ITA CE QADDARATA CHAPTER 7

ITA CE QADDARATA CHAPTER 7

  Noor d’aki ta koma,ko kad’an bata ji haushin rashin fitar su da Imran ba,dad’i ma taji coz bata son fitar””+ “”A mota Imran da Khairat nata hira Har suka kai,(SHOPRITE) anan yan gidansu ke siyan Shawarma A tare suka shiga Shawarma biyar ya siyan mata da Rubber ice-cream uku Khairat tace Yayana ai tamun yawa bazan iya cinyewa ba, Imran yace A’ah ke dai gashin nn kici kici har sai kin k’oshi,kinga yau ba sai kinci abinchin dare ba Tayi dariya tace Yayana kenan Har sun bar wajen shawarma sai kuma ya koma Guda biyu yace a bashi,da Rubber ice-cream biyu Khairat tace ai da baka siyo ba,ka bari munci wannan tare Imran yace no! K’anwata kar ki damu”” “”Shagon boutique na mata suka shiga Khairat da bakinta baya shiru tace me kuma zamu yi anan Yayana? Imran yayi dariya yace k’anwata kenan sarkin tambaya,ki zab’i abunda kike so A ranta taji dad’i,nan ta shiga zab’ar riguna da wando Imran gefen doguyan riguna yaje, yana ta zab’a ya d’auki sun kai kala goma Khairat kuwa sai dad’i take ji Imran na siyan mata Sashen inners ya koma Ya zab’o pants,bras,da underskirts kowanne guda shida Khairat kunya taji a ranta tace Yayana kenan maimaikon yace nazo na d’auka da kaina,shine yake zab’ar mun da kanshi Nan suka gama da boutique,ya biya kud’i suka fita Shagon Cosmetics suka shiga Khairat ita dai biye take dashi kawai Nan ma Imran yace ta zab’i abunda take so Ta shiga zab’a Shima ya kwashi turaruka,kayan shafa,brush,maclean In tak’aice muku dai siyayya sosai Imran yayi a Shoprite,hadda atamfofi ya siyo,laces da material Khairat dad’i kamar zai kasheta,ji take kamar ta had’iye Imran,Son shi na k’ara shigarta _Ni Zee na kalli 👀Qurratu nace dama son shi take_”” “”Sun dawo gida,Imran ya kwashi kayan da ya siyo Khairat a tunaninta kai mata zai yi Kawai taga yayi hanyar d’akin Noor Binshi da kallo kawai take,ta kasa furta ko A Ba dai kayan nan Noor ya siyo ma ba,No! It can’t be Nan ta ajiye kayan hannunta,tabi bayanshi Bakin k’ofa ta tsaya,ta lab’e”” “”Noor sallamar Imran kawai taji,Ya shigo nik’i- nik’i da kaya Ya ajiyesu gefe,ya samu wuri ya zauna Batace masa uffan ba Yace ba magana Noor,ko fushi kike dani,ai ke kikace mu tafi ba zaki ba Murmushi tayi tace ko kad’an bnji haushi ba,kawai naga ka shigo da kaya ne shine na tsaya ina mamaki Yai murmushi yace kayank ki duba kiga insun miki,in kuma basu miki,Sai ki shirya muje ki zab’i wanda ranki ke so Ya mik’e yace bari na baki waje, kiji dad’in dubawa”” “”Khairat tai saurin lab’ewa da taji alamun xai fito Ya fito ya wuce sashensu,ba tare da ya lura da khairat ba Khairat ta kawo wuya,zuciyarta har wani zafi-zafi take Sai hawaye A guje ta nufi sashen Hajiya _ko ta kayanta bata bi ba_ _D’akinsu d’aya da Ihsan_ Ta shiga d’akin tana kuka Ihsan tace lafiya khairat me aka miki? Nan ta fad’awa ihsan duk yadda aka yi Ihsan tace Dnt tell me,kina nufin siyayya ya mata Khairat na kuka tace sosai ma kuwa sai ma kinga kayan Ihsan ta rik’e baki tace lallai abun Ya Imran yayi yawa,amma ke yanzu me ye na kuka,kinsan dai kinfi k’arfin kayan da ya bata,zaki iya siyan ma kanki wanda suka ninka su Khairat tace kinsan irin son da nake wa Ya Imran,duk da shi baisan ina yi ba,bana son kowacce mace kusa dashi in dai ba muharramarshi ba Ihsan ta tuntsire da dariya tace lallai khairat,toh ai itama Noor muharramarshi ce ko kin manta matar Daddy ce Khairat tace Ya salam! Wlh mantawa nake,kar kiso kiji yadda zuciyata ke zafi,Tai ajiyar zuciya ta cigaba da cewa Wai! har na samu relief,but duk da hka bana son yarinyar Ihsan tace kisa ranki a ruwan sanyi,ba fah aure tsakaninsu ko da kuwa Daddy ya saketa,ina mai tabbatar miki Ya Imran baya sonta,tausayinta yake,Taya ma zai fara son Matar Babanshi,kema kiyi tunani abu ne da bazai tab’a yiwuwa ba Khairat tayi murmushi tare da jin wani sanyi a ranta Kayan da ta bari waje,sai mai gadi ne ya shigo mata dasu”” “”Noor bud’e kayan kawai take,ta saki baki tana kallo Wacce irin Zuciyar imani ce da Imran,a gsky samun irinshi sai an tona Wannan kaya kamar lefe Bata san taya zata fara mishi godiya ba Ledar shawarma da ice-cream ta bud’e Tasan ice-cream amma bata san shawarma ba,ta d’auko tana jujjuya tana cewa me ye wannan kuma? Ta d’an gutsira taji bala’in dad’i Tas ta cinye shawarma,dan dama bala’in yunwa take ji(tun dawowar Hajiya ta hana a rik’a zuba mata abinchi,sai dai tasha tea ko maltina,idan Imran ya tambayeta taci abinchi? Eh take ce masa)”” “”Bayan sallar isha’i,Tayi wanke-wanke ta gyara kitchen Sannan ta dawo,ta kwanta sai barci Imran bai k’ara shigowa d’akin ba”” “”Tunda asuba Hajiya ta tasheta da ruwan sanyi Tai saurin mik’ewa,tana rawar sanyi Hajiya rik’e da k’ugu tace Inyee! Kilewa Uban wa ya baki bargo Murya na rawa tace Imran Ina so ki wanke shi ki kawo mun Noor ta gyad’a kanta tace toh Hajiya ta cigaba da masifa “”Naga kwana biyu kin manta aikin ki na sharar tsakar gida da wanke motoci,Toh wlh daga yau kar ki bari in k’ara tuna miki Ta fice tana kumfar baki”” “”Noor murmushi kawai tayi,inda sabo ta saba Toilet ta shiga tayi brush,tayi alwala Tayi Sallah”” “”Sharar tsakar gida ta fara,ko da ta gama ta masifar gaji ta hau wankin motoci Imran yayi shirin shi tsaf( ya masifar yi kyau😍)zashi office Daga nesa ya hangota,tana wanke mota duk ta had’a gumi Kamar an watsa mai ruwan zafi haka yaji zafin ganinta A fusace ya k’arasa inda take Tsayawa tayi tana kallonshi sbd kyan da yayi Wa ya saki wannan aiki? Murya a sanyaye tace Hajiya A fusace yace wuce ki tafi d’aki Da ka bari na…… Ya katseta kar kice komai wuce kawai Jiki a sanyaye ta wuce”” “”Yana huci ya shiga falon Hajiya Haba! Haba! Hajiya ya za’a sa Noor wankin mota Hajiya ta ajiye kofin tea dake hannunta tace na sata zo ka dukeni Imran yace is not proper wlh Hajiya tace Imran! Imran! Imran! Sau nawa na kira sunanka sau uku koh Wlh kaji na rantse idan baka daina tuhumata akan aikin da nake sa Noor ba,zaka fuskanci mummunan b’acin rai,aiki yanzu na fara sata,Ko Ubanka da ya aurota bai isa ya hana ni,yi mata abunda naga dama ba balle kai,kuma wlh idan bata wanke motocin nan ba,kasheta ne kawai ba……… Bai jira ta k’arasa ba,ya fita a fusace,ya buga k’ofar falon kamar zata b’alle Zuciyarshi sai tafarfasa take kamar zata fashe Hajiya tace ku ganmu da yara,taja dogon tsaki Ta cigaba da shan tea’n ta hankali kwance”” “”Kayanshi ya cire,daga shi sai three-quarter da singlet Ya nufi wajen motoci yana wankewa duk ya had’a gumi ( _yafi so ya wanke akan ita ta wanke_) A ranshi yace gaskiya Mum bata da tausayi,yanzu hk Noor ke shan wahalar wankesu,daga yau nayi alk’awarin in dai ina numfashi a doran k’asa ba zata sake wankewa ba……………… Noor d’aki ta shiga tayi jigum tana tunani ta rasa me ke mata dad’i duniya Imran yace kar ta wanke motoci tasan kuma idan bata wanke ba,wata matsalar ce Nasan yanxu ya fita,bari naje na cigaba da wankewa shine rufin asirina ta fad’a a ranta”+ “Hango Imran da tayi yana ta faman wanke mota shi ya matuk’ar bata mamaki she couldn’t believe it,at the same time ya bata tausayi ganin yadda ya had’a zufa daga gani bai saba ba,Da sauri ta k’arasa inda yake Kanta a sunkuye k’asa murya sanyaye tace Me yasa kake wahalar da kanka Imran?me yasa zaka hana ni kai kuma kayi? Baka saba da wahala ba,ka bari ni da na saba nayi Da sauri ya juyo yana kallonta yaga yadda ta marairaice idonta sun kawo k’walla yace kar in kuskura inga hawayen nan maza mayar dasu,me ma ya fito dake,ba cewa nayi ki tafi ba Dan Allah ka bari na cigaba da wankewa, ta fad’a a shagwab’e Ya d’an yi ajiyar zuciya yace kina tsoro ne kar Hajiya ta gane bake kika wanke ba,toh be rest assure bazata sani ba,mai gadi da masu aiki duk nayi warning dinsu not to tell her,dan haka kije ki kwanta nasan bacci bai isheki ba Ta girgiza kanta tace A’ah ni bashi ba,kai nake tausayi baka saba ba Ya tuntsire da dariya yace Noor kenan wato ni kike jin tausayi Ta gyad’a kanta Yace come on kar kiji tausayina,am a strong Man zan iya jure duk wata wahala saboda ke,don’t forget alk’awari nayi xan kula dake,na kare ki,wanke motoci ai ba wani wahala bane a wajen maza,so kar ki damu kanki ,just go and rest Tsayawa tayi bata motsa daga inda take ba,kanta sunkuye k’asa,bata sake furta ko A ba,Tayi shiru tana jin wani abu na yawo a jinin jikinta game da Imran wanda bata san me ye ba? Imran wannan karon idonshi k’yam a kanta,duk da baya son kallonta,ya kasa d’auke idonshi a kanta,yana mamaki yadda duk ta damu dan yana wanke mota Yana jin wani abu na mai yawo a jinin jiki wanda shima bai san me ye ba? A hankali ya kira sunanta Noor! Ba tare da ta d’ago ba, ta amsa Na’am Kar ki damu kanki,ki tafi kawai Ba musu ta juya,jiki a sanyaye ta tafi, Ya bita da kallo,yana jin wannan abun nabin duk ilahirin jikinshi” “D’aki ta zauna tayi shiru,tana tunanin wane irin tausayi ne Imran ke mata haka?,duk yadda baba mai gadi da Lami ke tausayinta basu kai Imran ba,irin yadda take jin Imran a ranta daban da yadda take jinsu,SHI tana so a ko da yaushe ta rik’a ganinshi,tana jin muryarshi komai nashi burgeta yake,yana da wani matsayi babba a zuciyarta wanda duk duniya babu mai shi,ta rasa dalili ko kuma tsabar tausayinta da yake yi yasa haka Zuciyarta tace tabbas shine,dama zuciya nason mai kyautata mata,ko shakka babu kyautatawar da Imran ke miki, yasa kike jin haka game dashi Tayi wata sanyayyar ajiyar zuciya tace Allah ya saka maka da alkhairi Imran,(Ameen)” “Imran ko da ya gama,ya masifar gaji ya galabaita,yace ashe haka Noor ke ji(ni da nake namiji naji haka,ina ga Noor da take mace yarinya,yaji wani tausayinta ya kama shi) Sharp sharp ya sake having shower,ya shirya ya nufi office Yayi late sosai ko da ya isa office d’insu goma saura Kowa yayi mamakin lattin da yayi,an san shi da xuwa da wuri,sun sama ransu duk abunda yasa shi xuwa late ba k’aramin abu bane,shi kuwa ko a jikinshi,ko da zai rasa aikinshi idan akan Noor ne bazai damu ba A office ya kasa komai tunanin Noor kawai yake,wane hali take yanxu ko suna can suna azabtar da ita” “Cornflakes ta had’a kakkaura tasha,tayi wanka ta saka d’aya daga cikin rigunan da Imran ya siyo mata,Rigar ta mata kyau sosai charas charas da ita,ta kalli kanta a madubi,taga kamar ba ita ba sbd kyan da tayi(a ranta tace lallai komai nasan gyara, bata tab’a kyau irin na yau ba) “Kiran mun tsinanniyar can,wato ta gama wankin motoci ba zata xo ta gyara sashen nn ba,naga kwana biyu iskanci take ji xanci ubanta ne hajiya ke cewa Abu mai’aiki Abu ta tab’e baki tace hmm hajiya ai da bakya nan ko fitowa bata yi,sai dai a girka mata abinchi akai mata har d’aki,ta nad’e k’afa taci,Imran ya d’aure mata gindi Hajiya ta rik’e baki tace iyyeh samun wuri,kira mun ita da sauri” “Sai da ta k’are mata kallo sama da k’asa tace iyye anyi kilin samun wuri, hadda su kaza acin dank’o mutum bazai tsaya inda Allah ya ajiyeshi ba Noor ranta taji ya masifar b’aci a fusace tace kee Abu ki kiyayeni,kar ki manta matsayin matar Alhaji nake a gidan nan,banda k’addara ke baki isa kina gayamun magana son ranki ba,ki cigaba da zama gidan nan,kar hak’urina ya baki damar da zaki cimun fuska,zan d’auki cin mutuncin hajiya da ya’yanta dan ni na kawo kaina gidansu amma bazan d’auki na masu aiki ba Abu da mamaki take kallon Noor anya ita ce ke fad’ar magana haka Tasha jinin jikinta,ni dai hajiya na kiranki ta juya ta fita Ita kanta Noor mamakin kanta ta tsaya tana yi, yadda ta iya yin masifa (duk da a sanyaye ta fad’i maganar,daga ji bata saba fad’a ba)” “D’an kwalin rigar ta yafa a kanta ta fita Gaba d’ayansu suna zaune falo Imran ne kawai baya nan Yazeed ido ya zuba mata yana so ya tantance itace ko ba itace ba Tazo gaban hajiya ta durk’usa tace Gani hajiya Tashi! tashi tsaye in ganki Jiki a sanyaye ta mik’e Hajiya ta kalleta sama da k’asa tace wa ya baki rigar nn? Murya na rawa tace Im..im..ran Hajiya tace madallah! Ya kyauta da ya baki, dan ni kaina na gaji da ganinki cikin tsumman kayanki, ba mutunchi da k’imar gidan nan bane ace ana shigowa ana ganin mutane da yagaggun kaya, Ihsan tace gaskiya kam,dan bamu gaji tsiya ba Iman da khairat suka tab’e baki sukace wallahi dan abun kunya ne mutane suzo,su ganta a haka sai a raina mu Yazeed hankalinshi na kan Noor ya saki baki da hanci yana kallonta yana lasar baki,a ranshi yace lallai Allah yayi halitta anan Noor tana d’aga kai suka had’a ido Ya sakar mata wani murmushi,wanda ta kasa gane na me ye? Tasan tunda suke dashi bai tab’a mata murmushi ba,duk suka had’a ido murtuke fuska yake ,ya bita da matsayacin kallo buh yau shine da mata murmushi(me hakan ke nufi) Kawai tai saurin kawar da kanta gefe Hajiya tace ba tsaya mun zaki yi kai ba kamar yan sanda, wucewa zaki yi ki shiga ki fara gyara d’akuna Yazeed yai saurin cewa Ummm….mum pls ina so tamun wani aiki a sashenmu Toh taje ta maka,kina gamawa kizo ki gyara sashen nan Ta gyad’a kanta sama Yazeed ya tashi,tabi bayanshi,Gabanta na dukan uku uku _ohh shiyasa ya mun murmushi yasan muguntar da ya k’ulla zai mun Allah ya mun tsari da kai(ta fad’a a ranta)_……….. Noor na biye da Yazeed hr sashensu gabanta nata dukan uku-uku Suna shiga falo,yaja k’ofa ya rufe,Ya juya yana kallonta,kallo tun daga sama har k’asa yana murmushi tare da lumshe ido da lasar baki Noor kasa yarda tayi da irin kallon da yazeed ke mata,me yazeed ke nufi da irin kallo nan,tabbas haka Alhaji ya rik’a mata irin kallon nn daren da aka kawota,ba dai hkn na nufin abnda Alhaji yaso yi da ita shi yazeed ke son yi,Tai saurin cewa a ranta Noo it can’t be Muryar Yazeed ce ta katse mata tunani Noor! Ya kira sunanta da wata irin siga wacce bai saba kiranta ba, Bata amsa shi ba,Ya cigaba da cewa kayan nn sun miki kyau sosai,ashe haka kike da kyawon halitta,so sexy Tayi kamar bata ji me yace ba, tace fad’a mn aikin da zan maka hajiya na jirana, Ya d’an yi shiru kamar bai jita ba, idonshi k’yam a kanta,ya nisa yace ki shiga ki gyara d’akina,zan fita ki tabbatar kin gyara kafin na dawo Jin fita zai yi,yasa ta jin natsuwa ta amsa da toh,ta nufi hanyar d’akinshi Ya bita da kallo tare da yin wani matsiyacin murmushi” “D’akin Imran ya shiga yayi having shower,ya fito daga shi sai gajeren wando,Ya nufi d’akinsa Noor nata faman gyaran gado Kawai taji an rik’ota ta baya,A tsorace ta juyo,charaf idonsu ya had’u da na Yazeed,idonsa duk sun chnza yana wani lumshe su kmr d’an giya,Da sauri ta fisge kanta ta tunkud’a shi gefe tayi hanyar fita da gudu,Ya fisgota da k’arfi ta fad’o kan gado Noor plss ki taimaka mn,i am in desperate need of you,zan iya shiga wani hali idan baki bani had’in kai ba Noor innalillahi wa’inna ilaihir raji’un ta furta wannan wacce irin bak’ar rana ce take gani,Cike da tashin hankali,hawaye na bin kuncinta tace Yazeed kasan me kake shirin aikatawa kuwa,ni fah matar babanka ce,ko ni ba matar babanka bace babban zunubi kake shirin aikatawa ballatana ina matsayin matar babanka, kaji tsoron Allah Yazeed ta sake fashewa da matsanancin kuka A hankali ya shafa fuskarta tai saurin bige hannunshi ta mik’e tsaye Haba Noor ki tausaya mun mana,ni ba ruwana da natsayinki na matar babana,kawai ni dai ki biya mn buk’atata ni kuma na miki alk’awari zan baki duk wata kulawa,bazan k’ara bari su mum su cutar dake ba Da k’arfi tace Noo Yazeed bazan iya ba tana girgiza kanta,kasan bala’i da masifar dake cikin zina kuwa balle zina da matar babanka Gwiyoyinshi ya kai k’asa,kamar zai yi kuka yace Dan Allah Dan Annabi Noor ki taimaka mn ki tausaya mun,Wallahi zan shiga wani hali idan baki bani had’in kai ba A fusace tace ko mutuwa zakayi sai dai ka mutu Yazeed Tayi hanyar fita,ya fisgota da k’arfi ya jefata kan gado Dan kinga ina rok’onki toh zan miki ta k’arfin tsiya Dan Allah Yazeed kayi hak’uri kar kamun komai ni fah matar babanka ce Idan baki daina cewa ke matar babana bace zan fasa bakin ki wlh Tana kuka,tana k’okarin k’wace kanta,shikuma yana k’okarin had’a bakinshi da nata,Aka turo k’ofar d’akin Imran tsaye yayi yana kallonsu(bai gane noor bace dan bai ga fuskarta ba,ya d’auka matan banza da ya saba kawowa ne)jikinshi yayi sanyi a ranshi yace Yazeed bazai bar halin nn nashi na kawo mata ba koh Yayi tsaki ya juya zai fita Yaji muryar Noor nacewa plxxx yazeed ka k’yaleni kaji tsoron Allah Muryar wa nake ji kamar ta Noor,ya d’an tsaya,ya sake ji tace plxx Yazeed ka k’yaleni kaji tsoron Allah Ko shakka babu wannan muryar Noor ce A fusace da zafin nama Ya fisgo Yazeed ya jefar dashi k’asa,bai k’ara shiga tashin hankali ba sai da yaga Noor kwance kan gado,tana ta kuka A fusace,fuskarshi ta kad’a tayi jawur saboda b’acin rai ,ya jawo Yazeed tsaye ya fara falla mai mari, ya mishi mari yafi goma ya fara naushin shi👊🏻👊🏻,yana ball dashi Yazeed na cewa Dan Allah Yaya kayi hak’uri wallahi sharrin shaid’an ne Imran ko kad’an bai saurareshi ba ya cigaba da dukanshi ko ta ina,Yana cewa yanzu iskancinka har ya kai ga Noor matar babanka Yaya Dan Allah……kafin ya k’arasa ya kai mai wani wawan naushi a baki,bakinshi sai jini,Noor duk ta gama tsorata da irin dukan da Imran ke mishi, Noor na kuka tace Dan Allah Imran ka k’yaleshi Yau sai na kashe shi,sai na illata shi,iskanshi har ya kai ga KE,idan zai lalata ya’yan wasu toh banda KE Noor ta mik’e ta fita a guje sai sashen hajiya Hajiya! Hajiya! Kizo Imran na dukan Yaxeed zai kashe shi A firgice hajiya ta mik’e ,tabi bayan Noor da gudu,suma su ihsan suka bita” “Ko da suka je, Yazeed na kwance cikin jini baya numfashi,Imran na zaune kan kujerar falon yana huci,yana maida numfashi da k’yar, Gaba d’ayansu hankalinsu yayi mummunan tashi,Noor kad’ai ce ke furta innalillahi wa’inna ilaihir raji’un,Su ihsan ihu kawai suke da kuka Hajiya tayi kan Imran,tana marinshi tana dukanshi ta ko’ina,ka kashe dan’uwanka ka huta,me ya maka ka kashe shi,Imran anya kai d’a na ne kuwa? taya zaka kashe k’aninka jininka uwa d’aya uba d’aya,kana cikin hankalinka kuwa,ka kalli abunda ka mishi har ka kashe shi,Imran kai ba d’ana bane wallahi,d’an da na haifa bazai kashe d’an uwansa ba Imran janye hajiya yayi daga jikinsa ya fita ya bar d’akin, Hajiya ta bishi da kallo tace ko shakka babu,kai ba jinina bane Imran,biri yayi kama da mutum” “Ko kad’an Imran baya nadamar abnda yama Yazeed,ko da Yazeed zai mutu shima a kashe shi bazai yi nadama ba,Dan gwara yazeed ya mutu akn ya aikata mummunan aikin da yayi niyya akan Noor,bazai tab’a iya bari wani ya cutar da Noor ba ko ya kusanceta,a yadda yake ji yanzu ko Alhaji da yake da hak’k’i a kanta yaga zai kwanta da ita,sai yayi yunk’urin hana shi(Nikm Zee nace Dank’ari mak’ari babbar magana wai d’an sanda yaga gawar soja) ……………………………….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *