin aiwatar da nufinsa wanda ta saki wata muguwar kara ta shide saboda azaba, dif kuma ta dauke wuta shi ko ya samu hanya ya fara aikin sa hankali kwance yana ihu yana gurnani kamar wani zaki.





****************





Lawan shirye-shirye ya ke gadan gadan tsakaninsa da Allah, abokansa mamaki suke yanzu mutumin da mace daya ma ya kasa iya control din fushin sa a kanta, amma shi ne ya ke kokarin yin mata uku, kuma babban abun mamakin ban da Ummi ba wata wadda ya zabo da za’ace kamila, gwara ma Laila akan wannan uwar matar.


Shi ko dariya ma suke bashi dan basu san daga kan ta ya rufe kofa ba, dan shi yayi hudu rigis kuma dukkansu ban da Ummi duk su suka nace masa, saboda haka shi bai dauki matsalarsu gagaruma ba ko wacce yar iska zai iya da ita.


An daura auren Lawan da Hajiya Santalous, auren da ya hada manyan yan Kano to Jidda gogaggu wayayyu, wayanda suke ji da kudi duniya ke yi dasu, an zubar da naira mai sunan naira anyi daurin aure anyi walima, sun kuma hada zafaffiyar dinner da daddare.


Ita ko Laila tun washe gari ta je ta kwashe kayanta, lokacin Ummi uwar jaraba bata nan sai yaranta da suke jiran gidan, dan ita tun da ya furta aure ta haukace ta daga hankalinta bana nan bata can, ba ta wannan gidan bata wannan layin, masu bata shawarar arziki sun fi yawa amma sam ta kasa kwantar da hankalinta.


Gidan ta ta kai kayan ta ajiye dama ba yan haya sun tashi ba dadewa sun yi gidan kansu, gidan mahaifinta nai bayan ya mutu ta gaje shi suka ajiye kayan dan jibi zata tare, ta gaji da zama ba Lawan a kusa da ita.


Shi ko Lawan bayan an daura aure da yamma gidan Saudat ya nufa dan ya huta, kafin zuwa dare a taxi l dinner dan ya gaji, yasanta sarkin yawo bama lallai tana nan ba agogo sarkin aiki.


Yana zuwa ya bude gate abun da ya bashi mamaki shi nai hango motar da yai, amma ya da ke hankalinsa kwance ya shi ga gidan, dan yau Allah nai ya tona mata asiri Allah nai ya kamata.


Gaba daya ta rikice ta diririce shi ki hankalinsa kwance ya ke gyara kwanciya, “haba Saudat ya kamata izuwa yanzu ki shi amince mi aure,” daidai lokacin da ya shigo dakin ihu ta saka “wayyo Allah na shi ga uku na dan Allah kayi hakur ta fashe da kuka.


Gaba daya idonsa ya gama rinewa “Saudat iskancin ya kai a gadon da muke raya sunna ki kawon gardi, dan iska nai ni cikakke amma wadda ta amince nake nema, bantaba bin matar aure ba, amma da aurena ki kai zina da wani ko ina zuwa.”


Shi ko doctor dan fillo gaba daya ya shi ga tashin hankali, duk da basabon abu bane bin matan aure a wajensa, a gadon asibiti ma kwakule mata ya ke idan yana dubasu, amma bai taba tunanin bin matan aure da ya ke wani abu ba nai sai yanzu da ya ga Lawan ya haukace.


Shi ko Lawan yana fita bai zame ko ina ba sai kitchen inda ya tarar ta dora ruwan zafi a kettle ya dakko ya tunkaro dakin, yasa boxer din sa yasa vest yana kokarin sa wandonsa ya shigo ya daya ruwan ya kwara masa a gabansa Allah yaso yasa wando ya kelaye masa a cinya.


Wanda ita kan ta sai da ya kwarar mata a kafa lokaci daya su kai ihun azaba, wani ihun azaba ya saka ya zube a wajen, cikin zafin nama Lawan ya bishi da kutufo ta ko ina yai masa laga laga, bata taba sanin haka Lawan ya ke da karfi ba sai yau da yai fushi, ya jibgeshi san ransa, haka ya din ga jan shi kamar kayan wanki ya watsa shi waje ya watsa masa key din sa da kayansa, “ka kuma jira sammaci wallahi.”


Ya koma ciki jikinta kyarma ya ke yana rawa ga kafar ta na mata azaba “tabbas na tabbatar abun da ka shuka zaka girbe shi, amma Allah ya sani ban taba neman matar aure ba, amma tabbas aikin matan aure masifa nai Allah ka dai yasan da mazan da kike hulda kuma zaki ci ubanki.”


Gashin kan ta ya damka ya samo wani mayafinta ya daure mata kafafuwa, ya haye gado yana janta ya daure mayafin a jikin fanka, kan ta na kasa kafafuwan ta na sama ya din ga dukanta gaba daya ta fita hayyacinta ihu ta ke ba mai ceton ta duk ta gama fita hayyacinta.


Ya jona iron ya dau zafi ya nana mata a duwaiwakanta, sai da ta shide ga shi numfashin ta na barazar daukewa, ji tai gwara ya kashe ta da wannan tsananin azaba da ya ke gana mata, a karshe ya dakko yaji ya jajjaga attaruhu ya hada da citta ya hadesu waje guda, sannan gwaleta tana ihu yana kan gado har yanzu bai kwance ta ba ya gumbuda mata wata kara tai da ta sume a wajen.


Wata ajiyar zuciya ya saki sannan ya kwance ta ya yasar da ita a kasa ya debi duk wani abu da yasan zai bukata a gidan ya fice yana huci yana fita su kai ki cubus da……


“Maryam mai ya sameki haka kike kuka mai ya faru? Dubi yadda fuskarki duk ta kumbura sundum, ice ko dai lafiya gaba daya kun dagan hankali na rasa gane meke faruwa?


Naje asibiti amma ban gan kuba hasali na kasa gane me ake boyewa?’ Umma ce ta ce “Alhaji nai fa ba lafiya ta ke ta wannan kukan mun taho kawai ya yanke jiki ya fadi ashe hawan jini nai.”


Salati suka kama dukansu Mama ta ce “dama Alhaji na da hawan jini tsahon shekarun auren mu ban taba sani ba tun saurayi da budurawa? innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un!” Nafeesat ko kuka ta fashe da shi .


Tun dazu ta ke san tayi kukan dama abun ya gagara ba dalili amma yanzu ta samu dalilin yi, ta din ga kuka har da sheshsheka gaba daya ta basu tausayi dan ita Mama ta san kukan rashin mijinta ta ke da rashin kulawarsa gareta .


Mama ce ta ce “gaskiya ban yarda da wannan boye boyen ba tabbas akwai lauje cikin nadi, da fari Uwa ta fara daga bisani Uba ya dauka da naje na tarar da dan a gadon asibiti yanzu kuma mijin mu wai, me yake faruwa nai a gayan gaskiya?


Dan wallahi dama ni zuciyata tana zargi kala-kala akan wannan tarayyar ta auren Nafeesat, wallahi hankalina bai kwanta da wannan auren ba gaba daya bare yadda ake gudanar da zaman auren, ke mai kuke boyewa nai?” ta dakawa Nafeesat tsawa .


Gaba daya ta rikice ta fashe da kuka Mama ba sauki ta damko Nafeesat “wane munafinci kuke kullawa a cikin gidan naki har haka, dan wannan kulla kullar wallahi jikina ya bani daga gidan ki ta ke, dan mafarkin da nai jiya ba banza ba ke kuma zo nan.”


Ta damko Maryam kawai bin ta ta ke da kallo ta gwale idanuwanta ta kalli tafun hannunta “innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un!” ta fashe da kuka tana tafa hannaye kuka ta ke.


“Maryam yanzu zargin da na ke miki sai da ya tabbata zargin da na kewa mijin Nafeesat a kan ki ya tabbata ke nan, yanzu Maryam sakayyar da zakuyi mana ke nan ciki Maryam! ciki! ba tun yau na ke fusankantar halin da kike ciki ba.


Amma zargi na ke shi ya sa na ke hana alakar ki da wannan yaron dan ban yarda da shi ba, amma aka nunan iyaka ta to ga abun da na ke gudu ya faru dan ko kaffara ba zan ba shi yai miki ciki.


Kuka Nafeesat ta ke har da shidewa saboda kuka Maryam ma kukan ta ke gaba daya Mama fada ta ke kamar zata ari baki, Nafeesat ko har ta fara fita hayyacinta saboda kuka.


“Haba Nafeesat kiyi shiru mana” cewar Umma “komai yai zafi maganinsa Allah amma bai kamata ki ta kuka ba a wannan halin da kike ciki da kike karkashin kulawar likitoci.”


Story continues below

Cikin kuka ta ce “dan Allah Umma kar ki boyen komai ni kai na na fara zargin wani abu duk da har ga Allah bana zargin kanwata da cin amanata haka mijina, ina so ki gaya mun gaskiya dan girman Allah Umma da gaske Maryam ciki nai da ita wa yai mata dan wallahi ko kofar gida bata fita sai da ni.”


Umma tazo ta rungumeta ta fashe da kuka “tabbas Nafeesat sai hakuri dan Maryam da Arfan sunci amanarki sun zalunce ki sun munafinceki sun cutar da ke, sun hadu sun zaluncemu gaba daya Maryam dai ciki nai da ita kuma mijinki shi yai mata wannan ba abun boye-boye ba ne dan shi dan duma nai zai bayyana.”


Wani numfashi ta din ga fitarwa da kyar tana nishi da sauri Umma ta mike, “wayyo Allah! zoki duban ita Mama” gaba daya sun gigice cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa ta ke kiran Maryam.


Kafin ta karaso numfashin ta ya tsaya cak da gudu Maryam ta kwalla kara tai office din Doctor, wanda suka taho da sauri dauke ta su kai daga dakin suka sanja mata wani dakin nan ka shi ga kokarin ceto rayuwarta.


Abba ko da ya farka ya ga ba Umma ba almunta abun ya bata masa rai sosai tun yanzu ke nan iyalinsa sun fara juya masa baya saboda yarsa tayi cikin shege suna ganin laifinsa nai, to gaba kuma mai zai faru.


Daddy nai ya din ga kwantar masa sa hankali sosai sannan yasa ya kira masa sulaiman babban dansa, amma shi ba shi da hali shi ya sa bayayi da shi sam amma yanzu lokacinsa yazo dole ya nemeshi tun da ba shi da mai kula dashi.


Awa daya ya karaso hankalinsa a tashe ya zauna shi ya din ga jinyar mahaifin nasa shi da Abba, dan Momy tana wajen dan ta da har yau idan ya fara allura ake masa ta bacci ya koma saboda ba abun da ke bakin sai Maryam.


Satinsu biyu a asibitin Abba jiki ya warware matan ba wadda ta kara tako kafarta dubasu, dan suna cikin tashin hankali domin Nafeesat jiki yaki numfashi ma sai da oxygen Sulaiman ke kula da shi.


Kullum Daddy sai ya je yaga su Nafeesat dan hankalinta ba karamin tashin yai ba yadda yaga gaba daya na’ura ke sarrafata, har kuka sai da yai duk da zuwa yanzu hankalinsa ya fara tashi akan rashin lafiyar Arfan amma sam yaki nunawa.


Jikin Abba yai sauki yau aka sallameshi suka koma gida tun da ya shi ga gidan yake jin sam ba dadi, amma ya dake dan jikin nasa sai godiya dan yaso ya tabu maganarsa ma hardewa ta ke abun duniya ya ishe shi.


Arfan watan sa biyu a asibiti aka sallame shi suka koma gida amma bai normal ba su suka bukaci hakan, ya rame yai baki idan ba kyakykyawan sani kai masa ba bazaka taba tunanin cewa shi ba ne, dawowarsu gida ya tunkari mahaifinsa da maganar auren da ya ke so a daura masa da Maryam.


Wani mari Abba ya zabga masa wanda sai da yaga taurari “ashe baka da hankali Arfan? har yanzu baka san annabi ya faku ba, duk wannan wahalar da ka sha bata zame maka aya ba, ko kasan abun kunyar da ka jaza mana kayiwa Maryam ciki.”


“Alhamdulillah ya Allah! Allah nagodema ba abun da zai hanani auren Maryam a yanzu tun da tana dauke da cikina, naji dadi Abba” wani kallo yai masa “baka da hankali Arfan ka manta kana auren yayarta?” shi fa yama manta sai yanzu ya tuna “kuma ina so ka sani an riga anwa Maryam miji ko da baka auren yayarta ba kai ba ita kaji da lalurar da ke damunka.”


Cikin tashin hankali ya mike “tabbas na yarda Abba da gaske kai ma san Maryam kake, to wallahi bazan taba hakura na bar maka ita ba dai mu zuba ni da kai mai rabo ka samu, amma wallahi Maryam tawa ce ni kadai” sai kuma ya fara tari ya durkushe a wajen.






*******************





Sai ga Zubaida da dankareriyar sarkar gwal da bangles da komai ta kawo mata “gata nasan nayi kuskure ki yafemun kin san lefan da yawa ba’a ganewa, wallahi ban san zaki ganeba, kuma bani kadai bace Kulu ma ta dauki sarkar diamond, sai atamfofi da muka dauka da lesuna ni dai shi ka dai nasan na dauka.”


Cikin kuka Haule ta ce “ba wannan ya kawoni ba Malam Mato, Zubaida ita tai wa amaryarka asiri har yanzu ta ke ta bari, ita tai mata asiri ta ke zub da mugunyar ruwa, ita tai mata asiri kake jin ta na wari da hamami, kuma ita ta tunzura ni na aikata abun da na aikata a auren Malam da Indo har Malam ya sakeni ba wanda ya sani.


Ita ta aikeni nayo masa sata ana hidimar bikin nan dan kar yaiwa Maimuna kayan daki, shi nai ya kamani yai mun saki daya amma ba wanda ya sani.


Malam Mato Zubaida ita ce ta fara kai ni wajen Malam ita ta zugani na hana yata auren kowa sai mai kudi, ita ta zugani na lalata tarbiyyar yata ita ta bata tawa tarbiyyar har na bata yata ta” rushe da kuka.


Daga Malam Mato har amaryarsa an rasa mai magana dan gaba daya sun yi suman zaune suna mamaki! Zubaida ko duk ta tsure ta takure sai soshe-soshe ta ke kamar mai karzuwa tana hararar Haule tana kifta mata ido.


“Malam Zubaida ta sa na sai da komai nawa na dakina na bata kudin da zummar za’a dawo da hankalin Malam kai na ya mai dani dakina, da yadda yata zata samu zaman lafiya da mijinta ashe Malam kasheni taje ta ce ayi.


Mallakeni ta kai kudin akai mata ta din ga karbar kudi a hannuna sai da tasa na kadar da komai nawa, wallahi Zubaida kin zalunceni wallahi Allah ba zai barki ba sai yai mana hisabi, kin ci amanar kawance da aminta ashe kawancen yanzu ya zama masifa? Ashe kawa neman ganin bayan kawarta ta ke a wannan duniyar?”


Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un! Abun da Malam Mato ya furta kenan “tabbas Haule kin yi ganganci, gaba dayanku kun yi laifi mai girma amma ke nafi tausayawa kuma ki godewa Allah da ya ganar da ke gaskiya.


Kuma tabbas abun da ka shuka shi zaka girba a duniya Zubaida kin cuci kan ki kin zalunci kan ki, kin zalunci mutane da dama musamman wayanda suka amince miki, so uku kina sawa ana sakin mata a dakin su amma ban taba yarda ba sai yanzu, hasali har kanwarki kin kashewa aure saboda san zuciyarki amma muka gaza yarda.


Ba abun da zance da ke sai kije dan kan ki duniya ce tafi bagaruwa jima wanda baizo bama jiransa ta ke, ke kuma Haule ai kin ga izina kin ga sharrin kawaye ko? kin ga illar yadda da kawaye ko? ko yanzu kin ga izina saboda haka sai ki kiyaye, kije kita istighfari ki nemi yafiyar Malam sai Allah ya sassauta miki.


Ke kuma yau zaki girbi abun da kika shuka, tuni ta fara kuka tana ‘dan girman Allah Malam kayi hakuri wallahi na tuba wallahi bani kadai ba ce nake wannan aikin, wallahi nima zugar kawaye ce suka dorani a wannan hanyar amma na tuba ba zan kuma ba.”


Tun da kwayene sai ki koma gidan su ku zauna da su da saboda haka kije na sake ki saki uku dan bana fatan na bude idona naganki, kuma kwayar gero ban yarda ki dauka ba a gidan nan sai Haule tayi lissafin kayan ta an biyata masu binki ba shi a biyasu ragowar a baki kayanki.


Wani ihu ta zunduma na bakin ciki tai kan Haule da bugu, da gudu Amarya ta tare ta dan itama dama da nata haushin nan ta sauke fushin ta akan ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *