IN SO YAKI NE CHAPTER 16

IN SO YAKI NE CHAPTER 16

  A sulale take tafiya jikin ta na karkarwa, lab’e wa tayi a lungun da ya sada corridor da stairs tana lek’o su, duk abunda take yi idanuwan Ameer yana kanta. suna haɗa ido ya girgiza kai ya yi mata alamar waya da hannun sa a kunne, dafe goshin ta tayi da hannu ta ce a ranta “Kash!!! Me yasa ban yi tunanin hakan ba tun farko?” Kai ta jinjina wa Ameer alamar ta fahimci maganar sa,Da sauri ta juya zuwa d’akin tana duba inda zata samu waya don ita tun farfaɗowar ta bata da wata waya a hannu. A garin binciken ta d’aga bedspread kawai se ga wayar da Tasleem ta bata jiya haɗe da takardar sakin nan. D’aga wayar tayi tana bin shi da kallo sai lokacin ta tuna wayar da sauri ta danne power button don kunna wayar, gani take wayar bazata gama booting ba tsabar yanda jikin ta ke b’ari. Babu Numbar wani da ta sani a cikin gidan akayi Sa’a taga numbar Suraj a contacts an yi saving da Suraj Maleek. (Kasancewar wayar Muhseen ce). Hannu na b’ari tayi dialing bata ma lura da video call take yi ba har tana kara wa a kunne saida taji maganar sa sannan ta tsorita ta janye daga kunnen ta tana kallon screen ɗin wayar “Laylah????” Suraj ya k’ira sunanta da sigar tambaya da mamaki. Share gumin da ya karyo mata tayi sannan ta fara magana a gigice “Ssss…….suuu..r…. Suraaaaj!!! He is here! Ameer…..Ameer help he will…..” Maganarta sarkafe wa tayi karaf ɗaya taji bugun zuciyar ta yana k’aruwa hankalin ta ya kai k’ololuwa wajen tashi. __________ Tun da ya ga ta bayyana a fuskar wayar sa jikin shi ya bashi akwai matsala domin idanuwan ta sun shaida hakan, alamun ta ba na wanda ke cikin hayyacin sa bane. Nan da nan shima ya rasa natsuwar sa har rawa Muryar sa yake yace “What? What happened to Ameer?? Waye ya zo? Ki min maganar da zan fahimta gaba ɗaya bana gane Maganar ki Laylah!”. Da kyar ta iya yak’ar zuciyar ta dake neman datse mata numfashi kamar an jefo shi da kalmar sunan Sa’eed haka Suraj yaji, saida ya ji tamkar bashi da gab’ob’i, kasusuwan jikin sa kuwa tamkar an yi replacing b’argon sa da daskararriyar k’ank’ara, wani bazawarin murmushi ya sakar kafin ya sake maida duban sa gareta yace “Wanne irin wasa ne wannan ɗin? Laylah idan mafarki kike yi ki farka Sa’eed yana jail and……” Katse shi tayi tana kuka wannan karon “Suraj trust me Sa’eed yana nan cikin gidan nan kuma yana tare da Ameer, ban san yanda aka yi ya shigo ba ban kuma san yanda ya fito daga jail ba but i am sure about this that Sa’eed ne ke tsare da Ameer suraaaaj idan ya fahimci cewa da yara a gidan nan kuma ina cikin gidan na tabbata abunda zai aikata ba ƙaramin abu bane Please do something.” K’ara taji alamun takun ƙafa da sauri ta ruga zuwa k’ofar ta danna key tana haki Suraj ya lura tabbas rud’ewar nata ba na lafiya bane, ita kuma ganin ta isar da sak’on kawai ta ruga zuwa banɗaki inda yaran suke ta ja su a jiki suka yi jugum, muryar Iman kawai ke tashi don wasanta take hankali kwance Laylah ta rasa mafita, tsoro bai tashi kamata ba saida taji ana dukan k’ofar d’akin, ji take kamar ta tsiyaye fitsarin da ya cika marar ta a jikinta…….. Hayaniya ya jiyo hakan ya ɗauke kankalin shi daga video call ɗin da suke yi ya sa hannu yayi disconnecting call ɗin, da gudu wasu jami’an tsaro suke nufo inda suke hakan yasa Nurses da wasu marasa lafiya har ma da patient relatives suka dare gida biyu suna basu hanya shima Suraj hakan yayi, cikin rububi yaji wani na cewa “Wai prisoner patient ne yayi escaping daga asibitin nan yanzu haka zasu yi sealing hospital d’in ba shiga ba fita har sai sun kama shi”. Wani karairayewa zuciyar Suraj tayi bai san lokacin da ya furta sunan Sa’eed ba a fili daidai lokacin Habeeb ya dawo daga maida baby cikin d’akin nan. A birkice ya sanar da su yanda suka yi da Laylah dukkanin su babu wanda bai girgiza ba musanman ma da suka fahimci cewa they are stuck in the hospital domin kuwa babu fita ba shiga, Mubeenah, Khadijah da ma su ummi duka aka rasa mai rarrashin ɗan uwansa. Dialing numbar da Laylah ta k’ira shi yayi cikin rawar murya yace “Laylah…..listen to me, duk yanda za’a yi kada ki bari su fahimci kina wajen, na tabbata Sa’eed bazai cutar da Ameer ba cikin gaggawa, ba Ameer yake buƙata ba ni yake son gani a gaban sa sannan yasan yanzun nan ina zuwa bazan bari ya cutar da ɗan uwana da yarana ba, sadai duk abunda zai faru ya faru!” Tamkar yana ganin ta haka take gyad’a kai shi kuma da sauri ya nufi hanyar fita Habeeb na biye da shi, Mubeenah har ranta take jin yaran ta Ummi ta fara kwantar mata da hankali “Mubeenah, na tabbata yaran nan Laylah zata yi protecting d’in su with all her heart, kuma sannan Allah yana tare da su, ki daina kukan nan haka i’m za’a samu hanyar kub’utar da su, Khadijah ko maganar ma bata yi tayi imani a lokacin ko jinin jikinta baya gudana bata ma san tsaye take ba ko kuma a zaune….. __________ Da iya ƙarfin shi Sa’eed ya shak’e wuyan Ameer nan take ya rasa inda zai sa ransa, tun yana gani har ya soma daina ganin komai sai duhu, ganin Ameer ya daina ƙoƙarin kwatar kansa Sa’eed ya sake shi, nan da nan ya zabura yana ja da baya hannun shi riƙe da walking stick d’in shi saida yaji ya jingina da staircase sannan ya tsaya ya juya ya dubi tsayin benen sannan ya maida duban sa ga Sa’eed sai yace “Do your worst Sa’eed! But you will never succeed, ko da kuwa ka kashe ni ne na tabbata ƙarshen ka bazai yi kyau ba, domin ka gama kafirta, na tabbata tun ba yau ba Umma da Dad sun yi danasanin haihuwar d’a irin ka, na tabbata da ace ana rubuta halin ɗan adam a tafin hannun mahaifiyar sa da Umma bata yi rainon cikin ka ba I’m sure bazata bari ko kwana ɗaya tak kayi ba cikin mahaifar ta. Sa’eed where is the love? Ina soyayyar take? So ba hauka bane! Stop this madness ko zaka samu kayi kyakkyawar karshe Please” Kai Sa’eed ya kad’a yana wani irin murmushi na rashin imani kafin yace “Haven’t you heard one saying which says _Everything is fair in love and war_”?? Wannan shi nake yi! Just that wannan karon i am not doing it for love, i am avenging the insult Suraaaaj caused for me! Ka ɗauka abu ne mai sauk’i to live for 8 months inside that dark room without Mercy! ? Sai na fanshe watanni takwas ɗin da aka b’ata min na rayuwa ta…” Yana maganar Ameer idanuwan shi a kan ciwon da ke hannun Sa’eed ɗin. Tara ƙarfin shi yayi waje ɗaya tun ƙarfin shi ya chafko hannu ya dinga murza wa Sa’eed ya gigice nan take ya saki ƙara kafin ya zube ƙasa, ganin haka Ameer ya yi ƙoƙari ya mik’e da d’ingishinsa ya nufi stairs, har zai yi corner ya hango wannan k’aton mutumin Mayee yana ta faman dukan kofofin ɗaya bayan ɗaya, ya juya ƙasa kuma ya hango Sa’eed yana yunkurin tashi ya damk’e hannun nasa mai ciwon dake zubar da jini. Kafin ya maida duban sa ga Mayee yaji an fisgo shi da ƙarfin tsiya, cikin abunda bai fi kiftawar ido ba ya ganshi cikin d’akin Laylah, da sauri ta mayar da k’ofar ta rufe ta dannna lock jikinta na rawa ga uban zufa da ke bin fuskar ta sai goge shi take tana haki. Kallon ta kawai Ameer yake yana mamakin k’arfin hali irin nata, ruwa ta ɗauka da bottle d’in duk ta kafa shi a baki sannan ta maida kallon ta ga Ameer da har lokacin ita yake kallo tace “Kar kayi wani mamaki, this is the first time i did something heroic in my life I swear!!”. Wani dariya ta bashi da ya kasa riƙe wa duk da irin rud’anin da suke ciki sai suka tsinci kansu da fashewa da dariya hakan yayi daidai da ihun da Sa’eed yayi mai haɗe da sunan Ameer “AMEEERRR!!!!!!”. Ya fad’a ne cike da haushi da takaicin abunda Ameer d’in yayi masa nan take ya birkice yana ta faffasa decorations dake falon komai ya wawura sai ya haɗe su da bango Mayee yazo yana rirrik’e shi…. “Tunda haka ne Shikenan sai mu buga wasan a haka, his games mu rules! Find him! I’m sure ba shi kaɗai ne cikin gidan nan ba ku binciko duk inda suke ku kawo min su nan i don’t have time”…. “Yess Boss!!!”. Mayee ya amsa sannan ya ja ɗaya daga cikin yaran suka haura stairs shi kuwa ya d’aura ƙafa ɗaya kan ɗaya yana jira. Ƙaran takun da suka ji ya saka su gimtse dariyar su suna sauraraon tafiyar Mayee har sun ji wucewar sa kasantuwar k’ofar bathroom din bata rufe ba Iman ta fallatsa ihu da alama yunwa take ji don wasan ta take , da gudu Laylah ta nufi bathroom d’in ta d’aga ta tana rarrashin ta amma inaaaaa…… Mayee ya ankare da kukan basu yi aune ba suka ji ana dukan k’ofar da ƙarfin tsiya, nan da nan Laylah ta saɓa Iman a baya sannan ta rungume su Tasleem tana ta addu’a waya Ameer ya gani kan gado ya d’auka yayi dialing numbar Suraj. “Suraj…. listen we are in deep trouble here! Sa’eed ya haukace! Bazai ragar wa kowa ba ,you have to hurry, do something ka taimaka kar ya cutar da yaran nan i am helpless Suraj, sai yau nake takaicin wannan gazawar nawa.” Haki yake cikin tashin hankali ya sauk’e wayar daga kunnen sa yana kallon yanda mutane ke hayaniya da jami’an tsaron nan, shi ya ma rasa ta inda zai fara, tun da farko ya k’ira Inspector Victor amma bai k’araso ba don haka ya k’ira abokin shi da ya kasance wani babban soja ne *Captain Rasheed* ya sanar da shi duk abunda ke faruwa, abunka da masu zafin nama kafin Suraj ya gama maganar ma shi ya mik’e ya nufi hanyar fita ya bada umarnin yaran sa su biyo shi…………… Tunda Captain ya ɗauke shi daga asibitin tare da Habeeb Suraj gani yake baza su isa ba cikin lokaci, gani yake motar ma babu wani saurin da take yi. Dafa kafad’ar Suraj captain yai yace “calm down Arabian chap (sunan da yake k’iran Suraj kenan) i assure you they will be alright! Shidai bai ce qala ba yacigaba da furzar da iska daga bakin shi yana bubbuga k’afafu….+ Daga ƙaran da suka ji Ameer da Laylah sun tabbatar cewa k’ofa ta buɗe, sun kuma gama tabbatar wa kashin su ya bushe Laylah ta sake jan yaran a jikin ta duk sun gama tsorita. Kawai sun saddaqar cewa mai taimakon su a wannan lokacin sai Allah. Hakan kuwa akayi, cikin abunda bai fi mintina goma ba Sa’eed ya aikata abinda zai aikata ya yi tafiyar sa, lokacin da suka bar unguwar daidai lokacin motar su Captain ta danno kai tun daga gakin gate ma Suraj ya tabbatar aikin gama ya gama domin kuwa gate ɗin a wangale yake, Suraj ya ɗan ja numfashi yace “Na tabbata idan Sa’eed yana cikin gidan nan ba zamu sameshi a buɗe haka ba,” yana gama rufe baki ya buɗe k’ofar motan ya fita da sauri, mai gadi sai nishi yake a d’akin da aka rufe shi sannan sun tarwatsa security Camera’s tun daga gate har ciki, Wasu daga cikin soldiers d’in suka buɗe k’ofar gateman inda suka tarar da shi yayi zufa ga hannun shi d’aure ta baya , Habeeb yayi saurin taimaka masa suka kwance shi, Suraj bai wani saurari me zai ce ba ya fara ja da baya kafin ya juya da gudu ya nufi cikin gida, ya tabbatar idan har gateman ma abun ya shafe shi babu abunda zai hana Sa’eed illatar da su Laylah, yana taɓa k’ofar ta buɗe nan yayi ta kwala musu k’ira kamar makaho jikin shi na b’ari, kamar motsi yaki a sama don haka ya ruga upstairs su Habeeb ma lokacin suka shigo ganin ya haura da gudu suka bi bayan shi. K’ofar Laylah da ya gani a ɓalle ne yasa Suraj rasa balance ɗin shi, bai aune ba yaji ya durk’ushe bisa gwiwowin shi… Da kyar Ameer ke jan jiki yana ƙoƙarin daidaita idanuwan shi domin yanda jiri ke d’iban shi jinin dake d’iga daga goshin sa ne zai tabbatar da cewa an buge shi ne da abu mai ƙarfi kuma mai nauyi “Ahhh!” Ya saki ƙara a kasalance hakan yasa Suraj d’ago wa a hankali, ganin yanayin Ameer yasa yayi saurin mik’ewa ya rik’o shi tun kafin ya kai k’asa… “Ameer! Ameer what ……..Ina Sa’eed? Shine yayi maka wannan raunin???” Kai kawai Ameer ya gyad’a da sauri Habeeb ya mik’a musu ruwa Suraj ya bashi, bayan ya sha ne ya ɗan ji natsuwa a ranshi sannan ya dubi Suraj yace “I’ve failed as a father, as a brother and as a husband! I couldn’t even save any one of them, i hate myself Suraj, the worst part of it is that ɗan uwana ne yake aikata wannan abun, na sani cewa na aikata abubuwa marasa kyau a rayuwa amma abunda Sa’eed ya aikata yau it makes me regret kasancewa sa ɗan uwana, Suraj! A gaban idona ya ɗauke su bai ji tausayin yara ƙanana ba poor Laylah…….she did her best to fight back but she couldn’t, wani ɓangaren na zuciyana yana cemin the kids are safe with Laylah by their side but tashin hankalin shine yanda Mubeenah da Khadijah zasu yi reacting….” Kwalla kawai ke tsere daga idanuwan Suraj yana tunanin yanda Iman zata yi kasancewar ta y’ar shekara ɗaya tak, ga kuma Tasleem da hannun ta ya ke d’aure saboda gurdewa da tayi sannan Boboh. How can Laylah deal with all that?” Ameer ya ɗan jingina da gadon da suka kwantar shi, Habeeb na dressing masa ciwon nasa yace “One more thing!….. Laylah akwai waya a hannun ta….. Wayan Muhseen na ga lokacin da ta ɗauka ta b’oye shi cikin teddy bear d’in Tasleem kuma sun tafi da shi, na tabbata bazata bar teddy bear din ya fita daga sight d’in ta ba, let’s just hope she calls or give us a hint” Sosai Captain ya ji daɗin hakan don haka ya ce “In dai abunda ka faɗa gaskiya ne toh aikin mu ya zo da sauk’i zan tura numbar zuwa headquarters inda za’a yi tracking d’in ta idan ya so sai muga inda suke…….. Kafin wayewar gari news channels, jaridu duk sun bazu ko ina, tun Suraj yana amsa waya har ya daina d’aga waya, shi ya ma rasa abu guda da zai yi, ga Meenah a asibiti ta haihu ko dubata bai yi ba sannan ga kuma abunda Sa’eed ya aikata duk ji yayi tunanin sa sun cukurkud’e gu ɗaya. Mik’e wa yayi ya dubi Captain yace “A haka kenan zamu zauna muna jiran gawon shanu? Sa’eed ya aikata abunda yayi ne saboda in fito in tunkare shi, so what am i still doing here sitting down???”” Ya ƙarashe maganar yana mik’e wa, riƙe shi Victor yayi yace “No Suraj! Bazamu barka ka fita ba especially not this time, na tabbata Laylah zata k’ira……” STORY CONTINUES BELOW Wafce hannun sa yayi a fusace yace “Kamar yaya wai? Tun jiya kuke ta ƙoƙarin tracking numbar nan bata ma kunne wayar, me zai sa in yarda cewa Sa’eed bai illata su ba? I am going on my own! Zan yi abunda nake ganin ya dace kuma se kuyi yanda kuka ga shine daidai, but I won’t stay here and warm cushion while my kids are out there suffering”. Yana gama rufe baki wani daga cikin sojojin da ya kafe wata computer da ido yace “Captain!! We have their location over! Da sauri duk suka rufa ma computar da take nuna taswirar Abuja da kuma wani jan dot da yake ta blinking, kafin su gama lura ma Suraj ya ɗauke komai a ƙwaƙwalwar sa ya ɗauki key ɗin motar sa ya fice duk basu lura ba…….. ______________ A hankali ta buɗe ido tana k’are wa d’akin kallo kafin ta juya gefen ta taga babu abinda take gani sai duhu a haka ta fara laluma gefen ta muryar ta na rawa “Bo… Boboh…??? Tasleem? Tas…..” Chak ta tsaida maganar da take yi jin ta taɓa Iman, hakan ya tabbatar mata cewa yaran suna kusa da ita. Ajiya zuciya tayi sai kuma tunanin abunda ya faru ya faɗo mata. Lokacin da Mayee ya shigo d’akin Ameer yayi k’ok’arin faɗa da shi domin su Laylah su gudu, tare da yaran suka fice daga d’akin shi kuma Ameer dake ba k’arfin jiki yake da shi ba sai ya kasa, domin Mayee ya riga da ya fice, mik’ewan da zai yi yaji an doke kanshi da abu mai ƙarfi daga nan bai san inda yake ba, Laylah kuma tana fita da yaran suka tsinci kansu a gaban Sa’eed, tsoro ƙarara a fuskar su ta bayyana amma don ƙarfin hali Laylah ta yi yunkurin guduwa hakan yasa Sa’eed ya shaqa mata chloroform daga handkerchief nashi, nan take ta zube ƙasa, su Tasleem da suke ihu ya daka musu tsawa yasa aka ɗebe su zuwa mota duk da tirka tirkan da suke yi bai damu ba. Tasleem ta rungume teddy bear d’in ta a hannun ta mai lafiyan don a gaban ta Laylah ta kashe wayar ta saka a ciki. Basu san inda aka nufa da su ba basu san me zai musu ba……. “Ina ne nan ya kawo mu?” Ta tambayi kanta duk da ta san amsar ɗaya ce (i don’t Know) Ji tayi kamar takun ƙafa hakan yasa ta koma ta yi lamo a kan gadon da take kamar wanda bata farka ba, tana ji aka buɗe k’ofar sannan aka kunna wutar d’akin, sake k’ank’ame idanuwan ta tayi lokacin da taji ya k’araso daf inda take, K’irjin ta taji yana bugu tamkar zuciyan ta zai yi tsalle ya fita saboda yanda taji numfashin sa a kunnen ta, hannuwan sa kuma yana shafa su da yatsun sa, wani busasshen miyau ta haɗiye ji tayi tamkar babu jini a jikin ta, hannu yasa ya ɗauke gashin ta da ya rufe b’arin fuskar ta yana k’are mata kallo bata yi aune ba taji sauk’ar lips d’in shi a wuyan ta, ji tayi tamkar tayi tsalle ta burma da gudu amma ta tabbata idan har ta nuna cewa ta farka sai ya k’arasa k’udirin da yayi niyya akan ta, ana cikin haka ɗaya daga cikin yaran nasa ya danno kai cikin d’akin “Boss!! an gama shirya komai” Kai ya jinjina yace “go I’ll be right there!” Yana kai nan ya mik’e ya fice daga d’akin yana murmushi, wannan karon bai kashe wutar d’akin ba sai ya rufe k’ofar ya tafi, yana fita ta tashi firgigit ta zauna tana sauk’e numfashi sama sama da hannun ta kuma tana share guntun hawayen ta, a hankali ta juya tana kallon su Tasleem dake barci ta sa hannu a sulale ta janyo teddy bear d’in hannun ta na rawa ta ciro wayar ta kunna, gani take booting d’in ma b’ata lokaci yake har cije ɗan yatsa take……. Driving yake kawai hankalin sa ma baya jikin sa, bai taɓa wuni guda ba tare da murmushin yaran sa ba, its a very tough situation for him, bai ma san wayar sa tana ringing ba har wajen missed call uku, kamar flash haka kunnen shi ya ɗan dauko masa ƙarar wayar da sauri ya d’aga ganin numbar da ta k’ira shi yasa jikin shi trembling ya d’auka ya kara a kunne tun kafin yayi parking “LAYLAH!!..” Ya k’ira sunan ta, ji tayi sautin muryar sa ya ɗauke mata duk wani damuwa da fargaba da take ciki. “Suraj! Suraj please get us out of here! I’m scared Sa’eed will not spare us all, ban san inda muke ba but i don’t like it here he was trying to moleste me and……and …..” Maganarta ce ta sarkafe sai kuka ya kufce mata. Wani d’aci Suraj yaji a mak’oshin sa bai san lokacin da ya bugi sitiyarin motar sa ba yace “that son of a bitch!. Laylah listen kar ki yi wani abu na san inda kuke yanzu haka ina kan hanya just keep calm, and take care of the kids i am coming to get you out!” Wani sanyi taji a ranta har tana ajiyar zuciya kafin ta saka wayar a silent mode ta maida shi cikin teddy bear d’in ta koma ta kwanta lamo kamar babu abunda ya faru…. “Suraj abunda zamuyi shine…….” Datse maganar sa Inspector Victor yayi lokacin da ya lura Suraj baya tare da su a wannan lokacin, Captain ma da yaji yayi shiru sai ya juyo, mamaki ƙarara a fuskar shi da ya fahimci Suraj ya riga ya fice. “This is unbelievable! Ya fita fa already! Suraj will stop at nothing indai har bai samu su Laylah ba but ta yaya aka yi har ya fita bamu sani ba? We have to go after him kafin ya aikata wani abun cikin gaggawa yasa Sa’eed ya fahimci mun san inda yake.” Habeeb kam kasa magana yayi kawai ya kura wa Captain Rasheed ido don shi yafi su mamakin yanda akayi Suraj ya fice a sulale. Mai lura da computer n ne ya janyo hankalin su bisa computan yana cewa “She’s making a call! Numbar tana k’iran wani layi, the line is registered Suraj Abdoul-maleek! This means Laylah yanzun haka tana waya ne da Suraj.” Da sauri captain ya danna wani button wanda nan take ta kamo duk conversations tsakanin Laylah da Suraj, don haka suka shirya suka bi bayan Suraj ɗin…….. Tun farkawar ta take ta faman duba k’ofa daga ganin ta ka san akwai wanda take tsammanin gani, daga bisani dai ta yi ɗan tsaki “mtseww” ta juya gefen ta tana kallon babyn dake kwance tana barcin ta sai ta dubi Ummi tace “Me yasa har yanzu Suraj bai shigo ba?” Ummi ta ɗan yi shiru don kar ta fad’a mata abunda ke faruwa hankalin ta ya tashi, kamar bazata amsa ba hankalin ta yana kan babyn ta saki murmushin da babu shiri tace “Ai yazo tun baki farka ba, toh aiki ne ya taso na gaggawa a office shiyasa ya fita, ya dad’e ma anan” Kai Meenah ta jinjina tana murmushi kafin ta dubi sapna tace “Suraj must be happy seeing our little princess right?” Da sauri sapna ta washe hak’ora tace “ai idan kin ce happy ma yayi kaɗan he was elated, holding her in his arms for the first time, gani yake ma kamar babu wasu mutane a gefen sa, gaba ɗaya ya manta da cewa muna wajen saida Ya Habeeb ya tab’o shi”.+ Wani narkakken murmushi Meenah ta sakar kamar mahaukaciya a ranta tace “Finally Suraj na yanka wa kaina tikitin zamar da kai nawa ni ni kaɗai! You are mine alone! It’s just a matter of time i will make sure you kick Laylah out of your life for good”……. __________ Haka tayi ta barcin k’arya gudun kada Sa’eed ya cutar da ita, tayi mamakin yanda yaran nan suke barci hankali kwance, nan take wani tunani ya zo mata, a tunanin nata wai ko basa raye, da sauri ta dasa kunnen ta bisa K’irjin Boboh, jin tafiyar numfashin sa yasa ta sauk’e aiiyar zuci, haka tabi kan Tasleem da Iman ma kafin ta sauk’e wani sigh of relief, ji tayi kamar Sa’eed da mutanen sa sun yi nisan kiwo don haka ta mik’e a hankali ta nufi window tana leka wa a hankali, motace ajiye daf da windon wanda ya kasance marar tsawo gashi kuma babu wani fence ko gate zagaye da su. A hankali ta buɗe windon ta ɗan shak’i iskar da ya buso sannan ta cije leb’e, ta dubi yaran da ke barci ta sake kallon windon bata b’ata lokaci ba ta tada Boboh da Tasleem sannan ta sa Mayafin ta ta goya Iman, k’ofar d’akin ta rufe da lock ta ciki yanda kafin wani ya shigo de sunyi escaping, a hankali ta sauk’e su Tasleem sannan ita ma ta dira, da pin ɗin gashinta ta buɗe k’ofar motar, a haka ta saka Tasleem da Boboh tasa su d’aura seatbelt, wani murmushi ta sakar lokacin da ta fahimci cewa makullin motar tana ciki, saida ta gama observing area d’in taga babu alamar mutane sannan ta tada motar ,ko waiwaye bata yi ba tunda ta fara zanzara gudu ga uban zufa da ya mamaye ta saboda tsabar fargaban dake zuciyar ta, Teddy bear d’in da ta ajiye a gefenta ta kalla tana jin kukan iman daga wajen Tasleem amma ta basar don tasan idan ta tsaya tabbas Sa’eed zai cimmata. A ranta take jin cewa duk runtsi yanzu ya san cewa ta yi escaping , wayar ta dauko daga cikin teddy bear d’in tayi dialing layin Suraj….. “Suraj! I have managed to escape with the kid’s….. Yanzu haka ina dawowa from airport road, ni ban san sunan wajen ba but it’s out of the city am not far from the city though…… Wani burki Suraj ya taka kafin ya karya kwana yace “Don’t stop Laylah! Kar ki tsaya i think i saw your car yanzu na wuce ki, keep driving ina biye da ke!….. Kuma kar ki kashe wayar let’s keep communicating, ko ba kece a black lexus ba?” Kai ta gyad’a tamkar yana ganin ta “E………Eh!!! Nice”. Ta k’arashe maganar tana kallon motar sa dake biye da ita daga mirror, a lokacin ne su Habeeb da Captain suka kunno kai tare da wasu soldiers d’in da tasu motar, it’s almost maghrib garin yayi tsit kowa na haramar sallah masu kasuwancin dare sun fara the road was less busy. Captain ya lek’o kansa daga motar shi yayi wa Laylah alama da tacigaba da tafiya “keep moving.” Kai ta jinjina ta sake ƙara speed d’in motar Suraj ma bai tsaya ba yana biye da ita saida suka shiga gari sosai sai yace ta tsaya, kamar jira take kuwa ta yi sauri ta taka burki da sauri ya sha gaban motar ta da nashi ya fito. K’ofar ya buɗe ya kamo hannun ta bata yi aune ba taji ya janyo ta jikin shi ya rungume, Suraj bai san me yake yi ba all he knows is Laylah is back and safe , haka ya k’ank’ame ta tamkar wanda zai karairaya yana sauke numfashi, da sauri ta janye jikin ta cike da kunyar abunda yayi sannan ta buɗe wa su Tasleem k’ofa karb’ar iman tayi wanda har ta gaji ta hakura da kukan tayi shiru, shima da sauri ya ɗauki Boboh ya kama hannun Tasleem da tayi sharkaf da hawaye ya saka su a motar shi itama shiga tayi tana sauk’e numfashi, ta ja seatbelt ta d’aura, shi ma hakan suraj yayi sannan ya furzar da iska daga bakin shi sannan ya dubi Laylah dake rungume da iman tana hawaye yace “Are you alright?? Baki ji ciwo ba? He didn’t hurt you did he??” Harara ta watsa masa tace *Wanne irin alright? Ka san kuwa yanda na ji lokacin da Sa’eed ya……..” Da sauri ta gimtse maganar tana mai kawar da kai gefe gefe, a hankali tace “I want to go home!!” Yanayin maganar yasa Suraj yaji wani yarr a jikin sa domin sincerely take maganar a shagwab’ance, kai ya girgiza kawai ya tada motar ya d’au hanyar gida ________ Tun ƙarfin shi yake dukan k’ofar yana k’iran Laylah “Na san kina ji na open the damn door Laylah!!” Wani wawan duka ya kai wa k’ofar wanda hakan yasa tuni ta buɗe, kamar mahaukaci ya shiga d’akin amma ga mamakin sa yaga babu kowa a cikin sa, babu laylah balle kuma alamar ta, sannan babu ɗaya daga cikin yaran ma, wani abu ne ya tokare mishi makogoro ya doki bango da hannun sa sannan ya daka wa Mayee tsawa “Get them Baaaack! Na san basu yi nisa ba i will not simply accept defeat!!!”. Maye ya duk’ad da kai k’asa yace “Boss! Babu yanda za’a yi mu cim_musu saboda d’azu na manta key a cikin motar, kuma mota ɗaya ce daman gashi da ita suka tafi”. Ji hakan ya sa Sa’eed ya sake birkice wa bai yi wata wata ba ya d’aga bindiga ya harbe Mayee nan take ko shurawa bai yi ba, hakan ba k’aramin girgiza sauran yayi ba tsoro ya bayyana a fuskokin su ya dubesu ɗaya bayan ɗaya yace “A nemo ta kafin wayewar gari duk inda take! Idan kuma ba haka ba k’addarar da ta sameshi kuma zata afka kanku” Ai ko amsa wa basu tsaya yi ba suka fita da gudu suna dube dube kan streets din. Sun yi nisa sosai ɗaya daga cikinsu ya tsaya yana haki kafin ya k’ira sunayen su “Mazaje nifa na gaji bayan nan wace tsiyar ya tsinana mana? Daman saboda Oga mayee muka saurare shi kunga a gaban idon ku ya harbe shi kuma ko girgiza bai yi ba na tabbata yarinyar nan ta riga tayi nisa kuma a duk inda take dole ne ta samu taimako, ni a ganina tun kafin ta b’are da mu zai fi kyau ɗan kuɗaɗen dake jikin mu kawai mu samfe da su idan yaso shi ya rage masa, do ko da ace mun koma ma kashe mu zai yi tamkar kiyashi haka ya ɗauki rai, idanuwan sa sun riga sun bushe bana tunanin akwai ragowar imani a tare da shi “1 Da alama maganar sa tayi tasiri don yanda yaga suna gyad’a kai amma kafin su kai ga amsa masa suka ga gaba-daya an zagaye su, suna tsakiya sai juye juye suke a cikin firgici , gashi dukkanin su dauke yake da makamai amma sun san soja ba wasa bane don haka suka zubar da guns din suka d’aga hannuwa sama alamar surrender. “Ina. Shugaban naku yake?!!!” Nan suka yi bayani kafin kace me an kawo wata motar soja da suke kiran ta da Black maria duk aka hankad’a su ciki…… .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *