ITA CE QADDARATA CHAPTER 6

ITA CE QADDARATA CHAPTER 6

  “Ina su Mum?,Imran ke tambayar mai’aikin da ya tarar a falon hajiya Sun tafi Zaria Zaria kuma? Ya tambaya da mamaki,Eh! Ta gyad’a kanta Me suka je yi? K’anin hajiya ne ya rasu Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Shine basu sanar dani ba Wayarshi ya fiddo daga aljihu 20missed calls ya gani,Dad ya kira shi,Yazeed,ihsan, iman duk sun kira shi(wayar silent take dats why bai ji ba) Numbern Daddy yayi dialing Hello! Daddy Imran kana ina? Muna ta kiran wayarka baka d’aga ba Wayar na silent ne,wanne daga cikin k’anin mum ya rasu Suleiman ne Gaban Imran yayi mummunar fad’uwa,murya na rawa dan duk ya gama rud’ewa yace Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un,Allah ya jik’anshi Ameen ya Rabb Bari na kamo hanya yanzu A’ah yanzu yamma tayi yaushe ka iso,muka juya,muma yanzu zamu taso,ka bari sai gobe Toh!Daddy Allah ya kawo ku lfya Ameen””+ “”Sosai Imran yaji rasuwar Uncle Suleiman,he is one of his fave uncle,har gidanshi a Zaria yana zuwa hutu,lkcin yana secondary school,kuma har da girmanshi ma yana zuwa yayi kwana biyu haka”” “”Noor kwata kwata bata fito daga d’akin ba,bata ma san su hajiya basa nan ba,Abu har d’aki ta kawo mata abinchi,amma ba da son ranta bh,dan kawai Imran yace ta kawo ne Noor abinchi kawai taci,tasha magani,ta kwanta sai barci”” “”Daddy da Yazeed kad’ai suka dawo,acan suka bar Hajiya dasu Ihsan Yazeed ke cewa Imran Bro! Wallahi mutuwa bata yi,mutuwa mai yankan k’auna,kaga yadda ya’yen uncle suleiman ke kuka suna birgima,wlh sai sun baka tausayi,har k’walla sai da nayi,Aunty maryam(matarshi) itama sai kuka take Imran girgiza kai kawai yake,tausayinsu fal a cikin ranshi duk da bai gansu ba,ya nisa yace Allah ya jik’anshi ya mishi rahama Ameen bro Har kasa zuciyata ta karaya,ina ji kamar kar naje sbd bazan iya jure ganinsu ba Hmm! Hakanan zaka daure kaje ka musu gaisuwa Imran ya d’an yi shiru,zuciyarshi na zafi yace ina Khairat? Nasan yadda suka shak’u da uncle suleiman Yazeed yace hmm! Ita ai sai allurar bacci aka mata sbd kmr tab’abb’iya haka ta rik’a yi Imran yace nasan dole ne,ga yadda suka shak’u da Uncle Haka sukai ta jimamin rasuwar Uncle suleiman”” *8:00pm* Sai a lokacin Noor ta farka,ta tashi tana mutsittsika ido,Agogo ta kalla Ya salam! Ta furta,tai saurin mik’ewa Ta shiga toilet,ta kuskure bakinta tayi alwala tayi sallah Ta cewa kanta bari dai na lek’a sashen Hajiya na gaisheta,shirun yayi yawa Falo ta tarar ba kowa,tayi mamakin ganin ba kowa dan tasan irin lkcin nan ,suna kallon wani indian series(king of hearts) Toh lafiya ko basa nan Ta juya zata fita Kawai taji tayi karo da mutum,Mutumin yai saurin ja da baya,jiki na rawa tai saurin d’ago idonta taga waye? Idonsu ya had’u da na Imran(as usual dukkansu sai da suka ji fad’uwar gaba,kowannensu ya rasa dalilin da yasa,in ya kalli cikin idon d’aya sai yaji fad’uwar gaba🤔) Murya na rawa tace umm….ummm…Am… so..sor…ry Shiru yayi,yana mamaki dama tayi boko shirun da taji yayi ta d’auka bai ji bane,dan haka ta sake cewa Am sorry kayi hak’uri , Kanshi yayi nodding yana kallon gefe Yace its okay Dama kinyi school ne? Tambayar tazo mata a bazata,me zai sa ya tambayeta ko dan yaji tace Am sorry Ta kawar da tunanin tace A’ah, tare da tsura mai ido ko k’iftawa bata yi,ita dai kyanshi take gani,tana so tayi ta kallonshi Ya gane kallonshi take duk da shi ba kallonta yake ba,yaji kallon yayi yawa,tana matsayin matar aure,matar babanshi bai kamata ace tana mai wannan kallo ba, da ya wuce shari’a,shi kanshi yana son yai ta kallonta,sbd masifar kyanta da yake gani,bai k’i yai ta kallonta ba har k’arshen rayuwarshi, but sbd kallon bai halatta ba,yake sa baya kallonta Yai gyaran murya ba tare da ya kalleta ba,Yace ya dai? Tai saurin zabura,ta sunkuyar da kanta k’asa,duk sai taji kunya Bai sake cewa komai ba,ya rab’ata ya wuce(Ball yazo kallo dama,Subscription d’insu ya k’are,gashi dare yayi) Itama sumi-sumi ta wuce Garamm taji ta sake cin karo da mutum Wannan karon tafi tsorata Ji tayi an hankad’ata Kee! Mahaukaciyar ina ce,bakya kallon gabanki ne,kin wani tab’ani da k’azamammen jikinki, Mtchewww yaja dogon tsaki, Yazeed ne ke fad’ar haka Am sorry Dan Allah,wallahi ba intentionally bane Hahahha! Ya shafe da dariya yace wow! Intentionally ashe kinsan intentionally Infact ma dai sorry for yourself,jaka kawai,dole inyi wanka k’azama ta tab’ani,yana karkad’e jikinshi Ya wuce ciki”” “”Wani k’olulun bak’in ciki taji yazo ya tokare mata wuya,kasa kuka ma tayi Sai kuma yadda suka yi da Imran ya fad’o mata a rai, _yadda ya bita a hankali,ba cin mutunchi ba hayaniya,buh ji yadda Yazeed ya mata,Imran u re different,ina son halinka_ Ta wuce ta koma d’aki abunta,tana cewa wato Yazeed will never change his habit,he will always remain who he is,I pray su Hajiya sun chanza,infact ma dai ina suke ta tambayi kanta,ba abun ta tambayi masu aiki ba,su fad’a mata bak’ar magana”” “”Yazeed da ya shiga falon, Imran ke tambayarshi kai da wa ke hayaniya? Ni da waccan yarinyar mana, Imran ya b’ata rai yace baza ka daina shiga harkarta ba koh Bro!ita fa tazo ta bangajeni Tsaki kawai Imran yaja,ya juya ya cigaba da kallo”” “”Washegari tun da safe,Imran ya kama hanyar Zaria,sai da ya lek’a d’akin Noor yaga barci kawai take abunta,Ya ajiye mata kular breakfast,wanda aka mishi ne yaci ya rage mata,Tare da Yazeed suka tafi”” “”Sun isa garin Zaria,Unguwar low cost(gidan Uncle Suleiman) Yan’uwa sun taro,ana ta amsar gaisuwa,ana yan koke-koke Hajiya kanta tasha kuka, idonta duk sun kumbura Ya musu gaisuwa,Yace yana son ganin Khairat? Aunty maryam tace tana d’aki ya shiga Khairat na kwance kan gado,ita kad’ai a d’akin,tana rusa kuka kamar ranta zai fita Imran yai sallama ya shiga, Bata amsa shi ba,sai ma sautin kukanta da ya k’aru Gefen gadon ya zauna,a hnkli ya kira sunanta. k’anwata(sunan da yake ce mata kenan) Cikin dasasshiyar muryata ta kuka tace Na’am Yace tashi ki zauna,ba musu ta tashi ta zauna,tana shesshek’ar kuka Cike da tausayinta ji yake kamar yayi k’walla yace hak’uri zaki yi k’anwata,dukkan mai rai mamaci ne,Allah’n da ya karb’eshi yafi mu son shi,kuka ba naki bane,kinsan ba kyau yiwa mamaci kuka,sannan Allah nasan masu tawakkali da hakuri,Dan Allah ina rok’on ki,ki daina kuka da tada hankalinki,nasan mutuwar Uba ba dad’i amma haka zaki yi hak’uri,ki rik’a mishi addu’a ne ba kuka ba Kanta ta d’aga sama Yace yawwa share hawayenki toh Tasa hannu tana goge hawayenta Yawwa ko kefa,yanzu ki tashi kiyi alwala kiyi sallah,ki karanta Qur’ani ki mishi addu’a,zaki ji sassauci a ranki Murya a sanyaye tace toh Yayana nagode A’ah ki daina mun godiya k’anwata,Ya mik’e tare da cewa zanje na dawo Plx kar na dawo na tarar dake a kwance Tace toh”” “”Ka ganta? Aunty maryam ta tambayeshi, Eh! Na ganta Tana nn tana kuka koh a’ah yanzu ta daina Toh Allah yasa,munyi lallashin amma tak’i bari, In shaa Allahu yanzu dai ta daina, Allah yasa ta d’aure Ameen,bari naje waje Toh Imran”” “”Imran ko da ya dawo,ya sameta zaune tana karatun Qur’ani, ta daina kukan,sosai yaji dad’in haka Nan ya k’ara mata nasiha,Yace shi zai koma Har zaka koma Yayana? Ta fad’a da damuwa d’auke a fuskarta Eh! K’anwata Toh Yayana Allah ya kiyaye hanya Ta mik’e zata mishi rakiya Da kinyi zamanki k’anwata A’ah bari na raka ka”” “”Kowa yayi mamakin ganin khairat,Aunty maryam a ranta tace lallai! Ba k’aramin jin maganar Imran take ba,tunda har ya sata ta daina kuka Yai sallama da su hajiya da sauran mutanen gida,ana ta mai Allah ya kiyaye hanya Bakin k’ofar gida ta mishi rakiya,kasancewar waje cike yake da mutane Ta dawo cikin gida tana jin kamar kar Imran ya tafi,Sun saba sosai da Imran,infact ma dai hr su Yazeed duk sun saba,amma sunfi shak’uwa da Imran Duk dashi ba son kula mata yake ba,ko cousins d’inshi mata,but Khairat suna shiri sosai,coz ba laifi tana da natsuwa da kamun kai,shi kuma yana son yaga mace haka “” _Suleiman uwarsu daya,ubansu d’aya da Hajiya,shi ke bita,yana zama a Zaria, a can yake aiki,da matarshi d’aya Maryam ,Ya’yensu Uku,Khairat ce babba,shekararta goma sha tara,sai k’annenta biyu maza khaleefa da khaleed,U.Suleiman na bala’in ji da ita,kyakkyawace ,Chocolate colour,tana da dara-daran ido,da d’an k’aramin baki,ga hips,komanta dai mashaa Allahu,santaleliyar budurwace son kowa k’in wanda ya rasa,tana ABU level one Biochemistry_”” Noor da ta tashi daga barci,taga kula ajiye gefenta Murmushi tayi,dan da wata masifar yunwa ta tashi Bakinta ta kuskure,coz tayi Sallah da asuba Ta zauna taci breakfast d’in(Chips,plantain and fried egg) Ta had’a kakkauran tea’nta A ranta sai addu’a take yiwa Imran(coz shine sillar take samun abinchi haka) Tana gamawa wanka tayi,kamar kullum yagaggun kayanta tasa Ta d’auki kula ta tafi kaiwa kitchen Kular kawai ta ajiye bata tanka su ba Har ta juya zata fita D’aya daga cikin masu aikin wadda ake cewa Lubah tace wai me kike nufi Kwana nan da bakya fitowa kiyi aiki,ko dan kinga hajiya bata nan Noor tace dama Hajiya bata nan Lubah ta yatsina fuska tace ban sani ba Abu ta tsoma baki in ma dan kinga bata nan ne,kike iskancin nan, zata dawo ta same ki ne Noor murmushin takaici tayi tace kuyi hak’uri ba haka bane,bana jin dad’i ne Yatsina fuska suka yi,suka ce Umm….kar ma kiyi ,Zaki amsa kira wajenta idan ta dawo Noor bata sake cewa uffan ba,tasa kai ta fita””+ “”Dama Hajiya bata nan,toh ina taje? Tambayar da take wa kanta kenan Ni bama wannan ba,Yaushe zan bar gidan nan,in huta da wannan wulak’anci da cin fuska,duk da nasan can ma ba dad’i nake ji ba,amma gwara gidanmu da nan,Imran ne kawai bana son bari,in na tuna shi sai inji kamar nai ta zama a gidan nan amma cin fuskar yayi yawa Mik’ewa tayi tana kallon kanta a madubin d’akin,taga ta masifar rame,Amma bata yi bak’i ba(farinta na nan,jawur da ita) Hawaye ta fara, tacewa kanta wallahi idan ba’a d’au mataki ba,na cigaba da zama gidan nan mutuwa zanyi😭,Allah yasa su Hajiya su chanza behaviour d’insu towards me,idan kuma baza su chanza ba Allah ya kawo mun mafitar alkhairi,ni dai tun da na taso bansan dad’in rayuwa ba,sai wahalar rayuwa Allah gani gare ka,ni baiwarka ce na kawo kukana gareka kaji k’aina”” *4:30pm* dai-dai Su Imran suka shigo garin Abuja,Jikin Imran duk ya gama sanyi,mutuwar Uncle Suleiman ba k’aramin girgizashi tayi ba,hakan ya k’ara tabbatar mishi da duniya ba bakin komai bace,kuma a koda yaushe kana iya mutuwa, Wunin ranar da bai ga Noor ba( _coz lkcin da ya lek’a d’akinta tana barci,kuma ta k’udundune a bargo ko fuskarta ba’a gani_) Duk sai yaji yayi missing d’inta,so kawai yake ya koma gida ya ganta, Tambayar kanshi ya tsaya yana yi,to akan me zanyi missing d’inta?,dan wuni d’aya ban ganta ba,ba kwana ba,ba sati ba Wata zuciyar tace mishi tausayinta ne da ya maka yawa,ya yarda cewa eh! tausayinta ne”” “”Noor itama duk tayi missing d’inshi,kwanakin nn ta saba yana lek’owa ya tambayi lafiyarta,ko ya tambayeta tasha magani,inma bai lek’o d’akinta ba,Suna had’uwa a filin gidan Dan haka duk ta kasa sukuni,sai sintiri take a tsakar gidan(tasan by this time yana dawowa lunch) Ji take kamar taje sashen su(Imran da Yazeed) har tayi hanyar sashen,Zuciyarta tace mata baki da hankaline zaki je, toh kije kice mishi me,kuma idan kika je baya nan fah,kika ga Yazeed u knw Yazeed won’t allow you to go free, sai yayi hurting d’inki, Ta juyo ta dawo,d’aki ta koma, ta zauna tayi jigum,tana cewa Allah yasa ba k’yaleni zai yi ba,ni in kowa zai fita harkarta bazan damu ba,amma Imran bazan iya jurewa ba,i dnt knw why Imran ina jin shi har k’asan zuciyata( _kuma hankalinta bai bata ta duba motocin gidan ba_)”” “”Imran suna parking motar su yayi hanyar d’akin Noor( _dan ba wanda yake so yasa a ido kamar Noor_) Yazeed yace ina kuma zaka nan? Zan duba Noor Noor kuma bro Yes! Anything wrong with that Bro! Wai me yasa kake damun kanka akan yarinyar nan? Haba! Nasan kana da tausayi sosai buh please ka daina tausayin yarinyar nan,Green snake ce under the green grass,tana wani sumi-sumi kamar ta Allah Imran tsaki kawai yaja,ya girgiza kai ya wuce _coz bashi dama lokacinshi_ Yazeed yaji wani haushi ya mamaye zuciyarshi,shi yafi so Imran ya fita harkarta,yadda zai ji dad’in yi mata mugunta”” “”Sallamar Imran Noor taji,kamar an zuba mata k’ank’ara a zuciyarta haka taji,tai saurin mik’ewa zaune daga kwance da take, Ta amsa masa sallamar da muryar farin ciki Yasa kai ya shiga d’akin Kanta tai saurin sunkuyar tana murmushi,(coz ta tuna jiya,da ta tsura mishi ido yace ya dai) Kallo d’aya ya mata,ya kawar da kanshi gefe _wani sanyi yaji a zuciyarta da bai san dalili ba_ Shiru ba wanda yace komai Noor ji take kmr tace mishi ina ka shiga yau,sai kuma ta basar Cikin sanyin murya Noor tace Ina wuni? Yace Ina wuni kuma,Kina matsayin matar babana kina gaisheni,ai ni ya kamata na gaishe ki Dan haka ina wuni? Ranta taji ya b’aci da ya kirata da matar babanshi(ta tsani ace ita matar Alhaji ce) Shiru tayi bata amsa ba, Yasan dama zai yi wuya ta amsa gaisuwar,Yace tunda ba zaki amsa gaisuwar d’anki ba,Toh Ya jikin ki? Jiki Alhamdulillah! Hope kinci abinchi kin sha magani? Eh! Ta bashi amsa Ok! Good Murya a sanyaye tace Dan Allah ina su Hajiya? Ya d’an yi shiru,sannan yace Suna zaria,k’aninta ne ya rasu Noor bata san sanda tai saurin d’ago kai ba, ta kalli shi( _sai dai shi ba ita yake kallo ba_) Tace Subhanallah! Allah ya jik’anshi Ameen ya bata masa Ba tare da ya sake cewa komai ba yasa kai ya fita Ya bar Noor nata jimamin mutuwar (duk da bata san shi ba) *Bayan kwana biyu* “”Yan gaisuwa an fara watsewa,dan jiya aka yi sadakar uku Hajiya ma na shirin dawowa Abuja,Ta nemi alfarmar yan’uwa akan Dan Allah abata Khairat ta tafi da ita Abuja,tasa ta makaranta acan Barinta nan shi zai sa ta rik’a tuno da Daddynta,can kuma gasu Ihsan zasu d’ebeta kewa,yanzu gashi daga zuwan Imran,har yasa ta saki jikinta Ba musu Aunty maryam da Yan’uwa suka amince Kuma sunji dad’i sosai,dan Hajiya ta nuna zumunci Khairat d’inma ta amince,dan tafi so tayi nisa da gida,ko zata rage damuwa en she want to be close to Imran(tana son kasancewa kusa da Imran) _but zata yi missing mum d’inta da k’annenta_ Khairat ta had’a kayanta Washegari zasu dawo Abuja””……………… Masu aiki sai faman gyare-gyare suke yau Hajiya zata dawo,Noor ta fito tasa hannu an gyara sashen hajiya,Anyi girke-girke Hajiya bata sanar da Alhaji ta d’auko khairat ba,dan a ganinta itace mai gidan, hka su Imran basu sani ba””+ “”Noor ko kad’an bata farin cikin dawowar Hajiya,kwana biyun nan da bata nn,ta samu hutu duk da tana addu’ar Allah yasa su chanza Tana zaune d’aki tayi jigum tana karatun Qur’ani,a rayuwarta tana bala’in son ta haddace Qur’ani,a gidansu Baba mai gadi ke k’arbar mata hadda,har ta haddace hizib goma,kuma tana bala’in son mkrnta amma bata da wanda zai kaita,sai hawaye shaa ya wanke fuskarta Ta hau magana a fili _Ni bnga amfanin rayuwata ba,bani da kowa ,bana zuwa makaranta Allah balle ta boko,Taya zanyi ilimi,kullum ina zaune gida cikin wahala da k’uncin rayuwa,bani da k’awa,bani da masoyi_ Ya Allah! Ka d’au raina na huta…..ta k’ara tsananta sautin kukanta Kamar daga sama taji muryar Imran cikin b’acin rai yake magana Noor kina da hnkli kuwa,kinsan me kike fad’a,me yasa baza kiyi imani da k’addara ba,duk tsanani yana tare da sauk’i kuma Allah na tare da masu hak’uri,wasu ma an jarrabesu fiye da yadda kike fuskanta,hak’uri zaki cigaba dayi kina addu’a, Shesshek’ar kuka kawai take ta kasa cewa komai Imran har cikin ranshi yake jin kukanta,idan akwai abunda ya tsani ji shine kukan Noor Hannu yasa a aljihi ya zaro handkerchief ya mik’a mata,tare da cewa karb’a ki goge hawayenki,bana son ganinsu Jin yace baya son ganin hawayenta yasa ta saurin gogesu Yana kallonta yadda take ta saurin gogewa,tana k’ok’arin had’iye kukan Hakan ba k’aramin dad’i ya mishi ba(dashi knshi baisan dalilin jin dad’i dan ta daina kuka ba) Yayi ajiyar zuciya yace makaranta kike so? Tai saurin d’aga kanta sama tace Eh Rashin makaranta ke saki kuka? Ta sake cewa Eh Yace kar ki damu,In shaa Allah xn saki makaranta Kamar an mata albishirin kujeran makka,haka taji dad’in zancen Imran ko a mafarki bata tab’a tunanin xuwa makaranta ba Murya a sanyaye tace Nagode Allah ya saka da alkhairi Yai murmushi yace No!ki daina mun godiya,Duk abunda kike buk’ata duniyar nan zan miki shi, indai bai fi k’arfina ba, I will stand by your side no matter the situation Farin ciki ne ya mamaye zuciyarta kawai sai tunanin sakinta da Alhaji zai yi ya fad’o mata rai(tasan idan Alhaji ya saketa shknn gidansu zata koma ba zance mkrnta,ko kula da ita da Imran ke fad’in zai yi)dan haka murna ta koma ciki Idonta suka kawo k’walla bnda Imran da tabar hawaye sun xubo Ya dai? Imran ya fad’a Ta had’iye miyau tace tunani nake idan na bar gidan nan shikenan bani ba makaranta Imran ya d’an yi shiru,sannan ya nisa yace barin ki gidan nan abu mai wuya ne, sai dai Ikon Allah,dan nama Alhaji magana yace bazai iya sakin ki ba,wanda na rasa dalilinshi nacewa haka Noor tayi shiru taji dad’in zance,at d same time bata ji ba _tana son yin makaranta,haka tana son tashi daga matsayin matar Alhaji_ Ganin Imran na kallonta,yana jiran yaji me zata ce,Tayi murmushi tace Allah yasa haka yafi zama alkhairi Ya amsa da Ameen,kinci abinchi? Eh! Naci Toh kinsha magani? Eh! Good! Pls ki kiyaye shan magani da cin abinchi Tayi nodding kanta tace In shaa Allah”” “”Noor tasan dalilin da yasa Alhaji yace bazai saketa ba,ba zai wuce kan harkarsu ta caca ba,Mik’a al’amuranta kawai tayi ga Allah ya zab’a mata mafi alkhairi”” “”Su hajiya sun iso Imran da Yazeed ba k’aramin farin cikin ganin Khairat suka yi ba Imran na tausayinta sosai Gaba d’ayansu sun baje a falon sashen Hajiya, Imran yace Mum dama tare da Khairat zaku dawo shine baki sanar damu ba,mu shirya tarbonta Hajiya tace ina son nayi suprising d’inku ne amma yanzu bata b’aci ba,kuna iya tarbon nata Khairat tace k’yaleshi mum,ko kin fad’a musu,ba wani abu da zai yi Imran yace au haka kikace,shikenan na fasa abunda nayi niyya Khairat tace Sorry Yayana,wasa nake Imran yace a’ah ni dai na fasa Please!please! Yayana, ta fad’a tana shagwab’a Imran yace ji yadda ta wani marairaice,ba dan halinki ba,na hak’ura Khairat tayi murmushi tace Yawwa Yayana Hajiya kallonsu kawai take tana murmushi tana sak’a abubuwa a ranta”” STORY CONTINUES BELOW “”Noor ta mik’e daga kwance da take,Tace bari naje nama Hajiya sannu da zuwa Gabanta nata fad’uwa ta shiga falon Kowa ya bita da matsiyacin kallo,Imran kad’ai ne ya mata kallon arzik’i,Khairat ma wani irin kallo take mata na k’ask’anci(daga yanayin shigarta ya tabbatar mata yar’aiki ce) Noor duk ta gama tsarguwa,ta durk’usa gaban Hajiya,kanta sunkuye k’asa Murya a sanyaye tace Sannu da Zuwa hajiya,Ya hanya? Ya hak’uri? Allah ya jik’anshi Hajiya hannu tasa ta dakatar da ita✋🏻 Nace miki ina buk’atar gaisuwarki,Munafuka Imran yace haba! Mum me ye a ciki dan ta miki gaisuwa Hajiya tace Baza ka daina sa mun baki akan harkar yarinyar nan ba koh Imran yace Mum ba haka bane,naga ba wani laifi a ciki dan ta miki gaisuwa A fusace Hajiya tace toh bana buk’ata Ta juya kan Noor A tsawace tace tashi ki b’ace mun da gani kafin nayi k’wallo dake makira Yazeed yace Bro! Wai me yasa kake haka? A fusace Imran yace keep your mouth shut or else…. _ya riga ya kawo wuya zuciyarshi har zafi take,Yadda yake ji gwara a tsinka mai mari akan a tab’a Noor,ko bak’ar magana baya so yaga an mata_ Ganin yanayinshi yasa Yazeed yaja bakinshi yayi shiru,yasan halin Yayan nashi Tashi yayi ya bar falon Hajiya ta bishi da kallo tace sannu Uban yan tausayi Yazeed yace ni na kasa gane kan Yaya akan yarinyar nan Hajiya tace wai shi mai tausayi Ihsan tace but mum ai da baya tausayinta,yanzu ne ya fara Hajiya tace hmm! Wai ce mishi tayi ba da son ranta aka mata aure ba,hannun kishiyar mamanta ta tashi,bata tab’a ganin mamanta ba Yazeed dogon tsaki yaja yace and so,shi zai sa yaji tausayinta Hajiya tace kunsan haka zuciyarshi take kamar ta mata,har gwara ta wasu matan Iman tace mu dai gaskiya zai takura mana,ya hana mu dealing with her Yazeed yace wlh sai dai yayi duk abunda zai yi, amma bazai hana ni dealing with her ba Ya tashi ya fita a fusace”” “”Khairat ita dai sun sata a duhu Wacece ita? Ta tambaya Matar Daddy Ihsan ta fad’a Cike da mamaki take kallon Ihsan tace matar Daddy kuma(Hajiya bata gayawa kowa Alhaji yayi aure ba,dan a ganinta abun kunya ne) Ihsan tace Yes,tashi muje d’aki na baki labari Iman tace nima bari na tafi d’aki,mun dawo tafiya ko hutawa bamu yi mun had’u da crises d’in shegiyar yarinyar nan”” “”Imran tunaninshi taya zai b’ullo da al’amarin sa Noor makaranta,yasan ba k’aramin gwagwarmaya za’ayi ba kafin hajiya ta yarda,but kome zai faru ya dad’e bai faru ba,amma ya riga yayi alwashin sa Noor makaranta,da kud’inshi zai sata bayan buk’atar sulen kowa”” “”Khairat an sata makarantarsu Ihsan,level d’insu d’aya Khairat itama ta d’au tsanar duniya ta d’aurawa Noor,dama tana ganinta taji bata mata ba,da k’arin ganin yadda Imran ke rawar k’afa a kanta(Noor),duk da cewa itama yana bata kula sosai”” “”Duk yamma bayan sallar la’asar,Imran sai ya kira Noor garden,sun sha hira sai magrib suke tashi,yana yin hakane dan ya kawar mata da damuwa,sosai hkn ya rage mata damuwa( _duk da ita bata wani magana shine ke bata labari,kuma yakan tambayeta abubuwan da take so,da wanda bata so,ita kuma tana fad’a mishi tun bata sakin jiki dashi har takai ga yanzu ta saba,sosai take jin Imran a ranta,idan suna hirar bata k’i su kwana suna yi ba,gidan ba wanda ya sani_”” “”Yau ma zaune suke suna hira, Itatuwan dake garden nata kad’awa sanyin iskan na dukansu,Imran har wani lumshe ido yake idan iskan na dukanshi Meye babban burinki a rayuwarki? Noor na wasa da yan’yatsunta tace Naga mahaifiyata Ta bashi tausayi Yace baki san ina ne garinsu ba? Baba mai gadi yace mun asalinta yar Nijer ce,irin buzayen nan ne dake zama kongo,anan mahaifina ya ganta,ya aureta Imran yayi shiru na d’an mintuna a ranshi yace No wonder kike da kyau haka ashe ke buzuwa ce,snn ya nisa yace Allah ya had’aki da ita watarana Ameen ta bashi amsa Kallonta yayi yaga yadda kayan jikinta suka bala’in tsufa,atamfar duk ta k’od’e,Ya mik’e yace tashi muje wani wuri Ido ta zaro tace idan hajiya ko wani ya ganmu fah And so,Sai me,Ya fad’a da irin i don’t care d’in nan Noor kamar ba zata mik’e ba,a tsorace take Da d’an tsawa yace tashi mu tafi mana,ke matar Babana ce,so meye a ciki dan na fita dake,matsayin mahaifiyata kike Noor bata ce komai ba,ta mik’e, Yayi gaba tabi bayanshi”” “”Gani tayi yaja ya tsaya,itama ta tsaya Khairat ya dai? Ta shagwab’e tace dama kana nan tun d’azu ina ta nemanka Imran yayi murmushi yace Uhmm….k’anwata rigima,me kike so ne? Ta turo baki tace Shawarma nake son ci,ka kaini na siya Your wish is my command k’anwata,je ki d’auka mayafinki,dama yanzu zamu fita da Noor Sai a lokacin ta lura da Noor,tsaye bayanshi kamar munafuka Ta yatsina fuska tace zaku fita? Ina zaku? Imran yace ke dai kije ki d’auko mayafinki muje Ta b’ata rai tace No! Na fasa,sai kun dawo Imran yace me ya faru kuma? Idonta ya ciko da k’walla tace ba komai,ta juya zata wuce Yai saurin shan gabanta yace haba! K’anwata me ye na fushi kuma? Noor na ganin haka tasan saboda ita ne tace ta fasa,dan haka tace kuje,ka bari ni sai gobe maje Yace a’ah Noor ki bari mu tafi tare Ta girgiza kanta ta wuce Ya bita da kallo(dukkansu yana tausayinsu,baya son ya b’ata ran d’aya daga cikinsu) Khairat ta tafa hannunta saitin idonshi,ya juya yace na’am Tace Yayana wai me yasa kake damun kanka akan yarinyar nan? Yayi ajiyar zuciya yace tausayinta nake ji k’anwata Ta tab’e baki tace tausayi,lallai tausayi,gaskiya ka rage damun kanka a kanta Imran ranshi ya d’an soma b’aci yace kar kice mun kinbi layinsu Mum Ta girgiza kai tace A’ah,mu tafi Ok! Ina jiranki a mota,kiyi sauri Tace toh Yayana,ta wuce tana rausaya””

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *