KASHE FITILA CHAPTER 10 KARSHE END BY BATUUL MAMMAN

KASHE FITILA CHAPTER 10 KARSHE END BY BATUUL MAMMAN

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

Yakura wani karamin falo ta bude musu daga waje kofarsa take duka suka shiga suka zazzauna. Malam ne kadai akan kujera sauran kowa na kasa. Gimbi ya kalla a nutse ya soma magana bayan basmallah da korar shaidan.+

“Baiwar Allah Yaya sunanki?”

Ba karamin kwarjini gareshi a idonta ba tace Gimbiya.

“Na gaskiyar dai. Gimbiya ai ba suna bane”

A hankali ta fadi sunanta yadda ko Haj Fanta da tafi kusa da ita bata ji me tace ba.

“Sunanki mai daraja kuwa…ko zaki iya duba girman Allah ki fada min matsalarki batare da kinyiwa kowa karya ko sharri a cikin labarin ba?”

Dan tunani ta tsaya kamar bazata yi magana ba sai kuma ta fada masa abubuwan da suka faro tun daga lokacin da Awaisu yace zai dauko Maamu da komawarta  gida kafin su tare a sabon gidansu, zaman da tayi da Maamu, dinkewa da Anti Bebi da sakin da yayi mata har dai zuwa matsayin da suke a yanzu. Wasu abubuwan ta fada wasu ta sakaya.

Malam yayi ajiyar zuciya yana gajeren murmushi

“wato idan na fahimceki tsoron kada uwarmiji ta kashe miki aure yasa ki yiwa kanki rigakafi kika hau farautar farinciki da kwanciyar hankalinta a gidan danta.”

“Malam mata irin wannan Gombon wallahi annoba ne a cikin al’umma. Da Mujahid take aure da ta dade da komawa gidan ubanta..itama surukar taki ina tsamman asirin da kika yi mata bai gama sakinta ba” cewar Haj Fanta tana jin kamar ta hau Gimbi da duka don takaici.

Yakura ce ta dan tabata alamar tayi shiru. Malam yace “barta tayi idan zamana ne bata so a nan din sai na tafi”

Wannan karon Mujahid ne yayi magana “kayi hakuri don Allah”

“To ku bani hankulanku nan muyi magana ta fahimta” duka kuwa suka koma fuskantarsa.

“Tun duniya na kwance lokacin da abubuwa basuyi tsanani kamar zamanin yanzu ba kusan kowa a kowane bangaren duniya yasan da matsalar dake tsakanin uwarmiji da matar danta. Lokuta da dama mata sukan fasa aure idan suka tabbatar gida daya zasu zauna da surukai. Abin mamaki shine wannan rigima kusan iri daya ce a ko ina. *Kishi* ne mara tushe. Ita uwar miji tana ganin ta haifa wata bazata fita morar wahalhalun da tayi da danta ba musamman da tasan kaf duniya tafi kowa iko dashi. Mata kuma tana ganin mijinta ne dole ya sauke hakkinta dake kansa. Kowacce cikinsu tana da gaskiya sai dai duka suna mantawa da cewa matsayi daban garesu a rayuwar namiji idan kowacce ta tsaya a iyakar da Allah Yayi mata dangane da alakarta da mutumin to zata fi kowa samun nutsuwa a rayuwa”

Gimbi ta dakatar dashi tace “Malam ba fa da ka nayi abuna ba. Labarai da yawa naji wasu kuma na gani da idona. Kusa da gidanmu kafin nayi aure uwarmijin a kofar dakin dan take zama har ya dawo komai dare idan da leda ta karba ta raba ko ma menene a ciki nata yafi yawa ta bashi sauran ya kaiwa matar da yaransu. Nawa mijin babana ne ya sama masa aiki kaga kuwa ni nafi dacewa da kyautatawarsa fiye da Maamu.”

Harara su Haj Fanta suka rinka maka mata Malam ya jinjina kai “idan da mata goma masu surukai zasu tsaya a wurin nan to ina da yakinan takwas cikinsu zasu miki korafi da uwarmijinsu. Baiwar Allah duk abubuwan da kika sani game da su bazan boye miki ba yawanci duka gaskiya ne to amma fa akwai abin da baku zurfafa tunani akai. Kowacce halitta a duniya baka rabata da kishi. Kuma yawa yawan kishin yana faruwa ne idan kika ga wani ko wata yana samun fiye da abinda kike tunanin hakkinki ne daga wurin wanda ake kishin dominsa. Uwa da kuke ji da gani daraja da kimarta tafi karfin wasa. Baku san ayoyin da Allah Yake cewa ayi da’a gareshi Yake bin wannan umarnin da cewa a kyautatawa iyaye ba. Shi kuma Annabi SAW ya tabbatar mana da cewa a iyayen ma uwa tafi uba cancanta da kyautatawa har sau uku?  Cikinku wace bata san wahalar ciki, haihuwa da raino ba? Banda ke Yana muna da  miki fata samu amma ana haifa a gabanki ko. Kina mace ki kare wannan wahalar ki dawo gidan danki sai ya baki daki kamar akurki a bayan gida yana ganin alfarma yayi mata. Ita da ta haifa ya tare jikin mata idan taci sa’a ya leko suka gaisa kamar yana kan kaya zai tashi yayi gaba. Ya koma rayuwa daga shi sai iyalinsa ita uwa ko iyayen duka biyu kuji ana cewa haka zamuyi ta hakuri dasu har a rabu lafiya. Allah sarki iyaye mutuwarsu kawai ‘ya’yan ke jira su cigaba da fantamawa babu damuwar komai a ransu. Ana haka ko ba’a yi? “

STORY CONTINUES BELOW

Jikinsu ya fara sanyi harda Gimbi kuwa suka ce anayi. Malam yace “to wannan dalilin ga kuma rikici na girma suna taimakawa wurin sanya uwarmiji takurawa surukai. Itama taji labari ko ta gani ya faru da wata sai tayiwa kanta rigakafi irin yadda kika yi” ya yi maganar yana kallon Gimbi.

Shiru tayi tana tunanin rayuwarta. A iya saninta zata iya rantsuwa ko sau daya Maamu bata taba yi mata kallon banza ba tun kafin zuwanta Abuja. Kafin abubuwa su lalace ba ita kadai ba hatta Baaba Hure da ‘ya’yanta basu taba saka mata ido ba. Wata zuciyar tace mata amma duk don suna son turo miki Maamu ne da ‘yarsu ya aura. Kwanciyar maciji suka yi miki sai kin sakankance kiji harbi irin yadda suka so yi ba don kin taimaki kanki ba. Kallonta su  Malam sukeyi ta zurfafa a tunani. Ta dago kai

“yanzu kana nufin dai komai laifina ne, nayi ba daidai ba saboda na nemawa kaina da yarana ‘yanci?”

Wannan karon yaji ta soma bashi haushi ana ga yaki tana ga kura.

“Baiwar Allah da kinsan girman zunubin da kika aikata bana jin zakiyi magana irin wannan. Duk duniya babu zunubin da ya kai shirka kuma kinyi. Manzon Allah SAW ya fada mana mu al’ummarsa cewa mu dage duk runtse mu mutu muna musulmai, saboda Allah mai rahama ne da jinkai yasan cewa indai laifi ba hakkin wani muka tauye kamar yadda kika yi ba to idan Allah Yaso duk tulin zunubanmu sai Ya yafe mana Yace mu shiga aljanna cikin rahamarSa. Duk wanda ya mutu yana mai imani da bokaye da malaman tsibbu mushirikine ko yaki ko yaso.”

Gimbi ta dafe kirji “A’a fa  Malam ni ba imani nayi dasu ba tunda ina sallah ina azumi “

Murmushi yayi mai ciwo da nuna bacin rai saboda masu bin bokaye da dama haka suke cewa su musulmai ne alhalin daga lokacin da ka yarda wanin Allah zai iya biya maka bukata to ka tabe kai da rahama sai ranar da kayi tuba irin wanda sharia ta aminta dashi.

“Gimbiya! In tambayeki mana shin tunda kika shiga matsalolin nan kin taba daga hannu kin roki Allah Ya yaye miki a matsayin Ubangijinki majibincin lamuranki?”

Nan ake yinta, tabbas bazata iya tuna yaushe ta kai kukanta ga Allah ba. Hasali ma sai yanzu ta farga cewa kullum fa burinta a sami bokan da yafi kowanne kwarewa a aiki. Jikinta a take ya fara rawa kamar mazari da ta tuna duk wata kadararta ta kare a gidan boka.

Basmallah yayi yace ” *WA IZA SA’ALAKA IBADI ANNI FA INNI QAREEB. UJIBU DA’AWATAD DAA’I IZA DA’AN. FALYASTAJIBULI WAL YU’MINU BI LA’ALLAHUM YARSHIDUN* ” Ayar da duka suka ji Malam ya karanto kenan yana karewa sai hawaye ya ziraro daga idonsa daya.

Daga nan fa kwakkwaran motsi duka sun kasa saboda firgici da tuna ayar Allah musamman wadanda suka fahimci me ya fada da larabci.

Malam yace cikin murya da yanzu take nuni da bacin rai da son firgita mai sabo

“Kina ina Allah SWT girma, da isa da buwaya sun tabbata a gareshi baShi da matamaki azza wa jalla sarki zuljalali wal ikram Yake cewa Annabi Muhammad SAW idan bayiNa suka tambayeka game daNi ka fada musu cewa Ina kusa…wannan kusancin ina mai tabbatar muku cewa Allah Yafi jijiyoyin dake cikin jikinmu suna gudanar da jini kusanci damu. Sannan yace Shi Ubangijinmu mai jin addu’ar mai roko ne idan ya roke shi. Saboda haka mu roke Shi kuma muyi imani daShi ko zamu samu shiriya. Na rantse da Sarkin da Ya busa min numfashi wannan ayar tana kwantar da hankalina da sanya nutsuwa a lokacin damuwa. Idan har bawa ya tuna wannan zance na Mahaliccinsa kuma yana ikirarin imani da musulunci to babu abinda zai dame shi ya kasa daga hannu ya kai kukansa inda za’a share masa hawaye.”

Idanun Gimbi a take suka shiga kwararar da hawaye masu zafin gaske.

Malam kuwa cikin daga murya domin ya kara tada mata da hankali ya kori duk wani sauran shaidanci da yake yawo a zuciyarta ya cigaba da magana.

“Kina da Ubangijin Annabi Muhammadu me ya kaiki wurin boka? Kina da Sarkin da gyangyadi bai taba daukarSa ba me ya kaiki wurin wanda ko yau ko gobe rana zata zo da za’a turmutsa shi a kabari? Kina da Mamallakin sammai da kassai wanda Yace da zai biyawa dukkanin bayinSa na farko zuwa na karshensu dukkan bukatunsu to babu abinda zai ragu daga taskarSa. Har Annabi SAW ya bamu misali da cewa kamar fa a tsoma allura ne a cikin makeken teku a tsamota. Kai mata!  Kuna da Sarki mai _kun fa yakun_ me yake kaiku wurin kazaman bokaye a dazuka suna shiga tsakaninku da ganin hasken rayuwa? Bokayen da suke nema daga aljanu su kuma aljanun suke sata su basu ko kuma suje su yi ta sanya wasi wasi a zukatan bayi su farraka masoya su bata alkhairi su maye gurbinsa da sharri. Idan kura tana maganin zawo ya kamata bokaye sufi kowa kudi da samun manyan mukamai a duniya amma sai kiga mutum a jeji yace zai biya miki bukata amma sai kin biya wasu makudan kudade kin kuma bar ibada. Bayan kuma wanda Ya halicceki domin ki bauta Masa baYa gajiya da jin rokon bayinSa. Koda yake rashin hakuri shine babbar matsalarmu munfi son mu roka mu ajiye hannu tare da biyan bukata. Sai dai Allah Yafimu sanin me ya dace damu a kowane mataki na rayuwa. Shine mai biyan bukata take yanke sai dai Yakan jinkirta mana zuwa lokacin da amsawar adduar yafi dacewa.”

STORY CONTINUES BELOW

Zuwa yanzu ba Gimbi ba hatta Haj Fanta kuka suke yi sosai. Gimbi ta dafe kirjinta tana kiran ta shiga uku ta cuci kanta.

“Muddin kina numfashi baki shiga uku ba domin kuwa addua bata barin komai” cewar Dr. Yana.

“Ina so ku sani cewa rayuwa da mutuwa gaskiya ne kuma zaman kabari da busa kaho abu ne tabbacce da zai faru komai nisan lokaci. Gimbiya ki kiyaye ranar da zaa tona rami a kasa a sanyaki daga ke sai halinki Mala’iku su zo gareki domin amsa tambaya. Shirka bala’i ce, bokaye da yan  tsibbu da matsafa duka masifa ne, sannan duk wata halayya da mutum zai tsira domin haddasa husuma tsakanin mutane ko da ba masoya bane halaka ce gareshi. Allah mai rahama ne da jinkai…ni da ku duka muna kyautata Masa zato da kwadayin ranar da Zai umarcemu da shiga aljanna mu rayu cikin ni’ima. Jahannama da Qur’ani da  Annabi SAW suka bamu labarinta wuta ce da ko tururinta bazamu jura ba balle ita kanta. Kuma kada kuji da wai, ana gama hisabi zaa kawar da mutuwa babu wanda zai kara mutuwa. Rayuwa ce ta dindindin har abada. Ko ba’a tambaya ba nasan babu wanda zaiso yin yini daya cikin wuta balle rayuwa mara yankewa. Mijinki yana da rai sannan surukarki tana da rai saboda haka zabi ya rage naki”

Kuka mai tsuma zuciya Gimbi take yi saboda tausayinta su Dr. Yana ma kukan suke yi.

“Allah na tuba! Allah na tuba!! Malam yaya zanyi na kankare wannan masifar da na janyowa kaina da hannuna daga littafina? Malam yaya zanyi idan aka bani littafina ranar lahira a hannun hagu? Shikenan ni bani da rabo?” Zuciya a karye take magana cikin kuka.

Haj Fanta ta janyota jikinta itama tana kukan. Shi kuwa Malam bai barsu haka ba ya rinka janyo hadisai da ayoyi yana cika musu zukata da tsoron shirka.

Sunfi awa biyu a zaune sannan yace zai tafi. Gimbi ta rarrafa ta dan matsa kusa da kujerarsa “Malam yaya zanyi da iyayena, mijina da Maamu? Na yarda na rasa komai a duniya indai zasu yafe min na rabauta ranar lahira…wayyo ni na cuci kaina”

“Ki kwantar da hankalinki ki yiwa Allah kirari da yabo da godiya sannan ki tuba. Gafarar Allah yawa gareta har Yake cewa da bawanSa zaizo masa da zunubi kamar kumfar teku kuma ya tuba , to da Zai zo masa da gafara kwatankwacinta. Mu duka masu laifi ne mu yawaita tuba ko zamu dace da gafarar Allah. Mu kiyayi manya da kananun kaba’ira bakin gwargwadon iyawarmu Shi kuma Allah Zai kiyaye mana imaninmu Ya tsaremu Ya saka mana da rahamarSa da muke rayuwa a duniya domin nemanta. Allahumma innaka afuwun kareemun tuhibbul afuwa fa’afu anna.”

Gabadayansu suka amsa da Amin suna goge hawaye. Malam ma yana fita nasa hawayen suka sauko na tsoron Allah yana mai jaddada addu’a akan yin nasara a zuciyar Gimbi.

Haj Fanta kuwa hannun Gimbi ta kama ta kaita uwar dakin Yakura sannan da kanta taje ta zuba mata abinci ta kawo mata. Tana zuwa ta sameta a nan inda ta barta tana ta kuka har tana neman shidewa. Tunda tazo duniya bata taba jin tsoron azabar Allah kamar yau ba. Jin kanta take kamar wadda ta rayu cikin mafarki yau ne ta farka. Kusa da ita Haj Fanta ta zauna jiki a sanyaye

“Gombo kici abinci sai mu fara tunanin komawarki gida”

“Hajiya wane gida zani a yadda nake jin kaina lullube da kazanta? Kin san sau nawa kafafunnan suka kaini gidan boka? Sau nawa hannuwana suka yi amfani da magungunan bokaye domin cimma burina? Ku taimaka min muje na roki Maamu gafara wallahi idan ta yafe min nasan Awaisu zaiyi saurin yafe min shima. Ga iyayena sun dade da yin fushi dani. Ga Anti Bebi da nasa aljanu suka mayar da ita tamkar mahaukaciya” wani kukan ta saka Haj Fanta tayi ta bata hakuri.

******

Tun fitar Awaisu da safe Rumana ta gama gyara gida sannan tazo tayi girki saboda yace mata gida zai dawo yayi shirin zuwa sallar juma’a. Tana tsaye a gaban wardrobe dinsa  tana neman kayan da zata dauko masa taji ya bude kofar dakin da sallama.

A hankali ta amsa amma bata juya ba. Tana nan tsaye har yazo ya rungumeta ya rankwafa ya doro kansa a kafadarta.

“Duk fushin ne my sweet Son So, gaskiya na kula mijin nan naki  sarkin laifi ne amma nasan maganinsa”

Juyawa tayi har lokacin yana rungume da ita ta turo baki.  Tun asuba da ta tashi tana sallah ta tafi hada masa abinci duk da bacci da muguwar gajiyar dake damunta. Amma da ya fito kurba daya yayi wa tea tare da mata kiss ya fice yace yana sauri.

Waya ce ya samu daga DPO cewa anyi masa waya daga sama ance ya saki Ovi da kanwarta. Ita kanta Ovi bata san hakan zata faru ba ta dai gwada sa’arta ne ta kira wani mai babban mukami da sukayi hulda a baya ta nemi alfarma shine yace a saketa. Ko da yaje sun gama rufe case din DPO ya bashi hakuri. Ransa a bace ya wuce office sai yanzu da ya dawo ne yaji dadi da yaga Rumanansa.

Kallonsa tayi tana dan murmushi “to yaya aiki?”

“Lafiya kalau sai gajiya da yunwa”

Cikin shagwaba tace ita dai daga yau ya dena fita bai ci abinci ba. Yana rike da hannunta suka fita falo ta zuba masa yana ci suna hira.

“Kinga dai korafi da mita ta kare na dawo naci abinci gashi har ina da sauran lokacin yin wasu abubuwan kafin nayi shirin masallaci”

“Wani aikin zaka yi kuma daga dawowa?”

Kashe mata ido yayi yana wani murmushi “eh mana..aikin kula da amaryata”

A tsorace ta mike don ta fara fahimtar inda ya dosa. Ya damko hannunta kafin ta gudu

“Ina zaki kuma muna hira matsoraciya?”

Fuskarta kamar zatayi kuka tace “Son So bani da lafiya ne”

Hannu yasa a kasan habarsa “ohhh yarinyar nan ba dai fassara ni kikayi ba. Don da kin fara kiran rashin lafiya nasan me kike gudu” yana mata dariya

Tuni kunya ta kamata ta daure tace “ni dai babu abinda nake nufi, bance komai ba”

Dariya yake sosai ya tashi tsaye yana shafar fuskarta da bayan hannunsa ya soma magana kasa-kasa “ni din me kike tsammani ina nufi uhmm?”

Duk ta rikice ta rasa amsar bashi ya cigaba da tsokanarta har ta fara masa kuka.

“Idan kaga amarya na kuka fa rarrashi take so, bari ki gani” daukarta ta ga zaiyi ta gudu daki tana dariya.

Soyayya sosai da kulawa ya nuna mata sannan ya tafi masallaci. Da ya dawo a kwance ya sameta tayi sallah bacci ya dauketa. Shima kwanciyar yayi ya rungumota suka yi baccin tare.

******

Da kyar Gimbi ta iya shan tea da su Yakura suka takura mata sannan ta roki alfarmar a bata kudin mota Fika zata wuce. Sai lokacin Haj Fanta ta tuna da jakarta da tasa Bukarti kwacewa a hannunta ta mika mata sannan tace mata zasu tafi tare da ita saboda kada a ki gaskata ta.  Murna Gimbi tayi ta rinka godiya kalmar da ta dade banda boka da Ovi babu wanda take fadawa.

Daga nan ta roki su kaita wurin wannan malamin kafin ta tafi. Sai bayan masallaci suka je gidan nasa. Yana ganinsu yayi hamdala domin yasan canjin ra’ayi daga wurin Gimbiya shi kadai ne zai kawota gidansa.

Shima godiya tayi masa sosai yayi ta mata addua har yake bata labari akwai kaninsa limami ne a Abuja kwana biyu kenan da ya kirashi yana bashi labarin wata matar manajan banki da abubuwan da tayi. Ya kare da cewa yanzu kanwar babarta kamar dai naki lamarin ita yake nema saboda itace ta koya mata bin bokaye. Ya kira ne dama yana neman shawarar yadda zaiyi mata nasihar da zata shigeta.

Wani sabon kukan mai taba zuciya Gimbi ta soma tace “wallahi mijina ne, Malam ashe har yanzu bayan abubuwan da nayi Awaisu yana sona da alkhairi. Na cuci kaina na cuci mijina kuma naci amanar zaman tare da soyayyarsa gareni..gabadaya lamarin nan babu ta inda matsala ta taso min ni kadai na rinka kidana ina rawata gashi komai ya baci”

“Kuma komai zai gyaru da izinin Allah. Kin dai ga yadda ikon Allah yake wanda kika so cuta yana binki da kishiyar abinda kika yi masa. Ina jin har duniya ta tashi baza’a dena samun sabani tsakanin surukai ba amma ki tuna Manzon Allah SAW yace kada mu cuci kowa kuma kada mu bari a cucemu. To idan har daya zai faru gara ki jewa Allah a matsayin wadda aka cuta akan kije a macuciya. Komai runtsi komai wuya kiyi kokari kiga baki cutar da dabba ba ma balle dan Adam kuma musulmi. Wanda duk ya cuceki Allah zai isar miki ko a gaban idonki ko bayan kin koma gareShi. Allah Yayi miki albarka Nana mai sunan manya”

Tana kuka sosai tace Amin suka shiga motar Mujahid wannan karon harda Yakura suka nufi Fika.Wuraren uku da rabi wayar Awaisu ta soma ringing. Saurin amsa kiran yayi tare da kwantar da kan Rumana a kan pillow ya fita don kada ya katse mata bacci. Ganin sunan Harisu da yayi yasa shi murmushi ya amsa suka gaisa. Zai fara jansa da hira ya katse shi ta hanyar sanar  dashi zuwan Gimbi gidan tare da Dr. Yana da mijinta da wasu mata biyu. Mamaki ya kama Awaisu sai Harisu ya ce masa yayi kokarin tahowa ko zuwa da safe ne don tunda tazo banda kuka babu abinda take yi tace kuma bazata yi maganar abinda ya kawota ba sai Awaisun yazo.

Hankalinsa a take ya tashi yana tsoron ko wani sabon salon makircin ne ta kulla. Alh Mudi ya nema a waya yayi sa’ar samunsa ya sanar dashi halin da ake ciki. Shima nasa hankalin ne ya tashi yana tsoron me Gimbi taje tayi.

“Awaisu ni dai idan babu damuwa zan kira Harisu na fada masa a yau dinnan ba gobe ba zan tafi Fika na daukota. Lokaci yayi da zaka datse duk wata alaka da Gimbi don wallahi a yanzu ba iyayenka ba kai kanka kunyarka nake ji.”

“To abinda za’ayi Alhaji ku shirya har Mama idan zata iya zuwa da su Haris sai mu fito mu same ku drebana yaja mota daya nima naja daya. Sai dai kuyi hakuri zamuyi tafiyar dare kam”

Alh Mudi yaji ya kara son Awaisu yace kada ya damu zai nemi kanin Gimbi yaja su shi yaja tasa su hadu a gidan mai na fita gari sai su wuce tare tafiyar bibbiyun zata fi dadi. Sun yanke shawarar haduwa nan da hudu da rabi.

Dakin ya koma har lokacin bacci Rumana take yi. Yasan ta gaji tana bukatar hutu amma bazai iya tafiya ya barta ba gaskiya. A gurguje ya hada musu kaya shi da ita sannan ya tasheta yace ta shirya Fika zasu tafi.

A tsorace take sosai zai dauki jakar kayan nasu ya kai falo ta riko shi

“Don Allah me ya faru?”

“Kin fiye tsoro Rumana babu komai in sha Allah. Ki shirya zan fita nayi sallah ina dawowa horn zanyi miki. Ga keys nan ki kulle ko’ina”

Ai sai kawai ta fashe da kuka, gani take wani abu ne ya faru baya son fada mata. Idan ba haka ba me zaisa da yamman nan haka kawai yace su tafi Fika.

“Uncle ina da imani zan iya daukar kaddara, ko mene ne kada ka boye min” muryarta na rawa tace “tsoro nake ji”

Rungumeta yayi yana shafa mata baya. A nutse ya fada mata yadda sukayi da Harisu tace to Allah Yasa alkhairi a tafiyar.

Kafin biyar sun dauki hanyar Fika a hanya suka dauki Amir da Mu’allim suka dawo motarsu saboda kada su Mama su takura.

*****

Yau matan Harisu da mai girki da mara girki duka suna kitchen suna girki tare saboda bakin da suke kan hanya da su Gimbi. Dakuna aka gyara inda za’a saukesu.  Awaisu ma da yake barin key din dakinsa shima an gyara masa nasa dakin.

Sai shabiyu saura suka iso gidan. Lokacin su Daula duka sunyi bacci. A gajiye suke sosai musamman Awaisu da kanin Gimbi da sukayi tuki.

Suna shigowa hayaniya ta kacame ana murnar ganin su Haris da amarya Rumana. Ita kuwa sam hankalinta bai kwanta ba sai da ta ga kowa na gidan lafiya. Daga dakin da su Gimbi suke suna jiyo muryoyin mutanen gidan da su Amir masu cigiyar Mummynsu.

“Gimbi ba ke ake nema ba kuwa” cewar Haj. Fanta tana kallon kofa.

Murmushi mai ciwo tayi “Hajiya bana son yaran nan su ganni sai na tabbatar su Maamu sun yafe min. Wallahi ba don dare ba ni a yau naso a zauna muyi magana na roki gafara. A haka ji n nake kamar akan kaya”

Dr. Yana ta dafa kafadarta tana murmushi “kada ki damu don bana jin a yadda naga mutanen gidan nan zasu watsa miki kasa a ido. Ga dukkan alamu suna da kirki sosai”

“Kirkin nasu shi yasa nake kara tsanar kaina da abubuwan da nayi musu. Gara ka cuci mugu akan mai kirki doctor “

Daga bangaren su Baaba kuwa sun yiwa baki su Alh Mudi da Mama tarba da mutumci aka kaisu masaukin da aka tanadar musu. Yaran kuma tuni suka shige wurin ‘yan uwansu bacci ya gudu. Abinci suka ci kawai suka shiga hayaniya a gidan.

STORY CONTINUES BELOW

Anti Amarya ta kira Rumana ta bata key din dakin Awaisu

“Ga mukullinku nan har abincinku an ajiye a ciki”

Baki ta turo “to bari na kai masa na dauko kayana”

“Kada ma ki bari babanku yaji wallahi ki wuce bakinki alaikum ki tafi dakin mijinki ni babu ruwana”

Tafiyarta tayi ta bar Rumana saroro tana jin kunya ga su Maamu a wurin da mamanta. Antin ma tana sane tayi mata haka don ta kula da take takenta tunda suka shigo wurin ‘yan uwanta take neman shigewa ta kwana.

A falo Awaisu ne da Harisu da kuma Mujahid. Sun tambayeshi dalilin zuwan yayi murmushi yace su yi hakuri har zuwa wayewar gari tunda yanzu dare yayi. Ya dai kwantar musu da hankali cewa alkhairi ne ya kawosu.

Ba don Rumana taso ba Baaba da kanta ta korata dakin Awaisu tana cewa bata son sakarci. Bai nemi Gimbi ba dama saboda ganin dare yayi kuma yasan taji zuwansu. Tunda bata fito ba zai hakura zuwa safiyar kamar kowa.

Da ya shiga daki can karshen kujera ya tarar da Rumana a zaune ta takure. Tunda ta shigo tayi wanka take zaune a wuri daya. Yanzu ace duka gidan sun san tana dakin Uncle Awaisu ai da kunya. Murmushi yayi don kuwa yana jinta ita da Baaba Hure lokacin da tace mata dole ta tafi wurin mijinta. Kin kulata yayi ya shige bandaki yayi wanka ya fito. Tana nan zaune ya gama shirinsa duka baice mata komai ba ya kashe fitilar dakin ya kwanta.

Sheshshekar kukanta yaji yayi ‘yar dariya. A dan zamansu ya kula babu abinda Rumanansa taki jini kamar a shareta. Yana daga kwance yace

“waye nan”

“Shine ma kaki kulani” ta fashe masa da kuka bilhakki ita bata ji dadi ba.

A duhun ya taso ya ja hannunta “nima fa kin kulani kika yi, ashe babu dadi. Kuma ina ji sai da aka tilasta miki zuwa nan saboda baki damu dani ba”

Cike da shagwaba tace “na damu mana..”

“Ban ga alama ba”

Rungume shi tayi duk da tana jin kunya sosai “gashi kuwa..ni dama kunya nake ji yadda zan fita daga dakin nan gobe”

Matseta yayi a jikinsa sosai “Sarkin rigima nima ai kunyar nake ji, kada ki damu na kusa gama gini a nan mu koma can duk lokacin da muka zo ko”

Dariya yaji tana yi masa saboda yace yana jin kunya ya girgiza kai yana murmushi daga karshe ya sata yi masa tausa a kafa don ba karamar gajiya yayi ba.

*****

Karfe tara na safe duk wanda ya kamata yazo yana cikin falon Harisu. Su Anti Baraka, matan Harisu, Maamu da Baaba, iyayen Gimbi, Dr. Yana, mijinta dasu Haj Fanta sai kuma Rumana wadda Maamu tace ko me za’ayi ayi a gabanta tunda dai matar Awaisu ce.

Duk sun zauna suna sauraron Gimbi ta taso da idanunta kumburarru ta tafi gaban Maamu ta durkusa. Bude baki tayi zata fara magana sai kuka. Da kyar ta iya hada kalmomin Maamu ki yafe min.

Kowa a wurin banda su Haj Fanta yayi mamaki. Maman Gimbi kuwa sai kuka a ranta tana cewa Alhamdulillah yau sun ga sakamakon jajircewa wurin yi mata addua.

Maamu kanta hawaye ta soma yi “Gimbiya me ya sameki haka? Ko wani salon sihirin ne kika zo dashi?”

Girgiza kai ta rinka yi sannan cikin kuka da tun jiya ta kasa dainawa ta labarta musu komai tun tsoron kada Maamu ta rabata da mijinta zuwa Anti Bebi da kuma wannan zuwan nata Damaturu.

“Wallahi nasan bani da wani uzuri akan abubuwan da na aikata amma ina rokonku ku daure ku yafe min kada na mutu da hakkinku. Maamu ke nafi cuta shiyasa na damu nasan idan kika yafe min kowa a nan zaifi saurin hakura”

Haj Fanta ita ta karbe ta basu labarin zuwansu Maiduguri a jiya da yadda suka kare da Malam sannan ita da su Yakura suka cigaba da nemarwa Gimbi afuwar wadanda ta sabawa. Tuni falon ya kaure da kabbara. Awaisu ya kasa cewa komai sai kallonta da yake yi amma baka iya tantance me zuciyarsa take tunani.

STORY CONTINUES BELOW

Gimbi ta rike kafar Maamu “ki yafe min Maamu, mata irina da yawa suna cikin halaka. Wannan duniyar da bata da tabbas mun dauketa kamar bazata kare ba muna sabon Allah. Ina rokonku duka kuyi hakuri ku yafeni”

A hankali Maamu ta dora hannunta akan Gimbi “Allah Ya yafe mana baki daya na yafe miki”

Jikinta Gimbi ta fada tana kuka sosai. Dama can ita ba jahila bace son zuciya ne kawai ya kaita ya baro. Wurin da iyayenta suke zaune ta rarrafa suma ta basu hakuri. Maamu ma ta yafe bare su da suka haifeta. Haka ta rungume Mama tana kuka Alh Mudi yana mata addua. Daga nan shi da sauran manyan da suke wurin suka shiga yiwa kowa nasiha mai ratsa zuciya akan shirka da mu’amala da sihiri don neman biyan bukata. Allah SWT Shi kadai Ya cancanci a bauta Masa kuma a nemi taimako a gareshi domin Shine Ya haliccemu.

Kusan awa daya ana ta magana daya sannan da daidai kowa ya fita harda Rumana aka bar Awaisu da Gimbi. Kasa kallonsa tayi da dukar da danta yana kallon hawayenta suna diga akan mayafinta. Tashi yayi tsaye a sanyaye yace

“We used to be best friends Gimbi…what happened to us?”

Sai lokacin ta dan dago kanta itama ta mike  “son zuciyata ne ya faru Abban Haris, yau Maamu ko cewa tayi ka sakeni tun zuwanta gidanmu bai halatta na kaita wurin boka ba balle bata yi min komai ba. Ka yafe min mijina, ka taimakeni kada na nesanta daga rahamar mai rahama saboda wannan gagarumin sabon da na aikata”

Idanunsa ya rufe sai ga hawaye suna sakko masa baiyi yunkurin tsayar dasu ko sharewa ba. Hannunta tasa a hankali tana share masa itama yana share nata.

“Ban kyauta mana ba”

“Kaddara ce”

“Baka ce ka yafe min ba”

“Addu’ata Allah Yasa muna da rabon sake zama a matsayin ma’aurata a lahira”

Wata nannauyar ajiyar zuciya ta saki ta rungume shi tana kuka sosai.

“I love you Abban Haris”

Bai iya bata amsa ba sai bayanta da yake shafawa. Dago kanta tayi tayi masa murmushi “uwa ba abar wasa bace kuma nayi imani indai muna raye bazaka taba mantawa da yanayin da ka tsinci Maamu ba lokacin da ka dawo daidai duk lokacin da ka ganni. *Awaisu!* nasan duk duniya bani da masoyi kamarka amma da bakina ina rokonka ka sauwake min domin zamanmu bazai taba yiwuwa ba. Daga ranar da na fara kai kafata gidan boka na bata rayuwar aurenmu”

Hannunsa ya dora akan bakinta yana girgiza mata kai ita kuwa ta zame shi tace ya barta ta fadi gaskiya. Ta tabbatar soyayya dai ta gaske yanzu Rumana yake yiwa kuma bata bakinciki. Fatanta ya sami nutsuwar da ta hanashi da soyayya ta gaskiya.

A nasa bangaren ya yafe mata dama kullum fatansa ta gane gaskiya sai dai kamar yadda ta fada bazai taba mantawa ba. Maamu ita ce jigon rayuwarsa ta yaya za’ayi ya manta da hawayenta saboda soyayya.

Wata takarda ya dauko daga aljihunsa wadda ya rubuta tun ranar da taje asibiti da wannan izgar dokin ya rubuta. Niyarsa sai ya hadata da limamin nan sannan ya bata.

Hannu na rawa ta karba ta bude. Saki daya ne yayi mata idan aka hada da na baya ya zama biyu. Kuka ta saka duk da a ganinta ma yayi mata adalci da bai kai biyu ba ya raba tsakaninsu gabadaya.

“Abban Haris nagode, lallai yau hannu ya girbe abinda ya shuka.”

Hakika Allah Yayi gaskiya da Yace *_la’in shakartum la aziddanahum wala in kafartum inna azabiy la shadid_*. Yau ga Gimbi da Allah SWT Ya ni’imta da abubuwa marasa kirguwa ciki harda miji nagari da suruka abar kwatance sai gashi haka nan babu gaira babu dalili ta janyowa kanta nesanta daga dukkan jindadin rayuwarta.

“Allah mai gafara ne kisa wannan a ranki. All the best….my best friend. Ina miki fatan alkhairi a rayuwarki ta gaba”

“Kaima Allah Ya baku zaman lafiya da Rumana”

STORY CONTINUES BELOW

Share hawayenta tayi ta fito tsakar gidan tana kwalawa su Haris kira. Dama sun tashi suka fito a guje suna murnar ganinta. Dakin da aka sauki su Mama ta wuce tare da yaran ta basu takardar sakin.

Sun gama hada kayansu tsaf suka fito nan kowa ya san hukuncin da Awaisu ya yanke tsakaninsa da Gimbi. Sai da taje dakin kowa ta musu sallama sannan ta roki a barsu su tafi da yaranta tayi kewarsu sosai. Baaba Hure tace ai babu mai hanawa. A mutumce suka yi sallama Gimbi ta rungume Haj Fanta tana kuka

“Ki bar kuka Gimbiya inda rai da rabo kinji”

Murmushi Gimbi tayi “ina kika baro Gombo kuma Hajiya?”

“Tun jiya na nemeta na rasa sai Gimbiya uwar Harisu nake gani”

Dariya aka rinka yi da alkawarin zumunci sannan Mujahid yaja motarsa shima kanin Gimbi yaja tasu motar suka kama hanyar Abuja.

Rumana da Awaisu sai washegari suka tafi da sassafe don baya son ta sake fashin makaranta.

******

*Bayan Sati Hudu*

Rumana ta gama girkin dare Daula kuma ta wanke duk abinda suka bata wurin girkin Haris ne mai jere kwanukan akan dinning table suna ta surutunsu. Bayan sun gama Rumana ta zubawa kowa sannan ta tafi tayi wanka kafin Awaisu ya shigo.

Shiru bata fato ba suka gama ci suna kallon cartoon har Awaisu ya dawo. Da murna suka tare shi suna bashi labarin zuwansu gidan Mama yau da sakon Gimbi na gaisuwa gareshi.

“To ina amsawa bari naje nayi wanka  na fito. Inna Ammin ku?”

Mu’allim yace itama wanka taje tayi.

Dakinta ya fara zuwa bata nan sai ya wuce nasa dakin. A kwance ya ganta ta rufa da bargo tana bacci. Kasa shiga wankan yayi sai da yayi kissing dinta ya wuce yana tunanin neman mai aiki. Ga karatu ga aikin gida yasan abin yana mata yawa.

Har ya fito tana nan kwance ya gama shirinsa ya kula tana yamutsa fuska cikin baccin sai ya zauna a gefen gadon ya dora hannunsa akan goshinta zai shafa yaga tayi mugun zabura amma bata bude idon ba

“Don Allah Anti kiyi hakuri”

Abinda yaji tana fada kenan sai ga hawaye ta soma kamar famfo. Jijjigata ya somayi a rude taki tashi sai kiran Anti da take yi tana kuka. Rasa abinyi yayi kawai ya bude quilt din da ta rufa ya dagota sai kawai jikinta ya saki jini ya balle mata cikin dan kankanin lokaci ya soma bin gadon. Firgici da tsoro kan Awaisu ya gama yi. A guje ya dauko jallabiyarsa ya dora mata akan rigar baccin jikinta ya dauketa yayi falo.

Yaran duka suka taso yace musu bata da lafiya su kula da gidan zai turo azo a daukesu baya son su zauna su kadai. Duka sun tsorata ganin Ammi kamar yadda suke kiranta bata ko motsi.

Gudu sosai yake yi ya karasa national hospital saboda yana tsoron zuwa private ace babu likita. Sake daukarta yayi ya shigarda ita emergency nan suka karbeta aka fara bata taimakon gaggawa.

Awaisu yana reception ya dai kira Nuru ya fada masa yaje ya dauki su Haris. Shiru likitocin basu fito ba daga dakin da take har Nuru ya kaisu gidansa ya taho shima. Ledar jini uku aka karawa  Rumana. Tashin hankali karshe Awaisu ya gani a wannan daren. Da suka fito ne suka yi masa bayani cewa bari tayi ya kuma fita duka amma ba shi bane ya daga musu hankali kamar jinin da take zubarwa. Sai dai  suna ganin sun shawo kan matsalar yanzu in sha Allah. Yadda baisan da cikin ba ya tabbatar da wuya idan Rumanan ma ta sani. Tausayinta yaji ya kamashi ya tafi gida dauko mata kaya da shirin kwanciya. Amenity ya biya Nuru yace zai turo Kubra ta kwana Awaisu yace ya gode amma shi zai kwana da ita.

Shabiyun dare ya dawo asibitin har lokacin bata farka ba. Likita dai ya tabbatar masa da cewa bata cikin hatsari yanzu bacci ne kawai take yi saboda allurai da akayi mata.

STORY CONTINUES BELOW

A zaune ya kwana a gefen gadon. Sai wurin takwas na safe ta farka tana rike ciki. Kanta ne ya nemi juyewa bata gane ina suke ba.

“Son So…”

Da sauri ya taso daga kan kujerar yazo ya duka inda take kwance ya rungumeta yana ajiyar zuciya.

“Sannu kinji”

“Me muke yi a nan?”

Gabansa ne ya fadi “baki da lafiya ne na kawoki jiya. Ina zuwa zan fadawa dr kin tashi”

Hannunsa yaji ta rike “me ya sameni?”

Bai iya bata amsa ba ya fita can sai gasu sun dawo da likita. Dubata yayi ya gama rubuce rubucensa ya fita.

Taimaka mata yayi ta zauna ta sake tambayarsa me ya kawota asibiti.

“We lost our baby Umm Ruman”

Zaro ido tayi tare da dora hannu akan cikinta “dama…dama…ina da…?” Sai kuka kuma.

“Shhhh kada ki damu muyi fatan shine alkhairinmu kinji ko. Allah zai kawo mana wasu masu albarka”

A hankali ta gyada kanta ya rungumeta yana rarrashinta. Suna zaune a haka ya kira Harisu ya fada masa. Nan da nan duka gidan suka sani. Maman Rumana ta shiga damuwa sosai har Baaba ta kula da hakan ta fadawa Harisu gobe idan zasu tafi lallai a tafi da ita ta ga ‘yarta.

Yinin ranar Awaisu baya fita daga dakin sai sallah. Daga gidan Nuru aka rinka kawo musu abinci. Washegari da yamma su Maamu suka iso. Kafin su wuce asibitin da kanta ta yiwa Rumana girki. Miya ce ta ganyen alayyahu, ugu, shuwaka wadda taji wanki sosai babu daci sai zogale ga hanta, bushasshen kifi da koda anyita da manja. Kana ganin miyar kasan girkin ya sami kulawa daga maiyi. Tuwon semo ta tuka mai kyau da ya dahu taje yin wanka Maman Rumana ce ta kulle a leda suka shirya suka tafi.

Abin nema ya samu tana ganin iyayenta da Maamu sai shagwaba ta karu. Abincin ma cewa tayi bazata iya ci ba Maamu kuwa tace Awaisu ya zauna ya bata. Kunya kamar ya nutse ganin idonsu Harisu. Maamu ta soma fada idan bazai tashi bane ita sai tayi. Yana mikewa kuwa Mama da Harisu suka kusa karo suna neman hanyar ficewa daga dakin suma kunyar suke ji. Rumana da ta janyo abin daskarewa tayi a zaune tana takaicin me ya hanata ci da kanta.

Maamu ta kallesu duka tace “gulmammu”. Nuru da Kubra me zasuyi in na dariya ba.

Bayan kwana uku aka sallameta su Harisu suka koma Fika. A satin Awaisu yace a nemo masa ‘yar aiki aka samo wata mata zatayi kusan shekara arba’in Hanne. Ita take kula da shara da goge gogen gidan banda dakin Rumana da Awaisu. Sai taimakawa wajen girki da kula da yara. Zamansu suke cikin farinciki da kwanciyar hankali.

Wata biyu a tsakani Rumana ta sake samun ciki. Wannan karon ma basu sani ba saboda baifi sati hudu ba. Tana wanka Awaisu yana aiki a dakin yaji kamar ta fadi. Bai san lokacin da ya ture laptop din ba ya tashi da sauri ya bude kofar. A kwance ya sameta gefen baho ga jini yana bin kafafunta.

Tsoro sosai yaji ya dagota da sauri yana kiranta. Shiru kamar wancan lokacin sai Anti da take kira cikin galabaitacciyar murya. Wannan karon banda fargaba harda mugun bacin rai. Wancan lokacin baya son saka zargi a ransa amma yanzu tabbas abin ya zauna masa a rai.

Maamu ce tayi zaman jinyarta don sai da aka hada da wankin ciki. Tasha wahala sosai akayi sa’a cikin sati daya ta sami sauki.

Haka rayuwa taci gaba Awaisu na kula da iyalinsa sosai sai dai ya kasa cire abubuwan da suka sami Rumana. Ko da ya tambayeta me take gani kafin tayi barin cewa tayi bata iya tuna komai.

Karo na uku da ta sake yin barin kiransa akayi yana wurin aiki yazo makarantarsu. Kafin yaje sun kaita asibiti saboda irin jinin da take zubarwa. Tana zaune a aji kawai ta kwantar da kanta kamar mai bacci wadda ke zaune a bayanta ce ta sanar da malamar dake ajin tana bleeding. Da yake basu san tana da aure ba duk anyi zaton wata matsalar ke damunta.

STORY CONTINUES BELOW

Awaisu bai bata lokaci ba ya isa asibitin abinda yaji tsoro ne wato ta sake yin bari. Jikinsa har wani tsuma yake yi yana tabbatarwa ta sami kulawa ga Maamu a kusa ya tafi gidan Alh Mudi.

******

Cikin girmamawa ya gaishe da Mama yace yana neman Gimbi. Tana daki da yake yanzu can tafi zama tana karatu saboda masters da ta koma Mama tace Awaisu yana kiranta. Karamin hijabi ta saka ta fito falon.

Ko zama batayi ba Awaisu ya tareta cikin bacin rai

“Gimbi me nayi miki haka da zafi ne?”

Kallon rashin fahimta tayi masa ita kuwa Mama jin ya daga murya ta kasa karasa barin wurin ta tsaya daga bakin kofar falon

“Bangane ba?”

“To bari nayi miki kashedi gwaro gwari. Wannan ya zama karo na karshe da zaki zubarwa da Rumana ciki. Na rantse miki idan irin haka ya sake faruwa zan kawar da duk wani sauran mutumcin da yake tsakaninmu na dauki mataki”

Kirjinta ta dafe da yake neman bugawa saboda ciwon da yake yi mata. Wannan mugun son da take yiwa Awaisu har yanzu da tuni ta gama iddah bai barta ba sai ma abinda ya karu.

Hawaye ta soma yi “Abban Haris wani ne yace maka na zubar mata da ciki?”

Yatsunsa uku ya daga a gabanta “sau uku kenan Rumana tana bari. Ko yaushe idan abin zai faru sai dai ta kwanta kamar mai bacci tayi ta ambaton sunanki daga nan bazata sake farkawa da cikin ba. Na dauke kai iya yadda zan iya amma bazan zuba ido ki nakasa min mata ba”

A fusace ya fita tana kiransa ko waige babu. Ta juya ta koma daki taji saukar maruka masu radadi har uku a kuncinta. Mama ce tsaye tana hawaye tana hucin bakinciki

“Gimbi ashe tuban muzuru kika yi mana dama? Zubar da ciki har sau uku don rashin imani. Irin haka fa kika yiwa Dr. Yana gashi ita har yau shiru kake ji “

Gimbi na kuka take ta rantsuwar ba ita bace amma a banza. Alh Mudi Mama take jira ya dawo ta fada masa.

Da ta koma daki Dr. Yana ta kira ta tambayeta yanayin da ta shiga lokacin da tayi bari. Ta kasa fahimtar dalilin tambayar gashi Gimbin kuka take yi ta fada mata. Tana ji hankali a tashe ta dauki mukullin motar da take amfani da ita a gidan ta tafi gidan su Ovi.

Ita ce kuwa ta bude kofar tana mata murmushi “gaskiya Awaisun nan naki yana da hakuri indai sai yanzu kika sami sakona”

“Me kike nufi Ovi?”

“Ina nufin duka zubewar cikin matarsa bai taba nuna yasan kece ba sai na yau ko.” Dariya take yi ta shige ta bawa Gimbi hanya ta shiga cikin gidan.

Ovi da kanta ta fadawa Gimbi ita ke sawa boka ya zubar da cikin Rumana kuma ya tabbatar yayi yadda za’a zargi Gimbi.

“Mijinki ya bata min rayuwa duk iskancina ban taba kwana a cell ba sai dalilinku ke da shi. Ki dauka ramuwa ce kawai nayi amma bana jin zan taba bari ta haihu yadda kanwata bata shiga ba ita bari zata rinka yi mai ciwo ke kuma ayi ta zarginki”

Mari Gimbi ta sharara mata ta dafe kunci tace ta kiyaye abinda zai biyo bayanta. Fada sosai suka yi na cacar baki sannan Gimbi tazo fita tayi saurin jiyawa gefen kujera inda ta hango wata bakar tukunyar kasa. Dama tasan bokan Ovi ayyukansa yawanci da tukunyar tsafi ne tuni zuciyarta ta bata dashi ake tsafin zubar da cikin. A guje ta ruga ta daga tukunyar Ovi tana ihu ta rotsata da kasa. Kanta Ovi tayo ta fita da gudu ko takalmi bata saka ba Ovi na bayanta ta hankadata kasan benen gidansu dama a sama suke.

Duk abinda suke yi Rita tana daki tana jinsu kawai bata son shiga ne. Gudun da taji ne yasa ta fito daidai lokacin da Ovi ta hankada Gimbi. Duka sun rikice Ovi ta gudu daga gidan ita kuma Rita wayarta ta laluba ta kira Awaisu dama tana da numbarsa.

Yana tsaye gaban Rumana yana jin kamar yayi kuka sai ga Mama ta shigo tana share hawaye tana basu hakuri. Ko da Rita ta kira kamar kada ya daga sai kuma ya daure yasa wayar a kunne. Don kada ya ajiye yaki sauraronta fada masa Gimbi na gidansu ta farayi sannan tayi masa bayanin komai. Bai iya magana ba sai salati ya sake kwasa sai gidansu Ovi yana bin kwatancen Rita.

STORY CONTINUES BELOW

A kasa ya sami Gimbi bata motsi shima da hawaye baya masa wuya sai gashi sun zubo. A bayan mota ya sakata Rita tabi bayansa a taxi.   Emergency aka kaita suka duba ta sannan aka bata gado kusa da na Rumana. Rita gwiwa a kasa ta rokesu gafara sannan ta fada musu duk abinda Ovi tayi.

Mama na rungume da Gimbi tana kuka Rumana ta farka. Lokacin Awaisu ya kira abokinsa DPO ya fada masa duk inda Ovi take su kamata.

Sai gashi Rumana ta tashi amma Gimbi sai yamma ta farfado. Likitan da ya dubata yace ta sami sauki buguwa ce dama da karaya a hannu wadda suka gyara.

Waahegari haka su Awaisu suka sake biyo hanya shima Alh Saminun Kano yazo duka suka hado a asibitin ana yiwa juna jaje. Shuhada da iyayenta ma duka sunje.

Rumana bacci take yi lokacin likita yazo dubasu kowa ya fita. Wurin Gimbi doctor din ta tsaya

“Yanzu bazaki yarda na fadawa ‘yan uwanki ainihin ciwon da yake damunki ba?”

Gimbi ta girgiza kai tana hawaye “ko kin fada bashi da magani. Na rasa wace irin soyayya ce nake yiwa tsohon mijina”

“Har fa aman jini kike yi, ki bari a taimaka miki” doctor ta fada tana tausasa murya.

“Kada ki dami kanki ina bakin kokarina wurin cire sonshi daga zuciyata. Akwai kunya mai girma idan nace zan zauna dashi. Labarin darasi ne ga mata. Ke dai duk yadda zakiyi a rayuwa ki tabbatar baki cuci kowa ba, mafi alkhairi gareki shine a cuceki Allah sai Ya isar miki”

Hawaye ne ya gangarowa Rumana amma tayi dif kamar bacci take yi. Zantuka masu ban tausayi Gimbi take yi a take taji mugun tausayinta kuma ta kara sonta domin taji komai game da yadda ta fasa abinda akayi mata tsafi dashi.

Da daddare Rumana ta kafe babanta Harisu da ido idan zai juyo sau biyar sai sun hada ido. Hawaye ya gani fal idon sai yaji tace ya kaita waje tasha iska.

Awaisu da bai san ta tashi ba ya taso da sauri sai dai Harisu ya fuskanci bakinta da magana yace masa bari ya fita da ita shima kafarsa tayi tsami. Basu kawo komai ba ya rike hannunta tana tafiya da kyar.

Waje suka fita ya zaunar da ita kan wani benci sannan ya zauna a gefe yana rike da hannunta “Umm Ruman me kike son sanar da mahaifinki?”

Sunanta kawai da ya ambata ya karyar mata zuciya ta soma kuka. A haka ta fada masa abinda taji. Shima maganar ta tsaya masa a rai

Cike da kulawa yake mata magana “yanzu me kike so?”

Kai ta sunkuyar “Baba don Allah a mayar da aurenta da Son Son…auuuu” ta toshe bakinta da sauri tana dariya.

Shima dariyar yayi “kaniyarki wato Awaisu ya sa kinyi fatali da kunya ko” hannunta ya kama ta tashi.

“Allah Yayi miki albarka Rumana Harisu lallai na yarda da yardar Allah ku ma zaku zama mutane masu sadaukarwa domin farantawa ‘yan uwa musulmi. Ina alfahari dake domin kin kasance mai hakuri da biyayya. Muje ciki”

Dakin suka koma kowa na ciki suna shirin fita ne ma. Alh Saminu, Alh Mudi, Nuru, Alh Maitama sai Awaisu. Abin mamaki Baaba Hure  ke bawa Gimbi abinci a baki saboda karayarta ga Mamanta a gefe baki har kunne yadda take yaba kirkin wadannan mutane. Harisu ya nemi ganin mazan suka fito duka.

Yadda sukayi da Rumana ya fada musu Alh Mudi hankalinsa ya tashi jin cewa Gimbi na da matsalar zuciya. Awaisu ma ba karamin rudewa yayi ba.

Harisu ya dafa kafadarsa “tashin hankali ba namu bane tunda munsan matsalarta. Shawarata kamar yadda mukayi da Rumana shine Alhaji ka wakilta wani cikinmu ya zama waliyyin Gimbi a maida aurenta da Awaisu tunda akwai sauran igiya daya tsakaninsu.”

Da sauri Alh Mudi ya girgiza kai “inaaa, bana marmarin a sake komawa gidan jiya. Gimbi bata kyauta muku ba Harisu”

“Ashe bamu yafe mata ba kenan tunda har yanzu muna tsoronta bazamu iya zama da ita da zuciya daya ba.” Cewar Harisu

STORY CONTINUES BELOW

Awaisu bai iya magana ba sai mamakin Rumana da har ta san ta sowa wani abinda take so. Yana ji suna ta maganganu sai daga karshe yace musu shi dai ya amince a mayar da aurensa da Gimbi. Batare da bata lokaci ba Alh Maitama ya yiwa Gimbi waliyyi shi kuma Harisu ya nemi auren Gimbi ga kaninsa a wurinsa. Basu koma ciki ba sai da aka damkawa Alh mudi sadakin yarsa a hannunsa. Har kuka yayi saboda farinciki yana ta yi musu godiya.

Dakin suka koma akace duk su fito su tafi gida. Mama taso sake kwana da Gimbi Alh Mudi yace tazo su tafi yana da magana da ita. Ya rage dakin daga Awaisu sai matansa.

Gadon Rumana ya fara zuwa yana murmushi ya rike hannunta “Sweet Son So naji duk abinda kika yi bansan da me zan gode miki ko saka miki ba. I simply love you”

Gimbi tana jinsu hawaye ya zubo mata ta share tana murmushi “ehemm ehemm da mutum dai a kusa”

Awaisu yayi dariya “kinsan uwargida a ko ina ita ce gaba sai na sallameta zan zo wurinki”

Rumana taji gabanta yayi mugun faduwa ta matse hannun Awaisu. Kallon cikin ido yayi mata

“Kada ki karaya kinsan bazan taba wulakanta ki ba” hannunsa ya hade yayi mata alamar yana sonta yadda suke yawan yiwa juna sannan ya juya ya fuskanci Gimbi. Da sauri Rumana ta fice daga dakin tayi sa’a iyayenta da Maamu da Baaba ashe basu tafi ba. Jikin Maamu ta fada tana kuka duk suna bata hakuri Harisu ya sanar da su abinda tayi.

A cikin dakin kuma Awaisu bakin gadon Gimbi yaje duk da yaji kamar ya bi bayan Rumana.

“Amaryar Abban Haris yaya naki jikin?”

“Me kace?”

“Ina nufin dazun nan aka mayar da aurenmu da Gimbiyata”

Wani kuka ne ya taso mata ta rungume shi tana yi yana bata hakuri

“Rumana ce ko? Ashe zan sake amsa sunan matar aure kafin…”

Bakinsa ya hada da nata ya shiga kissing taji kamar yau ta fara ganin Awaisu yau ta fara sonsa.

“Abinda kuka yi min Allah Ya saka muku da alkhairi nagode. Allah Ya baku zaman lafiya da Rumana. Da zan sake haihuwa sai nayi mata takwara saboda tayi min halacci. Ta bani abinda ban taba zaton sake samu ba. Rumana ta hadani da farinciki mara misaltuwa. I love you so much”

Rumana dagewa tayi a sallameta a ranar dole suka bari ta tafi. Ita kuwa tayi haka ne saboda ta bar Awaisu da Gimbi su kadai.

Da suka koma gida su Baaba sai tarairayarta suke yi. Awaisu kansa sai waya yake yawan yi mata a karo na hudu da ya kira ta kashe wayar.

Washegari su Dr. Yana suka zo sai ga su Anti Baraka. Gida ya cika da mutane haka asibitin.

Anyi nasarar kamo Ovi Awaisu yaje police station din ba don an rike shi ba yadda ya fara kwallo da ita da itama a asibitin zata kare. Yana dawowa ya samesu a waje aka ce masa jikin Gimbi yayi tsanani. A firgice ya shiga dakin doctor zai salleme shi Gimbi a wahale ta hana. Gaban gadon yaje ya durkusa ya rike hannunta. Nan likitan yace zuciyarta a kumbure take za’ayi mata gwaje gwaje yace ya amince ko me zasuyi ayi mata. Fita yayi kiran masu daukarta a kaita dakin gwajin.

Awaisu ya shafi fuskarta “Me yasa kika boye mana rashin lafiyarki?”

Murmushi tayi cikin jin ciwo “gashi yanzu ya fito har ka kawo mij sauki”

“Nagode da dukkan soyayyarki gareni Gimbiya. I love you so much”

Kai ta kada a hankali “Abban Haris ka dade baka kirani da sunana ba”

Kanta ya dora a kafadarsa suna zaune kusa da juna hannunsu sarke ” _Nana Fadima_my best friend”

Ajiyar zuciya tayi sai yaji muryarta ta kara yin kasa tana ambaton Allah a hankali. Bayan kamar minti biyu yaji shiru sai sassautawa rikon da tayi kasa. A razane ya dagata ” *Gimbi!!!!*”

Kan kace me dakin ya cika Baaba Hure ta janyeta daga jikin Awaisu ta kwantar tare da rufe mata ido. Hakan yayi daidai da bugawar zuciyarsa ya sulale a kasa shima.

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun…Allah Ya jikanki Gimbiya” cewar Alh Mudi

Kuka ne ya kaure a dakin doctor na dawowa ya tabbatar musu ta rasu sannan aka bawa Awaisu taimakon da ya dace.

Sun ga tashin hankali Rumana ta rinka kuka ta tsorata da mutuwa. Ga su Daula da Awaisu abin tausayi. Kafin azahar an kaita makwancinta suna ta yabon yadda karshenta yayi kyau ana dada yafe mata.

Kamar daga sama Anti Bebi ta shigo gidan ta fada jikin Mama.

“Yaya Amina ki yafe min ni na sawa Gimbiya ciwon zuciya saboda muguwar soyayyar da aka dasa mata na Awaisu. Gimbiya ta tafi ta barni a wannan duniyar abar banza ko gafararta ban roka ba na cutar muku da ‘ya saboda keta”

Mama ta dago jajayen idanu “wadda kika yiwa ma ta tafi me zai hana na yafe miki Bebi? Duniya ce dai ki kiyayeta don bata da alkawari”

Zaman makokin kwana uku akayi sannan suka watse sai adduar Allah Ya jikan mamatanmu Ya bamu cikawa da kyau da imani.

****

*Bayan Wata Shida*

Rumana an gama SSCE ta dawo gida Awaisu ya shirya mata walima ta iya su mutan gidan. Taji dadi sosai suka wuni suna hayaniya da yara yadda suka saba.

Da daddare sun kwanta yake fada mata an kawo kudin Shuhada bikinta saura wata biyu.

“Ashe zamu girgiza jiki a wurin biki”

Baki ya rike yana kallonta “ke! Wa zaki je ki girgizawa jikina?”

Ta hau dariya dama tsokanarsa take yi tasan shi da kishi. To ma me zai kaita rawa gaban wasu da aurenta, yan mata ma ana musu nasihar su bari.

“Dariya kike yi ko. Kin fasa zuwa bikin”

Kafa ta soma bugawa “haba Son So nice fa”

Ya kalleta a karkace “ban sanki ba”

“Shuuuuhhhhh …wayyo bakina naga boni”

Daukota yayi ya dorata kan cinyarsa shima yana dariya “za dai ki ganshi yanzu, me ya sami bakin”

“Ka bani magani indomie mai romo naci”

“Ai ba sai kin roka ba”

Sun dade yana kissing dinta sannan suka kwanta ta kamo hannunsa tana wasa dashi

“Son So”

“Yes kwailar Awaisu”

“Na fasa yi maka albishir din ma”

“Yi hakuri ni da na shaida mata ta tafi kwaila”

Zumboro baki tayi ta tashi zaune tana shafa cikinta “little Gimbi kinji Abbanki yace min kwaila ko”

Zama yayi sosai yana kallon cikin “are you serious?”

Kunya taji ta kwantar da kanta a kirjinsa “jiya da nace maka zamu je asibiti da Amir yana mura harda kaina na kai. Kuma in sha Allah Nana Fadima Gimbiyar Uncle Awaisu da Umm Rumana zan haifa”

“Amin Son So Amin”

Bargo ya ja ya rufe su aka bude sabon shafin soyayya.

     *Alhamdulillah*

Dukkan yabo da godiya ya tabbata ga Allah Madaukakin Sarki da Ya bani ikon farawa da gamawa lafiya. Abinda na rubuta daidai daga Allah ne ina rokonSa Ya bamu ikon aiki dashi. Wanda nayi kuskure daga gareni Allah Ya yafe min daku baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *