JENNIFA CHAPTER 9
Hon yayi me gadi ya bude musu get ya shige gidan sai yanxu ya samu nutsuwa tun haduwarsu da yan fashi shikam haisam xuciyarshi ta tafi kololuwar tunanin ya akayi Jennifer taxo Dubai sata ?? Wacece ita ? Me takeyi a gidansu Sam hankalinshi baya tare dashi bude kofa yusuf yayi ya fito daga motar yana yiwa haisam wani irin kallo kafito mana haisam koda yake kaika Sani inma anan xaka kwana cikin motar ya wuce cikin gida yana mitar halin da haisam ya sashi bin Yusuf din yai da ido yana girgixa kanshi baka San mmkin dana ke cikiba nafika tashin hnklin da kashiga baikai Wanda nashiga ba yanxun nan kwakwalwarshi ta rude yarasa wanne irin tunani xaiyi waya ya janyo daga aljihu ya kira zahra ba ta dade tana ringing ba ta daga muryarta adashe da alama bacci takeyi kiran wayar ya tasheta arikice yake tambayarta ……..zahra ina jennifer da mmk ta amsa da bansani ba ya haisam me ya faru ??? No ! No ! Dubomin tana cikin gidan ta mike daga kwamciyar da tayi araxane menene wai ya haisam kafa dagamin hnkl da sauri ya canza voice dayin dariyar yake oh ! Zahra bakomai ina son sata wani aikine tayi ajiyar xuciya hade da yin dariya haba da katashi hankalina ta fito daga dakinta tai bangaren su jennifer a hanya ta ci karo da Sa,a ke xo ta kira ta a ladabce Sa,an taxo hade da sunkuyawa ina jennifer ? BATANAN TUN JIYA kaninta ne ba lfy ok ta katse Sa,an jeki kawai shima haisam din kashe wayar yayi dan yaji amsar da Sa,a ta bawa zahra batanan tun jiya baiji karashen zancen ba gumi me xafi ya rufeshi jikin shi ya fara rawa me ya ke shirin faruwa ?? Meyasa tahana akashe shi ?? Tabbas yasan ya kuntata mata dafe kai yayi arikice yarasa wani irin tunani xaiyi munafuka !! ya fada axuciye Allah ya Toni asirinki ya jingina jikin kujera xuciyarshi na ingaixashi Allah Allah ya keyi gobe tayi ya dawo 9ja yaji dalilin zamanta gidansu
Daren ranar baiyi baccin kirkiba gaba dayanshi arikice yake haka yaje meeting din batare da ya fahimci me aka tattauna ba da kyar ya saita nutsuwarshi ya fahimci kadan suna gama meeting din ya fito da gaggawa yai airport dan ya kagu yaxo gida ya tahumi munafukar yarinyar nan azzaluma macuciya barauniya
10:00pm ya iso 9jaa sai wajan 11 ya isa gida dare yayi haka yaita sintiri da ga bangarensu xuwa cikin gida da kyar bacci ya kwashe shi
Tunda wuri yadda ta saba ta fito dora musu break fast sbd kwananta 3 ba agidan ba tana wajan jinyar David suwaiba ta tarar a kitchen din suka yiwa juna murmushi suka gaisa suna girkin suna hira kwatsam suka ganshi akansu daga shi sai dan gajeran wando dama al,adar mazan kenan yawo da kana nan kaya kowanne irine da sauri ta kalleshi atsorace take gaishe shi ya kura mata ido yarasa tana ina xai fara tambayarta sbd xuciyrshi da take akufule miko min tee ya fada yana huci da sauri ta bude flask ta xubo masa a cup ta mika masa ya kalli tee din yana jujjuyashi ahannunsa ya watso mata shi cikin zafin nama ta goce duk da haka sai da ya samu gefen kafadarta ta kwalla kara sbd xafin da taji ya nuna ta da yatsa sai dai yakasa cewa komai sai girgiza kai kawai yake yakaiwa iska naushi da hannunsa yai tsaki me karfi ya bar wajan da sauri hade da ajjiye cup din hannunshi nesa da kitchen din su ya xauna yana tunanin hanyar da xai bullo mata abinda yabashi mmk dakiyar daya ga tayi cikin gwaninta da yaudara kamar basu hadu da ita a Dubai ba duk yadda akayi yarinyar nan bakar shedaniya ce bai kamata kai tsaye ya damketa ba kamun kazar kuku ya kamata yai mata xaibar wannan a cikinshi cikin lokaci kalilan zai mata mugun kamu binciken wacece ita xai farayi ya alkawarta sai yago dalilin zamanta cikin gidansu
Kuka takeyi sosai suwaiba na bata hkr kiyi hkr Jennifer wayeshi ? Cikin kuka take bata amsa dan gidan nan kanin ya mahboob ranar da aka kawoki ya tafi Dubai dama tuntuni baya kaunata suwaiba dan kawai addininmu ba daya ba ta kuma fashewa da kuka kiyi hkr Jennifer kin San kowanne kalan mutun da halinsa nikaina naga kiyayyarki sosai a kwayar idonsa kuma na fuskamci bashi da tausayi ko imani dan me imani baxaiyi abinda yayi ba bakomai suwaiba komai yana da lokaci addua suwaiba tacigaba dayiwa jennifer tana tofawa a inda ta kone inshaa Allah wajan bai tashiba kiyi hkr ki koma daki daki zan karasa girkin kai jennifer ta girgixa kibari mu karasa tunda kin min addua Allah ya saka miki suwaiba na fuskanci kina da adalci da daraja dan Adam in sha Allah xakiyi albarka arayuwarki dan mamana tana fadamin mutane masu kyawawan hali da daraja muatane yanuwansu masu adalci da biyayya ga ubangijinsu suna albarka arayuwarsi kin dace dan wannan halin mamana ta fadamin baiwace Wanda sai mai rabo ubangiji yake bashi murmushi suwaiba tayi hade da kura mata ido cikin xuciyarta tana adduar Allah yasa kina da rabon musulunci Jennifer kalanki da nutsuwarki da kamanninki irin namune Allah mai iko tana mamakin kasancewarta cikin wannan halin Allah y shiryaki Jennifer shirin addinin musulunci bayan sun gama suka jeresu a dining sannan suka koma daki sukayi nasu break fast din suna hira jefi Jefi Jennifer na duba konewar da tayi abinda ya bata mmk kokadan koniyar bata tashi ba ta kalli suwaiba tana murmushi suwaiba kinga ikon Allah tafashash shan ruwan xafine fa amma kinga koniyar bata tashi ba suwaiba ta saki fuska baxata tashiba jennifer na miki adduar annabi Ibrahim alaihis salam lokacin da aka jefashi cikin wuta duk irin wutar da ta tabaki kowacce irice in kikai saurin yinta kika tofa ta tofa yanda bata illata annabi Ibrahim alaihis salam babu abinda xatai miki ko da yarone ya kone shiru Jennifer tayi tana tunanin wani abu Wanda babu Wanda yasan menene ciki kuwa har da ni ummee🤔
1:30pm suka gama lunch suka kai musu dining sannan suka dawo daki suwaiba ta wuce toilet tayo alwala ta tada sallah Jennifer na satar kallonta ta fuskanci suwaiba tana da ilmin addini daidai gwargwado sannan tana aiki dashi dan akwai son yin ibada akan lokaci tanayin komai nata anutsu sabanin sauran yan aikin su Sa a da hadiza da ko shiga harkarta basayi tunda suka San wacece ita novel ta janyo na Hausa tana dubawa na suwaiba ne tagane tana son karance karancen litattafan Hausa in dai sungama ayyukamsu ta idar da sallar ta dauko musu nasu abincin Jennifer ta sakko tasa hannu tana kallon suwaiba tai addua sannan ta fara cin nata bayan sun gama ma sai da tayi abin ya birge Jennifer sallamr hadiza sukaji sannunku yanmata masu hadin kai to kuxo masu gida suna nemanmu a babban falo da murmushi suwaiba ta mayar mata da to yanmata marasa hadin kai muna xuwa dariya Jennifer sukayi ita da hadizan sannan ta bar dakin tana mitar wai suwaiba ta fiya mai da kurji ciwo
Gaba dayansu ma aikatan gidan suka taro a babban falo dady da Momy ne a ciki kusa da shi ya khaleel ne hnklinshi akan waya yana danne dannenshi Jennifer tarasa me yake dannowa da kullum baya gajiya tun xuwansu wajan babu wacce ya dago kai ya kalla cen gefe zahra ce rike da lpad itama tana game Rubayya hnklinta na kan tv sarkin kallon series films
Yayana sunnunku da xuwa daddy ya fada da sauri dukansu suka kalleshi cike da mmkin kiransu da yayi da yayanshi ya aiki ? Ya tambayesu cikin hadin baki suka amsa da alhamdulillah babu wata damuwa dai ko ya kuma tmbyr su babu damuwa dady to masha Allah na tarakune sbd jibi dukanmu nida iyalina xamuje umara saudiyya kowacce xata koma gidansu ajibin sai mundawo dan 2 weeks kadai xamuyi ma aikatan mu maza su zasu kula da gidan banda Ku mata yaxaro kudi masu yawa yararraba musu sukayi godiya sosai sannan ya sallamesu kowacce acikinsu murna take banda jennifer da take cikin damuwar rabuwa da yan gidan suna fitowa sukai karo da mahboob ya harareta suwaiba tasaki hannunta tai gaba ita kuma ta tsaya tana kallanshi itama ..kinsan fushi nake dake ?? Ya tambayeta tayi dariya a a Yaya mahboob bansani ba shiyasa na fda miki dan na fuskanci bakisan ina fushin dakeba xo muje garden hira xamuyi ta xaro ido aikinfa ? Baxa kiyi ba ya bata amsa yana kallonta ta kwabe fuska kar nabar suwaiba shiittt ! Ya katse ta hade da Sa yatsansa daya abakinshi muje aikinta ne itama tabi bayanshi bata soba akan dadduma suka xauna cikin grass idon shi akanta Jennifer menene yake damunki kwana 2 dinnan naga kamar kina cikin damuwa ?? Shiru tayi tana tunanin amsar bashi dan tasansa da bin kokwkwafi hakane David ne bashi da lfy yana fama da sicler idan ta tayar masa hnklinmu na tashi duka sbd muna son yaron rashin lfyr nasa yana takura masa Ayya! Ya fada cikin tausaya kuyi hkr kuyi masa addua Allah ya bashi lfy amin ta fada jibi xamu tafi umara naso ace tare muka tafi wani daliline me karfi yasa baxa mu tafi tareba amma next in shaa Allah tare xamu tafi murmushi tayi dan tasan dalilin shine kasancewarta Kristan ne hira sosai yai mata cike da tsari kasancewar Sa dan tsara zance ya dauko wayarsa sukayi photo tare kala kala dakyar ya bar ta tashiga gida yna fadin shi baigaji da hirar ba tana shiga cikin gidan taci karo da ya khaleel a tsaye hannuwansa cikin aljihu ya jefa da kallon da ya saba yimata Wanda takasa fassarashi
Saudiyya
Sun sauka lfy kwanansu 3 da xuwa haisam yana masallaci yna dawafi bayan an idar da sallar axahar ya fito dan yaci abinci yana sauka daga lifta karf idonshi ya sauka akanta tana sanye cikin dogowar riga Arabian gown suna tsaye da wata mata fara irin farin 9ja me kiba babbar mace mgn suke tana dariya ta riko hannun matar ta sumbata sukayi hugging din juna sannan tabar wajan da sauri yana tsaye ya kasa mgn mmk sosai da firgici ya kamashi da sauri yabi bayanta kafin ya cimmata tashige cikin mutane bat tabace masa da sauri ya dawo inda yabar daya matar batanan ya bige kanshi hade da fadin oshcc!! Meyake faruwa ne kasa ya dunkule hannunsa yana dukan tafin hannunshi da shi da gudu gudu ya bi wani wajen karaf yaci karo da wata ta hnkdashi hade da fadin baka da hnkl ? Cikin tsawa da sauri hnklinshi ya dawo kanta ya zaro ido yana mata wani irin kallo tayi tsaki tana masa kaskantaccen kallo mahaukaci ne kai ?? Irinkune sakarkaru da kuke tafiya bakwa kallon gabanku mahaukaci kawai tafada tana cigaba da tafiya ta dago yatsanta tana karkada masa nunin gargadi bai farga sai da takusa ficewa da ga masallacin sannan ya furta jennifer !! Akufule yabi bayanta da sauri 15/16