JALILA CHAPTER 1
Da sauri ta fito daga wanka ko mai bata tsaya shafawa ba ta zura kaya, ta rataya jakarta ta dauko safarta a hannu ta nufi hanyar waje, Goggo mahaifiyarta ce tai saurin cewa “Jalila ko karyawa bakiyi bafa.” Tace tana kokarin sa sandal “Goggo share abinci nan in driver dinsu Safeenah ya tafi ni kadai nasan uban tafiyar da zansha in banyi wasa ba inci duka in naje makarantar.” Tafada tare da gama saka sa sandal din,Goggo da sauri ta miko mata naira ashirin tace ” ungo to in kinje kya samu wani abin kici.” Jalilah ta amsa tare da yin waje da gudu. Tana zuwa motar na fita daga gidan da gudu ta karasa hanyar kofar sai dai kafin ta karasa sunyi gaba. Idanunta ne suka ciciko dan ta tabbatar anganta ko ta madubin mota ne, bayan yau aikin gidan ne ya mata yawa amma ko su tsaya ta, inda sabo ta saba sai dai tana kokarin kiyayewa dan kuwa makarantar da takeyi akwai nisa, duk da sudin makarantar kudi sukeyi ita kuma ta gomnati, sai dai ba nisa sosai tsakanin makarantun nasu.3 Sauri ta shiga yi dan tasan tabbas kafin ta isa sai tayi late. Duk hanya ba dadin tafiya sakamakon ruwan da aka sheka a daran jiya, dan ma bata sa safarta ta makaranta ba, jin yanda wata mota ta shararo da gudu yasa tai saurin matsawa, tare da bin motar da kallo, da gudu ya zo ya wuce da motarsa, wata muguwar harara ta bi mai motar dashi sannan ta ja wani tsaki juyawa tai baya taga duk yawanci mutanen baya motar suke bi da harara da alama kowa yaji haushin yanda motar ta kunno da gudu cikin layinsu, Jalila ta kara kallan motar wacce ta riga ta kule tare da kara tsaki tace ” wasu dai ba kai sai na daukar kaya”4 Cigaba da tafiyarta tai duk ta gaji, har sai da ta kusa isa makarantar sannan ta tsaya tare da ciro safarta ta tsaya a gefe ta saka sannan ta dan karkade jikinta, ita nufi makarantar, mamaki tai da taga kamar motar da gani dazu. Motar ta gani tayi gaba, baki tadan tabe sannan ta karasa gate din makarantar. Sabon Malaminsu ta gani tsaye a bakin gate da alamar shine yake tarar late comers, kanta ta sunkuyar har ta isa gun. Shikuwa tunda ta taho yake kallanta fuskarsa a dan hade tana matsowa yace ” Habiba Abubakar me kenan?” Kallansa tai da sauri tare da cewa ” Good Afternoon Sir!” Yace “Afternoon?now?” Da sauri tace” Oh sorry sir Good Mor…….” Katseta yai yace “Dama bakya zuwa school da wuri?” Kallansa tai tace ” No sir wlh yau ma tsaytsayi ne.” Fuska ya kara had’ewa yace ” Tsautsayi a ranar farko dana fara tsayawa a gate?” Kasa tai da kanta tana wasa da yatsun hannunta, yace “sai ki dau dustbin kiyi picking.” Kallansa tai dan ta dauka dukkanta zaiyi, murmushi ne ya bayyana a fuskarta tace “Thank you sir” Shima murmushin yai yace “Last warning in har kinaso mu shirya kenan.” Da sauri ta daga kai sannan ta dau dustbin tai gaba ta fara picking, kallansa ta juyo tai ta baya, ba shakka bata taba ganin wanda kayan Nysc sukama kyau ba irin Uncle Sagir. Jalila na gamawa ta wuce ajinsu, ganin ba kowa a cikin ajin yasa tai saurin juyawa ta nufi lap. Suna lap din chemistry ana musu practical, da sauri ta wuce gun groups dinsu, Zarah ta kalleta tace “Jalila kinga yarda idanunmu suka firfito muna tsoron kar a ce ya akai aka ganmu mu shida. Tace “Kedai bari nima na dauka zai ganni.” Haka sukai ta karatu har sai da aka tashi break sannan ta samu tasai biscuit na naira goma taci ta sha ruwan fanfo sannan ta ajiye naira goman.4 Ana tashi suka fito ita da Zarah suna hira, Zarah tace ” Jalila kinsan jiya sai ga Ya Amud da takardar jamb!” Jalila ta kalleta cikin jin dadi tace “Haba? Kice hankalinki ya kwanta dama kina ta tsoron kar ace za’a miki aure.” Tace ” ke dai bari jiya ai baccin dadi nai, dan banaji zan iya rabuwa da Nasir dina, kuma kinga shi level 3 yake a Buk.” Jalila ta tabe baki tace ” su soyayya manya, da alama kema makarantarsu zaki nema. Tace “sai ma kin tambaya….” Dariya sukai, Zarah tace ” ni nayi gida ke nasan sai kin jira ko?” Tace eh Dayake gidansu Zarah ba nisa da makaranta nan ta kwana, Jalila taja gefe ta tsaya kamar yanda suka saba, minti 30 ne tsakanin lokacin tashinsu dasu Safeena, abinda zai baka mamaki shine su in har suka shirya zasu taho to fa ba ruwansu da jiranta sai dai ita bata isa a tashi ta tafi ba sai ta jirasu.1 Tana nan a tsaye taji ance “baki tafi ba? Juyowa tai ta kalli malamin nasu wanda yanzu su yan aji shida kusan dukansu matan nan in suka zauna gulmarsa sukeyi, tace ” eh sir.” Ya dan daga littafin dake hannunsa kamar zai kwada mata, da sauri ta runtse idanunta, jin shiru bai dake taba yasa ta bude idanunta a hankali, kallansa tai ya harde hannayensa kawai yana kallanta cikin mamaki tace “ba dukana zakai ba?” Yace “me kikamin da zam dakeki? Dazu da kikai laifi ban dakeki ba sai yanzu?” Cikin mamaki tace amma naga ka daga…… Yace “sato ke bakya zuwa school da wuri sannan in an tashi kece karshe a tafiya, me hakan yake nufi?” A ranta tace “ni kaina wannan amsar nemanta nakeyi.” A fili tace ” hmmm, ai……” Wayar da aka mai ne ta katsesu ya dau waya tare da fara tafiya, alama ya mata da hannu akan ya wuce. Tace ” Okay Sir.” Bin bayansa tai da kallo, sannan tai ajiyar zuciya, nan ta cigaba da tsayuwa har suka iso, 2017 toyota sienna ce tai parkin a kusa da ita, tura kofar motar tai ta shiga. Sannan ta rufe kofar, Safeena ce wacce kana kallanta kasan bata wuce sa’ar Jalilan ba tace ” Ashe kuma yau da kafa kika taho.” Jalila ta kalleta tace ” Amma Safeena dazu tsakani da Allah baku ganni ba, sannan Malam Auwal ma bai ganni ba?” Safeena tace ” Ta ina zamu ganki? Sannan in ma munganki menene damuwarmu? Uban wa ya hanaki yin sauri?” Jalila ta juyo ta kalleta tace “Uban wa ya hanani yin sauri? Kwata kwata fitowata daga bangarenku minti nawa ne har kuka taho?” Tace “wannan damuwarki ce, naga kina wani hararata ni na saki aikin? Sannan in kinsan bakyasan kiyi late me zai hana ki dinga tashi karfe hudu?”2 Jalila ranta ya baci ta juyo gaba dayanta tace ” karfe hudu? Ku karfe nawa kuke tashi, ni daga na tashi sallar asuba me nakeyi? Bangarenku nake shigowa sai na gama muku komai har abinci sannan nake tafiya na shirya, sannan hakan ma ba birgewa nake ba har zakice indinga tashi karfe hudu?”1 Sultan kanin Safeena ne ya zare earphone din dake kunnensa yace ” will you please keep quiet, duk kun cika mana kunne da wani musunku.” Ya maida earphone dinsa, tare da kwantar da kansa kan kujera, Safeena tai kwafa tace ” in munje gida kya maimaitawa Mumy na abinda kika fada a motar nan.”1 Jalila a ranta tace ” yauma a kwai wani sabon shan wahalar kenan, ai wahala bata kisa.” Suna isa gida motar Dadynsu Safeena na parking, Safeena ta tashi kanwarta Yasmeen dake barci, tana ganin Dadynta ta ruga da gudu ta gunsa. Safeena ma tai gunsa tana murmushi, daga Yasmin yai yana cewa “Baby Yasmin an dawo?” Sultan ne ya karaso yace ” sannu da zuwa Dady.” Kallansa yai yana murmushi, Safeena kusa hannayenta ta zargo cikin nashi tare da cewa ” Dady kace da safe zaka dawo.” Yace ” Naso dawowa da safe sai dai akwai wani meeting da nadan yi ne da suppliers dinmu. Karasa maganar yai yana kallan Jalila wacce kullum take jiya iyau, irin yar kibar nan ko dan murmurewar nan batayi, Jalila tace ” Dady sannu da zuwa.”1 Yace “Jalila an dawo?” Ya fada tare da juya kai zuwa gun Safeena wacce ke harar ta, yace ” muje ko?” Nan suka nufi ciki Yasmin ma hannunsa ita kuma Safeena ta rikeshi. Murmushinnn takaici tai tace ” happy family, wazai kalleni yace mahaifinane?” Wucewa tai can cikin gida inda aka dan musu dakinsu daya da bandaki a can karshen gidan aka katangesu kamar masu aikin gidan…….. 4 ************* A hankali ta tura kofar d’akin bayan ya amsa sallarmarta, zama tai daga gefen gadon inda yake a kwance, kallanta yai sannan ya fara kokarin mikewa zaune, a hankali cikin sanyin muryarta tace ” Hassan bazakai breakfast da mu bane?” Yace “Ummy banajin yunwa.” Idanunta ne suka canja yanayi cikin tsananin tausayama dan nata tace ” Hassan sai yaushe ne zakai yaki da wannan matsalar dake damunka? Mun kaika duk wani asibiti da ake ji dashi a duniya amma ba wani ci gaba, dole ance kaine zakai yaki da wannan matsalar da kanka ba wani bane zai maka.” Kallansa tai cikin tsananin tausayawa tace ” Hassan ka tausayamin ko dan halin da nake ciki.” Kallanta yai yace ” Sau nawa zan ce miki ki cireni aranki Ummy? Dazu da safe nagama nazari ina tunanin abu biyu ko dai na bar kasar nan na koma egypt da zama ko kuma na bar gidan nan, ina tunanin wannan shine abinda ya cancanta na muku dake da Abba.” Kallansa kawai takeyi cikin mamaki tace ” Kana tunanin in kabar kusa damu hankalinmu zai kwamta ne ko me?” Kafafunsa ya sauko ya saukesu a kasa yace ” To ya kuke so nai? ” Tace ” ka zo muje gun likita ya sanar dakai hanyar da zakabi danyin yaki da matsalarka.” Yace ” Ummy please ki fita.” Mikewa tai dan tasan in bata fita bama ba wani abu dazai biyo baya, in har kaji yace mutum ya fita to tabbas karshen maganarsa tazo kenan, daga nan duk wani abu na duniya da zaka fada ko mai zafinsa bazai taba tanka wa ba. Tana fita ta rufo kofar sannan ta sauka kasa, mai gidanta ta kalla jiki a sanyaye, yana ganin yanda tai yasan ba’a dace ba, kansa ga saukar kan dinning din sannan ya dago ya kalli yaransa biyu dababba mai bin Hassan sai kuma mai binsa mace, duk yaransu ukun sun girma, dan karamar mace wato Ameera a Ss2 take. Sagir yana ganin yanda sukai duk jiki a sanyaye yai saurin mikewa sannan ya jawo Ummy ya zaunar da ita kan kujera yace ” Ummy kinsan jiya naje gidan Auty Nana?” Ta kalleshi tace “Da yaushe?” Yace ” bayan mun tashi a makaranta, Aina tace ai zata zo mana hutu karshen satin nan.”” Ameera da sauri tace “Ya Sagir da gaske?” Abba yai murmushi yace “Auta da alama kawa ta kusa zuwa.” Dukansu ne sukai murmushin. Suna cikin cin abinci ya fito rike da makulin mota, ko kallan inda suke baiyi ba yai waje, sam basu kula da wucewarsa ba dan falan babba ne sannan dining area din na bangaren kitchen. Mota kawai ya fada yai waje………… Gudu yai ta shararawa a mota sai dayaga har ya fita daga cikin gari sannan yaja motar ya tsaya sannan ya gangara gefen titi ya kashe motar, gani nai ya fito daga mazaunin driver ya koma baya ya kwanta tare da lumshe idanunsa.+ Bai dade da fara bacci ba yai wani irin zabura, a tsorace ya farka jikinsa ya fara karkarwa, jiyai numfashinsa na mai wahalar ja, jijiyoyin wuyansa ne suka firfito kamar wanda aka rikema hancinsa da bakinsa, zufa ce ta shiga keto masa da kyar ya jawo numfashi sannan ya mike ya zauna tare da hade kafafunsa, nan da nan idanunwansa suka canza. Wayarsa ce datai kara tasa ya dawo hankalinsa, kallan wayar yai sunan mahaifinsa ne a jiki, idanunsa ya runtse yana takaicin wannan rayuwar tasa, shi kadai ya hana iyalan gidansu samun farin cikin rayuwa. Lalai yana tunanin dolene ya bar kasar nan yaje inda ba wanda ya sanshi in ma rayuwar tasa a iya nan ta tsaya to shikam zai iya cewa Alhamdulila. Bai dau wayar ba har sai da ta katse. Fitowa yai daga motar ya hau samanta yana kallan bishiyoyi da sararin samaniya. Ya dade a haka sosai yana tunani kafin ya sauko ya •••••••••• A bangaren Jalila kuwa tana shiga ta tadda mahaifiyarta a zaune tana hada mafici, Goggo tana ganinta tace Jalila an dawo?3 Jalila ta shigo fuska a hade tace “Goggo yunwa.” Goggo tace “Yi maza ki cire kaya kici abinci kafin a kiraki daga cikin gida, ni kaina a zaune kawai nake anan amma hankalina na kanki.” Kayanta ta cire ta zura doguwar riga ta mikoma Goggo naira Goma sannan ta jawo kwanan abincin ta fara ci, Goggo tausayinta ne ya kamata dan dama tasan bazata taba kashe ashirin din nan ba, inda sabo ta saba wahala da rike yunwa. Batai nisa da fara cin abincin ba Safeena ta shigo bako sallama tace “Ke kizo inji Mumy” Bata kula taba sai cigaba da cin abincinta da tai, Safeena tace ” Malama ba magana nake miki ba?” Jalila tace “Malama taje koyo sallama.” Safeena tai kwafa tace ” Mumyn kike fadama haka?” Jalila ta tsame hannunta dan duk ma abincin ya fita akanta ta mike ta wuce ta gabanta, Safeena ta juya a kule tai hanyar cikin gida. Jalila ta tura kofar a hankali, Dady ta gani zaune da Yasmin a falo, suna kallo suna shan ice cream, sallamarta ya amsa yana kallanta, motsin Mumy da yaji ne yasa ya dauke idanunsa daga kanta. Mumy tana gaba Safeena na bayanta, bata kalli inda Jalila take ba sai zama datai kusa da Dady tare da kwantar da kanta akan kafadarda tace ” Abban Yasmeen kafadata duk ciwo take min.” Kallan ta yai tare da nuna tsantsar kulawa yace ” lafiya? Ko muje asibiti? Garin ya ya? Faduwa kikai?” Kallan Jalila tai hakan yasa ya fahimci mai take nufi, mikewa naga yayi cikin mamaki naga ya yi ma Jalila alama da hannu, takawa tai zuwa inda yake tana neman bada hakuri, wani wawan mari naga an sakar mata wanda ni kam tsananin mamaki sai da yasa na yarda pen dina, ya dora da cewa ” menene aikinki a gidan nan?” Idanunta ne suka fara zubar da kwalla dan tabbas taji marin har ranta tace ” duk wani aiki da akeyi a cikin gida.” Ta fada cikin kuka Yace ” akan me tunda kika dawo baki shigo kin fara aikinki ba har dai da kikasa ta yin aikin wahala? Da sauri tace ” Kiyi hakuri Mumy.” Mumy ta mike tare da kallansa tace “” Abban Yasmeen abin ai bai kai da duka ba, in ka mata fada ma ai ya isa.” Ya kalli Jalila a zafafe yace ” kece kikace kin daukema Mahaifiyarki aiki ko ba kece ba?” Tace “nice” Yace ” da haka kike tunanin yzaku zauna a gidan da yake nata kuci kusha da kudin ta ba tare da kunyi aikin biya ba?” Hawayenta ta share tace ” kayi hakuri.” Mumy ta dan canza fuska tace ” sai yaushe ne zaka daina cewa gidana da kudina? Abu na ba naka bane?” Yace ” na sani, sai dai agun wannan yarinyar da uwarta dole ne adinga tuna musu.” Tace ka bari please matarkace dai Kallan Jalila yai yace “Mata? Matar da bance inasoba aka likamin? Ko kuwa yar da batajin magana?” Jalila kam hawaye kawai takeyi, Yasmeen ce tasa kuka da sauri suka juya kanta. Dady yace “Auta menene?” Ice cream dinta ta nuna wanda ya fadi a kasa, Jalila da sauri ta nufi kitchen ba ta dade ba ta dawo da kayan gyara gun, Nan ta gyara gun tas sannan tace “Yasmeen kin sanma yan kasa?” Tace” ni kad’an zan san musu” Tace ” ki bar musu tunda sun shanye wannan nan gaba karki basu kinji?” Kai ta daga tare da yin murmushi. Jalila wacce tana gyara gun Mumy da Dady suka shiga ciki ta goge hawayen da suka bata mata fuska sannan ta kalli Safeena wacce ke bakin kofa tana murmushin mugunta. Bata bi ta kanta ba tai kitchen, Safeena ce ta biyota tace “Mumy tace kiyi fried cus cus da miyar vegetables” Tace to Nan ta shiga aiki tana yi hawaye na zubo mata, a duk sanda aka cima Mahaifiyarta mutunci wuni take tana kuka, sai dai abin bakin cikin ba kowa bane mai cima mahaifiyar tata mutunci ba sai Mahaifinta da zuri’ar sa dan kuwa zuri’arsa zatace, a iya sanin rayuwarta bata taba ganin mahaifinta ya shiga bangaren Mahaifiyarta ba balle mu’amala ta aure ta hadasu ba, in ta tuno irin kuncin da mahaifiyarta ta shiga a dalilin rashin so ba shakka sai taji nata ba mai zafi bane, gwara ita mahaifinta ne. A haka har ta gama girkin, tana girkin tana gyara gidan inda ya baci, sai da ta juye musu nasu sannan ta dauko tasu samirar ta dan zuba kamar yanda aka kiyaste mata sannan ta gyara kitchen din. Daukar na Mamar Mumy tai ta nufi sama inda take, Sallama tai sannan ta tura kofar bayan an bata izini, a zaune take sanye da glass tana karanta wata takarda, kana shiga dakin wani sanyin dadi da kamshi ne zai ratsaka, inda ake ajiye mata abinci ta ajiye sannan ta tsugunna tace “Inna barka da gida.” Bata tankata ba, inda sabo ta saba mikewa tai sannan ta nufi hanyar waje. Muryar inna taji cikin tsantsar isarta tace ” na dauka jiya ma sanar dake in kin dawo yau daga makaranta zaki kwashi wankina ki sauka dashi kasa? Da sauri ta juyo tace ” yahkuri Inna wlh na manta.” Bata kara tanka mata ba nan ta nufi inda kayan suke ta hadasu ta fito dasu. Sauko wa tai tana kallan su Safeena da Sultan rike da littafan karatu da shigar uniform na islamiya zasu tafi. Abinda take tsananin buri kenan a rayuwarta taga an sata a islamiyya. Haka ta sauko ta kai wankin Inna gun Auwal dan ya kai mata sannan ta mikama Goggo abincinsu ta dawo dan gyara dakin Safeena da Sultan, tana gamawa ta koma kitchen dan daura abincin dare. Haka rayuwar Jalila take, daga aiki sai aiki, makarantar boko kadai aka barta sai dare bayan magrib take samun zama da mahaifiyarta. ************** _Washe gari_ Yau kam tayi sa’a ba’a sata yin breakfast mai wuya ba, ta samu ta biyosu Safeena, a mota dama Yasmeen ce kawai mai magana ta kula Safeena ta kula Jalila dan ita yarinya ba ruwanta. Shi kuwa Sultan kamar baya cikin motar haka yake, earphone kawai yake sawa a kunnensa ya kwantar da kansa akan kujera har su isa. Suna zaune ita da Zarah, duk wata hira da zata fito daga bakin Zarah na Saurayinta Nasir ne, Jalila ta juyo tace “Nikam Zarah anya Nasir na sanki kamar yanda kike sansa?” Fuska ta canza tace ” wacce irin tambaya ce wannan?” Jalila xatai magana Uncle Sagir ya shigo, da sauri suka mike suka gaida shi. Idanunsa akanta ya fara sauka, a hankali wani murmushi ya banyana a fuskarsa. Sannan ya basu damar zama. “Mathematics” abinda ya rubuta kenan a blackboard sannan ya ruba “Quadratics Equation” Sannan ya juyo da hankalinsa kan d’alibai, Jalila ta dago suka hada ido da sauri ta sunkuyar da kanta tana wata da yatsun hannunta, haka ya shiga yi musu examples. Jefi jefi yana sauke idanunsa akanta haka itama, har ya gama period dinsa sannan ya ce a hada masa assignment din da ya bada. Nan monitor ta mike ta hada, kallan Jalila yai yace “Habiba inasan ganinki biyoni da books din nan.” Kallansa tai sannan tai saurin cewa “Yes Sir” Tare da fitowa ta amshi littatafan. Yana gaba tana dan binsa a baya sai jitaj yace ” yau saboda in kama wata nazo da wuri sai tai sa’a bata makara ba.” Tace “wata? Ni?” Ta fada tana kallansa,bai juyo ba sannan bai daina tafiya ba yace ” da yau na kamata lalai da shikenan na daina amsa ko gaisuwarta.” Tace ” Na daina zuwa late insha Allah, sannan jiya ma tsautsayine.” Yace ” a tare zamu gama, kuna gama exams ni ma ina kammala aikina.” Murmushi tai batace komai ba. Yace ” me kikeyi tsayawa yi in an tashi daga school kullum?” Tace ” Kanena nake jira a tashesu sannan a daukosu sai su biyo ta nan mu tafi.” Yace “Kannenki?” Ita kanta taji abin ban barakwai sai dai ko ma menene ai kannenta ne, tace “eh” Juyowa yai yace ” a wani school suke?” Tace “Crescent International School” Kallan mamaki ya mata sai dai bai kara cewa komai ba sai juyawa dayai, yana tafiya yana mamaki, kannenta na Crescent ita kuma tana makarantar Government? Sai data ajiye mai books din sannan ta fito, tana tafe tana mamakin tambayoyin da Uncle Sagir ya mata. Ana tashi sun fito ita da Zarah, Zarah na ce mata ni dazu me kike nufi? Ban samu munyi magana ba…….. Nasir da ta gani a tsaye ne yasa ta dakama Jalila duka a kafada tace ” Jalila kinga!” Jalila ta juya ta kalli yaran dake tsaye daga gefensu tace ” yayanki ne?” Yace “My Nasir ne, da alama ya gaji da missing dina ne.” Jalila ta kalli Nasir din sannan ta kalli Zarah wata dariya ta kirkiro wanda kana gani kasan ta dole ce tace ” Ohh shine Ur Nasir?” Zarah ta hade rai tace “Meye hakan?” Jalila ta girgiza kai tace “Kije naga ya kura miki ido kamar zai daukeki.” Murmushi tai sannan tace ” Kawata kalleni fuskata batai komai ba?” Kamar zatai kuka ta daga kai tace “Eh” Zarah ta fara tafiya cikin canza salo, Jalila kallansu kawai take cikin mamaki, wannan ai da alama makaranta ya samu da wuri amma ta tabbatar baiba Zarah shekara biyu bama, dan ma tace a level 3 yake ne amma lalai da tace sa’ansu ne,lalai ansha yarinta shiyasa. Tab itakam gaskiya bataji zata iya soyaya da sa’anta, ita tafisan saurayi kamar Uncle Sagir, da sauri ta girgiza kai tace “What am I thinking? Ahhhhh lalai banida kai.” Tana kallansu suna tafe suna rangaji irin na masoya, murmushi tai sannan ta koma gefe ta tsaya. A hankali duk aka yoye tana tsaye, ganin rana ta fara dishashewa ne yasa ta daga kai ta kalli sama, hadari taga yana haduwa abinka da damina kan kace me gari yayi daki, da sauri ta juya ciki ganin iska mai kura tana tasowa. Ji tai ta bugi abu, da sauri ta dago ta kalleshi. Idanunsa na kanta, ta matsa baya da sauri cikin jin kunya, sannan tace “Sorry Sir” Yace “anya yau sorry din nan zai karbu kuwa agurina? Da alama sai na hukunta mai laifin nan.” Kallansa tai sannan tace ” Wlh ban ku……..” Yanda yake kallanta ne yasa ta kasa karasa maganar dake bakinta sannan tai saurin juyawa, dan ji take gabanta na faduwa. Murmushi yai sannan yace “muje in kaiki gida.” Tace ” Naam” Yace “Baki ji bane ko bakya so ne? Hadari ne a garin in aka fara ruwa kina tunanin yanda zakiyi kije gida? Ko su Kannen naki ne bakyasan ki tafi ki barsu?” Shiru tai tana dan nazari kafin tace ” Nagode da kulawa Uncle Sagir sai dai in na tafi ba tare dasu ba fada za’amin.” Kamar zai sake magana sai kuma taga ya juya ya koma ciki, tana tsaye ya fito da lema ya mika mata bai jira tace komai ba ya hau mota yai gaba.1 Da kallo ta bishi yau da mota yazo? Hmm ita kadai tasan cin zarafin da za’ama mahaifiyarta in har ta tafi. Tana tsaye aka fara yayyafi da sauri ta bude lemarta ta shiga, kan kace me ruwa ya tsuge, ruwa ake mai karfin gaske wanda tana cikin lemar ma amma ba tsira tai ba, komawa gefe tai ta rakube. Kamar motar zata tsaya sai taga ta yi gaba da gudu, cikin tsananin tsoro ta kalli motar tare da kwalla kara da karfi tace “Safeen ina nan fa……” A cikin motar kuwa wanda Safeena tacema Malam Auwal da alama ta tafi ganin hadari, wanda akasan ranta ta tabbatar bata tafi ba, tsabar mugunta ce. Haka ta rakube dan tsoro takeji ta koma cikin makarantar ita kadai, ganin a tsayen ma tsoro ya kamata kawai ta fara tafiya tana tafe tana kuka mai sauti, sai dai kasancewar karar ruwa bai sa tasan da karfi take kukan ba. Yana zaune a cikin motarsa daga gefen titi wanda shi dama yafisan gurin shiru inda ba mutane, shiyasa mafi akasari zaka sameshi ne a zaune a cikin motarsa ya zuge glass kawai ya kwanta. Jikin motar ta tsaya da taga ruwan ya dan yi sauki duk jikinta ya jike jagaf, ga lemarma sai lankwashewa takeyi saboda iska. Juyawa tai ta kalli glass din motar, da yake motar mai tints ce sai ta shiga kallan kanta tana kara wani kukan,sam tunaninta bai kawo mata da wani a cikin motar ba. Kallanta kawai yakeyi sai sharar kuka take wiwi. Komawa yai ya maida kansa ya rufe idanunsa kamar mai bacci. Kara juyowa yai ya kalleta, kuka take sosai, kamar dama neman kukan takeyi, haushi duk ya isheshi kamar a kansa take kukan, kofar mazauninsa ya bude, a tsorace ta kalli motar, kallansa tai a tsorace, sannan ta kalli motar . Kallan tsoro tamai tace “Hmm hmm.” Hannunsa ya dago ya mata alama da ta matsa daga gun, tace “Ban gane me kace ba.” Alama ya sake mata da hannunsa akan tai gaba, sannan ya maida kofarsa ya rufe, da harara tabi kofar motar sannan tace ” wannan kuma wani kwarantancen dan duniyar ne? Maganarce yafi karfin yimin ko kuwa tsabar rashin mutumci ne?” Harara ta sake yi sannan ta juya, kallan motar ta sakeyi sannan tace “irin motar jiya” Taja tsaki tace ” da alama duk masu hawa irin motar nan basuda mutunci.” Sam ta manta da kukan da takeyi saboda masifa, tana tafe yayafi na digar mata tana yan mitocinta, sai da ta gama gajiya ligif sannan ta isa gida. Goggo kuwa duk ta kasa zama saboda tsoro ganin yanda ake ruwa ga har yanzu bata dawo ba. Tana shiga Goggo ta kalleta cikin tsananin tausayawa. Jalila fadawa tai jikinta duk da jikarta ta sa kuka, idanun Goggo suka ciciko sai kanta kawai da take shafawa. Jalila ta dago tana kuka tace “”Goggo Allah nasan da sanin Safeena, ai tasan ban taba tahowa ba.” Goggo tace “Kiyi hakuri” Jalila tace “Goggo sai yaushe ne zaki daina cewa inyi hakuri? Gaba daya rayuwarmu ni dake a hakuri ta kare, nikam ina takaicin cewa ma Dadyne mahaifi…….” Marin da Goggo ta mata ne yasata yin shiru, kallan Goggo tai kuncinta a rike,Goggo ta kalli hannunta cikin dana sani sannan tace ” taya zaki dinga kushe abinda Allah ya hada?” Jalila tace “kiyi hakuri Goggo bazan kara ba” Hannunta ta kamo tace ” na sani, na sani sosai abinda ke ranki Jalila sai dai bayanda zamuyi da hukuncin Allah, sannan komai zaiyi ko kowa zai zageshi to lalai banda ke, domin shine silar zuwanki duniya.” Tace “Na daina Goggo kiyi hakuri.” Goggo tai murmushi tace ” yi maza ki cire kayanki.” Mikewa tai ta shiga dan dakinsu. Tana cire kaya tai sallah sannan ta mike tace “Goggo bari naje” Goggo tace abinci fa? Naga da safe ma a tsatsaye kikaci, shiyasa kullum gakinan kamar a hure. Tace ” Goggo in na dawo naci” tace ban yarda ba sai dai ki tafi dashi can kici, ina zaki jira sai wajen magrib kici abinci? Jalila tai murmushi sannan tace ” to in na gama ma rana zam deba inci a namu.” Goggo tace “kin tabbatar?” Tace eh karki damu Goggo na Tana isa ta tadda Safeena a falo tana kallo, wata banzar harara ta maka mata sannan tace ” da kuka taho kuka barni sai kuma gashi mai rai da lafiya yayo gida da kansa.” Safeena tace ” au da gaske kina can dama? Ni danaga ana zabga ruwa sai naga ina mai hankali zai tsaya a cikin ruwan nan?” Jalila tace ” mai hankali kikace ai ni kuwa ina na ganshi?” Ta karasa maganar tana harararta, jitai ance ” Uban wa ya baki damar cimata mutunci?” Gabanta ne yai wani irin faduwa, duk gidan ba wanda take tsananin tsoron ya mata fada irin Inna, a tsorace ta kalleta idanunta sun firfito, bakinta ne ya shiga rawa tace “In nn nna……” Kallanta tai sannan ta kalli Safeena tace ” ke kuma Jalila matsayinku daya da zaki dinga zama tana fada miki kalamai irin haka?” Jalila ta hadiyi wani miyau me daci tace ” in na bahaka bane…….” “Dake nake magana?” Jalila gabanta sai faduwa yakeyi. Sultan ne ya fito daga kitchen rike da jarkar ruwa na faro yace ” Inna ita Safeenar itace da laifi bai kamata ku dinga yanke hukunci ba tare da bincike ba.” Kallansa tai tace ” Sultan shiga daki” Baice komai ba ya wuce ciki, Jalila kuwa kamar wacce aka tsunduma a wani ruwan haka takeji, muryar Dady ne ya ratsa falon wanda maganganu Inna ne suka sa shi fitowa, da sauri yace “Hajiya ki mata afuwa ni zan hukuntata da kaina.” Kallansa tai a wulakance tace ” kai har wani hukunci zaka iya? Ka saisaita yarinyarka in ba haka ba daga ita har uwarta zasu bar gidan nan, karka kuskura ka manta gida da dukiyar wanene kake mora daga kai har su.” Mumy ce ta rike hannunta tace ” Kiyi hakuri ki bari dan Allah.” Ta fada tare da jan hannun ta zuwa dakinta. Suna shiga tace “Inna sai yaushene zaki daina disga Abakar cikin yaransa? Karfa ki manta ‘ya’yansa sunanan kuma suna jin zafin abin.” Kallanta tai tace ” ke meyasa bakida hankaline? Kin nace sai kin aureshi dake da mahaifinki, bakya tunanin wannan cin mutuncin da nakemai shine dalilin da yasa yake nuna miki kulawa haka?”1 Tace ” Wlh Inna ke kike ganin haka Abbakar na sona kamar yanda nake sansa, dan Allah ki daina wulakantashi.” Ta karasa maganar cikin lalashi. A falo kuwa Dady a zuciye ya sa hannu ya fizgo Jalila ya kaita kitchen, cikin fada yace ” sai yaushe ne zakiyi hankali kisan darajarsu Safeenan kikeci ke da uwarki?” Kallansa tai cikin rawar baki tace ” Dady itace……..” Cikin tsawa yace ” so kike in fasa miki baki? Ko me ta miki bazaki hakura ba? Shashashar banza to wlh ki bala’in shiga hankalinki in har kinaso mahaifiyarki dake ku zauna a gidan nan.” Yana gama magana yai falo, yana shigowa Safeena taje da gudu da rungumeshi. 4 ************** Yana shigowa cikin gidan ya tadda mahaifinsa a zaune a falo, karasawa yai ya gaidashi sannan ya fara kokarin mikewa. Mahaifinsa yace “Hassan!” Komawa yai ya zauna tare da kallansa, Abba yai ajiyar zuciya sannan yace ” Baka manta badai karshen satin nan zamu koma asibiti ko?” Hassan ya kalleshi yace “Abba please ka hakura Abba cikin kulawa yace ” Ka taba ganin inda uba ya hakura da dansa? Karka damu insha Allah da yardar Allah wannan matsala taka zata warware sannan zaka samu sauki cikin yardar Allah.” Kallan mahaifinsa kawai yake shidai sun kasa fahimtarsa, mikewa yai baice komai ba zaiyi gaba. Kaninsa ne ya dafashi yace ” Yaya kace Ameen mana ko hankalin Abban zai kwanta?” Ummy ya kalla wacce ke tsaye ita da Ameerah yai shiru sannan a hankali yadan motsa baki yace Ameeen. Murmushi sukai dukansu m, Sagir ya dafashi yace ” Ko kai fa Yaya.” Hannunsa yasa ya ture nashi daga kafadarsa yai wuce, Ummy tabi bayansa da kallo sannan ta kalli Ameera. Kai Ameera ta daga sannan tai kitchen. Faten dankali wanda Ummy ta masa ta zubo a plate sannan ta dau spoon ta fito, sama ta hau sannan ta shiga dakinsa. Yana zaune a kasa kan carpet ta shiga. Gabansa ta ajiye abincin sannan ta ce “Yaya abinci.” Kallanta yai yace ” BAna……” Tace ” Na sani yaya baka jin yunwa dama ko da yaushe zancen kenan, sai dai Yaya ka ci ko dan Ummy ta samu sukuni a ranta.” Yace “Naji zanci, ke kuma fita.” Ta mike tace ” to” Waje tai sannan ta turomai kofar.