ITA CE QADDARATA CHAPTER 13 K
uyi hak’uri nayi missing page 78-83 but ga lil about d pages;+ Bayan tafiyar Imran, Nasser ya fara soyayya da Noor, Yayi iya k’ok’arin shi wurin ganin Alhaji ya saki Noor and he succeeded, Ya nuna yana son aurenta, kowa ya amince akasa bikin su lokaci d’aya da na Imran da Khairat, HAJIYA ta matsa mishi dole ya dawo ayi bikin shi da khairat, Ya dawo ba da son ranshi ba, Dan baya so ya hadu da Noor, Ya dawo ya tarar Noor zata auri Naseer ya Shiga tashin hankali sosai but he don’t have any option tunda ba aure tsakaninsu, Ana gobe d’aurin aure, Ya gano mahaifin shi d’an caca ne, A caca ya auri Noor, Yayi deciding ya bar gidan da komai da ya mallaka dan duk ta sanadin mahaifin shi ne, Yace ba zai cigaba da cin haram Imran bai zarce ko’ina ba sai gidansu Naseer, ko kud’in da zai ba d’an achaba bashi da, sai da ya karb’a a wajen mai gadi Yace “zai bashi”. “Frnd lafiya?, Ya na ganka haka duk ba’a hayyacinka ba?” Imran bai iya cewa komai ba, wuri ya samu ya zauna kanshi na masifar sarawa, Zuciyarshi na tafarfasa kamar ana hura mai wuta. Naseer ya koma kusa da Imran ya dafa kafad’arshi, cike da damuwa Yace “Please ka fad’a mun me ke faruwa? Wlh hankali duk ya tashi” Tsawon minti d’aya bai ce komai ba, Yaja wani irin numfashi Yace “A yau ina bak’in cikin kasancewata duniya, ban tab’a jin na tsani rayuwar nan ba sai yau, Naseer banyi dace Iyaye da Siblings ba…” Wasu hawaye na bak’in ciki suka biyo kumatunshi. Naseer Yace “ban gane me kake nufi ba? Wani abu ya faru ne?” “Wai Daddy d’an caca ne hasalima Noor a caca ya ciyota” Naseer baisan sanda ya mik’e tsaye ba Yace “What?, ban yarda baa Imran, a ina kaji zancen nan? gaskiya da sake”. Imran yayi murmushin takaici Yace “da kunne na naji” Ya bashi labarin duk yadda akayi Naseer Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un kawai yake fad’a, Zufa na keto masa, Tausayin Imran ya kamashi. Tsawon mintuna suka d’auka shiru, Naseer ya nisa Yace “hukuncin daka yanke shine daidai, dan bai kamata ka cigaba da ci daga haram ba, but ina rok’on ka Dan Allah ka zauna nan gidanmu har zuwa lokacin da Allah zai sa su Daddy su gane gaskiya”. “Am sorry to say bazan iya zama nan ba, kayi hak’uri, zanje na nemi halilata(halal d’inshi) bana son zama gari d’aya dasu Daddy, zanyi nisa dasu inje can inda ba’a sanni ba”. Cike da tashin hankali Naseer Yace “Dan girman Allah friend kar kamun haka, bani da wani aboki da ya wuce ka, ina raye zaka shiga duniya, kana so ka nuna mun baka d’aukeni a matsayin d’an uwa ba kuma baka d’auki su Umma a matsayin iyayenka ba”. Ran Imran ya d’an fara b’aci, cikin fad’a Yace “ka fahimceni mana Naseer, ina so nayi nisa dasu Daddy bana so su rik’a jin labarina, zama kusa dasu ba abunda zai haddasa mun sai bak’in ciki, wanda zai iya ja na rasa raina” Naseer ya d’an yi ajiyar zuciyarshi Yace “Na fahimceka frnd, Ina maka fatan alkhairi a rayuwarka, duk inda zakaje pls ka sanar dani, In shaa Allah zan rik’a kawo maka ziyara”. Kai kawai ya gyad’a mishi, Yace “Kira mun Noor, ina son magana da ita” Ba musu Naseer ya tashi ya shiga kiranta. Noor na kitchen tana taya Umma aiki suna suna hira cikin nishad’i, Meenal ta tafi gidan k’awarta, Naseer ya shigo kallo d’aya ya mata yaji gabanshi ya fad’i, ya maida kallonshi kan Umma “Sannunku da aiki” ya fad’a “Yawwa” suka bashi amsa a tare, “Noor kizo” “Toh”, Yayi gaba ta biyo bayanshi. Tana ganin Imran ta juya zata koma, Cikin sanyin murya ya kira sunanta “Noor” Har cikin k’wak’walwarta taji sunan, yanayin yadda yake kiran sunanta daban ne (ji tayi muryarshi ta k’ara dad’i), Chak ta tsaya ba tare da ta juya ba, “Dan Allah ki dawo muyi magana, nasan ban kyauta miki ba dana tafi na barki, maganar da zamuyi dake mai muhimmanci ce” Yana maganar kamar zaiyi kuka, Ba zata iya mishi musu ba, ko dan yadda taji muryarshi, Gabanta nata fad’uwa ta dawo ta zauna a k’asa nesa dashi, kanta a sunkuye k’asa. “Ki zauna kan kujera”, Kai kawai ta girgiza mai alamar a’ah ba tare da ta d’ago kanta ba, bata son kallonshi, maganarshi kad’ai tana sata a wani yanayi ballatana ta kalleshi. “Duk tambayar da zan miki ina so ki fad’a mun gaskiya” Ba tace komai ba, Ya cigaba da cewa “Kinsan Daddy da Babanki Yan caca ne?, kinsan a caca aka saki?”. Noor ba k’aramin girgiza tayi ba, Zuciyarta nace mata ta fad’a mishi gaskiya ko tace bata sani ba, wata zuciyar tace ki fada mishi gaskiya Murya a sanyaye tace “Na sani” “Me yasa kika b’oye mun, me yasa kika mun k’arya a lokacin da na tambayeki?”. Murya na rawa tace “Dan in kare mutuncin mahaifina da naku, bana so kusan sana’ar mahaifinku caca ta dalilina bana son na zama silar rugujewar farin cikinku” Yayi shiru a ranshi yana cewa “Tabbas Noor nada hali mai kyau, ba kowa ne zai jure duk wulak’anci da cin mutuncin da aka mata ba, alhali tana da hanyar kubuta amma saboda farin cikin wasu tak’i” Wani sonta yaji ya k’ara shigar shi. A fili yace “Gaskiya Noor kina da hali mai kyau, samun irinki cikin mutane sai an tona”, Murmushi tayi tace “Ni zan koma cikin gida na bar Umma na aiki ita kad’ai” ( har yanzu haushin Imran take ji akan tafiyar da yayi, ya dawo kuma bai nemeta ba). Murya a marairaice yace “har yanzu fushi kike dani koh?”, Tayi banza kamar bata ji shi ba, Ya d’an yi murmushin dole Yace “Kafin na fad’a miki dalilin da yasa na tafi, ki amsa mun tambayar nan, Da gaske kike baki tashi da mahaifiyarki ba?”. Hawaye ta fara, ta basu labarin da Baba mai gadi ya fad’a mata bata b’oye komai ba, Daga Naseer har Imran hawaye suke, ta masifar basu tausayi. Falon yayi shiru na mintuna, Imran Yace “Naseer ka fad’a mata dalilin da yasa na tafi na barta”, Naseer ya d’an yi ajiyar zuciya, ya bata labarin komai da komai, Tayi mamaki sosai, kuma ta tabbatar ma kanta babu mai sonta a duniya kamar Imran, itama tabbas duk abubuwan da take ji a kanshi son shi take ba komai ba, Hawaye kawai take ta rasa na menene tausayin Imran, Son shi, Murna ko na menene bata sani ba?. Har cikin ranshi yake jin kukanta, Ya taso ya durk’usa gabanta, Ya fiddo hankercheif daga aljihunshi, “karb’a ki goge hawayenki bana son ganinsu”, Ba musu ta karb’a tana gogewa, ta tsayar da hawayen, Wata sanyayyar ajiyar zuciya yayi, Ya tsura mata ido ko k’iftawa ba yayi, kanta a sunkuye k’asa ta kasa d’agowa ta kalleshi. Naseer mik’ewa yayi, ya fita bazai iya jure ganinsu haka ba, zuciyarshi wani irin zafi take da d’aci( Kishi). “Noor Zaki aureni?” Imran ya tambayeta da muryarshi kamar mai shirin kuka, “Taya zan aureka bayan na tab’a auren mahaifinka?” “Baki san auren da akayi a bisa caca haramun bane bai halatta ba, dan haka akwai aure tsakanina dake”, “Idan na amince da aurenka Naseer fah, yau saura kwana uku aurenmu idan na mishi haka ban mishi adalchi ba”, “Nafi Naseer sonki Noor, Ina miki son da duk duniya ba me miki irinshi, Nasan Naseer zai bar mun ke, Kina sona?” “Ban da amsar baka tukuna, sai da izinin Naseer”. Wani kishi yaji ya turnik’eshi “hakan ya nuna mun Naseer take so”, Ya fuzgar da wani iska mai zafi, Ya mik’e ya fad’a kan kujera, Ya rufe idonshi zuciyarshi na mishi masifar zafi kamar zata fito waje, “idan tak’i amincewa da soyayyata mutuwa zanyi”. Kallonshi take tayi, tana jin masifar son shi na shigarta da tausayinshi, but ba zata amince da soyayyarshi ba, sai in Naseer yace ya hak’ura da ita, ba zata iya juya ma Naseer baya ba. Duk maganganun da suke Naseer na tsaye bakin k’ofa yana ji, Sallama yayi ya shiga falon, Noor kad’ai ta amsa mishi, ta bishi da kallo, Imran yayi nisa a tunani, Kujerar kusa da Imran ya zauna, Yayi shiru na yan mintuna sannan Yace “Friend!”, Imran ya amsa da “Na’am” ba tare da ya bud’e idonshi ba. Naseer ya cigaba da cewa “Na hak’ura najanye zancen aurena da No…” Kafin ya k’arasa Imran ya bud’e ido ya rungumeshi Yace “Thank you so much Friend”. “Ba godiya tsakaninmu, dama can Noor taka ce, dalili yasa ka tafi ka barta har ni na fara sonta, bazan shiga tsakaninku ba, nasan irin son da kake ma Noor da halin da ka shiga duk akan sonta, Kafi ni buk’atar Noor kuma kafi ni sonta, Nasan Noor kai take so, bazanyi son kai na rabaka da abunda kafi so a rayuwarka ba, Noor ga Imran baki da wani masoyi da ya wuce shi, ki rik’e shi hannu biyu Amana” Ya k’arasa maganar kamar zai yi kuka (yasan shikam yayi bankwana da farin ciki tunda ya rasa Noor, yafi so ya rasa nashi farin cikin da amininshi ya rasa).+ Imran kamo hannun Naseer yayi ya rik’e gamm, Yace “tabbas Naseer kai abokine nagari, ina alfahari da kai, nagode sos….”, Yai saurin katse shi “bana son godiyar nan, tafiya zaka yi da Noor ko sai kaje ka samu wurin zama”. “Da ita zan tafi, a yau nake so a d’aura mana aure”, Naseer ya zaro ido Yace “Yau d’in nan?”. “Yes friend! The earlier the better, bana so mu dad’e cikin gidan nan dan Su Daddy zasu iya biyoni nan”, “Toh ita ka barta nan mana, tunda baka san inda zaka yanzu ba, idan kaje ka samu wurin zama, sai ka dawo a d’aura aure ka tafi da ita”, “kaga friend k’afata k’afar Noor, a yau d’in nan nake so a d’aura aure, mu bar garin nan”. Zai sake magana Imran ya dakatar dashi “See frnd Dan Allah ka yarda kawai yanzu muje masallaci a d’aura mana aure”, Naseer ba don son ranshi ba Yace “toh muje”. Noor ita dai bata ce komai ba, Farin ciki ta tsinci kanta dashi zata zama mallakin Imran abun kaunarta, Murmushi kawai take ita kad’ai, Naseer ya kai dubanshi gareta Yace “ki shirya kafin muje mu dawo”. Kai ta d’aga mishi sama, Imran bai ko kalli inda take ba ya fice (haushinta yake ji, saboda cewa da tayi sai da izinin Naseer zata amince da aurenshi) Naseer yabi bayanshi. Suna fita, Alhaji da Hajiya suka shigo gidan, Hajiya har lokacin bata bar kuka ba, Duk ta fita hayyacinta a d’an k’ank’anin lokaci, Sun tambayi mai gadi ko Imran yazo gidan?, Yace “bai zo ba”( dan sunyi warning d’inshi kar ya fad’a yazo), Wani irin ihu Hajiya ta saki “Shikenan D’ana ya shiga duniya, Wayyo Allah ga abunda son duniya yaja mana”, “Haba Hajiya Dan Allah kiyi shiru, In shaa Allah za’a ganshi, Imran ba k’aramin yaro bane komai daren dad’ewa zai dawo garemu”, Bata ce komai ba tana ta faman kuka, Yaja mota suka tafi, Mai gadi ya bisu da kallo yana girgiza kai. Goro, sweets da chingum suka fara tsayawa suka siya, Masallacin can kusan fita gari suka je, inda ba’a sansu ba, kuma ba zasu ga wanda ya sansu ba, Suka sami limamin masallacin suka fad’a mishi buk’atarsu, Liman yace ba damuwa, Ya tara mutane dama an idar da sallar azahar kenan, An d’aura auren Imran da Noor akan sadaki 20k, Naseer ya biya kud’in. Imran “Alhamdulillah” kawai yake furtawa, farin ciki ya lullub’e zuciyarshi duk wani bak’in ciki da yake ciki ya nemeshi ya rasa, Naseer kuwa ya rasa meke mishi dad’i, kwata kwata baya jin dad’in zuciyarshi. Noor tayi bankwana dasu Ummi, Ummi ta mata nasiha sosaii tare da bata wasu had’e had’e,ta fad’a mata yadda zata yi amfani dasu, Sun sha kuka ita da meenal, Driver ya kaita airport, Naseer ya siyan musu ticket zuwa Kano ( dan can Imran yace zasu) Yaba Imran cheque na miliyan d’aya Yace “Gashi nan ya nemi gida da sana’a, suna isa ya kira shi Dan Allah ya sanar dashi”, Imran zai mishi godiya ya hana shi tare da cewa “Ina muku fatan alkhairi a rayuwarku, i’ll miss ur company friend” Ya k’arasa maganar da hawaye, Shima Imran hawayen yake, Yace “I’ll miss you too Friend”, Ya juya ya tafi zuciyarshi na k’ona yana hawaye. Imran har suka shiga jirgi, jirginsu ya tashi bai kalli ko saitin Noor ba, Yana ta murtuke fuska duk da wutar sonta dake ruruwa a zuciyarshi da farin cikin ta zama mallakinshi, Tacewa kanta “Me yake nufi da haka? K’ila yana tunanin halin mahaifinshi ne, Tunani take birjik a ranta har bacci yayi awon gaba da ita. Yana satar kallonta yaga tayi bacci, Ya tsura mata ido yana kallon kyakkyawar fuskarta, ga d’an karamin pink lips d’inta ji yake kamar yayi kissing d’insu, bai tab’a mata irin kallon da yake mata yau ba( tunda yanzu ta zama mallakinshi). Wani irin wutar sonta yake ji na hurawa a zuciyarshi, ga wani irin sabon feelings da yake ji akanta, kamar ya rungumeta haka yake ji, Har ya kai hannu zai tab’a ta sai kuma ya fasa, Ya jinginar da kanshi kan kujera ya lumshe ido, Yana jin wani irin sonta na shigarshi……….. Noor tana ta tunane-tunane har bacci b’arawo ya saceta, Imran kuwa ko kad’an bai runtsa ba, Kiran sallar asuba yasa shi mik’ewa ya shiga toilet, yayi brush yayi alwala, Ya kabbara sallah bayan ya idar ya zauna yana karatun Qur’ani cikin k’ira’arshi mai masifar d’adi.+ Sautin k’ira’arshi yasa Noor farkawa, ta d’auko ma radio ne ya kunna dan karatun kamar na balarabe saboda dad’i, Ganin Imran ne keta rera karatun suratul Rahman, idonshi a rufe, Ido ta zuba tana kallonshi, a ranta tace “gaskiya Imran is damn handsome ga addini, am so lucky to have him as my husband duk da nasan ya wuce da aji na”, Ta lumshe ido tare da jin son shi na ratsa dukkan sassan jikinta. Da k’yar ta mik’e ta shiga toilet, Da ta idar da sallah, ta zauna tana karatun Qur’ani, har ta gama Imran bai tashi daga inda yake ba, sata idar da sallah, ta zauna tana karatun Qur’ani, har ta gama Imran bai tashi daga inda yake ba, sai dai ya daina karatun, idonshi a lumshe. Gabanshi ta durk’usa murya a sanyaye tace “Ina kwana?” Yayi banza da ita, sau uku tana maimaitawa yayi kamar bai ji ta ba, Muryarta kamar mai shirin kuka tace “Dan Allah idan wani laifi na maka, ka taimaka ka gaya mun na baka hak’uri”, Banza ya sake yi da ita, Kuka ta fashe dashi. Da sauri ya bud’e ido( idan yana son mutuwarshi yana son kukanta), “Mene ne na kuka kuma?, kin nuna bakya sona Noor, kin nuna Naseer kike so bani ba, Kinsan yadda zuciyata ke k’aunarki? amma kika k’i ta, Ya kike so na miki? Zuciyata ba zata iya hak’ura dake ba shiyasa na aureki da wlh na barki kin auri wanda kike so” Ya k’arasa maganar yana hawaye. Tana kuka tace “Wlh kai zuciyata ke so Imran, Kai nake so nake k’auna ba Naseer ba, tun kafin nasan me ye so nake sonka har daga baya na gane sonka nake, Ina sonka Imran son da bana ma kowa shi, nace sai da izinin Naseer ne saboda kar yaga ban mishi adalchi ba”, Jawota yayi ya manna k’irjinshi, Yana shafa bayanta yace “Kukan ya isa haka, bana son ganin hawayenki, kinsan yadda nake jin kukanki a zuciyata?”, Shiru tayi tai lamo kan k’irjinshi ta lumshe ido. Ya sake matseta, Yana ajiyar zuciya a hankali, Wani irin farin ciki ya lullub’e zuciyarshi yau Noor ta furta tana son shi, gata manne a k’irjinshi abunda ya dad’e yana buri, tsawon minti uku suna haka, ta d’aga kanta daga k’irjinshi tare da sunkuyar da kanta k’asa, Binta yayi da kallo sannan ya mik’e jikinshi a mace, Telephone d’in d’akin ya danna ya kira, Yace “a kawo musu breakfast”, Ya juya ya kalli Noor da ta zuba mishi ido, yayi murmushi itama ta mayar masa. Toilet ya shiga yayi wanka, ko da ya fito har an kawo breakfast, Noor na zaune bata fara ci ba, Yace “Noor me yasa baki fara ci ba?”, Murmushi tayi tace “kai nake jira muci tare”, Yaji dad’in furucinta, ya sakar mata murmushi mai cike da nishad’i yace “ok my queen”, Da sauri ya shirya, Ya sanya wando da riga yan kati cikin wa’inda ya siyo, Sun mishi kyau sosaii, Ya fesa turaruka, D’akin ya game da k’amshin turarenshi. Zama yayi yana bata a baki, Da farko k’in karb’a tayi, sai da yace yayi fushi, Ta karb’a, Chips ne da egg sauce, idan ya sama mata a baki sai yace ta gutsira, shi kuma sauran sai yaci, Har suka ci rabin plate d’in tace ta k’oshi, Yace “are you sure kin koshi?”, Ta d’aga mishi kai sama, Ruwa ya tsiyaya a kofi ya bata tasha, ta rage saura, Yasa bakinshi saitin da tasha shima yasha, Noor satar kallonshi take ta gefen ido bata so yaga tana kallonshi, sonshi na shiga cikin jinin jikinta, Tissue ya d’auko ya goge mata baki, ya goge nashi. Ya mik’e ni zan tafi cikin gari nema mana gida, da sauran abunda zamu buk’ata, Take care of yourself plx, if you need anything ki kira waya ki sanar dasu”, Allah ya dawo dakai lafiya”, “Ameen my Queen”, Har ya duk’a zai yi kissing d’inta sai kuma ya fasa, yasan kissing d’inta zai iya haifar mai matsala ko kallonta yayi ya yakeji ballantana yayi kissing d’inta. Yana fita, ta shiga wanka, bayan ta fito ta tsara kwalliyarta cikin doguwar riga material da ta mata kyau, Ta kunna Tv tana kallo tana tunanin Imran. Hausawa zoo road anan ya samar musu gida, Compound ne gida 6 ne a ciki, Kowa da apartment d’inshi, Two bedrooms da toilet, 1 parlour, 1 kitchen sai yar verandah, Gidan ba laifi yana da kyau, kujeru ya siyo saiti 4 yan 70k, sai manyan katifu guda biyu, kayan kitchen da na abinchi, komai madaidaici ya siyo kasancewar kud’in bazasu isa ba, ko kayan kallo bai siyo ba, an jera komai a gidan. A bakin gidan yasa aka buga mishi shagon kwano, anan zai zuba provision yana siyarwa, sana’ar da ya yanke shawara kenan ya rik’a yi tunda bai zo da takardunshi ba balle ya nemi aiki, kuma ya d’aukarwa kanshi alk’awarin zai nemi halal d’inshi duk wuyar da zai sha zai jure da ya koma gidan mahaifinshi ya cigaba da cin haram.