UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 9 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 9 BY SHATU

             Www.bankinhausanovels.com.ng 

Haka na dawo gidan bikin jikina a sanyaye, hannuna rike da wayata da Kuma novel din da ya kawo min. Dan guri na samu na zauna na cira wayar na cire ta daga flight mode da na saka ta kafin naje gurin Usman. A hankali naji Abu me dumi ya saukar min akan kumatu na, cikin sauri na goge hawayen tare da waigawa kada wani ya ganni Ina hawaye ayimin sharri ace saboda Ismail Bai aureni bane. Gaba daya se naji zaman ya gundure ni kawai so nake na kadaice, dakin su Amira naje, dake ana Shirin tafiya dinner yasa Babu mutane Dan haka na shiga toilet na rufe na tsaya gaban mirror din Ina kallon fuskata yadda ta koma so pitiful, se kawai na fara kuka tareda jingina jikina jikin bangon toilet din, nayi kukan me isata sanan na tatso wani face gel Dana gani cikin toilet trolley na wanke fuskar, Amma dukda

haka tayi ja Dana fito, haka Kuma idan na tuna ya tafi se naji hawaye na Kara taruwa cikin idanuna, I wonder me zuciyata take nufi dani da zata Zama so fragile kawai Dan abinda Bata so ya tafi, Ina ce tareda ita muka hada karfi wajen ganin mun koreshi ni Ina ikirarin bana son kishiya. Ammi ta kirani na fita na same ta tace ana ta nemana tun dasun, na zauna gefenta ita da Anty Safara’u da suke hira ta dubeni tace+

” Ya akai fuskar ki tayi ja, kuka kikayi?”

Na girgiza Kai nace

” A’a kaina ke ciwo”

Suka min sannu sannan Ammi tace idan bazan iya zuwa dinner ba na koma gida, nace Mata a’a zanje. Tasa aka rakani aka min light makeup a fuektaa, Ina tunanin shi ne Karan farko da foundation ta fara zama a fuskata, na zura ankon da mukai na lace maroon me Dan adon sea green a jiki. Skirt da riga nayi kamar ko yaushe Dan ita nake sawa na jini comfortable. Wajen takwas aka tafi tsadadden event center na Kano Kai kuwa abin manya, gurin kanshi abin kallo ne, sosae Yan uwanshi Yan gayu masu kudi ga sarauta na wajen baban shi suka zo. Na samu guri na zauna na maida hankali na kan littafin da Usman ya kawo min. Muna nan Babu jimawa ango da amarya Suka karaso, ko shedan ya kalla Hanifa se ya Kara kallonta ba karamin kyau tayi ba, kayan da ta saka masu duhu Dan haka fatar jikinta ta haska Kaya tayi kyau ga murmushi da take itada uwarta na cikar buri, na aurar abinda zuciya ke muradi, na shagala sosae Ina kallon su, idanuna ya koma kan Ismail that looks a bit complicated, fuskar shi Babu alamar annuri Amma dukda haka me kyau me kyau ne, yayi kyau a manyan kayan da ya saka. Suna Zama aka fara program din smoothly, ko inda nake ban daga ba seda aka fara spraying kudi sannan ne na maida hankalina kan yadda ake ruwan kudi wasu suna can Basu ci abinci ba. Haka aka tashi na fito a gajiye tikis. Ammi dama sun tafi so ta hadani da Yaya Nasir zai maudani gida, na fito dake Yana tawagar angwaye Dole se na jira sun fito, haka na tsaya gefen motar shi immersed a cikin wayata, inata kallon update din mutane bikin went viral Dan bikin famous mutane ne. Ina nan tsaye na fara jiyo dariyar su ga Yan matan amarya anata karairaya anga maza, Ina dago idanuna ya sauka akan na Ismail, nayi saurin dauke kaina Dan baisan nazo ba Kuma bana son ya sani, na maida hankalina kan wayata Ina ta lallashin Bature dake kumfar bakin naje dinner har after eleven ban koma gida ba, dagowa nayi jin kamshin turaren shi, hannun shi yasa ya amsa wayar hannuna tareda Danna lock yace

” Ashe kinzo ko liki bakiyi min ba”

Na danyi murmushi nace

” Bana spraying beside bana son kayi noticing presence Dina”

Ya kalleni looking Disturbed yace

” Me yasa kike son nunawa mutane baki Sona? Me nayi Miki sofiyya da kike kina haka?”

Na Dan gyara tsayuwaa na nace

” Dan Allah karka dakko maganar nan, ni bance bana sonka ba, I just turned down auren ka. Dalilin Kuma gaskiya bazan iya fada maka ba”

STORY CONTINUES BELOW

Ya hade hannayen shi biyu yace

” For God sake kin yadda na kwana dakin wata, ke ko kishi bakiyi, Sofy I love you kin sani ko?”

Ban Kai ga Masa magana ba naji karar takalmi, na dago idanuna Hanifa ce ta karaso ita da Yaya Nasir da wasu friends dinsa da nata itama, tana zuwa ta saka hannunta ta rungume shi tana kallona cikin idanu ta kwantar da kanta akan kirjin shi tace

” Dear na gaji kafafuna ciwo suke kazo Kuma kana Hira anan mosquitoes are biting me”

Ya kalleta sannan ya kalleni yaga hankalina Yana kan friends dinsa da nake gaisawa dasu sannan inama Yaya Nasir complain din ya barni inata jiran shi, matsawa nayi ya bude motar na kalla Ismail dake ta kallona Yana Kuma kicinayar yakice ta daga jikin shi naji haushi Amma ban nuna ba saboda nasan tayi ne Dan naji haushin ,

” I’m leaving Allah ya Sanya alkhairi ya bada zaman lafiya. Amarya Allah ya Sanya alkhairi”

Daga haka na juya Dan Shiga motar Nasir, maganar Ismail tasa na tsaya yace

” Nasir nace maka Zan kaita gida, do me a favor ka Mika amarya gidan su”

Nayi murmushi Ina kallon Hanifa data Bata Rai tana hararata na dubi Yaya Ismail na girgiza Kai tare da fadin

” No! Karka damu I’ll be comfortable here”

Ina Gama fada na Shiga Yaya Nasir ya shigo muka tafi, a hanya yayi dariya yace

” Mata da kishi, Hanifa haushin ki take ji”

Nayi dariya nace

” Da Zan bishi kawai dai nasan idan akai min hakan bazan ji dadi ba shiyasa, but ko yanzun tasan matsayina gurin shi”

Yayi dariya yace

” Duk Anty jidda ta hada wannan abun Kuma inshallah se sunyi Dana sanin wannan hadin da sukai, Dan nasan ayi ne a Bata muku Rai”

Ni bance komai ba kawai nayi dariya Ashe kowa ya gane motive din Anty jidda. Washegari a masarautar kano aakai budar Kai sannan aka karba Amarya, Shima banyi missing ba naje anan muka hadu da Anty jidda suna zaune ita da Ummaah tana hangoni ta kwalla min Kira, naje na gaishe su tace min

” Meye hadin ki da Ismail ?”

Ummaah ta kalla Anty jidda tace

” Me ya faru”

Nan ta fada Mata yadda Hanifa ta tsara Mata, Bayan ta gama nace

” Ni ban shiga motar shi ba, ba Kuma ni nace Zan bishi ba shi yace zai daukeni Dan haka banida laifi”

Na Mike tsaye Zan tafi Ummaah ta sake Kirana , na dawo na tsugunna tace

” Bakida kunya dama? Ko Dan ai Bai dace na tambayeki ba tunda dama kin gwada min na gani, Babu ke Babu Ismail kije can kici boko keda iyayenki”

Har nayi shiru se Naga idan Ina musu shiru zasu Raina ni Dan haka nace

” Ni bani zakiyi wa warning ba Ismail Zaki yiwa Kar ya Kara shiga harkata”

Se ta yo kaina zata dakeni, na tsaya cak Ina kallonta Ido cikin Ido Ina jiran ta dakeni, mutanen dake na kusa da ita Suka hanata, Amma tace se ta dakeni bacin ranta  kallon da nake Mata, wata dattijuwa ta shigo Wanda yasa parlon yin shiru ta dubi Ummaah tace

” Furaira menene haka, an Tara mutane Zaki Bata Mana taro, me tayi Miki?”

Ummaah tayi shiru se kawai ta girgiza Kai ta Kama hannuna muka fita Anty jidda tace

” Kunga fitsararriya yarinya, Kinga kallon da take miki, wallahi duk ranar da yarinyar nan ta Shiga hannuna se na karyata “

Matan parlon nata tofa albarkacin bakin su ni kam Muna waje tareda dattijuwar alamu sun nuna dangin Baban Ismail ce ta rikeni tana tambayata abinda ya faru nace Mata Babu komai, anan Ismail ya shigo Anata guda ya kalleni fuskata tayi ja yace

” Yakumbo me ya faru?”

Ta Masa bayanin abinda ta samu, ya girgiza kan shi yace min naje Ammi na nemana, wucewa nayi naji Yana Mata bayanin tsaknain mu, tunda na fadawa Ammi abinda ya faru tace kawai mu tafi Bata son masifa, muka shirya se Gumel, Amma abinda ya bani mamaki shi ne rashin zuwan Anty Rumasa’u.

Anty Rumasa’u sun Gama hada deal itada Anty jidda tun ranar da taji labarin Anty jidda na son bawa Ismail Hanifa shi Kuma Ismail na Sona sukai deal na Shiga bokaye, akan lallae duk yadda zaayi Hanifa zai aura, gashi Bayan mu namu bangaren, bangaren su na mahaifin shi yam Mata da yawa son shi suke, Dan haka Dole se de daya daga cikin su yayi missing bikin yaje ayi aiki har a daura aure. Bayan sun Gama magana da Anty jidda akan komai yayi daidai, ta dakko hanyar dawowa Funtua a Hanya sukai accident motar ta hantsila ta Kara hantsilawa sannan tayi daji!Wata irin Kara motar tayi a take wata irin kura ta mamaye gurin Wanda yasa motocin dake tafiya akan titi parking Suka firfito Dan kaiwa mutanen cikin motar agaji, Babu Wanda yayi tunanin idan sun Isa gurin akwai Wanda zai fito da ranshi saboda kowa yaga yadda motar ta hantsila kafin ta bigi katuwar bishiya, kilan da Bata buga ba Kuma baa San a Ina zata tsaya ba. Suna Isa Suka bude motar aka fara fito da mutane daga ciki, sede duk Wanda aka fito dashi to zaka ga ba kamar yadda ake tunani ba,daga kananan kurjewa se masu rauni kadan, driver ne ma aka fito dashi a sume. Anty Rumasa’u duk yawancin hankalin mutane yafi kaiwa kanta saboda ita ce me ciki a motar, tunda aka fito da ita take ihu tana fadin

” My kaini asibiti marata ciwo take kada na rasa abinda Zan Haifa, na Shiga uku”

Se ta Mike ta nufi mutanen tana hada hannayenta guri guda, matan dake gurin suka rirrike ta suna ce Mata tayi hakuri an Kira road safety suna Hanya, Amma Ina uwata Bata ganewa Bata fahimtar abinda suke fada, haka aka rirrike ta Dan jijjigar da take kadai ta Isa ta saka yaran a wani Hali ga jini daya fara bin kafar ta, tana gani ta tsala ihu tana fadin

” Shikenan na shiga uku idan na rasa shi Nima tafiya zanyi”

Babu Wanda ke gane me take fada su tunanin su zafin buguwa ne, nan kuwa ita tayi scan dinta ya nuna Mata sex din babyn namiji ne, tana ganin shi ne hidden card dinta da idan ta fito dashi to ta Gama winning game din, Kuma shi ne zai fita ko karasa wata takwas baiyi ba. Babu jimawa Sega siren din road safety sun karaso aka kwashi casualties akai asibitin dake kusa da inda accident din ya faru, ana zuwa scanning aka fara Mata Wanda ya nuna abinda ke cikin ta ya mutu, Kuma ba zata iya haifar shi ba Dole sede Emergency CS tukunna, Basu ma jira consent din relatives dinta ba aka samu babba a asibitin yayi signing sannan sukai contacting Baba, muna hanya ni dashi Zan koma Zaria, se kawai muka yanke hanya muka nufi Kaduna. Muna zuwa an fito da ita da gawar yaron da kamar ka taba shi ya tsallara kuka, sede Babu Rai haka ya fito, Babu jimawa aka fito da ita Baba yayi settling bills dinta sannan ya Kira Mama Altinne akan tazo ta zauna da ita, hankali a mugun tashe ta karaso asibitin, ta kalla yaron cikin kwali sannan ta leka window taga yarta kwance ko lifting yatsa ba tayi, unlike sauran wanda ake was anaesthesia ko Babu komai zakaga jikin su na motsi wasu ma zakaga har surutai suke. Dr Baba ya Kira akan yazo ya karasa Dani saboda shi zai je a binne yaron, nama Baba gaisuwa sannan muka tafi, a Hanya yaga hankalina kwance se game nake bugawa cikin wayata yace

” You supposed to be mourning, an Miki rasuwa ga step mum Babu lafiya”

Na kalleshi sannan na maida hankalina kan wayata nace

” So kake ba bi titi bayan titi Ina ihu?”

Hannunsa ya daga daga kan steerer wheel alamar sadakarwa yace

” Allah ya baki hakuri!”

Na dago na harareshi daidai yayi parking gefen Hanya zai saya abu, Shima kallona yake Dan haka se muka kurawa juna Ido, kallon cikin Ido fuskata dauke da murmushi Shima tashi dauke da madaukakin farin ciki

Actually if you know this, but when we first met, I got so nervous I couldn’t sleep, in that very moment I found my love and my life has found it’s missing piece! So as long as I live I love!

Ban kara komawa takan rashin lafiyar Anty Rumasa’u ba saboda a ganina ba abinda ya dameni bane, Ammi tace min taje ta gaishe ta ta Mata gaisuwa, sede tace min gaba daya ta birkice tamkar ba ita ba kadan ne Bata Mata kuka ba, Dan haka na daure naje na dubata. Ganin Ammi ta takura yasa kawai na shirya Bayan sati biyu da faruwar abin nu da Widad data riga ta Zama aminiyata muka tafi Kaduna, doctor ya kaimu. Tunda muka dauka hanya suke Hira ita dashi ni Kuma na maida hankalina Akan wani topic under comparative anatomy na Aves dake kokarin jaza min kwakwalwa, seda na samo materials da yawa Dan na nuna Masa ni Safiyya Abdullahi ce, karatu karya yake ya bani wahala, Dan haka hankalina gaba daya baya kan hirar da duke, seda muka je Kaduna muka Kira Baba ya bamu kwatancen gidan muka Kama Hanya, gidan su kana kalla kasan me gidan yayi arziki a da, ko daga tsarin gidan da unguwar da suke ciki, Amma kana shiga zaka San arziki yayi halin shi. Tun daga parlon nake jin ihu da zage zage, da mamaki muka karasa, mama Altinne na zaune ta kafa tagumi a parlon da ko kujeru Babu se katon rug dake shimfide a kasan. Tana ganina ta saki tagumin tare da Bina da idanu har na shigo parlon, Widad na bayana, hannayen mu dauke da manyan ledoji da Likita yayi musu shopping. Muka gaishe ta ta amsa Babu yabo Babu fallasa, kana kallonta kasan tana cikin damuwa, na dube ta nace

” Ya jikin Anty Rumasa’u?”

Ta Dan tabe Baki tace

” Da sauki”

Har lokacin ihun da ake baa Jima ba, gaba daya naga idanun Widad a warwaje suke, nace

” Zamu Mata sannu Muna hanya ne”

Kafin ta bamu amsa Sega Anty Rumasa’u ta fito, kana kallonta kaga wadda take hauka tuburan, nayi saurin mikewa, tuni Widad tayi waje gabana nata faduwa na tsaya Ina kallon yadda sisters dinta ke riketa amma kokarin kunce zanin jikinta take, na kalli Mama Altinne da hawaye ke zuba Mata nace

” Baba ya sani?”

Ta girgiza kanta, na dubi Anty Rumasa’u da ake janta zaa maida ta daki na musu sallama tareda adduar Allah ya Bata lafiya. A sanyaye na fita na samu Widad na tsaye gefen Likita duk idanunta a waje, nace

” Mu tafi ko?”

Muka shiga mota ya fara tuki, dukka munyi shiru se can Likita yayi breaking silence din da fadin

” Are you ok?”

Na gyada Masa kaina tareda dafe kaina saboda ciwo da yake min, can ya Kara tambayata nace masa

” I’m not, Ina tunanin Anty Rumasa’u ta samu Peuperial psychosis”

Ya kalleni da mamaki yace

“Me ya faru da ita?”

Na girgiza Kai nace

” She’s showing symptoms of psychosis, Kuma na taba karanta wani journal da nayi order sunyi magana akan postpartum blue, postpartum depression and postpartum psychosis. Shi ne abinda yake damunta”

Cikin damuwa yace

“Innanlillahi wa inna ilaihil rajiun!! Amma me yasa suka barta a gida”

Na tafa hannuna alamun rashin sani nace

” Who knows? Kamar ma Basu son a sani ko Baba Basu fadawa ba. Ina komawa Zan fada Masa”

Ya gyada Kansa yace

” It’s a good idea, gwara asan abinda ake ciki”

Da haka muka koma Zaria, na koma school with a heavy heart duk yadda nake jin na tsane ta Amma tausayi ta bani, hatta Mama Altinne ta bani tausayi hauka fa, psychosis ake magana, hadda tube Kaya! Na Kira Baba na fada Masa, ba karamin tashi hankalinsa yayi ba, washegari dashi da Gwoggo da Ammi Suka tafi Kaduna Dan ganin halin da take ciki, Ammi harda kuka, saboda tace min Anty Rumasa’u na ganinta ta fara kuka tareda nufar Mama Altinne tana fadin

” Kince idan na haifi namiji, zai sake ta me yasa sukazo tare? Malamin yace Ina haifar namiji komai nake so Zan samu Ina Dana?”

Ta fada da ihu tana shake wuyan mahaifiyar ta, a haka Baba ya fita ya Kira wani ogansa dake aiki a Rehabilitation center na Kaduna, nan aka zo aka tafi da ita se mental asylum aka daurata akan magunguna. Bahaushe yace faduwar yellow ganye izina ce ga sauran korayen. Tuni labari ya bazu cikin dangi akan abinda ya samu Anty Rumasa’u, mutane suna cewa Babu wani post partum psychosis asirin da takeyi ya dawo kanta. Anty jidda ta shiga tashin hankali, gaba daya ta tsure Dan gani take tata tazo karshe sede Allah ba hakan yake ba, idan Yana sonka Yana baka chance yaga ko zaka tuba sede ba kowa ke amfani da wannan damar ba, bama kowa ke gane cewa chance aka bashi ba. Ita dai Anty Rumasa’u good days dinta sun kare!!!

Se kunyi hakuri Dani Dan bana tunanin post zai Zama regular kamar kwanan baya, I’ll be very busy these coming days inshallah. Ina fata zaku karba uzurina. Inshallah da sannu zamu raka Sofy dakin mijinta ta gano Mana wacece UWARGIDAN BAHAUSHE!Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Babu dadi da dadi haka abin yake, idan yau tayi maka rashin dadi shi kuwan wani dadi take Masa, bazaka Hana wani yayi farin ciki ba saboda Kai kana cikin kunci, wannan shi ne concept din rayuwa, ability mu fahimci hakan Shima tamkar saukakawa rayuwa ne. Jikin Anty Rumasa’u ya Kara tsananta Amma dukda haka tana nan kulle mental asylum din, idan jikin ya danyi sauki se a fito da ita cikin sauran patients din, idan abin ya Kara birkitowa Kuma se a maida ta seclusion kamar yadda suke Kiran gurin. Wannan yasa Ayaan ta dawo gurin Ammi gaba daya da Zama. Ko a hakan aka tsaya ya kamata Mata mu zauna muyi tunani, komai a rayuwar nan talala ake Mana, gashi dai Anty Rumasa’u na da Rai, Dan da take kulafaci Bata Haifa ba, mijin da Yar da Suka rage Mata sun koma hannun wadda tun farko ta so ganin ta rabata da nata yaran, gashi komai da take fada a Kai a karshe baa je ki Ina ba sun dawo hannunta.+

Bayan anyi biki da wata daya Yaya Ismail yazo Zaria nasan ba Danni yazo ba specifically Amma Kuma ya karaso gurina, lokacin da yazo Ina cikin lecture din biochem, so seda ya jira ba fito sannan na sameshi a zaune cikin motar shi, ta bangaren shi na tsaya Ina Dan murmushi nace

” Ango, sannu da zuwa?”

Ya Harare ni, muryar shi a hankali yace

” Ki zagayo Mana”

Ya fada Yana bude min kofar gefen shi Babu musu na karasa na shiga ya rufe sannan ya tashi motar muka fita daga campus din Baki daya, ba dube shi nace

” Ina zamu je”

Ya girgiza Kai yace

” Yunwa nake ji, abinci Zaki rakani naci”

Se ban Kara magana ba har muka karasa wani classy eatery, muka Shiga aka kawo Masa menu ya zaba sannan ya maida idanun shi kaina, kallon shi nayi yadda yake kallona so intense, na Dan saki siririn tsaki nace

” Oh! Oh!! Kallon fa?”

Yayi murmushi yace

” I missed you”

Na dauke kaina tareda kokarin Ciro waya ta dake ringing daga pocket din rigar jikina. Ina fito da ita wata course mate Dita falmata tana Kirana, seda naga Kiran na tuna Ashe munyi dasu zamuyi brainstorming akan anatomy of apes, na dauka ko gaisawa bamuyi ba tace

” Sofy Gumel”

Kamar yadda suke Kirana dashi

” Nazo room dinku baki nan, karki manta fa”

Na sauke ajiyar zuciya nace

” Na Dan fita ne, Ina dawowa inshallah Zan Kira ki”

Mukai sallama na dubi Yaya Ismail dake cin abincin shi a nutse ba tare da ya kalleni ba nace

” Yaya Kai sauri I need to go back ana jirana”

Bai cemin komai ba na lura baya magana idan Yana cin abinci, seda ya gama ya nufi counter Babu jimawa ya nufo ni hannunshi rike da leda anyi packaging abincin, na dube shi muka fita seda ya tada motar sannan na shiga, ya fara driving sannan yace

” Baki tambayeni amarya ba, ko kishi kike?”

Nayi dariya Bayan na kalle shi nace

” Kishi fa? Ni zanyi kishin ka”

Se Naga ya Bata Rai saboda yadda nake dariya kamar I’m making fun of him

” Seriously kayi loosing duk wasu chances na aurena Bayan ka aura Hanifa, so ina son kayi hakuri ka manta munyi wani relationship..”

Se ya kats ni da fadin

” Relationship? It was just a sided feeling, ni kadai nake sonki ai.”

Na gyada kaina nace

” Dan Allah kayi focussing akan aurenka ka manta Dani,kayi hakuri it’s hard Amma just give it a try ka tuna nace maka bazan aureka ba nasan wannan zai baka karfin gwaiwar embracing matar ka”

Ya gyada Kai Yana murmushi yace

” I never thought Zan karba Hanifa, bayan ta tare na fahimci da gaske Sona take Kuma kokarin kyautata min take, se Naga gwara na barki haka na karba abinda Allah ya bani”

Nayi Murmushin Jim dadi nace

” Allah ya zaba mafi alkhairi”

Har muka karasa school hirar gidan shi kawai uake min, Hanifa tayi kaza Hanifa tace kaza, hakan ya tabbatar min zaman lafiya suke kenan baa nan gizo ke saka ba. Bamuyi da Likita zai zo gurina ba, Dan tunda na tashi ko waya bamuyi ba, Dan haka ban kawo a kaina zai zo din ba. Bayan ya dawo Dani makaranta mun Jima cikin motar muna Hira seda naga lokaci na tafiya Kuma a ranar zai koma Kano yasa mukai sallama Bayan ya bani abincin da yayi min takeaway, Ina zuro kafata idanuna ya sauka akan fuskar da bata taba zuwa gareni tana fushi ba, fuskar da kullum murmushi ne yalwatacce akanta mussaman idan Ina gurin. Yana tsaye sanye da kayan kullum wato kaftan, shidai nan duniya Yana son kaftan Kuma shadda precisely, yauma yayi kyau cikin wata shadda coffee, kanshi sanye da hula da akai Mata dinki da milk din zare yafi yawa, idanun shi da glasses sede fuskar Babu annuri abinka da fari fushin ko kadan Bai boyi ba, wayata na duba inajin yadda gabana yake faduwa, a wayata calls dinsa har uku da ban dauka ba, na dake na juya nayiwa Yaya Ismail bye bye sannan ya tafi ba karasa inda Bature ke tsaye nasan ran shi yau ya Gama baci, Amma dake ni ce Ina karasawa inda yake tsaye nayi Masa murmushi nace

” Baka cemin zaka zo ba”

Ya kalleni yadda idanun shi ke hayaki seda na Dan janye nawa kadan

” Da ban fada Miki ba gashi nazo na sameki da wani”

Anzo gurin na fada Ina gyara tsayuwaa ta nace

” Haba Likita Yaya Ismail ne fa ba wani ba”

” Shi din! Idan kina son shi ne ki fada min, ni I can’t take wannan haukan…”

” Hauka!”

Na maimaita Ina kallon shi, Shima kallona yake tunda banji tsoro ba Shima daidai yake dani, na nuna Masa kaina da middle finger nace

” Ni nake haukan?”

Ya kalleni straight idanuna yace

” Duk yadda Kika dauka hakan nake nufi, idan ni Zaki aura Babu yadda zaayi ki dinga biyewa mutanen da Basu San darajar ki ba, mutanen da suka wulakanta ki Suka cuzguna Miki, idan Zaki tsaya kaina to, idan Kuma bazaki tsaya ba se na kyaleki ki koma gurin shi”

Tabbas ya Gama sanin duk wani sirrin gidan mu, kafin meye Raina ya baci na juya a hankali na nufi hostel, Ina ayyana wannan shi ne karon farko da muka taba samin sabani dashi to Amma me yasa zai dauki zafi haka. Na wuce hostel na samu su falmata na jirana mukai karatu abinmu muka Gama. Da daddare nazo bacci ma duba wayata Babu call dinsa, Babu text haka ma a WhatsApp. Se nayi laakari da ni na Masa lafi ya kamata na fara Kira, Koda na Kira na farko Bai dauka ba na biyu Kuma se aka katse.

Wasawasa magana se ta Zama babba, har muka Shure sati daya Bai Kara nemana ba Nima Kuma na dage akan ai na kirashi yayi rejecting call din. Anan na tabbatar da cewar Ina son Bature da gaske,satin farko I was feeling very proud cewar dhi yayi min laifi, abin yakan dameni Amma nayi kokarin sharewa, a sati na biyu ne Kuma zuciyata ta fara gazawa na fara tunanin me yake nufi dani da zai shafe kwanaki Bai Kira ni ba, sede duk lokacin da nayi niyyar kiranshi pride da ego se su Hana ni, ranar da muka cika sati biyu na dawo a gajiye daki, ga Yunwa ga kuncin zuciyata ga naki fitowa na fadawa kowa halin da nake ciki dukda Widad na yawan tambaya ta abinda yake damunta sede nace babu, na kwanta akan gadon se naji vib din wayata da sauri na juya tunani na shi ne Amma se Naga Ammi haka muka danyi magana sama sama tana fada min naje na Kara duba Anty Rumasa’u nace Tom, tana kashe wayar se na saki kukan da nake ta rikewa, na janyo wayar Ina Kara jin audio notes din da mukai exchanging ta WhatsApp da Kuma daddar hirar mu, I felt heartbroken! Nayi kuka ranar har fuskata ta kumbura, Bayan na Gama na wanke fuskata na kwanta tareda wiping duka chat din mu na goge contact din shi daga wayata! Tirkashi fadan masoya ai hutu ne!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *