KALLON KITSE CHAPTER 10

KALLON KITSE CHAPTER 10

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

da sauri jafar ya isa inda take zaune, idonsa jajir, haba inna meyasa don Allah ki fadamin, dalili da yasa kike kyamata, wallahi ni mai gyaruwa ne, inna ki taimaka min,

tsakanin da da mahaifi sai Allah, inna taji tausayinsa sosai aranta

amma bazata iya yin abunda ya bukata ba, ta kauda fuskarta gefe, sam bata sauko ba, tace jafaru inkana so mu zauna lafiya dakai, ka maida wannan maganar dan bazai yiyu ba, bazan iya ba, kana jina?

Ta mike zata wuce, Alh. Yunusa yace, fati dan girman Allah ki sauko, wai me kike nufi da jafaru ne? Ki tuna duk dan Adam fa ajizine, bai taba cika goma ba.

Ta kalli Alh. Yunusa tace, “lallai  na yarda da maganarka, amma bazan iyaba namijin da mace daya tak ta juya masa rayuwa ba, dan haka ni na gama nawa, kaga babban yusrah ina ganin girmanka, amma wallahi bazan iya yarda da wannan abunba, don Allah adaina.” fuuu! Ta wuce daki ta kulle.

“lallai maganar da inna ta fada gaskiya ne.” Alh. Yunusa ya fadi hakan a zuciyarsa, toh ammma…..

Sai kuma ya mike tsaye, jafaru da sauri shima ya mike yabi bayan baba yunusa, idon nan nasa kamar zasu fado, don bacin rai.

Su kuwa su zainab duk jikinsu yayi sanyi, sam basa son yadda inna ta dauki zafi akan dan uwansu, ya kamata tayi hakuri haka.

Su kam su uwani suna wurin indo basu san abunda ke faruwa ba, tsokanar hafsat sukeyi, wai saurayinta kato ne, hafsat tace, eh nayarda kato ne ku ina naku samarin? Yauwa uwani ina saurayin nan naki wan kawarki lawisa?

Uwani tayi murmushi sosai tace, hamza? Yana nan wallahi, eh toh bana musaba gaskiya kika fadi, dan hamza ya mallaki abunda nakeso a da namiji, ada banyi tsammanin So wani abu bane, amma akan hamza na gano so wani abu ne, da bazaka san sanda zai shigeka ba.” hafsat tace, ‘yar uwa nima haka ta sameni, dan haka nasan abunda kike nufi.

Fa’iza kallonsu takeyi, ita dai bata fada wannan tarkon ba, dan haka saurare takeyi, a haka suka cigaba da hirarsu ta ‘yan uwa.

Jafaru zaune a dakinsa ya rasa abunda keyi masa dadi, dan me inna bazata amince da hakan ba, abunda bashir ya fada masa gaskiyane, inna bazata bawa wanda bataso uwani ba, gashi danta na cikinta bata amince masa ba, toh wa zata amincewa? Ya tambayi kansa, tare da kai kofin barasa bakinsa,ga kuma taba a dayar hannunsa na hagu, kulle kansa yayi a dakinsa, tunani bawanda baiyiba ahaka ya kwana ranar ko abincin kwari baici ba.

Ansamu kamar kwana uku da wannan maganar sannan ana bawa inna hakuri, amma sam taki, harda kawunsu yazo, musamman saboda maganar wato Alh. Hashimu, amma taki saurarensu, har gori take musu akan jafaru, ya maida su abokan wasan sa, duk ya dauko gantalin tunaninsa sai yaje ya dauko su, yadda suke tsammanin abun zai zo da sauki sam abun ba haka bane, dan har ta kai a yanzu inna bata amsa gaisuwar jafaru, abun ba karamin tada hankalinsa yayi ba, ya rasa abunda keyi masa dadi arayuwarsa, wai ya zaiyine? Ya tambayi kansa, wata dabara ta fado masa, dan haka shiryawa yayi, tunda safe ya tafi jega gun shatu, tana zaune bakin murhu, tana soya kosai abincin karinsu, taji sallama, ta amsa da sauri tana zuba ido, dan ta gane mai muryar. Ta kwallawa danta hafiz kira, shine na biyu, a tsakar gida akayi masa shimfida ya zauna, shatu tasa aka kawo masa kari.

Dakyar yake cin abunda ke gabansa, ba wai kyama yakeyi ba, a’a. Shatu nada bala’in tsabta duk da bakomai gareta ba, amma tanada wafatar zuci, dan bata taba rokonka abunka, indai ka bata zata karba, amma bazata roka ba, ko wani wata inna na hado mata goma na arziki, dan haka tsakaninta da inna sai addu’ bayan ya gama itama ta sami wuri ta zauna gefen sa, suna kara gaisawa, ita tasan akwai abinda ke faruwa dan jagaru yazo nan jega da ya dawo gari, amma ba haka yake zuwa mata ba, daka ganshi zaka karanci akwai abunda ke damunsa.

Tace, ina fata su inna duk lafiya suke jafaru? Tayi tambayar ne cike da zakwadin jin abunda zai fada.

Kansa akasa yace, kowa lafiya lau shatu, nine dai banda lafiya.” tayi ajiyar zuciya, “jafaru meke damunka? ya dago idonsa da yayi jajir yace, “inaso ki taimakeni, inna bata sona shatu, dan Allah kije ki bata hakuri, ta tsaneni, bata kaunata da rahamar duniya, toh ballantana na lahira.

Shatu ta kara numfasawa, “me yayi zafi haka jafaru, har kake furta wadannab kalaman da babu dadin ji? Lebensa ya ciza kafin yayi magana, “shatu tunda na shigo garin nan naku inna taki sakin jiki dani, nasan nayi laifi, amma nagane kuskurena, da har inaso in kulla abunda ina tunani bazisa nasake afkawa ga kuskuren danayi ba, amma sam inna tayi fir! Taki yarda, toh a lokacin nasan lallai inba haka nayi ba, toh rahamar duniya ko na can lahira bazata sameni ba, dan inna har yanzu tana fushi dani, bata yafemin ba shatu, ki taimakeni, ki tayani bata hakuri dan girman Allah shatu.

Duk karfin halin jafar saida kwalla ya fito masa a ido daya, yayi saurin gogewa, yana sauraren abunda shatu ke fada masa.karka damu jafar insha Allahu zan sami inna muyi magana, amma wannan abu bakaramin bani mamaki yayi ba, koda yake nasan inna da fushi, in abu yafice mata, toh yana da wahala ta karasa kanta aciki, toh amma inbanda inna harda danta na cikinta bazata raga masa ba? Toh Alla ya sawake, kabari insha Allahu gobe zan shigo kebbi…” bata karasa maganar ba ya dakatar da ita, “nifa shatu gaskiya tare zamu tafi, bazan bar garin nan ba saida ke.”

yau naji ikon Allah jafaru har yanzu kana nanda rigimarka da naci, dama asali haka kake da nacin tsiya kamar…..

Lokacin mal. Tasi’u ya shigo, cike da fara’a, a’a mutanen kebbi ne, lale marhabun, saukar yaushe dan nan sammako akayi haka? Ya sami wuri tare da mikawa jafaru hannu, sukayi musabaha. Bayan sun gaisa shatu tayi masa bayani tiryan-tiryan abunda ke faruwa, ta kara da cewa kasan jafaru da kafewa, nace ya bari har gobe inje, yace ba inda zashi saida ni.”

mal. Tasi’u yace “gaskiya wannan zancen babba ne, gara ki shirya kije, ko gobe ne saiki dawo babu damuwa.

Atake jafar ya soma godiya, mal. Tasi’u yace haba jafaru kaifa nawa ne, jinka nake tamkar wanda na haifa, dan haka dole in take maka baya, na goya bayanka dari bisa dari, dan haka taje a gani ko za a dace.”

tun a washe gari uwani taji wannan labarin, daga ita har inna babu mai samun barcin kirki, dan yadda uwani ta tada hankalinta sosai ko bacci batayi ba, dan haka inna ta dauki alwashi baza ayi auren nan ba, tunda itama uwani bata so, dan haka kullum tana cikin lallashi.

Ranar lajadi su hafsat suka wuce gusau tare da haj. Salaha, daga can zasu wuce abuja, amma sai sun kwana anab gusau, suma sun bada hakuri sam inna tayi jan ido taki saurarensu, har cemusu takeyi basajin tausayinta, dan idan sunji da basu bi bayan dan uwan nasu ba, insun manta ta tuna musu irin bakin cikin da ya cusa musu, da dai suka ga abun ‘yar tone-tone ce

dole suka kyaleta.

Da karfe sha biyu da kwata saiga shatu da jafar sun shigo falo, suna kwalla sallama.

Inna da take ciki ta amsa, da yake indo ta fita, ita kuwa ‘yar lelen tana daki kwance, bazatayi aiki ba, dan an bata mata rai.

Inna ta shigo falon ba tareda ta saki fuskar ta ba, ta zauna suna gaisawa da shatu, jafar ya gaidata shima, harara ta wurga masa, dayasa jikinsa yayi sanyi sanyi, ya kumayi saurin sa kansa kasa. Shatu tace, inna gunki nazo akan maganar dana, me yayi zafi haka inna? Don Allah kiyi hakuri, laifi fa kowa nayinsa, babu mahalunkin duniya da baya laifi, yo ko Allah munyi masa ya yafe mana, balle mu?

Inna don son annabin rahama, saboda Allah kiyi hakuri.” inna ta dubi shatu tace, “kingama? Shatu tace haba inna bansanki da zuciya irin hakaba, kiyi hakuri,”

inna ta dubeta, “gaskiya shatu saidai inki na son ki nuna min a yau ba nina haifi uwani…. .” da sauri shatu ta karbe maganar “haba inna…haba inna ya zaki fadi haka? Ni wallahi har a zuciya ta bantaba sawa raina hakaba.” inna itama tayi sauri ta karbe maganar

toh dan darajar Allah da hasken annabi ki fita harkan nan, yaron nan so yake ya hadani daku, amma idan kukayi tunani sam uwani batayi dacen miji ba….”  (nima dai nace uwani batayi dacen miji ba lolz) fuuuu! Jafar ya mike ya fita yana huci, duk ya canza kamanninsa, dan tsananin bacin rai, shatu ta kara narkewa inna tana bata hakuri, amma sam inna taki amincewa, saita dauko wani zancen, sunayi.

Can uwani ta fito falon, tanayiwa shatu sannu da zuwa, “ke kuwa meya sameki, duk kinbi kin rame, ko bakida lafiya ne? Inna tace lafiyar ta kalau, saidai ko ku kukeso ku saka mata ciwon, bata son jafaru, kuna nema ku takurawa yarinya, nikuma bazan takura mata ba, dan ba dole.” shatu gyara zama tayi, “Allah sarki yarinta, uwani kin iya karfin hali, kiri-kiri ki nuna baki son jinin inna, dan Adam butulu ne,….” inna ta katse ta, “ni batayi min butulci ba, dan dana nuna inason auren nan uwani bazata bani kunya ba, amma da yake ita bamai son bacin raina ba ce, dan haka bazata yiba. Kuma baza ayinba.

Uwani kam wani sabon kuka ta shigayi, shatu ta yamutsar da fuskarta tace, “iye samun wuri, wallahi yarinyar nan dadine ya miki yawa, lallai kin iya zaman duniya, amma kin bani mamaki, uwani kuma kin bani kunya…. .”

a’a nidai nidai na baki kunya ba itaba, dan dai nice nace baza ayiba

dan Allah shatu ki daina…kinfa fara bata min rai, haka kawai zaki sata gaba dan ita bata da gata, ko shi jafaru shine dan gata? Toh wallahi ba wanda ya isa yasamu dole akan wannan al’amarin.

Shima kuma ya dawo ya sameni, inji dalilinsa na gayyato min mutane kan maganar da bata gaskiya ba.”

washe gari aka nemi jafaru can kaduna, don wani course daya nema abashi, ya samu, dan haka zai daga hutunsa, har sai lokacin da ya gama course din, ya sami baba yunusa ya fada masa, banu damuwa jafaru insha Allahu za a dace, kada ka damu kanka, insha Allahu uwani takace, sannan inaso kasani matar mutum kabarinsa, indai matarka ce dole ka aureta.

Haka dai yata bashi magana, ya tambayeshi ko wata nawa zaiyi, “wata tara ne baba, can kasar somalia ne,

Can kasar somalia ne, kasan inaso abani major dan haka, dole ne saida course ko ince maka dole muje yaki ba yadda bata kasancewa, nidai kutayi min addu’a Allah ya dawo dani lafiya.”

insha Allahu zamuyi addu’a jafaru, kuma za a dace, dan Allah mai karbar addu’a ne ako da yaushe.” a sanyaye ya wuce gida, abun mamaki uwani ya gani tareda wani tsaye suna hira, bai taba tsammani yana son uwani ba, sai aranar dan wani irin kishi da bakin ciki ya kai masa wuya, ji yake kamar yayi ihu, sai dai yasha jinin jikinsa ya wuce ta gaban su, dan yaga irin mutumin daya fishi.

It kuwa data lura dashi, saita kara sakin jiki, tana ta kecewa da dariya, tareda fadin kai hamza bakada dama wallahi.” cike da nishadi, saida karfe tara saura sannan ta shigo gidan, takai wajahen zauren da zakabi ka shiga gida, saiji tayi an jawota, kamar wata kaza dan rashin nauyinta, a tsorace tace, “wayyo!” jafaru ya hadata da bango ya matseta, ita kuwa ta runtse idonta, tana bashi hakuri, “waye wannan dan iskan yaron, dana ganshi tare da ke waje?

Gabanta bama faduwar uku yakeyi ba, goma yakeyi, dan data kalleshi, yadda fuskar ta zama kamar ta zaki, amma saboda tsiwa iri tata, sai cewa tayi, “meye ruwanka dashi? Saurayi nane, shi nake so!.”

“ni kike fadawa magana? Hannunsa taji cikin rigarta, dai-dai cibiyarta, a lokaci daya ta kwalla wata irin kara wanda shi kanshi sai da ya razana, yayi saurin sakinta, yana saukar da numfashi yace, “gobe ma in sake ganinki dashi, saikin gane kurenki wallahi.” daga can bayansu inna ke kwallawa uwani kira, tana fadin subhanallahi, lafiya? Da gudu uwani ta bar wurin, ta karasa cikin gida tana kuka, ta rungume inna, ke lafiya? Me akayi miki?.”

daga can jafar ne yake magana, “inna tadi take da daddare.”

“da gaske ne uwani?

“karyane inna.”

“ni nake karya?.” yayi kamar zai zo gurin, da sauri ta gudu ta boye bayan inna.

Toh ai saikayi hakuri ko? Tun da ko mutuwa najin kunyar mahaifi.”

“inna yarinyar nan fa ta rainani, Allah zan daddakata.

A’a babbalta zakayi, wato ina baka hakuri, amma bakaji ko? Ai nasan nan gaba har ni saika doka, dan agane wannan soja daka shiga ka zamto wani tantiri a rayuwarka.”

sai a lokacin ya sauka, saidai bai daina huci ba, saikace kumurci, “inna ayi hakuri, dama nazo ne ince miki zan koma wurin aiki, an nemeni zan wuce course somalia, addu’arku nake bukata, dan kinsan ba zaman lafiya akeyiba a yanzu haka, inna kiyafe min, kiyi min gafar abunda nayi miki,” kwalla saida suka cika idon inna, amma sai tayi na maza tace, “toh Allah kiyaye, ya kuma baka abunda kaje nema na Alkairi.”

tunda ya shigo kebbi ba randa yafi jindadi kamar wannan daren, dan addu’ar da inna tayi masa, yasa inna ta yafe masa, har a zuciyarta, toh amma meyasa bazata bashi uwani ba?

Washe gari tunda safe ya bar kebbi cike da kewar ‘yan uwansa, saida yabi ta gusau yayiwa zainab bankwana, sannan ya wuce kaduna, da yake ta abuja zasu wuce, sai anan ne zaiyi bankwana da salaha, ranar asabar suka wuce, Allah ya dawo dasu lafiya (ameen)+

**** **** **** *****

Tunda jafar ya tafi uwani da inna sula sami sakat, dan duk sun saki jiki, uwani harda sa hamza tayo yaje ya gaida inna.

Inna kuwa ta amsa masa a cewarta ta san yanada mutinci, saboda dan babban gidane, soyayya sosai suka kulla kusan kullum saiya zo gidan hira. Ayau ma yazo sunata hira cike da nishadi, shin wai yanzu saura shekara nawa ki gama school?.” kanta a kasa tana murmushi cike da jin kunyarsa, “yanzu mun fara jarabawa, zamuyi hutun first term, na s.s 2 kenan.”

Ah ashe da saura uwani nidai na matsu.” ta kara fadada murmushinta tace, “tun yanzu? Nifa so nake ma in wuce universty?.”

gaskiya bazan iyaba uwani, sai dai in baki sona wannan kam.” sai a lokacin ta dago idonta, sukai ido hudu, da sauri tasa idonta kasa tace, toh ai kaima student ne.”

hakane, toh amma ai kafin nan da shekara na gama, sai in wuce service, ko kuma in bari har sai na aureki tukunna.” tayi saurin ware ido a ranta kuwa, tunani takeyi, anya ayi haka? Gaskiya ita tafi son ta auri mutumin daya mallaki hankalin kansa sosai, da dai zaiyi hakuri nan da shekara hudu sai a fara maganar aura, a lokacin itama ta kara girma sosai, amma ai inta gama secondary iyakarta shidda……

“uwani ya katse mata tunani, “kina saurarena kuwa? Ta murmusa, eh meka gani ne.”

kirr, wayar hamza ce ke kuka, yayi saurin mikewa, “kinga har na sha’afa mama na can na jirana, bari zanje indawo, inkuma ban dawo yau ba, sai gobe idan Allah ya kaimu, koya kika gani?

Yayi dai-dai ta kama hanyar gida, gara ka tafi kada ka bata mata lokaci.”

haka soyayyarsu ta kasance, sun shaku sosai, haka ma da inna itama tana son abunda uwani take so, dan haka hamza ya zama na gida a kullum zaizo harda shi a girkin gidan.

Inna na zaune a falo, uwani da lawisa suka shigo kamar wadanda aka jefo, inna tace wannan wace dabi’ace kuma, kamar wadanda aka jefo?

“wallahi inna mun gaji, yunwa mukeji, kinsan yau muka zana jarabawar karshe, sannan an bamu hutu a yau din.”

“toh Allah bada sa’a,

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *