YANAYIN RAYUWA CHAPTER 10

😔YANAYIN RAYUWA😱😭🌸🌷💐🌷🌷🌸 CHAPTER 10 By 

halimatusadiya Saleh Akabar aunty hapsat akanta, ana kiran sallah azahar hapsat ta shiga toilet tayi alwala,ta fito tayi sallah, ta dade akan sallah yan tana lazimi kafun ta tashi tanade sallaya tayi ta maidashi gun zaman sa. Gun zali ta kuma da haryan zu barci take,turo kufan taji akayi da sallama,amsawa tayi. Ya Umar ne ya shigo da leda a hannun shi, ” Sannu yayah.” Aunty hapsat tace mai Ya amsa cikin sakin fuska yace ” yauwa ya me jiki,hope da sauki yanzu.” Kallon inda zali take tace ” Da sauki kam dun tunda zu datayi barci bata farka ba.” Cikin yanayin tausayin kanwar tasa yace ” Wich her speed recovery.” Ajiye ledan yayi ya juya ze fita se kuma yadawo, sayawa yayi a kanta yasa hannun sa a wuyan ta ya ji jikin ya rage zafin, kafun ya juwa ze fece yace ” Inta tashi kikirani.” Kai kawai hapsat ta daga mai,yana fita bai juma ba mom tashigo,wuri tasamo tazauna kusa da hapsat. Tace ” Yade hapsy bata tashi bane.” Hapsat tace ” eh! Kinsan tasha wahala,kuma bata sababa shiyasa, amma mom gaskiya zali ta tsora tani.” Murmushi mom tayi tace ” kinsan kuwa dana shi, Allah de yakawu mata sauki.” ” Ameen.” Hapsat ta amsa Mom tace ” ban jakan chan mana.” Dauko mata hapsat tayi,bude wa mom tayi ta ciro kudi zeyi 5k tace ” Gashi wannan,kije kishirya kije kasuwa kisaya mata p*** da su skin tight, se ta hada da nata tayi amfani dashi kafun nan, kisaya Ginger, garlic,da tumeric. Baze wuci 200 bane azu an tapasa mata tanasha saboda kariya daga infection dun shima yanasa ciwon ciki lkc period.” Karba aunty hapsat tayi tace ” Ok sena juyo inzan rafi.” Fita tayi tayi dakin su dun yin shiri, bude ledan mom tayi maganine wanda ya Usman yace a saya Umar yasa da kuma fruit a dayan ledan. Murmushi tayi ta kalli zali tace ” Innama ace inkin gane mekike yi ki yarda da dana a masayin mijin ki, da kuwa zanfi kowa farin ciki a duniya.” Abunda mom bata sani ba tun shigo wanta zali ta tashi amma taki bude ido ne tana kwance ne kawai saboda jikin ta ba karfi. Mai da jakan tayi gun da hapsat tacire mata ta dawo ta kwanta agefen zali. After 20 minutes zali ta dan musa kadan dun gyra kwanciyan ta, dasauri mom tatashi tace ” Sannu zali jikin ne.” Bude ido zali tayi a hankali har ta bode su dukka, idon ta har sun kankance saboda wahala. Cikin murya irin na wahala tace ” Mom yunwa nakeji.” Tayi magana kaman zata yi kuka,dukda yanzu bata jin kumai se kasala da yunwa. Murmushi mom tayi tace ” Ok, bari maryam ta kawu miki abinci.” Sauka zata yi daga kan bed din taji hapsat na bude kufa. Issa tayingun su tace ” Harkin tashi sannu ko ” Kai kawai zali ta daga mata,juyawa hapsat tayi gun mom tace ” To zan wuce.” Cikin macin rai mom tace ” daman tun dazo me kikeyi ?” Yamusa fiska hapsat tayi tace ” inna shiri man.” Mom tace ” to kiyi maza kitafi,inkin fita kice ma maryam ta hada tea amma karta sa sugar sosai tasa abinci a plate ta kawu min da ruwa, khalil kuma ya dauko min plate da knife ya kawunin, yanzu nan inna jiran su, kar subsri in fito.” Dasauri ta amsa da to tayi waje dun gudun kar takara batama mom rai. Khalil da maryam ne suka shigo dakin rike da abunda mom tace sukawo mata. Gaishe da zali sukayi da jiki da gyr ta iyya amsa wa, khalil ne ya fita ya barsu. Mom takalli zali ceke da kulawa tace ” Uwar masu gida tashi ki ci abincin to.” Tashi tayi tasaukar da kafanta kasa a hankali,abincin mom ta bata tafara ci tana yamusa fiska, dagyr ta iyya ci kadan ta jiye, tea mom taba ta shima kadan tasha,se fruit da aka bata apple kawai ta karba ta kusura sau biyu tace ya isheta. Magani mom ta bare ta bata tasha da gyr dun batasun magani kuta kuta. Tana gamawa mom tace ” inkin dan huta se kije kiyi wanka ki gyra kanki.” Cikin kunya ta amsa da” to” kanta akasa dun ma se yanzu ta tuna me ke damun ta,dun already aunty hapsat nagaya ma batun shi tun kafun takai haka. Fita mom tayi tabar maryam a gunta mom nafita maryam tace ” Yammatan yayah an girma yanzu kam 😜” Tafada cikin zulaya, turo baki zali tayi tace ” Amam Adda Maryam banaso.” Tayi magana kaman zatayi kuka, maryam tayi dariya kafun tace ” Hhhhhh nayaushe kuma,daga baya kenan kede tashi kije kishirya kar yaya yazo yasamo bakiyi wanka ba.” Hada fiska tayi tace ” To inna ruwana dashi base yazoba, wannan ke yadama.” Ta fada tana kukarin tashi,dariyan rainin wayo maryam ta mata. Zali kam bata kara cewa kumai ba dun kar tagaya mata magana, dun sister tace. Wanka tayi ta shirya cikin wani gawon blue da stone da aka zuba ma rigan shi yafitar da kywn shi ta daura kanta da karamin gellen shi. Tayi kyw kaman ba ittane take kwance dazo ba,maryam kam se binta kawai take da ido dun tayi mata kyw matuka. Juyowa zali tayi daga gaban dress merron datake tace ” Muje waje ko kina nan .” Tashi maryam tayi batare da tace kumai ba dun intana sake ma zali dewa zata rena ta. A kitchen suka sami mom dun ba kuwa a falon sun fara tayata sega su ya Usman sub dawo. ” Yayah sannu da dawwa.” Inji zali tafada tana kallon ya Umar koze yi magana. Ya Usman yace ” Yauwa little sis yajikin ki.” ” Da sauki” tace mai Maryam ma tamusu sannu da dawwa, zali kam ta kasa yima ya Umar magana se da yace mata ” Yammata ya jiki.” Sunkuyar da kanta kasa tayi tace ” Alhamdulillah.” Gaishe da mom sukayi kafun suka wuce dakin su. Muryan aunty hapsat sukaji tana cewa ” mom i am back.” Mom tace mata ” ok u ar well com.” Daki tawuce da kayan . Suna gamawa abinci duka jera a daining , zali ta wuce dakin su, tana shiga ta tarar da aunty hapsat har tarar da aunty hapsat ta chanza kayan ta. Jin ambode kufa ne yasa aunty hapsat dagowa taga waye ne, zali tagani murmushi tayi mata itta ma zalin murmushi tayi. Aunty hapsat tace ” Mom na daki ne?” ” Eh!.” Kawai tace mata kafun tasamo gurin tazauna,fira aunty hapsat tayi ta wuce dakin mom. Zali kam hapsat nafita tayi tagumi tace aranta ” Wai me mom kenufi ne in yarda da auren ya umar ?bayan kuma tacs inna samo wanda nake so ze sake ni, kuma yanzu tace inna yarda zata fi kuwa farin ciki. To ni yazanyi ne gaskiya bazan iyya son shi amasayin miji ba, i can’t do that he is my brother.” Jitayi hawaye nabin kuncin ta da batasan name neba,share hawayen ta tayi dataji anafaman bude kufa. ” Zali mom is calling u .” Aunty hapsat tace tana fada tayi kuma dakin mom. Zuciyan tane yasinke fatan ta kar Allah yasa maganan auren su da ya Umar ne. Fita tayi jiki a sanyaye tayi dakin mom, da sallama tashiga aka amsa mata cikin fara’a wanda yasa itta ma tayi murmushi batare da shiri ba. Guri tasamo ta zauna tace ” Gani mom.” Mom tace ” yauwa, maman mu,kakan su, ga wayen nan kayan kiyi amfani dashi kihada danaki kafun nan”. Tafada tana nuna ledan kayan da hapsat ta kawo,dauka tayi tace ” Nagody mom Allah saka da akhairi.” Murmushin jindadin maganan ta tayi tace ” Ameen Ameen, ke kam bake gajiya da godiya. Allah miki albarka yata.” Wani dadi zali taji har cikin ranta, har taji abuda ke damun ta yatafi, haka duk lukacin da mom tace mata yar ta se ta jidadi ji take kaman ummi ne tace mata. Daukan ledan tayi ta sa a Wooldrup, nan ta zauna suka yita hira har aka kira mangariba,kuwa yawuce dun yi sallah itta kam ta dauki wayan mom tafara game. Allah barmu tare Fan’s. 😔YANAYIN RAYUWA😱😭🌸💐🌷🌷🌷🌸🌸 By halimatusadiya Saleh🥰 After sun idar sallah suka kuma falo. Tashi maryam tayi tanufi daining,zali ta kalle tace ” Sis nima wlh enwa nakeji.” Binta tayi sukaje daining din suka ci abinci,bamai yawa zali taciba,se fruit data dan sha. Setting room suka kuma nan fa suka kama hira,har su ya Umar suka dawwo. Zali kam inanyi magana daga eh, a’a, to kawai take fada,dun duk lkcn da idonsu yahadu daya aliyu se ta tuna maganan mom. Daga tagaji da zama tace ” Mom nina ciga ciko seda safe.” ” Atashi lfy ” mom tace mata. Tashi tayi tawuce dakin mom,kwanciya tayi, tanata tunanin maganan mom har barci ya dauke ta. ✨✨✨✨✨✨✨ Dad na falon sa da mom. Gyran murya dad yayi yasa,yasa mom ta juya tana kallon shi,dun tun dazu ta lura kaman yanason yin magana. Dagowa yayi ya kalli mom yace “Mom khalil,kinsan de yanzu yaka mata ace hapsat ta fitar da miji,seki gayamata. ” Tace ” To, Allah yabata miji nagari.” ” Ameen” dad ya amsa mata,nan suka cigaba da hiransu. Zali ce da aunty hapsat adaki,tana tayata nade kayanta. Budewan kufan dasuka jine yasa suka dago,mom ce tashig. Da faraa tace ” nade kaya kukeyi ne?” Zali ce tace ” Eh mom ,kin fito?” ” Am,inna maryam ne?” Mom ta tambaya Aunty hapsat tace ” Tana kitchen,tana wanke wake ne.” Kai kawai mom ta daga,kafun ta kalli hapsat tace ” If u ar done, meet me in my room.” Tafada tana fita dakin,hapsat tace ” Ok mom.” Suna gama nade kayan ta wuce gun mom zali ko tashiga wanka. ” Assalamualaikum.” Hapsat tace yayin da take bude kofan dakin mom. ” Wa’alaikumus salam.” Mom ta amsa tana kallon kofan dakin . Shiga tayi ta samu guri tazauna akan sofa dake dakin. Murmushi mom tayi tace mata ” Yayan ku sun dawo ne.” ” A’a, may be suna hanya.” Kai kawai mom ta jijjika alaman eh,nan ta kwashe abunda sukayi da dad tagamata. Hapsat kam tunda mom tafara magana ta sunkuyar da kanta kasa ko a ba iyya ce kumai ba. Shirun da yayi yawane yasa mom tambayan ta ” Lfy kikayi shiru, ko baki shirya bane?” Kai ta girgiza,nan mom tagane dauyin magana takeji. Murmushi mom tayi irin tasu ta manya tace ” To zanbaki lkc inkinyi shawara se kimin magana,dun ke kawai muke jira, zaki iyya tafiya.” Ay kaman jira take mom tayi magana,tashi tayi tafita jiki a sanyaye. 🥰🥰🥰🥰🥰🥰 Yau saura kwana biyu a bude school,se shirye shirye suke yi musamman ma zali da zataje ss1. Nunnu nama mom kayan da suka saya takeyi,mom kam se binta take da ido. Monday 🌷 Dawuri taga shirin ta cikin uniform nata,riga,wando da himar. Rigan da himar white color ne se wando kuma black,tasa socks white da Snickers black daya sha Polish. Jakanta tadauko tayi waje,a falo tasamo, har maryam da khalil sungama itta suke jira. Gun mom tanufa da take zaune a daining tana breakfast. Kallon mom tayi da murna tace “Mom zamu wuce,se munda wu.” “Allah kiyaye hanya” mom tace ma “Ameen” ta amsa tana faman juyawa batasan ya Umar na gunba se kawai taji ta buge mutum. Dasauri ta daga idon ta tana sun duba wayene, kawai taji ankama ta. Hada fiska yayi yace ” Wai kekam bakida idone?” Jan hannun ta takeyi dun yasake ta saboda wani irin shock dataji jikin ta keyi. Tace ” Kaiyi hakuri,ka sakeni.” Ture tayayi yayi wuce wanshi,ze shige dakin su mom ta dakamai sawa tace ” baka da hankaline, dazaka ture ta intaji ciwo fa.” Bayi magana ba yawuce dakin su ranshi abace yace ” Wai kan zaline mom zata mai fada,to zata gani se yayi maganin ta kuwa,batana ganin ta girma yanzu ta kuyi taurin kaiba,she will see.” Yafada yana wani kunkuni shikadai. Tashi tayi daga fadowan datayi tawuce gunsu maryam. Mom tace mata ” Sannu zali,bakide ji ciwo bako.” Kai tadaga alaman ehh,nan fa suka wuce dun lukaci ya kusa. After suntafi ne,su ya umar suka shirya suka tafi kasuwa da dad. Suna issa kasuwa,shagonan biyu dake guri daya daaka zuba a tamfufi, lessees, shoe’s, dade sauran su. Yanuna ma Umar nashi,ya nuna ma Usman nashi.kafun suka wuce office na dad. 💞💞💞💞💞💞💞 Suna dawwa school, adaki zali tasamu mom. Tanashiga ta ajiye jakanta ta cire hijab nata ta ajiye. Mom ta kalle ta tace ” Uwar masu gida andawo kenan.” Murmushi tayi tace ” Eh! mom, ya gida.” Tafada tana faman cire socks nata, mom tace ” Alhamdulillah, ya studies.” ” Alhamdulillah mom.” Cire kayanta tayi tashiga toilet dun wasa ruwa. Tana shiga mom ta fita waje. Tana fitowa ta shirya cikin riga da wando, ta shafa lotion dinta tasa fissa turare tafita falo. Guri tasani kusa da mom ta zauna,kallon mom tayi cikin fara’a tace ” Mom daman innaso weekend inji induba ummi.” Murmushi mom tayi tace ” Ok Allah kaimu.” ” Ameen” zali tace. By halimatusadiya Saleh 💞

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *