ITA CE QADDARATA CHAPTER 9

ITACE QADDARATA CHAPTER 9

  Noor jiki a sanyaye ta mik’e,ba wanda yace mata uffan ta tashi ta bar falon,Yazeed ya bita da kallon sha’awa Hajiya har lokacin bata ce komai ba,Yazeed shima ya tashi ya bar falon,haka su Ihsan kowa ya tashi Hajiya kad’ai ce zaune tana al’ajabi+ Imran da ya bar falo,d’aki ya nufa,ya kwanta kan gado yana kallon ceiling duniya ya rasa me ke masa dad’i,Yana maganar zuci “taya za’ace a rabani da Noor,bayan bazan iya jure rashin ganinta ba,bazan iya bari ta cigaba da shiga halin k’unci,i must find a way out,but ita a yadda na lura bata damu ba,duk da taji furucin Hajiya still take goyon bayan Yazeed,Bayan duk gidan nan a wurina kad’ai take jin sanyi, but still ta gwammace a rabamu da na fad’i laifin yazeed,Noor why are yhu like diz? Bazan iya jure rashinki ba, wlh da na fita harkarki a yau d’in nan, tunda ke kika zab’i haka,amma tausayinki yama zuciyata yawa,gashi yanxu wasu feelings nake ji game dake, bansan na me ye ba,da na k’yaleki dasu Hajiya da yazeed” Ya k’arasa maganar kamar zai yi k’walla Ta b’angaren Noor itama kwance take,hawaye na kwaranya daga idonta,Tana maganar Zuci “Ya zanyi da rayuwata an rabani da Imran,shi kad’ai nake jin sanyi a gurinshi,bani da wani masoyi da ya wuce shi,rayuwata na cikin had’ari muddin babu Imran a kusa dani,gashi ina son ganinshi a ko da yaushe,ina jin muryarsa,Hanya d’aya ce in fad’i abunda Yazeed yamun kuma bazan iya fad’a ba,Ya Allah ka kawo mun fita” Ta fashe da matsanancin kuka Khairat,Ihsan da Iman ne zaune a d’aki suna hira Ihsan tace “ni har yanxu i couldn’t believe it Ya yazeed ya hana Mum dukan shegiyar can” Iman tace “Nima wlhy har yanxu abun yawo yake mun a brain, yadda ya tsani yarinyar nan but shine yau da kareta” Khairat tace “ni duk ba wannan ba mamakin dukan da Ya Imran yama Ya Yazeed nake,akan kawai ya mare ta,ki duba so da shak’uwar dake tsakaninsu amma a kanta ya mishi haka,ni na rasa gane me ya d’auki Noor d’in nan” Ihsan tace “shegiya wlh ni ban yarda da ita ba,yanzu haka Aljana ce ko mayya,Daddy ya jajubo Mana” Khairat tace “koma wacece zata ci ubanta dan wlh na tsaneta tunda naga Ya Imran na rawar k’afa a kanta” Iman tace “ke fah kishin tsiya ne dake sis,ba fah aure tsakaninsu amma kin kasa kwantar da hankalinki” “Ba zaki gane bane Sis ina masifar son Yayana at d same ina kishin shi,ko kad’an bana so naga mace ta rab’e shi” “Son maso wani kenan,shi kinga bai san kina yi ba” “Very soon zai sani” Ihsan tace ” yanxu ba wannan ba,ya kamata muyi planning yadda zamu ci uban yarinyar can yadda da k’afarta sai ta bar gidan nan ko Daddy bai saketa ba,dan wlhy i hate seeing her” Nan suka yi k’asa k’asa da murya suna planning yadda zasu yi(duk yadda na kai ga kasa kunnena banji me suka ce ba😉) Yazeed sad’af sad’af ya shige d’akinshi tsoron had’uwa yake da Imran,Mamaki kawai yake yadda Noor ta rufa mishi asiri,coz idan ba don ita ba da Imran ya tona shi,Toh me yasa zata rufa mishi asiri shine bai sani ba Tunaninta ya hau yi,Suffar jikinta na mishi yawo a k’wak’walawa,wata irin masifar sha’awarta yake,dan masifa ga raunukan dake jikinshi amma ji yake kamar yaje ya tarar da ita a d’aki Har aka kwana biyu ba abun da ya faru,Hajiya kwata kwata bata bi ta kan Noor,harkokinta kawai take amma ba wai hakan na nufin ta k’yaleta bane,Su ihsan ma hka dey re busy planning abunda zasu mata, Imran kuwa duk ya sukurkuce ba damar xuwa wajen Noor ko abinchi baya iya ci sosai,bacci da k’yar yake yinshi,Noor kawai yake san sawa a ido ba dama,hajiya na nan tasa a ido, har k’ara ce mishi tayi idan yasa Noor a ido Allah yasa bata yafe mishi ba hkn ya k’ara d’aga mishi hankali,har mamakin kanshi ya rik’a yi,Me yasa zai damu kanshi sosai haka,just dan 2days bai ga Noor ba🤔,Tunaninshi yanxu bai wuce yadda zai shawo kan Hajiya Noor ma hka take bala’in son ganin Imran ba dama, sai dai tai ta kuka,bata da aiki sai tunaninshi sauk’inta Su Hajiya basu bi ta kanta ba,But duk da haka ta rasa duniya me ke mata dad’i Duk tsofaffin kayanta ta kwashe ta zubar,kayan da Imran ya siyan mata da wa’inda yasa aka d’inka mata su take sawa,Ba k’aramin kyau suke mata ba Yazeed yaji sauk’i sosai,har yanzu bai bari sun had’u da Imran ba,Imran kullum idan ya dawo daga office yana d’aki ya daina magana da kowa baya walwala kullum fuskarsa a tamke,ita kanta Hajiya wannan halin nashi ya fara damunta, Yazeed yai shirin shi tsaf zashi lectures zai biya ta sashen Hajiya ya gaisheta,Noor ta fito sanye da riga da skirt,da suka kama jikinta dai dai ita,suka mata masifar kyau Kawai suka yi kacib’us,Gabanshi ne yayi wani irin fad’uwa,yai saurin had’iye miyau tare da cewa “Ina kwana Beauty?” Noor tai saurin juyowar da kanta,ta rab’a ta gefenshi zata wuce,Ya jawo hannunta baya Juyowa tayi fuska a murtuke ta mishi wani matsayacin kallo,Wani yarr yaji a jikinshi,wata masifar sha’awarta ya sake kamashi ji yake kamar ya had’a jikinshi da nata A fusace tace “Mallam dallah sakar mun hannu” tana k’ok’arin k’wace hannunta,ya rik’e hannun gam “Haba! Beauty listen to me Now” Ta murgud’a baki tace “ka sakar mun hannu toh,kuma ni ba sunana beauty ba” Tsayawa kawai yayi yana kallon yadda take murgud’a baki,duk ya bashi sha’awa kamar yayi kissing d’inta “Zan sake ki amma sai kin mun alk’awari ba zaki tafi ba,zaki tsaya kiji me zance miki” “Nayi” Ya sakar mata hannu yana wani irin numfashi,yayi ajiyar Zuciya “Noor please Dan Allah Dan Annabi ki tausaya mun,wallahi baki san ya nake ji ba,wlhy ko nawa kike so zan baki,ke da bauta gidan nan har abada,zan baki duk wata kulawa i promise” Murmushin takaici tayi tace “lallai Yazeed kana da k’arancin ilimi,matar baban naka kake son LALATA(Sadnaf) da ita,kaji tsoron Allah,Wlh ko wahalar duniya zata kasheni bazan baka had’in kai ba,na gwammace mutuwata da wannan abun da kake nema a gurina”,bata jira mai zai ce ba,ta wuce abunta Yazeed tsaye yayi kasak’e yana mamaki wai yau shine yake neman abu wajen Noor take wulak’anta shi,”toh wlh bazan hak’ura ba,i will continue trying my luck,in ma ta kama ko fyad’e ne sai na mata” A makaranta ciwon mara ya tasowa Yazeed haik’an sai murmud’e-murmud’e yake,yasan ba abunda ya haddasa mai sai masifar sha’awar Noor,dole ya bar lecture hall,Ya nufi Grand Ibro hotel inda ya saba sharholiyarsa da yan’mata,ya kira d’aya daga cikin yan’matansa Imran ya dawo daga office da wani azababben ciwon kai,kanshi yayi zafi rau,zazzab’i na neman rufe shi Khairat ce me kawo mishi abinchi kullum Ta tsara kwalliyarta cikin material mai kyau,Khairat kyakkyawace son kowa k’in wanda ya rasa,Da sallamarta rik’e da tray a hannu ta shigo d’akin,ta ajiye tray,Ta zauna kan bedside drawer, “Yayana” ta kira sunanshi, “Na’am k’anwata” “Ga abinchi na kawo ma” “Toh sannu,je ki wajen Mum ki k’arbo mun panadol” “Subhanallah baka jin dad’i ne” “Ehh” Murya cike da damuwa tace “Sannu Yayana Allah ya baka lafiya” “Ameen k’anwata” “Bari naje na k’arbo ma maganin” Cikin mintuna kad’an sai gata ta dawo tare da Hajiya “Imran me ke damunka?” Hajiya ta fad’a tare da k’arasawa inda yake tana tab’a kanshi “Subhanallah ai asibiti ya kamata mu tafi” “No Mum ba sai munje asibiti ba” Cike da damuwa tace “Saboda me Imran” “Saboda magani na na hannunki,yanzu Mum bakya tsoron hawan jini ya kamani” Hajiya jikinta yayi sanyi tana masifar k’aunar Imran duk abunda zai tab’a shi bata so,duk cikin ya’yanta tafi son shi “Bana fata Imran, kai d’a na ne jinina,bazan so abunda zai cutar dakai ba,Bana hana ka alak’a da Noor bane don wani abu,sai dan kar zumuncin dake tsakaninka da yan’uwanka dani kaina ya samu tangard’a,tun zuwanta gidan nan muke samun matsala da kai wanda da ba haka bane,amma tunda abun ya zama haka na yarda ka cigaba da mu’amalarka da Noor but plx don’t cross ur limit,or try to stop us frm doing anytin to her” Da saurin Imran ya mik’e yace “naji na yarda Mum,tanque soo much” Hajiya mamaki take yadda ya d’au son duniya ya d’aura akan Noor(dole ta barshi ya cigaba da alak’a da Noor ko dan a zauna lafiya) Khairat ta cika,haushi duk ya gama dabaibayeta ” yanxu akan Noor ne Yayana ya kwanta ciwo,ji yadda yake murna dan ance ya cigaba da alak’a da ita wlh sai naci uban yarinyar nan dole ta fita sabgar Yayana” Taji hawaye na k’ok’arin gangaro mata Hajiya ta lura da ita,dan haka tai saurin jan ta suka fita d’akin Bata mata magana ba har sai da sukaje sashenta,har d’akin Hajiya sannan tace “Haba Khairat me ye na tada Hankali Imran naki ne ke kad’ai,ba fah aure tsakaninsu da Noor dan haka tada hankali na me,Ke Matar Imran ce,nan ba da dadewa ba zan mishi magana,In shaa Allahu wata shekara kamar yanxu kina gidan Imran,k’ila ma kin kusa haifo mun jika”,Khairat tai saurin sa hannu ta rufe fuska ta fita d’akin cike da murna,Hajiya ta bita da kallo tana murmushi Duk da haka Khairat ta riga ta d’aukarwa kanta alk’awari ba zata kyale Noor ba,hakanan hankalinta yak’i kwanciya game da Noor,masifar kishinta take………………… Imran mik’ewa yayi cike da murna,gaba d’aya ya nemi ciwon kai ya rasa( _dama na missing d’in Noor ne_) Toilet ya shiga ya watsa ruwa,Ya sake shiga cikin kaya yan kanti marasa nauyi,Ya taje gashin shi tare da shafa ma mai(mai k’amshi da sa kai santsi)Ya feshe jikin shi da turaruka designers masu masifar k’amshi _Gaskiya ba k’arya Imran ya had’u yana cikin jerin maza ajin farko_ (Ni Zee a raina sai cewa nake wannan gayun, Imran ina zashi?).+ Garden ya nufa,Ga flowers da itachen wurin nata kad’a iska mai dad’i da sanyi,kasancewar yanayi ne na damina(Ruwa) Mai kula da garden ya kira Yace “ya kira mishi Noor”. Noor na zaune d’akinta kan dadduma,ta idar da Sallah tana lazimi, Taji sallama,mik’ewa tayi ta lek’a, “Wai kizo inji Imran yana garden” Ta d’an zaro ido waje “ni kuma?” “Eh” A ranta tace “me zai sa Imran yace nazo?,baya tsoron Allah ya isa Hajiya ta kama shi but nasan Imran nada ilimi hknn ba zai ce nazo ba,ba tare da izinin Hajiya ba” Tayi sanyayyar ajiyar zuciya “kaje kace mishi ina zuwa”. Cikin d’aki ta koma,ta nannad’e daddumar,hijabin jikinta ta bari bata chanza ba,Zuciyarta cike da farin ciki zata ga Imran Yana zaune kan d’aya daga cikin kujerun iska mai dad’i na ratsa shi,yana kallon sararin samaniya Noor cikin siririyar muryarta tace “Assalamu Alaikum” Da saurin ya waigo yana kallonta wani kyau yaga ta k’ara mai sai dai ta rame,Ya mata murmushi tare da amsa sallamarta, Kujerar kusa dashi ta zauna,tana kallon k’asa hknn ta tsinci kanta da jin kunyarshi Tsawon seconds ba wanda yace Uffan Imran yayi breaking silence d’in da cewa “Noor ya kike?” “Lafiya lau” ta fad’a murya a sanyaye “Ya naga kamar bakya farin cikin ganina?,ko da yake nasan ni kad’ai nayi missing d’inki,ko zamuyi shekara bamu ga juna ba,ba zaki damu ba” Tai saurin d’agowa ta kalleshi (a ranta tace lallai ma baka san yadda na rik’a ji ba) Suna had’a ido tai saurin sunkuyar da kai “Kin kalleni ko k’arya nayi” “Baka yi k’arya ba amma ka fad’i ba dai dai ba” Ya d’an yi murmushi yace “Noor ni fah hadda rashin lafiya akan rashin ganinki na rasa dalili ko dan shak’uwar da muka yi ne🤔” Shiru tayi “ashe bani kad’ai ke jin haka game da kai ba,ko shakka babu shak’uwar da mukayi ne”ta fad’a a ranta “Kinyi shiru” ya fad’a tare da tsare ta da idanu “Eh shak’uwar da mukayi ne ta jawo haka” “In shaa Allahu ba abunda zai k’ara rabamu muna nan tare abadan da’iman” Tayi murmushin takaici tace “dama hakan zai kasance but kash watarana dole zamu rabu daga ranar da Alhaji ya sakeni shikenan rabuwar tazo” ta k’arasa maganar kamar zata yi kuka “Ki kwantar da hankalinki Noor,ko Alhaji ya sake ki ina tare dake,ke ko aure kika yi bazan gujeki ba,sai dai in kece kika zab’i na barki” “Har abada bazan tab’a zab’ar haka ba,kamun abunda har in mutu bazan tab’a mantawa dashi ba” Sosai yaji dad’in furucinta Haka suka cigaba da hira mai dad’i da natsuwa,Yake gaya mata In shaa Allahu sai yayi iyakar k’ok’arinshi yaga ta shiga makaranta( _bata damu ta tambayeshi ya akayi Hajiya ta yarda ba,dan tasan ko shakka babu ta hak’ura_) Sai gab da magriba suka tashi,Suna ji kamar kar su tashi,suyi ta zama da juna har k’arshen rayuwarsu( _Kowanensu naji ina ma Aure ya halatta a tsakaninsu da sun more aure_. Wata irin sabuwar shak’uwa ce ta shiga tsakanin Imran da Noor,idan baya office toh suna garden suna hira,idan ya dawo lunch tare suke ci a garden,haka abinchin dare( _sai dai kowa a plate d’inshi_) Har d’aukarta yake su fita yawo,yayi mata siyayya Hajiya ta sani amma bata da damar hana su,gudun kar Imran ya kwanta ciwo _but tsanar Noor na nan a ranta_ Su ihsan abun ba k’aramin haushi yake basu ba,tun ba Khairat ba,tafi kowa jin haushi( _ita da zai aura ita ya kamata suyi wannan shak’uwar ba Noor ba_) Tasha alwashin raba su. Da sanyin safiya Noor na kwance k’udundene cikin bargo tana sharar barci,Taji an fisge bargon da k’arfi,Tai saurin bud’e ido tana mutsittsika su Hajiya ta gani tsaye a kanta “Hutun ya isa haka,sai ki tashi zuwa share-share da gyaran gida” Noor bata yi mamaki dan tasan Hajiya ba zata k’yaleta ba “Toh” Hajiya ta juya ta fita fuuu Wanke fuskarta tayi,tayi brush dama tayi sallah tunda asuba ( _wani abun mamaki shine shekarar Noor goma sha shida amma har yanzu bata fara al’ada ba,ita kanta abun na damunta,buh wani lokacin sai tayi tunanin k’ila daga yanayin halittar tane_). Sharar falo take tayi,Hajiya na zaune gefe tana shan tea da chips,Imran yai sallama ya shigo,office zashi ya shigo ya gaida Hajiya, _Ganin Noor na shara, ranshi ba k’aramin b’aci yayi ba,kawai ya basar dan bashi da yadda zai yi,yana yin magana Hajiya zata taso mishi,yana tsoron abunda zai sa a k’ara rabashi da Noor_ “Mum ina kwana?” “Lafiya lau Son har ka shirya zuwa office ne?” “Eh mum” “Dama magana nake so muyi dakai,dan anjima zan tafi Zaria” “Lafiya dai ko?” “Lafiya lau ” “Toh Alhamdulillah” “Ina so ka saurareni da kyau,akan Khairat ne,a bisa dogon tunani da nayi da nazari,Kaga Khairat marainiya ce,tana buk’atar kula da kuma wanda zai rik’eta tsakani da Allah,Dan haka na yanke shawarar had’aku aure” A kid’ime ya kallo hajiya Yace “Aure” Noor ma kallon hajiya tayi a kid’ime “Sosai kuwa aure ko akwai wani abu ne” Muryarshi na rawa Yace “naga ai Khairat yarinyace bata isa aure ba, kar taga an shiga hak’k’inta” “Ba wani yarinya sa’aninta nawa aka ma aure,zance shiga hak’k’i kuma babu shi dan Khairat na sonka,kasan mace da kunya shiyasa ta kasa fad’a ma” Shiri yayi ya rasa abun cewa _bai tab’a jin yana son khairat da aure ba,yana dai mata son yan’uwantaka,Khairat nada qualities d’in da ake nema a wajen Matar aure but shi sonta ne ba yayi_ “Kayi shiru” “Zanyi tunani akai” “Ba shawara nake nema a wajenka ba,umarni nake baka,yau zanje Zaria mu tattauna da Maryam(maman khairat) dan bana so a d’au lokaci” Kai kad’ai ya iya gyad’a mata,ji yake kamar ya kurma ihu Jiki ba k’wari ya tashi ya bar falon Hajiya ta k’ara da cewa “Auren ka kai da Khairat kamar anyi an gama,ko kana so ko baka so,yo me ye khairat bata dashi,kai da ya kamata kafi kowa farin ciki an had’a ka da yar’uwarka” Noor k’irjinta taji yana masifar zafi kamar zai fito waje,hankalinta gaba d’aya ya tashi,hawaye na kwaranya daga idonta tambayar kanta take “me ye sa nake jin haka Dan ance Za’a had’a Imran da khairat Why? Why?” Fans ko zaku bata amsa😉 Da k’yar ta gama shara tayi mopping da goge goge,dan har wani dishi dishi take gani. Ranar taci kuka kamar ranta zai fita da ta tuna furucin Hajiya,sai taji wasu sababbin hawaye,zuciyarta na zugi _ta rasa dalilin kukanta_ Imran da ya dawo lunch,yai ta knocking k’ofar d’akinta tazo suyi lunch Tana ji tayi banza dashi _hakanan taji bata son ganinshi,a ranta tace “kaje kaci da Khairat mana ita da zaka aura”_ Da yaji shiru yayi tunanin ko bacci take,tunda yau da wuri ta tashi Haka ya tafi ranshi bai so ba,Lunch d’in kasa ci yayi sai dai ya koma office yanaji dama bai dawo gidan ba. Kiran Sallar azahar da taji yasa ta mik’ewa ta shiga toilet,Kanta taji na masifar sarawa kamar zai cire,Da k’yar tayi sallah,nan ta Zauna kan dadduma tana lazimi,zuciyarta na zafi,Al Qur’ani ta d’auko tana karantawa,wani sanyi taji ya ziyarci zuciyarta Bata ankara ba taji bacci na son awon gaba da ita,Qur’anin ta rufe tayi addu’a ,anan bacci ya d’auketa kan dadduma.+ Imran a office kasa cigaba da aikin komai yayi,tunanin Noor kawai yake, Yacewa kanshi “Da tana da waya da na kirata naji lafiyarta ko nan in rage zafi” Yayi siririn tsaki da ya tuna had’ashi aure da Khairat da ake so yi”Taya zan auri wacce banso? Ina tausayawa Khairat zanso ta samu wanda zai rik’eta amana,kwata kwata ba aure a tsarina yanzu,Am just 23 ina da sauran lokaci bansan rushing d’in me Mum keyi ba,kuma ta rasa da wacce zata had’ani sai Khairat She is 19 ba sa’ar aurena bace,Ya Allah! Help me through” ya fad’a tare da dafe kanshi Knocking yaji anayi, “Yes! Waye? Come in” “Naseer ashe kai ne?” “Eh wlh” ya fad’a tare da zama kan kujera,Ya cigaba da cewa ina ta kiran ka baka picking” “Really? ga wayar a kusa dani fah but banji ringing ba” “Ina fah zaka ji ringing kana can kana aiki,Wlh ina mamakin yadda baka wasa da aikin ka,Allah kad’ai zai biyaka” “Friend wannan karon bama aiki nake ba,na dai yi nisa a tunani” “Tunanin me? Ko dai wata ta sace Zuciyar abokin nawa ne?” “Baka rabuwa da tsokana,sanin kanka ne bani da lokacin wata,bama aure a tsarina yanzu,i want to further my studies,har PHD sai nayi” “Ok then,what are you thinking of?” Imran yai ajiyar zuciya Yace “Ina Cousin d’ita Khairat da nake baka labari wacce Dad d’inta ya rasu kwanakin baya” “Yeah” “Wai ita Mum ke son had’ani aure da ita nan bada dad’ewa ba” Naseer yayi dariya Yace “Kai abokina to me ye a ciki,kai da ya kamata kayi farin ciki an had’aka da yar’uwarka and Khairat bata da wani makusa” “My friend bazaka gane ba,bana sonta,just ina sonta as my cousin” “Hak’uri zakayi kabi umurnin Mahaifiyarka,sai kaga bin umurninta ya zama alkhairi” Shiru yayi,a ranshi yana tunanin yadda za’ayi ya auri Khairat Naseer ya cigaba da bashi shawarwari da kwantar mai da hankali. Yazeed yanzu kullum sai ya kwanta da mace,wanda da ba kullum yake yi ba,ba abunda ya haddasa mai sai masifar sha’awar Noor da yake Yau lectures d’in 12-2pm yayi,Around 3 ya shigo gidan,Sashensu ya nufa yayi having shower,Ya saka wando three-quarter da shirt mara hannu Yazeed ma kyakkyawan guy ne kuma had’ad’de Ya fito sashensu yana tako d’ai d’ai bai yadda ba shi gaye,Hanyar d’akin Noor naga yayi,Ya murd’a k’ofar d’akin a rufe Hannu kawai naga yasa a aljihu ya fiddo spare key(a raina nace lallai Yazeed kai criminal ne ko a ina ya samu spare key d’akin oho) Noor na kwance nata bacci,Yana ganinta wata masifar sha’awarta ta sake kamashi,baisan lokacin da ya k’arasa inda take ba,a hankali ya cire hijabin jikinta (Noor wani irin nauyin bacci ne dake ?da har za’a cire miki hijabi baki ji ba🤔) A hankali ya shiga shafata,yana shak’ar dadd’an k’amshin turarenta,Gaba d’aya hankalinshi baya jikinshi Kamar a mafarki taji ana shafa ta da sauri ta bud’e ido,ganin Yazeed a kanta shi ya masifar firgita ta,ta mik’e tsaye tare da hankad’a shi Jikinta na rawa ta d’auki hijabinta ta tasa Kneeling yayi “Dan Allah Dan Allah Noor ki taimka mun wlhy ina cikin wani irin matsananci yanayi” “Yazeed wlh tlh bazaka samu abunda kake so ba” “Dan kinga ina rok’on ki ko,toh ta k’arfi da yaji zan miki” Yayi kanta,Da sauri ta rarumu kwalbar turare ta buga mai a goshi sau biyu,kwalbar ta fashe,Ya dafe kai jini na tsiyaya Ta nuna shi da yatsa “Wlh wlh idan baka fita harkata ba,zan tona asirinka kowa ya sani a gidan nan,kaga daga nan girmanka ya fad’i,daga kan Alhaji,Hajiya k’annenka,masu aiki ba wanda zai sake ganinka da mutunchi a gidan nan,bunsuru kawai” Ta fice d’akin tana tunanin yadda akai ya shigo d’akin,Keyn da ta gani ta waje tace “Lallai Yazeed criminal ne,Allah yamun tsari dashi” (Ni zee nace Ameen Noor). Gaba d’aya fuskar shi ta wanke da jini,a daddafe ya fita d’akin,Ya nufi chemist d’in kusa dasu,aka mishi dressing,ya dawo gida Zaune yayi jigum a d’akinshi da tunani birjik a ranshi “Noor Noor Noor wlh bazan hak’ura dake ba kome zaki mun,kasheni kad’ai zakiyi ya hana ni cimma k’udirina a kanki,Yanxu ya zanyi” Can ya tuno wata idea yayi murmushi Yace “Yes i think this will work”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *