MRS AMIDUD CHAPTER 2

MRS AMIDUD CHAPTER 2

“Fito kinji babu abinda zai miki.” “Humm kawai ki kore hi zan fito.” Dafe goshinta Hajiya Adawiyah tayi sannan tace. “Yi hakuri fito,na Kore shi.” Dakyar tafito daga bayan kujera, tana zare idanunta. Zauna da ita tayi akan kujera, aikuwa ta buga tsalle sai da Yaran gidan suka fashe da dariya. “Buhayyah kalli abin dariya.” Wacce aka kira da buhayyah, murmushi tayi sannan ta mika mata hannu, tace. “Parih! Har kin manta damu ne! Aarib! Wannan arusa kin tunashi kika ce haka kuke kiran katu a Dabji, sai Ni kika ce idan da a Dabji nake me kyau za a kirani, sai Amrozia. Kin tunamu” Rau-rau tayi da idanu sannan cikin kankanuwar Murya tace. “Zaki mai dani gurin Kakata wallahi daga zuwana naga Bala’in da suka fi karfina,” Dariya suka yi sannan ce. “Toh ai kin dawo kenan bazaki kuma zuwa dabji ba.” Kura musu ido tayi kafin tayi wani irin yatsuna fuska, sannan ta ware murya ta fasa musu kuka, tanayi tana bubuga kafa a kasa, duk suka rud’e aka rasa wanda zai iya dakatar da ita, ihu take tare da buge buge, tana ture komai na gurin.+ “Wayyo Allah! Da nasan haka zaki koma da banyi kasassabar dauko ki ba, kiyi shiru” Dakyar suka rarrasheta Hajiya Adawiyah ta shiga da ita ciki. Suna shiga daki ta bud’e baki tana kallon duniyar dake cikin d’akin, kallon katon madubin jikin wardrob tayi, tare da yiwa kanta gwalo, sannan ta fashe da dariya, tace. “Wallahi naganni babban a wannan madubin, wannan ba Irin na Iyah bane nata iya fuska kake gani, wayyo dube Ni, na zama katuwa” “Jan muje kiyi wanka.” Nuna mata ban daki tayi, sim-sim ta wucce, har cikin ban dakin. Tana taka dan capter din da ake sakawa a bakin kofa ta fasa ihu, ta juya da mugun gudu ta koma bayan Hajiya Adawiyah, jikinta na rawa, sai da ta rike ta har cikin ban dakin, taga ruwa a cikin abin wanka, ga karafunan panpo. Shiga suka yi Hajiya Adawiyah ta nuna mata ruwan wanka, da yadda zata yi tace mata. ” Bari na kawo miki brush da closeup” Shiru tayi sannan tace. “To kuma meye borus da kilozef,” Juyawa tayi ta kalli yadda karafunan suke, kai hannunta tayi ta dabo wani panpo wanda aka saka alamar jan paint, na ruwan zafi, aikuwa tana tsaye a kasar panpon ruwan me zafi ya shiga saukowa akanta, da ta buga waya suwa ta fita da mugun gudu tana wancakalar da hijabin ɗinta da dan kwalinta. Tana ihu tare da birgima, Ga baki dsya mutanen gidan suka taru akanta sai cewa take. “Wayyo Allah na, yau naga buni. Wato tsige Ni za ayi ta tsakar ka. Alkur’ani bani kuma shigewa wancan dakin.” Tsaki wani matashin Saurayi yayi sannan yace. “Dad! Yaushe ka dauko wannan bararojin, dub’eta fa, tazo tana ihu kamar wacce aka tsige namar jikinta.” “Jalal! Ina wasa da kai ne, ina ruwanka da ita, fita ka bamu guri.” Kukan da take yi ne ya kare tabi Jalal ɗin da ido, ta kalli irin gashin da ya bari, irin azonto din nan. “Wannan gahin sa, kamar hikar angulu” D’agowa duk suka yi tare da kallon gashin aikuwa suka kwashe da mugun dariya, har Dad din su, sai dariya suke mishi, kamar zai saka kuka ya juya tare da zabga mata harara. Sannan yasa kai yafita yana fadin idiot, kallon su tayi sannan tace. “Toh kuma meye uduwat” Fita Dad yayi daga dakin yana darawa. Riko hannunta Hajiya Adawiyah tayi suka shiga ban daki, da kanta tacire mata kaya, tana kallon halittar da Allah yayi, ga kyau ga diri, dan ba karya Fulanin Dabji kyakyawa ne, bafa muna kyawawan ba, idan kaga baki a cikin dabji bakone, Jan Parih ba fara ce kuma ba za a kirata baka ba, dan zamu iya kiranta da kalar fatar Mawakiyar nan ta U.s rihanna sannan Allah yayi mata baiwar gashi, Kuma baki sid’iki, Daga yanayinta kawai zaka tabbatar da zatayi tsayi, sannan bata da yawan jiki sirirya ce, fuskar ta shima dan Karami me zagaye da siririn hancin da karamin bakinta, kawai ka nazarci yadda pari take. Kin cire rigar tayi, Hajiya Adawiyah tayi dariya sannan tace.. “Wanke miki kai zanyi na kuma miki wanka.” Kamar zata yi kuka tace. “Ai Iyah ta dade da daina min wanka.” Zaro ido Hajiya Adawiyah tayi cikin mamaki tace. “Sabida me?!” Tura baki tayi can cikin bakinta tace. “Sabida na balaga mana” Zaro idanu ta kuma a karo na biyu tace.. “Kin balaga?! A ina kenan?!” Watsar da hannu tayi sannan tace. “To ai nima yanzun yan mata ce kinga an daina min wanka.” Da Hajiya ta gaji da surutu kamata tayi ta cire mata kaya har da kwalin kanta, ta zauna ta wanke kanta fess anayi tana jifar Hajiya Adawiyah da tambaya. “Hajiya kince ban balaga ba, meye ya rage? Kuma idan na balaga ya zan zama babba kenan? Gaskiya gwara na balaga dan bana son ana min wankan,” Kallon Bakin Parih tayi kamar ta buge, amma sai tana ganin Absham da Amatul Islam. Tana mika mata towel ta jefo mata tambaya. “Hajiya! Ni kam wannan karfen me kunshe da ruwan tsigeka da ranka ne?!” Ba bita kanta ba tafita tabarta a ban dakin, abokiyar zamanta tasamu tace. “Auntynsu lafiya?!” Tsaki tayi sannan tace. “Malam almu yazo yana jiran Daddy, kuma wancan satin fa ya bashi kudi wannan satin ma yazo.” Shiru tayi sannan ta dauko mai zata bawa Parih amma babu ita babu dalilinta, Ita kuwa Parih daga jin maganar sune tayi waje da towel a daure, tana zuwa taga tsohon a zaune, kusada shi taje, ta fara tona rami, tsohon yace. “Jikata me kike haka babu kaya.” Sunkuyawa tayi tana kallon ramin, sannan tace. “Ayya baba tsoho ina hango kabarinka ne, domin duk wanda yazo nan gidan yanzun da nazo sai na leko karbarin shi.” “Ke ja’iran ina ne, dan gidanku a ina kika tab’a jin an hango kabarin mutum.” “Laaa! Kaji min bana tsoho wai da gundira mishi karya, don Allah zo na nuna maka Alkur’ani ga kabarinka nan.” Jikin tsohon ne ya shiga kerrma, da cira kafin ta bud’e baki tuni ya arta a guje sai tashin Babbar rigarshi a iska kake gani (🤣😂) Parih……. Juyawa tayi abinta Jalal na hangota, daga window dakin shi har ta wucce cikin gida, lokacin har su Hajiya Adawiyah sun fito daga cikin gidan suna nimanta, a kofar falo suka gamu, sai wiki-wiki take da idanunta. “Parih! Ina kika je ko kaya baki saka ba.” “Mamie waje take gurin Malam Almu! Ban san me ya faru ba sai tashin Babbar rigarshi kawai nake gani” Kallon ta Hajiya Adawiyah tayi domin jiran karin bayani daga bakin Parih. Tura nan ƙaramin bakinta tayi sannan tace. “Yoh naga kuna mitar ya dame ku hine na kore hi” Zaro ido suka yi gabaki d’aya su suka ce. “Meye!!!?” Wucce su tayi tare da watsar da hannun ta a iska, tace. “Eh koran hi nayi bayi kuma zuwa muku sai dai ku ji labarin ya hige gidan nan.”+ Bin ta suka yi da ido, musamman Jalal da yake binta da wani irin kallo. Fita yayi daga cikin gidan ya nufi, inda d’akin shi yake ya faɗa gadon shi yana rintsa idanunshi, tuno yanayin tariyar yayi. ….. “Parih karki kuma fita babu kaya a jikinki! Kinji dan akwai masu yanka mutane a unguwar nan kina jina,” Gyada kai tayi idanunta a waje, can ta d’ago kai tace mata. “Hajiya! Idan an yanke kan mutum cinyewa ake?” “Eh toh musamman idan mutumin ya kasance magananne! Kuma me fita ba kaya” Ta karshe maganar ta hanyar haka. Shafa mata Jet Hajiya Adawiyah tayi zata taje mata uban gashin kan ta, ta riko hannun ta cikin ihu tace. “Alkur’an! Baki taje min gahina haka! Kutt kin manta inda ruwan tsige mutum da rashin ya zuba min ne, da zaki taje min Alkur’an kina tajewa hita gahin zai yi kamar yadda ake sale gahin kaza!” Mamaki ne ya rufe Hajiya Adawiyah tace. “Toh shi kenan! Bari na miki a hankali yadda bazai miki zafi ba tunda zan tsige miki gashi me” Shigowar Buhayyah da Amrozia yasata kwace kanta tace. “Don Allah! Zo ki duba min tsakar kayina ko an tsige min gahina” Zuwa Buhayyah tayi ta leka kanta! Da gaske yayi ja amma ba wani na tashin hankali ba. “Sannu! Amma ba wani ciwo bane da kawai ja gurin yayi sabida kalar skin dinki’ Kallon Buhayyah tayi sannan ta yatsina fuska tace. “Me kika ce?” “Kinga zo ki saka kayan Buhayyah kafin mu shiga kasuwa.” Juyawa tayi gashin kanta yayi tsage tsage, taki kuma a gyara mata. Cikin shagwaɓa Buhayyah tace. “Mamie yaushe zamu tafi Gida dubu?” Kallon ta Hajiya Adawiyah tayi sannan ta cigaba da abinda take yi, dan tasan dalilinta na son guduwa daga gidan, sabida dodon su da zai dawo gidan wato Babban Yayansu. Narka fuska tayi sosai kamar zata fasa ihu, ita ko PARIH tana gaban madubi tana aiki. Wato zama tayi ta bud’e kwalbar maganin mura ta juye a cikin roban man shafawa. “Please Mamie!” Juyawa Parih tayi a fusace, kamar wacce aka yi da ita. “Ke dilla can! Kin dame mu da wani abu wai fidda” Rike baki suka yi sakamakon b’ata fuskar ta da tayi wai nan ta kure a daka, idan kaga fuskar tankar an shafa bakin paint. Dariya Buhayyah ta saka tare da rike cikin tace. “Wallahi kin koma kamar Yar auta!” “Zo na goge miki! Amma fuskar ki tab’aci!” “Alkur’an baki goge min kwalliyata!” Duk yadda suka so goge mata kwalliyar taki, karshe haka suka kyaleta, ta suka fito kowa sai dariya suke mata, abincin ta Amrozia tayi ta ajiye mata a gabanta. Kallon abincin tayi sannan ta d’ago kanta kamar zata fasa kuka tace. “Meye sunan wannan abincin me kama da gwazarma?” Wato makaroni! Take tambaya, Leka kwanon tayi sannan ta d’ago kanta da sauri kamar wacce taga dodo tace. “Alkur’an bani cin abincin nan!” “Kici macaroni ce!” “Markarome! Jifa sunan abu sai kace markaɗe! Wallahi bani cin sa” Kuka tasaka tare da kwanciya tayi a kasa, tare da birgima tana ihu. “Wayyo Allah na! Wallahi bani cin wannan gwazarman nan, Alkur’an ku mai dani gurin Kaka Iya, ta bani gaya naci.” Sai da Alhaji Muhmood ya sauko daga sama, ya zauna kusada ita yace. “Ku kawo min tuwon da aka min!” Aunty Amarya ce ta kawo mishi tuwon akayi ya dauka ya zuba mata, a cikin filet kallon tuwon tayi ta ganshi ruwan kasa wato semo miyar egusi, d’ago kai tayi sannan tace. “Wannan abu me kama da bayan garin nan kuma nufin Ni ce zan ci! Wallahi bani cin shi”2 Dafe goshin sa tsabar tashin hankali, Rigimar da tasaka musu, kad’ai ya isa. Asalin Alhaji Muhmood dan misau ne daga kauyen Dabji, su uku iyayensu suka haifa, Alhaji Muhmood sai Hajiya Fatimah tana aure a Gamawa, sai Abtisham Mahaifin Hal Parih. Alhaji Muhmood yana da mata biyu, Hajiya Adawiyah sai Amaryanta Aunty Mariyah. Sannan yana da yara goma, Hajiya Adawiyah tana da Yara shida, Amiduddawlah shine babba sai Sabriyah tana aure A gida dubu itace Buhayyah take cewa zata gurinta. Sai Ahmad wanda yake binta Sabriyah, sai Fahmeedah da Fahhamah yan biyu ne, autarsu ce Buhayyah. Aunty Mariyah tana da yara Hudu, Jalal shine Babban sa’an Ahmad, sai Hashmat take binshi ita kuma sa’ar su Fahmeedah da Fahhamah, sai Amrozia wacce suke sa’anin da Buhayyah, tsakanin su da Aarib shekara d’aya suka bashi Gidan ana zaman lafiya sosai dan Hajiya Adawiyah ta kame girmanta, ita kuma Aunty Amarya ta rike kankantar ta, sannan taja Amiduddawlah a jiki sosai wanda ya zama ɗan d’akin ta ne. Sai Hajiya Fatimah tana da yara uku, Najmuddawlah shine babbar, Huwaydah sannan karamar su Jadwah. Sai Mahaifin Jal Parih, Abtisham, Parih kadai suka haifa. Asalin sunanta Jal Parih ce, bayan Rasuwar Iyayenta da aka bawa Kaka Iya tace ita bazata iya kiranta da Jal PARIH ba, sabida bata iya kiran sunan ba, da farko ma Jar Fara take kiranta dashi, sai daga baya Kawun Parih yake ce mata bafa haka sunan yake ba, Sunan Jal PARIH ce, tace ita bazata iya ba sai da abinda yazo bakin ta takirata da Jan Parih…..1 Spain… Madrid…. Shine babbar birnin Spain, zaune suke a gefen Coach dinsu sai tsara musu yadda wasan zai kasance yake, duk wannan maganar da Ake bai sashi d’ago kanshi ya kalli me horonsu ba, asalima ya b’ata shiru ne, sabida tuno alkawarin da yayiwa Aunty Amarya nacewa idan ya dawo zai amshi auren Yar abokin Daddynsu ne yake damun shi. Matsalar shi d’aya ce yarinyar da ake so ya aura ta cika rawan kai shi a tsarin shi ya samu macen da zai sanya doka tabi, yana bukatar mace renon shi wacce sai yadda ya lankwasa ta. Ba wacce zai sha wahala da ita ba. A haka suka shiga filin wasan suka. Wannan shine wasan su na karshe, a wannan kakar wasan bana, kuma suna gamawa zai tarkato kayan shi zuwa Naija. ***** Bauchi State Nigeria. Kallon tuwon shinkafa tayi tayi kyau fara da ita, sai ɗaukar ido take. Ba tare da dogon nazari ba takura sokawa tuwon finger ta darasi rabin tuwon ta raba gida biyu sannan ta shiga yanka tuwon kananu sannan ta fara riga wata mahaukaciyar loma. Ta kuwa cika bakinta da tuwon miyar kukan na bin bayan hannunta ta kuma zabtar wani tuwon ta cika baƙinta sannan tace. “Yoh ai miyar nan gwanin dad’i yaƙe! Dama lokacin da ake miyar naga Iya talatu ta d’and’ana miyar sai da yawunta ya kusan dig’a a cikin tukunyar dahuwar”+ Shiru falon yayi dan basu san me zasu ce ba, ta gama cika musu kunne da kuka yanzun kuma tazo tana musu surutun banza. “Ai lokacin da kika fita daga madafin naga wancan yar gajeruwar ta cika abu a kwano takai kofar gida.” Kar ku manta baƙinta cike yake da tuwo, take wannan surutun. “Ai sau biyar ina ganin lokacin da take d’and’ana miyar.” Lashe hannunta tayi har bayan hannun ta kuma lashe bakinta, tare zurma hannun duka a baƙinta ta lashe wannan ta kuma cewa. “Alkur’an sau ba adadi ta dangwali miyar” “Kinsan Allah kici tuwonki ko kuma nazo na taka bakin kin nan mara kunya da goshinta kamar na jinjirin jaki.” Wani irin kallon ta auna mishi kafin ta cika baƙinta tace. “Toh ula uban ifiritai! Da wani katon kai kamar tukunyar girka! Ko nace ka kulani ne mutum sai mugun fushi kamar wanda aka zage ubanai” “Ke bani cikin rashin kunya! Sa’anki ne da zaki dube shi ki zage shi, maza bashi hakuri ” Inji Aunty Amarya, dan ta rama abinda Jalal yace mata. D’ago kai tayi kamar zata fasa kuka tace. “Toh baki ji abinda yace min bane” “Kaniyar ki, da abinda yace miki” Tashi tayi ta shure filet din tabar falon, ta koma can gefe ta zauna, tana wani kwaɓa fuska kafin su an kara ta fashe da uba ihu wai nan tana kuka. Hajiya Adawiyah da take cikin d’akinta, ta fito da sauri. “Ke Parih lafiya kike zumduma ihu haka!” Sai da taka wani kugi kafin tace. “Zagina suka yi wallahi sai kin mai dani gurin Iyata.” Duk yadda Aunty Amarya taso kare kanta ita da Jalal Parih ta hanasu domin suna bude baki da niyyar magana zata fasa ihu me karfi dan dole Hajiya Adawiyah ta rarrashi ta, suka koma cikin d’akinta. ***** Washi gari da safe, bata karya ba ta tashi ta sulale zuwa waje. Kallon gidan tayi da kyau, hango yar gajeruwar Yarinyar nan tayi taga ta shige cikin ciyawa, wato flower da sauri itama bin bayan Yarinyar tayi har bakin wani kofa, taga yarinyar tashiga. Tura kanta tayi ta juyo muryan Jalal yana cewa. “Yawwa nan zaki rike min” sai magana yake yana nishi. Aikuwa ta burma musu kai, da sauri suka buga tsalle kowa ya kama maboyar shi. STORY CONTINUES BELOW Rike k’ugu tayi tace. “Me kuke yi ne?” Haushi ne ya rufe Jalal ya fito a fusace yace. “Kaniyar ki muke yar banza!” Juyawa tayi taga kowa ba, sannan ta maida idanunta kan shi, tace. “Ya naganka babu riga” Dafe goshi yayi kafin ya dawo daga tunani ta kuma jefa mishi tambaya. “Au bujen ka ne wannan?” Ta d’ago unders din Hansiya! “Zaki fita ko sai na zo na balla miki haɓɓa.” Tura baki tayi gaba sannan tace. “Wata uwar kuke da baku son na gani” Mikewa yayi a fusace zanin gadon ya zame, yayi maza ya rike tare da finciko wayar chajin sa yayo kanta ai kuwa ta arta a guje, Hango get tayi ta fita da gudu, tana isa ta bankad’e kofar, tana kallon mutanen da suka zo maula, murmushi tayi sannan shiga kirgasu, tana gamawa tace. “Me kuke yi a gurin?” “Ayya Yarinya munzo gurin Alhaji ne!” Gyad’a kai tayi sannan tace. “Baku da labarin ko!?” Zuba mata ido suka yi tare da jiran karin bayani, gyara tsayuwar ta tayi sannan tace. “Toh kenan baku fahimci abinda ke faruwa ba?” “Yarinya meke faru?!” Gyad’a kai tayi sannan tace. “Zaku iya higowa” Jikin su na rawa suka biyo bayanta, tare da murna sun sami damar ganin Alhaji Muhmood cikin ruwan sanyi. Su uku ne dama mutanen, kuma sun manyanta. Suna shigowa ta nuna musu kujera, duk suka Zauna sannan ta koma ta rufe gidan suna kallonta. Murmushi tayi masu sannan ta kalli yadda suka zauna kamar mutanen arziki take ta ware hannunta kamar wacce zata yi abin arziki ta shiga cewa. “Duk wanda ya higo gidan nan, bayi kuma hita sai dai gawar hi, ya kai aljani butubutu me kan goriba! Ya kai aljani bunburutu me kan giginya! Ya kai Aljani rugurgurasa! Ya ku manyan Ifiritai ku hito ga kalace sunzo muku har gida, duk wanda ya higo gidan nan ba a kuma hita dashi sai dai gawar hi, hahhhha” Wato da suka shiga zaga gidan tare da salati, niman kofa suke amma sun gaggara samu.2 “Wayyo Allah! Ku taimake mu bamu sake zuwa gidan nan ba, Don Allah kuzo ku fitar damu” “Allah baku hita ko ina sai an zuke jininku” Da kyar d’ayansu ya sami kofa kafin ta juya gare shi tuni ya cikawa bujensa Iska! Sauran ma suka rufa musu Anan suka bar takalmar su. Juyawa tayi suka yi ido biyu da Alhaji Muhmood. Sunkuyar da kai tayi a hankali yazo zata wuce ya riko hannunta suka shiga cikin gida ba kowa a falon, zaunar da ita yayi bisa kujera sannan ya kura mata ido yace. “Me yasa kika Kore su?!” Kanta a kasa tace.. “Baffa sun yi sammako ne.” Shafa kanta yayi sannan yace.. “Karki kuma kinji zan kai ki makaranta ma kije kiyi ilimi.” “Ba dai inda ake koyar da yaren nasara ba” Zaro ido yayi waje. “Waye ya gaya miki haka!” Tura baki tayi sannan tace. “Iyata mana” Jin motsin Yarinyar da ta gani a dakin Jalal yasata juyawa tana dariya tace. “Baffana! Ka ganta can na kalle su babu kaya a jikin su ita da me sheker ungulu” Jikin yarinyar kallonta Alhaji Muhmood yayi dan ba wai ya fahimci zancen Parih bane, ita kuwa Parih mik’ewa tayi ta bar falon ta nufi kitchen, ta samu bana talatu tana gyara kayan miya, ga dumamen da take yi a gefe zama Parih tayi tana kallonta, sai da ta bari Bana talatu ta sauke dumamen aikuwa ta sunkuto tukunyar baki daya tayi waje dashi tace. “Ai abincina ne aka ce ayi min bayan ji kin tsame min arzikin miya shine yau Bara ki barni na karhe ladana ba. Kuma yau ku kirb’a min tuwon yayi lauhi ya, miyar kukata me kukan dad’i” …….. Riƙe baki Bana talatu tayi tana mamakin Parih, tab’e baki tayi cikin masifa tace. “Yar banza Y’a me shegen fitinar tsiya daga zuwa ta dami kowa da surutun bala’i.” “Hmm! Baba talatu ai mako me sauki ne saura kiris ta yanke min shan ruwana a gidan nan.” Zaro ido Baba talatu tayi cikin garaje tsce. “Ke yar nan garin ƙaƙa?!” “Dan naje gyarawa Jalal dakin shi da” Kura mata ido baba talatu tayi sannan tace. “Anya hansatu! Kuma ba tayar baya bace.” Shiru hansatu tayi, kafin Bana talatu tai magana. Suka jiyo muryanta. “Ke tulaliya bani hanya kin wani tokare kofa kamar giwa! Sai tarin tsokoki! Yawwa me abinci, gulmata takawo miki ko?” “A’ah Fara! Zaro ido tayi ta kalli gefe da gefenta, ta ga abubuwa abinda ya duba aikuwa ta fasa ihun tana buga kafarta a a kasa. Da sauri Alhaji Muhmood ya shigo shida Hajiya Adawiyah suna tambayar su. “Lafiya!” Cak tayi shiru kamar wani abu bai faru ba, tace. “Ku Tayani duba kafad’ana akwai inda fufuke yake dan nima ina son gwada tashi sama ne”🙄 Ta ware idanu akansu tana jarin me zasu ce. “Waya ce miki mutum yana da fukafukai” Juyawa tayi irin ta fuskar nan ta kalli Baba talatu, ta kwad’a mata harara sannan tace. “Baga me abinci ta kirani da Fara ba.”+ Girgiza kai Alhaji Muhmood yayi sannan ya bar kitchen ɗin, Hajiya Adawiyah ta kalli Baba talatu tace. “Sunanta Jal Parih” Cab’e zance tayi da cewa. “A’ah Jan Parih dai ko” Dafe goshinta Hajiya Adawiyah tayi sannan tace. “Toh naji! Baba talatu kindai ji sunanta.” Kafin ta rufe baki Parih ta fice daga kitchen ɗin ta nufi inda ta ajiye tukunyar tuwon ta, a Tsakiyar center table ɗin falon, ta hau ta zauna tare da lankwasa kafarta, tana cin abincin. “Parih! Sauka kici abincin a kasa mana ai nan an ajiye shine ɗan kwalliyar falon.” Kamar zata yi kuka tace. “Wallahi da kinsan daɗin da nake ji na danne sama ina cin abinci sai kin jinjina min! Kin ma tab’a cin abincin a samar nan?!” Girgiza kai tayi tace. “Toh aini dake ba d’aya bane, ke karama ce Ni kuma babba ce kinga ina hawa fashewa zai yi ke kuma babu abinda zai same ki.” Ware idanu tayi waje tace. “Ince ba a mutuwa dai!” Itama ware mata idanu tayi sannan tace. “Mutuwa kai! Ai mutuwa ma d’aya kika ji, kana faduwa akai sai mutuwa ko shurawa baka yi.” Kafin ta idar da maganar tuni Parih tayi masauki a kasa tana raba idanunta. “Hajiya!” “Mamie dai! Kamar yadda yan uwanki suke kirana” Gyad’a kai tayi sannan tace. “Mamie!” Kura mata ido Hajiya Adawiyah tayi musamman yadda takira sunan mamien, “Ina jinki” “Tunda na sauka ince bani mutuwa” “Parih kowani mutum da kike gani dole ya mutu dan ita muke jira! Koda ciwo ko ba ciwo idan ajali tayi kira dole kaje” “Toh Ni dai lokaci na bayi ba, dan sai na tsufa.” “Toh Parih ai babu wanda zai so ki mutu baki tsofa ba.” Haka tayi ta jefawa Hajiya Adawiyah tambaya ita kuma tana gaya mata abinda ta sani. **** “Lamisah! Ina kike kai jama’a a haka kike tunanin wancan miskilin zai karbi aurinki da shegen nawarki nan ki fito” Sanye take da doguwar riga ruwan hanta, sai farin gyalen da ta yane kanta, tayi kyau ba laifi a hankali take takawa har inda Mamarta take, tana murmushi. U “Ummi kiyi hakuri” “Muje kina b’ata mana lokaci.” Fitowa tayi suna jera tana tambayar Uwar. “Ummi ina zamu” “Gidan Alhaji Muhmood! Kisan Amiduddawlah ya kusan dawowa! Kuma ina son naje na daina Hajiya Adawiyah.” Shiru tayi sannan tace. “Ummi dole ne sai dani zamu je?” “Ke bani ciki da rashin hankali idan bazaki ba koma sakarya kawai.” Haka suka shiga motar tana sababi, har suka kusan isowa gidan. ….. Tunda suka iso ake shirya musu gabansu Lamisah sai sunkuyar da kai take, Uwar kuwa ta zauna sai gyata karya take. “Ai Hajiya! Da kyar ta biyo Ni wai kunya take ji.” “Karya ne! Wannan me idanun kamar ta budurwa kare, sam bata kama da me jin kunya ba, yadda take kallon namar kazar gabanta” Dukkan su suka d’ago kai suna kallon Parih, wacce ta jagalgala fuskarta da Eyeshadow. “Parih bana hanaki shiga maganar manya ba” Sunkuyar da kai tayi cikin karamar murya tace. “Kuyi hakuri bani kumawa Amma Mamie Alkur’an batai kama da wanda take jin kunyar ki ba, wai ma tukun su din suwaye? Ita din wacece da take jin Kunyarki?” Jan hannunta Buhayyah tayi suka koma dakinsu, Inda tabar Amrozia tana fushi ta farfasa mata Eyeshadow ɗinta, Buhayyah tace. “Ke itace zata auri Ya AMIDUD” “Kutt! Wannan me kana da muciya da zanin ce, zata yi aure i dai haka ne toh lallai noma sai an daura min aure”😏😒 “Ke lafiyarki Parih! Ina ke ina aure idan Mamie taji zata fasa miki baki.” Murguda bakin tayi sannan tace. “Allah da gaske nake sai an daura auren dani.” Duk yadda Buhayyah da Amrozia suka so hanata fita haka tafito, ta tsaya musu tsagege tace. “Mamie! Nima aure zaku min” Dafe goshin Mamie tayi, sannan ta daka mata tsawa. “Fita ko na zaneki yar nima fitinanniya kawai.” Amadadin ta shige cikin gida waje tafita da gudu, ta shige jikin flower tana kuka. Zama tayi a gurin tayi ta kuka. Bayan fitar ta Hajiya Adawiyah ta kalli Mahaifiyar Lamisah tace. “Kuyi hakuri! Daga kauye aka kawo mana ita, ina ga zaki tuna da mahaifinta, Abtisham.” “Haba ina ta kallon fuskarta ashe Yarmu ce! Kamar tayi yawa, Allah sarki Allah jikan iyayenta, Ai zaman kauye shi ya maida ita haka.” “Eh wallahi gata nan tunda yazo sai hana mana Gwari take” Haka suka hira har aka fara kira sallah, sannan suka tashi zasu shiga dakin Hajiya Adawiyah, Mahaifiyar Lamisah tayi ita kuma Lamisah ta shige dakin Aunty Amarya! …… Tun hudu da Parih ta fita take kuka bata daina ba, karshe fitowa tayi daga cikin flower ta zauna, a inda Alhaji Muhmood yake parking, ta zauna tana kuka motar shi, na shigowa gidan kuka ta kara har ya iso yayi parking, kuka take. Da sauri ya fito yazo inda take, yace. “Parihna! Waye ya tab’aki” “Baffana! Aure za’a min, wai nace a min Shine Mamie tayi min fada” Dariya ta bashi, girgiza kai yayi sannan ya riko hannunta yayi yana murmushi har suka isa bata daina kuka ba. Suna shiga falon da Sallama ya nemi guri ya zauna, Aunty Amarya ce ta fara fitowa, tana fitowa taga yadda Parih take shashekar kuka. Karban jakar shi tayi tare da mishi Barka da zuwa, can sai ga Mamie ta fito, nan taga Parih tana kuka. Nan take tambayar ta lafiya dan har ta manta abinda ya faru, sai da ya labarta mata abinda ya faru, nan taruka baki tana dariya sannan tace. “Toh waye mijin da za’a daura miki aure dashi” Watsa hannun ta tayi sannan tace. “Toh Ni koma waye ina ruwana ni dai aura min kowa ma!” Dariya ta basu sannan Alhaji Muhmood yace. “Shi kenan zan aurar dake haka yayi miki amma kuma zaki yi karatu yadda zaki ji dad’in auren.” “Yoh wani karatu, ai kome ma Zanyi amma Baffana ince ka kai aure” “Har kin wucce ma” Tsalle ta buga tace. “Yawwa dole ma na nunawa Aaraih Ni ba sa,arta bace

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *