ITA CE QADDARATA
CHAPTER 15
amma bazai iya jure ganin Noor najin yunwa ba (yasan tana da ulcer baya son abunda zai cutar da ita),+
Ya kalli gefenshi tana ta sharar bacci abunta Ya sumbaci goshinta a ranshi yace,
“I will not allow any harm to come to you my angel I promise”,
Mik’ewa yayi ya Shiga toilet, Yayi brush yai wanka, Ya shirya, Saitin Noor ya tsaya Yace
“Zan tafi nema miki abunda zaki ci my angel, zan jure duk wata wahala a kanki”
Kasancewar weekend ne ranar Noor bata farka ba sai wajen k’arfe goma, ta duba gefenta bata ga Imran ba, Falo da kitchen ta lek’a nan bata ganshi ba, A ranta tace “toh ina Imran ya tafi da sassafen nan”
Cikinta yayi k’ara k’olulu alamar yunwa, Shafar cikin tayi, Tayi murmushi tace
” Allah kasa yunwar nan da nake ji, Imran baya jin irinta, Ina tausayin Imran, bai saba wahala ba, bai saba da yunwa ba, gwara ni na Saba, Allah ka azurta Imran ta hanyar halal Allah ka tsare mai imaninshi” Ta fashe da kuka, nan ta duk’a tana ta kuka.
Imran fita yayi yana ta yawo cikin gari, Yana tambaya a ina zai samu aiki kowane iri ne zai iya, a biyashi, Wani mutumi yazo siyan abu a shagon, yaga Imran na tambayar Mai shagon ko akwai wani aiki da zai mai ya biyashi, Mai shagon Yace “Babu”.
Mutumin ya kirashi
“Zo d’an samari”
Imran ya k’arasa wajen mutumin
“Zaka iya mun wanki in biyaka, na dad’e ina Neman Mai wanki ban samu ba, Ni bak’o ne a garin nan bamu dad’e da dawowa nan ba, ni da iyalina”
Imran jiki na rawa Yace “Eh zan iya”
“Toh muje gidana kusa ne nan ba nisa”
Kayan wanki ne masu bala’in yawa, Imran na ganinsu sai da gabanshi ya fad’i,
Haka ya zage ya dinga wanki yana ta zufa, Yana yi yana hutawa, Bawan Allah abun tausayi, Tunanin Noor kawai yake ko wane hali take ciki yasan tana can tana jin yunwa, k’walla ne ya zubo mishi.
Sai azahar ya gama wankin, Ya masifar gaji, jikinshi ko’ina ciwo yake mai, Ga bayanshi ya masifar rik’e yana mai ciwo, Mutumin dubu biyu ya bashi, Imran ya mishi godiya ya tafi a ranshi yana cewa neman kud’i da wuya but I will do anything for you Noor.Restaurant ya zarje, Ya siyo takeaway na jollof rice da nama, sai lemon roba(sprite) mai sanyi da ruwa, Ya nufi gida da chanji dasu zai siyana mata abincin dare.
Noor hankalinta ya tashi jin Imran shiru ,
“Toh ina ya shiga?”
Tambayar da take ma kanta kenan, Sai faman kuka take, Ameerah na lallashinta tana fad’a mata kalamai masu kwantar da hankali
“Imran zai dawo ba abunda ya sameshi In shaa Allah”
Sallama yayi ya shigo falon, Da gudu Noor ta tashi ta rungumeshi, Ajiye ledar dake hannunshi yayi Ya rungumeta shima, Tana hawaye tace
“Ina ka shiga?”
“Naje nema mana abunda zamu ci”
“Hankalina ya tashi da naga ban ganka ba”
“Cry cry baby”
Yasa hannu yana goge mata hawayen fuskarta, hannu yasa ya shafi cikinta
“Am sorry babyna na tafi na barki da yunwa muje kici abinci”
“Uhmm kaima nasan kana jin yunwa”
“No ni bana jin yunwa”
Ameerah kam tun shigowar Imran ta fice.
Plate ta d’auko da spoon da cup, Ya juye abincin a plate, Ya d’auki spoon ya fara feeding d’inta,
“Bani spoon d’in nima in baka”
“No my angel am okay”
“Idan ba zaka ci ba toh nima bazan ci ba”
Ta juyar da kanta gefe, Juyo da kanta yayi suna kallon juna ido cikin ido
“My angel rigima na gaya miki am okay, idan kina so nayi amai toh”
Da sauri ta girgiza kai alamar a’ah
“Toh idan bakya so nayi amai kar kice dole sai naci”
Abincin ya cigaba da bata, cikinshi yayi k’olulo alamar yunwa(muguwar yunwa yake ji), Kallon tuhuma Noor ke mishi
D’an murmushi yayi Yace
“Cikina ya lalace tun d’azu nake ziyartar toilet”
“Ayyah me kaci toh?”
“Nima shine ban sani ba”
“Sannu my dear kasha magani”
Nodding kanshi ya bata Mik’ewa yayi, Jiri ya fara d’ibarshi, gaba d’aya jikinshi is weak ga yunwa ga wahalar aikin da yasha, Ya tafi zuu zai fad’i, Noor ta rik’o shi tana
“Sannu, ko zan kira Dr ne”
“A’ah had’a mun ruwan wanka masu zafi”
“Tohm”+
A daddafe yakai d’aki yana shiga, Ya fad’a kan katifa, Yana maida numfashi kamar yayi ihu haka yake ji saboda yadda jikinshi ke ciwo, abunka da wanda bai saba ba.
Ta had’a mai ruwan, Tazo saitinshi tace
“Na had’a maka ruwan, muje in kama maka kayi wankan ko kaji k’arfin jikinka”
Kai kawai ya iya d’aga mata,
Durk’usawa tayi gabanshi kamar zatayi kuka, ta rik’o hannunshi tace
“Cikin ne?”
“A’ah my angel jikina ke ciwo”
“Ya salam, wane aiki kayi da yasa maka ciwon jiki?”
“Wanki”
Da k’arfi tace
“wanki, me yasa kake son wahalar da kanka Imran? Why zakayi wanki, kasan baka saba wahala ba”
“Its my duty Noor, to take care of you, to do everything for you”
“Idan a kaina ne daga yau na hanaka, bana so Imran”
Ta fashe da kuka, Zai yi magana ta dakatar dashi da hannunta, tare da mik’ewa ta fita daga d’akin.
Ruwan zafi ta zuba a roba, ta d’auko towel da Rub,
Rigar jikinshi ta kama mai ya cire a hankali, Ya kwanta rub da jiki
Towel d’in tasa cikin ruwan zafi, Ta matse tana danna mai bayan tana hawaye, Hawayenta ne ya d’iga a bayanshi, Da sauri ya juya ganin tana hawaye, Ya rungumota jikinshi
“Haba my angel, me yasa kike son azabtar da zuciyata? Kinsan yadda nake jin kukanki a raina?”
D’ago fuskarta yayi, Yasa harshe yana lashe mata hawayen, har sai da ta daina zubar da hawayen, Yace
“Please kar ki k’ara zubar mun da hawayenki”
“Bazan iya jure ganinka cikin wahala bane”
“Sai kinyi hak’uri my angel, jarabawace Allah kuma ya baku ikon cinyeta”
“Ameen, juyo in k’arasa ma”
Kwanciya yayi ta cigaba ta danna mai bayan har k’afafunshi, Sannan ta shafa mai rub, sosai yaji dad’in jikinshi ciwon ya rage.
Sallar la’asar da magriba duk a gida yayi, Tare sukayi sallar, Da suka idar nan suka zauna suna karatun Qur’ani har aka kira isha’i,
Imran ya mik’e Yace
“zai tafi masallaci a can zai yi”
“Zaka iya zuwa masallacin?” Ta fad’a da alamar kulawa
“Eh jikin ya daina ciwo ai, my darling wife tasa ya daina” (fad’a kawai yayi amma har lokacin bayanshi na ciwo but ya rage ba kamar d’azu ba, Yace zashi masallaci ne dan ya samu ya siyo mata a binchin dare)
Murmushi tayi tace
“Tohm a dawo lafiya my dear, ka kula da kanka please”
“In shaa Allah i will”
A masallaci yayi sallar isha’i, Bayan ya idar ya tafi siyo mata abinchi, Tuwo da miyar egusi tasha kifi yayi mata takeaway, Sauran naira d’ari ya rage kud’in ya siyo garin hamsin, gyad’ar hamsin, dan wata irin masifar yunwa yake ji.
Noor fuskarta d’auke da damuwa tace “My dear ka dad’e, a ina ka tsaya?”
“Restaurant naje na siyo miki abinchi”
D’an dafa goshinta tayi tace
“Me yasa kake son wahalar da kanka, baka gama warkewa ba ka fita”
Hannunshi biyu ya had’a wuri d’aya
“Am so sorry my angel, forgive me”
“Ok ya wuce my dear, but plz ka daina anything da zai tab’a lafiyarka bana son abunda zai tab’a ka”
A ranshi sosai yaji dad’i yadda Noor ke Nuna damuwarta a kanshi+
“Zan kiyaye In shaa Allah my angel, muje kici abinchi”
Tare sukaci abinchin, dan k’in ci tayi, ba yadda baiyi da ita ba, sai dai sukaci tare.
Bayan sun gama ci suka kwanta, tana kwance kan k’irjinshi, da k’yar bacci ya d’auke Imran dan tunani yake abunda Noor zatYace gobe, gashi tana zuwa school, ko kud’in motar da zata makaranta babu.
Da yaje sallar asuba, Limamin masallacin ya fad’a ma matsalarshi Yace
“Dan Allah ya tayashi addu’a”
Limamin yace “akwai aikin d’aukar blocks idan zai yi”
Imran Yace “eh zai iya Neman halal d’inshi yake”
Liman yace
“Anjima kamar k’arfe tara na safe haka yazo ya sameshi” Ya zaro d’ari biyar ya bashi, Godiya yama limamin sosai,
Gida ya nufa cike da farin cikin ya samu aiki, duk da aiki ne mai wuyar gaske
Noor da ta ganshi ya dawo gida cike da farin ciki ta tambayeshi
“My dear ya akayi naga kana ta farin ciki?”
Murmushi yayi Yace “Aiki Liman ya Samar mun zan rik’a Lura da ginin da ake. Ma uban gidanshi” (Yasan idan ya gaya mata d’aukar blocks ne Bazata barshi ba)
Farin ciki ne ya bayyana a fuskar Noor
“Alhamdulillah Allah mun gode ma, Allah ya daukaka ka my dear, ya azurtaka ta hanyar halal”
“Ameen my angel” Ya fad’a tare da kissing d’inta a goshi
D’ari biyar d’in ya zaro daga aljihu
“Gashi my angel, Yau bazan samu Kai ki makaranta ba, kinga idan nace zan kaiki kud’in ba zasu isa ba, idan kinje makaranta sai ki siya abinchi kici”
Girgiza kanta tayi cike da tausayin Imran tace
“A’ah idan na karb’i kud’in kaci me?na hak’ura da zuwa makarantar har sai ranar da ka samu”
Hannunta ya jawo ya damk’a mata kud’in
“Don’t worry my angel, can wurin aiki za’a rik’a bani abinchi”
“Are u sure?”
“Yes sure” ya fad’a tare da d’aga mata kai.
Peck ta mishi, Ji tayi ya had’a bakinshi da nata, yana isar mata da sak’onni masu rikatarwa, itama martani ta Fara mayar Masa, Sun dad’e a haka, Sannan ya saketa yana maida numfashi, Lumshe ido tayi son Imran na ratsa dukkan sassan jikinta.
Jiki ba k’wari ta shirya, Imran ya rakata har waje, ya tarar mata Mai keke napep ta hau,
Cikin gida ya dawo ya fad’a kan gado, Idonshi ya rufe yana tunanin rayuwarsu, Ba abunda yake tunawa yaji farin ciki sai Noor, Yayi missing Hajiya, Alhaji, siblings d’inshi da Naseer but yayi alk’awari bazai koma ba, sai ya nemi halal d’inshi, Ya samu abunda zai rik’e kanshi, yanda idan ya koma ko ruwan gidan bazai sha ba, Kuma koda yaushe yana rok’a ma iyayenshi shiriya.
Tausayin Noor yake ji, He want to give her d best life, tunda ta taso cikin wahala take da k’uncin rayuwa, a ranshi Yace
“I promise to give u d best life my angel, da k’arfina da lafiyata zan nemi halal d’ina”
Mik’ewa yayi ya d’auko garin da ya siyo da gyad’a, Ya had’a da sugar yana sha yana yamutsa fuska, tunda uwarshi ta haifeshi bai tab’a shan gari ba, Da k’yar yake sha, Yunwa kad’ai tasa yasha shi , Ya gama ya wanke kofin, Yayi wanka ya shirya ya nufi Gidan liman.
Imran duk wahalar d’aukar blocks haka ya jure saboda ya riga ya sama ranshi he will endure it, But by mere looking zaka san bai saba wahala ba, sai zufa yake.
Rayuwa kenan Imran ne wai da d’aukar blocks, I pity you Imran😥
Noor ana tashinsu, wata k’awarta yar ajinsu tace “tazo su rik’a tafiya gida tare tunda unguwarsu d’aya, Noor ba musu ta bita tare da mata godiya, Har k’ofar gida suka kaita tace
“Gobe da safe ta shirya da wuri zasu biyo su d’auketa”
Uniform ta cire, tayi wanka, tasa riga da skirt na lace, ta feshe jikinta da turaruka masu bala’in k’amshi, da yake taci abinchi a makaranta so bata jin yunwa, Qur’ani ta dauka tana karantawa.
Gab da la’asar Imran ya shigo gida a gajiye, gaba d’aya joint d’inshi ciwo suke ga yunwa, Noor ta tarbeshi da murnarta, ta had’a Mai ruwan wanka yayi wanka yasa kayan shan iska.
Tausa take Mai, tana tambayarshi
“Ya wajen aiki ba wata matsala dai koh?”
“Eh babu my angel”
“Tohm Allah ya taimaka”
“Ameen”
“Kaci abinchi?”
“Eh naci, ko banci ba ganinki kad’ai ya isa ya k’osar dani”
Dariya tace
“I Luv yhu so much”
“I Luv yhu more n more”
Yai mata peck, itama ta mayar masa.
Ta gaya mishi tare da k’awarta zasu rik’a tafiya suna dawowa, sosai yaji dad’in haka sun samu sauk’in kud’in mota.
*Bayan wata hud’u*
Haka suka cigaba da rayuwarsu yau akwai gobe babu, Imran bai taba barin Noor da yunwa ba duk yadda zai yi ya samu mata abunda zataci sai yayi, Kullum sai yaje aikin blocks, har yanzu Noor bata San aikin da yake ba kenan, Imran duk ya rame yayi bak’i kmr ba Imran d’in nan handsome classy guy ba, Ramar shi na damun Noor kawai ba yadda zatayi ne, Duk da talaucin da suke fama dashi hakan bai hanasu nuna ma juna tsantsar soyayya ba, kullum kamar zasu had’iye juna, Noor har yanzu ko b’atan wata bata tab’a yi ba.
Imran suna zaune a majalisar k’ofar gidansu, Wani jibril Yace
“Imran ji yadda kayi bak’i ka rame kamar ba kai ba”
Murmushi yayi Yace
“Toh yana iya, halin rayuwa kenan”
“Me zai hana kabar sana’ar nan ta blocks wlh bata dace da kai ba, ji yadda ka lalace”
“Idan na barta toh nayi Yaya? Ita kadai ce hanyata ta samu”
Shiru yayi na seconds sannan yace
“Akwai wani Alhaji da zan had’aka dashi yana Bada keke napep, amma kullum zaka kai Masa #1,500 sai dai matsalarshi d’aya bashi da mutunci ko kad’an tun ba akan kud’i ba, zaka iya in had’a ka dashi”
Imran ajiyar zuciya yayi
“Zan iya dan yafi mun sana’ar block d’in nan”
“Toh madallah, Gobe in Allah ya kaimu da safe kafin na wuce wurin aiki sai na kai ka wurinshi, Ku daidaita”
“Nagode sosai”
“Ba komai ai, Kar ka damu”
Daya koma cikin gida yake sanar da Noor yadda sukayi da Jibril, Murna sosai tayi kuma ta godewa Allah,
Hannunta ya rik’o yasa cikin nashi
“My angel kiyi hak’uri da situation d’in nan da muke ciki, In shaa Allah watarana komai zai wuce”
Murmushi tayi tace
“Ban damu da halin rashin da muke ciki ba, ko da k’wanzo zan rik’a ci kullum, kasancewata tare da kai shine farin ciki na da kwanciyar hankalina, damuwa da kaga inayi is because of you, nasan baka Saba wahala ba”
Rungumeta Imran yayi
“I soo much luv u my angel more than my own life, please ki daina damuwa dani, am okay with this life, akan naci haram”
“I love you Imran, I care for you, all I want is ur happiness, so dole zan damu”
“Bana kina damuwa my angel, I love u unconditionally
Wuyanta ya Fara kissing yana lasa, ya dawo kan fuskarta yana ta kissing ba tsayawa, Noor lamo tayi ta lumshe ido tana jin dad’in abunda yake mata, Romancing d’inta ya fara, itama nan ta fara romancing d’inshi, Imran gaba d’aya ta gama rikita shi ya kawo climax , Ba b’ata lokaci suka tsunduma wata duniya lol😜
Duk Sanda ya kusanci Noor, sai yaji sonta k’ara ninkuwa a zuciyarshi saboda natsuwar da yake samu daga gareta, kullum daban yake jinta (taimakon Ameerah lol)
Tare sukayi wankan, Bayan sun shirya tana kwance kan k’irjinshi yana hura mata iska a kunne, sai lumshe ido take, Har bacci mai dad’i ya d’auketa, Shima daga baya Imran baccin ya d’aukeshi.
Basu farka ba sai asuba, Yayi alwala ya tafi masallaci, Ita tayi sallarta a nan, Bayan ta idar tayi karatun Qur’ani, da azkar
Ruwan liptop ta dafa musu tasa a flask, dan shi kad’ai ne dasu a gidan, Wanka tayi tasa uniform tana jiran Imran ya dawo daga masallaci, su sha tea.
D’ari biyun da ta rage mai a aljihu, Ya siyo bread na d’ari,
A k’ofi d’aya suka sha ruwan liptop d’in, Yana sha yana bata, Bread d’in cewa yayi tayi taci ita kad’ai, Tace ba zata ci ba, sai dai suci tare, Tare suka ci, Ba don kowannensu ya k’oshi, sai dai su d’au na Annabawa
D’arin data rage, Ya bata
“My angel kiyi hak’uri da wannan”
Karb’a tayi tai murmushi
“Don’t worry my dear, Allah ya baka Sa’a ya kare ka ya Sada ka da alkahirinshi a duk inda zaka Shiga”
“Ameen my angel, ina jin dad’in addu’o’inki a gareni, U’re d best wife ever”
“U’re also d best husband ever”
Sukayi dariya, Yayi hugging d’inta tare da amta kisses a fuska
“I Luv angel”
“I Luv u too my dear”
Jakarta ta d’auko tayi waje, dan taji horn na motarsu k’awarta Amal, Imran bin bayanta yayi da kallo yana murmushi sonta na ratsa jinin jikina, A fili ya furta
“NOOR KECE HASKE NA, KE KIKE HASKAKA RAYUWATA, IDAN BAKE RAYUWATA ZATA YI DUHU”
(Ni zee nace NOORUL IMRAN kenan hasken Imran).
Shiryawa yayi tsaf, Suka fita da Jibril, Ya kaishi wajen Alhaji Iro Na mata(Ana ce mishi Na mata ne saboda shegen son matanshi da auri sakin bala’i, indai akan mace ne zai iya kashe ko nawa ne, amma fa bashi da mutunci ta fannin kud’i, akan naira biyar sai yasa a d’aureka), Yayi introducing d’inshi wajen Alhaji ya tafi, Alhaji Na mata ya yaba da hankalin Imran, Bayan ya gindaya mai sharud’d’a, Ya bashi sabuwar keke napep dal a Leda, Yace daga yau zai fara aiki, Imran nata murna yana godiya
“Kar ka damu d’an samari, ni dai kawai inji dumus(wato kud’i)”
“In shaa Allah ba za’a samu wata matsala ba Alhaji”
“Yawwa haka nake son ji, sai na jika”.
*Rayuwa kenan, Imran handsome guy ya zama D’an Adaidaita, Toh Noor Allah yasa kar mata su k’wace miki shi dan yanzu sana’ar mata zai Fara, Har sai ya gaji da ganinsu lol*