JALILA CHAPTER 4
Wajen karfe 12 na dare tana zaune akan kujera a kusa da mahaifiyarta ta kwantar da kanta a kusa da ita, Goggo ce ta bude idanunta a hankali tare da kokarin yin motsi da hannunta, Jalila cr ta farka wanda dama tana rike da hannun Goggo gam. Tace “Goggo jikin ne?” Goggo ta girgiza kai ta mata alama data kwanta a kusa da ita sannan ta matsa mata, Jalila tace “ya za’ai in kwanta anan Goggo? Ki bari zan kwanta a kasa.” Goggo tace “kwanta anan mmagana zamuyi.” Jalila ta mike ta kwanta akan karamin gadon wanda ya musu kadan, Goggo ta rike hannunta tace “Jalila duk abinda zai faru karki yarda da abinda mahaifinki ke shirin yi miki, daga shi har zuri’arsa, kinada wanda kikeso dan haka ni mahaifiyarki na baki shawarar bin zuciyarki.” Jalila cikin sanyin murya tace “Goggo me yasa muke zaune a cikin mutanen da basa kaunarmu?basu damu da rayuwarmu ba?” Goggo idanunta suka canza kala zuwa damuwa da bakin ciki tace” Sunana kamar yanda kika sani Khadija, amma Kubra ake cemin, muna zaune a can wani kauye mai suna Chabai wanda yake karkashin karamar hukumar Misau a gariin bauchi. Kasancewar karamin kauye ne sannan haka al’ada ta saba yarinya tun tana tsuma ake mata miji, haka zata taso har lokacin da zata isa aure a aura mata shi. Mahaifiyata itace mace ta uku a cikin matan mahaifina, sannan itace ta tsakiya, ‘ya’yan gidanmu mu 23 ne, nice ta 5 sannan ta biyu a gun mahaifiyata, a ranar da ake radamin suna a ranar ne Mai garin mu wanda ya kasance mahaifin Habubakar yamai kamu na.+ Na taso mace marasan hayaniya dan a garin yara sa’anina har tsiya sukemin saboda asaranci irin nawa da rashin iya fada, Habubakar kuwa mutun ne dan gayu wanda tunda ya tasa yake bin yan garinmu Misau, Lagos da kano in zasu tafi rani. Ko sau daya bamu taba kebancewa da sunan saurayi da budurwa ba saboda shi gani yake yafi karfina, sannan sam baima fiya zama a garin ba. Ya yawan kasuwancinsa ne ya hadu da wani babban mutum mai kudi a garin kano, wanda suke safarar kayan abinci. Habubakar nada kokari da himmar yin aiki shiyasa mutumin ya amince dashi sannan yasan harkar gona sosai, ganin yana moruwa da Habubakar ne yasa mutumin ya nemi shawararsa akan sa shi yayi karatu, haka Habubakar ya shiga makaranta ba tare da ya sanar a gida ba, a aji hudu aka sashi saboda girmansa, ya dage sosai saboda shi mutum ne mai tsananin buri da san ya zama wani abun, haka ya share sama da shekara 8 a garinkano yana harkokin karatunsa da taimakon Uban gidansa. Sam ba abinda ya dameshi da tushensa inda iyayensa suke. Ni kuwa a lokacin sa’anina duk sunyi aure dan alokacin shekarata 15 duk inda naji tsiya akemin akan nayi kwantai, hakan yasa ko fita nadainayi, sannan Innata ta ma daina bani talla dan haushi ma takeji itama akan kullum ta bani tallan kunu kwantai yakeyi. Shi kuwa Habubakar ya zama dan gayu yana ta hidimominsa, alokacin ne kuma Mumy taji kaunar Habubakar ma ratsata saboda duk wani abu datake so kafin ta nema zakaga ya mata shi, wanda shi a gunsa ba wai so bane tsabar neman gun zama ne a gidan. Mumy wanda asalin sunanta Fatima ta bayanna ma Habubakar san da take mai,ba wani kokonto ya amince da ita saboda a lokacin ne ya tabbatar da arzikinsa ya tabbata. Haka ya dinga nuna mata tsantsar kauna ba tare da sanin iyayenta ba, Fatima tayi zurfi a kaunar Abbakar wanda ya canzama kansa suna zuwa na gayu. Hajiya Zinaru wacce take mahaifiyarta ta mata hadin aure da dan uwanta, sai dai Fatima ta sanar dashi bata san sa ita Abubakar take so kuma zata aura. Alokacin ne akan san da soyayyar dake tsakaninsu, duk yanda Zinaru tai ta rabasu abin yaci tura, shi kuwa Abbakar ya dinga riricema Fatima akan kaunar da yake mata. Fatima taki ci taki sha ita fa sai Abbakar, mahaifinta shikam dama yana so, Zinaru kuwa ganin abin na Fatima yayi nisa dolene ta amince amma da sharadin dolene ya zauna dasu sannan ya cigaba da karatunsa, sannan duk abinda ta unarceshi dolene yayi. Abbakar hankalinsa ya kwanta dan yanzu yasan tabbas ya zama wani abun, Mahaifin Fatima ne yace yaje gida ya sanar ma iyayensa. Sam Abbakar baiso ba danshi babu komawa kauyensu a tsarinsa. Haka ya shirya ba’a san ransa ba yace zai taho, key din motarta Fatima ta bashi tace yaje da ita dan ya dawo da wuri. A yanzu shekaruna 18 duk garin har iyayena sun gallabeni gashi mahaifin Habubakar yaki yarda a hadani da wani, a lokacin akwai wani babban mutun wanda yakeda mata biyu dayaso ya aureni amma yaki. Haka rayuwata ta koma cikin tsangwama da wulakanci a garin, kuka kuwa nayishi har ba iyaka. Kwatsam ranar mahaifina ya shigo cikin farinciki yake cewa Habubakar ya dawo. Sam ko mikewa banyiba daga aikin da nakeyi saboda ni maganar mutunci ma bata taba hadamu ba. Randa Ya isa gidansu mahaifinsa ya haushi da fada ta ko ina bai ma jira maganarsa ba, sannan yace a ranar zai daura mana aure. Ran Habubakar ya baci sosai yace shi ba wanda ya isa ya aura mai yar kauye, haka aka turo gidanmu akan washegari da azahar za’a daura auranmu. Bakin ciki yasa Habubakar ya fita can bayan gari gidan wani tsohon abokinsa inda suke zama da yaje ya aika a kirani. Da kamar bazanje ba tsautsayi yasa na fita, haka yaran dan aiken ya kaini har gidan. Tsayawa nai a waje saboda bansan dakin ba. Habubakar ya bude kofar yasa hannu ya fizgoni ciki, ba abinda yacemin sai gefe daya koma ya cigaba da cin abinsa yana dadana waya. Na gaji da tsayuwa haka Yasa nace zan tafi. Mikewa yai yazo kusa dani yace ” ni kike jira na aureki? Na miki kala da dan garin nan? Ko mijin wata kuchaka kamarki?” Nace “naji koma menene ni ba damuwa amma kabarni na fita.” Dariya yai sannan ya sa abu ya rufe kofar ya koma yai zamansa. Kafafuwana har suka gaji suka fara rawa saboda tsayuwa, nan fara kokarin bude kofar ji nai an fizgemin hijab dina ta baya an yar a kasa, tsoro yasa na fara kuka ina matsawa. Dariya yamin sannan ya koma ya zauna, baifi minti biyu da zama ba mukaji ana buga kofa da karfi, muryar mahaifina da mahaifinsa mukaji suna cewa Habubakar ka bude kofar nan ko kuwa? Mamaki ne ya kamani da naga ya cire rigarsa ya bar vest sannan ya taso ya bude kofar. Yana budewa ya koma gefen kafita yana cewa Baffa kayi hakuri. Nikam hawaye na nacigaba dayi, ganin abinda ke faruwa yana zuwamin a baibai. Mahaifina na zuwa ya kwadamin mari ya fara makamin kafa, nan na hau kuka sosai. Mahaifinsa ma ya hau dukanshi, yan kauyenmu na waje suna gulma. Kuka kuwa kamar zan mutu haka na dinga yinshi. Kallansa nai nace “Habubakar ka hadamusu gaskiya ni wlh ba abinda nai.” Mamaki ne ya kamani da naga ya min dariya ta kasa, anan ne na fahimci shiri ne nashi. Nan na shiga yin kuka, shikuwa ya dauka in yai haka mahaifina zaisa a hanashi ni, baisan suma duk sun gaji dani ba, haka suka dauramana aure bayan sallar asuba wanda tunda muke a kauyen ranarce ana ta farko da aka taba yiwa mace aure da asubahi. Ranar dukan da na sha ba’a magana, Habubakar kam bakin ciki kamar ya kasheshi. Yaso guduwa da asuba amma yaji an rufe kofarsa, haka yana ji yana gani aka hanashi fita. A ranar da rana aka kawoni ba tare da wasu kayan daki ba, kuka kuwa nayishi kamar in kashe kaina. Shikuwa bakin cikin an hadamu daki daya yasa ya huce a kaina wai ai ni matarsa ce. Wannan ita kadaice ranar da wani abu ya shiga tsakanina dashi, sannan itace ranar da aka samu cikin ki.1 Inna ta goge wata kwalla wacce ta zubo mata, tace haka aka sashi dole ya tafi dani, naje gida sallama sai mahaifina cemin yai duk randa na tako garin nan ba tare da Habubakar ba bazai taba yafemin ba, ya kuma fadi haka ne har bayan ransa. Innata ma ta kara jaddadamin hakan, haka aka sani a motarshi a dole yaja muka tafi. A hanya sai wayarsa yakeyi da Fatima, yana gamawa ya hau ni da masifa akan shi a duniya ba abinda ya sani sai kansa, sannan duk abinda zai aikata sai dai yai abinda yasan zai amfaneshe. Haka ya kaini can wata unguwa wanda ya kamamin gidan haya daki daya ya sani, sannan ya bani kudi. Tundaga ranar ban kara sashi a idona ba sai dai lokaci lokaci wani yaro yana kawomin kudi wanda nake sana’a. Shikuwa sunyi auransu da matarsa suna shan soyayyarsu. Gidan hayar kullum habaici sukemin akan cikin shege ne a jikina. Cikina ya kai kusan wata bakwai abin duniya ya dameni, sai ranar kwatsam Habubakar yazo. Baiyi mamakin ganina da ciki ba, sai dai baice min komai ba ya ajiye abinda ya kawo ya fita. Ashe gidansu yaje ya sanarma mahaifin Fatima hadin auran dolen da akamai da cikin da nake dashi, ya karasa maganar yana kuka yana cewa shi in har Fatima tace ya sakeni to ba wani kokonto zau sakeni ne. Mahaifinta yace a’a sannan ya sanar dashi ya daukoni ya dawo dani boys Quaters. Fatima tasha bori balle da taji inada ciki wanda itama a lokacin tanada ciki. Haka ya sata a daki ya dinga lallabata har ta yarda sannan ya mata alkawarin bazai kara shiga dakina da sunan tarayyar aure ba. Zinaru kuwa tasha mita sai dai ba yanda zatai saboda umarnine na mijinta. Wannan shine dalilina na komawa gidan, mahaifinta shine ya sa miki suna Jalila bayan an sa miki asalin sunan mahaifin Habubakar….. Kuka ne ya ci karfin Jalila wacce bakin ciki da takaici sukama yawa………… Goggo tace “Jalila bana ganin laifin mahaifinki domin tun farko ya nuna bayaso, iyayena sune basu damu da rayuwata ba… Jalila cikin kuka tace “kowa nada laifi Goggo ta ya za’a maida rayuwarki kamar rayuwar dabba?ta ya ta ya………… Kuka ne yaci karfinta wanda ya hanata magana… A hankali ta tura kofar dakin, Tana kokarin shiga nurse din na kokarin fita, jiranta tai ta fito maimakon ta shiga sai tabi nurse din. Tana gaisheta, Nurse din ta tsaya ta amsa, Jalila ta matso tace ” Aunty ya jikin Goggo?” Tace “da sauki, ya akai? Kina tsoro ne?” Jalila ta goge kwallarta tace ” Aunty kina ganin kamar kwanaki nawa zamuyi kafin kafar Goggo ta samu sauki?” Tace “maybe 3 to 4weeks” Jalila ta zaro ido tace “da tsayi haka?” Tace “Umm.” Jalila tai shiru, Nurse din tace ” ba wata tambayar?” Jalila tace “in tabar asibitin fa?” Nurse din cikin mamaki tace ” ta ya za’ai tabar asibitin tana cikin wannan state din? Ko asibitin kuke san canzawa?” Jalila ta runtse ido can tace ” Aunty kudin ne…….” Muryar Sultan taji yace “me kike anan?”+ Idanunta ta bude da sauri, Nurse din ta wuce ganin kamar bazata iya magana ba. Sultan ya karaso yana kallanta. Ya kara cewa “me kike anan?” Jalila bakinta ne ya shiga rawa ta kasa magana, Hannunta ya rike yace “meye hakan?” Kamar ya tabota kawai tasa kuka, mamaki ya kamashi can yace ” Mumy ce?” Kai ta girgiza, yace “Dady ne?” Nan ma kai ta girgiza, sam bai kawo Inna ba saboda ba kasafai take shiga harkar rayuwar gidan ba, yace “Jikin Goggo?” Hawayenta ta share tace “Sultan ya zanyi?” Yace “name?” Tace “tsakanin rayuwata data mahaifiyata.” Yace “wace irin tambaya ce wannan, sannan in amsa kike so ai ke yarinya ce mai kuma lafiya, ita kuwa Goggo ba lafiya ne da ita ba.” Jalila ta shiga daga kai tana cewa “haka ne, Goggo itace gaba da komai.” Kallan mamaki ya kara mata, ta kakaro murmushin takaici tace “nagode Sultan.” Leda ya miko mata yace “gashi, Ni bari na wuce.” Tace “kai kadai?” Yace ” inada kudi a jikina, nan ya zaro dubu biyu yan dari biyar biyar, mika mata dubu daya da dari biyar yai ya maida dari biyar aljihunsa yace ” gashi ko zaki sai wani abin.” Ta amsa tamai godiya, juyawa yai ya fita, da kallo ta bishi sannan ta goge fuskarta ya tura kofar dakin. Goggo na zaune shiru ta shiga, Jalila ta karasa tana cewa “Goggo a zaune kike?” Goggo ta kalleta tace “kin dawo?” Tace “eh.” Jakar hannunta ta kalla tace ” baki daukon kaya ba?” Jalila ta bude baki tace “wayyo, wlh na sha’afa sam, ni fa dama jakar nan kawai naje daukowa.” Goggo ta kalleta cikin zargi tace ” me ya samu idanunki? Abubakar ya miki wata magana ne?” Ta zauna kusa da ita tace “Kai Goggo, ni ko ganinsa ma banyi ba.” Goggo tai ajiyar zuciya tace ” sai yaushe zamu bar asibitin nan?” Jalila tace “tab aima ki gyara zama goggo, dan wlh yanzu Nurse take cewa sati uku zuwa hudu.” Goggo cikin mamaki tace “Wannan asibitin mai tsada? Kina tunanin zasu biya mana kudin?” Jalila tai murmushin takaici tace ” karki damu da wannan, ke dai ki kwantar da hankalinki, kinji dai mai likita yace jiya.” Goggo tai murmushi, Jalila ta bude ledar da Sultan ya miko mata, ruwa ne mai sanyi faru tace “ruwa kika aikeshi?” Tace “Allah sarki Sultan cewa nai ya bani ruwa in akwai, ashe wai babu shine naga ya fita.” Jalila a ranta tace “dama sai a dinga kawo abinci ba ruwa.” Haka tai ta kokarin boyema Goggo damuwarta. ********* Sagir na komawa gida ya hau sama dan dauko wayarsa, ganin irin kiran da Jalila tamai yasa hankalinsa ya tashi, nan ya shiga buga mata waya shima, sai dai duk yanda ya kira No Answer kawai ake rubutamai, Fitowa yai ya shiga mota ya tafi makarantar su, ba ta nan, ya akai baiyi tunanin amsar address din ta ba? Wai shi yana ganin yasai mata waya, kwatancen gidansu bazai zamarmai wahala ba. Kai ya shafa cikin takaici, ina ne gidansu? Haka ya dawo gida jiki a sanyaye. Abba ne bayan Magrib ya shiga d’akin Hassan, yana zaune rike da littafi a hannunsa yana karantawa, Jornal ne. Yana ganin Abba ya rufe littafin sai dai baiyi motsi ba daga inda yake bai kuma yi magana ba. Abba ya shiga ya zauna kusa dashi, Shiru ne yadan ratsa dakin, can Abba yace ” Me zakayi gobe?” Hassan ya mai kallan mamaki, me zaiyi? Shi daka rayuwarsa ai kullum iri daya ce, Abba ya kalleshi yace “Gobe da yamma ko bayan magrib kuje kai da Sagir ku ga yarinyar.” Kallan Mahaifinsa yai cikin mamaki yace ” inje ince mata me?” Abba yace “kaje ku gaisa ta ganka, ka ganta.” Hassan yai shiru can yace ” Ai wannan tun a farko ya kamata kuce naje, Abba abinda ya kamata kuyi tun farko kenan, ta ya zaku sa rana ba tare da yarinya ta ganni ba?” Abba yace “Hassan bakasan me nai ba akan samar maka abokiyar zama.” Hassan ya kalleshi yace ” me kake nufi?” Abba ya mike yace “Ka taimaka gobe kuje kai da Sagir, wannan rokone uba yake ma dansa.” Hassan yai shiru baice komai ba, fita Abba yai tare da rufe mai kofa, shiru Hassan yai yana tunanin wannan abun, shi gaba daya ya kasa hasko rayuwarshi da wata mace, macen ma wacce bai sani ba. ********** Wajen karfe d’ayan dare ta mike daga kwanciyar datai dan dama ba bacci take ba, fitowa tai daga dakin ta zauna a kasan matatakalar benin, shiru tai tana tunani, ya zatai? Gaba daya duk yanda taso ta canza shawarar dake zuciyarta in ta auna lafiyar mahaifiyarta wacce ta rayu cikin bakin cikin da namiji bataji zata iya canza wata shawarar, rayuwar mahaifiyarta itace gaba da komai a rayuwarta. Kanta ta kwantar akan gwiwowinta tana tunano rayuwar da sukai da Sagir da irin rayuwar da tai fa mafarkin yi dashi. Wasu zafafan hawaye ne suke zubo mata, a wannan rana bacci baiga idanunta ba. Wajen karfe 1o aka kawo musu abinci sannan drivern yace mata “Inna na jiranki.” Ta fahimci me yake nufi, kallan Goggo tai tace “Goggo zanje na kwaso kayan, akwai abinda kikeso?” Nan ta fada mata abubuwan da takeso ta taho mata dashi, har zata fita sai ta dawo da sauri ta rungume Goggo idanunta na neman kawo kwalla. Goggo tace “Jalila menene? Badai jiya karya kikamin ba? Ance miki wani abun a gidan ko?” Dagowa tai tana dariya tace “Goggo kenan, kema kinsan bana iya boye miki komai a dunia, me zaisa in ki sanar dake? Inaji fa ganin kin kwanta yasa jikinsu yayi sanyi da zancen.” Goggo tai tsaki tace ” duk yanda naso in zauna dasu lafiya in har suka sake suka miki zancen hadin aure wlh sai sunsha mamaki.” Jalila tace “ni inada ke a duniya me zaisa inji tsoro Goggona?” Murmushi sukai a tare, Jalila ta juya ta fara takawa a hankali, daga sanda tasa kafa tabar dakin nan ta shiga motar ta tabbatar rayuwarta shikenan ta canza, bazatai dana sanin fita daga dakin nan ba kuwa? Ai dana sani tun kafin ta fita tasan rayuwarta lalai tana cike da danasani, domin kuwa batasan wani irin zama zatai ba. Sai data kai kofa ta juyo tama Goggo murmushi sannan ta fita. Mota ta shiga tai shiru tana kallan waje, mutane take ta kallo kowa yana nasa rayuwar, haka har suka isa gidan. Sai dayai kusan minti biyar da parking sannan ta bude kofar ta fito. Inna ta kalli Mumy dake leken window ta dakinta, Mumy da sauri ta juyo tace “ta iso kuwa Inna.” Inna ta kalli Dady tace ” sai ka kyautata mata kai kuma, ka tabbatar bata nunama mijin nata tsana ba.” Dady yace “to.” Mumy ta matso tace “Dadyn Yasmeen let us try our best.” Murmushi yai mata na dole sannan ya mike. Inna tace ” in zaku siyo ragowar kayan gida kudinga daukanta a asibiti.” Yace to, sannan yai waje. Yana isa falon tana shigowa, tsayawa tai tana kallansa, wai mahaifinta? Wanda hakkinta ke rataye a wuyansa? Dady ne ya matso kusa da ita, ya sa hannu a aljihunsa yace “Jalila ya mai jikin?” Kallansa kawai take batace komai ba, sai idanunta da sukai ja, bata amsa mai ba. Yace “me kike tunani?” Kai ta girgiza alamar bakomai tace ” kawai ina tunanin yanda Allah ya rataya wa uba hakkin dansa a wuyansa ne.” Dady yai shiru, zaiyi magana Mumy ta karaso tace “Jalila, yanzu muke shirin zuwa asibiti.” Jalila tai shiru a ranta tace “tunda kunsamu abinda kukeso ai dole.” Nan ta haura sama batare da tace komai ba. Inna na zaune sai data zauna sannan tace “YA YA? Kin yanke shawarar?” Jalila ta kalleta dan tana tsananin shakkarta ta daure tace “Amma kimin alkawari biyu.” Inna tace “inajinki.” Jalila tai shiru kafin tace ” da farko zaku kula da Goggo, zaku samo mata wacce zata dinga taimaka mata, sannan na biyu karku fada mata komai har sai ta samu lafiya.” Inna tace “duk ba matsala bane, Jalila ta kalleta a ranta tace me zata samu da take bin ta kowace hanya dan ganin ta min auran nan?” Dagowa tai da sauri datai tunanin wani abu tace “Inna tsoho ne?”2 Inna tace “a’a saurayi ne” Jalila cikin tsoro take kallanta, anya? Me suke tunani? In har ba wata matsalar mai zaisa su bar yarsu su zabeta? Inna tace ” ki tashi ki sauka kasa, bayan kinyi aanka kinci abinci ki shirya, ance bayan la’asar zaizo.” Jalila ta mike ta fito zuciyarta fal da tunani kala kala. Bangarensu kawai ta nufa ta kwanta, karar wayarta taji. Da sauri ta jawota, ta daga. Muryar Uncle ne ya daki kunnenta, ji tai wasu zafaffan hawaye sun zubo mata. Sagir yace “Jalila ina kika shiga haka? Ba dai wani abin bane ya faru ko?” Kasa magana tai, hankalinsa ne ya tashi. Ya shiga tambayarta, can ta daure tace “Uncle yaushe zamu hadu? Akwai maganar da zamuyi dakai.” Yace ” ko yanzu ma in kinaso.” Tace “a’a banda yau.” Yace “nima na manta yau zan raka yayana wani gun, gobe fa?” Tace ” to, Allah ya kaimu, zan kiraka goben.” Haka kawai tace ta kashe wayar saboda yanda taji zuciyarta ta karye. Tana kashewa kuwa tasa kuka. Shikenan Uncle, soyayyar da muke ma juna ashe anan zata tsaya………1 Sagir na kashe wayar shima yai shiru, tabbas akwai abinda ke damunta…… Sake kwanciya tai, ta kwantar da kanta akan katifa, itada take burin auren soyayya? Yanzu me kenan? Idanunta ta bude a hankali, tana kallan dakinsu, rayuwarsu da mahaifiyarta ne ta shiga dawo mata, rayuwace wacce sukai ta talauci da tsana, sai dai a tsakaninsu rayuwace mai cike da dinbin kewar juna da shakuwa, zata iya rayuwa ba tare da Goggonta ba? Haka tai ta saka da warwara har bacci yai gaba da ita. Sai wajen karfe uku ta farka, shima mafarki ne ya tasheta wanda ya sata razana da sauri, sai dai me? Duk yanda taso ta tuno wani mafarkin tai ta kasa sam, wayarta ta dauka da sauri ta yima Sagir text. Uncle please mu hadu a makaranta ko na minti goma ne, i really want to talk to you. Ajiye wayar tai ta mike, gaskiya dole ta sanar ma Uncle abinda ke faruwa taji me zaice. Mikewa tai ta kalli kayan da aka kawo mata ta saka, nan tai wanka ta saka ta fito sidif sidif tai waje. *****+ A can gidansu Hassan kuwa, Sai da Ummy ta mai magana ya kimtsa, da kananan kaya ya saka tasashi ya koma ya sako manya kaya. Fitowa yai daga dakinsa sanye da dakakiyar shad, cyan color wanda mukafi sani da bluegreen, shadar ta mai kyau sosai, dan shi dama bai fiya sa manyan kaya ba, daga kanana sai jallabiya, Abba ne baya gajiya da dinkamai. Ameera da kanta ta d’aukomai hula ta mikamai. Hassan kallansu kawai yake dan bayasan magana ya amsa. Takalmi ya saka sannan ya sauko kasan, Sagir sai janshi yake da tsokana wai kai Yaya gaskiya wannan kyan kamar ranar auranka. Hassan ko kallansa baiyi ba bare ya tankamai, shima Sagir din manyan kaya ya saka. Ummy ta jawo Sagir tace “Sagir ka taimaka kar a samu matsala, kasan halin yayan naka.” Sagir ya daga kai yace “Karki damu Ummyna, ki bar komai a wuyana.” Murmushi tai tace “godiya nake dan lele na.” Haka suka fito kowa yana farinciki, Ummy ta mikama Sagir gift din da zasu kai mata. Aina’u na jikin dakin Ameera tana kallansu, komawa tai cikin dakin ta kwanta ranta ba dadi. Motar Hassan suka nufa, Hassan na shiga ya rufo kofa, Sagir ya zagawa ta bangaren kusa da driver yana cew “Yaya na dauka da Mamman zamuje saboda shi yasan gidan. Jiyai kofar a rufe, cikin mamaki yace “Yaya me kenan?” Hassan ya zuge glass dinsa yace ” ka shiga motar ka Mamman ya jaka, ni daga can wani guri zanje.” Sagir ba tare da tunanin komai ba ya juya ya shiga motar sa shida Mamman. Haka suka fita da motoci biyu, su Sagir na baya shi yana gaba. Suna tafe suna hira sam hankalinsa baikai kan wayarsa ba domin yanzu harkar yayansa ce a gabansa baya tunanin akwai wani abu da zai ratsa wanda zaiyi distracting dinsa. A kofar gidan Mamman yasa signal sannan aka bude mai gate ya shiga, maimakon Hassan ya shiga kawai sai yai gaba. suna parking Sagir ya juya baiga motar Hassan ba, mamaki ya kamashi da sauri ya fito wajen gidan yana lekawa, sai dai ba shi ba labarinsa. Haka suma mutanen gidan, dan tun lokacin da Mumy ta aika Jalila tazo ta karasa shiryata, taki zuwa hankalinsu ya tashi, ta fito ta duba bangarensu bata ganta ba. Hankalinsu yayi tsananin tashi dan sun duba ko ina basu ganta ba, Mumy kam kamar tai ya ya. Nan Dady ya fito nemanta. Can ita kuwa tana tsaye a inda suke haduwa, tana duba agoggo, taji ance bayan la’asar zaizo shiyasa take sauri Uncle yazo suyi magana ta koma kafin hudu da rabi. Agoggon hannunta ta kalla, karfe 4:30jiki a sanyaye ta juya, lalai yanzu wata zuciya tana sanar da ita Uncle bai damu da ita sosai ba, wata zuciyar kuma neman yi masa uzuri takeyi. Haka ta tako jiki a sanyaye ta tsaya akan titi dan neman adaidaita. Tana tsaye mota tai parkin ta bayanta kadan, kallan motar tai dan ta dauka uncle ne, batai ma tunanin motar waye ba kawai ta nufi motar. Shikuwa yanda tazo saitinsa ne yasa cikin mamaki yake kallanta. Sai dataje jikin kofar sannan tai tunanin ba shi bane, lalai zuciyarta a matse take da san ganin Uncle, baki ta turo sannan ta juya jiki a sanyaye. Yana zaune a ciki yana kallanta, da yake motar tint ce itakam bata ganshi ba. Haka ta tsaya a titi zuciyarta duk ba dadi, sai kara leka hanya take ko zata ganshi. Yana kallanta harta samu mota ta shiga, kai ya girgiza sannan ya kashe motar, yasa kansa akan kujera yana tunani, shikam ta ina zai fara kallan mace da sunan zance? Sannan in tsautsayi yasa matsalarsa ta tashi fa? shikam hankalinsa ya kasa kwanciya, ya san kuma Sagir zaisan me zaice mata. Haka ta samu adaidaita ta hau jiki a sanyaye, ajiyar zuciya taitayi a cikin adaidaitar har suka isa, tana kokarin biyan kudin adaidaitar su kuma suka fito daga cikin gidan. Motar tabi da kallo, taga mutane biyu a zaune sai dai hankalinta ba’a kansu yake ba. Haka ta taho a hankali ta tura gate din gidan. Mumy ta ganina waje itada Dady suna magana, suna ganinta suka juyo suka zuba mata idanu. Dady a zuciye ya fara takowa, ganin haka yasata ta tsorata. Hannu ya daga zai shara mata mari, da sauri ta runtse idanunta, tsayawa yai sannan ya kalleta rai a bace, yatsa ya nuna mata yace “ni zaki cima mutumci?” Mumy ta matso ta sauke mai hannu tace “Dadyn Yasmeen meye hakan?” Kallanta yai yace “yanzu da badan shima dalili ya hanashi zuwa ba fa?sannan da kanin nasa bai fahimcemu ba fa?” Mumy ta kalleshi tace “tunda dai komai yazo da sauki ba shikenan ba?” Yace “in Inna taji fa? Me kike tunanin za’ace?” Mumy tace “sai muce mata ta ganshi sun gaisa harya tafi.” Dady ya kalleta cikin jin dadi, wanda baisan a ranta ba wai damuwa da Jalilan tai ba balle tace batasan a mata fada ne, tayi hakan ne dan abin ya kara karfafa. Jalila ta kalla sannan tace “Hassan din wani uzuri mai karfi ya tasomai a hanya bayan sun fito, dole ne yasashi kin zuwa, shiyasa ya turo kaninsa. Jalila ta dan tabe baki kadan, dan itakam ba damuwarta bane. Mumy ta rike hannunta tace “muje ciki ko?” Jalila tace “A’a Mumy asibiti zan koma.” Mumy ta jinjina kai tace “bari mu kaiki.” Jalila fuskarta dama a daure take tai bangarensu. Kayan da Goggo tace ta dauko mata ta dauko sannan ta fito. Suna tsaye suna ta wani abu wai su a dole mata da miji, ita Mumy sai wani shagwabewa take, haushi ya kara kama Jalila a ranta tace “mutum ya girma amma jinsa yake kamar yaro.” Ta gabansu tazo ta wuce, Mumt ta riko hannunta tace “Jalila tare zamu tafi.” Jalila tai shiru tana kallan Dady. Mumy ta bude mata baya sannan ta shiga, ita kuma ta shiga kusa da Dady. A hanya tayi shiru tana kallan waje, wayarta ce ta fara ringing, da sauri ta zarota. Uncle? Da sauri ta daga tace “Uncle!” Jalila i am………… Bata gama jin mai zai fada ba, Dady yai wani irin parking, wanda ya tsoratata, sam ta mantada mutane a motar. Mumy ta fizgi wayar tana cewa “Jalila me kenan?” Jalila a tsorace ta kalleta, sunan da ke jiki ta kalla MINE? Nunawa Dady tai ya kashe wayar yace “uban wa ya sai miki waya?” Idanunta ne suka firfito tai shiru. Mumy tace “Jalila zance kike a bayan idanun mu?” Jalila ta kallesu sai dai ta kasa magana, cikin salo Mumy tace “shiyasa take neman bijerawa maganarka kenan? Lalai samarin zamani sun iya siyan zuciya, da har zasusa ‘da ya bijirema mahaifinsa.” Dady cikin takaici yace “Uncle? Malamin ku ne kenan? Dama abinda kike a makarantar kenan?” Jalila da hawaye suka fara zubo mata tai shiru tana kallan ikon Allah. Dady yace “wato ina miki magana ma kinfi karfin amsawa ko?” Jalila tace “ba haka bane Dady.” Mumy tace ” Jalila yaushe kika zama haka?” Jalila jitai hawaye suna gudu a idanunta, wannan shine a dakeka a kuma hanaka kuka. Haka tana kallo Dady ya zare sim din ya karyashi sannan ya cilar waje, sannan ya ajiye wayar cikin motar sa. Jalila tana kuka tana cewa “dan Allah dady ka barni ko magana daya muyi.” Dady ko kallanta baiyi ba ya ja motar sukai gaba. Mumy tana cewa “lalai Jalila wato ya baki kima saurayinki magana?” Juyawa tai tana kallan window tana wani irin kukan takaici.1