ZUCIYA CHAPTER 24

ZUCIYA CHAPTER 24

Mikewa yai daga zaman da yake tare da furzar da wata iska sannan ya d’au wayarsa yama Nafi da mumy sako akan su shirya saboda tafiyarsu. Nafi kam kallan sakon take tayi, duk da tana masifar san zuwa kasa mai tsarki sai dai abin ya zo mata a ba zata, na farko ga bikin Jibiya wanda ya matso daf sannan ita a iya saninta Hajj ake fara yi tunda shine farilla. Sai dai taci alwashin yima Ashraf magana in ya dawo. ********* Sai Yamma ya fito daga office station ya wuce inda acan ya samu Umma, kana ganinta kasan tana cikin wani halin kusa da ita ya karasa yace ” Umma lafiya?” Hawaye ne ke zubowa a idanta tace ” Ashraf banga alama Mansir nada niyyar taimakama Asim ba, na sanshi sarai akan dukiyarsa zai iya hakura da Asim a matsayin d’ansa ni kuma na tattare dukiyata naba Asim ya sa a kudin company din da ya siya.”+ Ashraf yai shiru tabbas ganin halin da take ciki ya sa ya tausaya mata sai dai bazai taba yin bailing Asim ba dan kuwa shine key dinsa na kama Ubansa. Umma yaji ta kamo hannunsa tace ” Ashraf na sani tun kana karami ba sanka nake ba, ban damu da harkarka ba sai dukiyarka, har rayuwarka na nemi salwantarwa ni da Asim, sai dai a yanzu ina dana sanin hakan, banida wanda zan iya roka akan ya taimaki Asim sama da kai, ka sani iyayena ba masu karfi bane ga girma ta zo musu, ni kuma banida uban kudin da ake bukata, Ashraf ka dubi girman Allah ka taimaki Asim.” Ashraf ya kalleta cikin kulawa zuciyarshi ta farayin sanyi, sai dai tunowa dayai ita kadaice taga Auwal Max a yayin da yake lalata birkin mahaifinsa yasa ya dake. Yace ” Umma karki damu muna tattaunawa da ‘yan sandan insha Allah komai zai yi daidai.” Idanu ta runtse tace ” Nagode Ashraf ban taba tunanin zan nemi taimako a gunka ba.” Ashraf yai murmushi sannan ya mike. Gun Kb ya nufa, Kb yace ” ya za’ai da kudin nan?” Ashraf yace ” ka kai banki a jiya bayan komai ya kammala zamu maidamai kudinsa.” Kb ya jinjina kai alamar gamsuwa sannan yace ” what are u planning to do next?” Ashraf yace ” D’an Siyasan nan fa? Har yanzu shiru?” Kb yace ” yau muke sa ran dawowar yaron daya tafi binciken.” Ashraf yace ” Allah yasa a sameshi wannan karan.” Kb ya amsa da Amin. Gun Asim ya shiga, Asim har yayi baki ya rame, dan tunda yazo gun nan ya kasa cin abincinsu. Ashraf ya kalleshi yace ” Asim ance baka cin abinci, kasan dai dole ne kaci abinci ko ma samu mu gama wannan fadan da ya tunkaromu lafiya ko?” Asim wanda kansa ke kwance kan tabir din ya dago ya kalli Ashraf yace ” Nasani ni kuma tawa ta riga ta kare.” Ashraf yace ” Haba Asim da hankalinka kuwa?” Asim yai wata dariya ta tsantsar takaici, yace ” rayuwa kenan, mahaifina da na dauka duk duniya yafi damuwa dani sai gashi lokacin da nake bukatar kulawarsa ya nunamin karema ya fini matsayi a gunsa, sannan kai da nake ganin kaine babban makiyina a duniya yau gashi kaine kake kula dani.” STORY CONTINUES BELOW Ashraf ya hade rai yace ” kai dai ka daina wannan tunanin na shirme ka kula da kanka har Allah ya kawo mana mafita.” Asim yai murmushin takaici baice komai ba. Ashraf tare suka taho da Umma a motarsa tana sauka shima ya sauka yai bangarensa. Ya sani Anisa na gun Umma hakan yasa ya fito falo bayan yayi sallar magrib sanyi da singlet da kuma gajeran wando. Tv ya kunna yana kallan labarai, sai dai ya rasa ke yasa yau yakejin tsananin kewar Nafisansa, gyara kwanciyarsa yai ya koma rufda ciki, duk da yasan ba’asan kwanciyar sai dai yana ganin ita kadaice mafita. Ganin hakan ma ya kasa kwantar mai da hankali kawau ya mike ya hau exercise, kwankwasa kofa yaji, sam ya manta shigar dake jikinsa ya karasa ya bud’e. Nafi ya gani a tsaye fuskarta a maze. Bari kofar yai a bud’e shikuma yai ciki, ta shigo tare da maida kofar ta rufe. Sai da sukaje tsakiyar falo sannan ya tsaya tare da juyowa ya kalleta, Nafi itama kallansa tai, Ashraf kam wani abu ya dingaji yana taso mai, Nafi ta daure ganin kamar zuciyarta na neman yin rauni da kallan da yake mata, wanda shi kansa bai san yanayi ba. Ta daure tace ” Yaya mai kake nufi da zancen tafiya jibi?” Ashraf kallanta kawau yake baice komai ba, ta dan motsa baki sannan tace ” Yaya ke ka daukeni? Kaza? Tattabara? Ko me? Ba ka damu da ni ba, ka daina shiga harkata sannan kawai sai ka min sako akan inshirya wai jibi zanyi tafiya? In har a matsayin mutum kadaukeni banaji zaka dinga min abu haka, na rasa ya kakeso inyi da raina, ka daina kulani, na dauka na huri zuciyata nima na jure da kulaka, ka daina ko amsa wayata wannan ma na huri zuciyata na jure sai dai inma sako yanda kake min, sai dai banaji duk wannan abun da………..” Yanda bakinta yake motsi tana magana gashi tasa jambaki light pink kawai yake kallo, kasa jurewa yai ya kai bakinsa cikin nata, wanda ya hanata karasa maganar da takeyi. Wani irin salo yake mata wanda duk yanda taso taki biyemai ta kasa, kiss suke sosai wanda kana gani kasan lalai masoyan sunyi rashin juna da yawa. Bakinsa na cikin nata suna mikama junansu sakon ni mai cike da kewa Ashraf kam duk ya rikice, ya saka controlling din kansa kan kace me? Ita kanta ya rabata da kayan jikinta, nan suka fada kan kujera……..Hmmmm babban al’amari nikam ina ganin haka nai gaba. Ashraf ya dade yana kwasar garar da ya dade bai ji ba, sai dai ya rasa dalili yau jinta yake daban ita kanta yau tasan Ashraf yayi missing dinta. Suna gamawa ya rungumeta tsam a jikinsa, yana fitar da wani numfashi na farinciki, Nafi ma idanunta ta lumshe tanajin kaunarsa na kara ratsata, cikin wata irin murya mai cike da ma’anoni da yawa yace ” Baby i really miss u.” Hannu ta runkule ta dan naushi kirjinsa tace ” then y?” Ya kara jawota jikinsa yace ” dole ce ta sani hakan, saboda inasan amfani da Anisa.” D’agowa tai ta kalleshi idanunta suka ciciko tace ” rashin yarda dani ne yasa baka sanar dani ba?” Kai ya girgiza mata alamar a’a yace ” Duk duniya kece mace ta farko dana yarda da ita 100% banaji dar a kanki, sai dai ina tsoron abinda ke zuciya.” Kallan mamaki tamai tace ” kamar ya?” Yace ” in har kikasan ba da gaske nake ba, bazaki taba nuna jin haushin ki da kishinki ba yanda zasu aminta ba.” Ta dan maka mai harara tace ” shine nima kai using da feelings dina?” Sumbatar lebenta yai fuskarsa da daf da tata yace ” do u think it’s easy?” Murmushi tai, tace ” amma duk da haka ka wahalar dani.” Sumbatar idanunta yai yace “am sry Baby, na wahalar dake ni kaina na sani, shi yasa nace zan amshi punishment dina.” Ta sake murmushi tace ” maganar tafiya fa?” Yace ” Yanzu it’s eye for eye, thooth for thooth, we are in a war ni da kawu i am afraid kar wani abu ya samarmin ke ta dalilin revenge dina.” Baki ta turo tace ” Amma……” Hannu yasa ya toshe mata bakinta yace ” Baby please.” Idanunta ta rufe sannan a hankalu ta bude jiki a sayaye ta daga kai alamar to.” Mikewa yai ya dauketa yai toilet da ita. Sai daya cika musu bahon wankan sannan ya sa kayan kamshi na ruwa sannan ya sata a ciki shima ya shiga. Ta kalleshi tace ” Allah baiyi zan tsaya bikin Jibiya, thanks to someone.” Idanu ya kankance yace “someone? Do u mean me?” Ta dan murguda baki tace ” nidai ban fadi suna ba.” Kallanta ya tsaya yi, ta debi ruwa a hannunra ta watsa mai tace ” yallabai kallan fa?” Dariya yai yace ” fada kikeso?” Ta tsuke baki, shima hannu yasa duka biyu ya riga watsa mata ruwa, nan itama ta dage tana watsa mai, dariya sosai suke yi wanda kana ganinsu kasan suna cikin tsananin kaunar juna. Bayan sun gama wanka, ta jawo towel d’aya ta rufa sannan tace ” na fita.” Kallanta yai yace ” nifa?” Tamai gwallo tace ” ka dauka da kanka.” Tai d’akinsa tare da zama kan gado tana dariya. Ashraf ya fito yana zuwa ya sa hannu a gugunta ya matse da karfi, wanda ya sa ta saku kara yace ” ni kika ki daukoma towel?” Tana ihu da dariya tace ” sry Yayana na tuba na daina.” Yace ” inaa baki dainaba sai na hukuntaki tukun na.” Ganin yaki saketa yasa tace ” Yaya Nisa?” D’agowa yai da sauri ta mike da gudu tana dariya. Murmushi yai sannan ya mike sambal akan gado tare da rufe idansa. Ahhh na kosa in gama wannan case din in ganni tare da matata kullum. Abinda yake fada kenan a ransa. Washegari da safe bayan Kawu ya fita, Dan Litti yazo ya dauki Mumy da Nafi yai abuja dasu dan tacan zasu tashi gobe. Little kam taji takaici sai dai Nafi tace mata ai ita saboda makaranta, tunda su sai nan da 1mnt akace list dinsu ma zai fito. Ashraf sai dayaga tafiyarsu sannan ya kira Kb yace ” a ina kace an samu Dan Siyasan?” Kb yace ” yana nan asibitin Murtala ashe bashida lafiya ne shiyasa akaita nemansa aka rasa.” Ashraf yai murmushi sannan yace ” ganinan zuwa ka turon ward din da yake da number d’akinsa.” Nan take Kb yamai Text Ashraf yaja mota yai gaba. Bayan ya isa asibitin ne ya tafi ward din masu cancer sannan ya duba number d’akin. Knocking yai nan akace ya shiga, a hankali ya tura kofar d’akin, wani ne a kwance jikin nan duk ya rame kamar me kanjamau sannan ga wani matashi a kusa dashi a zaune. Jiki a sanyaye Ashraf ya shiga tare da karasawa bakin gadon. Matashin wanda baifi shi ba yace ” ban gane ba?” Ashraf yai murmushi sannan ya dauko complimentary card dinsa ya mika mai yace ” sunana Ashraf.” Kallansa yai, wanda hakan yasa Ashraf yace ” ba Dan siyasan dayai House of rep bane da?” Matashin yace ” shine.” Ashraf ya kalli mara lafiyan yace ” Alhaji Uba ka san Mansir?” Kallan Ashraf yai fuskarsa dauke da alamar tambaya, Ashraf yace, ” Mansir kanin Abbas marigayi mai A&A Food. Ltd?” Haryanzu dai bai fahimta ba sai dai ya maimaita kalmar A&A?” Ashraf yace ” eh wanda yake auren kanwar Hisham.” Jin sunan Hisham yasa ya fara kokarin mekewa zaune, hakan yasa d’ansa ya taimakamai ya zauna, kallan Ashraf yai yace ” ina Hisham? Ka taimaka ka kiramin shi.” Ashraf yace ” baya kasar ne yanzu haka ma shiya turoni nadubaka, baisan baka da lafiya ba.” Hannun Ashraf ya kama guda d’aya wanda Ashraf ya dana start da d’ayan hannunsa a wayarsa dake aljihunsa. Mutumin yace ” Yaro ka ba Hisham hakuri, a zahirin gaskiya nayi laifuka da dama a rayuwata ta duniyar nan, wasu na nemi yafiya wasu kuma banma san inda mutanen dana cuta suke ba, na hau mulki, dadinta yasa na manta da Allah na kwashi dukiyar jama’a sannan na cuci jama’a Hisham na d’aya daga cikin mutanen da bazan taba mantawa ba saboda nine sanadin talaucewarsa.” Ashraf yai shiru tausayin mutumin ya kamashi, ita dama rayuwa haka ne, yau in kaine gove ba kai bane. Mutumin ya cigaba, ka san kanin mijin kanwarsa?” Ashraf ya ce “eh shine Mansir din ai.”, Mutumin yai ajiyar zuciya yace ” kacema Hisham wlh wannan mutumin shine ya sani komai, shawara yazomin da ita ta neman kudi, nikuma alokacin idona ya rufe, zuciyata ta zarme ina ganin zan samu kudi mai yawa da xai sa inyi campaign ba tare da matsala ba, shi yasa na dauki shawararsa, sai dai dalilina yasa aka kama dukiyarsu mai yawa har hakan yakai ga ajalin mahaifinsa, wanda tsoro yasa nakasa fadar abinda ya faru a lokacin, ina tsoron kar nima azal ta fadamin.” Kuka ne yaci karfin mutumin ya shiga yin tari a hankali,yace ” yanzu gashinan kowa ya gujeni, wannan yaron shi kadai ke taimaka ta, shi kuma ba jinina bane rikonsa nai, nawa ‘yayan duk sun gudu sun barni.” Idanun Ashraf ne ya ciciko, yasa stop sannan yace “amma wace irin cancer ce ke damunka?” Murmushin yake yai yace ” blood, anyi maganin har an gaji shiyasa nace shima yaron nan ya barni kawai a gida in kwanana yazo in tafi.” Ashraf ya kalli matashin, hawaye yaga yana gogewa, tausayi ya kara kamashi, ya kalleshi yace ” ya sunanka?” “Abdulmalik.” Ya fada Ashraf yace ” wani aiki kake?” Yace ” kasuwanci nake a kwari, inada karamin shago.” Ashraf ya kara tausaya mai, yace ” aure fa?” Yace ” shekarar Alhaji 5 kenan ba lafiya ina ni ina tunanin aure?” Ashraf yai shiru kafin daga baya yace ” ka zo ka sameni a address din dake jikin katin, inada sha’awar kasuwanci inyaso sai in bude ma babban shago sai ka dinga mana.” Kallan mamaki Abdulmalik yama Ashraf, shikam Uba kuka kawai ya saka yana godiya kamar me, Ashraf yace ba komai, sannan ya ajiye musu kudi dubu 30 ya fita. Yana fita ya runtse ido cikin tsananin tausayi yace ” Rayuwa kenan.” ********** Kawu ne zaune kusa da Asim ya kalleshi yace ” wlh kaji na rantsema yau itace rana ta karshe da zaka ganni anan, in har baka fadamin inda ka samu takardun nan ba.” Asim jiki a sanyaye cikin tsoro yake kallan Mahaifinsa. Kawu yace ” to shikenan, ka karashi rayuwarka anan ni dakai kuma……” Da sauri Asim yace ” Sata nai a d’akin Ashraf.” Idanu kawu ya zare cikin tsananin mamaki yace “mene?” Nan Asim ya bashi labarin abinda ya faru. Hannu kawu yasa cikin takaici ya wankama Asim wani wawan mari yace ” bakada hankali ne? Me yasa ne nikam kwakwalwar kifi Allah ya d’orama? Kana tunanin Ashraf Shine zai ajiye takardunsa a fili? Yaron da nafi shekara 10 ina sawa a min bincike akan ma yawan dukiyar Abbas daya barmai amma sam hakab ya faskar saboda tsananin wayau da takatsantsan irin na yaron, shine kakeso kacemin ya ajiye takardu a d’akinsa?” Asim yai shiru, Kawu ya naushi iska cikin takaici yace ” kana xaune sokon banza ya kamaka cikin ruwan sanyi, kai wannan yaro nikam bansan jakantarka ba.” Waje yai da sauri cikin takaici, yana fitowa Anisa ta kirashi tace “Abba nikam Mumy tayi tafiya ne?” Cikin fada yace ” kamar ya?” Tace ” a’a naga bangarenta ansa kwado ne sannan su Afra sun koma bangaren Little shine dazu da Afra tazo tacemin ai Mumy tayi tafiya.” + Cikin tashin hankali yace ” ina Ruma zataje ba da sanina ba? Sannan d’azun nan fa na barta a gida.” Kashe wayae yai a zuciye ya kira wayar Mumy a kashe ya jeta, nan fa idanunsa suka kada. Ya na kokarin saukowa daga steps din gun sai ga Ashraf. Kallansa ya dingayi harya iso, Kawu ya kalleshi yace ” ina Uwarka?” Ashraf yai dariya yace ” haba kawu wannan ai wayan zagine, kace ina matarka dai?” Kawu ya fara huccin takaici, Ashraf yai murmushi tare da girgizamai dan yatsa yace ” no no no ai bai kamata ka nuna tashin hankalinka tun yanzu ba, inkai haka u will spoil the game, it won’t be fun.” Ya sake murmushi sannan yai ciki. Wani irin ihu kawu yasa na takaici, Ashraf ya wani murmushi sannan yai ciki😏 Kawu cikin tashin hankali yai gida, b’angaren Mumy ya nufa ko mota ma bai rufe ba, yana zuwa kuwa yaga kwado a kofar da zata sada ka da b’angaren, Ruma! Ruma! Ruma! Abinda kawai yake fada kenan cikin tsananin tashin hankali, kofar ya taba tare da rike kwadan. Ya dade a haka kafin ya koma na sa bangaren cikin takaici, ba shakka dolene ya nemo Ruma dan kuwa in har bai ganta na kwana biyu ba bayaji hankalinsa zai kwanta, a iya saninsa mutane kan ce in har ka auri mutum ka zauna dashi na shekaru to fa soyayya na gushewa sai dai zaman hakuri da na ‘ya’ya, shikam a yanda yakejin zuciyarsa gaskiya bai yarda da hakan ba, kaunar Ruma da yakeyi bayaji ko tsufa yai da ita zai daina santa. Ashraf kam gun Kb ya shiga Kb yace ” kaje kuwa?” Ashraf yace ” naje sai dai abin ba dadi.” Ganin bayasan maganar yasa Kb yace ” yanzu mutuminka ya fita.” Ashraf yadan yi tsaki kadan yace ” na ganshi, ya waccan fa?” Ya fada yana kallan inda aka killace Asim.” Kb yace ” yanacan.” Ashraf ya kalli Kb yace ” bari inje inada abinyi.” Nan ya fito, baiga kawu ba hakan yasa yai murmushin mugunta yace ” ko kaifa, dan banaso ka badani.”+ “********** Kawu kuwa gida ya taho da gudun gaske yana zuwa ya ajiye mota ya fito, ko kofar bai rufe ba saboda tsananin firgici, bangaren Mumy ya nufa, kwado kuwa ya gani daga kofar da zata sadaka da bangarenta, kofar ya shiga jijigawa cikin wani irin kunar rai, ba shakka bazai taba yarda a dauke mai Rumansa ba, shifa a iya saninsa yaji ance in har mace da namiji sukai aure na wasu dan shekaru to fa soyayyarsu na tafiya sai dai kimma da hakuri yasa zama ya d’ore, sai dai shikam abin ba haka yake ba, yanaji dole ne ya zauna da Ruma ko ya samu nutsuwa, kofar ya dinga jijigawa, ganin ba yanda zaiyi yasa yai b’angarensa cikin tashin hankali. Waya ya dauka ya dinga kiran layinta sai dai duk a kashe, tashin hankali kam ya shigeshi a wannan ranar. ******** A can bangarensu Nafi kuwa, sun isa Abuja lafiya, sai dai tun da suka sauka Nafi ke kwara amai, gashi sam ta kasa cin komai, Mumy cikin damuwa tace ” Nafi anya kuwa ayi tafiyarnan dubifa yanda kiketa amai.” Murmushin yake Nafi tai tace ” Mumy karki damu, tafiyar mota ce kawai ta sani haka, kinsan mu filanuwa akwai mu da hararwar mota.” Mumy ta gamsu da zancen Nafi, a haka har suka kwanta bacci. Da safe kuwa jirginsu ya d’aga. Sai kasa mai tsarki. *********** Shikam Ashraf da safe bayan ya tashi ya fito daga gidan shi da Dan Litti, wata envelope ya mikama Dan Litti yace ” yaje gidan Dady kawai ya ba mai gadi yace a bashi, ya juyo karya bari Habib ko wani daga cikin gidan ya ganshi.” Dan Litti ya amsa da to, sannan ya ja mota yai gaba, yana zuwa kofar gidan kuwa yai sa’a ba kowa a gun sai mai gadi, hakan yasa ya mai horn, mai gadi ya taso da sauri, Dan Litti ya kwama sunglasses tare da kallansa ya mikamai envelope din nan yace ” kaga mai gidan.” Mai gadi ya amsa yana kokarin tambayarsa inji wa, yaga Dan litti ya ja mota yai gaba. Cikin rashin kulawa ya koma ciki ya nufi ban garen Dady, Dady lokacin yana kishingide a falo abin duniya duk ya taru yamai yawa yaji kwankwasa kofa, nan yace a Shigo. STORY CONTINUES BELOW Mai gadi ya shiga a hankali ya gaidashi tare da mikamai sakon, Dady yace ” inji wa kenan?” Mai gadi ya dan sosa keya yace ” wlh ni kaina ban sani ba.” Dady ya sallameshi sannan ya bude wannan envelope din wata karamar Mp3 ce ta fado tare da yar karamai takarda. Fuskarsa dauke da mamaki ya sa earphone din a kunnensa tare da danna play. Kallo d’aya zakamai kasan yana cikin tsananin tashin hankali da jin abinda ake fada, mikewa yai tsaye cikin tashin hankali idanunsa suka kada sukai jaa, mamaki tare da firgice ne suka kamashi, takardar ya sunkuya ya dauka a kasa bayan ya gamajin sharhi daga bakin Alhaji Uba, address ne kawai rubuce a jiki na asibiti tare da number d’aki. Makullin mota kawai ya dauka ya fito da sauri tare da fadawa cikin motarsa, ya ja ta da gudu yai waje. Bai tsaya a ko ina ba sai asibitin Nassarawa. Nan yabi address har zuwa inda ya isa number d’akin, jikinsa ne yai sanyi ya kasa bude dakin, ba shakka in har abinda yaji gaskiya ne shikam rayuwarsa ta kare, kenan ya zalinci Abbas akan hakkin da ba ruwansa, kenan duk yanda ya dauki Mansir ashe shi ne babban soko yana zaune ana amfani dashi. Dashi Mansir yai amfani yai achieving din duk abinda yakeso a duniya. Yana tsaye rike da kofar yaji an bude kofar daga ciki, wata nurse ce ta fito, kallansa tai ta gaisheshi sannan tai gaba. Kofar a bude take hakan yasa daga waje yana kallan Uba wanda ke kwance duk ya tsome, shikanshi Uban kallansa yake dan tabbas bazai iya manta fuskar Hisham ba. A hankali Hisham ya fara takawa zuwa ciki har ya isa kusa da gadon ya kalli Uba zaiyi magana Uba yai saurin katseshi da cewa ” Hisham na gode da ka ziyarceni kafin rayuwata ta kare, ka yafemin abinda ya faru.” Dady kallansa yai cikin wani yanayi yace ” me nakeji game da Mansir…..” Uba ya kamo hannunsa hakan yasa Dady ya zauna kusa dashi, Uba ya kara zayyanamai komai daya faru tare da doramai ” nayi babban laifi, sai dai ba’a maida hannun agogo baya, Ka yafemin Hisham.” Hankalin Dady yayi mugun tashi, ya mike jiki a sanyaye ba tare da yace komai ba yai waje. Tafiya yake kamar mara laka a jiki, har ya isa motarsa, ya shiga ciki ya zauna tare da dora kansa akan sityarin motar, me na aikata? Abinda zuciyarsa ke tambayarsa kenan, waya ya dauka dan kiran kanwarsa, sai dai a kashe ya jita, haka nan ya tada mota cikin karyewar zuciya yai gidansa. Yanzu kam ya gane komai daya faru dama trap ne da Mansir ya shirya. ********* Ashraf bayan ya ga Dady ya koma gida dan yana biye dashi shima ya nufi gun aiki.” Bayan azahar suka shiga meeting, sai 4 suka fito, sun fito dukansu Kawu na tsakiyar mutane suka dan tattaunawa, Hisham ya karaso gun. Hisham nada tsananin zuciya wanda duk itace tasashi yin abubuwan da suka faru a baya, sam ransa ya gama b’aci baima kula da mutanen dake tsatsaye a gun ba, ya karaso gun Kawu. Cikin tsananin mamaki kawu ya kalleshi yace ” Yaya ya…….” Mari yaji an tsinkamai nan fa kowa ya kallesu, kawu mamaki ya kamashi, ya rike gun yace ” Hisham ba kada hankali ne?” Dady yai wani murmushin takaici yace ” au yanzu dakaji mari ka manta da yayan?” Kawu ya kalli mutanen dake gun ciki kuwa harda Ashraf wanda takaici ya kara kamashi, ya daure yace ” yaya muje office dina da alama ranka ne a b’ace.” Dady sai a lokacin ya kula da mutanen gun, suka hada ido da Ashraf, nan sukai office din Kawu. Ashraf yai murmushi yace ” Whoa lalai Dady ba sauki.” Nan yai nashi office din hankalinsa a kwance. Kawu kam suna shiga yasa key ya kalli Dady yace ” Yaya meye hakan…..?” Idanun Hisham sunyi jaa na takaici yace meye hakan? Dady yace ” wai me……” Jiyai Hisham ya karamai wani marin, dady ya fusata yace ” malam meye hakan?” Dady yace ” waccan marin na farko na rainamin hankali dakai ne, wannan kuma na takaicin hada zuri’ata dakai danai ne.” Kawu ya hada rai yace ” wannan wani irin banzan zance kake? Mu bayara ba ba komai ba?” Hisham ya nuna Kawu da dan yatsa cikin kunar rai yace ” wlh kaji na rantse maka bazan yafe ma rainin hankalin daka min ba, ba zan yafema sanadin mahaifina dakai ba, bakuma zan yafema amfani dani dakai ba ka auri kanwata, ba kuma zan yafema na amfani dani dakai ba wajan kashe Abbas ba.” Kawu kallan Hisham kawai yake, sai yanzu ya fara gane inda zancensa ya nufa, cikin rashin damuwa Kawu yace ” ni ban fahimceka ba.” Hisham yace ” naji komai daga Alhaji Uba, munafikin banza da wofi, wlh Mansir nayi danasanin saninka a rayuwa, kai kani ne ga Abbas sai dai ko kadan halayenku ba iri daya bane, shiyasa a koda yaushe kake losing akansa, dukiyar da kake takama da ita ficika ba kai ne kai wahalarta ba, tarawa akai ka kwaceta karfi da yaji, matar da kake takama da ita, ba sanka take ba, ita ma karfi da yaji ka kwace ta, ko da wasa bazaka taba zama Abbas ba duk wannan abun daka kwata kuwa.” Idanun Kawu suka rikide babban takaicinsa a duniya ace mai daga dukiyarsa har matarsa ba nash bane, wani irin abu ya fara da fuskarsa, hannu yasa ya shake Dady. Cikin wani mugun yanayi yace ” karyane, komai nawane, uban waye ya isa yace dukiya da Ruma ba nawa bane?” Hisham da kyar ya fizge hannun Mansir, cikin tsananin mamaki ya kalleshi yace ” kana tunanin wannan abun da kakeyi shi zai sa su zama naka? Ruma da kake tunanin wai hakan santa kakeyi yanzu na fahimci obsession ne ke damunka, lalai kana cikin gararin rayuwa, kuma wlh ka gaggauta ba kanwata takardarta.” Yana kaiwa nan yai waje. Wani irin ihu Kawu ya saki yana cewa ” waye ya isa yace ba nawa bane?” Ya dade a haka kafin hankalinsa ya dawo jikinsa, nan fa ya shiga tunani uban waye ya sanarma Dady abinda yake a b’oye?” Fitowa yai ya nufi office din Ashraf. Kofar ya bude ba tare da kwankwasawa ko sallama ba, a zaune yaga Ashraf yana aiki yana kuma kurban tea dake gefensa, kana ganinsa kasan hankalinsa a kwance yake, jin yanda aka bude kofar ne yasa ya kalli gun, ganin kawu ne yasa ya sakar mai murmushi tare da dagamai hannu yace ” Hi!” Ran Kawu ya kara b’aci matsowa yai gunsa ya kuramai ido. Ashraf ya kalleshi cikin rainin hankali yace “ya akai? Ko shayin zan hada ma?” Kawu yanasan ya tambayeshi ko shine ya fadama Hisham sai dai yana tsoron karya buloma kansa aiki, yaje haka kawai Ashraf din bai san komai ba ya sanar dashi. Daurewa yai ya juya, har ya kai tsakiyar gun yaji Ashraf yace ” Ba tambaya kazo kayi ba?” Kawu ya tsaya cak tare da juyowa ya kalleshi, Ashraf ya mike tare da matsowa inda kawu yake cikin gadara, ya dan tafa hannayensa biyu a hankali yace ” Ohhhh kana tsoron kar inji?” Kawu ya buga mai wani kallo, Ashraf ya dan rike kunne yace ” sry kanin Abba, sai dai ya zamuyi? Da alama Dady fa yasan komai.” Idanu kawu ya zaro cikin rawar murya yace ” kai kai ne ka…..” Dariya Ashraf yasa yace “kawu meye hakan? Kar ka badani mana, ya muryarka zatai rawa daga nan?” Kawu ya daure ya nuna Ashraf da yatsa yace ” Ashraf wannan shine last warning dina akanka, ka shiga hankalinka dani, kada kai tunanin komai yana tafiya yanda kakeso kai tunani kaci riba akaina, wlh kayi min kadan, tsohon ka ma bai isa yaja dani ba bare kai da aka haifeka a gabana.” Hannu Ashraf yasa ya kankame jikinsa yace ” Ahh so Scary!!” Kawu ransa ya kara baci yace ” ina tausaya ma dan wlh…….” Ashraf ya hade hannayensa biyu yace ” plzz na rokeka kar ka tausayamin dan Allah, Dan Allah na rokeka kana kwafsamin in naji zancen tausaya war nan.” Zuciyar kawu ta cika taf da takaici, a zuciye yai hanyar fita, Ashraf yace ” ka tabbatar kanacin abinci mai kyau kafin ka shiga prison dan naji labarin abincin can ba dadi.” A zuciye kawu ya bankade kofa yai waje. Yana fita ya kara kallan kofar cikin takaici yai kwafa yace ” in ni banje ba kai ka ziyarci kabarin ka ai.” Daga ciki kuwa yana fita Ashraf ya furzar da wata iska tare da zama akan kujera Ya kira Uncle Salim. ********** Su Nafi an isa kasa mai tsarki sai dai Nafi kam jiki yaki dadi sam, haka suka shiga d’akin da aka basu a kasar madina ita kam duk ta gama fadawa. Mumy cikin kulawa tace ” Nafi ya kamata muje asibiti nikam naga hararwan nan ta isa ga ba abinci kike ci ba.” Nafi ta dago tace ” Mumy Allah in na huta nasan komai zai tafi.” Kallanta Mumy tai tace “kinga yanda kika rame kuwa?” Nafi tai murmushi tace ” Allah ba komai Mumy.” Shiru Mumy tai jikinta yai sanyi. Nafi kam gata dai a kasa mai tsarki garin da take masifar san gani amma gashi tazo a kwance ba lafiya. ************** Da yamma Ashraf ya koma gida, yana fitowa daga mota yaga Anisa na tahowa, hade rai yai jakarsa ya dauka yai kamar bai ganta ba, Anisa ta karaso da saurinta ta rike rigarsa ta baya. Dole hakan yasa ya tsaya, juyowa yai ya kalleta yace ” ya akai?” STORY CONTINUES BELOW Idanunta ne suka ciciko tace ” yaya.” Kallanta yai yace ” ya akai?” Ta share kwallarta tace ” jikin Umma ba dadi, ga ya Asim har yanzu shiru.” Kallanta yai kawai baice komai ba. Anisa ta rike hannunsa tace ” yaya muje dan Allag ka duba Umma, itama tun dazu take nemanka.” Bai musa ba nan suka nufi bangaren Umma. Tana kwance a d’aki tana ganin Ashraf ta shiga kokarin mekewa zaune. Ashraf ya kalleta sannan ya kalli Anisa yace “dan bamu guri ko?” Anisa ta juya ta fita. Umma ta karasa zama sannan ta kalli Ashraf tace ” Ashraf ya maganar Asim?” Kallanta yai sannan yace ” Asim? Ina zan sani in har ku iyayensa baku sani ba?” Mamaki ne ya kamata tace ” Ashraf na rokeka dan Alla…….” Ka tseta yai yace ” duniyarnan al’amuranta na bani mamaki, har kasan zuciyarki daga ke har dan naki banaji akwai daidai da kwayar zarra da san ‘yan uwantaka da kukemin, banda neman halakani da kukeyi, amma wai ko kunya ni kike cewa in taimaki danki?” Umma jikinta yai sanyi dana sani suka ziyarceta tace ” Ashraf na sani sai dai……” Katseta ya sake yi yace ” ni a wannan lokacin ba abinda zaki fada da zan aminta dashi, abu d’aya nazo fada miki yanzu, in har kinason danki ya fito, sannan kinasan farincikin ‘yarki to inaso nima kimin abu d’aya.” Da sauri tace ” zan maka shi ko menene.” Ya kalleta yace “inaso idan na nemi shedarki akan mutuwar mahaifina ki bada shaida yanda kika sani tsakaninki da Allah.” Cikin tsoro ta kalleshi tace ” Ashraf me kake fada haka?” Yace ” wannan ba damuwa ta bace, iya abinda zance da ke kenan, in kuwa har kikaki bada shaida kamar yadda nace to ki jira abu biyu, na farko danki dolene ya ziyarci gidan yari, na biyu kuwa ki jira takardar mutuwar auren ‘yarki kinsani sarai yanda Anisa take sona, na tabbata bazata taba yafe miki ba inhar taji kece sanadiyar mutuwar aurenta.” Hankalin Umma ne yai mugun tashi,Ashraf yace ” sai ki zab’a da mijin da bai taba sanki ba, bai kuma damu da ke ba da ‘ya’yan da kika haifa kike sansu kamar ranku suma haka, sai ki duba kiga wanene zai fi miki amfani nan gaba.” Yana kaiwa nan yai waje. Hawaye ne ya biyo kuncin Umma lalai yau tana ganin tashin hankali ina zata sa kanta da rayuwarta??????? ************ Dady zaune a d’aki kusa da matarsa cikin kunar rai yake sanar da ita komai, hankalinta yayi tsananin tashi da jin abinda ya faru sai dai abinda basu sani ba, Habib wanda ya taho d’akin, cak ya tsaya jin zancen da sukeyi. Hankalinsa yayi mugun tashi da jin abinda ya faru, muryar mahaifiyarsa yaji tace ” Dadyn Habib yanzu ya zamuyi da hakkin maraya da kuma wanda ya rasu?” Dady cikin mamaki ya kalli matarsa yace ” dama kin sani?” Kallansa tai cikin kulawa tace ” najiku a ranar da abin ya faru da safe kuna zancen, wanda hakan yasa nai saurin kiran Ruma na sanar da ita sai dai bakin alkalami ya riga ya bushe dan alokacin Abbas ma yana cikin mota.” Jikin Habib ne ya shiga rawa, muryar Dady yaji yana cewa ” Na shiga uku, tunda nake a rayuwata ban taba tunanin zan hada kai in kashe wani ba sai gashi nayi akan mijin kanwata wlh kinji na rantse miki tun bayan faruwar wannan abun duk sanda na kwanta sai nayi mafarkin Abbas yana min murmushi wanda hakab ke kara karyamin zuciya sai dai san abin duniya yasa na kasa yin nadama sai ma tunanin yanda zan kara mallakar wata dukiyar tasa da nakeyi.” Gaba d’aya jikin Habib ne ya shiga rawa, da kyar ya iya saukowa daga saman dakin, d’akinsa ya nufa ya zube a kasa sam kwakwalwarsa ta dauke ya rasa ma tunanin mai zai fara abu d’aya kawai yake mai yawo a zuciya mahaifinsa da mahaifin Little sune suka hadu suka kashe mahaifin Ashraf wannan wani irin mugun al’amari ne????? ************ Kawu ne a d’aki sai safa da marwa yakeyi dole yasan matakin dazai dauka akan wannan yaron, dan kuwa baiga mai rabashi da Ruma ba baiga kuma bai rabashi da dukiyarsa ba. Akwatinsa ya dauko na karkashin gado, sai dai ya zaro takardar wasikar da Abbas yamai yaga tagardar ba komai, hankalinsa ya tashi matuka ya fito daga d’akin ya nufi bangaren Umma. Anisa ce kadai zaune a falo, ya shigo kallansa tai tace “Abba kazo duba Umma ne?” Fuskarsa a hade yace ” ke kika bud’emin akwatin kasan gado na?” Gabanta ne ya fadi cikin i-ina tace ” ba ni bace.” Tsawa ya daka mata yace ” tun bayan shigarki d’akina ba wanda ya kuma shiga bazaki fadamin gaskiya ba.” Shiru tai sai gabanta dake faduwa, jitai yace ” Ashraf kika ba?” D’agowa tai ta kalleshi a tsorace tace ” wlh ba ruwan yaya ni……” Lebensa ya ciza da karfi yai waje a zuciye. Bangaren Ashraf ya nufa wanda rabansa da bangaren har ya manta. Jin kwankwasa kofa yasa Ashraf ya mike dan dama yana zaune ne tun dazu yana neman wayar Nafi tunda yasa layin Mumy shi ya amsa da kansa to na Nafin kuma sam ya ki shiga. Yana bud’e kofa yaga kawu a tsaye. Ashraf cikin mamaki yace ” lafiya?” Hannu kawu ya mikamai yace ” bani wasikar daka dauka a d’akina.” Ashraf ya mai kallan mamaki yace “wasika?” Kawu yace ” wanda kasa Anisa tadaukoma.” Ashraf yace ” ohhh wannan? Nikaina bansan inda yake ba.” Kawu yace ” mene?” Ashraf yace ” kunya kakeji kayi karya ka b’oye akan Mahaifiya yace karna auri ‘yarka?ko kuwa kunyar mai illa dakai kakeyi?” Kawu ya juya bai kara magana ba cikin takaici lalai dole ya dau mataki akan yaron nan dan kuwa da alama ya gama Rayuwa tayima mutane 4 zafi, na farko Kawu wanda yake tunanin yanda zaiyi ya halaka Ashraf ba tare da sanin kowa ba. Na biyu Habib wanda kunnensa ya jiyomai tashin hankalin dayafi karfinsa. Na uku Umma wacce ta rasa ina zata sa kanta, ‘ya’yanta zata ceta ko kuwa mijinta. Sai na karshe Hisham wanda nadamada danasani suka taru suka mai yawa. Yau kwanan su Nafi 4, da barin gari, jikinta dai haryanzu ba wani sauki sai dai ba kamar da ba, yanzu tana dan cin kayan itace (Fruit) Mumy kam ta kasa daurewa ranar suna zaune a d’aki ta kalleta tace ” Nafisa anya ba ciki gareki ba? Nafi cikin tsananin mamaki ta kalli Mumy gabanta ya fadi. Mumy ta matso kusa da ita tace ” bakida kowa a garin nan da ya wuce ni, shiyasa nima na cire kunyar surukantaka na tambayeki, Nafi a matsayin ‘ya na daukeki ba sirika ba, nayi dana sani sosai na kin amincewa dake danai tun farko har nake nuna miki cewa mace mai ilimi itace ta dace da Ashraf.” Kan Nafi na kasa ta kasa dagowa. Mumy ta dafata tace “muje asibiti.” Da sauri Nafi tace ” a’a Mumy.” Dariya Mumy tai tace ” me? Kunya kikeji?” Nafi tai kasa dakai. Haka Mumy ta matsa mata dole da yamma suka nufi asibiti. An mata gwaje gwaje nan aka tabbatar musu tana da ciki na sati bakwai, farin ciki agun Mumy baya misaltuwa, ta kalli Nafi cikin zumudi tace ” kinsanar da Ashraf?” Kanta ta girgiza alamar a’a tace ” ni ai ko waya bamuyi ba tunda muka taho.” Mamaki ya kama mumy tace ” akan me?” Nafi tace ” wlh bakomai, kawai dai nasan yanada al’amuran dake gabansa ne dayawa.” Mumy tai shiru, jikinta yai sanyi ba shakka kam yanada su dayawa. Nafi ta kalleta tace ” Mumy karmu fadamai harsai ya gama.” Kai Mumy ta daga alamar amincewa. ************ Ashraf na zaune gidan Uncle Salim dashi dasu Auwal Max. Ashraf ya kalli Auwal yace ” kayi hakuri kaga haryanzu bamu maidakai ba.” Auwal ya girgiza kai yace ” ba komai, acan din ma me nakeyi banda wahala, matata ta rabu dani ko ince tunda taga banida komai ta fitineni sai dana bata takardarta, ‘ya’yan da muke dasu guda biyu ta kwashesu, ni ba sana’ar arziki ba sai dai inyi can inyi can.” Ashraf ya kalleshi cikin tausayawa, Auwal yai murmushi yace ” na sani alhakin Abbas ne ke bina, mai gida ya kula dani sosai amma naci amanarsa.” Ashraf ya mike jin idanunsa na rawa ba shakka an zalunci mahaifinsa dayawa, shiyasa akullum in ya tuna akwai ranar hisabi sai yaji zuciyarsa tayi wani dadi. Sako ne yashigo wayarsa daga Little. Cikin mamaki ya bude _Yaya dan Allah kazo gidan gona na Mumy dake bayan gari akwai matsala._ Abinda aka rubuta kenan a sakon, shiru yai yana kara kallan sakon. Kb ya kalleshi yace ” ya akai?” STORY CONTINUES BELOW Ashraf ya mika masu wayar, sannan yace Auwal ya shiga ciki. Kb ya karanta yaba Salim shima ya karanta, Ashraf ya kalli Kb yace ” bari inje.” Uncle salim ya kalleshi yace ” anya Ashraf baka tunanin da matsala kuwa?” Ashraf yai murmushi ya kalli Dan Litti yace ” Mutumin muje?” Dan Litti ya mike, Kb ne ya dafa Ashraf yace ” Ashraf.” Ashraf yai murmushi yace ” karka damu, kawai dai nan da 20mins ka kira ‘yan sanda kuzo gurin.” Kb ya kalleshi cikin kulawa, Ashraf ya kalleshi sannan ya kalli Uncle yace ” cikin abu biyu akwai d’aya, ko dai da gaske wani abun ne ya samu Little kaga kuwa in naki zuwa ko me ya sameta daga baya bazan iya yafema kaina ba, ko kuma trap ne Kawu ya shirya min.” Salim yai shiru tabbas ya gamsu da bayanin Ashraf, ya mike yace to muje tare. Ashraf ya girgiza kai yace ” A’a Uncle karka damu ba abinda zai faru.” Sun fito dashi da Dan litti suka shiga mota sukai gaba. A hanya ya turama Little sako akan gashinan zuwa. Sun isa can waje gari inda gidan gonar Mumy yake, da sauri ya fito ya shiga ciki. Yana shiga cikin gun yaji daga baya ta waje an datseshi. Tsayawa yai cak ya kurama kofar kallo. Sannan ya kalli cikin gun, ba komai agun, kajin ma babu ga kajinan nan wayam. Dan Litti daya taho yazo yin kwana yaji an kwadamai wani katako. Nan ya fadi kasa a sume. Ashraf kam da sauri ya koma bakin kofar ya fara jijiga. Wayarsa ce tai kara, nan ya zarota. Ganin number Little yasa ya daga da sauri. Jiyai an sheke da dariya, da sauri ya danna record a jikin wayar sannan yace ” Kawu ina Little?” Kawu ya sake dariya yace ” kai da Little sai dai ranar tashin kiyama, dan kuwa kai daga nan sai kabarinka.” Ashraf cikin mamaki yace ” me kake shirin yi?” Kawu ya sake dariya yace ” me? Are u scared?” Ashraf yai shiru. Kawu yace ” Kasan dai Maryam ‘ya tace, ‘yata kuma wacce na haifa da Ruma, kana tunanin zan iya halakata ne? Na dauka u are smart ashe kaima kan baya jaaa.” Ashraf cikin fada yace ” me kake tunanin yi?” Kawu yasa dariya yace ” kanada sako gun tsohuwarka ne?” Ji yai alamar kauri hakan yasa ya jujuya mai zai gani? Wuta ne ya fara ci ta waje. Kawu yace ” ina jiranka.” Ashraf yace ” ka kashe mahaifina yanzu ni zaka kashe? Sannan kacigaba da zama da mahaifiyata?” Kawu yai murmushi yace ” it’s unfair ko? To amma ya zakai, wannan itace kaddararka Abbas na kasheshi ne saboda ya kwace komai da nakeso a rayuwa, kai kuma zan kasheka ne saboda kana neman rabani da abinda ya zama mallakina.” Ashraf zai sake magana kawu yace ” kaje kai lokacinka yayi mu ba yanzu ba.” Yana kaiwa nan ya kashe wayar. Dariya ya karayi sannan ya fito daga bangarensa ya goge last call din dayai ya kaima little yace ” Little wayar Nafin ma shiru, na kasa samunsu duka.” Little tace ” insun kira zan kawoma Abba.” Yace “yauwa my Little sannan yai gaba.” *********** Ashraf kam suna gama waya da kawo ya kalli wayarsa sannan yai wani murmushi tare da kiran Kb, yace “kuyi sauri.” Nan kb ya amsa da to. Ashraf nan ya shiga tuno abinda ya faru. A safiyar yau ne ya samu Little da kansa har bangarensu. Ya kalleta yace ” duk sanda Kawu yace ki bashi wayarki karkiyi musu ki mikamai sannan karki tambayeshi me zaiyi dashi.” Ta amsa da to. Sannan ya fito ya tafi shida Dan litti sukai gidab Salim. A hanya ya kallu Dan Litti yace ” mutumin nasan baka da tsoro sai dai abinda nake shirin yi har lafiyarmu zai taba.” Dan Litti yace ” karka damu yallabai ai komenene indai har bai sabawa shari’a ba to bazan taba yima musu bama bare inkiyi.” Bayan sunga wannan sakon Ashraf ya mai murmushi kafin ya mikamai, dama Kb ya san komai. Murmushi ya sakeyi yace ” abinda nakeso kayi ka taimaken kayi cikin gaggawa Alhaji Mansir, dama burina shine kayi nufin kasheni wanda hakan zai kaimu gun ‘yan sanda daga nan kuma komai zai fara fitowa dala dala.” Zafin wutar ne ya fara damunsa gashi har ya fara shigowa ciki. Tari ya shiga yi dan hayaki sai shigamai hanci yakeyi duk ya dameshi. Tari yake sosai wanda hakan ya kaishi ga suma. Dakyar su Kb suka iya b’alla kofa, nan suka ciroshi akai asibiti dashi. ‘yan kwana kwana dama suka kira. Dan Litti kam ana samai ruwa a hanya ya farka, sai dai gefen kansa sai jini yake yi. Sun isa asibiti da sauri akai emergency dasu. Dan litti aka mai dinki shi kuma Ashraf har drip aka samai. Nan Kb ya kira shugabansu na gun aiki ya sanar dashi ga report nan ankawo musu anyi anyi attempting din kashe wani. Nan shugaban yace “yanzu zai turo Team dinsa su dau case din.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *