KAINUWA CHAPTER 6

KAINUWA

CHAPTER 6

Shiru tai tana tunani, kayan da aka aikomai dashi wanda ke kan gado ya d”an kura ma ido alamar tunani kafin ya dawo da kallansa kan mahaifiyarsa yace ” Umma zan shirya.”

Kai ta d”aga sannan ta mike ta dafa kafadarsa d”aya tace ” duk hukuncin da ka yanke ina tare da kai dan kuwa na tabbata d”ana bazai bani kunya ba.”

Bata jira amsarsa ba tai waje.

Abu Turab ya shirya tsaf ya fito daga d”akinsa, inda yake zama ya wuce dan bayin sa su nad”amai rawani.
Tunda ya shigo suke kallansa dayake sunsan baya gani yasa suka kura mai ido kowa da abinda ke ransa nan fa suka dan fara gulma da ido wanda duk yana ganinsu.+

Rawanin dayake so ya basu nan suka nad”amai, ya sa takalmi yace su tafi.

A kofar gida yaga wani bawa rike da doki yasha ado, bawan na ganin Abu Turab ya taho da gudu ya dan rusuna yace ” Ranka ya dade ha doki nan inji magajiya.”

Murmushi yai sannan yace ” ayya? Ya za”ayi? Gashi na riga na aikama Barga akan ya aikomin doki sai dai ma maida wannan gun Bargan gudub kar a maka fada akan rashin isar da sakonka da wuri.

Bawan yai saurin sunkuyawa yace “Tuba nake D”an Sarki.”

Abu Turab yai murmushi sannan yace ” ba haushi naji ba ina dai gujema fada ne.”

Kallan d”aya daga cikin bayinsa yai yace ” sanar da Barga ya baka dokina.”

Cikin mamaki yace ” Ranka ya dade ai ba”a mai…..”
Katseshi yai da cewa ” hakan nakesansa.”

To, abinda ya fada kenan yai saurin fara tafiya.
Bai dade ba sai gashi da rike da dokin Abu Turab ya hau.

Sai daya bari Sarki zai fita hawa sannan ya shiga cikinsu, bai bari sun ganshi a gida ba.

Tunda ya shiga cikinsu kuwa ake kallansa, kowa mamaki wannan wanene haka?

Dama tawagar Abdulmajid ya shiga, dan kara gudun dokin yai ya matsa bayan Abdulmajid kadan.

Nan fa kowa ya fara kallansa, mutand sai juyowa suke ana nunashi da hannu, ganin yanda ake nunuwashi yasa Abdulmajid ya tsargu ganin saitinsa ne.

Kallan na kusa dashi yai yace ” menene?”

Juyawa yai shima, cikin mamaki ya kalli Abu Turab sannan ya matso inda Abdulmajid yake yace ” Yarima ai kaninka ne yake bayanmu.”

Murmushi yai dan dama yasan da zuwan nashi, sunyi shiri sosai dan kuwa d”inki Magajiya tasa aka mai irin wanda zai saka a wannan ranar, wanda hakan sab”awa ne ga al”adarsu ace anyi anko da Sarki balle kuma bai sani ba.

Ya sake murmushi tunawa dayai dokin ma kwalliyar irinta Sarki sukasa akamai.

Sai yanzu ya fahimci dalilin dayasa ake nuna Abu Turab.

Sai da sukaje inda Sarki zai d”an tsaya kafin ya juyo alokacin ne Abdulmajid yaga yanda ake ta nuna Abu Turab, dariya ya kunshe ya juyo dan ganin yanda ma kayan yamai.

Sai dai me????

Idanu ya zaro sosai cikin tsananin mamakin abinda idanunsa suka ganemai, me ke faruwa? Menene hakan?

Shi kansa Sarki ya fahimci yanda mutane suke nune nune, hakan yasa ya tambayi Galadima yace ” meke faruwa?”

Nan Galadima yasa aka bincika.
Matsowa yai wajen kunnen Sarki ya rad”amai.

STORY CONTINUES BELOW

Ransa ya b”aci sosai nan ya bada alama akan su juya.

Haka sukabi har suka koma gida.
Abdulmajid kam sukuku ya karasa wannan hawan zuciyarsa tana ta san taga wani irin hukunci Mai Martaba zai yankema d”an lelen nasa.

Suna isa akazo aka sanar ma Abu Turab akan Mai Martaba na nemansa a fada.

Yasan za”ai haka shiyasa ya sauka zuciya d”aya ya bada dokinsa ya nufi fadar.

Dayaje zai shiga sai ya ajiye sandarsa sannan ya shiga ciki.

Zama yai irin zaman gurfana d”in nan, Mai Martaba ya kalli dumbun manyan mutane masu mukamin sarauta dake gun, sai dai wannan karan yazamarmai dole duk san da yakema d”an nasa ya mai tambaya a nan Saboda yau a matsayin Sarki yake ba uba ba.

Abu Turab ya kalla fuskarsa a had”e sosai yace ” Me zaka fad”a game da wannan shigar ta cin zarafi dakai?”

Nan fa aka kara kallansa, Abdulmajid wanda ya shigo yanzu yai murmushin jin dadi tare da zama.

Abu Turab yai shiru baice komai ba, kallansa Mai Martaba yai yace ” in har bakada amsa akan hakan to lalai ne ka fuskanci hukuncin masarauta.”

Ya fad”a tare da kauda kai.

Abu Turab kansa na kasa yace ” Tuba nake in har shigar danai laifice a tsarin masarautarmu.”

Nan fa kowa ya kara kallansa, rigace ta shadda wacce ta tsufa kana ganinta kasan tsohuwace, sannan na babbar riga a jikinsa ya maka wani tsohon rawani, wannan shigar ko a cikin gida ba yinta yake ba balle a gun hawa cikin jama”a.

Hisham ya kalleshi yace ” kanasan kace shigarka batada laifi kake nufi ko me?”

Abu Turab ya kalleshi fuakarsa a sake yace” kuskure nane sai dai ina fatan amin afuwa.”

Cikin takaici Mai Martaba yace ” Abu Turab! Nasan ba gani kakeyi ba dan haka laifin bayinka ne zasu amshi hukuncin barinka kayi wannan shigar dolene su fuskanci hukunci mai tsauri.”

Abu Turab ya kara kasa dakai cikin kalar tausayi yace ” ko wani hukunci ne amin domin kuwa sun bani kayan da ya kamata insaka sai dai daga laushin kayan da yanayin su yasa nasan ba nine na dace da kayan ba, sai dai hakan baisa na musa ba na saka kayan dan kuwa bansan ya suke ba da idona, ka gafarceni Mai Martaba ina fitowa aka sanar dani kayan irin naka ne sak, sannan dokinma irin kwalliyarka ne dashi, wannan yasa na hanzarta na janyo kayan dabansan ya suke ba na saka sannan na aika Barga ya bani dokina nasa amaida mai waccan.”

Jin kalamansa lalai sun ba kowa mamaki, Abdulmajid kam cikin tsoron kar asirinsu ya tuno yai saurin cewa ” menene shaidarka ta fadar haka? Kana tunanin ko me kace yarda zamuyi?”

Abu Turab wanda ana cemai Mai Martaba na kiransa ya tura Salau(mai kula dashi wanda suka fi shiri) akan ya d”aukomai kayan nan,sannan ya aika Barga yazo.

Nan yace ” Salau!”
Daga waje Salau ya amsa da karfi.

Nan ya shigo rike da kaya.
Abu Turab yaba shi kuna ya ware kayan anan kowa ya gani, to fa!
Nan aka fara magana kasa kasa.

Abu Turab yace ” ka gafarceni Ranka ya dade ba gani nake ba bare nasan da haka.”

Barga! Nan ya amsa shima daga waje sannan ya shigo.

Abu Turab yace ” wani irin kwalliya ne da dokin danasa a dawom dashi?”

Nan Barga ya musu bayani.

Mai Martaba cikin tsananin mamaki yace ” wanene ya aikoma da kayan da kuma dokin?”

Abu Turab yad”an sadda kai tunowa yai da yanda suka karashe da mahaifiyarsa.

Harta fita ta dawo tace ” Abu Turab! Me kake san yi dan hankalina bazaj kwanta ba sai naji.”

Ya kalleta yace ” bazansa kayan ba haka kuma bazan hau dokin ba, na tabbata akwai wani makirci akasan wannan kayan da dokin zanje inga wani irin makircine sannan insan abinyi.”

Muryar Galadima ne ya katseshi da cewa ” kayi shiru.”

Cikin Abdulmajid da Waziri ne ya d”ebi ruwa, tsoro da fargaba ya kamasu, duk suka runtse ido saboda tsoron abinda zai ce.

Abu Turab ya d”ago yace ” ina wannan wanda baya ganin zai sani? Tuba nake ranka ya dade sai dai nikaina bansani ba andai aiko ne ance ga kayan dazansa.”

Mai Martaba ransa a b”ace yace “dolene abinciko wanda yai wannan laifi dan kuwa bazan laminci irin haka ba.”

Abdulmajid ya kurama Abu Turab ido lalai ba shakka yaran nan da saninsa.

Suna fitowa ya bi Abu Turab zaimai magana, ya tsaya kusa dashi yace ” kai!”

Abu Turab ya kalli gefensa sannan yad”an matso kadan yace ” karka damu nikaina bansan waye ya kawo kayan ba.”

Yana fadar haka ya juya suka tafi.

Mamaki ya kama Abdulmajid ya bishi da kallo, kallan na kusa dashi yai yace ” na fadamai dalilin kiran danamai?”

A”a sunansa kawai ka kira.

Abdulmajid yai dan murmushi yace ” wasa farin girki.”

Abdulmajid da sauri ya karasa bangaren Magajiya, ko salama baiyi ba ya fad”a, tana zaune tana duba wasu kaya da tasa aka kawo mata, kayan mata ne aka d”inko kala kala.

Jin shigowar mutum yasa ta d”ago dan ganin wanene.
Abdulmajid ne ya karaso inda take ya zauna ransa a b”ace.
Kallansa tai yace ” Yarona lafiya ko sallama babu.”+

Ya kalleta yace ” Umma da alama mun sakema yaran can dayawa.”

Ta kalleshi tace “bangane ba? Ni na dauka zakazo cikin murna kamin bayanin abinda ya faru da yaran can, shiyasa naki yardama kowa ya sanar dani nafisan inji daga bakinka.”1

Abdulmajid yai dan ajiyar xuciya yace ” Ai baisa kayan ba, da alama mun sakema yaran nan dan yana makaho shiyasa har yake ganin zai iya takara damu.”

Magajiya tamai kallan bata gane ba, nan ya kwashe komai ya gaya mata, wani sansanyan murmushi ne yaga ta saki ta kalleshi cikin murmushin tace ” shine kake wannan fushin?”

Kallanta yai cikin mamaki, ta sake wani murmusawa tace ” yaro man kaza, karka badani mana Yarimana.”

Kallanta yai baice komai ba, tace ” yaushe ma aka auri uwarsa, yaushe shima aka haifeshi, yaushe aka daina mai tsarki da wanka? Yaushe ya san kansa?”
Ta sake wani murmusawa tace ” ko kamanta haryanzu baisan kalar fuskarsa ba bare yasan na uwarsa bare kuma tamu?”

Abdulmajid ya fahimceta, dariya yai sannan yace “a maida anin kan uwarsa?”

Magajiya tace ” in har Mai Martaba ya nemi jin ba”asi to ka tabbatar komai ya koma kan Uwarsa.”

Dariya ya saki yace “Allah yabarmin ke Umma Magajiya.”
Murmushi tai tace ” yaune isowar Khadija fa.”
Ya kalli kayan yace ” au shiyasa naga kaya kala kala a gabanki? Ashe “yar d”akinki ce zata dawo.”

Cikin jin dadi tace ” daurewa kawai nake na rashinta, amma kaga yanzu tunda Inna Lami take akwance sannan ga shi ina tunanin turawa takarda had”in aure zuwa masarautar Kano shiyasa nakesan ta dawo.”

Kallanta yai yace ” auren wa?”
Tace “auranka mana dolene in nemi masarauta mai karfi in had”a auranka saboda nan gaba ko menene ba wanda ya isa tunanin saukeka daga matsayinka ko kwace ma mulkin ka.”
Kallanta yai yanasan magana amma ina bazai iya ba, dan bai taba mata musu ba, kayanta tacigaba da dubawa.
Jiki a sanyaye ya mike yai waje, shikam bai shirya wani aure yanzu ba amma bai isa cewa komai ba, a tsarinsa yafisan yai auren farinsa auren soyayya tunda dai yasan dama shi dolene yai mata dayawa, yana tunanin ina shi ina soyayya da wani bayan an riga an mai aure?

******
Washegari.

Yana fitowa daga d”an nesa ya hangota tana tafiya, tsaki yaja yace ” sai na takama yarinyarnan birki.”
Kallan na bayan sa yai yace ” kiramin yarjnyarcan, ina bangarena.”

Ya juya zuwa bangarensa.
Yana shiga yaga an kawo mai abinci ga bayin da suka kawo nan a tsatsaye suna jiran isowarsa.
Zama yai baice musu komai ba, umarni ne ya basu dolene in suka kawo mai abinci sai yaci yaji yamai kafin su tafi.

Da sallama ta shigo fuskarnan tata a d”aure tamau, shima fuskarsa ya had”e bai amsa mata ba ya d”ago ya kalleta.
Kanta na gefe, jitai yace ” duk ku fita kubarni da yarinyarnan inasan magana da ita.”

STORY CONTINUES BELOW

Nan sukai waje, itakam haryanzu kanta na gefe.
Kallanta yai yace ” ke baki iya gaisuwa ba?”
Bata tanka mai ba.
Ya kalleta yace ” zo ki zubamin abinci, tunda naga alama uwarki bata isa dake ba, kullum kina hanyar gantali.”

Wani mugun kallo ta bugamai sannan tace ” ko karuwanci nakeyi meye naka a ciki?”

Hannu taga ya had”a ya fara tafi sannan ya mike ya tako zuwa kusa da ita, idanunta ta kawar tace ” malam lafiya?”

Ganin yanda ya matso daf da ita yasa ta fara matsawa, haka ya dinga matsowa har takai jikin bango.
Hannu yasa a jikin bangon ya tareta yace ” abinda kukeyi kenan da makahon?”

Kallansa tai ta had”iyi yawu sannan ta daure tace ” yaushe raban ma daka ganni a gidan? Wai ni mena tsolema ne?”

Dariya yai yace ” na tsani duk wanda yake san makahon can, balle ke harda dadin rashin kunya.”

Sauri tai ta sulale ta kasa ta juya da sauri zata fita, hannunta ya fizgo da karfi, ya dawo da ita gabansa yace ” me? Bakyasan kwalliyar da kikai ta goge ne ba tare da kinje gunsa ba?”
D”agowa tai takalleshi cikin takaici.
Ya saki murmusawa yace ” ahh ya zakiyi? Gashi kuma baya gani bare ya yaba.”

Hannunta tashiga kwacewa, ganin yaki saketa yasa tace ” wlh zansama ihu, kasani sarai kuma zan iya.”

Kafad”a ya d”aga mata alamar ko a jikinsa yace ” Go ahead.”

Lab”anta tad”an ciza sannan ta kalleshi ta kara hade rai tace ” malam sakeni ko?”

Kallanta yai ba alamar yana da niyyar hakan.
Ta kara cewa Malam sakeni ko?”
Yace “Mairo kenan, inhar kinasan in kyaleki dolene ki daina zuwa gun waccan yaran ki dinga zuwa guna duk da nidin bawai sanki nake ba ko burgeni kike ba sai dai inasan yanayin fuskarki da shape na jikinki.”

Iska ya hura kad”an a bakinta tace ” hakan kadai kakeso.”
Gira ya d”aga mata alamar eh, yamai murmushi sannan tace ” sakeni to, indai wannan ne kacal.
Nan ya saketa yana kallanta, tace ” nagode sai anjima.”
Zai sake magana yaga tayi waje.

Hakoransa yad”an had”e yace ” na tsani yarinyar nan, bawanda ya rainani kamarta.”

********

Mairo kam tana fita ta gyara mayafinta tafiya kawai take amma gabanta sai fad”uwa yakeyi, haka ta isa b”angaren Basira.

Bayan sun gaisa ne, Basira ta kalleta tace “Mairo yanzu sam kin daina zuwa, yauma sai dana aika kizo sannan kika zo.”

Kanta na kasa batace komai ba, kai kadauka irin salahan nan ce.
Basira tace ” dama so nake ku fita da Abu Turab gari, na tabbata yau yana bukatar iskar cikin gari bawai ta gidan nan ba.”

D”agowa tai tanasan tambayarta abinda ya faru, sai dai bazata iyaba.

Tace ” To.”
Basira ta kalleta cikin kauna tace ” bari a kirashi.”
Ta kara cewa to.

Abu Turab yana d”aki a zaune yana karatun alqur”ani, nan aka sanar dashi sakon Basira.

Mikewa yai ya bud”e drawer din da kayansa ke ciki dan canzawa.

Kurama d”ankwalim dake ajiye a gaban kayan ido yai, baice komai ba sai dai ya dade a tsaye yana kallan d”ankwalin.
Kafin ya jawo wani kaya,har ya rufe kofar ya bud”e ya janyo d”ankwalin yardashi yai a kasa sannan ya sura kayansa, ya kara kallan kasa sannan yai waje.
Ya rasa dalilin dayasa yakejin zuciyarsa ba dadi bayan ya yarda dankwalin, sai dai menene dalilinsa na ajiye kayan yarinyar da tunda ta tafi ko sakon gaisuwa bai kara samu ba? Wata zuciyar tacemai wa zata aika? Bayan duk ba sanka suke ba? Shikam ya rasa me yasa yakejin zafinta bayan ya tabbatar ba laifinta bane.

Haryakai kofa ya koma d”aki ya d”au d”ankwallin ya maida cikin drawer din sannan yai waje.
Yana shiga yaga Mairo a zaune, karasa wa yai ya kara gaida mahaifiyarsa.

Mairo ta gaisheshi ya amsa.
Basira tace ” tunani nake ko zaka fita gari yawo.”
Kallan gefenta yai yace ” gari kuma?”
Tace ” eh, kullum kana gida a zaune shiyasa nai tunani ko zaka zaga gari dukda ba gani zakai ba amma ina ganin zakaji dadin hakan.”

Kai ya jinjina alamar gamsuwa yace ” bari na sanar ma…..”
Da sauri tace ” ku fita kai da Garzali da Mairo kawai.”
Kallanta yai yasan me take nufi, dan dama ya dade da sanin so take wata alaka ta shiga tsakaninsu da Mairo.
To.
Abinda yace kenan ya mike.
Mairo itama ta mike ta musu sallama.
Garzali na bayansa ita kuma tana d”an kusa dashi kadan, shikuma yana tafe rike da sanda.
Sun shiga gari ta gefen ido yana ta kallan yanda mutane suke haba haba, ba shakka wannan shine burinsa ya zauna cikin mutane kamar yanda kowa yakr yi bawai gidan sarauta ba.

Jitai yace ” Mairo yanzu anbar rigima dai da alama.”
Kallansa tai tace ” lalai Yaya sai kace wata yarinya?”
Yace ” ah lalai ashefa kin girma.”
Baki tad”an turo tace ” shekarata fa 1.”

Yace “16? Amma bakiyi aure ba?”

Fuska ta d”an had”e tace ” ba mijin ne.”

Ya d”an juyo kadan yace ” wanda rannan ya biyoki fa?”
Tsaki tadan yi tace “rashin aikinyi ne yamai yawa.”
Yace ” da alama dai akwai wanda kikeso ne shiyasa.”

Kallansa tai a ranta tace “sosai ma.”
Ta d”auka a zuciyarta ta fada sai jitai yace ” da gaske?”
Kallansa tai tace ” wasa nake.”
Murmushi yadanyi yace ” kar ki tsaya ruwan ido ki samu saurayin da yake sanki ki aura, bawai wanda ke kike so ba.”

Kallansa tai zuciyarta ba dadi tace ” kamar yanda haryanzu baka manta da Khadija ba?”

Tsayawa yai cak, ba tare da ya juyo ba, matsowa tai inda yake tace ” karka damu Ya Turab ba wanda yasan hakan, ko ince ba wanda zan fadawa.”

Bai san sanda ya kalleta ba, yace ” me kike nufi? Ko kin tabaji da bakina na fada miki haka?”

Murmushi tamai tace ” wani sa”in sai inga kamar kana kallona.”
Fuska ya had”e ya juya kai yace ” amsarki nake jira.”
Daurewa tai tace” a lokacin da Khadija ta tafi bafa yarinya bace ni yaya, ban manta abinda ya faru a lokacin ba, sannan duk sanda muka zauna dakai zancenka kenan khadija tace kaza, ko khadija tayi kaza, a lokacin bansan me hakan yake nufi ba, sai dai daga baya na fahimci meke faruwa.”

Abu Turab ya juya yace ” banasan wannan maganar, sannan ni khadija banaji ko ganinta ma in nai zan iya ganeta.”
Yana kaiwa nan ya cigaba da tafiya.”

**********

Tunda suka taho a hanya take kwance kamar mai bacci sai dai zuciyarta fal take da tunani kala kala, Ya Turab!
Abinda zuciyarta take fada kawai kenan, anya zata iya ganeshi? Dan ita kamanninsa ma harsun fara bace mata.
Ba shakka tasha wuya sosai bayan komawarta kano, sai datai sati biyu tana zazzabi zancen ta kenan a maida ta gun Ya Turab kai kace shine ya haifeta.

Yaran gidan har tsokanarta sukeyi suke cemata Aunty Turab.

Duk sanda zatai addu”a kafin ta fara rokon komai sai tamai addu”a, ita har mamaki ma take da haryau bata taba mantawa da addu”ar ba in har tai sallah.

Ko zai ganeta? Dan wani zuwa da Abdulmajid yai shekarar data wuce data tambayeshi Abu Turab cemata yai wai soyayya suke da Mairo, sannan gwara ma ta cire wani lamarinsa, dan shi kam ya ma manta da ita.

A da bata taba tunanin wai san shi take ba, itadai a matsayin yaya ta d”aukeshi sai dai ganin ta kasa cireshi a ranta yasa Aunty Nana wato babbar yarinyar gidan ta fada mata soyayyace bawai “yan uwantaka ba.”

Kanta ta kara kwantarwa jikin motar, ya zatayi in har yama kasa ganeta?
Dama gashi iyayenta nema suke su had”ata da wani yaron babban d”an siyasa a garin kano yake.

Ajiyar zuciya tai sannan ta kara lumshe idanta.

A hanyarsu ta dawowa ne wani ya biyo Mairo da gudu, yana kwalla mata kira.
Abu Turab yanaji ganin taki tsayawa bare amsawa yasa shima bai tanka mata ba, sai dayazo daf dasu yanata haki na gudu yace “Mairo kina jina?”
Kallansa tai tace ” nibanji ka ba, lafiya?”
Ta fad”a tana kallan Abu Turab daya cigaba da tafiyarsa.
Leda ya miko mata yace ” gashi.”
Cikin fada tace ” nameye shi kuma?”
Kai ya sosa yana shirin yi mata magana, yana d”agowa yaga bata gun, kallanta yai yanda take dan sauri.

Da sauri itakam ta karasa gun Abu Turab tace ” Yaya ba jira?”
Yace ” har kin gama zancen?”
Tace “zance kuma?”
“ki koma dan muma gida zamu wuce, sai da safe.”
Abinda ya fada kenan ya cigaba da tafiyarsa.
Turus tai agun idanunta suka d”an ciciko, meyasa Abu Turab baya ganin yanda ta damu dashi?+

Shikam ko a jikinsa har suka isa gidan.
Yana shiga daga bakin gate yaji ankira sunansa.
Yasan muryar waye, fuskarsa yad”an saki kadan ya juyo saitin inda yaji kiran.

Sabi”u d”an gidan galadima ne ya karaso gunsa, cikin farin ciki yace “Ranka ya dade daga ina haka?”
Abu Turab ya d”an murmusa kadan yace ” naje ganin gari.”
Sabi”u ya kalli Garzali yace “dafatan ba abinda ya faru?”
Garzali zaiyi magana Abu Turab yai saurin cewa ” ba abinda ya faru, sannan inhar ka damu da ni nan gaba inzan fita kazo ka d”aukeni.”

Dariya Sabi”u yasa yace ” Angama Ranka ya dade, nima daga gun Mai Martaba nake akan maganar binciken abinda ya faru yau.”
Fuska Abu Turab ya had”e yace “kai akaba aikin binciken?”
Fuskarsa d”auke da mamakin ganin yanda Abu Turab yai yace ” eh, da wani abun ne?”
Abu Turab ya girgiza kai alamar a”a sannan yace ” ka koma gida ka kwanta kace bakada lafiya, inyaso zuwa gobe sai ka turo fada a sanar da rashin lafiyarka.”

Sabi”u yace ” saboda me? Ni ai ina ganin nine na dace da binciken saboda sanar ma Mai Martaba gaskiya abin.”

Abu Turab yace ” shine dalilin dayasa ai banasan ka amshi wannan aikin.”
Kallan Mamaki Sabi”u yamai, Abu Turab ya sa hannu alamar yana nemansa, da sauri Sabi”u ya rike hannunsa yace “ganinan”

Hannunsa ya rike yace ” Sabi”u ka manta wacece Magajiya ne? Ina tsoron karkaje daga bincike ta juyo da rashe kanka, dan na tabbata bazata taba bari a gane itace ba, saboda haka ka barni da ita ni zansan wanda ya kamata yai binciken.”
Sabi”u ya fahimceshi kwarai hakan yasa bai musa ba yace ” shikenan zanyi yadda kace.”
Nagode.
Abinda Abu Turab ya fad”a kenan.

********

Tare suka shiga cikin gidan suna tafe suna “yar hirarsu.

Yazo yin kwana inda zai shiga b”angarensa, wata budurwa ya hango a tsaye a jikin katangarsa, kanta na kasa da alama ba shiga zatai ba kuma da alama basan barin gun takeba.

Harya dauke idanunsa ya kuma maidasu kanta, baiga fuskarta ba sai dai kallo d”aya zaka mata kasan “yar wani ce.

Sabi”u ne shima idanunsa suka kai kanta, daidainan ita ma ta d”ago, suka had”a ido.
Da sauri ta juya ta shige ta baya.
Sabi”u yai murmushi yace ” yau kuma wa na samu?”

“kai da wa?”
Kansa yad”an shafa yace ” wata ce da alama biyoni tai sai sai kunya ta hanata tsayuwa.”

Kai ya girgiza yace ” kana fama.”

Tana tsaye ta lungun ta zuro kanta kad”an, idanunta ne suka ciciko da kwalla a hankali wani zazzafan hawaye ya taho mata, kallansa kawai takeyi tana mamakin yanda zuciyarta ta kasa mantawa dashi, har yanzu baya gani? Abinda zuciyarta ta fada kenan.

STORY CONTINUES BELOW

Hawaye ne suka cigaba da zubowa sosai sai dai sam ta kasa tsayar dasu.

Har suka shiga tanannan a gun ta dade sosai kafin ta juyo ta fara tafiya.

B”angaren Magajiya ta shiga.
Da sallama ta shiga.
Magajiya ta mike cikin tsananin farinciki ta rungume ta.

“lale lale da zuwan Khadija ga, Uwata barka da zuwa.”
Mamaki sosai bayinta suka shiga yi, hatta Abdulmajid yayi mamakin ganin Uwarsa ta mike tsaye saboda taro wani ba sarki ba.

Khadija cikin farinciki tace ” Nasameku lafiya Umma?”

Magajiya ta saketa ta jawota suka zauna, kallan bayinta tai tace ” ku kawo mata abinci.”

Tsugunawa tai tagaida Magajiya sannan ta kalli Abudulmajid ta gaisheshi.

Kallan ta yai shima cikin farinciki ya amsa sannan ya d”ora da cewa “inakika tsaya bayan tun dazu aka aiko akan kin shigo?”

Kanta ta sunkuyar batace komak ba, Abdulmajid ya hade rai cikin kuluwa yace “badai Gun……”

D”agowa tai fuska a had”e itama tace ” bangane ba?”

Zaiyi magana Magajiya ta katseshi da cewa ” Yarima banasan haka, akan me zaka takurawa Uwata daga zuwanta? Na tabbata nan ta fara zuwa.”

Khadija ta d”auke idanta daga kanshi, shikam ido ya kura mata yana zargin anya kuwa ba gun waccan yaran taje ba?

Abinci kala kala aka shiga jerawa, Magajiya tasata a gaba tana ci suna hira, bayan ta gama ta sa aka d”auko mata jakar kayan datasa akadinka mata, Khadija cikin jin dadi tace ” nagode sosai Umma.”

Magajiya ta kalleta tace ” yaushe zakije duba Inna Lamin?”
Khadija tace ” zuwa gobe, amma ya jikin nata?”

Abdulmajid yai dan kasa da kai yace ” jiki fa ba sauki tana nan dan ko fitsari a kwance take, “ya”yanta duk sun kama gabansu ba mai kula da ita, hmmita kam wannan gwara ma ta mutu ta huta.”

Magajiya ta d”an tabe baki, khadija ta kalleshi tace ” ko ma menene Yaya bai kamata ka fadi haka ba, addu”a kawai zaka mata, amma nikam Umma bakya ganin Baba ne yakamata ya d”aukota ta zauna a gunsa, ta yaya za”abar ta ita kadai a gida?”

Magajiya ta kalleta tare da canza fuska tace ” kin fadama Hisham din haka?”

Tace ” yanzu abin ya fad”omin.”
” Tun kafin ya hauki da fada karma kimai wannan zancen, ke dai kije ki dubata gobe.”

Khadija zata sake magana Magajiya tace ” Khadija bansanki da musu ba.”

Shiru tai batace komai ba, sai dai tana ganin hakan bai dace ba, yaza”ayi ace “yan uwanta da “ya”yanta duk sun watsar da ita?”

*******

Bayan anyi sallar isha”i ne Jakadiya tazo ta sanarmai da sakon Mai Martaba akan yana san ganinsa.

Shida Garzali suka fito, bayan ya shiga ya zauna ne Mai Martaba ya kalleshi yace ” Nayi dogon naxari akan abinda ya faru sannan na sanar ma Sabi”u akan yai bincike akan abinda ya faru, tunda naga shine na hannun damanka.”
Abu Turab kansa na kasa yace ” Abba!”
Kallansa Mai Martaba yai ba tare da ya amsa ba, dan raban dayaji ya kirashi da Abba tunda ya mallaki hankalin kansa.
Abu Turab ya cigaba ” wani hukunci zaka d”auka akan wanda ya aikata hakan?”
Sarki yace ” dole ne ya fuskanci hukunci mai karfi.”
Murmushi ya saki sannan yace ” ko da kuwa Magajiya ce?”
Kallansa yai yace ” me kake nufi?”
Abu Turab yace ” a matsayin d”a nazo gunka inaso d”a da mahaifinsa suyi magana bawai sarki da d”ansa ba.”

Sarki ya kalleshi yace ” shine nace mai kake nufi?”
Abu Turab ya d”anyi shiru kafin yace ” zaka iya hukunta Matar da take da mukami fiye da kowa?matarda yayanta yake waziri?matar da d”anta yake magajinka?matar da duk yawancin masu mukamin nan suke a kasanta?”

Sarki ya kalleshi ranshi a b”ace yace ” Turab!”
Abu Turab ya d”an sunkuyar da kai yace ” tuba nake ranka ya dade bawai da wanj abin na fadi hakan ba sannan ba wai nace itad”in ce tai ba sai dai ina tunanin mu binne maganarnan inhar hukunta mai laifin zai iya zama wani abu.”

Sosai ran Mai Martaba ya b”aci mai Abu Turab yake nufi?

” bance itace tai ba sannan ban san wanda ya aikata hakan ba, ina tsoron kar ka kasa yanke hukunci ne in laifi ya fada hannun manya.”

Sarki ya kalleshi jiki a sanyaye yace ” kaima kanasan kacemin baka yarda dani ba? Kaima kana ganin nid”in ragon sarki ne wanda bazai kya hukunta Matarsa ba?”

Kai Abu turab ya girgiza jikinsa shima yai sanyi yace ” bawai hakan nake nufi ba sai dai banasan na zama sanadiyar saka cikin tsaka mai wuya.”

Murmushin takaici yai yace ” na sani ban kula da ku ba kaida mahaifiyarka lokacin kana yaro sannan na sani laifinane da bana shiga duk wani harka data shafeku sai dai na sani bazaka taba gane dalili na nayin hakan ba.”

“so kake ka karemu, bakasan a gane damuwarka a kanmu bare a mana illa.” jin wannan zance daga bakin Abu Turab yasa ya kuramai ido.

D”agowa Abu Turab yai ya kalleshi, jiyai zuciyarsa ba dadi, ko dai ya dau abin da zafi ne?”

Ga mamakinsa gani yai Sarki ya saki wani sansanyan murmushi sannan yace ” Alhamdulila d”ana ya girma.”

Baisan sanda ya kalleshi ba cikin mamaki.
Sarki yamai alama da hannu akan ya matso.

Da sauri yad”auke idanunsa, Mai Martaba ya kara mai alama da hannu sannan yace ” na sank kana gani Turab.”1

Idanu Abu Turab ya zaro Sarki ya mike da kansa yazo inda yake, kansa ya d”ago saitin sa yace ” na sani da dadewa, na janye idona ne daga nuna maka saboda banasan ruguza abinda mahaifiyarka ta shirya ya ruguje.”

Idanunsa ne suka ciciko, kai ya girgiza mai yace ” ka manta mai kace? A matsayin Uba kakeso muyi magana? Yau a matsayin uba nake, daga kabar nan zan koma sarki in kuma manta da abinda ya faru tsakanin mu.”

Idanu ya runtse yama kasa magana sam, Sarki yad”an had”e fuska kadan yace ” ina Abu Turab dina wanda baya shakka ta? Jarumin da nake farincikin samun d”a kamar sa?”

Baisan sanda yad”an murmusa ba.

Sarki ya kalleshi yace ” me ka shirga game da abinda Magajiya ta maka?”

Abu Turab ya kalleshi yace ” bazan iya fadama Sarki ba, sai dai ina neman alfarma akan kaba Abdulmajid umarnin yin binciken abinda ya faru.”

Bai kara tambayarsa va yace ” shikenan, sai me kuma?”

Yace “inaso ka taimaka ka cigaba da nuna rashin damuwa dani da kuma hukuntani sosai in nai ba daidai ba.”

Yace “shikenan, sai kuma me?”

Kai ya girgiza yace ” su kenan.”

Murmushi sukama junansu.
Abu Turab ya mike zai tafi, jiyai mahaifinsa yace ” yanzu mun zama d”aya kenan ko?”

Ba tare da ya juyo ba yace ” dama can d”aya muke.”
Yana kaiwa nan ya bud”e kofa.

Yana fita ya had”e fuska sannan ya tsaya a waje kamar irin an mai fadan nan sosai, ya dade a tsaye kafin jiki a sanyaye ya fara tafiya, tuntube yai saura kiris ya fadi da sauri Garzali ya taimaka mai sukai gaba.

Jakadiya ta tabe baki sannan tace ” da alama ansha fada, ai naso a nan akai ba a kuryar d”aki ba.”

Nace hmmmm

Abu Turab yana shiga d”akinsa ya rufe tare da jingina a jikin kofar, tausayin Mahaifinsa ne yake ratsa jikinsa ace kana san abu amma saboda kana mulki baka isa ka nuna ba? Lalai shikam wannan mulkin sam baya kansa.

Haka ya kwanta bacci zuciyarsa fal da tunani kala kala.

********

Washegari a fada Mai Martaba ya umarci Abdulmajid akan ya d”aurashi akan aikin binciken abinda ya samu kaninsa.+

Ba Abdulmajid ba kowa na fadar sai da yai mamakin wannan al”amari, ai ko ba”a fada ba kowa yasan ba wata soyayya ko mutunci a tsakaninsu, amma ace shine zaiyi binciken?

Andulmajid ya kalli Mai Martaba cikin tsananin mamaki, kafin ya daure yace ” insha Allah zanyi binciken abin in sanar maka.”

Yana fitowa Hisham ya biyoshi, Hisham ya kalleshi yace ” me ke faruwa?”

Abdulmajid ya dan kurama kasa ido sannan yace ” abinda ke faruwa?” Umm yad”anyi ajiyar zuciya yace ” wannan shine tambayar da zan fara nemanma amsa.”

Hisham yace ” muje gun Magajiya nikaina inasan ganinta.”

Bayan sun isa gunta ne sun gaisheta, Abdulmajid ya sanar da ita abinda ke faruwa, murmushi ne mai sanyi ya bayyana a fuskarta ta kalli d”an nata tace ” hmm lalai Turab ya girma sai dai Tsohon doki yafi sabon takalmi.”

Abdulmajid ya mata kallan rashin fahimta, “Tsi tsi tsi tsi” abinda tai da bakinta kenan tana jijiga kai tace ” karka badani mana Abdulmajid, ba shakka Turab abinda ya nema mahaifinsa yamai kenan jiya.

Hisham yace ” nima naji labarin zuwansa sai dai naji ance fada aka mai?”

Baki ta tabe tace ” ko da wasa ni nasan ba fada aka mai ba in har fada ne mezaisa ya shiga kuryar d”aki? Sannan da yamma ya riga ya umarci Sabi”u akan yai bincike sannan yau da safe ya maidashi kan Turab ne hakan yake nufi?”

Hisham ya kalleta yace “amma hauka yake da zai umarci Abdulmajid? Bayan yasan ba sanshi yake ba.”

Abdulmajid ya kalli Magajiya yace ” Umma kina nufin yayi hakan ne saboda karmu d”aurama mahaifiyarsa laifi? Tunda yasan ai ni ban isa ince mahaifiyarsa bace hakan zaisa a zargeni.”

Magajiya ta mai alamar jinjina da hannu tace ” kwarai kuwa Yarima na ashe ka harbo jirgin.”

Dariya Abdulmajid yai yace ” lalai yaran nan, yana makaho har……”
Katseshi tai tace ” munyi sakaci da muka ragamai muna tunanin makaho ai baya ganin komai, masarauta fa muke?sannan jinin mahaifinsa da kakansa suna yawo fa ajikinsa.”

Hisham ya kalleta yace ” yanzu meye abinyi?”

“Hmm farko dai tunda ya maida wasan kanmu dole ne mu buga wasan, ai hakorin dariya shi yakanyi cizo.”

Kallan mamaki suka mata, tai kalli Abdulmajid tace ” ka nutsu sosai kaga yanda zan buga wasan.”

Shiru yad”an biyo baya kafin Hisham yace ” ni kuma wani abu d”aya ne yake damuna, me yasa haryanzu sarki ya kasa neman ma Abu Turab magani?tunfarkon zuwan sa da yadanyi na shekaru kad”an yanzu sam baya turo masu magani, ko ya hakura ne da makantar yaron…..”

Magajiya ta d”an kankance ido tace “ko kuma ya warke ba.”

Idanu suka zaro suka kalleta, shiru tai tana tunani kafin ta mike da sauri tace ” me yasa hakan baizo min ba?”

Da sauri ta kalli Hisham tace ” Hisham aika a kiramin yaron nan.”

STORY CONTINUES BELOW

Abdulmajid shima ya mike hankalinsa a tashe yace “Ya zamuyi in har yana gani? Kenan za”a iya bashi mulkina!”

Magajiya ta bugamai wani kallo tace ” so kake ka zama rago akan wani makahon daya warke?”
Hisham ne yai waje da sauri ya tura baiwar Magajiya akan ta aika a kira Abu Turab.
Shiru tai tana tunani kafin tace ” aika a dafomin ruwa mai zafi sannan a zubo a roba, a kuma zubo ruwa mai sanyi shima a roba.”

Shiru tai tana tunani kafin ta fita da kanta, ba shakka hankalinta ya tashi, ya zatai in har yana gani? Kenan tunda raina musu hankali yakeyi kenan.

********

Zaune yake yanashan ruwan zafi wanda yasa aka dafa mai da kayan kamshi, zafin cittar yasa yake d”an lumshe idanunsa, shigowar Garzali ce tasa ya bud”e idanunsa.

Zubewa yai a kasa ya sanar dashi sakon nemansa da Magajiya takeyi yanzu.

Bai amsa ba ya cigaba da shan shayinsa.
Sai daya gama sannan ya mike ya shirya ya fito, Garzali ya taso da sauri yazo kusa dashi.

Tafe suke yana rike da sandarsa, idanunsa ne suka kai gun jiya inda yarinyarnan ta b”uya, ya rasa me yasa yakeji kamar ana kallansa.

Yana kallan gun kuwa suka had”a ido.
Da sauri ta b”oye tare da dafa kirjinta dayake bugawa da sauri, a tsorace tace ” ya ganni?”
Kai ta girgiza tace ” ta ina zai ganni?”

Shikansa jikinsa ne yai sanyi yana tunanin abinda ya gani, kawar da abin yai a ransa har suka karasa b”angaren Magajiya.

Tana zaune a kilisarta, Abdulmajid na gefenta, Hisham ma na d”aya gefen nata ya shigo.

Sai daya zauna sannan Garzali ya fita.

Gaisheta Abu Turab yai ta amsa tana karema idanunsa kallo kansa na kasa, kallan zargi takema a haka tace ” Me ya faru ne sam ka daina zuwa gaisheni.”

Murmushi ya d”anyi yace ” Da alama Umma Babba san ganina ne yasa kika manta nazo kwanan nan.”

Kallansa tai tace “haba? Amma ya akai nakeji kamar na dade banga d”ana ba?”

Yace ” zan dinga zuwa akai akai in har kinasan ganina.”

Tai dan murmushi sannan tace ” bari a kawo ma abinci kaci, yau takanas nasa a ma d”ana abinci, dan na kula bana baka kulawa yanda ya dace.”

Ya jita sai dai bai tanka mata ba, nan tasa aka jera mai a binci tace ” bismillah.”

Hannu ya saka yana shashafa kwanukan alamar baya gani, kwarai yaga ruwan zafin dake daf dashi, tunani ya fara yi me ya kawo ruwa wanda yake turiri kusa dashi? Kana kallan ruwan kasan yanzu aka juyeshi, ba shakka zargin ganinsa takeyi, bazai taba ba mahaifiyarsa kunya ba dan kawai ya faranta ransa ba, hannunsa yakai kan ruwan zafi da saninsa ya sa hannunsa zuciya d”aya.

Azabar dayaji ne yasa ya zare hannun da sauri ya rike hannun cikin jin zafin zugi da radadin da yakemai.
Kallan juna sukayi suka saki murmushi ba shakka baya gani.

Da gudu ta karaso ciki tashin hankali, hannunsa ta kama da sauri ta saka cikin ruwan sanyi.

Kuka kawai takeyi hankalinta yayi tsananin tashi.

Magajiya ta mike itama tace ” lafiya Abu Turab?”
Ta fada tare da nunama Abdulmajid ya d”auke ruwan zafin.

Nan ya d”auke ruwan.

Kallansa tai tace ” garin yaya? Ina lilahi wa ina ilaihi raji”un, me ya faru? Badai ruwan wanke hannu danace su kawomin bane suka kawo na zafi, inaji sun d”auka kafata zan gasa wacce ma bige jiya.”

Ba wanda ya kulata tsakanin Abu Turab da Khadija.

Shikam yama kasa komai zafin hannunsa da kuma ganin Khadija sun sa sam yama kasa cewa komai.

Kuka take sosai ta mike da gudu ta fita, dawowa tai d”auke da zuma a kofi ta shafamai, Magajiya duk ta rikice.

Abu Turab ya daure ya kwace hannunsa sannan ya mike yace ” bakomai Umma Babba ba laifinki bane na sani, ke mai zaisa kisa a kawoma d”anki makaho ruwan zafi haka? In har dama ba neman halakashi kike ba, wanda nasan ke kuma ba hakan bane a gunki.”

Ta bud”e baki zatai magana yai waje.

Ba shakka ta tabbata magana cikin magana ya fada mata.

Khadija ta kallesu dukansu cikin kunar rai sannan tai waje da gudu.

Binsa tai inda yake ta rike hannun daya kone ta sama tace ” yaya muje a baka magani.”

Fuska ya d”aure tamau sannan ya kalli Garzali yace ” wacece wannan d”in take tabani?”

Garzali ya kalleta, zaiyi magana tai saurin cewa ” Yaya Khadija ce, nice kasani ba cutar dakai zanyi ba.”

Hannunsa ya fizge yace ” ta ina kenan na san ba cutar dani zakiyi ba? Ko na sanki ne da harzan iya miki shaida?”

Sakeshi tai idanunta suka ciciko a hankali tadanyi baya kadan tana mai kallan tsananin mamaki.

Garzali wuce muje.

Tana tsaye anan har suka kule sam tama rasa abinda zatai tunani.

Jiki a sanyaye ta koma b”angaren Magajiya.

Taje shiga taji suna dariya, Hisham yace ” da alama dai idannan bam yake baya ganin komai.”

Dariya Abdulmajid yai yace ” tab amma fa ya daure dan ruwan zafi ba wasa bane.”

Bud”e kofar tai da karfi cikin tsananin mamaki ta kallesu.

Tace ” da saninku?”

Dif sukai kowa ya kura mata ido.

Hawaye ne suka shiga zubo mata ta girgiza kai tace ” kuna “yan uwa, ko ba “yan uwantaka ai akwai na musulunci, tayaya zaku samu mutum wanda Allah ya d”auke ganinsa ku samai ruwa ya kone? Nazo da niyyar muku magana akan barin Inna Lami a halin da take bayan na dawo daga gunta, sai in tarar da wanda yafi nata?”

Kuka ne yaci karfinta tace ” anya akwai tausayin imani a zuciyoy……”

Wani wawan mari Hisham ya mata wanda batai zatan jinsa ba.

Kuncinta ta rike ta kalleshi, kasa magana tai, waje tai da gudu taba kuka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *