JAWAHEER CHAPTER 3B

JAWAHEER





CHAPTER 3B




Hannu yasa akan lebanta alaman tayi shuru tunda ta kasa magana, dukansu shuru sukayi na wani lokaci babu mai cewa komai sai bugun da zuciyarsu keyi, ta gefen jawaheer babu komai a ranta sai kaunar m samir tare da burin ya zama mijinta, shiko ta gefenshi babu abunda yake tunani sai yanda zaiga mum dinshi sannan ya mutane zasu daukeshi yanzu tunda bada aure aka haifeshi ba,wani irin ajiyan zuciya ya sauke wanda yasa jawaheer ta dawo daka duniyar tunanin data fada, da sauri ta fara kokarin tashi daka jikinshi amma saiya kara kamota tare da fadin ina zaki? Cikin siririyan muryanta tace zan koma can ne, sakinta yayi tare da danyin murmushi wanda ake cema yafi kuka ciwo dan a halin da yake ciki yanzu ji yake kaman ya mutu ya huta dan takaici da bakin ciki, cikin wani irin murya yace jawaheer kin san yola a nigeria? Kallon mamaki tayi mishi kafin tace eh na sani, yace yaushe zamu je ki rakani? Wannan karan tambayan tashi ta bata tsoro dan haka tace mai zakayi a can wa kuma ka sani? Yace mum dina, kallonshi tayi cikin rashin fahimta amma ta kasa cewa komai, jin tayi shuru yasa yakai idonshi kanta yaga irin kallon da take mai irin na mamaki, yace jawaheer wani hawaye ne ya gangaro daka idonshi da sauri jawaheer ta tashi ta nufeshi tare dasa hannunta tana goge mai hawayen cikin murya irin wacce take cike da damuwa tace maiya sameka? Miye matsalanka? Yace jawaheer ina cikin damuwa…. Dan Allah ka fadamin miye matsalanka bana son ganinka cikin damuwa koda a filin ball naga ka fadi ina shiga cikin mugun tashin hankali har sai naga ka tashi nake jin sukuni, bazan iya juran ganin kukanka ba, dan Allah ka fadamin ko miye zanyi maka shi, ajiyan zuciya ya sauke cikin tausayin jawaheer wacce ta mutu a kanshi amma sai akai rashin sa’a baya jin komai a kanta, yace jawaheer inaso inje nigeria in nemo mum dina, zatai magama ya dakatar da ita tare da fadin nasan idan na fada miki matsalata zaki iya kyamata na, but dan Allah kiyi min alkawarin zaki zame min ido a nigeria ma’ana duk inda zani zaki bini tunda ban san ko ina ba, kai ta daga tare da fadin bana tunanin akwai abun da zaka aikata in kyamace ka, nayi maka alkawarin kasancewa dakai a ko wani hali….. Ido ya kura mata sannan yace jawaheer iyayena bata aure suka haifeni ba, a yau nasan wannan labarin wanda ya kusa tarwatsa min zuciya ta, labari ya bata na komai kaman yanda dad dinshi ya fada mishi, cikin hawaye yaci gaba da fadin ina son ganin mum dina tako wani hanya, jawaheer cikin kuka ta fara magana kayi hakuri na maka alkawarin tayaka nemanta a duk inda take, hannu ya mika mata alaman su gaisa mika mishi tayi itama yace you r my friend now, murmushi kawai tayi wanda bai kai ciki ba, amma koh ba komai tunda ya ajiyeta a matsayin kawa aita sami mukami, jin tayi shuru yasa ya hura mata iska da bakinshi akan fuskanta firgit tayi alaman tsoro duk da ranshi a jagule yake saida yayi dariya tare da fadin mai kike tunani? Kai ta girgiza alaman babu komai, ganin irin kallon da yake mata yasa tace jibi nace zan koma kasata so ban san ya zamuyi yanzu ba, yace karki damu zanyi arranging din komai, kai ta daga alaman toh, tare da tashi kallonta yayi yace ki zauna bari dr yazo ya dubaki, murmushi tayi tare da fadin lafiya na qlau indai ina tare dakai bana tare da ko wani damuwa, kallonta yayi na wajan minti daya sannan ya tashi ya dauko wayanshi ya kira dr din, zama ya dawo yayi yana kallonta mamaki yakeyi na sabon da yayi da ita lokaci daya na farko dai shidai bawai sonta yake ba bama yajin komai a game da ita amma yana son yin fira da ita dan tana dasa mutum nishadi, jin karan nocking din da akeyi yasa ya dawo daka duniyar tunanin daya afka, dan haka da sauri ya tashi ya nufi kofa dr ne tun a kofar suka gaisa sannan suka karaso nuna mai jawaheer yayi tare da fadin ga tanan, dr kallon jawaheer yayi sannan ya kalleshi yace iz she ur gal friend? Kai kawai ya daga ma dr din alaman eh dan baya son tambaya, jawaheer baki ta sake tana kallonshi lokaci daya wani irin dadi ya mamayeta, dr yace wow she iz beautiful u r lucky, murmushi kawai m samir yayi nan dr ya dubata yace jikinta yayi weak, magani ya bata har dr zai fita ta kira sunanshi da fadin dr, waigowa yayi sannan tace ya duba m samir shima dan bayajin dadi, dr yayi murmushi tare da fadin nima naga alama musamman idanshi daya kumbura, m samir yace nop lafiya na qlau, jawaheer tace plz ka bari a dubaka bai kara magana ba sai zama da yayi dr ya dubashi yace tunani ke damunshi shima dai magani aka bashi tare da shawarwari, sannan dr ya fita.




Bayan fitan dr ne ya kalli jawaheer tada daura hannu biyu a fuska alaman tagumi, daka ganin alama tayi nisa cikin tunani, ba komai take tunani ba illa auren da tace ma mum dinta ta yarda dashi gashi yanzu m samir yana kokarin jagula mata lisafi, jinshi tayi kusa dashi ya kamo hannunta duka biyun ya matse su tare da kura mata ido, yace tunanin mai kikeyi haka? Tace abunda ka fadama dr dagaske ne am ur gal friend? Murmushi yayi tare da fadin bana son tambaya ne sai yasa nace haka…… Dan shuru yayi ya kura mata ido lokaci daya kuma yace jawaheer kina da kyan da duk wani namiji zaiyi burin samunki a matsayin mata, jawaheer bani da burin auren mace fiye da daya a yanzu sonia ita kadai nake jinta…… Hannu tasa mishi a baki alaman ya isa haka, tace na fahimta na kuma gode dama inason in tabbatar da maganan daka fadama dr ne, ajiyan zuciya ta sauke tare da fadin ina zama a kasar nan ne na wani lokaci, kallonta yayi dan bai fahinceta ba, tace wata daya aka bani inyi a wannan kasar in nayi nasara in kuma banyi ba za’a dauramin aure, ganin bazan yi nasara ba yasa na fadama mum dina a fara shirin biki na……. Kuka yasa ta kasa karasa maganan shima shuru yayi yana nanata maganan a fara shirin biki na……….



Lokaci daya kuma ya furta nasara akan me? Bata bashi amsa ba dan kuka takeyi sosai ganin bata da niyan bashi amsa yasa ya tashi ya dawo kusa da ita zama yayi kusa da ita tare dasa hannunshi yana share mata hawayen dake zuba a fuskanta, yace jawaheer kibar wannan kukan koma miye insha Allah zaki samu ki dage da addu’a kinji kai ta daga alaman toh, sannan ta tashi tare da fadin sai anjima, bai tankata ba har takai bakin kofa ya kira sunanta tare da fadin inane gidanki? Tace can, dariya yayi tare da fadin can ina? Tace kazo muje saika gani, tashi yayi yana jan kafa dan har yanzu bawai ya warke bane tana gaba yana biye da ita a baya komai nata yana burgeshi kyanta nutsuwanta, maganan ta, tafiyanta kai komai nata ya mishi sai dai baya jin sonta a ranshi amma ya dauketa a matsayin kanwarshi domin so daya ne ya kuma bama sonia wacce bai san inda take ba a halin yanzu dan tunda ta tafi basuyi waya ba duk da yama dad dinshi alkawarin rabuwa da sonia amma baya jin zai rabu da ita dan itace rayuwanshi,…. Maganan jawaheer ne ya katseshi da take fadin shigo mana, sai a sannan ya gane sun zo gidan, shiga yayi da sallama, tace ya zauna a falo, bayan ya zauna ne ta nufi kitchen dan ta hada mishi coffee bata dauki wani lokaci ba ta kawo mai amsa yayi ya fara sha, sannan ya dago kai suka hada ido murmushi ya sakar mata yayin da ita kuma tayi saurin kawar da fuska dan taji kunyar kamata da yayi tana kallonshi, jinshi tayi yana fadin ina son idonki yana min kyau, bata iya cewa komai ba sai murmushi kawai da tayi, shima bai kara magana ba harya gama shan coffee din wayanta ne yayi kara dan haka ta tashi ta dauko taga ozil ne , dauka tayi da fadin kabir nayi fushi wlh sai yau? Yace kiyi hakuri m samir nasan nayi laifi tace uhm ni bazan hakura ba gaskiya, ban san mai yace mata ba naga ta saki dariya tare da fadin zan baku mamaki ku dukanku, nan dai sukai ta fira cikin harshen hausa har sukai sallama,



Bayan ta kashe wayan ne ta kalli m samir daya zuba mata ido yana kallonta, saurin kawar da kanta gefe tayi, murmushi yayi tare da fadin wannan wani yare naji kinayi? Tace hausa, kasa fadin hausa yayi dan haka abun ya bata dariya, yace ya akeyi yana son ya iya, tace babu wuya mu a nigeria shine yaran da kowa yakeyi akasarin mutanan kasata koda wata kabila ne zaka sameshi yana jin hausa koda babu yawa domin hausawa sunfi yawa a kasar, yace a nigeria yare daban daban akeyi? Tace eh akwai yare kala kala, akwai fulani, hausa, igbo, yaruba, tibi, igala, idoma, ibra, kurama, gwari, da sauransu, yace kai yare da yawa haka a kasa daya kuma duka yan kasar ne? Tace eh duk yan kasar ne, yace wow inaso inga wa innan yaren, ke miye naki yaren? Tace fulani ce ni, dan shuru yayi sannan yace dayan yaran da naji kinayi ba naki bane kenan? Tace eh, yanda take mishi bayanin abun na sashi cikin nishadi yayin da take ta kara bashi labari akan kasarta shi kuma yana jin dadi, ganin irin kallon da yake mata yasa tayi shuru tare dayin kasa da kanta tana wasa da hannunta, murnushi yayi tare da kiran sunanta yace jawaheer dago kai tayi suka hada ido tayi saurin yin gefe da idonta, domin indai suka hada ido wani irin yanayi take shiga mai wuyan fassaruwa, yace kece mace ta farko da nake son yin fira da ita, idan ina magana dake inajin dadi sosai, i will like you to be my sister, murmushi tayi tare da fadin thanks alot yau ina cikin farin ciki daka daukeni a matsayin kanwarka, insha Allah zakai farin cikin zamana kanwarka tare da alfahari dani, mika mata hannu yayi alaman su gaisa, tashi tayi ta nufeshi tare da bashi hannu yace i luv you sister, shuru tayi domin ta lula wata duniyar inama ace yau wannan kalman daya fada mata a matsayin masoyiyyarshi da bata san wani irin farin ciki zatayi ba, hawaye ne ya fara zuba a idonta, jin hannunshi tayi yana goge mata da sauri ta dago ta kalleshi, shima dai ita din yake kallo, tace yau ina cikin farin ciki ban taba tunanin zan ganka ba a rayuwa na, wannan kukan da nakeyi na farin ciki ne, yau gani ga ka, kafin in ganka an fadamin ganinka tashin hankali ne amma da yake Allah mai tausayin bayinsa ne sai ya hadani dakai ba tare da nasha wahalan da ake fada ba, sai yasa ake cewa kar bawa ya cire rai da ikon Allah, na tabbata addu’ata ce Allah ya amsa sai yasa ya hadamu cikin sauki, yace hakane sister babu abunda Allah bazai iya ba, komai ya faru da bawa ya dauka a matsayin kaddara ne a rayuwanshi…… Shuru yayi lokaci daya kuma yace tabbas dad dina bashi da laifi dan an sameni bata hanyar aureba, lallai haka Allah ya tsara babu wanda ya isa ya canza hakan, laifi daya dad dina yayi daya raba mum dina dani, jawaheer tace shima yana cikin kaddaranka, kallonta yayi ta daga mishi kai alaman eh tace haka Allah ya tsara maka sannan gashi ta sanadin haka mun kara samun kusanci haduwa na dakai shima yana cikin kaddaranka……..


*ina yinku masoya novel din jawaheer kaman yanda kuke son novel din jawaheer nasha kira da message kuyi hakuri na jina shuru insha Allah zan dinga muku posting kullum koda ba yawa😆*


Yace kaddarana?? Kai ta daga mishi alaman eh, tare da fadin gashi ta sanadi na zaka kasata nigeria, murmushi yayi tare da fadin hakane harna kosa inje koh Allah zaisa inga mum dina, inko hakan ta faru ban san wani irin farin ciki zanyi ba, jawaheer tace insha Allah zaka gan….. Bata karasa ba tayi shuru tana kallonsa shima din ita yake kallo cikin sanyin murya tace kana da pic dinta?? Shuru yayi can yace a’a bani dashi, tace sunan anguwansu a yola din fah? Shima yace bai sani ba, jawaheer tace toh taya zamu nemota?? Wannan ba abu bane mai yuhuwa dole muna bukatar sunan anguwansu ko kuma hotan ta, wani irin zufa ne ya keto ma m samir wanda gaba daya shi baiyi tunanin haka ba dan yana ganin yana zuwa nigeria zaiga mum dinshi toh taya ma zai ganta shida bai santa ba, bai taba ganin hotanta ba, hannunsa ya buga a dayan hannunshi tare da tashi ya kalli jawaheer yace zanje wajan dad dina ya fadamin sunan anguwan su, coz i only know her name, fita yayi da sauri, duk da dingishi yakeyi, koda ya fita security dinshi na nan tsaye suna jiranshi, yace ku dauko mota muje gidan dad, daya ne ya tafi sai gasu da mota har biyu ya bude ta farkon ya shiga, kai tsaye gidan dad dinshi ya kara nufa, a falo yaga dad din nashi a zaune idanshi yayi ja, yana ganin dan nashi ya tashi da sauri ya rungumeshi yana kuka, jikin m samir yayi sanyi tare da tausayin dad din nashi, cikin kuka dad din ya fara magana samir yanzu zaka gujeni koh? Zaka koma wajan mum dinka gaba daya, bazan bar hakan ya faru ba, dad din mum dinka yaki bani ita bai lura da irin son da nake mata ba, dan kawai ni farin fata ne bai lura da cewa duk musulmai daya bane, samir har yanzu ina son mum dinka sai yasa nake masifar sonka ban san damuwa a tare dakai in wani abu ya sameka inaji kaman mum dinka ya sama, plz dnt leave me, m samir ya danja jikinshi daka na dad din nashi ya fara magana kaman haka dad bazan taba gudanka ba kaine mahaifina nasan irin son da kake min amma dad plz ka barni inje inga mum dina koda once ne in my lyf, tasan danta bai mutu ba sannan tasan danta baya mugun hannu, na tabbata har yanzu bata cikin nutsuwa tunda danta ya barta, dad din kai ya girgiza yace ina tsoran kaje kaki dawowa son, m samir yace dad indai ka fadamin inda take one week zanyi kawai in ganta in dawo kasan inada wasa nan da sati biyu, dad din shuru yayi can ya nisa yace sunan anguwansu guyuk idan kaje kace a nuna maka gidan liman, murmushi m samir yayi najin dadi yace ashe kakana liman ne a anguwansu, dad din yace eh, sannan yace toh taya zaka kaida baka san kasar ba? Yace dad akwai wata yar nigeria tare zamu, dad yace wacece a ina ka santa? Murmushi yayi tare da fadin haba dad nifa duk wanda nace maka na sani ba abun mamaki bane, dad yace hakane amma ya akai tazo wajanka harta ganka kuka hadu kuka saba, dariya m samir yayi yace hadin Allah ne, dad din murmushi yayi tare da fadin ina son ganinta, m samir yace gobe zan kawo ta bari in sanar da minister zan tafi nigeria jibi suyi arranging dad din yace ok m samir tashi yayi tare dayi ma dad din sallama.



Tunda m samir ya fita jawaheer taji wani iri amma taji dadin sabawansu lokaci daya ido ta lumshe tana jin nishadi, burinta har yanzu bai wuce ace yau ya yarda zai aureta ba ita koda zai aureta baya sonta zata so haka, amma tunda yace a matsayin kanwa ya dauketa hakan ma abun alfahari ne a wajanta wasu ma signing dinshi suke nema su samu amma abun yaci tura ita kam gata gashi har kissing dinta ya taba yi wani murmushi ta saki cikin jin dadi haka har bacci ya dauketa.



Washe gari da safe tunda jawaheer tayi sallah asuba tayi wanka, ta koma bacci bata farka ba sai wajan karfe goma tana tashi ta kara komawa tayi wanka, tasa wata doguwar riga tare da daura karamin gyalen rigan, kitchen ta nufa ta hada tea dan gidan babu masu aiki tunda su mum suka tafi suma suka wuce, tana cikin shan tea din taji nocking tashi tayi ta nufi kofar tare da tunanin ko waye, tana bude kofar taga mutum a tsaye cikin riga da wando yayi mugun kyau ya hade hannunshi biyu yana kallonta tare da sakar mata murmushi ganin irin kallon da take mai yasa yazo kusa da ita tare da mata peck a goshi yace morning sis, firgit tayi ta fara kame kamen mai zata ce, ganin haka yasa ya kamo hannunta tare da shiga cikin gidan yace nazo ki rakani wajan dad dina yana son ganinki, ido ta zaro tare da nuna kanta alaman ni zai gani, kai ya daga mata tare da fadin yes ke zai gani, matsowa tayi kusa dashi tare da fadin Allah yasa ba laifi nayi ba? Yanda tayi maganan cikin sanyin murya ya bashi dariya hancinta yaja tare da fadin bakiyi komai ba kawai yana son ganinki ne, ajiyan zuciya tayi tare da fadin yaushe zamu? Yace yanzu, tace ok ina zuwa dakinta ta shiga ta canza kaya tasa jallabiya tare da yafa gyalen jallabiyan tayi kyau sosai sak balarabiya, ga kamshi dake tashi a jikinta falon ta nufa lokacin data fito ido ya kura mata yana murmushi ganin irin kallon da yake mata yasa ta danji kunya, kaman ya lura da hakan yace sis kinyi kyau tashi yayi ya janyota tare da daukansu hoto yana fadin bani da pics dinki dama, ya daukesu da yawa sannan yace ta bashi wayanta, mika mishi tayi yayi dialing no dinshi cikin nata, sannan ya kalleta yace bani no dinki na kasarku, murmushi tayi tare da fada mishi ya rubuta, sannan yace suje, motarshi suka shiga wacce cikin motan kaman daki seat din motar ma kanshi abun kallo ne, ga tv har biyu a manne a motan dayan camera ne amma sai yayi kaman tv duk wani abu da akeyi a waje yana kallo ta ciki, jawaheer ta kara tsorata dashi domin tasan lallai m samir ba karamin mutum bane lallai haduwansu hadin Allah ne, Allah ya amshi addu’anta dole ace ganinshi tashin hankali ne amma sai gashi Allah yasa ta ganshi cikin sauki, wani hawaye ne ya gangaro mata, jin hannunshi tayi akan fuskanta yana goge mata, lokaci daya ta dago kai suka hada ido, sunyi wajan minti daya suna kallon juna, kowa da abunda yake sawa a ranshi, shine yayi karfin halin kawar da idonshi tare da janyota jikinshi yana shafa mata bayanta yana fadin jawaheer mai yake damunki? Cikin wata irin murya tace ina farin ciki da Allah ya hadani dakai cikin sauki, lallai haduwa na dakai akwai wani boyayy…… Shuru tayi domin taji abun ya mata nauyi, yace inaji akwai me? Tace babu komai murmushi kawai yayi tsayawan motar ne yasa ta gane sun zo inda zasu, fita sukayi m samir ya kamo hannunta zasu shiga tare tayi sauri ta janye hannunta kallonta yayi ba tare da yace mata komai ba, ganin irin kallon da yayi mata alaman tambaya yasa ta fara fadin kar dad yaga ka riqeni zaice banda kunya, murmushi yayi sai yaji ta burgeshi sosai, haka suka shiga cikin gidan koda suka shiga ya nuna mata waje ta zauna gina ta fito suka gaisa ta kawo mata coffee jim kadan sai ga dad da m samir, dad ido ya kura mata ganin suna isowa yasa ta tashi ta tsaya a tsaye har dad ya karaso dad yace ta zauna mana zama tayi a dan takure tare da gaida dad din ya amsa cikin sakin fuska tare dayi mata tambayoyi akan iyayenta tana bashi amsa dad ya yaba da tarbiyanta sosai kuma yaji ta burgeshi dan haka ya saki jiki da ita yana ta janta da fira sosai, suna cikin haka wayanta yayi kara dubawa tayi taga mum ce dauka tayi bayan ta gaida mum cikin harshen hausa tace mum zan kiraki tare da kashe wayan, tana gamawa m samir yace ta tashi su tafi, wata leda ta ciro cikin jakarta ta ajiye a gaban dad tare da fadin dad kayi hakuri babu yawa, dad rasa bakin magana yayi lallai yarinyar nan tana da kirki tarbiya ladabi sannan al’adunta abun burgewa ne, dad yana ta mata godiya, har mota dad ya rakasu tare da fadin ta kulan mishi da yaro sannan in komai yayi dai2 shima zai zo nigeria haka suka tafi cikin jin dadi, suna mota m samir ya kira sunanta jawaheer ta dago suka hada ido tayi saurin kawar da ido, kara kiran sunanta yayi alama ta waigo ta kalleshi, kin waigowa tayi, ganin haka yasa ya janyota jikinshi suna hada ido ta rufe idanta wanda hakan ya bashi daman kallanta dakyau tare da aiyana abubuwa da dama a ranshi……




Gaba daya ya gama karema jikinta kallo yayin da duk wani sassa na jikinshi ya mutu wani irin yanayi ya shiga mai wuyan musaltuwa jawaheer tana da kyau na bugawa a jarida tana tarbiya wacce za’a so ace mutum ya sameta a matsayin mata sai dai kash baya jin sonta, idanshi ne ya sauka akan lebanta wanda kallo kawai zakai mata ka gane yana da laushi ido shima ya lumshe tunawa da ranan da yayi kissing dinta, bai taba shiga cikin wani irin hali mara misaltuwa ba kaman ranan duk da ba’a hayyacinta ya mata ba, inda tana cikin hayyacinta kuma da yardanta hakan ya faru da ya zaiji?…. Karan wayan jawaheer dinne yasa ta bude ido wanda shima yayi dai2 da bude nashi caraf suka kara hada ido wanda wannan karan sun kasa daukewa daka kallon junansu har wayan ya tsinke, shidai yasan baya son jawaheer sonia yake so amma yana jin wani abu a tare da jawaheer wanda bayaji akan sonia….. Karan kiran nata ne ya kuma katsesu wannan karan dauka tayi taga mum dinta, tace mum …… Mum tace inata jira ki kirani kinki kira ya maganan dawowan naki gobe? Kallon m samir tayi taga yana danna waya, tace mum gobe zan dawo amma bana tunanin abuja zan sauka,mum tace kaman ya ina zaki? Tace yola zani mum tace what?… Kina da hankali kuwa uban me zakiyi a yola jawaheer wlh zanyi mugun saba miki, ki tabbata gobe kin sauka a abuja inba hakaba zaki hadu da fushina wlh, tace mum pl…… Kit mum ta kashe wayan jawaheer kallon wayan ta tsayayi tana mamaki toh miye abun zafi dan tace zata yola, bama an barta tayi wata daya bane a nan ai bata ma kai wata dayan ba, jin hannun m samir tayi a kanta yana fadin what r u thinking sis? Murmushi ta saki tare da fadin babu komai, a hankali ya furta nagode da kyautarki da kika ba dad dina i really appreciate it, bata fuska tayi tace nima fa dad dina ne, yaji dadin magananta, domin yana son dad dinshi duk wanda yake son dad dinshi toh shima yana son shi, a haka har suka karasa gida gidanshi ya shiga itama ta shiga nata.



Yanzu karfe 8 na dare a kasar spain amma zukata biyu sun kasa sukuni domin kuwa ko wanne yana burin ganin dan uwansa, jawaheer tana mugun san ganin m samir cikin daren nan, haka shima ta gefenshi babu wacce yake burin gani sai ita amma shi a nashi ganin ya danganta hakan ne da daukinshi na zuwa nigeria kuma itace zata kaishi, tashi yayi yasa riga ya fita, tana kwance tana tunanin m samir taji ana mata nocking tashi tayi taga ita sai rigan bacci dai2 gwiwanta ta nufi kofa, tana budewa taga flower a wajan amma babu kowa, dubawa farayi ko zata ga mutum, amma bataga kowa ba dan haka ta dauki flower din tayi shuru lokaci daya kuma ta shiga ciki dashi, dan karamin kwalin data gani ta dauka ta fara karantawa kaman haka….. *Hey am hare missing you u r d best sister in d world* ido ta lumshe domin yanzu tasan waya ajiye mata wani irin farin ciki taji yana shiganta, wayanta taji yana kara da sauri ta nufi bedroom dinta ganin number din da yake kiranta yasa ta dauka da sauri amma saita tsinci kanta da kasa magana, muryanshi taji yana fadin kinyi kyau cikin night gown kiyi bacci da wuri kin san gobe zamu tafi, tace ok yanzu zanyi bada dadewa ba, murmushi yayi tare da fadin ok sis good night tare da kashe wayan, wani irin murmushin murna tayi tare da rungume wayar a jikinta sai kace m samir dinne a gabanta ta rungume haka, ranan bacci tayi cikin nishadi haka shima ta gefenshi.




Washe gari tun karfe 7 jawaheer ta dan ta makara da sauri ta shiga toilet tayi alwala sannan tayi sallah tare da neman gafaran Allah, bayan ta gama ta shiga toilet tayi wanka tasa wata doguwar riga, tare da hada sauran kayanta, tana gamawa kiran m samir ya shigo wayanta dauka tayi da sauri tana gaidashi amsawa yayi cikin murmushi tare da fadin zan turo a dauki kayanki 9 zamu wuce tace ok, basu dade da gama wayan ba taji nocking dan haka ta nufi kofan ta bude security dinshi ne suka shigo suka kwashe kayanta yayinda suka rufe komai na gidan da farin kyalle gudun kar kayan suyi kura tunda za’a bar gidan, bayan sun gama ta bisu suka tafi gidan m samir tare a falo ta ganshi shida dad dinshi cikin girmamawa ta gaida dad din nashi ya amsa cikin sakin fuska tare dayi musu addu’an samun nasara akan abunda zasu nema, fira suka farayi har 9 din yayi suka fito inda dad din m samir yake ta fadama jawaheer ta kula da m samir domin ya yarda da ita, tace insha Allah, da haka har suka nufi Airport, nan mutane suka fara ihu ganin m samir yayin daya rike jawaheer a makale dashi yan jarida nata dauka domin suna ganin budurwanshi ce duk yanda sukaso yace wani abu amma bai ceba koda suka zo shiga jirgi daukanta yayi ya daurawa sannan shima ya hau suka haura tana gaba yana binta a baya, daka shi sai security dinshi guda goma suka shiga jirgin aka rufe domin private jet ne, kusa da jawaheer ya zauna basu dade da zama ba masu aikin jirgin suka zo tambaya mai suke so, kallon jawaheer yayi yace ta fadi abunda take so, coffee tace kawai shima yace a kawo mai coffee din, kallon juna sukayi sukai murmushi wanda a dai2 lokacin jirgin ya daga domin zuwa nigeria……. Hmmmm ku biyoni dan jin yanda zata kaya ga m samir a nigeria


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *