KALLON KITSE CHAPTER 4

KALLON KITSE CHAPTER 4

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Bata kalle shiba tace “a’ah nagode, Allah ba komai, ya jere da ita suna tafiya, “kin gane ko bai kamata ace kina irin wannan wurin ba, so kizo muje inyi dropping dinki.

Ibrahim yace kibi shi, kada Ammi taji shiru. Ta danyi jim tace toh shikenan.

Da saurinsa yaje ya bude mata kofar gaba ta shiga, shima ya zagaya ya bude na tuki ya shiga, yace “a ina unguwar ku take? Ta fada masa cikin nutsuwa a hankali suke tafiya, kamshin turaren motar ya kasheta sai dadi takeji, ya tsunka mata tunani, “ya sunan ‘yan matan?. Tayi kamar bataji ba, saida ya kara da cewa dan Allah ki fadamin. Ta nisa tace “marly.

“what a sweet name? Nan kuwa kamar na taba ganinki wani wuri your face luck familia? Bata kalle shiba tace “uhm”.

Haka yaci gaba da tambayarta hanyar dazasu bi, har suka kai gidan magajiya, tace nan ne gidan.

Yayi parking “nagode. Ta fada tare da bude kofar,

ya zan iya zuwa gobe? Inaso in gabatar da kaina sosai zuwa gareki marliya.

Tayi shiru gashi mu ba’a bari muyi hira a gidan mu.

No dont tell me, at your age ace ana hanaki hira, kina fadamin bakida wanda ki keso kenan? Toh shikenan inaso inkara haduwa dake, ya za ayi kenan?

Ta langwabe kanta, saidai inbaka number ta.

“yes…yes bani. Ta fada masa yana sawa a wayarsa, yayi dialing tata ta soma ringing tace, saida safe.

Ta fice a guje, saida ya samu minti biyar a zaune inda yake, shi ya rasa meya haukansa, duk yaji yainyar ta shiga ransa ba kadanba, kamar ta fito ya sake kallonta, ashe haka mutum yake ji inya soma son mutum? Ya tambayi kansa. Jikinsa yayi sanyi lakwas a haka ya kama hanya ya tafi.

Tana labe a kofar gida tana lekensa saida ya tafi, sannan ta kira ibrahim yazo ya dauketa, tun a cikin mota suke dariyar keta, har saida suka isa.

Aranar celebraty akayi na musamman, bata taba tsammani abun zai zo da sauki haka ba, “gaskiya kin iya pretending marly baby, danaga kina acting din kamar ‘yar shekara sha tara.

Suka kwashe da dariya.

Ranar ta kasa barci saboda murna.

Washe gari tunda safe taje gun ammi, bayan sun gaisa, ammi tace “kinsan zan wuce london jibi, amma ke kinki ma ki shirya taki tafiyar bamunyi zamu hadu a dubai ba? Tasa idonta kasa tace, Ammi inada magana.

Hajiya magajiya lunke kaya takeyi, saita tsaya tareda kallon marliya, sai yanzu ta lura da yadda marliya ta rame, duk ta fita hayyacinta, meya sameta? Kar dai wani ciwo ya sameta?.

Ta tanbayi kanta, inko hakane na shiga uku ‘yar nan itace mai taimaka mini.

Haka ta sake fada a zuciyarta, tsam ta cire hanunta akan aikin data keyi, ta nemi wuri kusa da marliya ta zauna tace maganar me zaki fada min ina saurarenki.

Marliya ta gyara zama ta dubi mahaifiyarta cikin idon ta, “Ammi aure zanyi!!!.

“what? Wane irin magana ki keyine marliya?

“you hard me right Ammi maganar kenan aure zanyi, kuma ba wanda ya isa ya hanani.

Ammi tayi ajiyar zuciya ta kara duban ‘yarta cike da zagwadin jin amsar tambayar da zata je fawa ‘yarta, “wazaki auran? Itama ajiyar zuciya tayi, tace, wani bacholor ne, dan jihar kebbi 2 let jafar yazo yin wani course ne anan, amma asali a N.D.A yake, shi likita ne kuma soja ne.

“oh my God, kar dai dan yaro kike so marliya?

“eh toh bazai wuce thirty three ba.

Kinsan abunda kike fada marliya? He is five years younger than you?

“toh ai ammi ba haram bane, aiba akaina farau ba, kuma ba akaina za a daina ba, common Ammi nifa tunda inasonsa to koda shekara ashirin ne.

Ta juyar dakai gefe tace, “ina fatan yanada abunda zai dauke nauyi na dan kinsan fa dama kece mai bani, dan yanzu bazan iya…..”.

Ammi wannan ba abun damuwa bane zai iya kula da irinki goma ma, so abunda nakeso, inaso kisa hannu mu hadu, mu kamashi a hannu tukunna,”

“hey! Magajiya tasan ‘yarta tanada taurin kai, intasa abu a gabanta, to saita ga bayansa, kuma sau dayawa tana cin nasarar kudirinta, dan haka tasan ko yanzu za aci nasara shiyasa ma gabanta bai fadi sosai ba, tace dont worry my girl, zaki aure shi insha Allahu, ki saki ranki zan baki 100% hadin kai. “yauwa Ammi nagode, yau zai fara zuwa gidan mezamu shirya masa?

O.k, kice yau zan kasance da in-low dina, its going to be special, da kaina zanje kasuwa yanzu in sawo kayan girki.

“nagode Ammi, kamar kinsan jiya ban samu barciba, dan haka Ammi ni zanje in kwanta, yace zaozo da karfe biyar na yamma….yauwa na manta in fada miki Ammi, dole kiyi pretending as irin iyaye masu daukar addini da muhimman ci, ina nufin ki kasnce maisa hijjabi, sannan ki nuna masa mu masu tarbiyane.

“nida ko hijab bana dashi marliya.

“karki damu na dauko na hafsat, zan baki saiki sa.

Ahaka sukai ta shirin zuwan jafar alkali Bello,shima din matsuwa yayi lokaci yayi yaje ga wannan baby-face din da ya gani jiya, tunda ya fita sallar la’asar bai koma office ba, saiya wuce shopping mall yayi tsaraba, baisan ma nawa ya kasheba, da kayane ya cika boot din motarsa. Ya isa gida yayi wanka, ya shirya, kwarjininsa ya bayyana sosai, ya feshe jikinsa da turare.

Karfe biyar saura minti goma sha biyar yana harabar gidansu marliya, ita kuwa tana daki dadi ya cikata, 

ita kuwa tana daki dadi ya cikata, ta saka jallabiya light green da dan karamin hijab dai-dai lokacin da hajiya magajiya ta shigo, tace ya iso dame za a fara?

“haba Ammi ya zaki saka siket? Nace miki fa you have  to look decent, ga hijab din dana karbo nan ki saka.

“kewai meke damunki nagane duk kinbi kin zauce, saboda wannan dan karamin alhakin, kin manta irin sharrin da mukewa maza ne? Komai jin kansu da barazanarsu muna juyasu you dont need to pretend my dear.

“Ammi kinyi alkawarin bani hadin kai, dan haka inaso kiyi abunda nace, saboda wannan gayen is different from others am in love with him.

Ta rike kafadarta “am sorry, zan baki hadin kai marliya, i promise to you.

Tayi ajiyar zuciya tace, thank you,

a lokacin kaninta mansur ya shigo, sister bakonki yana falo.

“yauwa thank you, amma inaso ka kama kanka, banaso ka rinka shishige masa, ka ganeko?

“nawa za a bani in na hada kai daku? Tayi murmushi, “bet me, zaka so tayina, yayi dariya ya fita.

Ta iske shi ya dan kai bayansa a kujerar da yake zaune akai yana danna wayarsa, ta shigo tare da yin sallama, ya amsa ya koma zaune, ta sami wuri ta zauna tareda gaisheshi, yaji dasin yanda take kama kanta, sai yaji tana kara shiga ransa, ya amsa tareda da ajiye wayarsa kan centre table, “ya akayi aka bari na shigo cikin gida bayan baki fadiba?

Tadanyi jim kadan sannan tace, nima ban saniba, yayi murmushinsa mai kashe ‘yan mata yace, “toh kefa a gaskiy narasa dalili jiya na hadu dake amma harda kasa barci a daren jiya. Ina sonki marliya, kuma dan Allah ba maganar wata wasa ta kawoni ba.

Ta muskuta kadan tace bakomai Allah yasa mudai-daita.

Ya amsa mata, tamike, “ina zuwa.

Kayan ciye-ciye takawo masa, ba abunda baici ba, yanaci suna tba hira, ko ince ma shiyaketa zuba duminsa, ita kuwa daga eh sai a’a, haka hirar tasu taci gaba, sun sami kamar awa daya, sannan tace bari in kira Ammi ku gaisa.

Ta fita, yabita da kallo, yarinyar ta hade dayawa a idonsa, yana mamakin yanda son yarinyar yayi yawa atare dashi.

Haj. Magajiya ce tayi sallama, da sauri ya koma kasa, ta nemi wuri can nesa dashi tace, “Dan nan ya kake?. Ya sunkuyar da kansa kasa sosai yana gaidata.

Bayan sun gama tace jafar kake dan nan?

“eh hakane Ammi. Tace “toh ga dai marliya nan, amma sai ahankali, kasan yara, nidai kam ban taba haduwa dakaiba, amma sainaji ka kwanta min, da alama kai dan mutunci ne,kanada decipline dan haka na baka amanar marliya, tun daga yau, bata sauraran samari amma kai nayi mamakin da har ta kawoka gidan nan, dan haka arike amana.

“nagode, nagode Ammi, kuma zan rike amana, Allah yasaka da alkhairi, tamike ta fita, ya kallo marliya yace, toh ke kinji Ammi ta bani ke, har abada its means in fara shirye-shiryen aure kenan?.

Tayi masa kallon datasan zataja ra’ayinsa tace, in ni na amince kenan ko?

“toh nidai Ammi ta bani ke, dan haka nasan banida matsala.

Haka dinne kuwa, bai samu matsala ba, dan cikin wata biyu suka kamashi a hannu, zan iya cewa tun daga lokacin cinsu da shansu ya koma hannunsa, ko a labari yaji tana son abu toh gobe zai kaimata shi, cinsa da shansa ya koma gidan, dan a kullum sai yaje gidan sau uku, acan yake karin kumallo wanda akasa asirai kwamacala iri-iri yaci shi, duk da baya jin dadin abincin haka yake daurewa yaci, ya rinkayin kamar baitaba cin irin wannan abincin ba. Can kuwa wasu kyama ma suke bashi, acikin wata ukune da haduwarsu yaje ya fadawa inna, ai kuwa bayan komawarsa da sati biyu akaje tambaya, abun mamaki su baba yunusa da kawu hashimu da wani Alh. Sabi’u limamin masallacin baba yunusa, sukaje neman aure yadda sukaga irin tarbar da akayi musu shiya fara daure musu kai, wani matashine ya amshesu da ganinsa bai wuce warin jafar din ba, sannan ko ruwa saida suka roka, sannan aka basu, abun mamaki shima ruwan a kananan kofi, abunda suka lura dashi, jafar baima damu da abunda ke faruwa ba, baba yunusa yace sunaso su biya kudin komai a yau, harda sadaki saboda gari da nisa, kawu hashimu yace, inma da dama sai asa rana.

Saurayin yace angama duk abunda aka shirya dai-dai ne, saboda shima yafi so next month a daura auren in sun shirya.

Eh kam mu a shirye  muke, sai ayi wami watan, sha shida ga watan dan yakama ranar asabar kenan,

yayi dai-dai dasai mata sun kawo lehe.

An yake sadaki akan nauyin gold, waisu da gold suke sadaki, dan haka saida  aka zabo gold dankarere na kusan dubu dari uku da hamsin, harda ‘yan canji akai.

Ya biya kudin shiga gida dubu dari da hamsin, sannan su dabino dasu sweet duk aka hada aka kai musu,

washe gari da zasu tafi baba yunusa duk jikinsa yayi sanyi saboda tausayin jafaryasan ba karamin rayuwa ya shiga ba……”saida ya gansuma ya gano ba ‘yan ainihin maiduguri bane, ‘yan sadakayalla ne, tunda a maiduguri a kwaisu ai kuwa hashimu yace,  “muyi masa addu’a ba abunda zai sameshi in Allah ya yarda,

yayi ajiyar zuciya anya zamu fadawa fatima wannan labarin?

“a’a karmu fada mata, mu nuna mata komai yayi dai-dai, in muka fada mata tana iya hanawa.

“toh amma in muka boye mata kanmu muka cuta hashimu saboda bamu kyauta mataba, bamu kuma kyautawa jafar din ba…….jafar ne yayi sallama ya nemi wuri ya ajiye musu abincin karin daya siyo musu, ya sami wuri ya zauna, sannan ya gaidasu, kawu yace, “jafaru anya wannan aure da kake nema zaiyi tasiri a rayuwarka?.

Gaban jafar ya fadi, ya dago kansa, yace, baba meka gani ne?

“gani nayi wannan gidan ba gidan mutunci bane, kobaka lura bane?

Baba yunusa yayi saurin amsar maganan, kar kaje son zuciya ya saka cikin halaka, dan nan idan fatima taji bazata yarda ayi wannan auren ba.

Ai kuwa jafar kuka ya saka musu wiwi, saikace karamin yaro.

Nan da nan kuma hankalinsu ya tashi, ya rinka fadin don Allah baba kar ku fadamata, inason marliya, wallahi aka fasayi da ita, toh bazanyi aure ba, har in mutu.

Sunajin haka sukace bazamu fadaba jafaru, tunda ai kai zaka zauna da abarka, ba damuba, zamu baka hadin kai, yi hakuri kabar kukan hakanan. Jafar ya share kwallah yana godiya.

Da yake jirgi suka shiga nan da nan suka isa kebbi, sun kaiwa haj. Fatima labarin komai, amma banda lala cewar wurin, tayi farin ciki sosai, don ko ba komai ta matsu dan nata yayi aure, hatta kudin sadaki basu fada mata ainihin abinda aka biya, dubu dari sukace, amma duk da haka saida ta jinjina wannan kudin.

Bayan jafar ya bar airport gun lawal ya wuce, yana fada masa ansa ranar bikinsu da marliya, lawal akoda yaushe abun na daure masa kai, ya danyi ajiyar zuciya dama jafar kana nan kan bakanka, saika auri yarinyar nan, bayan nabaka labarinsu da ita da ‘yan uwanta? Why? Meyasa zaka auri tsohuwa a tsofaffin ma kucaka? Don Allah ka……”

“indai haka zaka rinka yimin, duk in an zomaka da maganar marliya, toh wallahi zan daina zuwa, kuma wallahi zan iya rabuwa da duk wanda yace zai rabamu.

Lawal yace, meya dameni? Allah ya baka hakuri, ni inta nine ka hada guda dari irin su meya dameni? Nidai na fadamaka gaskiya ne, tsakanina dakai na abokan juna, amma tunda baka ganeba its o.k. Ai bani zan zauna da itaba, she is all yours, Allah ya ganar dakai.

Idanun jafar sukai jajir yama rasa me zai cewa lawal, amma ba yadda zaiyi, dole ya hakura da duk wulakancin dazaiyi masa, saboda anan kam shi kadai ne abokin shawararsa dan bai yadda da kowa ba, kamar yadda ya yadda da lawal, dan haka sai ya maida abun wasa yace, “dama ni zan zauna da abita, dan haka kai dan kallo ne, ba ruwanka, inaso muje dakai gun marliya a matsayin babban aboki, dan ashirya komai, ka gane ko? Amma bance kaje kata yaba maganaba, kamar ranar farko da nayi introducing dinka, don ranar kaban haushi.

“nasani ai , well its your life, dan haka zanyi abunda ya kamata.

“thank you my friend zamuje gobe da daddare zan zo in daukeka.

Kudi yaba marliya ta fara sayayyan kayan aure, shi kuwa wani yaronsa emmer yaba kudi yaje kano ya siyo masa atamfofi, shima din ya shiga shaguna duk abunda ya burgeshi saiya saya, akalla saida suka sai kaya set dari, banda gyale da under wears, abun nayi ne, dan dai jafar ya kashe kudi ba kadan ba, inka ganshi ya zama abun tausayi, duk ya rame, yayi fari dan dama shi fari ne, troly ce manya-manya guda biyar, duk an cikasu da kaya, sai masu binsu guda hudu, sai kanana guda uku da kit. A dakinsa ya ajiye akwatinan, ana saura sati daya daurin aure, zainab da salaha, da matan Alh. Yunusa su biyu da wasu kannan mahaifinsa goggoninsa su uku, ta wurin inna kuwa su shida suka hadu, saura sai ana saura kwana biyu daurin aure zasuje da mota, amma wadannan da jirgi zasuje.

Da karfe dayan rana suka isa, mota biyu suka shiga shida lawal daya jeep ce ta daukesu, kai tsaye gidan jafar suka nufa, da yake gidan ba laifi yanada girma, four bed room ne da makeken falo, anacin abinci ya shigo suka kara gaisawa, ya kira emmer yace yaje ya dauko akwatina su duba, in akwai abunda za a kara, sai a kara.

Da emmer ya soma fito da akwatina kallon juna suka farayi, dan abun ya basu tsoro, abu kamar hauka, akwati goma sha hudu. Inji zainab ta fadawa salaha a kunne.

Salaha kuwa sai girgiza kai take, tama kasa magana, sai ajiyar zuciya, da kyar emmer ke daukosu, duk da yadda yake jin karfi. Daya gama salaha da goggo mairo suka soma budewa, ya mike yace ina zuwa, bari inje in dawo kafin ku gama.”

“toh kai ba anan bane za a kawo amarya munzo mun tare?

“a’a ai insha Allahu next month zan gama course dina, in koma kaduna, dan haka sukace gara abar jere sai an koma kaduna, sai ayi.

Tace “toh aina zata zauna yanzu?.

Ya nuna dakinsa, a wancan dakin zata zauna, akwai gidan abokina daya aramin da yake shima iyalansa na kaduna, acan zansa sauran baki.

Toh Allah yasa ayi lafiya.

Tunda suka bude kaya suke mamaki,

Babu abun banza aciki, duk kayana ne masu tsada, hatta takalma daga gucci sai vince ire-irensu aka saka, ko waye abun na bashi mamaki, zainab tace, lallai kuwa Allah yasa alheri.

Da daddare suka kwashi akwatuna musamman akori-kura aka samo musu suka kwashe, sukuma suka shiga jeep, saidai ba dukkansu suka tafi, daga zainab sai salaha, goggo mariya da goggo zulaihat matar Alh. Yunusa, su shida suka kama hanya,.

Suna isa aka bude get suka fito, abun mamaki ba wacce ta fito tarbarsu, har saida sukayiwa mai gadi magana, “shin mutanen gidan na nan kuwa? Yace suna nan, inaga suna sama, bari inyi musu magana.

Da yake babu wurin zama a kasa haka sukayi cirko-cirko a tsaye, sunfi karfin minti goma sha biyar, har zainab ta fara tsekuwa tace, “kodai ba a fada musu zuwan mu bane? Uhm! Bari ku gani”.

Ta hau har sama abun mamaki mata ta gani sunkai su bakwai a zaune, ko wacce ta kame a kujera kamar sarauniya, sun caba kwalliya, tayi sallama ta karasa ciki da fara’a tace, “mutan gidan ashe kuna nan, muna can muna jira azo ayi mana iso? Ga kaya can dan Allah azo a tayamu dauka.

Dayansu tamike tayi ciki, sai tafito tace “sannu dai, ai sai kuyi kokari ku dauko, dan gaskiya mu bazamu taimaka mukuba, haka zaku rike mana ‘ya kenan sai mun taimaka muku?.

Baki daya falon suka kwashe da dariya, suka shareta, ta koma kasa, fuskarta ba kyau, salaha ta biyota, “ya akayi yaya?

“menene ba ayiba, wai mu dauki kayan mukai sama, su bazasu iya taimakawa ba.

“tabdijam me suke nufi? Mu zamu dauki kayan mukai sama?.

Goggo mairo tace ba komai kuzo mu dauka, ai mune muke nema, kila al’adarsu ce haka.

Haka suka dunga daukar kaya suna kai sama, ba abunda yafi baya musu rai, kamar yanda suke masu wani irin kallon ko in kula, wani lokacin kuma suyi dariya. Saida akazo kan manya jakuna, salaha tace gaskiya goggo bazamu iyaba, musa mai gadi yakai da direba.”

“toh ai kila basa so namiji ya shigar musu gida.

Zainab dama haushi ya kamata, tace wallahi goggo saidai suji haushi, amma ba yanda za ayi mu wahalar da kanmu a banza, kai direba kira mai gadi kuzo ku tallabi kayan nan zuwa sama.

Mai gadi ya zaro ido yace, “kiyi hakuri basu bani iznin shiga gidansu ba, ai sai akoreni dan Allah kuyi hakuri.

Zainab taji haushi tace, kuzo sama goggo ku huta, ko ruwane kusha, dubi yadda kuka gaji? Basuyi musu ba dan gaskiya zainab ta fada, da suka isa falon saima juya musu baya da sukayi, can gefe suka samu wuri suka zauna, sai kallon-kallo akeyi. Can goggo ta mike ta isa tsakiyar falon tace “wai wannan mutane kunsan darajar mutane kuwa? Ku sanifa aure muka zo nema, sannan kunsan dai inda ba dan ya so ‘yarku ba da baku ganmu nan ba, toh ga kaya nan, mun kawo Allah yasa ayi lafiya, ku tashi mutafi.

Da suka fita cema driver sukayi su wuce masauki, acikin mota mita sukai tayi jafaru ya dauko musu wulakanci. Salaha tace ni ai matsuwa nayi in fito kunji wani karni a gidan, anya ‘yan maiduguri ne mutanen nan kuwa? Kowa dai yasan ‘yan maiduguri da turare.

“a toh kedai kya fada, nikam bari mukai dole in kira inna in fada mata irin mutanen da jafar ya jajibo mana.”

“a’a zainab kada ki tada mata hankali, kin san fa bazataji dadi ba. Saboda haka ki bari har sai munje gida, duk abunda za ayi sai ayi.

Zulaihat tace ko kunsan sadakinta dubu dari uku da hamsin da wani abune?

“ke don Allah? Amma jafar cewa yayi dubu dari ne.”

“uhm haka suka shirya da iyayensa maza, suma haka suka cewa inna, saboda jafar kuka ya rinka yi musu tamkar karamin yaro, shiyasa suka rufe abun, don haka muma ba ruwan mu, dan sun ja mashi kunne yaki.

Zainab tace shikenan kuma sai musa masa ido, dan ya nawa?.

Inji zainab shine karami dole shi ya kamata ya bimu, bamu zamu bishi ba.”

“amma kinsan ba yaro bane, da yanzu haka ya tasamma talatin ko?

“hakane, amma ai babba, babbane ako da yaushe karami take ganin na kasa dashi, dole muyi masa magana.”

sun isa gida sun iske shi zaune anata hira, yana jin horn ya fita da sauri ya taryesu, yanda yaga kowacce ta sha jinin jikinta, ya san akwai wani abu, ya nemi wuri ya zauna, su zainab kam kwanciya sukayi, dan sun gaji. Goggo mairo ce tace “jafaru anya mutanen nan sun san darajar ‘yan uwan miji kuwa?

Ya dan saki murmushi, “goggo su haka al’adarsu take.

“eh hakane tunda kai ba ayi maka, baka ga yanda suka wulakanta mu bane.

A take ya dauki waya ya danna numbers din marliya, kamar da gaske, nan kuwa duk barazana ce, dan ba abunda zai iya.

Goggo tace wa zaka kira?.

Yace “marliya zan kira in fada mata magana, dan menene zasu wulakanta min iyaye?.

Tace, toh ai ita bata saniba, iyayenta ne da laifi, in baka saniba ko ruwa basu bamuba bare kujerar zama.”

“tabdijam ai dole in samu Ammi in fada mata a yau suka karbi kudi guna, wai zasu taryeku, dole su shiryawa baki……..zainab ta katse shi, “nikam kasan Allah auren nan ba dole bane jafar, kayi hakuri ka nemi wata, kasan inda shanun gaba tasha ruwa, toh na bayama nan zata sha, ka hakura da auren nan ka nemi wata.

Idonsa sukayi jajir kamar garwashin wuta, ya dubi zaiba, “haba yaya ya zakice haka?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *