JAWAHEER
CHAPTER 3
Yau su mum zasu koma nigeria dukansu sun shirya an saka musu kaya a mota dan zuwa airport, mum tana tama jawaheer nasiha tare da kara tuna mata ta rike mutuncinta na diya mace, har suka fita suka nufi airport, aka fara kira nan su mum suka fara shiga cikin jirgi jawaheer tana ta daga musu hannu, har jirginsu ya tashi sannan ta koma gida, koda ta nufi gida wanka ta fada tayi tasa wata top mara hannu tare da wani wando 3quater tasa boyfried jacket mai dogon hannu tasa botir din boyfried din tare da saka wata hula a kanta duk da batai makeup ba tayi kyau sosai dan ita jawaheer bata cika son yin kwalliya ba, tafi son zama haka, ta gaban wani daki taje ta zauna da yake gidan gidan sama ne ta wajan dakin yana nuna maka ko ina da ina da gidajen dake kusa da nasu da kuma motoci masu tafiya da mutane masu wucewa zama tayi tana ta kallon masu kaiwa da komowa, lokaci daya kuma ta fara tunanin m samir amma idan ka ganta zaka dauka mutane take kallo amma hankalinta baya wajan gaba daya wani siririn hawaye ne ya zubar mata a ido tunawa da tayi taga m samir ido da ido amma ta kasa yi mishi magana lokaci daya kuma ta saki murmushi domin ta tuna da irin murmushin da yayi mata ido ta lumshe tare da fadin nasan kaima zaka soni kaman yanda nake sonka haka taita tunani a wajan har yamma tayi ta shiga cikin gida.
Bayan m samir ya fito daka toilet karema dakin kallo yayi lokaci daya kuma yayi tsaki domin bashi da kayan sawa a nan, jikinshi daure da towel ya fita falo yaga sonia tana kallon news sunanta ya kira tare da fadin bani da kayan sawa a nan, murmushi tayi tare da tashi ta nufeshi tayi hugging dinshi tana fadin karka damu ai babu inda zaka nafi son ka zauna a haka inyi ta kallonka…. Dai2 lokacin dad dinshi ya shigo da yake sun bar kofar falon a bude jin sallaman dad dinshi yasa ya dan jata baya amma saita kara manneshi tana fadin come on, dad dinshi ranshi bace ya juya ya fita daka gidan, ganin haka yasa ya ture sonia yana fadin mai kikeyi haka? Bakiji dad dina bane? Tace naji toh mai kakeso inyi mishi? Magananta ta dan bashi haushi amma saiya dake yace daya shigo saiki sakeni sannan ki dawo ki zauna kalla fah yanda nake daka ni sai towel so kike yayi tunanin ko wani abu mukayi? Tace sai me dan yayi tunanin hakan ni ba damuwa ta bane, cikin bacin rai yace look sonia inaso ki sani idan ke ba damuwanki bane toni damuwa nane, domin addini na bai ce inyi haka ba nd….. Ta dakatar dashi tare da fadin ya isa haka ni nace ka shiga cikin addininka mai takura ma mutum addinin da baya ba mutum yancin kansa so ya kamata ka gane gskya ka dawo christen dan shine hanya mai bullewa, shuru yayi yana kallonta cikin mamaki harta gama, sannan yace u r wrong sonia addinina shine addini mai bama mutum yanci addini mai haske dat islam addinina ya haramta zina sai yasa Allah yaba namiji daman auren mata har hudu domin gujema baraka…… What u mean ur religion allow u to marry more dan 1 women? Kai ya daga mata alaman eh, cikin zafin rai tace what kind of religion iz dis how can man marry 4 wife dan murmushi tayi mai zafi sannan tace kana nufin idan mukayi aure zaka kara auran wata?? Kai ya daga mata tare da fadin bani da burin auren mace fiye da daya amma ban san abunda Allah zaiyi ba, cikin rashin fahimta tace bata ganeba, yace idan Allah yasa zan kara zan kara in kuma bai sa…. Ta dakatar dashi cikin kuka tare da fadin ita ba zata iya aurenshi ba dan me zaice zai kara wata mace bayan ita, sannan yasan ita a nata addinin mace daya ake aure kallonshi tayi cikin fushi tace bazan zauna dakai ba yau zan tafi sannan bazan dawo kasar nan ba ko inzo gareka ba har sai ka canza addini domin bazan iya auren muslim ba tunda haka addininku yake tana fadin haka ta fita yana ta kiranta amma bata tsaya ba gashi babu kaya a jikinshi, koda ta fita daukan jakarta tayi a motar daya kawo su ta wuce, zama yayi ya daura hannu a kai alaman damuwa lokaci daya kuma yayi tsaki tare da ware hannu alaman ban damu ba daki ya koma ya dauko waya ya kira waya dan a kawo mai kaya yana gama fadin abunda yake bukata ya kashe waya
Jawaheer kullum bata fita sai dai tazo wajan dakin nan taita kallon mutane masu wucewa yauma tana zaune har yamma taji gaba daya zaman ya isheta dan haka ta fito waje ta tsaya ta gaban gidan tana kallon gidan dake kallon nasu domin gidan ya birgeta yana yin yanda aka tsara gidan a hankali ta furta duk yanda akayi suma nan kasar nan area din yana daya daka cikin wajan da masu kudin kasar suke dan gaba daya tsarin gidajen dake wajan gwanin sha’awa, ganin giftawan mutum tayi daka gidan dan murmushi tayi tare da fadin bari inyi karan bani in leka gidan ko zan saba dasu, dan zama mutum daya babu dadi, dan shuru tayi tana nazari nan fah kasar waje ne ba nigeria ba toh in taje mai zata ce musu? Wata zuciyar tace kije may be ma sun san m samir dinki dariya tayi lokaci daya kuma ta nufi gidan, koda ta karasa kofar gidan mutumin da taga ya gifta ta gani yana tsaye da ledoji a hannunsa alaman yana jira a bude mai kofa cikin harshen turanci take cemai sannu ni….. Bata kai ga karasa magana ba aka bude kofar tsayawa tayi cak tare da zare ido tana nuna wanda ta gani da hannu alaman kai ne ko gizau ne, lokaci daya kuma tayi murmushi tare da fadin no no ido nane ba m samir bane mai yasa idona kamin Karya mutumin da ganinshi ance min bamai yuhuwa bane sai gashi da towel a gaba na, duk cikin harshen turanci take maganan shiko mamaki abun ya bashi ganin yanda take mamaki kaman bashi ta gani ba, lokaci daya kuma yayi dariya tunawa da yayi itace shima yake nema matsawa yayi kusa da ita tare da riketa ya hura mata iska a fuskanta yace nine M samir nine a gabanki fadowa tayi jikinshi ganin kaman bata motsi yasa ya fara jijjigata……
Daukanta yayi cak ya shiga da ita cikin gidan bai ajiyeta ko ina ba sai cikin dakinshi akan gadon dakin ya kwantar da ita, mutumin daya kawo mai kaya ya ajiye ya wuce, toilet ya shiga ya dibo ruwa a hannunsa ya yayyafa mata wani irin ajiyan zuciya ta sauke mai karfi, tare da bude idonta dishi2 ta fara gani fuskan M samir ta gani wanda yasa ta bude idan nata da sauri tana fadin bashi bane bashi bane mafarki nakeyi taya zan ganshi lokaci daya ba tare da nasha wahalan da ake fadamin ba, ganin kaman tana kwankwanto yasa yakai bakinshi cikin nata ya fara kissing dinta, gaba daya komai nata ya tsaya cak, saida yayi kissing dinta na wajan 1minute sannan ya saketa dan ya tabbatar yanzu zata cire komai da take tunani tasan shi dinne dagaske, amma ga mamakinshi sai yaga ta tsaya cak, kai ya dan buga wanda hakan ya nuna mishi shine first time da aka taba kissing dinta dan murmushi yayi tare da jan hancinta da hakorinshi ihu ta saki, tana kallonshi yace yes nine a gabanki, nunashi ta farayi tana murmushi lokaci daya kuma ta fara kuka, kallonta ya tsayayi yana mamaki, rungumeshi tayi tana ci gaba da kuka ta fara fadin ban taba tunanin zan ganka ba a rayuwa na, duk da nazo nan kasar dan in ganka amma ance min ganinka ba abu mai sauki bane kullum nayi sallah sai na roqi Allah domin ya nuna min kai koda sau daya ne a rayuwa na, na ganka a asibiti lokacin ban san dalilin da yasa na kasa yi maka magana ba, saj gashi yau Allah ya nuna min kai gaka a gabana jikina a cikin naka duk da bada son raina nayi hakan ba, tsabar farin ciki ne…. Cire jikinta tayi daka nashi taci gaba da fadin bana kallon ball amma ranan dana fara kallo na ganka lokacin kaci ball naji anata kiran M samir tunda na ganka naji Allah yasa min sonka, idan ina magana iyayena suna min kallon kaman bani da hankali amma ni daya nasan abunda nakeji bani da wani buri daya wuce in zama matarka, amma ance min hakan bamai yihuwa bane saboda celebrity bazai taba auren yar nigeria ba, koda burina bai cika ba zanyi farin ciki na ganka kuma kaine namiji daya daka dara kissing dina na farko a rayuwa na, dan shuru tayi tana kallonshi shima kallonta yakeyi lokaci daya ya fara magana cikin turanci shima yace lokacin dana ganki a hspt irin kallon da kike min nasan kina da magana a bakinki domin na saba ganin mutane kala2 amma ke irin naki kallon na daban kike min nd kuma lokacin da zamu tafi naga sanda kika fadi kina kuka….. Dan shuru yayi sannan yayi ajiyan zuciya yace ya sunanki? Tace jawaheer kai ya daga tare da kara nanata sunan yace nice name, amma baki kama da yar nigeria ba kinfi kama da yar dubai, murmushi tayi cikin jin dadi, yaci gaba da fadin ngd da kauna da kuma so da kika nunamin amma am sorry to say ina da wacce nakeso na gode da kauna, idonta ne ya kada yayi ja kirjinta ya farayi mata zafi lokaci daya taji wani abu yana son taso mata, ganin halin data shiga yasa ya tashi ya dauko mata ruwa ya bata amma bata ma san yanayi ba ganin haka ya bude ruwan yasa mata a baki babu shiri ta bude bakin ta fara sha, lokaci daya kuma ta kawar da goran ta fara kuka mai karfi tare da ruko hannunshi ta fara fadin bana tunanin akwai wacce zata soka kaman yanda nake sonka wlh son gskya nake maka bana wasa ba ka kalli idona babu komai sai sonka, tashi yayi yabar wajan jim kadan sai gashi yasa kaya, tashi tayi tazo inda yake tana kuka ta rungumeshi tana fadin i luv u, dan janta yayi ya mata peck a goshi sannan yace ta daina kuka, sakinta yayi tare da fara tafiya yace zai fita zuwa wajan dad dinshi, yana fadin haka ya fita kasa tayi tana ta kuka sosai kaman ranta zai fita, tayi wajan awa daya tana zaune a wajan tana kuka sannan ta tashi dakyar ta nufi gidanta har wani jiri2 take ji, koda ta shiga gida a falo ta kwanta tana kuka gwanin ban tausayi tare da surutai kala2 dama mum ta fadamin babu abunda zaiyi dani mai yasa na kasa yarda da mum mai yasa yaki yarda dani kuka ta kuma saki tana fadin mai yasa mai yasa, tana kuka.
Shiko yana fita driver yaja shi zuwa gidan dad dinshi, koda suka karasa tafiya yake dakyar yana jan kafa, a falo yaga dad dinshi, gaidashi yayi dad din ya amsa fuska daure, murmushi M samir yayi tare da nufa wajan dad din nashi ya kamo hannunshi yana fadin kayi hakuri dad danka baya abunda kake zargi ka yarda dani, dad din yace bana zarginka dayin komai wanda ya sabama sharia, amma kasan idan mace dana miji suka kebe na ukunsu shaidan ne, ina jin tsoran ka fada halaka, samir bana sonka da wannan yarinyar kwata2 nafi son ka auri musulma yafi yanda yaranka zasu taso cikin cikakkiyar tarbiya, m samir yace okey dad naji amma saika fadamin who is my mum nd i want to see her picture, idan ka fadamin zanyi duk abunda kace min, cikin fushi dad din yace karka karamin irin wannan tambayar M samir cikin damuwa yace why dad mum dina kace ta rasu mai yasa kake boyemin labari na? Why dad? Dad din yace i dnt want you to knw anything about your mum, shima cikin bacin rai din m samir yace why dad miye a ciki dan na sani? Dad din yace wani abu ne because she’s still alive…… Shuru dad din yayi domin baiyi zaton maganan zata fito ba, M samir yace what?……
Dad din shuru yayi ba tare da yace mishi komai ba, m samir yace dad u mean u r telling me lies ol dis yrs, why dad mai yasa ka boyemin mahaifiyata why dad maina maka dana fuskanci wannan hukuncin? Dad tel me ina mum dina i want to see her plz kuka ya saki yana fadin mai yasa ka rabani da mum dina ol dis yrs mai yasa?…… Kuka ne yaci karfinshi ya kasa karasa maganan da yayi niya, dad din cikin tashin hankali yace samir ina jin kunya tare da takaicin fada maka koya akayi na sameka, shekaru talatin da suka wuce……….
LABARI
Nayi aiki a nigeria a garin abuja amma da yake aikin contract ne na titi and kuma lokacin company dina akaba aikin, so dole yasa nazo nigeria ganin yanda akai aikin yayi kyau yasa aka kara bama company dina wani aikin wanda yasa dole na dawo nigeria amma wannan karan a wani gari na sauka yola garin akwai wani yare ana ce musu fulani ina son al’adun garin and kuma akwai abunda suke saidawa nono ina son abun sosai akwai wata yarinya mai suna khausar ,kullum tana kawomin nono ina siya batajin turanci ni kuma bana jin yaransu haka zami ta magana kaman kurame har na dan fara koya mata turanci da yake tana da hazaqa saita fara ganewa wanda bata ganeba tayi shuru in naga tayi shuru sai in gane bata gane bane, aikin da zanyi a yola yana da yawa, mun saba sosai sai daka baya na gane ashe sonta nakeyi domin kuwa akwai lokacin da tayi kwana biyu bata zoba na shiga damuwa sosai gashi ban san gidansu ba, a cikin yaran da suke mana aiki na tambayi wani ko yasanta yace eh ya santa ya san gidansu, a lokacin da naje gidansu na sami babanta bayajin turanci sai mutumin da naje dashi yake fassara mishi abunda nake fada, nan na tambaya ya jikin khausar yace lfya da sauki,inda na bukaci in ganta tana jin jiki sosai taji dadin ganina inda nace ma mahaifinta mu kaita hspt yace a’a basa zuwa asibiti su a gida suke magani babu yanda banyi ba amma tsohon nan yaki yarda haka na hakura na dawo cike da tausayinta ga sonta daya kamani lokaci daya, ganin bazan iya jurewa ba yasa na dauko dr yazo ya dubata dakyar babanta ya yarda, nan aka dubata aka gano maleria ne ke damunta, an bata magani cikin kwana biyu ta warke kaman ba ita ba, babanta yaji dadi sosai inda a nan nake fadama babanta ina son aurenta, tam ya tamke fuska tare da fadin bazai taba yihuwa ba yarshi ba zata auri bature ba, kai koh bahaushe ma bazai bama yarshi ba balle shi dama ba dan kasar nan bane, haka na dawo gida jiki a sanyaye tare da tarin tambayoyi, shin miye laifina danni badan kasar nan bane? Nima fa musulmi ne kaman su, rannan ina zaune sai gata tazo cikin dare tana kuka wai dama ina sonta ban taba fada mata ba? Gashi yanzu babanta yana kokarin aurar da ita ga wani dan uwanta hankalina ya tashi sosai na shiga damuwa amma irin kukan da takeyi shi yasa na fara rarrashinta har takaini da taba jikinta inda shaidan yayi nasara akan mu muka aikata aikin dana sani, ranan nayi nadama sosai haka itama babu abunda muke mu duka sai kuka, haka ta tafi gida tunda ta tafi ban kara ganinta ba na shiga damuwa sosai har takaini da kara zuwa gidansu dan inga mahaifinta koh zai hakura ya bani ita amma yaki babu irin magiyan da ban mishi ba amma yaki saurarana daka karshe ma korana yayi, ana cikin haka kwatsam sai gata tazo ta sameni tana kuka wai tana da ciki innarta ta gano tana roqona in bar garin domin idan ta fada shine ya mata cikin komai zai iya faruwa wanda zai aureta zai iya kasheni domin bashi da imani, da farko naki yarda amma irin kukan da tkeyi da roqan da takemin yasa nabar kasar gaba daya, ina nan spain ina fama da tunaninta da kuma watan da zata haiyu, har lokacin yayi na koma nigeria ban bari kowa ya ganni ba na nufi gidansu cikin dare suna bacci na dauko ka na gudo dakai kasar nan tare da taimakon wata abokiyar aikina wacce itama yar nigeria ce ta zauna a matsayin mamanka, tun kana karami kaman ka sak na mahaifiyarka sai dai ka dauko farina duk da itama fara ce amma na fita, tunda na daukoka ban kara komawa nigeria ba har yau amma nasan mamanka tana raye sannan har gobe ina son khausar wannan dalilin ne yasa naki yarda inyi aure.
Kuka M samir yake sosai tare da fadin yanzu dama bata aure aka sameni ba, ni shege ne? Kuka yaci karfinshi dad duk da wannan abun da kuka aikata saida ka raba mum dina dani? Why? Why? Dad kasan irin ciwon da zata ji kuwa? Kasan wani hali zata tsinta kanta? Shin kasan ya zataji inta tashi bata ganni ba? Duk bakai wannan tunanin ba ka rabata dani, kuka yake sosai lokaci daya kuma ya fita yabar gidan dad din yana kiranshi amma kota kanshi baibi ba ya wuce abunsa cikin tashin hankali koh mota bai shiga ba a kafa yake ta tafiya yayinda mutane suka fara ihu tare da zagaye shi, security dinshi dake binshi dakyar suka fito dashi daka cikin mutane suka sashi a mota, kallon driver din yayi yace ya kaishi gidansa tunda ya fadi haka bai kara cewa komai ba sai kukan da yakeyi har suka karasa gida da sauri ya shiga ya fara dube2 lokaci daya ya furta whr iz she? fita yayi da sauri ya fara tambayan security dinshi ina yarinyar da tazo dazu ina take?……
Cemai sukayi basu san inda take ba, daura hannu yayi akai cikin wani irin tashin hankali dakyar ya iya shiga cikin gida koda ya shiga shima a falo ya zauna yana kuka sosai wanda na rasa gane na bakin ciki ne kona farin ciki, amma zan iya danganta kukan nashi dana bakin ciki, lumshe ido yayi tare da tunanin yanzu shi shege ne bata hanyar aure aka sameshi ba, innalillahi wa inna’ilaihira jiun, yanzu duk wani kimarsa da darajansa zata ragu a idon al’umma idonshi ne ya kada yayi ja yanzu mahaifiyarshi tana nigeria a garin yola, shida bai taba zuwa nigeria ba taya zai nemeta yasan dad dinshi da wuya ya kaishi, jawaheer ita daya ce zata taimakeshi saboda itama yar nigeria ce, ido ya lumshe tunawa da yayi lokacin daya barta tana kuka akan ya sota, lokaci daya ya kawar da tunanin dan bashi bane yanzu a gabansa burinshi yanzu yaga jawaheer ta taimakeshi domin yaga mum dinshi.
Jawaheer tana kwance akan kujeran falo tana ta rusgan kuka, lokaci daya zazzabi ya kamata mai zafi, wanda yasa duk wani gaba dake jikinta ya mutu, ga kanta dake faman sara mata wanda kukan da tasha ya haddasa mata ciwan kai din da zazzabi, dakyar ta tashi tayi alwala tayi sallah a zaune dan bata ji zata iyayi a tsaye, kuka take tana roqan Allah akan ya zaba mata mafi alkhairi a rayuwanta, harta gama ta kwanta wajan da tayi sallah din, gaba daya taji zaman garin ya isheta burinta ta ganta a nigeria domin kuwa tasan M samir bazai taba sonta ba har abada, dakyar taja jikinta ta dauko wayanta dake ta faman ruri tun dazu, sunan mum ta gani dan haka ta dauka da sauri tare da fadin mum….. Sai kuma ta saki kuka hankali tashe mum take tambayanta maiya faru jawaheer lafiya kuwa? Cikin kuka tace mum magananki gskya ne, tabbas gskyan hausawa ne da suke fadin duk abunda babba ya hango yaro bazai taba hangosa ba, mum cikin damuwa tace jawaheer dan Allah ki fadamin maike faruwa, wani abu aka miki? Tace mum inaso a fara maganan biki na kaman yanda kike so da duk mijin da kuka ga ya muku, mum tace jawaheer dagaske kike? M samir fa? Kina nufin kin hakura dashi? Duk lokaci daya mum ta jero mata tambayoyi wanda yasa jawaheer din wani sabon kuka, cikin kuka taba mum labarin duk abunda ya faru tare da fadin mum jibi zan dawo gida, ki fadama dad yama PA din ambassador magana, mum tace shikenan jawaheer zan fada mishi kiyi hakuri ki cire komai a ranki insha Allah komai zai wuce, tace mum bana tunanin zan cire komai domin son M samir a jini na yake na amince da zanyi aure ne saboda alkawarin da nayi mum inaso ki sani wlh duk wanda na aura gangar jikina ne kawai a tare dashi amma zuciyata tana tare da m samir mum ki tayani da addu’a kawai Allah ya bani hakuri da dangana amma ina cikin wani hali mum tana fadin haka ta kashe wayan tare da sakin kuka mai karfi, a yanzu jawaheer bata bukatan komai face ta ganta a kasarta nigeria domin ta cire tsammanin m samir zai sota, sai dai koba komai zatai alfahari da ganinshi da tayi tare da kissing dinta da yayi duk da tasan ba abu bane mai kyau tunda ba mijinta bane, sai dai a yanda take jinshi koda jikinta ya nuna yana bukata bata tunanin zata hanashi dan tana mai mahaukacin so, wanda bata ganin kowa sai shi, sai dai kash shi ta gefenshi ba haka bane irin yanda ya nuna baya sonta yasa take ganin kaman zata iya rayuwa da wani wanda ita da kanta tasan karya ne, m samir kadai shine burinta shine namiji daya da zata samu tayi farin ciki a rayuwa koda kuwa zai dinga dukanta ne kullum, lokaci daya ta tashi da sauri duk da bata jin karfi a jikinta tafiya take tana tangal tangal kaman zata fadi kofar gidanta ta nufa ta bude ido ta kurama gidan m samir din wanda hakan ya nuna mata alaman ya dawo yana gida, tunda taga security dinshi, kirjinta taji yana buga mata da karfi, lokaci daya ta fara tafiya domin zuwa gidan har ta kusa shiga ta tsaya, lokaci daya kuma ta juya zuwa gidanta da sauri dan bata jin zata iya zuwa gareshi yanzu, amma koda ta shiga gida kasa sukuni tayi wanda yasa dole ta kara nufa gidan duk da kirjinta na buga mata dan bata san mai zata tarar ba yanzu, amma haka ta daure ta shiga cikin falon gidan a kwance ta ganshi akan kujeran falon kallo daya zakai mishi ka gane yana cikin wani hali dake bukatar taimako, da sauri ta nufeshi tare da fadin m samir, nufanshi tayi tare da fadin baka da lfya ne? Idonshi ya bude daya kada yayi ja ya sauka a kan fuskanta, murmushi ya sakar mata tare da kokarin tashi amma ya kasa, dan haka ta fara kokarin dagashi amma ta kasa, murmushi ya kuma saki tare da fadin na miki nauyi koh? Dan shuru tayi sannan tace baka da lafiya jikinka da zafi u need to see a doctor, ido ya kura mata yace jawaheer kema jikinki zafi kina bukatan ganin dr tashi yayi dakyar tare da janyota jikinshi yace maike damunki? Kirjinta ya fara bugawa da karfi wanda hakan yasa ta kasa magana domin gaba daya tunda ya janyota jikinshi wani irin shock ya kamata tare da shiga cikin wani irin yanayi bakinta sai rawa yake alaman tana son cewa wani abu amma ta kasa, ido ya kura mata yana kallonta lokaci daya ya furta she iz pretty.