UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 1 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 1 BY SHATU

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kamar yadda kullum nake fada mishi yau ma haka na Kara maimaitawa cikin kunnuwan shi+

” Wallahi! Kaji na rantse Babu wata Mata da zata juya ni a cikin gidannan! Yadda take jin aurar ta kayi Nima haka ka aureni, I’ve sense of belonging a cikin gidannan…”

Katse ni yayi saboda na lura ya gaji da jin maganganu na

” Meye matsalar ki ne? Yanzun ni ban Isa nace ki bar Abu ki Bari ba kenan?”

Na kalleshi Ina sassauta abinda nake ji a zuciyata nace

“Kuji wata magana? Me kace na daina ban daina ba? Kafi kowa sanin bani da matsala, ni bani da fitina Amma ni bana Bari, baza ayimin Abu na Bari yayi sliding haka kurum ba! Wallahi se na rama”

Zama yayi yana dafe kanshi, showing me his tiredness akan maganar da nake Yi. saboda Ina son shi, son da nake mishi ba kadan bane,it’s immeasurable se naji ban jin dadin yanayin da yake ciki, Amma kuma bazan iya dauke kaina akan abubuwa da dama ba,inada tsoro, tsoron da nake kada Nima ayimin abinda akai yiwa uwata, bazan dauka ba. Shiyasa tun kafin ya aureni na fada Masa a zuciyata inada kullin kishiya,babban tanadi nayi Mata, saboda ni uwata ta Zama UWARGIDAN BAHAUSHE, Bata ji dadi a hannun kishiya ba, haka Nima bazan Bari ta faru akaina ba. Idan ta zauna lafiya Dani I’m a peaceful person idan ta nuna way round ni kuma Zan nuna Mata lallai Nima Yar yau ce.

Ganin har lokacin ina tsaye a kanshi bani da niyyar Zama yasa ya Mike ya Kama hannuna tareda Dan matsawa kadan, hakan yasa na kalleshi cikin idanu, da sauri na sunkuyar da kaina Ina tura baki nace

” Saboda kasan wannan shi ne rauni na shi ne zaka min hakan?”

Se yayi dariya kadan yace

” To ya zanyi? tunda kin koya rigima bani da wani solution kuma, for goodness sake ba Zaki barni na huta ba?”

Zama nayi gefen shi Ina tura mishi baki nace

” Ni na fada maka ka dauke kanka, kayi kamar baka gani ba..”

Bai ma barni na gama maganar ba ya hade bakin mu guri daya, seda muka nutsu na ture shi nace

” This is cheating!”

Ya Mike Yana wani irin murmushi yace

“Ko? Ai nasan idan ba hakan na Miki ba bakin ba zai rufu ba, kuma Naga kema you were submissive!”

Kaina na girgiza na barshi kwance bakin gadon na fita parlona, na Jima tsaye Ina kallon parlon ba tareda nasan tunanin me nake ba, hannun shi naji ya zagaye kuguna hakan yasa nayi firgigit na dube shi, da idanun shi yake tambayata akwai wani Abu se na girgiza kaina kawai.

Wajen karfe Tara ya shigo part dina, Ina kwance a parlor na kammalla dukkan abinda ya kamata nayi, shi daya nake jira ya shigo mu kwanta, gefena ya zauna tareda Kama hannuna yace

” Sub ya Kare ne?”

Ganin bana kallo, TV dinma a kashe. Kaina na girgiza na tashi na zauna nace

” Ko daya, kawai na gaji da kallon ne”

Se yayi murmushi tareda fadin

” To tashi muje mu kwanta!”

Mikewa nayi Bayan na kakashe bulbs da fankoki na kuma rufe kofa, take Ammah ta fado min, kullum zamu rufe kofa se ta jadaddda Mana kan addua kafin a rufe kofar. Na tofa Auzhu bi kallimattillahi tamatti min sharri ma khalaq! Sau uku sannan na juyo, Yana tsaye yana kallona na shiga kitchen na gama sannan na wuce bedroom din shi. Gefen shi ya nuna min hakan yasa naje na zauna tareda kwantar da kaina kan kafadar shi, hannuna ya rike cikin nashi, se na Kai dubana kan hannun and I found out hannuna yayi karami cikin palm din shi Amma kuma it perfectly fit in.

“Sofy!”

Na kalleshi Dan nasan maganar babba zaayi, ban amsa ba Amma yasan Ina jin shi

” Fada min idan akwai abinda kike ganin Ina Yi muku na rashin adalci ke da Kubra a zaman mu”

Dago kaina nayi daga kafadar shi na kalla idanun shi nace

” To me ya kawo wannan maganar kuma? Babu komai fa, ni na fada maka tunda na aureka I don’t have problem whatsoever da Kai, kullum kokarin kwatanta adalci kakeyi! Ni matsalata matar ka ce”

Yayi shiru yana kallona, yanzun kafin ya shigo ya daga wajen Kubra yake same tambayar da yayi Mata kuma amsar data bashi kusan iri daya ce , though ita tace ni fitsararriya ce bani da kunya.

” Kimin alfarma ki zauna lafiya keda ita. Dan Allah Sofy!”

Murmushi na Masa nace

” Tohm!”

Se ya rungume ni daga haka kuma we became so intimate and affectionate, darennan jin shi nake Yi kamar shi ne dare na na farko da shi.

              ***

Sunana Safiyya Amma mafi yawan mutane Sofy suke ce min bansani ba ko saboda Ammah ma haka take fada min, shiyasa kowa ke fada min hakan. Na yadda nickname Bai fiya bin ka ba se idan mahaifiyar ka na fada maka itama. Mahaifina Baba Dan asalin gumel me ta jihar jigawa, mahaifin shi wato kakana shi baffan sarkin garin ne, kenan mahaifina cousins suke da me martaba sarki! Gumel lautai birnin mamman! Shi ne kirarin mu. Mahaifiyata Ammah Yar malam madori ce. Abinda na sani mahaifan su abokai ne. Baba shi ne na uku a gidan su mafi yawancin Yan uwanshi to Mata ne, sauran kadan daga ciki su ne maza. Kasancewar shi ya fito daga gidan sarauta yasa Babu Wanda baiyi karatu ba a gidan, ni Baba bama a Nigeria yayi ba, lokacin colonialism aka tura shi London yayi karatu. Yana dawowa ya fara aiki a matsayin likita Wanda babban cigaba ne ga gidan su da garin baki daya. Bai Jima da dawowa ba aka fara pressurizing din shi akan yayi aure, lokaci yayi me zai zauna jira, tunda Yana aiki ai kawai yayi aure. Baba irin introvert mutanen Nanne da a muryar su zaka fahimci sanyin halin su. Matar da ya fara nema a wani gari take Dan ladin gumel, shi bama shi ya neme ta ba, babanta ya Masa alkawari saboda yayi jinya, Baba happens to be the doctor in charge, yayi musu kokari shi kuma ya saka masa da bashi Yar shi ya aura. Akai dukkan formalities se jiran ranar biki kawai, ranar daurin aure tazo abin mamaki Ashe tunda baban yace Mata zata auri Abdullahi likita ake drama da ita, tace ita ba zata aura Wanda baya son ta ba kawai zai Mata Kara ne, ita tana da Wanda take so . Baban yayi kokarin ganin ya danne abin da duka da zagi har ta rusuna, Ashe iya baki ne kawai Bata rusuna ba. Idan Baba yaje zance zata fito su gaisa Amma ba zata ce komai ba kuma, shi wani negativity shi ne last thing da ya kawo a ranshi. Asubar ranar daurin aure ta gudu da wannan saurayin nata, ba kuma a ankare ba seda aka taru daurin aure aka fahimta, babanta ya rasa me yake damun shi, ya Tara manyan mutane an samu matsala, ya zaiyi Dole ya fito ya bayyana halin da ake ciki, mafi yawan Yan uwan shi musamman matan were against auren, a cewar su Bata da ilimi balle wayewa da zata shigo family kamar nasu.shi kenan se luck ya fada hannun su aka fasa auren Amma kuma se Alhajin malam madori ya fitar da Baffan gumel kunya, yace shi yasan ya Isa da Yar shi Dan hakan ya Basu auren Hajara wato Ammah. Wannan shi ake Kira da rabo idan ya rantse!

Aka daura aure, sannan Suka tafi gumel, Alhaji ya wuce malam madori, a wañnan lokacin normal Abu ne kawai ka shigo gida kace ka bada Yar ka, matar ka da yarka zasu karba zancen hannu bibbiyu, shiyasa nake ganin Mata sunyi biyayyar aure dukda yanzun wasu sun bijire Amma Ina ganin circumstances ke kawo hakan. Da yaje gidan Bai fada ba se dare sannan ya samu Mahaifiyar Ammah ya fada mata, tayi shiru sannan tace

” Indai hakan ya maka Babu damuwa!”

Ya kalleta yana iya hango rashin jin dadi a fuskarta, karewa Ammah na makaranta a aji biyar na secondary

” Nasan zakiji ban kyauta ba, ga yayunta ban dauka kowa ba se ita, saboda ku din nasan na Isa daku. Nasan anan zaayi min biyayya!”

A hankali tace

” To ya makomar karatun ta”

” Ya danganta da abinda mijin ta yace, idan zata cigaba shikenan, ni yanzun ta fita a hannuna, na karba sadakin ta”

Ta gyada kanta alamar ta fahimta, sede tana jin kamar an tauye mahaifiyata, a lokacin Alhaji Yana da damar gindaya sharaddin Dole zata karasa secondary kuma ya zauna tunda dai shi yayi musu halarci, to Amma a kullum namiji namiji ne! Tunda maganar ta fita sauran matan gidan ke zunden kakata, suna fadin ya daya da aka kwallafawa Rai kuma anyi auren sadaka da ita, Bata ce komai ba sede kawai ta cigaba da aikinta Amma abin damunta yake kamar zai kada ita!Ammi na makaranta Bata ma San wainar da ake toyawa ba a gida, tsam da ranta tana can tana karatu with the high hopes of ta gama karatun ta  ta Zama abinda a karamin garin su zata Zama abinda kowa zaiyi alfahari da ita, musamman dake girl child education is not that rampant a wañnan lokacin.+

Idan da zaa tambayeni Zan iya cewa worst feeling shi ne kaga an Yi maka katsalandan a cikin rayuwarka, duk da dai ya halatta ka zabawa yarka Miji but ba wai kayi forcing dinta cikin auren Wanda Bata taba gani ba. Bayan auren seda aka Kara sati har bakwai kafin akai ma su Ammina hutu, irin wannan farin cikin da kake ji cikin rayuwarka, daga wannan term din zakai waec shi kenan ka Gama secondary School gaba ki daya! Tunda ta shigo gida taji ta so different ba kamar ko da yaushe ba, ta Saba idan ta dawo Babu inda mahaifiyar ta ke zuwa, zasu kule daki suyi ta hira musamman idan Bata da girki ranar, Amma wannan Karan Kam tunda Suka gaisa se mahaifiyar ta ta fice zuwa tsakar gida tana kirkiro ayyuka duk Dan kada su kadaice balle ta Mata wata tambaya.

Can yamma Ammi ta samu Mahaifiyar ta a tsakar gida tana zaune Babu abinda take se kallon yaran gidan dake shige da fice da kuma wasanni a tsakar gida, dan Babu karya suna da yawa a gidan ita dai kadai ce a gurin mahaifiyar ta! Gefen ta ta zauna tace

” Baba ya Kika zo nan Kika zauna kuma? Kin barni ni daya kawai a daki”

Kallonta tayi da murmushi tace

” Dakin ne zafi”

Da mamaki Ammi ta kalleta jin amsar data Bata amma se Bata Kara magana ba kuma, Daga nan Suka fara hira sosae kowa Yana wucewa Yana kallon su masu dariya suna dariya masu yada magana nayi, idan da sabo sun riga da sun Saba shiyasa Ammi Bata kawo komai ba. Wajen sallar maghrib gidan ya sarara da hayaniya kowa ya koma daki, Ammi ta dakko fitilar kwai ta kunna sannan tayi sallah,6

” Baba shiru har yanzun Alhaji Bai dawo ba”

Yace Mata

” Zai shigo yanzun inshallah, yi kokari kiyi wanka dai”

Ta mike ta zo tsakar gida ta ja ruwa a rijiya ta Kara da Wanda Baba ta Bata na zafi, tun tana bandaki take jin maganar Alhaji, ta dinga murna har ta fito sede baya tsakar gida Yana can dakin innah uwar gidan su. Dakin taje ta tarar Baba ta fito Mata da wata atamfa me kyau, se kanshi kayan sukeyi. Kallon kayan tayi da alamar tambaya tace

” Baba wannan kayan Zan saka? To nida zanyi bacci ma”

Da yake dakin Babu yalwar haske sosae shiyasa Bata ga yanayin dake fuskar Babar tata ba, tace

” Ki saka kawai”

Bata Kara cewa komai ba ta saka kayan ta zauna gefen gado, Bata Jima ba taji sallamar Alhaji, cikeda murna ta Mike tana ta murmushi yace

” Alhaji sannu da dawowa”

Shima murnar yake yace

” Uwata ta kaina, ya makaranta?”

Suka zauna tana ta bashi labarin extra couching da ake musu na waec, seda ta gama sannan Shima ya fara Mata nashi bayanin, tunda ya fara Mata maganar yarda da kaddara taji kawai atmosphere ta Zama dull, gabanta Yana ta faduwa, seda ya gama sannan ya fada Mata ya Mata aure. Dukkansu tunani suke irin ihun da zatai Amma se tayi murmushi kawai tace

” To Alhaji nagode Amma Zan karasa secondary Dina?”

A farko baiyi wannan tunanin ba, dan shi numfin shi ta kammalla karatu kenan, Amma ganin yadda ta bashi hadin Kai yasa yace Mata ya Mata alkawari. Ya sanar Mata mijin nata Yana Hanya zai karaso kowanne lokaci Yana data su sasaanta Allah ya Mata albarka. Daga haka ya fita zuwa masallaci, tabbas a zuciyar ta taji Babu dadi Amma kuma ita dama ba saurayi gare ta ba balle ta damu, wannan lokacin babban burinta karatun ta, to tunda Bai taba Mata karatun ta ba ai komai me sauki ne. Baba ta Mata nasiha itama sannan sukai sallah, baa Jima ba yayanta yazo yace taje Alhaji na Kira ta, anan gabanta ya dinga faduwa tana tunanin yadda zai amshe ta, karfin gwiwar da Baba kw Bata yasa ta yafa mayafin dake kanshi ta fita, a kofar gidan ta same su akan tabarma suna gaida Alhaji, Yana ganin ta ya Mike ya Basu guri tunda waje ne bazai yiwu yayi musu nasiha ba se yace su shiga ciki su same shi. A sitting room din shi Suka zauna yayi musu nasiha sosae sannan ya fita, lokacin ne ta gaishe su tana sunkuyar da Kai. Abokin shi yace

” To Babandi kayi shiru, Amarya ga Angonki na kawo Miki shi”

Batace koami ba, ganin hakan abokin ya fita se lokacin ya samu ya daidaita kanshi ya fara Mata magana, a hankali take amsawa a karshe yace Mata

” Bazan taba manta hallacin da kikai min ba, a gurina Zaki Zama tauraruwa wadda hasken ta bazai taba gushewa ba”

Inaga Ammi ba zata taba manta wannan maganar ba, saboda halfway Baba ya cika alkawarin but along the way se ya karkace, na kan so yiwa Baba uzuri Amma wani lokacin se naji na gagara, zuciyata na kuncin yadda ake yiwa uwata Abu.

Har cikin gida Suka shiga ta raka shi dukka dakuna abokan zaman Baba, ya gaishe su sannan ya dawo dakin Baba ya gaishe ta cikin mutunci da karammawa da kuma bada girma. 

Tunda ya tafi Inna ta tada masifa tsakar gida akan Alhaji ya cice ta yasan tana da Yara Mata da suka Isa aure Amma ta rasa dawa zai hada auren seda Ammi, ta dinga masifa bayan yasan gidan hutu ne, Babu Wanda ya kulata cikin su Ammi se sauran Yan koronta shikam Alhaji ko kallonta baiyi ba.

Baa dauka lokaci ba aka yanke ranar yini, akai biki sannan suka dauki amaryar su Suka kaita gumel, anan akai biki na gani na fada sannan aka watse taro. A gidan su Baba Ammi ta kwana se da sukai sati daya sannan Suka shirya zata koma katsina inda yake aiki!

Na yadda a kowanne aure tabbas there are bound to problems, yadda aka ce idan kayi aure ka cika rabin addinin ka then se mu saka a ranmu ba Abu bane me sauki Dole akwai jarabbawa da zasu shiga cikin rayuwar ku. Tun kafin Ammi tasan cewar anyi Mata aure dangin mahaifina were strongly against auren, suna ganin a dangi irin nasu, masu kudi Yan boko haka kuma Yan sarauta, wayayyu ta Yaya zaa auro musu yarinyar talakawa wadda ko wayewa Bata dashi balle tayi suiting taste dinsu. Amma sede a gani na Mata mune matsalar kanmu, mu muke karawa kanmu matsaloli. Dukkan mu aure muke cikin wani dangin Amma se muce matar da aka auro a gidan mu ba zata zauna lafiya ba, bayan muma a wani family muke Kuma idan da zaa Mana yadda muke Mata se munfi kowa korafi, Amma hakan ya Zama Abu ne a gidan BAHAUSHE.

1

Ba lallai ka fara ganin matsaloli ba har se lokaci ya Dan ja, se Zama Zama yayi zama kafin halin kowa ke bayyana, kafin kowa ya bude jakar halayens hi ya kasa nashi. Kwanan Ammi biyar a gumel sannan Suka koma funtua, a wañnan Dan zaman da tayi Babu wani Abu da zata iya adarwa akan family dinsa, Dan kadan ta hadu dasu. Gidan da Suka fara Zama anan cikin quarters din asibiti yake. A zaman su sun dawammar dashi cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna. Tunda yasan cewar Bata kammalla secondary ba ya nema Mata makaranta anan makera dan tayi waec din, cikin hukuncin Allah ta fara karatun ta tana jin Babu wani matsala a tattare da ita, mijin ta na sonta suna zaman lafiya sannan kuma tana karatun ta. Bayan wata daya da biki aka fara Shirin sallar Gani, duk Wanda yasan Yan Gumel yasan yadda suke mutunta sallar Gani wani lokacin ma sunfi ji da ita Akan sallah karama ko babba!

Tun saura sati daya Suka dauki hanya saboda Yana son tadan jajje gurin Yan uwanshi su saba. Haka suka tafi Gumel da farin ciki. Suna zuwa Kano ya nufi da Ammi gidan babbar yayar shi Ummaah. Anan sallari take, tana auren Dan sarkin Kano. Suka je gidan tunda ta fito take ma Ammi wani irin kallo irin na kaskancin nan. Ammi ta dakko har kasa ta gaida Ummaah, ciki ciki ta amsa ta maida hankalin ta kan Dan uwanta, sunata hira ta maida Ammi kamar ma baa hallice ta a wajen ba. Ana Kiran azahar ya tafi masallaci itama ta Mike tace da Ummaah zatayi alwala, se tace Mata taje bakin famfo tsakar gida tayi alwala, Ammi ta danyi Jim sannan tace Mata

” Ina son Zan Dan shiga bandaki ne”

Wani kallo ta Mata tace

” Badai bandaki na kike nufin Zaki shiga ba ko?”

Tana fadar haka ta juya ta shige ciki, tsakar gidan ta fito tana waige waige nan ta hanga bandaki ita kanta Bata ma lura da dattin da yayi ba seda ta gama abinda zatayi sannan taji amai na Neman durkusar da ita, Ammi mutum ce me tsafta, me kuma tsantsani Amma ta shiga wannan bayin, ko Dan BAHAUSHE yace idan kaji ana raka ni Kashi ba zawo bane!

A parlon tayi sallah sannan ta koma ta zauna tana ta rarraba idanu, Baba ya dawo shida me gidan Suka gaisa sosae da Ammi nan aka kawo abinci, Ummaah ma ta fito ta zauna tace

” Matar ka bakunta take, nayi nayi taci abinci taki ci wai a koshe take”

Da sauri Ammi ta dago ta kalleta se Kuma ta maida kanta kasa, Baba ya dubi Ummaah sannan ya dubi Ammi yace

” Mun ci abinci, ba bakunta bace”

Ya fada yana matsar da table din da aka jera abinci, shi yasan fulako matar shi tayi, ya kuma San from start Yan uwanshi Basu Santa tun kafin su ganta, so Dan ya Kare martabar ta shiyasa ya hakura da cin abincin. Daga karshe Bai Kara mintina goma ba Suka tafi, a irin wannan gidan ya kamata ace da zasu tafi an Mata kyauta Amma Koda shi kan shi Tafida yayi Mata Ummaah Bata bayar ba. Tunda suka fita ta daidaita yanayin fuskar ta tana kokarin yiwa Ummaah uzuri. Da yayi niyyar zasu je gidan Anty sakina Amma se ya fasa Suka nufi Gumel kawai. A gajiye Suka Isa, straight gidan su Baba suka wuce. A bangaren Gwoggo mahaifiyar Baba suka sauka, dattijuwar kirki me karamcin da tasan mutunci, ta musu tarba ta karamci dama tuni tasa an share gidan su tsaf, se dare suka tafi can. Ammi Bata ga komai ba se ranar da Suka hadu dukka ana gobe zaa fara sallar Gani, ita tana gidan ta ma Baba yace taje duk Yan uwanshi Mata da matan brothers din shi sun zo, ba yadda ta iya ta shirya cikin wata Dutch wax ta fita zuwa gidan, gidan a cike da jikoki da kuma Yaya Dan kusan Baba shi ne na karshen aure cikin Yan uwanshi, kunsan yadda yan boko suke!

Dukka suna zaune ana ta hira, ta shiga cikin sanyi murya, Gwoggo dake can karshen parlon ta fara fadin

” Sannu Hajara, kin karaso”

Kanta ta gyada da murmushi ta karasa ta gaida Gwoggo sannan ta dawo ta gaishe su daya Bayan daya Amma mutum biyu kawai Suka amsa Mata da dadin Rai, wasu ma Yi sukai kamar Basu ganta ba, ba tace komai ba ko yanayin fuskar ta ya canja ba ta samu guri ta zauna, sunata hira suna Shirin yadda gobe da jibi zata kasance. Ammi taji kamar hoto ko daya batayi fitting a gurin ba. Anty jidda kanwar Baba tace Mata ta tashi ta yiwa Yara wanka, dake hankalin Gwoggo ya koma kacokan kan wani abin yasa har ta fita Bata lura ba, yaran sun kusa biyar ko ma sunfi ga kiriniya haka ta dinga wanka kamar Yar aiki, tana gamawa ta shigo ciki Ummaah tace su hadu da Yan aikin ta su kwaba cincin da sauran abinda zaa bawa baki washegari, batayi musu ba ta wuce ta shiga cikin su Suka dinga aiki har maghrib. A irin wannan lokacin da suke taruwa dukka, mazan ma ana sallar maghrib suke shigowa, a tare Suka shigo Amma duk yadda Baba ya baza idanun ganin Ammi Amma shiru, ban sani ba ko Anty jidda ta manta Baba na gurin da Gwoggo tace

” Waccen bakauyiyar Hajaran ko me suke Basu Gama aikin ba”

Anty Ma’u matar Baba Zubair ta zungure ta, se tayi shiru tana rarraba idanu, Gwoggo tace

” Aiki kuka saka ta shiyasa tun dazun ban ganta ba? Me yasa kuke haka? Yanzun duk Yan aikin dake sashennan se kun saka ta aiki”

Se ta Mike kawai ta nufi kitchen din da kanta, ta samu tana sallah a Dan varrender kitchen din, Gwoggo taji ranta ya baci haka ta bada sakon ace tazo idan ta idar, komawa tayi ta dinga fada ta Hana kowa magana

“…kuna ganin ta yarinya shiyasa zaku cuce ta, ku sani Allah na kallon…”

Shigowar Ammi yasa tayi shiru, ta zauna tace

” Gwoggo sun ce kina Kirana?”

Gwoggo tace

” Aiki aka saka ki shi ne baki fada min ba”

Ta girgiza Kai tace

” A’a Gwoggo kawai naji na Taya su ne fa”

Babu Wanda ya yadda da abinda tace, se kawai Gwoggo tace ta zuba abinda zata ci, kadan ta zuba ta shiga ciki, babban yayan su Baffa Umaru ya fara fada yana nuna musu muhimmancin Ammi Amma Babu Wanda ya jishi kawai dai Dan Babu Wanda yakai abinda ya fada zuci. Wannan shi ne mafarin komai tun Ammi na Yi musu uzuri har ta fara yada da abinda zuciyar ta ke fada Mata akan tabbas basa sonta Amma ko say daya Bata taba nunawa Baba ba. Ta kammalla secondary Gwoggo tace lallai ya nema Mata makaranta ta cigaba idan ta goge Babu yadda Yan uwanshi zasuyi. Sede ana Shirin tafiya makaranta se ciki ya bullo jikinta me azahar wuya, tunda ta gane tanada ciki take karbar wuya irin ka shiga watanni sunyi nisa ka daina laulayi Abu ba fa Bai tsaya ba, haka nan har se da ta haihu sannan taji sauki.

Ni ce yarinyar fari a gidan mu, sunana Safiyya sunan Gwoggo, dake a can Gumel aka haifeni akai suna da komai , tace ita Bata son a boye min suna, ace min Safiyya Dita yadda kowa zai San sunan ta naci, duk da hakan se take cemin Sofy and shikenan Sofy ya bini!

Bayan suna Ammi da kanwar Babarta Yaya Talatu Suka zauna suna babbude kayan da aka kawo Mata na barka, kowa cikin katuwar leda ya kawo da sunan shi a manne, na dangin Baba kenan tunda ta fara budewa take cin Karo da kaya masu asalin kyau Kuma masu tsada, dukka na jarirai se Wanda Zan saka ko na shekara biyar, Amma abin mamamki ko fallen zani da zata daura Babu. Hatta kayan barka na alada da ake kawowa daga gurin miji kayan sawata where exceptionally beautiful Amma nata kadan sannan kuma duka Babu na kirki. Yaya Talatu ta kasa hakuri tace
+
” Ni Kam Hajara wanne irin kayan barka ne haka, kowa se ta yarinyar yake Banda taki”
Se tayi murmushi kawai ba tace komai ba, haka Dole seda Baba ya sake sayan wasu kayan na fitar suna da zata saka. Ranar suna dake ba cikin babban gidan akai taron ba, Babu Wanda ya leko idan ka dauke Anty Mannira immediate din Baba se Kuma Anty Rahma matar kanin Baba su kadai Suka leko, wasu ma Basu zo garin ba balle suzo sunan.
Bayan Ammi tayi arbain ta je yawan alada zuwa Danladin Gumel, kowa ya ganta se ya Kara kallonta ta Zama Yar gayu kana kallon ta kasan tana jin dadi sede kowanne Dan Adam ka gani kasan behind him lies a story, tayi sati sannan ta koma funtua. Matsalar da aka samu Baba Yana son Yan uwanshi kada ma Ummaah taji labari dukkansu suna sonta Kuma suna jin maganar ta kamar Gwoggo ce tayi magana. So Dan hakan se yayi shawara da ita Akan komawar Ammi makaranta, ya manta cewar alkawari yayi Kuma umarnin Gwoggo ne. Ummaah ta zuga shi tas tace kada ya Kai Ammi makaranta, su dinma duk secondary suka gama yanzun wanne ilimi take nema kuma., Da ya dawo gida se yace ma Ammi saboda ni banyi kwari ba ta Bari se ta yaye ni.
Bata Kara tayar da maganar ba saboda Bata da hayaniya, Ammi nada hakuri, tana da kawaici ni nasan da nayi gadon halinta da banyi taasar da nakeyi yanzun ba, kwata kwata halin mu sun banbanta, ni halaye na irin na dangin ubana ne, not munafurcin su, a’a fadan su da rashin hakuri nan nayo gado.  Tafiya ta tafi Babu irin kulawar da Baba Bai bamu ba nida Ammi, shiyasa a zuciyata nafi son Baba akan Ammi, Ina son shi ko laifin shi Ammi ta fada se ta bani hakuri saboda kiri Kiri nake nuna Mata Raina ya baci, ko na nuna bana son maganar, mafi yawancin lokaci idan tace min yayi kaza se na Bata rashin gaskiya dukda deep down inside me nasan shi ne bashi da gaskiya Amma uzuri kullum cikin Yi Masa nake. Ya nuna Mana soyayyar da dukkan mahaifi zai yiwa Yar shi, Zan iya cewa har extra miles yake zuwa.
Banyi shekara daya ba Ammi ta samu wani cikin, me laulayi Wanda yafi nawa, hakan Dole aka yaye ni aka ce a maida ni Gumel wajen Gwoggo, tunda Yan uwan Baba suka ganni suka dinga kananan magana, wai ta Zama akuya se haihuwa kawai take, burinta ta karya Masa tattalin arziki, shi kuma farin ciki yake a ganin shi compensation ne na aure da baiyi da wuri ba, at least ya Tara ko ya kamo sauran kannen shi. Wannan ne karon farko da ta fara samun shi tace
” Baban Sofy ko zamu zubar da cikin nan ne?”
” Saboda me?”
Hawaye Suka fara Mata zarya tace
” Baka jin abinda suke fada, kowa se tsangwama ta yake ana cemin akuya. Ni ya zanyi ya ake so nayi ne?”
Se ya fara lallashin ta Yana nuna Mata maganar su a banza take, decision dinsa shi ne abinda zatayi amfani dashi. Da wannan Suka cigaba da rainon ciki har ya Isa haihuwa, Bata taba zuwa wani taro da zai hadata da Yan Gumel ba duk Baba na Mata haka saboda kada su Bata Mata ranta Kuma anyi nasara Babu wani babban Abu da ya faru har cikin ya Isa haihuwa. Wannan karon ma mace ta Haifa, akai suna anan funtua aka saka Mata Rayhana sunan Baba ta Dan ladin gumel, itama baa boye Mata suna ba se take ce Mata Rayha!
Kowa yasan a alaadar bahaushe dangin Mata su ne kan gaba a suyar Naman suna, Amma a wajen mu abun se ya juya, Su Anty jidda da suka zo su suka soya Suka raba, ke Kya rantse da Allah Basu taba cin nama ba, Aa tsabar mulki ne da nuna su din gidan Dan uwansu ne. Mama mariya yayar Ammi ce da suke uba daya, ta kasa shiru ta fito tsakar gida tace
” Ni Kam Dan Allah Ina na taba jin dangin miji da suyar Naman suna?”
Anty jidda ta juyo tareda wurga Mata harara tace
” Gashi kin gani! Ko akwai Wanda ya Isa yace baza muyi ba”
Mama mariya tayi dariya tace
” A’a! Allah ya bada saa”
Ae se suka juya maganar ta Zama babba, gidan ya hautsune da fada, karshe Babu arziki haka Yan uwan Ammi Suka tattara Suka bar funtua ransu a bace, Ammi tayi kuka ta gode Allah saboda ba karamin cin mutunci sukai ma dangin ta ba. Koda Baba yazo Bai ma saurari maganar ba kawai yace tayi hakuri watarana zai wuce.
Aka wuce wannan guri, rayuwa ta cigaba da tafiya, Ammi tayi kokari sosae wajen ganin Bata shiga sabgar kowa ba, indai ba muhimmin Abu bane to Bata barin funtua, Dan nisan da mukai yasa aka Dan Jima Babu matsala! Rayha nada watanni hudu akai rasuwa a Gumel Dole Ammi ta tattara mu da Baba muka tafi Gumel. Muna zuwa ko cikin gida Bata shiga ba ta wuce gidan gaisuwar kafin ace tayi laifi, Rayha a bayanta ni kuma a hannunta, anan tayi gaisuwa ta samu Gwoggo da sauran na nan. Babu Wanda yace Mata ya muke itama Gwoggo kawai ta kuntawa Rayha ta gani, bayan ta Mata addua ta maida ta baya. Seda aka gama makoki Suka koma gida sannan da daddare ta gama Shirin bacci Baba ya shigo ranshi a bace, Wanda Abu ne da Bai cika faruwa ba, shi ne bacin ransa, it’s hard kaga ranshi a bace. Tunda suka hada idanu tasan an zigo shi, ya fara tambayar ta abinda ya faru gidan gaisuwa, tace ita Babu komai tunda ba zata tuna sunyi fada da wani ba, se yace me yasa Bata bawa su Ummaah Rayha sun ganta ba, tace Basu nema ba, aiko ya fara fada Yan uwanshi se sun nema zata Basu Yar su gani, ai ba ita kadai ke iko da Yar ba, itadai Bata ce Masa uffan ba ta kwanta kawai Amma ranta idan yayi dubu to ya baci, ta kasa gane wanne irin kaddara ce wannan,me yasa suke son incriminating dinta a wajen Baba. Har washegari Yana ta fushi, haka ta shirya ta Kai Rayha gidan Ummaah ta Bata hakuri, ta kalla Rayha tace inda Allah ya ceci yaran ma suna yin kyau, yanzun kuma se kiyi kokari ki haifi namiji , matan sun Isa haka.
Wannan fadar da tayi se ya Zama wani maganar, dukkansu Suka fara ce Mata uwar Mata, ta kasa haifar namiji, Kuma a cikin su akwai wadda Bata taba haihuwa ba, akwai wadda batada namiji ma baki daya!
Mun tashi nida Rayha tamkar Yan biyu, Bayan Kama da mukeyi se Kuma kanmu daya tunda fikon dake tsakanin mu baifi shekara daya ba. So hatta makaranta ma class dinmu daya aka kaimu, komai da ake Yi Mana iri daya Babu wani banbanci, Baba Ammi sun bamu tarbiyya daidai wadda zamu shiga cikin mutane mu kame, duk inda muka shiga se ance yaran nan sunada tarbiyya, tun a early years munsan idan Ammi tayi baki to zamu Basu guri, haka kowa yazo zamu tsugunna mu gaishe shi, gamu da kyau dukkan mu kamar Ammi muke se fari na dangin Baba, Suma Ammi farare ne Dan asalain Babar Ammi Yar malam madori ce, Kuma kowa yasan Yan malam madori sunfi Kama da kwarori. Duk wannan abin da tayi Bai sa ta wanku a gurin su Ummaah ba, se cewa sukai ai ta koya Mana iyayi da kwainane. To idan Bata fita ba se yaushe, anan na fahimci akwai mutanen da karka kuskura ka Bata lokacin ka wajen nuna musu good side dinka, bazasu taba fahimta ba Koda kuwan zaka yanka mahaifiyar ka ka Basu to wani se yayi complain. Akan Ammi na fahimci just live your life kada ka zauna impressing wasu.+
Tafiya tayi tafiya nakai shekara shida Rayha nada shekara biyar, Ammi Bata Kara haihuwa ba.munata karatu, se Baba ya tsiro da tafiya hutu,duk hutu se a kaimu gidan aunties din mu gurin cousins dinmu, Ammi Bata so Amma Bata taba fadawa Baba, sede Babu Wanda yake treating din mu wani iri kowa ya karbe mu hannu Bibbiyu, sun riga sun nuna cewar bamu bane ba da so Aa uwar mu ce Basu so. A hankali muka fara girma muka shiga primary halayen mu Suka fara bayyana. Ni banida hayaniya banida yawan surutu Amma ni kuma banida tsoro tun Muna Yara bana Bari wani ya taba ni, I’m a bookworm Ina son karatu, ko Muna Yara aka bamu homework Ina dawowa na cire uniform Zan dira akan shi, Ammi da kyar zata lallashe ni na yadda na dawo a islamiyya kafin nayi, ita Kam Rayha nada kokari Amma batada naci irin nawa, wani lokacin zata iya barin back pack dinta a makaranta, ko kuma ta dauka lunch box dinta ta bar school bag a gida, ita kawai tayi kwaliyya ta huta. But duk da hakan Ammi na kokarin daidai ta mu. Muna primary four Ammi ta Kara haihuwa, wannan Karan Baba yace Babu taron suna, so se ta samu lafiya, ko dangin ta Babu Wanda yazo se Mama Talatu, itama sati biyu kawai tayi ta tafi. Wannan karon ma mace ta Kara Haifa, me Kama Dani you can mistaken her for me, Kama muke sosae da Ammi. Sunan Ummaah taci, bayan min girma mukan tsokane ta wacece me sunan munafukai wadda aka saukar musu da surah guda, tayi ta kuka ta fadawa Ammi, se ta dinga Mana fada wai ai Babar mu ce, mudai jinta kawai muke.
Sunanta Furaira, saboda munin sunan Dole Ammi ta saka Mata Anisah. Ummaah Bata taba zuwa gidan mu ba se haihuwar Anisah, tunda aka ce sunan ta aka saka ta taho da goma ta arziki, ta kwana daya ta juya, Amma wannan kwanan se tace Ammi na almubazzarancin abinci, sannan ta sauke ta a dakin mu, to Ina zata kaita kwata kwata dakuna uku ne a gidan, dayan Babu komai a ciki se kayan wasan mu da shelves din karatu kamar dai play room dinmu ne hade da  study room. Daya namu bedroom dayan na Ammi da Baba, to lokacin da tazo Baba na gida ba call yake ba, Ina zata kaita.
Muka kammalla primary muka shiga secondary school da farko anan funtua zaa barmu, Amma Ammi tace yakaimu FGGC Bakori, haka aka kaimu boarding school. Komai namu iri daya da Rayha kana kallon mu ko baka son surname din mu ba kasan gidan mu daya, dukda mu munsan bama wani Kama kamar yadda ake zuzutawa kowa se yace mu Yan biyu ne se Ammi tace mu ce mu Yan biyu ne. Bamu Sha wahala ba saboda kowa son mu yake kunsan Yan biyu da farin jini, hatta kawayen mu daya , Babu wani wannan da kawar shi wai wannan da tashi, Ammi duk visiting take zuwa shi Kuma Baba duk bayan sati biyu yake zuwa.
Haka rayuwa ta tafi Ammi Bata bar kuncin da take ciki ba, bamu fara fahimtar abinda ake ciki ba se watarana anyi hutu zamu shiga js3 lokacin,muka tafi gidan Ummaah tana auren Danta Yaya Ammar , daga makaranta Baba da Ammi Suka dauke mu muka wuce Kano, tun a hanya naji Baba Yana ce Mata
” Nasan baki son zuwa bikinnan, Amma kiyi hakuri inshallah Babu abinda zai faru”
Bata ce komai ba, so kunsan intelligent people are very curious, for the rest of journey nake ta tunanin me ye Baba yake Bata hakuri, Kuma meye bazai faru ba, se na tuna lokuta da dama Ina ganin Ammi tana kuka idan Baba baya nan, bansan kukan me takeyi ba. Haka muka Isa Kano jikina duk yayi sanyi, Rayha Bata cemin menene nace Mata Babu komai. Ina rike da Anisah muka shiga gidan, dake karamin jiki ne dani irin na Ammi yasa zakai tunanin Rayha ce babba, dan Rayha already ta fara period Kuma haka boobs sun fara fito mata ni ce aka Bari a baya. Tun a lokacin ta fini tsayi. Tun daga gate Yaya Ayna’u ta karbi Anisah tana Mata Wasa tana fadin
” Uwata ta kaina”
Na tabe baki Dan yadda suke ji da Anisah ko ni dake da sunan Gwoggo albarka, muka gaishe ta tace
” Sofy Yan boarding, Rayha Allah ya taimake ki ke kan baki kwaso gajarta ba”
Minds din mu are clean, so baai exposing dinmu da habaici ko wani Abu ba shiyasa ban gane Ammi take yiwa baa ba, na dai San Bata gaishe ta ba. Muka shiga ciki,abinka da bikin manya gidan cike yake, straight gurin Anty Safara’u muka je, ta hade mu ta rungume tana cewa Ammi ya Hanya, sune kadan da suke son Ammi Wanda take sakewa a cikin su, daki ta kaimu muka zauna ta kawo Mana abinci Amma Ammi tace
” Anty Safara’u Bari naje mu gaisa da sauran kafin nazo mu ci abincin”
Tace
” Eh hakan yayi Amma bar yaran kije su su Dan huta”
Har zata fita se tace ai tunda yanzun zamu dawo gwara muje duka, se tace muje to tasan kaffa kaffa take ayi taro a watse lafiya. Tun a parlon naji muryar Anty jidda tana fadin
” Ni Kam har yanzun Ummaah har yanzun Hajara Bata zo ba”
Anty Hadiyya tace
” Wacece Hajara Kuma?”
Anty jidda tace
” A’a! Hajaran Babandi Mana”
Se Anty Hadiyya ta doka tsaki tace
” Kice kashi da Rai kawai, yo wannan meye amfanin zuwan ta, mts…”
Na kalli Ammi idanuna sun ciko da kwalla, ita Kuma Rayha ta Bata Rai se ta girgiza Mana Kai muka shiga da sallama, Suka bimu da kallo, Anty jidda ta nufo ni tana fadin
” Uwata Kuna Hanya Ashe”
Na Bata Rai na zauna gefen Ammi muka gaishe su, Ummaah tace
” To ku kuma da kuka nane Mata ciki zata maida ku ne? Ko kuma wani sabon kinibinbin ne?”
Juyawa tayi ta kallemu tana hararar mu, hakan yasa muka fahimci abinda take nufi, Rayha ta nufe su ni kuwa na Kara Bata fuska na kwantar da kaina kan kafadar Ammi tasan halin ya motsa baza ni ba kenan, janye jikinta tayi na kusa faduwa Anty Safara’u tace
” Dole Mana shiyasa Bata kiba, zo nan Sofy Ashe tsangwamar ta akeyi”
Ammi ta bude jakar ta Ciro sabbin 1000 notes bandit daya ta ajewa Ummaah tace
” Allah ya Sanya alkhairi!”
Daga haka ta Mike ta fita Zan bita tace
” Kina fitowa se naci ubanki!”
Nasan halin ta Sarai na koma Amma a wañnan shekarun nasan sun Bata ran uwata, gulmar ta suke, tazo Basu amsa gaisuwar taba se naji na tsane su, naji haushin su nake ji. Kamar yadda Baba yayi fata anyi biki lafiya aka watse, muka je Gumel sannan muka koma funtua.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *