JALILA CHAPTER 6
Har yasa hannu zai bude dakin nata, sai kuma naga ya maida hannunsa, komawa yai d’akinsa, yana shiga ya rufe. Bandaki ya shiga yai wanka sannan ya kwanta. Jalila kuwa tayi gurum a d’aki, tana nan a zaune, da kyar ta iya tashi tai fitsarin da ya matseta. Shiru tai tana tunanin abinda ke faruwa, Goggo! Hawaye ne ya zubo mata, haka ta kishingida a kan gado har bacci yai gaba da ita. Zazzabi ne ya kara hawa mata, wajen asuba ta farka. Haka tai ta karkarwar sanyi har aka shiga sallah, da kyar ta mike tai sallah sannan ta samu ta kara kwanciya.+ Sai wajen karfe 10 Ummy ta turo Ameera dan kai musu abincin safe. Yanda taga Jalila ne yasa tasan ba lafiya ba, a ranta tace ko first night din ne? Ameera ta daure ta mika mata tiren tace “Ga breakfast dinku.”3 Jalila kuwa da kyar ta iya cewa “Banajin yunwa nikam.” Yanda taga Jalila tayi ne yasata saurin cewa “Lafiyarki kalau kuwa?” Jalila tace “bana d’anjin dadi ne.” Cikin mamaki Ameera tace “ina yayan?” Jalila ta girgiza kai alamar bata sani ba. Da sauri Ameera ta ajiye tiren ta sauka kasa da gudu. Ummy na zaune akan dinning itada Sagir tana tambayarsa menene dan ta kula jiya sai dare sosai ya dawo, sannan yanzu ma taga yana kokarin fita shine ta sashi zaman cin abincin dole. Ameera ce tazo da sauri tace “Ummy batada lafiya fa.” Ummy tace “wa? Jalila?” Sagir ne ya mike da sauri, a rikice ya haura saman. Tana kwance sharkab a kasa hankalinsa yayai mugun tashi, har yakai hannu zai dagota sai ya fasa, da sauri ya fito yana yina Ummy magana da karfi. Ummy kizo, Ummy. Ummy da itama take ta sauri ta shigo d’akin hankalinta a tashe. A kasa suka ganta. Ummy ta rungumota jikinta, zafin da jikinta ya dauka ne yasa hankalinta ya tashi. Ta kalli Sagir rai a bace tace “buga mai kofa.” Sagir ya mike ya nufi dakin Hassan. Yana kwance akan sallaya yanajin lecture na Sheik Ahmad Deedat, jin knocking yasa ya mike ya bude kofar. Sagir ya kalleshi yace “kazo.” Haka kawai yace ya juya, bai musa ba yabi bayan Sagir, gani yai ya shiga d’akin sa na da. A bakin kofar ya tsaya, Jalila ya gani a kwance a jikin Ummy. “Ummy!” Kallansa tai rai a bace tace “Hassan me kenan?” Yace “me ya faru?” Sagir ta kalla, tace “Sagir muje akaita asibiti.” Sagir da sauri yai waje, duk ya rikice, gani yake kamar duk laifinsa ne. Ummce y ta kalleshi tace “ni zan kaita mota?” Karasowa yai ya d’agata. Jin an d’agata yasa ta bude ido a hankali, kallansa kawai tai sannan ta maida idan ta rufe dan wani irin jiri take ji. Shikam fuskar nan a hade ya ajiye ta a bayan mota. Ummy ce ta fito itada Ameera ta kalli Sagir tace “Sagir ku kaita asibitin, sai muje ya ake ciki.” Yace to, sannan ya shiga mota. Ko kallan Hassan batai ba ta juya ciki. Sagir ya kalleshi yace “Yaya mu tafi?” Yace “kuje ni banasan asibiti ka sani, amma me ya sameta?” Ameera tace “Yaya aikai za’a……” Kallan daya mata ne yasa ta guntse maganar ta, juyawa yai kawai yai ciki. Sagir ya kalli Jalila dake cikin mota, shiga motar yai yaja suka fara tafiya. Ameera tace “muje Standard tunda yafi kusa.” Bai musa ba ya wuce, Ameera ta kalleshi tace “Yaya menene? Naga hankalinka a tashe.” Kai ya girgiza kawai baice komai ba. Shiru sukai har suka isa asibitin. Ameera ce ta kamata suka shiga ciki. Sagir yaje a ciro musu file, yace Ameera ta zaunar da Jalila. Jalila ta kalli Ameera tace “Dan Allah zan hau sama.” Ameera cikin mamaki tace “me zakiyi?” Jalila tana numfashi sama sama tace “Dan Allah ki rakani.” Ganin yanda ta damu yasa ta rike hannuunta suka hau sama. Suna zuwa kusa da dakin Goggo, Jalila ta zare hannunta daga cikin na Ameera sannan ta tura kofar d’akin. Goggo na kwance tana bacci, Jalila ta shiga. Ameera cikin mamaki itama ta shiga d’akin ta tsaya a jikin kofa. Jalila ta karasa kusa da gadon Goggo sannan ta riko hannunta. Wasu hawayene suka taho mata, Goggo ta bude idanunta jin an riketa, kallan mamaki tama Jalila tace “Jalila kece?” Jalila tace “in ba ni ba wacece Goggo na?” Goggo tai dariya tace “wato dana ce ki zauna a gida ki huta kasa zama kikai ko?” Tace “ina zan iya zama banganki ba?” Goggo ta kara riko hannunta da sauri ta mike zaune sannan tasa hannunta a goshinta tace “Jalila! Bakida hankali ne? Kina irin wannan zazzabin kika fito?” Jalila tai murmushin yake tace “karki damu Goggo ba wani wahala yake ban ba.” Goggo tace “ga wanda bai kalleki ba kenan, duk kin rame a dan kwana biyun da ban ganki ba?” Jalila tai kasa da kanta. Ameera ta kalla sannan ta kalli Jalila, tace “wannan fa?” Ameera ta matso ta gaisheta sannan tace ” ni kanwar yaya……” Da sauri Jalila tace “kawatace Goggo, biyoni tai dan ta gaisheki.” Mamaki ne ya kama Ameera wacece wannan da har batasan asan matsayin ta? Sai dai ba shakka suna tsananin kama, dan kamar ma harta baci. Jalila ta kalli Ameera, Goggo ta kara kallanta tace “Allah sarki na gode sosai.” Ameera tace “bakomai.” Kallan Jalila tai tace “bari inje gun Ya Sagir.” Ta juya ta fita, tana rufe kofar ta kara bin kofar da kallo, tabbas dabadan ance yar Mumy bace da tace wannan ce mahaifiyarta. Kwanciya Jalila tai a gefen Goggo dan tana jin jiki, Goggo ta shafi kanta tace ” ki koma can ki kwanta dda kyau mana.” Jalila ta girgiza kai tace “barni anan.” Goggo ta kalleta tace ” naji yarinyar nn tace Yaya Sagir? Ko Sagir din da ake bani labari?” Jalila tai shiru dan batasan me zata ce ba. Goggo tai murmushi, Jalila kam idanunfa ta rufe kawai, tana san sanar da mahaifiyarta sai dai tana tsoron kar jinjnta ya sake hawa, dan kuwa sanda aka kwantar da ita sai da akace a kiyaye sata a damuwa, wanda ta tabbatar in Goggo taji, ba magana kawai….. Acan gidansu kuwa Hassan ya shigo cikin gida, Ummy na zaune afalo tai shiru. Tsayawa yai yanasan mata magana kuma baisan ta inda zai fara ba. Ganin bata da niyyar kallansa yasa ya juya jiki a sanyaye zai hau sama, jiyai tace “yanzu Hassan abinda kai ka kyauta min?” Juyowa yai sannan ya matso kusa da ita, yace Ummy ni ban gane me na aikata ba. Tace “kafi kowa sanin yanda matsala da lalurar cikin dare ke faruwa, taya zaka bar yarinya ita kadai a daki, yanzu inda ciwon ya gama cinta cikin dare fa?” Yace “Ummy kinfi kowa sanin bana iya kwana da wani kusa dani…..” Tace ” Hassan kanaso kace bakasan dalilin dayasa muka nemarma aure ba? Ko kuwa san kanka ne ya maka yawa da baka duba halin da nake ciki?” Kallanta yai jiki a sanyaye, tace ” akoda yaushe hankalina baya kwanciya da barin ka kai kadai a daki, saboda ina tsoron abinda zai iya faruwa, sannan yanzu an maka aure nan ma kace kai kadai zaka dinga kwana? Fad’amin Hassan menene marabarka da kafin kai auran?” Kallanta yai sai dai baice komai ba. Tace “In har na isa dakai na kuma isa in fadama kaji to daga yau inganku a d’aki daya, ban damu da duk abinda zai biyo baya ba sai dai jiya ya zama rana ta karshe da zaku kwana tare, sannan ko kunya ka barsu suka tafi asibiti kai ka shigo.” Yace “Ummy kinsan bana san asibiti.” Kallansa tai kamar zatai magana sai ta fasa, dolene subi komai a sannu tunda gaggawa ma aikin shedan ne. **** Sagir ne ya kalli Ameera yace “ina kuma kuka je?” Nan ta fadamai abinda ya faru, cikin mamaki yace “yanzu tana can?” Tace “eh.” Sagir ya haura saman. Jalila na kwance kusa da Goggo suka bude kofar tare da sallama. Jalila na jinsa ya shigo, kallab Goggo yai sannan ya gaisheta. Ta amsa fuska a sake tace “Malam Sagir ashe da rabon zan ganka?” Dasauri Jalila ta d’ago ta mike tsaye tace “Goggo sai mun dawo.” Mamaki ne ya kama Sagir, ya mike yana cewa “ki zauna….” Tace “muje kawai.” Sai da suka kai kofa sannan ta ma Goggo salama suka fita, suna sauka ta kan beni mai kula da Goggo tana hawa. Gaisawa kawai sukai suka sauka. An mata gwaje gwaje sannan aka bata magunguna, akace su jira a gama test, Ameera tace “Ya Sagir ka maidamu gida, kai ka dawo ka amsa.” Shiga d’aki yai ya tsaya yai shiru, tunani yake mai yai? Shi dai a iya saninsa baiga laifin da yai ba. Bandaki ya shiga yai wanka, zama yai shiru, ga wunya da ta fara cinsa, yau Ummy mantawa dashi tai? Ko laifin daya mata ne yasa tai fishi dashi? Kwanciya yai ya d’au jornal din da yake karantawa. Jiyai yau karatun sam ba dadi, shi yace amai aure? Mikewa yai zaune sannan ya shafi fuskarsa, makullinsa ya d’auka da wayarsa ya fito, ba kowa a falon hakan yasa yai waje. Yana kokarin shiga mota, su kuma suna shigowa. Sai daya jira sukai parking sannan ya shiga mota ya tada ta. Sagir ya fito da sauri yanasan mai magana, kafin ya karaso Hassan yaja motarsa yai gaba. Sagir yabi motar da kallo, a ransa yace “anya nama Jalila adalci kuwa?” Ameera ce ta bi motar sa da kallo sannan ta kalli Jalila ta mika mata hannu, Jalila tai murmushin yake sannan ta fito. Ameera ta kamata suka shiga ciki. Ummi najin motsin mota ta fito, tana kallan sanda Hassan yai waje, ga Abba tun safe yau ya tafi Abuja. Suna isowa falon Ummy ta rike Jalila ta shigar da ita dakin Ameera tunda a kasa yake. Ummy ta kalli Ameera tace “Ameera dauko abinci.” Nan Ameera ta fita, Jalila ta fara kokarin mikewa tana cewa “Ina kwana?” Ummy tai saurin riketa tace “Karki damu, ma gaisa inkin ware.” Sagir na tsaye a jikin kofa yana murmushi, yasan halin Ummy ya tabbatar Jalila bazata taba wulakanta ba indai har Ummy na nan, kaf a duniya shi agunsa bai taba ganin mace kamar Ummy ba.+ Ameera ce ta shigo da tiren abincin, Ummy tace “zubo mata dankalin kadan” Ameera ta zuba mata ta mika ma Ummy, da kanta ta gyara mata zama sannan ta mika mata abinci, kallan mamaki Jalila take mata, bata taba tunanin zata samu kulawa haka ba, balle daga zuwanta ko sanin ta ba’ai ba. Haka ta dinga dan ci dan samon kanta tai da kasa yima Ummy musu, sai data gama Ummy ta miko mata magani da ruwa. Sai data sha, sannan Ummy tace karki kwanta kidan jira abincin ya tsirga miki kadan sai ki kwanta. Jalila ta d’aga kai, sannan ta maida idanta kasa. Ummy tai murmushi ta fita. Ameera ta mike ta biyota. Sagir na zaune a falon suka fito, yace “Ummy na!” Tace ” Sagir sannu da kokari.” Yai murmushi sannan yace “Ina Yaya yaje? Naga ya fita yanzu.” Yanayin fuskarta ne ya canza, tace “yaushe rabon da insan inda Hassan zaije?” Sagir yai shiru dan ya fahimci yayi laifin tambayarta, Ameera ya kalla yace “Ashe kawarki ta koma gida?” Ta dan turo baki tace “sai yanzu ma ka kula?” Yace “kinsan dazu muna kan Jalila sam ban kula ba.” Ya mike yai kitchen. Ameera ta kalli Ummy tace “Ummy nikam dazu a asibiti, na rasa wa taje dubawa.” Ummy tace wa kenan? Ameera tace “matar yaya.” Ummy tace “ya sunanta ita matar yayan?” Ameera ta kalleta tace “Ja…..” Kallan da Ummy ta mata ne yasa tai saurin cewa “Yaya Jalila.” Ummy tace “me ya faru?” Sagir ne yai saurin katseta yace “to uwar gulma, ki bari ita Ummyn ta tambayeta da kanta mana.” Ameera ta turo baki, Ummy tace “Sagir ya akai?” Hannunsa rike da plate din da ya zubo abinci ya zauna akan dinning yana cewa “Wlh nima bansan wacece a asibitin ba Ummy, sai dai yanda hankalinta ya tashi da alama mai mahimmancice a gareta…..” Ummy tace ” shikenan, zan tambayeta.” Sagir shiru yai ya kasa ko kai loma d’aya bakinsa, tunawa yai sanda suna zance da Jalila a makaranta yawanci in zatai abu zai ji tace ai Goggo kaza, ai Goggo kaza. Kallan Ummy yai da sauri yace “Ummy wannan matar data kawo Jalila itace “Mahaifiyarta?” Ummy tace “eh mana.” Sagir yai shiru can yace “me suke ce mata?” Ummy tai murmushi tace “ina fa na sani? Dan jarida?” A tare sukai dariya ^********^ Jalila tayi bacci sosai dan sai azahar ta tashi, Ameera na dakin tana sa kaya sanda Jalila ta farka. Kallan Agoggo tai sannann ta mike da kyar ta kalli Ameera tace “Dan Allah zanyi alwala.” Ameera tace “ki shiga ga toilet.” Jalila ta mike tai alwala, Tana idar da sallah Ameera tace mata ga abinci nan kici, Jalila tace “banajin yunwa. Bata sake mata magana ba, ta karasa kwalliyarta dan fita zatai ta fito daga d’akin. D’akin Ummy ta shiga tana zaune tana ta kiran number Abba, tun safe take ta ringing amma no answer. Ameera ta shigo tace “Ummy dawa zan kai sakon gidan Aunty Nanan?” Ummy tace ” dama abin gara ne, gashi ba driver a gidan, ki duba ko Sagir nanan.” Har ta juya Ummy tace ” yayar taki ta tashi ne?” Tace “eh tayi sallah ma.” Ummy ta mike ta fito tare da ajiye wayar. Sama ta hau dan taji alamar dawowar Hassan dazu, dakin ta kwankwasa. Yana kan sallaya rike da littafin Riyadul Salihin, ajiyewa yai ya bude kofar. Kallansa tai tace “Hassan ya jikin matar taka?” Kallanta yai yace “Ummy ni ai banganta ba?” Tace ” baka ganta ba? Tana ina kenan?” Yace “ina na sani ni ai tun da suka fita ban kara ganinta ba.”4 Tace “ko?” Baice komai ba sai kallan mamaki da yake mata, Ummy me take mai haka? A iya saninsa batasan abinda zai bata mai rai, sannan ko magana zatamai a cikin sanyi take mai. Kallanta yai yace “Ummy na kasa gane me ke faruwa, kince na amince da auran nan na amince ba tare da na musa ba, yanzu kuma gaba daya kin canza.” Kallansa tai, yanayin fuskarta ya canza, abinda bataso dan ta kula in tama Hassan lago lago tabbas yarinyar nan zata kuntata a gunsa. Tace “Hassan ko kare ne aka baka shi akace ma gashi an baka shi, baka tunanin ya zama hakkinka ka kula dashi? In har kasa hannu ka amsa a iya tunani na dolene ka bashi hakkinsa, Hassan dabba ma kenan, balle dan adam, dan adam din ma mace mai rauni, yarinya karama.” Kallanta yai baice komai ba, tace ” yanzu da ace gidanku daban kenan haka zaka barta har ciwo ya mata illa?” Hassan ya kalleta yace “ba gaku nan ba,Ummy? Na tabbatar abinda zaku mata ni bazan mata ba.” Tace “Hassan zuciyarka ma ta fara rikidewa?” Kallanta yai sannan ya kauda kai gefe, tace ” a iya sanina yarona mutum ne mai tausayi da kula da abinda yake nasa da wanda ba nashi ba, Hassan yaushe zuciyarka ta fara rikidewa zuwa rashin tausayi?” Shiru yai jikinsa yai sanyi bai ce komai ba, tace ” na haramta mata kwana a d’akinta, daga ranar jiya Hassan ko me zai faru in ganta a d’akin nan. Yace “Ummy….” Tace “zan kulle d’akinta ne ma in tafi da makullin, zan sa Ameera ta dawo da kayan sawarta nan dakin.” Ran Hassan ya baci sai dai bai iya cewa komai ba, yana ji ta juya ta sauka, da kallo ya bitaa sannan yai ajiyar zuciya, dama ba auran ba, azomai da wasu sababbin al’amura shi ya tsana, sanda sukesan yai auran ba acemai komai ba, sai yanzu da yai auran ake san a canza mai rayuwarsa, me yasa basa duba yanayin lalurarsa tana bukatar sirri da kadaicewa? Ameera bata samu Sagir ba, tazo ta sanar ma Ummy, ba tare da damuwa ba Ummy tace “a kai gobe, yanzu muje sama.” Tace “Sama kuma?” Haka suka shiga d’akin Jalila tasa a kwaso kayanta, tayi mamaki sosai dataga duk an d’auke kayan lefen da suka sa mata masu tsadar ciki, sai dai bata nuna ma Ameera wani abu ba, Hassan na jin alamunsu yasan me suke shirinyi. Fitowa yai ya sauko kasa ransa a bace zai fita. Jalila ta fito dan neman yarinyar da batasan sunanta ba, tanaso tace mata ta nuna mata inda kayanta suke tanaso ta dauko abu (wanka take sanyi ga batasan inda inners dinta suke ba.) Tana fitowa ta nufo falo tana tunanin inda zata ganta, tangamemen falon ta shiga kallo, dan dazu da yake kunya take sannan ba lafiya ce da ita ba ko kai bata daga ba, haka gidan yake? Kallan gidan ta shiga yi shi kuma ya sauko daga sama, san bata kuka dashi ba, shi kuma ransa a bace yake yana san fita. Tana tafe shi kuma ya taho da karfinsa ya bigeta, tsoron faduwa yasa ta riko rigarsa suka fadi a tare. Zafin faduwar ne yasa tai dan kara kadan, dagowa yai ya kalleta, itama kallansa tai. Idanunta ne suka fito dan ta ganeshi shine na jiya, wato shine angon nata kenan, kura mata ido yai sosai wanda yasa ta tsarguwa. A ina ya santa? Kallanta ya sakeyi, sannan ya mike tsaye. Haushi ya kamata duk da batajin dadi ai yaci ace ya mata sannu dan ta tabbatar yasan ta bige sosai. Hararsa tai wanda shi kuma daidai lokacin ya juyo da fuskarsa, hada ido sukai tana harararsa da sauri ta wayance tace “yaji ne ya shigarmin ido?” Wai ita adole bata ma kula dashi ba, magana take da kanta. Hassan kallanta yai sannan ya tuno harararnan an masa ita sau biyu, har ya juya sai kuma ya kara juyowa yai ya kalleta dan ya fahimceta sosai, itace takan hanyarnan da wacce ta harareshi a adaidaita. Oh, a ransa yace mai kuka? Jalila ma shiru tai tana tunanin faduwarnan, bashakka ta tuno, da sauri ta d’ago ta kalleshi. Mikewa tai tsaye, tana kokarin mai magana shikuma yai waje. Da sauri tace ” ba kai bane?” Bai tsaya ba balle tasa ran tanka mata, kara kankance ido tai tana tunani, tabbas shine, wanda ya fadi akan titin nan. Zata kara magana taga harya fita, da kallo ta bishi sannan ta dan tabe baki tace “ba dai sanda ya kusa kadeni ya sanni ba?” Ganin batada amsar tambayarta yasa ta juya tana neman Ameera tare da rike bayanta, dan ta bugu sosai. Ummy tasa aka matsar da kayansa bangare guda, sannan aka jerama Jalila nata, hatta kan madubi sai da aka matsar da kayansa akasa nata. Ameera ta kalleta tace “Ummy kina tunanin Yaya zai barta kuwa?” Ummy tai shiru, meye amfanin yi masa auran in basa tare? Haka suka gama sannan suka sauko. Jalila kam ganin ba alamar kowa yasa ta koma dakin ta zauna. ********** A can gidansu Mumy kuwa, Dady na kwance yayi shiru, Mumy ta shigo dakin, kusa dashi ta zauna ta sakalo hannu ta gefen cikinsa ta rungumeshi tace “Dadyn Yasmeen tunanin me kake?” Fuskarta ya shafa yace ” Tunanin ki?” Tace “ban yarda ba, tunanin Jalila kake?” Yace “A’a why should i?” Tace “karka boyemin komai plx, sannan kaima kaga gidan Taura ai, kasan daidai mata ne zasu samu zama a irin wannan gidan.” Yai murmushi, tace “yaushe za’a fadawa Goggonta?” Yace “karki damu, ko ta sani yanzu ba abinda zata iyayi, macece mai hakuri, indai taga yarta cikin farinciki bazata iya cewa komai ba.” Mumy ta jinjina kai, yace “ya gun Safeena?” Tace “suna Abujan, wai sai gobe zasuje ayi visa din.” Yace “okay.” Tana zama bata dade ba taji anyi knocking din kofar sannan taji ance “Ameera!” Gabanta ne ya fadi jin muryar Uncle, wai nan fa gidansu ne ko? Sunanta Ameera dama? A hankali tace “batanan.” Shiru yai shima kafin yace “Jalila dan bude.” Mikewa tai ta bude kofar ba tare da ta bari idanunsu sun hadu ba. Sagir ya miko mata ledar dake hannunsa, kallansa tai bata amsa ba sannan batace komai ba. Kallanta shima yake sannan yace ” test din ya fito, shine sukaban magunguna, dama kinada typoid ne?” + Bata amsa mai ba ta amshi ledar ta bude, bayan magani taga yoghurt da exotic a kasa, zare ledar maganin tai sannan ta mikamai ledar kasan wanda ke dauke da yoghurt din. Kallanta ya sake yi sannan yace “kinsan wasu basa san shan magani da ruwa shiyasa…..” Kallansa tai kamar zatai magana sai ta fasa, tace ” Ameeran bansan inda tai ba.” Juyawa tai tana neman rufe kofar, hannu yasa da sauri ya rike kofar, juyowa tai ta kalleshi idanunta sun canza suna neman yin kuka. Yace “Jalila wacece dazu a asibiti?” Tace ” me kake so ka sani?” Yace “Kina nufin haka zamu zauna ko magana bakyasan ta hadamu?” Kallansa tai zuciyarta na kuna, sannan ta juya da sauri ta banko kofar. Hannu tasa ta rufe fuskarta saboda bakin ciki, wasu hawaye ne suka gangaro mata, ba santa yake ba, ta tabbatar yanzu kila kawai tausayin halin da ya ganta yakeyi. Sagir tsayawa yai ajikin kofar tare da kurama kofar ido kamar tana gun, sannan ya juya jiki a sanyaye. Yana neman fita yaji Ameera nacewa “Ya Sagir!” Juyowa yai ya kalleta, yana tsaye harta karasa gangarowa daga saman benan, ta matso gunsa tace “ina zaka?” Leda ya mika mata yace “Gashi kiba matar Yaya.” Amsa tai tana cewa “menene ya Sagir? Sam ka canza gaba daya yanzu bakasan magana sosai.” Murmushi yai na dole yace “Ummy fa?” Ta nuna sama da hannu tace “tana sama” sannan ta matso kusa dashi sosai alamar rada tace “Ummy fa ta dage sai yaya ya amince da matarsa.” Sagir ya kalleta yace “bangane ba….” Tace “tana sama tana hada musu daki daya.” Wani abu ne yaji ya harba kirjinsa me kake tunani Sagir? Abinda wata zuciyar ta tambayeshi kenan?. kallanta yai yace “haba.” Dakyar yai maganar, tace “Ai Ummy ta dage wannan karan.” Harararta har sannan ya ture kanta yace “yaushe kika zama mara kunya? Wato harkin fassara zamansu a daki daya kena?” Tace ” ko yaro dan shekara sha biyar ai yasan me ake nufi a wannan lokacin.” Buge kafadarta yazoyi ta zille da sauri yace “Ameera? Kece kuwa?” Dariya tasa tace “ni ba ruwana Ya Sagir.” Da kallo ya bita yana murmushi harta shige daki, tana shiga yanayin fuskarsa ya canza, daki daya? Wata zuciyarce ta kara cewa me kake tunani ne wai? Daga lokacin da aka daura aure ai kaima kasan abinda ya kamata. Juyawa yai jiki a sanyaye ya fita. Tana zaune tana kuka Ameera ta turo kofar, da sauri ta goge hawayenta, Ameera ta kalleta tace “jikin ne?” Kai ta daga alamar a’a sannan tace “Sunanki Ameera ko?” Tace eh, Jalila tace “ni sunana Jalila.” Ameera tace “na sani.” Jalila tai murmushi tace “Oh, yahkuri.” Ameera ta kalleta tace “Ummy ce ta fadamin, sannan na gani a katin daurin aure.” Jalila ta jinjina kai, Ameera ta mika mata ledar tace “gashi inji Ya Sagir, ah bakisanshi ba ko?” Jalila ta kalleta batace komai ba, Ameera tace “shine kanin Yaya, daga shi sai ni, mu uku ne.” Jalila tace “Yaya?” Ameera tace “Ya Hassan fa nake nufi mijinki.” Jalila batasan sanda tai wata dariya ba wace ni kaina bansan irinta ba, miji? Mijin da sai yanzu ma tasan sunansa? Kallanta tai a ranta tace Husainin fa? Tace Hassan sannan tace Sagir. Kamar Ameera tasan me take tunani tace “ya rasu, dan uwan nasa.” Jalila ta kalleta tace “Ayya Allah ya jikansa.” Ameera ta ajiye ledar tana cewa Ameen. Jalila ta dau maganin tasha. Jalila can tace “wanka nakesan yi kayana fa dan Allah?” Ameera tace “muje sama.” Jalila ta mike ba tare da ta musa ba, Ummy na saukowa suna fitowa, Ummy ta kallesu murmushi tai sannan tace “Jalila kin mike?” Kai ta daga tare da sunkuyawa, tsugunawa sukaga tayi tace “Ina wuni.” Ummy tasa hannu ta dagata sannan tace “ke da bakida lafiya?” Jalila kanta na kasa, Ummy tai murmushi sannan ta kamo hannunta, maimakon su hau sama sai ta riketa zuwa falo. Ameera ta kalla tace “Ameera asa mana abincin dare.” Ameera tace “Ummy yau ma nice?” Ummy tace “ai na fada miki dama, daga kin shiga aji shida shikenan girki ya kamaki, yanzu kuwa kunyi hutun canjin aji kinga kuwa a matsayin yar aji 6 kike.” Ameera ta shagwabe fuska ta nufi kitchen ranta ba dadi, ita kam tana ganin ya kamata a samarmusu mai aikin yin abinci amma taki, mai musu aiki ma suna gama gyara gidan suke tafiya sai kuma gobe. Ummy ta maido da hankalinta kan Jalila ta zauna sannan ta zaunar fa ita a gefen ta. Jalila ta zauna a darare, Ummy ta riko hannunta tace “Jalila!” Jalila ta kalleta kadan sannan ta maida kanta kasa tana kallan yanda Ummy take rike da hannunta, Ummy tace ” ya jikin naki?” Jalila tace Da sauki. Ummy tai shiru kafin tace “da rokonki nake san yi.” Jalila ta kalleta da sauri tana san jin menene, sai dai bazata iya dadewa tana kallanta ba, da sauri ta maida idanunta kasa. Ummy tace “rokonki zanyi akan ki saki jikinki da mu, ki maida gidan nan kamar gidan ku koma sama da gidanku, nasan zama da iyayen miji ba abune dayake da dadi ba, abu ne mai wahala tun balle ga yarinya, sai dai mu lalurace tasa muke sanki anan gidan, sannan bawai dan mu cutar dake bane sai dan muna ganin in kina kusa damu hankalinki da namu sai yafi kwanciya.” Lalura? Abinda yazo mata a ranta kenan sai dai batace komai ba har Ummy tace “Jalila mun miki laifi wanda nikaina nasan bamu kyauta miki ba.” Jalila ta kalleta tace “Laifin me?” Ummy ta saki hannunta sannan jiki a sanyaye tace “mun miki laifi gun b’oyemiki larurar Hassan.” Kallanta tai sannan ta tuno sanda ya fadi akan titin nan, aljanu? Hauka? Abinda ya fado mata arai kenan, Ummy tace “Hassan nada larura wanda mu kanmu iyayensa bamu sani ba, haka kawai tundaga mutuwar dan uwansa da dan kanin mijina Hassan ya koma haka, duk yanda mukaso musan matsalarsa mun kasa, munje asibitoci kala kala sai dai maganar daya ce, ba abinda ke damun kwakwalwarsa sai dai bamu san meke damunsa ba.” Ummy ta juyo tare da goge kwallarta tace “Jalila ki yafe mana wannan laifin da muka aikata.” Ganin Matar da ta sani a rana d’aya tana share kwalla sai taji gaba daya hankalinta ya tashi, batasan sanda tace “Bakomai na yafe muku.” Ummy ta kalleta cikin jin dade sannan ta kara riko hannunta tace ” jikina yana bani ke alhere ce a gareshi da mu kanmu, daga sanda naganki hankalina ya kwanta dake, Jalila ki daukeni a matsayin mahaifiyarki, ni kuma zan yi miki duk wani abu da uwa takema danta.” Jalila tai murmushin jin dadi, dan haka kawai taji tanasan matar, dazu kukanta kadai yasa hankalinta tashi. Ummy ta kalleta tace “wa aka kwantar a asibiti?” Jalila ta kalleta idanunta suka ciciko, a hankali hawaye ya fara zubo mata. Ummy hankalinta ya tashi tace “ya isa haka nan Jalila, bazan kara tambayarki ba harsai sanda hankalinki ya kwanta da ki sanarmin.” Jalila share hawaye kawai take, Ummy ta mike tace “tashi kije dakin nasan abu zakiyi na tsayar dake.” Jalila ta dago sannan ta mike, sama ta fara hawa, Ummy taji tace “dakin kusa da wanda aka kaiki jiya zaki shiga. Jalila tace to, nan ta tura kofar dakin, sanyin Ac dake kadawa a dakin da wani sansanyan turare ne suka bugeta, idanu ta lumshe a hankali sannan ta kalli dakin, yanayin kan madubin kadai yasa tasan dakin hade yake da namiji. Da sauri ta fito ta nufi dakin data shiga jiya, jin dakin tai a kulle, komawa tai dakin ta bude wardrobe gefe daya kayanta ne kaf, dayan kuma na namiji. Daki daya zasu zauna kenan? Inners dinta ta ciro sannan ta shiga wanka, kamar ba dakin namiji ba dan komai nashi a tsars suke, haka ta fito ta saka wata doguwar riga sannan ta kwanta agefen gadon, tana tunanin rayuwa, tabbas itakam zata fadama Ummy matsalar Goggo dan bazata iya kwana biyu ba bata ganta ba. Ta tabbatar Ummy zata fahimceta. Batasan bacci yayi gaba da ita ba, dan dama in tana zazzabi ta dinga bacci kenan, tsabar bacci ya mata dadi har da kara kwanciya, sanyin Ac din yasa ta jawo bargo. Bacci take hankalinta a kwance. Kofar dakin ya turo, gaba daya shi gidan ma baya san zama, tunda ya fita yana cikin mota a zaune. Sai yanzu daya gangaro gida, ganin magrib tayi, ya tabbatar Ummy yanzu zata shiga nemansa. Cak ya tsaya a kofar dakin yana kallan ikon Allah, tunda yake yau ne rana ta farko da wani ya taba bajemai akan gado haka, harda jan bargo? Ransa ne ya turnuko dan shi sam bayasan yaga wani a dakinsa, kusa da ita ya matso ya sa hannu ya fizgi bargon da karfi. Jan bargon da yai yasa ya hado da kasan doguwar rigarta yadan kwaye ta. Da sauri ta bude idanu, kallansa tai a zabure, shima idanunsa ne suka kai kasanta daya kwaye, da sauri ya dauke kansa, ita kuma ta mike zaune da sauri tana gyara rigarta tace “Malam me kenan?” Kallanta yai yace “Malam? Malam me kenan?” Bakinta na rawa tace ” Umm.” Ya hade rai yace “will you get up?” Kallansa tai cikin rashin fahimta, yace ” bakyajin yaren?” Nan ma tai shiru, yace “banasan magana please tashimin daga kan gado.” Jalila ta kalleshi tace ” dan zaka ce in tashi sai ka min haka?” Wani kallo ya buga mata wanda batasan sanda ta mike ba, yace “a haka kika gadon?” A ranta tace “ahh yau ga wani irin mutum.”1 Kallanta yai sannan ya kalli gadan, Jalila ta fara gyara gadan da karfi kana gani kasan na mugunta takeyi, tana yi tana dan murguda baki. Kallanta yai a ransa yace wannan kana gani kasan batada kunya wannan bakin sai ba fasashi wata rana. Jalila kuwa tana gyara wa tana cewa yo matsala ma ai basai an tambaya ba, mutum ba mutunci ai babbar matsalace. Toilet ya shiga ya d’auro alwala, yana fitowa ya kalleta, tana tsaye tsuru dan itama jiransa take ya fito, ga fitsari ya matseta. Tana gani ya fito ta shiga ciki, kallan kofar data rufo yai ransa ya kara baci dan bakin cikinsa ya ganta a dakin nan. Tada sallah yai, bayan ya idar ya zauna ya fara addu’oinsa, itakam daga gefe ta dan rakube tai sallah, tana idarsa ta zauna agun tana yima Goggonta addu’a. Ameera ce ta buga musu kofa tana cewa “Yaya Jalila ki fito kici abinci” Juyowa yai ya kalleta ransa a bace, mikewa tai da sauri zata bude kofar. Batasan ya mike ba sai gani tai ya rigata sa hannu ajikin kofar. Kallansa tai yanda taga idanunsa sunyi yasa taji tsoro. Da karfi ya bude kofar sannan ya kalli Ameera. A tsorace Ameera tace “Yaya kana nan?” Kallanta ya sakeyi,ba sai ya mata magana ba tasan me yake nufi. Da sauri tace “Yahkuri yaya bansan kana nan ba.”+ Jalila ya kalla, itama kallansa tai sannan ta kalli Ameera, bata fahimceshi ba sai cewa tai “me zanyi?” Hannu yasa ya turata waje sannan ya rufe kofarsa, Ameera ta kalla sannan ta kalli kofar tace “menai?” Ameera tasa hannu ta jawota tana mata alamar tai shiru. Suna sauka kan steps din tace “bayasan magana da hayaniya.” Jalila ta kalleta batace komai ba, haka suka sauka kasa.1 Ummy nakan dinning tana rike da waya, kara neman number Abba takeyi amma shiru sai taita ringing harta katse ba’a dauka ba. Sagir ne ya ajiye kular daya dauko daga kitchen yana cewa “Ummy haryanzu Abban bai dauka ba?” Ta kalleshi tace “haryanzu, baka tunanin ko wani abun ya faru?” Zama yai a kusa da ita yace “bakomai insha Allahu, maybe ko aikin dayaje yi ne ya rikeshi.” Su Ameera ne suka sauko, Ummy ta kalli Jalila tace “Jalila ban yarda da kici abinci ke kadai ba dan ba lalai kice dayawa ba.” Jalila tai murmushi sannan ta zauna kusa da inda Ameera ta zauna. Bata kula da Sagir ne a saitinta ba, sai da Ummy ta mika mata serving spoon. Jalila ta amsa sannan ta kalli Sagir, idanunsu ne suka hadu da sauri ta maida kanta kasa, tana kallan plate din, ta ina zata ci abinci a nan?” Ta dan zuba abincin kadan, Ummy ta kalleta tace “Jalila wannan dan abincin fa?” Jalila ta kalleta tace “Ummy wlh haka cin abinci na yake.” Ameera tai dariya tace “irin cin abincin Yaya kenan, hmm kunyi anko.” Idanunta ta dago kadan ta kalli Sagir wanda yake ta juya abincin. Shiru ne ya biyo bayan falon sai dan karar cokula da suke tashi, Ummy ta rasa me yasa gabanta ke ta faduwa. Mikewa tai dan abincin da kyar take danci, ta kalli Ameera tace “ki dauko mata magungunanta tasha.” Ta karasa maganar tana wucewa d’aki. Ameera ta mike tai daki, ya rage daga shi sai ita agun, Sagir ya kalleta yace “Ya jikin naki?” Bata kalleshi ba tace “na warke.” Shiru suka karayi yace “Jalilah…..” Ajiye cokalin tai da sauri sannan ta mike, dan batasan jin kalma daya daga gareshi, ina zata? Nufar dakin Ameera kawai tai, Ameera na fitowa ta kalleta tace “ina zaki?” Tace ” hmm bandaki zan shiga.” Ameera ta mika mata maganin, amsa tai ta shiga ciki. Tunda ta mike yake kallanta harta shiga, idanunsa ya rufe yana neman tsari daga sharrin zuciya, shikam ya san ya hakura sai dai yana san ya warware misunderstanding dake tsakaninsu. ********* Acan Abuja kuwa Abba ne ya kalli abokin nasa yace “wai kai da mukazo yin signing contract me ya kawomu nan?” Ya fada yana kallan wani gidan da abokin nasa yai parking. Abokin nasa mai suna Hafiz ya kalleshi yace ” abu zan amsa gun wani, yanzun nan zan fito. Fitowa yai daga motar yabar Taura a ciki, tsaki taura yai shi ya kosa su gama ya koma masaukinsa dan ya manta da wayarsa garin sauri. Sam bai kula ba sai jiyai ana kwankwasa glass din motarsa. Zuge glass din yai tare da kallan windown, wani irin kamshi ne ya shiga ratsa cikin motar, kallanta yai yarinyace wacce batafi shekara 28 ba, fara ce wanda har farin nata ma yasa zakasan ba cikakiyar bahaushiya bace, kana ganinta zaka san irin matan nan ne shuwa. Tasha kwalliya irin na zamani, kamshin da takeyi kuwa ba’a magana. Ya rasa dalilin dayasa ya kasa dauke idanunsa daga kanta. Murmushi tamai sannan tace “Yaya yace ka shigo kaci abinci.” Yace “Yaya?” Tace “Eh ai mijin yayatane.” Yace “oh gidanshi ne kenan?” Tace “eh.” Gani yai tasa hannu ta bude lock din cikin motar sannan ta bude kofar. Kallanta yai, kayan da ke jikinta irin material ne mai kyalkyali, mace ce mai suna mace dan shape din ta ma abin kallo ne. Kai ya girgiza da sauri dan shikam mace baiga kyan da zaisa ta rinjaye shi ba. Kauda kansa yai daga kanta, matsowa tai saitin kunnensa tace “Please.” Baisan sanda ya mike ba yace “muje.” Gaba tai tana wani murmushi, dan dama wannan shirin sunfi wata biyar sunayinshi, tundaga sanda taganshi a Abuja yazo shida matarsa wani taro, kayan jikin matar kadai ta kalla tasan kudi ya zauna musu, data tambayi mijin yayarta shine ta karajin irin kudin da yake dashi. Tun daga lokacin suka fara shirin jawoshi inda suke. Haryasa kafa zai shiga sai ya tsaya, juyowa yai ya kalleta yace “kicemai yai hakuri inada abinyi.” Ya fada tare da juyowa tana mai magana bai tanka mata ba. Motarsa ya shiga ya jata da sauri. Ita kuwa Zaliha tana shiga cikin gida ta hade fuska, yayarta ta kalleta tace “ya ya?” Kai ta girgiza mata kawai sannan ta wuce daki cikin takaici. Yayarta ce ta kalli mijinta tace “Hafiz ya haka?” Yace ” Taura namiji ne da bai kallan matan waje kuna tunanin daga haduwa daya zai amince?” Harararsa tai sannan tai gun kanwarta. *********** Abba na koma wa dakinsa ya dau wayarsa, kiran Ummy ya sau goma, sannan yaga kiran Sagir sau biya, sai sauran wanda abune na aikinsa. Yana shirin kiran Ummy wayar Hafiz ta shigo, dagawa yai cikin takaici yace “Hafiz bakada hankali ne?” Hafiz yace “kayi hakuri dan Allah wlh dana shigo ciki ne matata ta dage akan sai na kiraka kaci abinci shiyasa nace Zaliha ta kiraka.” Yace “meyasa to baka fadamin gidanka bane?” Yace “banasan ne kaji ba dadi, haba Taura dan Allah kayi hakuri.” Kashe wayar yai sannan yai cilli da ita kan gado, ya rasa me yasa yarinyar ta tsayamai a ransa…… *********** A can gidansu Hassan Kuwa jalila tana zaune a dakinsu Ameera, har wajen karfe 10, Ameera ta kalleta tace “ki tashi kije ki kwanta kafin Ummy tai magana.” Jalila tai ajiyar zuciya sannan tace “bazan iya kwana anan ba ko?” Ameera da sauri tace “a ina? Ba ruwana wlh.” Jalila ta kara yin ajiyar zuciya sannan ta mike, ta fito. Haka ta haura sama jiki a sanyaye, hannu tasa a hankali ta murda kofar dakin, yana kwance akan gado yana karatu. Kamar munafuka haka ta shiga cikin dakin, ko kallanta baiyi ba ya cigaba da karatunsa. Jalila tana tsaye har kusan minti ashirin, jitai kafafunta sun gaji nan ta matso kusa da gadon kadan, ta karasa kan kujerar dake dakin ta zauna tana dan matsar da littatafan dake jere agun. Jitai ance “karki kuskura ki hargitsamin abu, komai da kika gani agun a jere yake.” Baki tadan tabe sannan ta daina taba litattafan, dama haushi yakeji dalilinta duk an canzamai tsarin dakinsa. Shiru ne ya kara ratsa dakin sai sanyin Ac dake kara sanyaya dakin. Bacci ne ya fara kamata dan har 11 ta wuce, tana zaune tana tunanin Goggonta. Ganin bashida niyyar fadamata inda zata kwanta yasa ta mike ta dau pillow din dake gefensa sannan tazo tana san daukan bargon dake kan gadon. Kafafunsa ne akai ta kalleshi tace “zan dan dauka.”1 Kallanta yai yace “banaji naki ne.” Tace “a ina zan kwanta?” Alama ya mata da kasa da hannunsa ba tare da ya dauke kafarsa ba. Jalila haushi ya kamata, harararsa tai cikin takaici, sannan ta sa pillow ta kwanta a kasa, ai bayau ta saba kwanan kasa ba, dama saboda sanyi takesan luluba. Shikuwa bai kalleta ba sai dai ya tabbatar ta harareshi dan ya kula idanunta sun kware da harara sannan bakinta ya kware da murguda a bayan fage. Kwanciya tai ta lulube kafarta da zani, bacci ne yai gaba da ita……. Kallanta yai sannan shima ya juya ya kwanta, abinda zai baka haushi bafa luluba zaiyi da bargon ba haka kawai……… Wajen asuba ya farka, yai hamdaka da samun bacci mai kyau dayai, dan dama ba kullum abin tashi ba. Dome light din dakin ya kunna sannan ya mike. Alwala yai sannan ya dauko sallaya zai shimfida, kallan Jalila yai tana kwance a inda yake shimfida sallayarsa, bacci take sosai kafa yasa ya zunguri kafarta. Kara gyara kwanciya tai, ya kara sa kafa ya dan kara zungurar kafar tata, a hankali ta bude idanunta. Ganin namiji tai a kanta da doguwar riga fara, tsorata tai, da sauri tai baya tare da yin ihu, tace wayyo Allah…… Da sauri ya rufota ya rufe mata baki, yace meye hakan? Sai alokacin ta tuna ashe fa wai a wani gidan take, sannan daki daya da namiji. Shiru tai sannan ta kalleshi, shima kallanta yai sannan ya mike yace ” bakiji kiran sallah ba?” Tai shiru, dan batasan me zatace ba. Mikewa tai ta nufi ban toilet. ******** Inna ce ta kalli Dady tace “bazaka iya ba?” Yace “ba wai bazan iya bane sai dai banga dalilin dazaisa a dauketa daga asibitin da take ba zuwa wani ba.” Ranta a bace tace “kayi abinda na saka kawai, ko kana tunanin zan cuceta ne?” Kallanta yai yace “ba haka nake nufi ba.” Tace ” kamaida ita Premier m, sannan kasa a gyara mata bangarenta, asa mata duk wani abu da ya kamata.” Mamaki ya kamashi, a canza mata asibiti sannan a gyara mata bangarenta? Ya tabbatar wani abun take shiryawa na cigabanta ko na cigaban yarta. Bai musa ba yace to sannan ya mike ya fita.18 Shiru tai tana tunani……..