ITA CE QADDARATA CHAPTER 12 M
intuna kad’an Naseer ya iso gidan Ya tsorata da ganin yadda Imran ya haukata d’akinshi ga hannunshi nata jini, Ya k’arasa inda yake, Ya rik’o shi “Friend me yasa kama kanka haka? Haba! Frnd tashi muje chemist a maka dressing hannun”, Imran ya girgiza kai Yace “No! ba dan shi na kira ka ba,rad’ad’i da nake ji a zuciyata ya ninka zafin ciwon nan sau dubu” “Nasan da haka but ka bari muje a maka dressing,ji yadda hannunka ke bleeding” ya k’arasa maganar cike da damuwa “Don’t worry, bari na fad’a maka dalilin da yasa na kira ka” “Ok ina jinka” “Na yanke shawarar barin k’asar nan”.+ A kid’ime Naseer ya kallo shi Yace “Why?”, “Dan in nisanta kaina da Noor, nasan idan nayi nisa da ita na tsawon lokaci zan cire sonta a raina,but idan ina ganinta kusa dani sonta k’aruwa zai cigaba da yi wanda hakan ba k’aramin cuta bane a gareni kuma zan sab’awa Allah”. Naseer yayi ajiyar zuciya Yace “tabbas hakane kawai mafita, but me zaka cewa su Hajiya? ,and ita Noor kayi yaya da ita tunda bata da kowa sai kai?”, Imran ya nisa Yace “zan tafi Turkey ne yin masters d’ina dama tuntuni ya kamata na tafi, so ko nace musu zan tafi ba zasu zargi komai ba, Noor kuma tana tare da Allah, i will make her understand ba barinta nayi ba, sannan zan bar amanarta a hannunka, please Naseer ka kula da Noor ka dauk’eta tamkar Meenal(k’anwarshi)” “In shaa Allahu na maka alk’awari zan rik’eta amana, Yaushe zaka tafi?” “Gobe In shaa Allah” “Haba! Friend gobe fah, ba zaka bari sai jibi ba” “No am leaving tomorrow, the earlier the better, muje ka rakani office na sanar dasu” “Ok muje daga nan a maka dressing hannun”. Chemist suka fara tsayawa aka ma Imran dressing hannunshi, Sannan suka nufin office, MD ya samu ya mishi bayani zai koma ya cigaba da karatu, Md yace “ba wata matsala( dama abokin Alhaji ne) Allah ya taimaka ya bada sa’a yasa a k’aru ilimi mai amfani””Ameen nagode sir” Ya bashi cheque d’in dubu d’ari Yace “yasha ruwa a hanya” Sosai ya mishi godiya sannan ya tafi. “Imran yana ganka haka duk ba a hayyacinka ba, kamar wani mai ciwo,me ya samu hannunka?” Yayi murmushin yak’e yace “bacci nayi, hannuna kuma ina yanka lemo na yanke” “Ayyah, Sannu Son” “Yawwa mum” “Dama ina so na koma turkey nayi masters d’ina” “Kaii amma naji dad’in wannan zance tuntuni nake so ka tafi kayi masters d’in nan, Yanzu yaushe zaka tafi?” “Gobe In shaa Allah” “Gobe Goben nan?” “Eh” , “Toh Allah ya kaimu, yasa a k’aru ilimi mai amfani””Ameen” , “Zancen aurenku da Khairat fah, kasan nan da wata uku ne” “Zan dawo idan lokacin yayi”, “Toh Allah ya tabbatar mana, ya kuma nuna mana lokacin amma zamuyi kewar ka” “Ameen” kad’ai yace, Ya mik’e ni zanje na cigaba da shirye-shirye ( baya son doguwar magana,coz shi kad’ai yasan pain d’in da yake ji a zuciyarshi,he want to be alone). Kwance yake d’aki yana tunanin yadda zai tunkari Noor da zancen tafiyarshi gobe, bai san a halin da zata tsinci kanta ba idan taji zancen nan, tabbas idan ya gaya mata zata shiga tashin hankali, tashin hankalin da zata shiga zai iya chanza mishi ra’ayi ya fasa tafiya dan bazai iya jure ganinta haka ba, Mik’ewa yayi ya d’auko paper da biro ya fara rubutu kmr haka: _Assalamu Alaikum, Dafatan kina lafiya, Bansan taya zan fara fad’a miki ba,kiyi hak’uri da abunda zan gaya miki,Zan tafi masters d’ina yau,bazan iya fad’a miki baki da baki ba sbd bana son ganin damuwarki shiyasa na rubuta miki a letter, ki sani Noor ba da son raina zan tafi na barki ba sai dan tafiyar ta zama dole, But zan dawo idan komai ya daidaita,ki kula da kanki Noor Allah na tare dake, kuma ga Naseer nan Aminina zai maye miki gurbina, Ina miki fatan Alkhairi da samun farin ciki a rayuwarki, kimun alk’awari idan kin gama karanta letter nan ba zakiyi kuka ba ko ki tada hankalinki, idan kinyi zanji a jikina dan haka nake rokonki kar kiyi, Allah na tare dake_ _IMRAN_. Yana hawaye ya nannad’e letter, ya jawo bedside drawer yasa, Ya mik’e ya nufi sashen Alhaji, Alhaji yayi farin ciki sosai da jin Imran zai koma karatu, yasa mishi Albarka tare da mishi fatan Alkhairi. Noor kwance take ta rasa me ke mata dad’i, kwata-kwata bata jin dad’in jikinta, nata fad’uwa, Ga rashin shigowar Imran tun safe da ya shigo bai k’ara shigowa ba, duk ta damu shi kawai take son gani, Shiru har dare bata ganshi ba, ta fara tambayar kanta “Lafiya Imran bai shigo ba?, ko dan yaga ina jin kunyarshi? ” Tasa ma ranta tabbas dan yaga tana jin kunyarshi ne, but gobe da safe idan bai lek’o ba zata cire kunyarshi taje da kanta sashen, dan ba zata iya jure rashin ganinshi ba( Wayyo Noor har kin fara bani tausayi😰) Haka tayi bacci da tunanin Imran a ranta. Imran ya had’a komai da komai nashi, dama ba wasu kaya mai yawa ya d’iba ba, idan yaje can zai siya Daren ranar kasa bacci yayi, yana ta mirgine-mirgine a kan gado, da ya rufe ido Noor yake gani, Ya rungume pillow tsam, Yana kukan So,k’auna da zafin Rabuwa da Noor. Ana kiran assalatu ya tashi yayi alwala, ya fara gabatar da raka’atanil fijr, sannan yaySallah, A sujada yana rok’on Allah ya cire mai son Noor, Yasa tafiyar nan da zai yi shine mafi alkhairi a gareshi, Wanka ya shiga yayi, Ya shirya cikin english wears, sun mishi kyau but daka kalleshi zaka san yana cikin tsantar damuwa, Naseer yai sallama ya shigo,. Bayan sun gaisa Yace “ka dai shirya ko kasan flight d’inku k’arfe 7 ne” “Eh na shirya” “Kayi sallama da Noor kuwa?” “Wallahi banyi ba, dan bazan iya fad’a mata but ga letter na rubuta mata” Ya jawo drawer ya fiddo letter yasa a aljihu. “kana ganin hakan yafi” “Yes friend” “Ok muje”. Naseer ya nufi wajen motarshi, Imran kuma yayi d’akin Noor, gabanshi na fad’uwa, Cikin sanyin murya jiki a sanyaye, Yayi sallama ya shiga d’akinNoor dake kwance ta tashi zaune, tare da amsa sallamar. Yana daga tsaye Yace “ina kwana? Ya jiki?” Ganin yanayinshi tasan ba lafiya ba( a ranta tace ko dai Imran bashi da lafiya ne?) A fili ta amsa “Lafiya lau” Ba tare da ya k’ara ce mata komai ba ya zaro letter ya mik’a mata, itama bata ce mishi komai ba, ta k’arba Ya juya ya fita yana hawaye. Su Hajiya duk sun fito za’a tafi rakiya hadda Alhaji, Imran kam jiki a sanyaye, Hajiya sai da ta tambayeshi “me ke damunshi?” Yace “ba komai” Khairat ma jikinta duk yayi sanyi, bata son tafiyarshi hadda yan’ matan hawayenta. Noor yana fita tai sauri bud’e letter tana karantawa, Hankalinta ne yayi mummunan tashi sai hawaye, ta jefar da takardar, a guje ta fito, ko da ta fito har sun tada mota maigadi ya bud’e musu gate Da k’arfi ta kira sunanshi IMRAN, but its too late motar su ta riga ta fita, Nan ta fad’i tana kuka kamar ranta zai fita. Har suka isa airport Imran bai ma kowa magana ba, Ba abunda Zuciyarshi ke yi sai tafasa, Yana ji a jikinshi Noor na can cikin tashin hankali but bashi da yadda zai yi dole ya tafi ya barta.+ Ko da suka isa har an fara kiransu, jirginsu zai tashi, Ya kalli Hajiya yace “Mum please ki mun alk’awari idan na tafi, ba zaki cigaba da sa Noor aiki ba” kamar zai yi kuka duk ya zama abun tausayi Gaba d’aya tausayinshi ya kama ta tace “Na maka alk’awari Son” “Nagode sosai Mum” Ya juya kan Naseer “Friend Dan Allah ka rik’e amanar da na baka” “In shaa Allah Frnd, na maka alk’awari” Khairat ta marairaice tace “Yayana plx kana isa ka kirani naga numberka ta can” Kai kawai ya d’aga mata, Nan yayi sallama dasu, Yazeed duk yaji ba dad’i zai yi missing Yayanshi Suna ta waving d’inshi har ya b’ace musu, Suka juyo suka dawo jiki a sanyaye. Noor kuwa tunda suka tafi take nan durk’ushe tana kuka, Zuciyarta na mata masifar zafi, mai gadi yazo yayi ta lallashinta ta tashi, tayi banza dashi har ya gaji ya tafiyarshi ya barta nan. Anan su hajiya suka dawo suka tarar da ita, bata ishi kowa kallo ba, Yi sukayi kamar basu san da ita ba, Khairat kad’ai ce tace “ko ke kika haife shi sai haka,munafucin banza” tai tsaki ta wuce ciki abunta. Naseer ne ya k’araso inda take, Ya durk’usa gabanta duk ta bashi tausayi “Noor” Ya kira sunanta A hankali ta d’ago ta kalleshi Take yaji gabanshi ya fad’i tunda yake bai tab’a ganin kyakkyawa kamar Noor ba, a ranshi Yace “Dole Imran ya fad’a tarkon sonta, bai ga laifinshi ba” Yayi saurin kawar da tunanin Yace “Please ki kwantar da hankalinki Noor, Allah na tare dake kuma zan maye miki gurbin Imran In shaa Allah”. Cikin muryarta da ta dashe tsabar kuka tace “Me zai sa Imran ya tafi ya barni? Bayan yasan bani da kowa sai shi, Yasan tafiya zai yi ya barni me yasa ya bari muka shak’u?” Tasake fashewa da matsanancin kuka. Tausayinta ya sake kama Naseer “Please Noor kar kiga laifin Imran, wlh ba da son ranshi ya tafi ba, ina mai tabbata miki yafi ki jin zafin rabuwarku, yana da babban dalili da yasa ya tafi” “Wane dalili ne dashi? Dama duk cewa da yake zai kula dani ba zai tab’a barina ba, ashe duk karya ce” “No! Noor kar kice haka, kar kiga laifin Imran, nan gaba zaki san dalilin shi nayin haka” “Hmm” tace ta fara share hawayenta ta cigaba da cewa “Bai kamata na cigaba da zubar da hawayena a banza ba akan wanda bai damuna dani ba, ko da yake yama ce kar nayi kuka ko na tada hankalina which means yin hakan bashi da amfani, Imran baka mun adalchi ba” “Kar kice haka Noor, ba wanda ya tsani ganinki cikin damuwa kamar Imran, tun jiya yake kukan rabuwa dake, har ya tafi kuka yake”.Tayi murmushin takaici tace “kai dai kawai kana kare abokin ka ne, da ace Imran da gaske yake baya son rabuwa dani bazai tafi ya barni ba, no matter the situation bayan yasan yadda nake a gidan nan” Naseer yayi ajiyar zuciya Yace “Hmm! Noor kenan ki sani babu mai sonki da tausayinki kamar Imran, duk abunda zance miki ba zaki gane ba but ina fatan nan gaba ki gane” Murmushin takaici tayi tace “Hmm! Ni zan koma cikin gida” “Ok plx ki daina damun kanki, ki kwantar da hanklinki, am here for you” “Ok nagode da kulawarka” “Ba komai sai na dawo anjima”. Kan kafita ta fad’a ta cigaba da kuka mai tsuma rai, duk yadda taso ta tsayar da kukan ta kasa, Zuciyarta na mata zafi da rad’ad’i, Tana tambayar kanta “wane dalili ne zai sa Imran ya tafi ya barta?, Yanzu ya zatayi rayuwa a gidan nan ba Imran? Tabbas Imranya zama wani sashe na rayuwata wanda rashin shi kusa da ni babbar matsala ce a gareni, Imran me yasa zaka tafi ka barni a lokacin da nafi buk’atar ka?, baka mun adalchi ba, da kasan barina zakayi da baka bari mun shak’u ba”. Mik’ewa tayi, tayi alwala, ta kabbara sallah tana rok’on Allah ya cire mata duk wani abu da take ji a ranta game da Imran, Allah yasa tafiyarshi shine mafi alkhairi a gareta”. Imran a cikin jirgi zaune yake jigum, Ya rufe ido kamar mai bacci, ba abunda yake sai tunanin Noor, Wane hali take ciki yanzu? Ya rayuwarta zata kasance idan bashi? Shi kanshi bai san ya rayuwarshi zata kasance babu ita ba?, but ya zama dole ya nisanta kanshi da ita, Wasu zazzafan hawaye suka fara zubo mishi. Noor nan ta zauna kan dadduma tanakaratun Qur’ani, Kanta taji na masifar sarawa kamar zai cire, Ta rufe Qur’anin ta ajiye, Panadol ta d’auka tasha, Ta kwanta but still ji take kanta yayi nauyi, Zuciyarta na d’aci.+ Hajiya ta kira yan gidan daga kan masu aiki zuwa su Yazeed tace musu “Daga yau Noor bata cikin mutanen gidan nan, su d’auka cewa babu wata mai suna Noor a gidan nan, bata so taga kowa ya shiga harkarta, ko abinchi kar wanda ya kuskura ya bata, She is on her own ” Duka suka masa da “Toh” Su Ihsan sunso abar su, su cigaba da azabtar da ita, Yazeed hakan dad’i ya mishi, a ranshi yace “idan ta matso ba mai kula da ita, yunwa ta addabeta dole ta bani had’in kai ko dan na taimaka mata” Naseer da masifar tausayin Noor ya koma gida, Ya cewa kanshi “Tabbas Noor na buk’atar kulawa, nayi alk’awari In shaa zan maye mata gurbin Imran, duk wani kulawa In shaa Allah zan bata, da ba igiyar aure a kanta da nan gidan zai maidota but duk da haka zanyi iyakacin k’ok’arina” Bacci ya koma, ya d’anyi na 30mins sannan ya tafi office, Office d’insu d’aya da Imran. *Waye Naseer?* Naseer d’a ne ga Alhaji Isma’il Borno, Asalinsu yan borno ne, Mahaifinshi hamshak’in mai kud’i ne, dan yafi Baban Imran kud’i,Sana’ar man fetur yake, Yana da gidajen mai wanda duk Naseer ke tafiyar dasu, Ya mallakawa Naseer d’aya daga cikin gidajen, Hajiya Asma’u itace mahaifiyarshi, itama asalin yar’borno ce, Yana da Yaya d’aya mace Sameera tayi aure, Sai shi Naseer d’an gaban goshin Ummi da Abba, Meenal ita ke bi mishi tana Ss2 sai autarsu Salma tana js1 suke nn iyayensu suka haifa, Kyawawa ne, su farare, amma suna da kyau sosai, Iyayensu naji dasu, Sun d’au son duniya sun d’aura akan su, Suna zaune lafiya cikin kwanciyar hankali, ga girmama da mutunta junansu, ba wata matsala da suke fuskanta a familynsu. Naseer da ya taso daga office, Restaurant ya biya, Ya siyo take-away da lemun kwali guda biyu masu sanyi, Ya nufi gidansu Imran A harabar gidan yayi parking, Ya kira mai gadi Yace “ya kira mishi Noor”. Noor bata je school ba, kwance kawai take da tunani birjik a ranta, Tayi tayi ta cire tunanin Imran a ranta ta kasa Mai gadi yayi sallama yace “Tazo inji Naseer” , ta amsa da “Toh”. Bakin motar ta tsaya, Ya bud’e k’ofa ya fito, tare da jingina jikin motar, Murya a sanyaye tace “Sannu, Ina wuni?” “Lafiya lau Auntynmu” Ya tsura mata ido, _Masifar kyanta yake gani_, Yace “Ya school? , har kin dawo?” “A’ah banje ba”Ya d’an zaro ido waje Yace “Akan me baki je ba?” “Imran ke kaini dama” Ya d’an dafe kanshi yace “Oops! Am sorry na manta, daga yau driver dake kai su Meenal makaranta zai rik’a zuwa yana kai ki, yana d’auko ki” Tayi murmushi tace “toh nagode” “Aah kar ki mun godiya, ki d’aukeni tamkar Imran” Kai kawai ta d’aga mishi, a ranta tace “Ba zaka tab’a maye mun gurbin Imran ba, matsayinshi daban ne a zuciyata” “Ina fatan kin cire duk wata damuwa a ranki?” Ta d’aga kanta sama “Yawwa haka nake son ji”. Ya bud’e mota ya fiddo ledan take-away da lemu, Ya mik’a mata Yace “Gashi nan, nasan ba’a baki abinchi ba tunda Imran baya nan” Tayi murmushi tace “Ai da ka barshi”Ya d’an b’ata fuska Yace “da Imran ne haka zaki ce mishi” Tace “Am sorry” Yace “Apology accepted, but kar ki k’ara” Ta gyad’a kanta tare da sakin murmushi _Murmushinta ba k’aramin burgeshi yayi ba_ Ya mik’a mata ledar, ta karb’a Yace “Ni zan tafi sai na dawo anjima” “Toh sai anjima nagode” Ta juya ta tafi, Ya bita da kallo yana murmushi, Yana sak’a abubuwa a ranshi. Imran suna isa, Ya siya sim, Ya fara kiran Naseer “Assalamu Alaikum” “Wa alaikassalam mutane turkey Ya hanya?” “Alhamdulillah! Ina Noor? Ina fatan bata damu kanta ba?” Naseer yayi murmushi yace “Noor na nan lfya lau, bata cikin wata damuwa” “Are you serious?, kar ka mun karya dan ka kwantar mun da hankali” “Friend believe me, gaskiya nake gaya ma, ko d’azu naje wurinta” Yayi wata sanyayyar ajiyar zuciya yace “Alhamdulillah! Plx abokina ka kula da ita, idan ka kula da ita ka gama mun komai a duniya” “Kar ka damu frnd” “Ok tnx, bye sai mun sake magana” “Ok bye” Ya kashe wayar yana tunanin yadda Imran ya damu Noor. Ta b’angaren Imran, taxi ya shiga ta kaishi hotel, kafin gobe ya nemi gidan da zai zauna, Ruwa ya watsa, yayi sallolin da yayi missing, kasa cin komai yayi, Ruwa kad’ai yasha, Ya kwanta ya rufe ido ko bacci zai zo ya kasa, tunanin Noor kawai yake, ba wanda yake son gani kamarta, Ji yake kamar yai ta buga kanshi a bango ko zai ji sassaucin abunda ke damunshi a zuciya.