UMM ADIYYAH CHAPTER 18 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 18 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 


MUN TSAYA 

To shi kenan. Allah Ya bada sa’‘a, ana dai gamawa a dawo, ba sai mun biyo sawu ba.” Ta fada tana kallon bangaren da Zaid yake tsaye, ya yi shiru kamar ruwa yaci shi, Www.bankinhausanovels.com.ng
koda ya zaci fada za su yi ta yi a kansa, kamar kaji, oho masa. A’a Ummu A. Ai ba wata fargaba, bayan ga ki a nan, Za ki wakilce mu, ai sai na gama hutawana, sannan na dawo.” To ka ji me ka yiwa uwargidanka sati kacal da ‘yan duriya, tace sai ta dauki hutu kan
ta zo?” Idan ta dawo ta ba ki labari, hakan inaga zai fi armashi.” Juyawa ya yi bangaren
driver din. “Malam Garba, ku je kar dare ya yi maku, ku je a hankali dai banda gudu.”
“To Sis. Sai anjima, ki koma ki ci-gaba da aikinki, sai mun yi waya.”
Kafin Umm Adiyya ta ba ta amsa, ta ji hannun Fatima sun zagayeta tamkar a da idan sun hadu yadda ba sa son rabuwa da juna. Tana sakin ta. Umm Adiyya ta
sakar mata murmushi wanda tana tantama idan ba a raunane ya fito ba. “Take care.” Ta ji muryar Zaid ya ambata, kafin ta bar wurin, wanda ya haddasa
mata wani irin turniKi a ranta, yau ta ga ta kanta, wai me ke faruwa da ita ne? Www.bankinhausanovels.com.ng
Ba ta ga shigowarsa ba, tana tsammanin ya fita ne, bayan ta shigo, haka ta koma kan Karashen aikinta na ranar.

*********

Daga tafiyar Fatima zuwa yau kwanaki takwas ne cif! Tun wancan rana kuwa ba ta

ZAMU TASHI 

saka Zaid a idanu, sai idan sun zo fitowa zuwa wurin aiki. Bata sanin inda yake wuni kaf, abinci kuwa daman ba ta taba yi da sunansa ba, idan ma ta yi, to don cikinta ne, ko baKi ma ba su cika yi ba, don an san tana fita aiki. Tun da yamma saKon Zaid ya shigo wayarta, ta yi kusan minti goma tana nazarin saKon. Ba ta san yadda za ta kasafta saKon ba, don haka ta share tamkar ba ta gani ba. Haka nan ta ji sha’awar taci abincin gaske, ta gaji da kame-kame, kullum daga ofis suke odan abinci a kai masu. Yau kam tana dawowa kicin ta shiga ta dora abinci. Ba wani wahalallen abu take yi ba, da ya wuce shinkafa da miya, sai ta yanka avocado da ta samu a cikin firij. Nan ne ma taci karo da abubuwan da akwai a kicin din, wasu an sa su haka a firij, wasu suna (Store).


Gadarar Zaid, sai shi, ko ya fada mata ma ya kawo kaya a kicin din, ta san wannan Www.bankinhausanovels.com.ng
sayayyar ba su shige kwanaki biyu ba, duba da rabonta da kicin din kenan. Ta dade tana kimtsawa tana gyara, tana girki har ta kammala, daidai lokacin da abincin ya nuna. Kankana ta yanka ta sa wasu ‘yan kwanuka masu ban sha’awa. Duk abinda ta yi a food flask ta sanya, ta ajiye kan teburin cin abinci, ta debi nata ta koma falon sama ta fara ci, zamanta ke da wuya, ta ji motsin mutum a gidan.
Ba ta fito ba, ta san Mai-gidan ne, a nan ya sameta a zaune. Sallamarsa kawai ta amsa ta ci-gaba da karatunta, ba ta dago kai ba, ganin bai da niyyar tafiya, baisa ta bar abin da take yi ba. Sai ma juya shafinta na gaba da ta yi. Kin tashi mu je ko?””Ina?”
“Ba ki ga saKona bane, zaki ce ko meye?” “Na gani, kawai ba na jin fita ne.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Kallo ya Kare mata, sannan ya Karasa daya daga cikin kujerun falon ya zauna a kai.
“Kin san da cewa idan na ga daman sa ki a gaba a gidan nan, zan sa ki, kuma zan miki abinda za ki rasa inda za ki sanya kanki ki ji dadi ko? Amma na zabi kar nayi hakan, saboda abubuwa da dama. Idan kuwa zan iya yin hakan, don a tafi a daidai cikin kwanciyar hankali, ina tsammanin ke ma sai ki kwatanta hakan. Ki daina abinda ki ke tunanin zai fissheki,
saboda ba shi zai fissheki ba, the faster you accept this the better, it is wa dukanmu,
saboda haka Umm Adiyya for the last time, ki san da wa ki ke magana, idan kina magana. Ki tashi, ki shirya yanzu mu tafi.” Kau da kanta ta yi gefe, ta bude sabon fejin littafinta a KoKarinta na son yin karatu, duk da a halin yanzun zuciyarta kawai ke tafasa, amma ta daukarwa kanta cire damuwarsa a ranta, don haka ba za ta bari ya san cewa ma al’amuransa sun shafeta ba. Bata ji ba, ba ta gani ba, kawai ta ji hannunta a cikin nasa, kan ta bude baki kuwa, ya daga ta zaune yana kallonta, ba sai ya bude baki ba, ta fahimci a fusace yake. Saboda idanunsa kadai sun isar mata da hakan. Wani abu ta hadiya, sannan ta ajiye littafin rai a Dace, ta miKe ta dauko abayarta ta fito don su tafi, bai sake mata magana ba, har suka kai gida. Ganin su Maami ya sa
ranta ya yi dadi, ta ji kamar ta buya, a nemeta a rasa. Amma ba yadda ta iya, dole Www.bankinhausanovels.com.ng
bayan sun gama gaisawa, sun dan tafa hira su Kara komawa nasu gidan.
Ikon Allah, wai yau ita ce a gidan Zaid a matsayin matarsa, amma abinda ke cikin Kirjinta ya hanata sukunin sakewa ta ji dadin wannan baiwa ta cikan burinta da Allah ya yi mata. Tabbas ta fawwalawa Allah lamuranta, duk kuwa da tsantsar soyayyar da ta taba yiwa Zaid ba ta taba roKon Allah ya ba ta shi ba, a kullum ta tashi addu’arta guda ce. Allah ya zaba mata abu mafi alkhairi a gareta. Ga yadda abubuwa suka kasance, ba ta isa tace ba shi bane mafi alkhairi gareta ba, tunda ba ta san dai-dai ba. Allah ne kawai ya san dai-dai. Wannan ya sa ranar a
hanyarsu ta komawa gida ta Kudurtawa ranta ta daina yiwa Zaid isgilanci. Tunda kamar yadda ya ce shi mijinta ne. Amma kamar yadda ba za ta yi masa
isgilanci ba, haka ta daina kula sabgarsa, duk abinda ya ga dama ya yi mata, nata idanu har zuwa ranar da zai gaji don kansa, ko kuwa ranar da zai san kimarta. Dangane da abinda ya aikata kuma, wancan ya rage tsakaninsa da mahaliccinsa, tunda abinda ya sa ta kambama shi ta daukaka shi ma don daman zuciyarta ta samu buguwar da ba ta taba tsammani bane, tunda yanzu kuwa ta daina sonsa, bata ga me zai daga mata hankali ba.

*************

Zaid yana tuKi, amma ilahirin hankalinsa da tunaninsa sun raja’a ne kan Umm Adiyya da take gefensa. Bai taba tsammanin abin da ya faro kamar KanKanin abu zai girmama har ya jefasu a cikin halin da suke ciki yanzu ba. Ya gama bilayinsa, yasan cewa dole sai ya fuskanci matsalar da ke gidansa, kafin ya samu sassauci, amma ta yaya zai tsaya yarinya Karama tana masa abin da take so, saboda kuskure
Daya tal! A tunaninsa, son shi take yi, har ya jawo hakan, amma cikin tsakanin kwanakin nan yana Www.bankinhausanovels.com.ng tantamar abinda ya gani a tare da ita, sam babu abin da ya saba gani a tare da Adiyya, ta canza gaba daya, ya san shi ya janyo komai, amma bai yi tsammanin zata samu abinda take so, daga gare shi ba. Motsinta ya bi inda take zaune a gefensa. Gyarar murya ya yi, daidai lokacin da ya tsaya a Kofar gidansa ya matsa hon din motar. Har suka shiga cikin gidan, ba ta ce komai ba, haka shi ma. Kwarai ya ji mamakin hakan, tunda ya san zuwa yanzu yaci ace ta takalo wani abin fadin. Ki hada min kayana. Dakin yana gefen damarki, idan kin hau sama.” Ya fada a dake, sannan ya wuce wurin Karamin firij da ke falonsa. Sai da ya dauki lemun sha
guda daya ne ya juyo ya ganta a tsaye, har lokacin a inda ya barota, ya tsaya da murda marfin gorar da yake yi. Kallo ya Kura mata, “Me ki ke jira?”
Karasowa ta yi inda yake tsaye, ta dube shi, sai kuma ya ga ta saukar da idanunta, kafin ta kalli gefe. Yana kallon yadda yatsun Kafafunta suke wasa da kafet din da suke tsaye a kai, ya san a dole za ta yi masa maganar da take shirin yi. Uhmm, ba zan iya shirya maka ba.” Daga girarsa ya yi cikin tsantsar mamakin kalamanta. “Kar ka dauka da wata
manufa, kawai na yi nazari ne, na duba na ga na gaji, ba zan iya fadan abin da ya riga ya faru ba, idan na yi hakan, tamkar na yi da Kaddarata ne. Amma don Allah ina roKonka alfarma daya, kar kasa na shiga sabgarka, domin na yiwa kaina iyaka da duk wani abinda ya jiBanceka. Kamar yadda duniya suka fara
sanin ka a matsayin mijina, ina so ya tsaya a hakan, ka tsaya a matsayin mijina a idanun duniya kawai. Don haka ka hada kayan tafiyarka da kanka. Allah ya kiyaye hanya.” Zaid bai iya cewa komai ba, yana kallo akan idanunsa Umm Adiyya ta juya ta hau matakala zuwa sama. Ya dade abu bai girgiza shi ba irin kalamanta na yanzu. Bai san ko rashin Www.bankinhausanovels.com.ng
tsammantan hakan bane ya janyo, ko kuwa zurfin kalaman nata. Runtse idanu ya yi, domin yanzu ya san tabbas koda bai aureta ba. Umm Adiyya ba za ta taba tona abin da ta sani na daga abin da ta gani ba.
Ajiye gorar lemun ya yi a cikin firij din, ya juya zuwa dakinsa.

************

Tunda ta koma dakinta ta ji kamar ta sauke wani babban nauyi a Kirjinta, a karo na farko tunda aka soma batun aurenta da Zaid ta samu barcin da babu katsewa, tabbas ba za ta kira shi ni’imtaccen barci ba. Amma ta dai samu ta runtsa, har aka kira assalatu kafin ta farka. Ba ta yi Kasa a gwiwa ba, ta shiga shirin tafiya wurin aiki abin ta, kitchen ta shiga ta samu mayonnaise a fridge, ta dafa Kwai ta mutsuka a ciki ta sa sweet corn ta gauraya, biredin da ta gani kan teburin kicin din ta dauka ta shafa hadinta a ciki ta samu wuri ta yi zamanta a kicin din.
Mutum kawai ta gani a gefenta, ba ta san yaushe ya shigo ba, sai kuma Kamshinsa da yake fita a hankali, wanda ya dabaibaye ilahirin kicin din, shudiyar jamfa mai haske ce a jikin sa, kansa ba hula. Kifta idanunta ta yi, ta kau da kanta ta ci-gaba da cin abincinta.
Hannu ta ga yasa ya dauki daya sandwich din kan farantinta, “Ba dakai na yi ba.” Ta fada a taKaice. Ta so ta ba shi dariya, yadda ta hakiKance, “To a sammin.” Bata
kula shi ba, ta dauke farantin ta matsa can daya Dangaren Island din da ke tsakiyar
kitchen din hade da jan kujerar wurin ta zauna. “Allah ya ba ki hakuri.” “To ai ba ka ce na yi da kai ba dama.”Yanzu na fada to.” Tura masa farantin ta yi, ya dauka, ya ja kujera shi ma ya zauna
suna ci, ba wanda ya cewa dan-uwansa komai. Yana gamawa ya dauki gorar ruwa ya sha, sannan ya mike. “Ba rakiya ne?” Ta san magana yake nema, ba ta ba shi amsa ba, don haka, yace, “Sai mun yi waya.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Allah ya kiyaye hanya.” Kawai ta iya fadi. Bai amsa mata ba, ya wuce kai tsaye inda ya bar akwatinsa, a hanyar falo, tana jin lokacin da Mai-gadinsa ya shigo ya fita da jakar. Ba ta tambaye shi inda zai je ba, haka shi ma bai fada mata ba, ita dai ta san
hakan ya fi mata komai dadi Wata Kila idan ya tafi, za ta samarwa kanta hutu. Ta yi tunani Kwakkwara  don samun mafita.

***********

Gaba daya wurin aikinsu, ba wanda ta fadawa ta yi aure, hakan ya sa ta ji wani iri da taga Oga Musa da dan ledarsa na kayan itatuwa ya ajiye mata akan teburinta lokacin birek, wataran haka yake kawowa kowa, amma lokuta da dama ta kula ya fi kawowa idan sauran suna da aiki a gari ko na tafiya.
Ba tun yau ta fahimci inda ya dosa ba, ita dai tana masa sama-sama ne, don ba dadi
ta sace masa gwiwa, don mutumin kirki ne, amma ba ta ba shi fuskar ya ga kamar akwai yiwuwar wani abu a tsakaninsu ba. Sai dai tana zaune, ta ga Hasan ya ja kujerarsa gefen teburin Ayo, “Kai Wallahi
mayen aiki ne, mutum yana so ya yi maka magana ma, sai ka kama ka wani tottoshe kunnuwa da iya fis.”
Kada kai ta yi, ba tun yau ba ta saba da sabgarsu. Hasan son surutu. Ayo shiru shiru, ba daman ya yi wa Ogannin nasa shiriritarsa, don haka Ayo ya raina, shi yake damu kullum da surutu, duk gulmar ofis din a bakin sa zaka samu. Ranar kam ma aiki suke da shi a server room, amma ta tsaya ta duba wasu
abubuwa a komfutarta. Kwatsam! Ta ji Hasan ya ce, “Kai ka na da labari anyi bikin Oga Zaid kuwa?” “Eh mana.” Tabdijan! Yaya aka yi duk ba mu sani ba, sai kai Ayo? Yanzu na ke ji manyan kawai suka samu halarta, kai meye naka da har ka samu labari?”
“Gayyata ta aka yi, ka san sai jigogi ake gayyata irin wadannan abubuwan.” Umm Adiyya ta gimtse Www.bankinhausanovels.com.ng dariyarta, ta san Ayo ya yi ne kawai don ya rabu da damuwar Hasan. Amma dai kam wannan bikin, sai ka ce wani aikin sirri, mu da muke ta jira abin ya zo, don mun san dole ayi abu wurin auren Oga Zaid, akwai shi da aji, komansa daban yake yi.” Lokacin ne ya dago kai ya kula da idanun Umm Adiyya a kansu, da sauri ta kawar da kanta. Yi haKuri Hajiya, kar ki ce na tabo yayanki fa yau.” Murmushi ta Kakalo kawai ta
girgiza kanta. “Amma Hajiya ko ki gayyace mu ki ce gidanku akwai aure, ai da mun zo cin kaji da jollof.”
“Kai da ka ce mai auren bai gayyace ku ba, ni kuma yaya zan gayyace ku? Ga shi ka yi masa fatan alkhairi, ai ya wuce komai.” “Kuma sai ki ka yi ta zuwa abin ki aiki. Ai ni ciwon Karya zan yi na Ki fitowa.” “Sai ka ce mace, kar ka bada ku dai Hasan.” Ta fada tana tattara ababen da za ta
bukata a server room din, don idan ta tsaya a nan, ba tantama abubuwan da ta danne za su taso. Hasan bai iya dago zance ya bar shi ya wuce ba.
Yana komawa wurin zamansa ne ya ce. “Na so na ga irin liyafar da aka yi a auren Oga. Ayo wa ka ce ya fada maka batun auren?” Ba ta tsaya jin amsar da Ayo ya bayar ba, ta fita daga ofis din tana saKe-saKe a ranta. Yau kwana guda da tafiyar Zaid, ba ta kira shi ba, haka shi ma bai kirata ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Koda suka yi waya da su Mama a yammacin jiya, bayan ta kira ta ne. Umm Adiyya ta ce bari ta kira, ta kashe wayar Maman, sannan ta sake kiranta.
Ina wuni Mama?” Lafiya Kalau, yaya wurin naku su Maami duk suna lafiya?” “Alhadulillahi. Lafiyarmu Kalau;” Malam ma sun kira da safe, wai sun wuce, ko kun ji isarsu?” Nan aka bar Umm Adiyya da wurkila idanu. To me za ta ce? Ba ta ma daga wayarta
ba bare ta gwada kiransa ko kuwa ba ta da lambarsa ne? Na biyun ya fi armashi. Don haka ta ce, “Bai kira ba dai tukun, ba lambarsa ta can, anjima zan sake gwada na gidan, mu ga ko yana amfani da ita a can.”
To ai shi kenan. Allah ya kai mu. Ki gaida su Abban naki.” “Za Su ji, a gaida su Fadeela. Ba ta yi hutun ba ko?” Mama ta yi ‘yar dariya ta ce, “Ga su nan dai tukun suna shirin jarabawa, ai ta dage ita tana hutu, sai wurinku za ta tafi.”
“Muna jiranta, a gaida su Anty.” Suna ajiye waya ta saki ajiyar zuci. “Whoah,” Yau ta sha da Kyar. Dole yau ta kira shi kenan, ko don Mama, ita fa sam sabgarsa ce bata cika son shiga ba. Tana isa gida, ruwa kawai ta watsa, sannan ta zauna da wayar a hannunta tana kallon fuskar wayar.
Ta yi minti goma da wayar, tana tunanin ta kira ko kar ta kira. Tana kira zai Kara daukar kansa sama da yadda yake ji yanzu, idan bata kira ba, kuma ta yi rashin kirki. Zabura ta yi lokacin da wayarta ta saki kuwwa, kasancewar ta yi nisa a nazari, kallon
wayar ta tsaya yi, har dai ta tsinke, a karo na biyu ne ta daure ta daga. “Assalamu-Alaikum.”

********

BABI NA SHA SHIDA “Assalamu-Alaikum.”

“Wa’alaikumussalam, kina lafiya?” Abin da al’ajabi, amma ta tabbata da gaske hakan ne, wani abu ne ya girgiza dan cikin Kasan Kirjinta, dakewa ta yi ta amsa. Lafiya Kalau. Alhamdulillahi. Kun _ isa Www.bankinhausanovels.com.ng lafiya?” Ba mu dade da isowa ba, da wannan lambar zan dinga kiranki, ki adanata, zan kiraki can anjima, idan na samu natsuwa.” “Uhum, Mama ma ta kira dazu.” “Eh, yanzu zan kirasu duka.” A huta gajiya.”

Dif! Shiru ya ratsa tsakaninsu, kowane cikin

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *