ITACE QADDARATA CHAPTER 11
Naseer na zaune d’akinshi yana operating system, Imran yayi sallama ya shigo.+ “Ah! Abokina ya naga ka dawo?” “Just gidan so bored nace bari nazo nan muyi hira” (Duk yadda suke da Naseer bai tab’a fad’a masa about Noor ba, dan baya so yasan babanshi ya auri yarinya) “Amma ka kyauta wlhy, nima zaune kawai nake na rasa abun yi shine na d’auko system ina duba wasu abubuwa, ” ina fatan lafiya ka tarar da mutanen gida?” “Lafiya lau suke” “Toh madallah” Nan suka dasa hirar duniya, Sai k’arfe goma Imran ya dawo gida Yaso ganin Noor a daren, but yasan tayi barci kuma ko bata yi barci ba yanzu dare yayi ya shigar mata d’aki. Haka ya kwana da tunaninta a ranshi, da k’yar barci ya d’aukeshi, Hajiya kuwa tana yi tana lek’a window daga sashen Alhaji, taga ko Imran ya dawo, sai da taga dawowarshi hankalinta ya kwanta. Su khairat kuwa,da na sanin plan d’insu suka rik’a yi, maimaikon suyi succeeding komai ya lalace. Yazeed bai dawo gida ba sai 3,(da mai gadi yake had’a baki yace mai gadi yace da wuri ya dawo) Kusan kullum sai yaje Club, yau ma club yaje, Yana dawowa ba sallah ba salati kawai yabi lafiyar gado dan wani irin bacci yake ji. Washegari da sassafe around 7,Imran ko wanka bai yi ba yana sanye da jallabiya,ya nufi d’akin Noor Tana zaune kan dadduma(praying mat)tana karatun Qur’ani, tunda tayi sallar asuba bata koma ba Yai sallama ya shiga, Ta amsa mishi sallamar tana murmushi. “Kin tashi lafiya? Ya jiki?” “Lfya,Alhamdulillah” “Kin sha magani?” “A’ah sai nayi breakfast” “Plx kar kiyi wasa da shan magani,ina zuwa” Ya fice Kitchen yaje, ya samu masu aikin nata k’ok’arin had’a breakfast Yace ma Abu “Ta had’a breakfast d’inshi, ta kawo mishi d’akin Noor” Tace “Toh” A ranta tace “sabon salo,kiran sallah da usur, yau kuma d’akinta zakayi breakfast”. D’akin ya koma, Ya zauna gefenta d’an nesa da ita kad’an Yace “tunda muke dake ban tab’a jin kinyi karatu da k’arfi ba,yau dai ina son jin muryarki kina karatun Qur’ani” Tayi murmushi tace “ai muryata bata da dad’i,bani da k’ira’a” “Ni dai ina son ji” Tace “shikenan” Tayi gyaran murya ta fara zuba karatu cikin k’ira’arta mai masifar dad’i muryata sak ta Sudais kai kace Sudais ne ke karatu, Gaba d’aya ta gama tafiya da imanin Imran har wani lumshe ido yake dan dad’in karatun Shafi d’aya ta karanta a cikin Suratul bak’ara, tana kawo k’arshen shafin tayi shiru, Imran ji yayi kamar kar ta tsaya “Mashaa Allahu Barakallahu, Noor haka kike da dad’in k’ira’a gashi kin iya karatu, kin sauke Qur’ani ne?” “Eh na sauke” “Hadda fah?” “Na dai haddace hizib 15 dama Baba mai gadi ke k’arbar mun hadda” Wani dad’i yaji ya lullub’e shi da ya rasa na me ye? Yace “Gaskiya ya kamata ki cigaba da hadda,In shaa Allah zan nemar miki islamiyyar nan kusa damu ki rik’a xuwa,nima anan nayi haddata(Imran ya haddace Qur’ani tun yana shekara 17) Kamar tayi ihu dan murnar za’a sata islamiyya tace “Nago…..” Da saurin ya katseta “shhhh in kina mun godiya zamu samu matsala” Tayi shiru tana murmushi. Abu ce tayi sallama,suka amsa mata,ta ajiye breakfast d’in ta juya ta fita Chips da egg sauce,sai kayan tea Ya had’a musu kakkauran tea,kowa a kofinshi,ya zuba mata a plate ya ajiye gabanta Yace “gashi nan ki cinye ki sha magani” har zata mai godiya sai ta tuna tace “Sannu” Ya zuba shima yaci,Shi ya d’auko mata maganin tare da zuba mata ruwa a kofi,ta karb’a tasha Sannan yace “shi zai koma sashen su, kar ta kuskura ta fita ko’ina ta zauna d’aki ta huta,kwanukan zai aiko Abu ta kwashe” Noor ta amsa da “Toh” Tana jinjina irin d’awainiya da ita da Imran keyi, wanda take zaune gidan danshi bai masan da zamanta ba. Wanka yayi ya shirya cikin k’ananan kaya,Ya zauna falo yana kallon Discovery channel Hajiya ce tayi sallama ta shigo falon Ya juya ya kalleta fuska a d’aure ya amsar sallamar, tare da cewa “Ina kwana?” (UWA UWA CE,dole ya bata girmanta komai ta aikata kuwa) Dad’i taji da taga ya gaisheta amma ta lura fuskar shi a d’aura take, Ta amsa “lafiya lau Son” tare da k’arasawa inda yake, ta zauna kujerar da yake, Ta dafa shi “Ya jiki?” “Alhamdulillah” “Haba! Imran yanzu da ni mahaifiyarka kake fushi,idan akan abunda nake ma Noor ne yasaka shiga damuwa hadda ciwo,wallahi na tuba na daina daga yau,xan fitar da hannuna a al’amarin Noor” Da saurin ya kalleta “Da gaske kike mum?” “Yes son” Ta gyad’a mishi kai Rungumeta yayi, Yace “Thank you so much mum, I love you” Hajiya mamaki ne ya cikata yadda Imran ke murna buh tasan shi da tausayi tun yana yaro tace “i love you too son,Allah ya maka albarka” Ya saketa tare da cewa “Ameen Mum,me kike so in miki da zai faranta miki rai” “Ba komai Son,bari naje nayi breakfast” “Toh Mum” Ta tafi a ranta tana cewa “ko dan farin cikin ka da lafiyarka Imran nayi alk’awarin bazan sake tab’a Noor ba, dan farin cikin ka shine farin cikina”. Imran dad’i ya cika shi,ya rasa inda zai sa kanshi ,Alhamdulillah kawai yake furtawa,Yanzu Noor zata samu hutu babban burinshi kenan,sai kuma Alhaji ya saketa, dan bata dace da Alhaji ba. Bayan sallar la’asar,Imran sashen Alhaji yaje, Ya same shi zaune a falo Yace “Daddy Dan Allah ina so nasa Noor a makaranta,ka amince?” Alhaji a fusace yace “toh ni ina ruwana,idan kaga dama ka sata a mak’abarta ba makaranta ba” “Daddy gani nayi a matsayinka na mijinta,kana da hak’k’i a kanta ya kamata a sanar dake” “Kaga Imran kar ka k’ara danganta ni da mijin Noor ko ranka yai mummunan b’aci, fitar mun daga falo ya nuna mai hanyar fita” Imran tab’e baki yayi ya mik’e ya fita a ranshi yana cewa “kasan baka sonta me yasa ka aureta? Kuma yanzu dan me da baza ka saketa ba?”. Noor na d’aki kwance tana hutawa duk ranar bata fito ba, kuma ba wanda ya nemeta coz Hajiya tayi warning d’insu Ihsan akan kar wanda ta k’ara gani ya shiga harkar Noor(hakan ba k’aramin haushi suka ji ba, tun ba khairat ba da taci alwashin azabtar da Noor) Imran ne ya shigo d’akin Yace “ta tashi suje islamiyya” Ta mik’e zaune tana cewa “Da wuri haka” “To me za’a tsaya jira” “Ka gayawa Hajiya?” Yayi murmushi Yace “yanzu Hajiya ai tace ba ruwanta da al’amuranki,ta tuba” Noor dariya tayi har hak’oranta na fitowa tsabar murna kasa cewa komai tayi, a zuciyarta tace “Alhamdulillah” Sosai yaji dad’in ganin yadda take dariya. Sunje islamiyya, an mata interview an d’auketa, Imran ya biya duk wasu kud’i da ake buk’ata har na uniform d’inta, Malamin yace “Gobe ta fara zuwa makaranta” An nuna mata ajinsu, Suka dawo gida. Grade height Academy nan Imran ya nemar ma Noor, Sun d’auketa bayan an mata interview, Js3 class(aji uku) aka bata saura sati d’aya su fara JSCE,ba k’aramin kud’i ya kashe ba kafin su d’auketa saboda bata da takardun makaranta Noor farin ciki kamar zai kasheta burin ta ya cika na son zuwa makaranta Wani farin cikin ma, sai ranar da zata fara zuwa tana sanye da Uniform d’inta da suka amshi jikinta, charas-charas suka mata kyau,tasha farar safa da black cover shoe, sai Side bag da ta rataya. Ba k’aramin kyau tama Imran ba, har hoto ya d’auketa a wayarshi ita kuwa sai wangale baki take murna duk ta cika ta, Shi ya kaita makaranta, Ya mata nasiha sosai akan tayi karatu banda biyewa k’awaye tasan ita matar aure ce,ta kula sosai da karatun ta(haushi taji da ya kirata matar aure but bata nuna mishi ba), Tace mishi “Toh” Ya zaro d’ari biyar ya bata, Yace “Ga kud’in break d’inki” “A’ah ka barshi” Banza ya mata kamar bai ji ta ba Yace “sai na dawo d’aukar ki” Yaja motarshi ya tafi. Yan’ajin duk girmansu d’aya da ita sai dai zata girmesu a shekaru,Yan’ajin kansu ta burgesu gata kyakkyawa suna ta kallonta,Suna ta mata sannu tare da tambayarta Sunanta,Tace musu “Noor” “wow nice name” suke ce mata A ranar tayi k’awaye Ilham da Kausar, Suna ta janta a jiki,Daga ganinsu ya’yen masu hannu da shuni ne kuma wayayyu(Saboda makarantar ta ya’yan masu kud’i ne). Ana tashin su Imran yazo d’aukarta, A mota yake tambayarta “Ya makarantar? Ba dai wata matsala koh?” Ta amsa da “Eh Babu” Yace “Ok Gud”. Suna isa gida, Ta cire uniform ta watsa ruwa, ta saka doguwar riga mara nauyi, Kuloli ta gani ajiye gefe d’aya, Baki ta saki tana kallonsu, Imran ya shigo tare da sallama(shima ya sake wanka,ya saka kayan shan iska) Yace “Ni nasa a kawo su nan, Lunch d’in mune zauna muci” Ya k’arasa maganar tare da zama Tayi murmushi tace “Toh bari naje na gaida Hajiya” “Ok kiyi sauri” “Toh” ta fice Ya bita da kallo a ranshi yana mamakin sanyin hali da hak’uri irin na Noor,duk da abunda Hajiya ta mata but zuwa zatayi ta gaisheta.+ Hajiya na kishingid’e a falo ita kad’ai, Su ihsan duk basa nan suna school “Hajiya ina wuni” “Lafiya lau,Ya jiki?” Ba k’aramin mamaki ne ya kama Noor ba ta amsa “Jiki da sauki” “Toh sannu,Allah ya k’ara lafiya” “Ameen” Ta tashi ta fito tana mamakin Hajiya, a zuciyarta tana cewa “Lallai Hajiya ta chanza” Hajiya kuwa a zuciyarta ba abunda ke ciki sai tsantsar tsanar Noor, ba yadda zatayi ne kawai saboda Imran. Ta dawo d’aki tana ta far’a, Imran yaji dad’in yadda ya ganta, Yau ce rana ta farko da Noor taje wajen Hajiya bata sata kuka ba,ko ta gaya mata bak’ar magana, Imran ya zuba musu abinchi kowa a plate d’inshi,sukaci tare da mango juice Nan ya zauna suna hira, Yana tambayarta about school, Kiran sallar la’asar yasa shi mik’ewa ya fita Noor itama ta mik’e, tayi alwala tayi sallah,tasa uniform d’inta ta nufi islamiyya, A islamiyya ma tayi k’awa Saudat,shekararsu d’aya da Saudat sai dai Saudat ta d’an fita girman jiki,Ajin akwai manya da suka girmi Noor ba kamar boko ba. Rayuwa haka ta cigaba Noor bata fuskantar wata matsala daga wajen Hajiya ko su Ihsan,Yazeed kuma bai fasa bibiyar taba yana rok’onta ta bashi had’in kai, dan har yanxu masifar sha’awarta yake idan ya ganta ma abun k’aruwa yake, ita kuwa tana nan akan zancenta na ba zata bashi had’in kai ba. K’unarta ta warke har an cire bandage d’in,Tana maida hankali sosai akan karatun ta both boko da islamiyya, Islamiyya kullum sumuni take bayarwa hadda( Malaman har mamaki take basu,kuma ba’a wani cinta gyara sosai,wataran ma ko gyaran ba’a cinta,Malamai da d’alibai duka suna sonta,kowa burgeshi take), Boko sun fara JSCE,karatu take ba wasa, Imran kuma na helping d’inta ya mata explaining wasu abu da bata gane ba. A school suna zaune tare da k’awayenta Ilham da kausar, Suna karatu kafin a shiga exam, kawai Noor taji mararta ta masifar murd’awa “Ya salam! ” ta furta, Abu kamar wasa taji mararta ta rik’e tana masifar ciwo kamar zata cire, ta dafe mararta tana kuka, tana kiran Sunan Allah, Ilham da Kausar suka yi kanta suna tambayarta “Lafiya?” Tace musu “mararta”. Nan suka kamata suka kaita clinic d’in makaranta,Nurse tace “su tsaya daga waje zatayi magana da ita” Noor nata sharar k’walla “Me ke miki ciwo?” Ta nuna mararta dan bata iya magana saboda azaba “Kina period ne?” Noor tuni ta zube k’asa tana birgima dan azaba Nurse ta tsorata da ganinta tace “wannan irinsu ne masu wahalar ciwon mara, har kwantar dasu asibiti ake dan haka tafi k’arfina sai asibiti” Su Ilham ta kira,sukayi kan Noor suka d’agota suna cewa “Sannu” sai dukansu take tana birgima tana karanta duk addu’ar da tazo bakinta Nurse kuwa tuni ta fita ta sanar da Principal, Nan take Principal ta kira Imran(dan kowanne student akwai numbern guardian d’inshi,ta sanar dashi halin da ake ciki. Cikin mintuna kad’an Imran yazo makarantar hankali a tashe, Ya tsorata da ganin Noor sai zufa yake duk ya gama rud’ewa, Nurse yasa ta d’auketa ta kaita mota Ya figi mota a 360 bai tsaya ko’ina na sai asibitin MANAN(Dangin mahaifina) Nurses suka kama aka shiga da ita, Yau sunzo a sa’a dan Dr.Aysher basma na nan, ita da kanta tace zata duba Noor ( duk taji tausayinta) Bayan ta gama dubata,ta bata maganganu hadda nasa bacci, anan take barci ya d’auke Noor, Tana kwance kan lallausar cushion d’in dake office d’in Dr.Aysher mai kamar gado Imran yace “Dr wai me ke damunta?” Dr Aysher tace “Ciwon mara ne wanda mata keyi idan zasu fara al’adansu, toh gaskiya ciwon ma ba kowa ne keyi ba, masu yin ma, na wani yafi na wani, kaga in her case ita tana layin masu irin azababban ciwon marar nan wanda idan ba’a ci sa’a ba duk zata yi sai ansa mata drip”. Zufa ta fara k’etowa Imran duk da sanyin Ac dake office d’in Yace “yanzu ba wani magani da za’a iya mata?” “Magani d’aya ne a mata aure” A kid’ime ya kallo Basma Yace “Aure?” “Ofcourse dats d only solution, but xan bata maganin da zai d’an taimaketa but gsky ku mata aure shine kawai” Wata zufar da k’ara keto mishi a ranshi Yace “Tana da aure but ba damar Alhaji ya kusanceta, sakinta kuma ba rana, ko an saketa waye zai aureta?” Ya dafe kanshi “yanzu haka Noor zatai tashan wahalar nan, i can’t bear to see her suffering” k’walla yaji na k’ok’arin zubo mishi yai saurin mayar da ita Dr. tace “Ya dai? Naga duk ka tada hankalinka , akwai matsala ne?” Murmushin dole yayi Yace “No ba komai just ina tausayinta ne” “Ohh ni zan d’an fita na duba wasu patients, nan da like 30mins zata farka” “Ok Dr mun gode” “Ba komai ai” ta fice. Tsurawa Noor ido yayi ko k’iftawa baya yi, wani irin tausayinta yake ji a ranshi, ga wani abu game da ita dake ratsa dukkan sassan jikinshi, ji yake kamar ya rungumeta just to comfort her. Bayan minti 30, Noor ta bud’e idonta charaf suka had’u dana Imran, a take zuciyar kowannensu ta buga fat, haka suka zubawa juna ido har na tsawon seconds 30. Imran ya kawar da kanshi tare da cewa “Noor kin farka? Ya kike jin jikin ki yanxu?” “Da sauki, ya rage mun ciwo” “Toh Alhamdulillah” Yana rufe baki, Dr.Aysher tayi sallama ta shigo rik’e da d’anta Aseem Ta k’araso cikin office d’in tace “patient har kin farka, Ya ciwon? Ya rage?” Noor tace “eh ya rage but ina ji kad’an kad’an” Ok, sannu” Ta juya kan Imran “ko zaka iya excusing d’inmu zamuyi magana” Imran yace “ok” tare da mik’ewa ya karb’i Aseem a hannunta dan yaron ya burgeshi. Dr.Aysher cike da tausayin Noor, Tace “kin fara period ne ko this your first time?” Noor ta zaro ido tace “ban tab’a ba, period na fara ne?” Dariya ma taba Dr yadda ta zaro ido “kar ki damu ba wani abu bane kowacce mace nayi, nasan kinsan da haka” Noor ta gyad’a kanta sama, a zuciyarta murna kawai take dama ta dad’e tana jiran wannan rana, Fargabarta ciwon mara da take yanzu haka zatai tashan wahala duk zatayi kenan?, sannan Allah yasa Imran bai san period ta fara ba, Dr.Aysher ta bata shawarwari sosai tare da bata leda pad hud’u da magunguna kyauta, Ta kira Imran tace zasu iya tafiya, Sun mata godiya sosai a ransu suna yaba kirki irin nata, Imran ji yayi kamar kar ya rabu da Aseem coz yana son yara. A mota babu yadda Imran bai yi da ita ba, ta bashi ledar yaga magungunan da aka bata tak’i tace mishi “ai ba sai ya gani ba, Dr ta mata bayanin komai”, Ba komai ya sata k’in bashi ba sai dan kar yaga pad d’in dake ciki, Ya gane shiyasa kawai ya k’yaleta, Da suka dawo gida, Imran yai saurin fita ya zagaya ya bud’e mata k’ofa Tazo fitowa leda ta fad’i pad d’aya ta fad’o, Da sauri ta duk’a ta d’auka tana b’oyewa cikin hijabi, kasa d’agowa tayi dan wani masifar kunyar Imran taji, Shi dariya ma ta bashi,ganin tak’i d’agowa, Ya juya ya wuce abunshi dan yasan in dai yana tsaye ba zata tashi ba. Sashen Hajiya ya nufa, tana zaune falo kamar kullum ita dasu Yazeed suna hira, “Mum ina wuni?” “Lafiya lau Son,ina ka shiga ne? ina ta kiran wayarka baka picking” “Am sorry mum nakai Noor asibiti ne” “Me ke damunta?” “Ciwon mara” , “Allah ya bata lafiya”, ” Ameen” Yazeed naji an ambaci ciwon mara yai murmushi Yace “very good, shegiyar itama sha’awa ta fara damunta, na kusa cimma burina” yai wata dariya dad’i ya lullub’e shi, Hajiya ta cigaba da cewa “Zancen aurenka da Khairat, duk da Khairat yar’uwarka ce but a al’adance ana kai kayan an gani ana so, toh dan haka za’a kai daga nan iyaye zasu zauna a tattauna asa ranar aurenku dan hadda sadaki za’a kai, na riga nayi magana da Alhaji shi kuma ya sanar dasu Bawa( k’anin Alhaji), Jibi In shaa Allahu zasu tafi” Imran kamar ana soka mai kibiya haka yake jin zancen Hajiya, idan yana k’aunar mutuwarshi yana k’aunar aurenshi da Khairat, ya tsani zancen aurensu Hajiya tace “kayi shiru” “Eh! Naji Allah ya tabbatar mana da alkhairi””Ameen” Ya mik’e ya bar falon rai a b’ace Hajiya ta lura da yanayinshi a ranta tace “ko ka k’i ko kaso sai ka auri khairat” Khairat dake gefe sai washe baki take, murna duk ta cika ta.D’akinshi ya nufa,ya rufe kanshi gaba d’aya ya rasa inda zai sa kanshi yaji dad’i, da matsalar Noor zai ji, ko da auren da ake so a had’a shi da Khairat, Why mum zata mishi auren dole? He is still young yana da lokaci kwata-kwata ba aure a tsarinshi yanzu, Fridge ya bud’e ya d’auko bottle na ruwa, ya kwankwad’a ko zai ji sanyi a ranshi still zuciyarshi sai tafarfasa take, Kan gado ya kwanta yana kallon ceiling da tunani birjik a ranshi.+ Noor kuwa yana tafiya ta mik’e jiki a sanyaye ta nufi d’aki, Kwanciya tayi kan katifarta coz har yanzu tana jin ciwon kad’an-kad’an, ga jikinta yayi weak, A ranta tana tunanin yadda zata iya k’ara had’a ido da Imran dan yanzu masifar kunyarshi take ji. Har dare Imran na d’aki bai fito ba, Sallah kad’ai yake tashi yayi ya koma ya kwanta, Yana so yaje yaga Noor yana tunanin ko yaje ba zata bari su had’u ba, dan yasan yanzu kunyarshi take ji. Noor kuwa rashin shigowar Imran ba k’aramin dad’i ya mata ba, Tea kad’ai tasha tasha magani, Ta kwanta but ta kasa barci. *9:30pm* Yazeed ne ya fito daga sashen su, Ya nufi d’akin Noor( ohh ni zainab amma Yazeed da nacin tsiya kake), Yana murd’a k’ofar ta bud’e (ta manta bata rufe ba) Yayi murmushi a ranshi Yace “yau har da barin k’ofa a bud’e, wato jirana take nazo” Ya k’arasa cikin d’akin, Tana kwance ta d’aura hannu d’aya kan mararta, Ya zauna kan katifar yana lasar baki yana murmushi, Da sauri ta tashi zaune tace “Lafiya? Me kake mun a d’aki? Maza tashi ka fita kafin na maka rashin mutunci” Ya fashe da dariya Yace “me ye na d’aga murya, dama ance tabarmar kunya da hauka ake nad’eta me ye na pretending, nasan abunda ke damunki ki taimaki kanki kawai kizo mu hole” A fusace tace “me ke damuna? Ni dallah tashi ka fita bunsuru kawai” Ya sake fashewa da dariya “me ke damunki kuwa banda sha’awa ,gashi kina ciwon mara” Da sauri ta toshe kunnuwanta, ta rufe idonta tace da k’arfi “Ka fitar mun a d’aki ko na maka ihun kwarto” Jin haka yai saurin mik’ewa yace “waitt….abun duk be kai ga haka ba dama zuwa nayi muyi helping juna, ni zan tafi ki zauna kiyi shawara” Yasa kai ya fice. Dafe kai tayi tace “Yanzu Imran zuwa yayi yana fad’a ga ciwon dake damuna, Ya Allah! Kasa shima ba tunanin da yake mun ba kenan, Yazeed kuma ina rok’on Allah kai muntsari dashi” Ganinta da Imran bai yi yaji duk yayi missing d’inta, Yayi shirin office tsab sanye yake da manyan kaya da suka masifar yi mishi kyau, Sashen Hajiya yaje bayan sun gaisa, ya nufi d’akin Noor Tana zaune rik’e da hisnul muslim tana azkar Tana jin sallamarshi gabanta ya fad’i, tai saurin juya mai baya, Murmushi kawai yayi, ya gane har yanzu kunyarshi take ji “Noor ina kwana?” Ba tare da ta juya ba ta amsa “Lafiya lau” “Ya jiki? “Da sauki” , “Ni zan wuce office” , “Allah ya kai lafiya” (daurewa kawai take tana bashi amsa dan ta matso ya bar d’akin) “Ameen” (yaso ganin fuskarta kafin ya tafi). Rayuwa haka ta cigaba, Su Alhaji sun je, Manya sun zauna an tattauna ansa biki nan da wata uku, Ranar Imran ji yayi kamar ya had’iyi zuciya ya mutu dan bak’in ciki, Noor kuwa tasha kuka kamar ranta zai fita, tana cewa yanzu shikenan nan da wata uku zata rabu da Imran, Gashi tunda aka sa rana Khairat ke k’ara shisshigi mai. Soyayyar da suke ma juna sai dad’a ruruwa take ba tare da sun sani ba, Imran wani irin masifar so yake ma Noor, baya iya komai ba tare da yayi tunaninta ba, kusan kullum sai yayi mafarkinta, kullum so yake yai ta jinta kusa dashi, yana jin muryarta komai nata so yake, idan abu ya sameta gaba d’aya rud’ewa yake ya shiga tashin hankali, Tsayawa bayyana muku irin masifar son Noor da ya kama Imran b’ata lokaci ne, kowacce kawai ta ayyana irin azababben son da zuciyarshi ta kamu dashi na Noor. Abun ya fara damunshi har ya fara fita hayyacin shi *SO*, Yana zaune office ce kad’ai ba abunda yake sai tunanin Noor, Yana kallon hotonta da ya d’auketa ranar da zata fara zuwa makaranta, Tambayar kanshi yake “Me yasa nake jin haka game da Noor? Me ye wannan nake ji?, Dole in sanar da Naseer,abun har yana so ya tab’a lafiyata” Mik’ewa yayi ya d’auki mukullin motarshi da waya. Ya figi mota sai gidansu Naseer, Naseer na zaune falo yana kallo, “Abokina lafiya? Ya na ganka haka kamar ba’a hayyacinka ba” “Hmm! Wlh Friend ba lafiya ba, ina cikin wani yanayi” “Subhanallah! Me ya faru?” Nan ya fad’a masa komai game da Noor, Amma bai fad’a mishi matsayin Noor a wurinshi ba Naseer ya fashe da dariya yace “My friend you are in love, Who is the lucky girl da ta rud’a mun aboki” Imran idonshi tuni ya kad’a yayi jajir bai tab’a jin tashin hankali irin na yau ba, bai san sanda ya furta “How can i fall for my father’s wife, Me zai sa na SO matar babana Why? Why?”Naseer da ya kasa fahimtar abunda abokin nashi ke cewa Yace “what? What are you saying Imran” Ya kamu hannun Naseer gam ya rik’e yana hawaye Yace forgive me friend, i have been hidden something from you ba dan komai ba sai dan na kare mutuchin mahaifina” Naseer cikin rashin fahimta yace “me kake cewa ne frnd, ni fah ban gane ba” Nan ya fad’awa Naseer tun farkon aure daddy da Noor har zuwa yanxu Naseer ya masifar girgiza da jin zancen at d same time ya tausayawa abokinshi Yace “friend diz is a very serious issue, ka fad’a tarkon Son matar babanka, we have to find a way out” Imran na hawaye yace “ya zanyi friend, am madly in love with her, yadda nake ji yanzu bazan iya rayuwa babu ita ba” Naseer ya dafe kanshi yace “Ya salam! SO bai maka adalchi ba abokina,son matar babanka is a big crime”.Imran nata hawaye, Zuciyarshi na tafarfasa kamar zata fito waje Naseer nata lallashin shi “Kayi hak’uri abokina, we will find a way out” Imran ya mik’e Yace “i have to go home now” “Ok abokina plx ka kwantar da hankalinka, zamu samu mafita In shaa Allah” Kai kad’ai ya iya d’aga mishi, Ya mishi rakiya har bakin mota yana k’ara bashi baki, Naseer ya dawo cikin gida cike da tausayin abokinshi Imran driving yake kwata-kwata hankalinshi baya jikinshi, Allah ne ya tsare ya kawo shi gida lafiya. Rufe kanshi yayi a d’aki, Yana kuka yana magana shi kad’ai ” Why? Why? Zan fad’a tarkon son matar babana, I deeply love her me zai sa na fara son matar da ba aure tsakaninmu? In rasa wacce zan fara so sai matar Daddy”, Kanshi ya fara bugawa a bango yana “ya zanyi da raina?, how can i survive without her? Taya zan cire sonta a raina, Zuciyata ta kamu da masifar sonta, Why? Zan fara sonki Noor kina matar babana, tabbas wannan ITACE K’ADDARATA son matar mahaifina, Nan ya fara jefar da kayan d’aki yana fashe-fashe yana buga kanshi a bango, Kwalbar da ya fasa ya d’auko, Yana tsaga hannunshi ko zai rage zafin rad’ad’in dake zuciyarshi, hannunshi nata jini ko kad’an baya jin zafin yankar, Zuciyarshi kawai ke tafasa, Kan gado ya fad’a duk ya fita hayyacinshi a yan’ awanni *ME YE FITA YANZU?* Wata zuciya tace mishi “Dole ka nisanta kanka da Noor na tsawon lokaci i think thats d only way da zaka cire sonta coz idan kana ganinta sonta k’aruwa zai cigaba dayi” Wayarshi ya d’auka ya kira Naseer yace “Yazo gidansu yanzu zasu yi wata important magana”.