KASHE FITILA CHAPTER 9 BY BATUUL MAMMAN

 KASHE FITILA CHAPTER 9 BY BATUUL MAMMAN

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Bai sami damar bata amsa ba Harisu ya dawo. Cigaba da buga mata bayan yayi ai kuwa ta sake kwashewa da dariya. Da aka bata ruwan kurba daya tayi ta ajiye amma bata yarda ta sake kallon Awaisu ba.

Harisu ya sake maimaita tambayar a karo na uku ta sadda kai kasa tace “Uncle ne”

“Ya wuce Uncle dinki Rumana. Mijinki ne kuma nasan cewa bakiyi kankantar da zaki kasa fahimtar me ake nufi da wannan kalmar ba”

Idonta taji ya ciko da hawaye ta kasa dago kanta don kada su gani. Tana ji ya cigaba da magana tun tana daurewa sai ta soma kuka.

“A da kinsan Awaisu a matsayin kawunki ne kawai. Amma yanzu igiyar aure ta shiga tsakaninku saboda haka ina ja miki kunne wallahi Rumana kada ki kuskura raini ya shiga tsakaninku wai don kina matarsa. Aure girma ne dashi da daraja. A

yanzu duk duniya babu mai iko dake sama da Awaisu. Kamar yadda na sanar da yayunki biyu da suke gidan aure kema ina horonki da ki rike Allah da ManzonSa iya tsahon rayuwarki. Ke ganau ce ba jiyau ba akan abubuwan da suka faru a gidansa a baya. Da wannan nake baki shawara ki zama zama tauraruwa mai *kunna fitila* a gidan da aka dade da *kashe fitila*. Ki kiyaye dukkan gabobinki daga sabon Allah musamman shirka ita kam kinsan Allah baya yafewa mai yinta idan ya mutu bai tuba ba. Ana ta cewa ke yarinya ce an aurar dake amma ni nasan kuruciya daban zaman gidan miji daban. Kada ki bani kunya kuma kada ki bawa mijinki kunya. Soyayyar da yake yi miki kada ki bari ta zama makaminki na musguna masa. Abu na karshe da zan fada miki kuma gashi a gabana shaida shine ki sawa ranki kinyi aure na mutu ka raba. Duk ranar da taku ta hadaku saboda rayuwar yau da gobe har shaidan ya baki shawarar kiyi yaji to ki sani kiyi kayanki a cikin gidanki. Baki da masauki a gidan nan indai ba ziyara ce ta kawoki ba. Su Haris kannenki ne kuma ‘ya’yanki yanzu. Ki rungumesu fiye da yadda kika saba a baya.”

Kuka take yi sosai tana jin kamar yanzu za’a kaita gidan miji. Harisu ya juya ga Awaisu yana murmushi.

“Abu daya zan fada maka dan’uwana. Kai miji ne kuma uba ga Rumana. Ka tafiyar da ita da fuskar da ta dace ku zauna lafiya.”

Daga nan yace Rumanan ta fita ta jirasu a bakin kofa. Haka ta fita fuska duk hawaye da majina. Hannun Awaisu Harisu ya rike.

“Sai kayi hakuri yara biyar ne yanzu a gabanka. Mata duk girmansu basa rabo da shirme da shiririta. Nasan ba sai na fada maka ba amma don Allah ka rike min ita amana”

Duka su biyun zukatansu sun karye. Awaisu ya kara karfin rikon da suka yi da hannuwansu na dama.

“In sha Allah nayi maka alkawarin bata dukkan kulawar da ta dace. Allah Ya saka muku da mafificin alkhairi. Zanyi kokari naga cewa kamar yadda kake alfahari dani a matsayin kani zakayi a matsayin suruki”

Harisu ya kai masa duka a kafada “ana maganar arziki ka sako wasa. Tashi kuje Allah Ya bada zaman lafiya. Na manta ban fada maka ba munyi magana da Alh Saminu yace iyalinsa zasu je Abujan idan an gama biki. Abin Maamu dai baiyi masa dadi ba”

“Yaya ya muka iya. Nagode”

Yana fitowa ya ganta a durkushe a wurin har lokacin bata dena kuka ba. Hannunta ya kama jikinta a sanyaye suka tafi dakinsa. Kamar kada ta shiga da ta tuna yadda suka kare daga cin tuwo. Sai ta daure don jin nasihar Harisu take tamkar a lokacin yake yinta.

Bandaki ya nuna mata shi kuma ya zauna “jeki ki wanke fuskarki magana zamuyi”

Allah Yasa ba wani fada shima zaiyi mata ta fada a ranta sannan taje ta wanko ta dawo.

A kan kafet ta zauna nesa dashi sai ya rabu da ita.

“Umm Ruman”

A ladance tace “na’am”

“Duk kinji abubuwan da Yaya ya fada ko?” Ta gyada kai. “Don Allah ki zama irin matar nan da ko miji yana so ko baya so sai ta shiga aljanna saboda kyawawan dabi’u da mu’amala”

Tana goge hawaye tace “to”.

“Ranar monday ya kamata ku koma school amma bazaki je ba. Yaya ya nemi Principal dinku za’a karbo miki takardar transfer. Na cike miki form na wata makarantar so nan zaki koma kiyi SSCE dinki”

STORY CONTINUES BELOW

Kanta har lokacin a kasa tace tafi son komawa makarantar da ta baro.

“Uhmm uhmm Umm Ruman. Bana son surutu ne a school kawayenki su san kina da aure. Yawancin makarantu basa yarda su dauki matar aure. Inda zan kaiki ma ban fada musu ba kema ko yaya kike da kawa ki bar zancen sai kin gama jarabawa.”

“To shikenan nagode” ta iya furtawa.

Tasowa yayi yazo kusa da ita ya kama hannunta yana murzawa.

“Duk kin zama wata saliha ko fadan ya shiga ne da kyau. Amma kada ki manta kinci bashin kirana Son So a gaban Yaya”

Dago kai tayi ta soma dariya.

“Lallai yarinyar nan baki da tsoro amma nasan ta inda zan kamaki. Sati biyu ne fa ya rage miki ki biya bashi”

“Wai da gaske sai na biya. Na zata ko bashin naci kaine zaka biya. Nice fa Uncle, Rumana Son So” ta langabe kai

“Abin naki harda blackmail kuma. To Son So na hakura duk abin da ya biyo baya ba biyan bashi bane so ne kawai”

Sonta yake ji ko ina a jikinsa yadda take langabewa tana shagwaba. Hancinta ya ja yana son kissing dinta amma baya jin zai hakura a nan gara ya bari sai lokacin da ta dawo gidansa gabadaya.

*****

Gaban maigadi Gimbi taje ta zaro wuka daga jakarta jikinsa ya hau bari kamar mazari.

“Ko ka bude min ko na yanka kaina kuma nace kaine kayi niyar….”

Bai jira ta gama fadin abin da tayi niyya ba ya tashi ya bude gate din a gaggauce. Dariya tayi ta shiga mota tana takaicin yaya akayi wannan tunanin baizo mata ba tuntuni. Da zata fita ya leko yana sauka lafiya ta sha kunu.

“Idan ubangidanka ya sami labarin na fita zaka iya rasa aikin nan”

“Wa ya aikeni Hajiya. Ke dai Allah Ya kiyaye hanya kawai”

Gidan Ovi ta je kai tsaye. Ko shiga batayi ba suka fito ita da Rita suka wuce gidan Boka. Gimbi tana kuka tana fada masa matsalolinta da rashin biyan bukatarsu.

Fuskarsa a murtuke yace “Gimbiya kiyi hakuri daga yau babu sauran aiki a tsakaninmu”

Yadda gabanta ya yanke ya fadi ko iyayenta ne suka rasu iya tashin hankalin da zata ji kenan. Dan akwatin sarkar ta dauko ta bude ta ajiye a gabansa.

“Ka taimakeni ka rufa min asiri ka magance min matsalolina. An raba ni da yarana da mijina ga kishiya. Iyaye sun juya min baya. Bani da kowa sai kai sai su Ovi”

Wata rawa ya tashi yayi yana juyi a gabansu sai ga tusa ta fito mai uban karfi hade da wari. Suna toshe hanci sai Rita ta saki tata Ovi ma tayi. Gimbi wari kamar ya shaketa ta rasa dame zata rufe hanci Boka yace “kinga dalilin da yasa bazan kara yi miki komai ba. In takaice miki ma dai babu wani abu da zan sake baki yayi tasiri “1

Ga wari ga tashin hankali “Boka me nayi haka da zafi?”

“Kinsan Gogojiya?”

“Abinci ne?”

“Aljana ce da ban taba mu’amala da ita ba. Wannan tusar ma ita ta sakani sakamakon aikin karshe da nayi miki. Bansan wa ya turo ta ba amma tayi alkawarin yi min kisan wulakanci idan na sake yi miki aiki kuma tace ki kiyaye haduwarku. Aljanu na kaf sunki zuwa wurin nan saboda ita”

Gimbi ta rasa me zata ce. Boka dai ya dage yace ta fita daga ita har su Ovi. Da suka fito su biyun tusa suke kamar su tada jejin Gimbi da gudu ta arce ta barsu. Ji tayi kamar ana binta a guje duk tsigar jikinta ta tashi….Gogojiya tayi wata dariya. Albarkacin musuluncin da ta karba lokacin da Mal Ridwan ya rabata da Fanta yasa bata sabauta Gimbi ba a wurin. Hajiya Fanta bata nemi taimakonta ba saboda shawarar malam amma taji komai kuma babu wanda ya isa ya dagawa Haj Fanta yatsa tana gani ta kyale.

Duk yadda Gimbi taso zira mukullin motar tamkar an shafe wurin bata ganin wurin zirawar ta saki mukullin tayi gaba. ga tsoro da gudu tayi titi tana tsayar da motoci da kyar wata tasi ta tsaya ta shiga. Tana ji ana ja mata dankwali da zani irin yadda tasa akayiwa Anti Bebi. Da kyar ta iya karasawa gida ta shiga kamar walkiya maigadi dai bakinsa alaikum.

*****

STORY CONTINUES BELOW

Washegari tun bayan asuba Awaisu ya gama shiri saboda baya son suyi tafiyar dare. Gashi akwai aiki ranar litinin yana bukatar ya dan huta ko yaya kafin wayewar gari.

Ruwan tea kawai ya iya sha ya shiga wurin Maamu. Sun dade suna hira duk da sun raba dare jiya. Nasiha take masa akan rikon addini da dena sakaci da addu’a. Daga wurinta yaje ya jima wurin Baaba ya fada mata karshenta bazai sami dawowa ba har a gama bikin.

“Babu komai ai dani za’a kawo amarya sai ka gyara dakuna biyu. Wai ina ma take ne miji zaiyi tafiya ana ta baccin asara.” Ta fada tana tashi.

Awaisu yace “Baaba kyaleta kinsan bata jindadi “

“Bari na tura a kirawo min ita kuma bance ka kulata ba tunda kace a kyale mara lafiya”

Murmushi yayi ta fita ba jimawa sai ga Rumana ta shigo tana murza idanu bacci bai isheta ba.

“Baaba gani” tace tana neman wurin kwanciya akan gadon. Jin ba’a amsa ba tayi kwanciyarta. Sai lokacin ta kula da Awaisu akan kujerar da take gefen kofa. Da sauri ta tashi tana gyara hannun riga. Dogon wando ne da yar riga mai karamin hannu. Kankance ido yayi daga inda yake “Son So haka kike yawo a cikin gida nan da wannan kayan? Bana so please ki rinka saka mayafi ko hijab a kai”

Jikinta ne yayi sanyi tana tunanin ko tayi masa laifi ta soma bashi hakuri. Ganin garin da duhu baifi bakwai da rabi ba gashi tasan dai babu kowa sai iya su na gidan.

Bakin gadon ya dawo ganin ta damu “ba fushi nayi ba amma ina da kishi bana son kina yawo a haka kowa na ganinki.” Goshinta yayi kissing ya tashi zata fito yace ta zauna a dakin ta nemi hijab kuma ya yafe rakiyar kada ya wuce da ita. Daga dakin tayi masa adduar sauka lafiya ta koma tana jin ba dadi. Shi kuwa bata san ganin da yayi mata a haka bane ya ruda shi. Yana mata kallon yarinya ashe ta wuce yadda yake tunani. Ko kadan bazai juri cigaba da ganinta a haka ba shiyasa yayi saurin tafiya.

******

Sun isa Abuja da wuri kamar yadda yaso suna shiga gidan yaga babu motar Gimbi. Maigadi ya tambaya yace tana ciki amma bai san inda mota take ba.

Da ya shiga a bakin kofar dakinta ya tsaya tana kwance akan gadonta da kayanta tun na jiya har lokacin batayi wanka ba.

“Gimbi ina motarki?”

A gigice ta tashi sai lokacin ta tuna inda ta baro motar. Jikinta ne ya hau rawa ta rasa amsar bashi. Ya kula da yadda take yasan bata da gaskiya.

“Na baki zuwa gobe ki dawo min da motar nan” kawai yace ya juya ya tafi dakinsa.

Gimbi ta shiga tashin hankali. Ovi ta kira ta nuna mata jiya basu ji dadi ba ta tafi ta barsu amma basu ga mota ba. Bayan kuma ko awa daya basuyi da mai saya ba sunyi sa’a duka takardun suna ciki suka yi cinikin gaggawa shi kuma yaji arha banza ya biya ya dauka.

Ba karamin tashin hankali suka yi tayi da Awaisu akan motar ba taki fada masa inda take. Kyaleta yayi ya cigaba da shirinsa na zuwan Son So Rumana.

A can Fika suma nasu shirin suke yi. Amarya tana ta shan gyara daga wurin iyaye ko ta ina. Ana gobe fara bikin wata ‘yar abokin babansu na bayan layi wanda da yayanta yaso Rumanan tazo. Lokacin suna daki da yayyenta mata ana ta chapta da ‘ya’yan gwaggwaninta su Baraka sa’aninsu.

Da sallama Zee ta shiga tana ta washe baki “Rumana amarya yaya shirye shirye”

A darare ta amsa mata saboda ko da can ba wani shiri suke da ita ba.

“Dama cewa nayi bari nazo muyi maganar shirin bikin. Naga baki aiko mana da kati ba mu da sauran kawayenmu gashi gobe za’a fara “

Sauran fita sukayi sai Iman da Rumana. Rumana tace mata bikin ne yazo a gaggauce ba wani abu zasuyi ba daban da na iyayen.

Sake washe bakin nan nata tayi “Hakan ma yayi amma kin ware kawaye masu rakaki Abuja? Kinsan dole aje da kawaye saboda komai yafi tafiya daidai. Idan wata bata rigani ba zanyi miki babbar kawa”

Iman ta soma dariya ita kuwa Rumana cewa tayi  ” Zee baki ji haushi ba ko saboda yayanki?”

Zee ta firfito da idanu “akan me idan ba bakinciki ba haushin me zanji. Abuja fa zaki koma zaman aure. Ni dai don Allah aje dani ko abokin mijinki na samu ya ajiyeni a can. Kodayake ance mai kudin kawun nan naku ne. Ni wallahi ko drebansa ne ina so kiyi min hanya kinji”

Iman kasa boye dariyarta tayi suka ce indai an yarda a gidansu zasu tafi da ita Abuja. Ledar viva ta hannunta ta nuna musu.

“Ai tuni na tambayo a nan ma zan rinka kwana har a gama bikin.”

Washegari da safe aka fara biki irin na Bolewan Fika. Sunyi taronsu na kwana uku ana gobe  za’a kaita aka yi mata lalle mai kyau ja da baki.

Tsabar gyaran da ake mata ta chanja gabadaya ta cicciko sai shekin amarci take yi.

Ranar asabar da sassafe aka kama hanyar Abuja. Motoci biyar akayi da guda daya ta kaya a haka ma ana ta rage masu zuwa. Tasha kuka dai kamar bazata tafi ba. Maamu tayi ta bata baki tace mata tana nan tafe. Ita da Baaba sunyi rawar gani a wurin bikin nan.

Baya gidan suka iso sai Gimbi a daki ta cika tayi fam saboda bakinciki. Guda su Hindatun Bomai da Tikeke suke yi da gayya don taji haushi. Dakunansu duka wani matashi cikin samarin Fika da yake kaiwa shago shine ya nuna musu. Nan aka shiga sauke kaya suna ta hayaniya a cikin gidan.

Rumana ta idar da sallah Iman ta miko mata wayarta dake ta ringing. Ta dauka da sallama ganin sunan mai kiran harda faduwar gaba.

“Wa alaikum salam wa rahmatullah wa barakatuhu….welcome home Son So. Ina hanya in sha Allah na fita ne saboda bakin su fi saurin sakewa. Ki gaida min su Baaba kafin na iso”

Jikinta ne taji yayi sanyi sai kuma tsoro da fargabar yadda zata zauna da Uncle Awaisu a matsayin mijinta.

Awaisu na ajiye wayar ya mayar da hankalinsa ga abokinsa Nuru wanda yake ta masa dariyar shakiyanci.+

“Angon Rumana kana burgeni fa. Wani salon soyayya nake gani da ban sanka dashi ba”

Awaisu ya shafa sajensa da aka gama gyarawa tare da aski.
“Dole ka sami bakin tsokana mana tunda ka baro aikin da ya hanani zaman gida na tarbeta”

“Seriously abar maganar wasa wallahi so nake na taimaka wurin kara kafaka a zuciyar Rumana. Kasan na dade ina ce maka yarinyar tana da nutsuwa tun sanda na ganta a gidanka”

Tunawa yayi da yadda ta rinka tsokanarsa zuwansa na karshe har tana kiransa Son So a gaban Harisu dariya ta kufce masa a zuciyarsa yace idan ma da nutsuwa akwai fitina.
“Yanzu dai a ina zan sami riga irin wadda nake so tunda kaga komai ya kure?”

Nuru matarsa ya kira ta kwatanta masa wani babban shagon sayar da kayan mata da yake tashe a Abuja suka dauki hanya shi da Awaisu yana yi masa bayanin cewa abincin tarbar su Baaba gidan Alh Mudi sun dauke masa. Shi har kunya yake ji ma duk da abubuwan da suka faru yasan suna yi ne domin rage girman laifin Gimbi.

Kimanin kwana biyar baya kenan da ya bawa Nuru labarin abubuwan da suka faru a gidansa da auren Rumana . Sosai Nuru yaji haushi dama amininsa ne tun Jami’a a Bauchi. Sai dai shi a wani kamfani mai zaman kansa yake aiki.
Awaisu bashi da yawan surutu kuma da kunya dai kace uwar ‘ya’yanka ke bin bokaye. Shiyasa ya kasa fada da wuri. Nuru ya tausaya masa duk da yace a baya ya dan kula da abokin nasa ya sauya amma baya son zurfafa bincike a rayuwarsa tunda alakarsu bata chanja ba sai in ka cire rashin barinsa ya kawo tasa mahaifiyar su gaisa da Maamu, kullum yayi magana sai ya bashi uzuri har ya hakura.
A gaban matar Nurun ya bada labarin itama ta kadu sosai amma dama can ba wata aminta sukeyi da Gimbi ba. Shi kuma yace ya bayar ne saboda itama da surukarta suke zaune ya kare da yi mata ‘yan nasihohi akan son zuciya.

Washegari sai ga Nuru a bankinsu yace Kubra ta dage sai anyi taro a gidan Awaisu na tarbar amarya. Da fari baiyi tunanin hakan ba amma abokin nasa da matarsa suka dage cewa hakan ba karamin farantawa Rumana da iyayenta zaiyi ba. Dadin dadawa ‘yan hotuna da amare keyi da mazansu lokacin biki itama zata samu. Wannan zai taimaka masa wurin kara saka mata nutsuwar zama dashi. Da gaske suka yi ta jan ra’ayinsa sai gashi ana ta shirye shirye sun kama wuri inda za’ayi event din. Abokansu da matansu suka gayyata da gidansu Shuhada da suka dawo daga tafiya sai kuma mutan Fika da basu san za’ayi ba ma. Kusan komai sun gama sai kayan da Rumana zata saka ne Awaisu yake ta ruwan ido gashi har sun iso gari kuma washegari bayan magariba suke son ayi.

Kamar yadda Kubra ta kwatanta kofar wani babban shago suka tsaya mai suna *J.J.Maji Palace*.

Wurin yaji kaya na gani na fada masu kyau sai tsada. Nan ma dai ruwan ido Awaisu yake yi kowacce ya taba sai yaga tafi dayar kyau. Burinsa Son So ta fito sosai ta kece raini. Yarinyar shagon ya tambaya ko akwai irin wadda amarya zata saka amma fa ba fara ba ta auren nasara. Cewa tayi tana zuwa ta shiga wata kofa sai gata sun fito da wata kosasshiyar mata. Kiba gareta sosai tana tafiya da kyar ta baza zobba a kusan duka yatsunta da awarwaro. Da fara’a ta tarbe su.

“Suna na Hajiya Fattu.  Ku biyoni akwai wasu rigunan a wannan dakin irin wanda kuke bukata”

Suna shiga idon Awaisu ya sauka akan wata doguwar riga golden mai matukar kyau anyi mata ado da yellow din duwatsu marasa turuwa. Doguwa ce da dogon hannu kuma bata cika ado ba amma kana ganinta zaka ji kamar ka dauka. Dariya Fattu tayi don tasan rigar yake so saboda kyaunta. Ganin yadda yake taba jikin rigar a ranta tasan dole ya dauka tuni ta kara dubu goma akan kudinta.

STORY CONTINUES BELOW
Bai musa ba Nuru yana rike masa hannu ya dauko rigar yace yana bukatar mahadi. Fattu ta dauko masa wani mayafi mai wasu irin dutsu mai kyau shime light yellow ta kawo yace saura takalma da jaka. Komai ta hada masa ya bata kati da kanta ta zura a POS ganin manyan costumers ne gashi harda su sarka da abin hannu duka ya saya.

“Yallabai naji kuna zancen taro gobe hala mai saka kayan gobe zatayi amfani dasu tunda kun ce na amarya ne?”

Nuru yace “ikon Allah ke dai ki cire kudinki mana ki bamu mu tafi”

Ta sake dariya “ai naji dadin ciniki ne shine zan fada muku ina kwalliyar amare idan kuna so. Wallahi ba kowa nake yiwa ba ma saboda yanayin aikina.”

Awaisu ya dan sake kallonta. Lebenta wani irin janbaki ne yayi dau shi ba green ba shi ba shudi ba ga su eye shadow komai ya fito rambajau. Baya fata ko kadan Rumanansa tayi ado irin wannan. Kula tayi da yadda yake kallonta tayi yar dariya
“Don’t mind me haka nake tawa kwalliyar amma ka bani dama ka ga yadda zan fitar muku da amaryarku”

Bai sake magana ba suka fita. Zasu tafi yarinyar shagon ta biyosu tana magiyar kada dama ta wuce su bata taba jin Fattu tayi tayin kwalliya ba duk da kwarewarta. Nacin da ta kafa musu yasa shi amincewa tare da sharadin ana gamawa idan batayi masa ba bazai biya ba.

Nuru ya fara ajiyewa a gida sannan ya wuce gidansa zuciyarsa tana dokin haduwa da Son So.
*****

Kaf duniya Gimbi gani take babu wanda yake cikin damuwa da bacin rai irin nata. Tasan basu taba zancen daga kanta babu kari ba duk da kishinta amma ko Awaisu zai karo aure ba irin wannan cin fuskar ba. Laifin da yake ikirarin tayi masa har yanzu bata gani ba. Yanzu da bata dauki mataki da wuri ba dama niyar Maamu ya auri Rumana da tuni tasa ya saketa anyi auren. Wane makircin uwarmiji ne bata da labarinsa. Abu daya ta sani tunda bai saketa ba yana sonta har yanzu. Amma ina mafitar dawo da fadarta zuciyarsa ta koma Gimbiyar Awaisu?

Anti Bebi ce ta fado mata. Ba don taci amanarta sun rabu ba ai da itace mai bata shawara. Kuma ta tabbatar da sun dade da mantawa da matsalolin nan saboda ita Anti Bebi ko babu boka zata iya zama da makircinta.

Tsaki tayi dole itama ta tashi tsaye ta nemi hanyoyin da zata tsorata Rumana ta fita da kafarta ko da asiri ko babu. Guda ta jiyo daga falo hakan ya tabbatar mata da dawowar Awaisu. Mikewa tayi zata fita taji kanta yayi mugun sarawa dole ta zauna zuciya na tafarfasa.

Murmushi yake ta yi matan da suke falon suna ta tsokanarsa. Abinci ne kuloli manya uku a wurin suna ta zubawa. Anti Suwaiba tace masa su Baaba suna dakin Maamu.

Yana Sallama Rumana na fitowa daga wanka. Dama bandakin ne farko kafin a shiga ciki babu wanda ya gansu. Cak ta tsaya suka hada ido sai ta koma ciki da sauri ta bugo kofar harda hadawa da yatsanta don sauri. Ihu yaji ta saki daga ciki tana washh yace maganin me gudun miji kenan a hankali sannan ya wuce yana murmushi.

Kafin ya gaishe da Baaba su Anti Ummukulsum suka yi masa caa ana ta barkwanci. Haj Umma yayar Maman Rumana da matan ‘yan uwansu maza sune suke tare masa ana ta dariya.

Dadi ya kama Baaba tayi masa sannu da zuwa sannan tace basu gane dakin Rumana ba sannan suna jiransa ya nuna inda zaa jera mata kayan kitchen domin da safe zasu koma.

“Haba dai Baaba kamar ana korarku. Akwai walima da za’ayi gobe bayan magriba tafiyarku sai gata ma. Jibi ku huta”

Anti Baraka tace “amma dai wasa kake yi ko Awaisu”

“Wallahi da gaske nake abokina da matarsa ne suka shirya. Ai dai bazaku tafi muje mu kadai kamar marasa dangi ba”

Duk da suna masa kawaicin basa son dadewa a gidan amma ya kula sunji dadi da har yayi wannan tunanin. Tashi yayi da ledojin hannunsa Hindatu tana shigowa lokacin tace suna jira a raba kazar amarcin a aiko musu. Nan fa ta bude kofar sabuwar tsokana ya fita yana dariya.
STORY CONTINUES BELOW
Dakin Gimbi ya wuce tana zaune kamar wata sabon kamu yace yasan tunda suka zo bata fita ba taje ta gaishe da Baaba.

“Amma ka rainani Awaisu. Ni Gimbi naje na gaishe da kakar kishiya sai kace wadda aka cewa jeki kya gani” tana magana tana huci

Shi kuwa ko a jikinsa yace “to meye maraba, kuma ina so ki kiyaye Rumana ba kishiyarki bace”

Zaro ido tayi sosai “to meye matsayinta? Kada kace min nemanta kake yi babu aure da yardar iyayenta”

Hannu ya kada yana fita  “wannan kuma ya rage naki. Kishiyoyi a sanina miji daya suke aure….”

Yafi minti biyar da fita Gimbi tana ta juya maganar Awaisu a ranta. Me yake nufi???
******

Kafin ya shiga dakinsa ya nuna musu kitchen yace suyi jeren kayan a nan sannan ya bude dakin da ya tanadarwa Rumana wanda duka kayan bukata na dangane da furtuniture da electronics ya zuba.
Daga Fika sun taho da bedsheets da ‘yan abin da ba’a rasa ba tunda babu iyayen da zasu so aurar da yarsu sikau.

Wanka yayi ya kwanta don ya gaji da wuri ya fita. Rumana yake son sake gani amma idanun jama’a yayi yawa kada a ga rashin hakurinsa.

Anti Ummukulsum ya kira ya fada mata ya siyowa Rumana riga yana son ta gwada kada gobe a sami matsala. Ya nuna mata baya so kowa ya gani sai goben.

“Ko dakinta kuje ta gwada bari na miko miki rigar”

“Dakinta da mutane ana gyara zan turo maka ita”

Kafin ya sake magana ta katse wayar. Dariya tayi tasan yana son ganin matarsa ne kuma babu dalilin hanawa. Dakin Maamu ta koma ta kirawota. Daga wurin korido suke tsaya tace taje dakin Awaisu yana kiranta zai bata sako.

Gabanta taji yayi wani irin bugu ta kasa ko da daga kafa balle ta tafi. Anti Ummukulsum ta zare mata ido tace ta wuce kafin ranta ya baci.

Yatsanta data matse a kofa ta dagowa Antin idonta cike da hawayen tsoro tace “ciwona ne yake zafi Anti bazan iya zuwa ba”
Haba ta rike tana kallonta “Rumana ke da ba da yatsun hannu kike tafiya ba meye zai hanaki zuwa. Daure kije sai kice nace ya baki magani “

To kawai tace ta nufi dakin nasa rike da hannun da ta manta yana zafi sai yanzu. Anti Ummukulsum ta girgiza kai tana tausaya mata. Tunda suka iso ta kula jikinta yayi sanyi. Zama a matsayin matar Awaisu kadai ya isheta to ga Gimbi kuma a gidan abin yayi mata yawa.

Da kukan tayi sallama ta shiga dakin bayan ya amsa. A bakin kofa ya tarota jin tana kuka.

“Waye ya taba min Son So uhmm? “

Yatsun da ta matse guda biyu ta daga tana nuna masa. So take kawai yace ta fita don ji take kamar ko numfashi tayi a dakin idan ta fita za’a gane. Karo na farko da ta taba shiga dakinsa kenan duk zamanta a gidan. Ba don a tsorace take ba da tace dakin ya hadu kamar mai shi.

Hannun nata ya kalla “me ya same shi?”

“Anti tace nazo zaka bani magani. Matsewa nayi da kofa”

Idanunta sun cika da hawaye yasan tsoro ne ya cikata yace akwai aiki a gabansa.
Yatsun ya kama sai kawai ta fashe masa da kuka. Yanzu duk wanda ya ganta cewa za’ayi daga dakinsa ta fito ko da tace Anti ce ta turata karbar magani.

Hanyar gadonsa ya ja hannunta ta soma turjewa jiki na rawa. Kin sakinta yayi sai ga hawaye kamar an bude famfo. Cikin kuka tace
“Ayya Uncle ni kam naga boni yau din nan”
Dariya yaso yi sai ya matse yace “ina yake” yana zaunar da ita akan gadon.

Kallon rashin fahimta tayi masa yace “kince kinga boni ni kuwa ban ganshi ba”

STORY CONTINUES BELOW
Kanta ta nuna “ba gashi ba.ni.anan dakin.da…..daa…kai!”

Daga mata gira yayi yana tsaye a gabanta “amma kina da matsala, ke da kika zo karbar magani. Dauko miki zanyi kisha saboda kada kiyi zazzabi”

Yana kallo duka hannuwanta biyu tasa ta dafe kirjinta irin na hankali ya kwanta ta dago kai harda murmushi “ashe magani nazo karba fa. Bani sai na sha a wurin Baaba” ta mike tsaye sai ya sake komawa gabanta ya tsaya.

“Ki dena murna nan din dai zaki dawo ki kwanta. Yarinya sai tsoron tsiya duk kin firgice” yantsun nata biyu ya riko har ta danyi kara sai ta ga ya saka a bakinsa.

Kunya irin wadda bazata misaltu ba ta kamata tayi kasa da kanta jin yadda ya mata a yatsun. Rungumeta yayi yana jin harbawar zuciyarta da gudu. Sun dauki lokaci a haka sannan ya cire yatsun daga bakinsa ya dago kanta suka hada ido tayi saurin rufe nata.
“Ga maganin nan, idan kinji ciwon ya dawo kizo na sake baki”

Yana kallon bakinta ta dan turo shi ido a rufe tace “shiyasa nace maka naga boni don Allah ka barni na tafi kada a nemeni”

“Zaki ganshi dai amma ba yau ba. Kuma babu me nemanki duk ‘yan rakiyar nan wurina suka kawoki”

Bakinta yayi ta bi da ido sai kuma ya dauke kansa shi kadai yana ayyana abubuwa.
“Ga kaya can ki gwada na gobe ne”

Ido daya ta fara budewa don bata son hada ido dashi. Ganin ba ita yake kallo ba ta bude dayan tana kallon inda ya nuna. Gaban ledojin taje ta durkusa tana budewa. Kayan sun tsorata ta saboda kyaunsu ta dago rigar tana dariya

“Uncle” tace ya bata rai tayi saurin gyarawa “To Uncle Son So kayan mene ne?”

Komai na Rumana yana burge shi. Sai ya tuna da Nuru yace masa wannan soyayyar kila hadda hakkin rikonta da ya kasa yi a baya Allah Ya jarabce shi da son ta. Hamdala yayi a zuciyarsa shi kam ya dace .
“Akwai walima gobe da na shirya to welcome you Son So”

Tashi tsaye tayi harda tsalle “da gaske? Kuma wannan kayan zan saka? Unc….Son So nagode. Bari naje na gwada”

Hanyar fita tayi ya janyota ta fado jikinsa suka zube akan wata resting chair doguwa a dakin.
“Not so fast Son So, a nan dakin zaki gwada. Kina so kowa yaga kayan ne kafin gobe?”

Yanayin da suke ne ya sa ta shiga tashin hankali ya fada a kwance tana kansa ga ledojin hannunta sun zagayesu. da taimakonsa ta tashi yace tayi sauri ta gwada tunda kiyastawa kawai yayi girman. Takalmi dai yasan size dinta rigar ce baya son a sami matsala.

Tasan bazai bari ta fita da ita ba sai ta nufi toilet. Tana murda handle din yace yanzu yayi wanka ya jika ko’ina. Jinsa kawai take yi bata yarda ba.

“Ki saka a nan kada ki jika musu idan batayi ba zan mayar ne”

Hawaye ya sake gani ya girgiza kai. Su amare wato kuka baya yi musu wahala. Ango na murna suna kuka. Da taushin murya yace
“Ba kya so na kalleki?”

Bata iya amsawa ba sai gyada kai.

“To bazan kalla ba yi sauri ki gwada”

Wurin wani working table da kujerarsa yaje ya zauna inda ya ajiye laptop da takardu. Da sauri ta cire rigarta tana yi idonta kyam a kansa kada ya juyo ta saka gown din. Laushin rigar kadai ya isheta jindadi bata san sanda ta fara juyi ba kasan rigar yana budewa ta soma dariya da tafi.

Dogon takalmin mai madauri ta saka ta tashi sai ji tayi kamar zata fadi. Anya zata iya tafiya dashi kuwa ta tambayi kanta. sai dai fa komai na kayan ya burgeta sosai ta sake yin juyi taji ta tafi luuu zata fadi.

Awaisu da yake ta kallonta ta screen din laptop dinsa batare da ta sani ba ya taso da sauri ya rikota.

Ajiyar zuciya tayi tana kallon yadda komai yayi mata daidai a jikinta. Shima kallon nata yake yi tun yanzu ba karamin kyau tayi ba.

STORY CONTINUES BELOW
“Kinyi kyau Son So”

Tayi wata dariyar jindadi “thank you”

“Idan takalmin zai baki wahala sai na siyo miki wani da wuri”

“A’a don Allah ina son wannan din. Ina naji zan fadi sai na rike Iman”

“Zaki sa na cewa dreban da ya kawosu ya mayar da ita Fika yanzu. Idan zaki fadi mijinki ne support dinki kinji ko”

“Naji Uncle Son So…nagode”

******
Washegari da wuri suka sake tashi aka karasa duk wani gyara da za’ayiwa dakin Rumana da kitchen. Hatta kayan sawarta wanda suke cikin akwatuna uku manya manya da Harisu yayi mata duk an jere a drawer Anti Baraka ta kwashe mukullan.
Rumana da Iman da sauran ‘yan uwansu daki daya suka kwana cikin na baki. Yayyenta mata biyu suma duka tare suke sai Zee da take ta jiran ganin ma’aikatan gidan maza don ta mika kokon bararta. Ita dai ta sami mai aiki a Abuja kowane iri ne yadda a Fika ana cewa a ina take aure za’a ce a Abuja. Nacin da ta kafa musu yasa Mama da kanta tace a taho da ita.

Tun karfe biyar Hajiya Fattu ta iso gidan. Dakin Maamu aka kaita ta gaishe da Baaba sannan ta nemi ganin amarya.

Rumana na shigowa Fattu ta tashi ta tarbota tana kare mata kallo  ” _perfect_, gaskiya angonki ya iya zabe. Yanzu wanka zaki fara yi kafin mu soma kwalliya”

Baaba ta dafe kirji tana kallon fuskar Fattu da irin kayan jikinta. Sarka har ciki ga su awarwaro ko yaya ta motsa sai kaji kachauu.

“Kece mai mata kwalliyar?” Baaba ta tambaya.

Hajiya Fattu ta wani murmushin burgewa “angonta ma bazai ganeta ba idan na gama”

Baaba tace “kwarai kuwa, Allah Yasa kada yayi tunanin gamo yayi. Bari na baku wuri….Rumana sai ince yau kinga boni da kike yawan kira ra’ayil aini”

Sai da kowa ya fita Fattu ta bata wani mulmulen abu a leda ashe sabulu ne tace tayi wanka dashi.

Rumana ta shiga tana saka masa ruwa kamshinsa mai matukar dadi ya gauraye bandakin. Ta jima a ciki tana wanka sannan ta dauro alwala ta fito.

Man da zata shafa ma ita ta bata. Nasa kamshin ya ninka na sabulun. Dadi ya kamata  ta saki jikinta da Fattu. Wasu turaruka masu maiko ta sake bata ita dai komai akace tayi tana yi. Jikinta tuni ya koma wani sulbi da kamshi sannan Hajiya Fattu ta soma nata aikin.

Zee aka bari gadin kofa sai da aka kira magariba Iman ta chanjeta lokacin sun gama shiryawa itama taje ta shirya. Anti Baraka ce tace kowa ya fita Awaisu yace a kaisu wurin taron.
Ya gama nasa shirin cikin wata suit mai bala’in kyau coffee brown sai shirt din light brown da tie shima coffee mai farin stripes Sai takalmi da agogo duka kalar shirt din. Kallon kansa yayi a madubi yayi dariya wai bikinsa ne da Rumana.
Da ya fito ko’ina tsit duk an tafi dama yace kada su jira zai taho da Rumana.
Gimbi ya gani ta fito tana leka falo saboda shirun da taji. Ganin yadda yayi mata kyau sosai yasa ta tsaya kallonsa tana tuhumar kanta me tayi ya rabata da masoyinta.

“Dama yanzu zan fada miki zamu je wurin walima kada kiji gidan shiru”

Harararsa tayi “sai yanzu zaka fada min?”

“Kinga laifina? Naji tsoron sanar dake da wuri kada ki kira bokayenki ku shiga ku fita taron yaki dadi. Sai mun dawo.”

Wuce ta yayi sai dai a ransa yana jin wani iri. Tausayi Gimbi take bashi ba na komai ba kuwa sai na yadda taki saduda ta dawo daga rakiyar shaidan…idan mutuwa ta risketa a wannan yanayin shikenan tazo duniya a banza. Mata da yawa suna aikata shirka da sunan soyayya amma idan zasu duba zukatansu sosai sun san cewa son zuciya ne kawai yake dibarsu.

STORY CONTINUES BELOW
Kofar dakin Maamu aka bude Hajiya fattu ta fito tana masa dariya “ango na cika aikina. Yadda yarinyar nan ta shiga raina na yafe kudin”

Gabansa ne ya dan fadi ganin irin nata adon ya fara nadamar daukota. Matsawa tayi gefe Rumana ta tako a hankali yana binta da ido har ta iso gabansa ta tsaya. Ganin ya kasa motsi bare magana sai tasa tattausan hannunta ta riko shi harda lankwashe yatsun cikin nasa.

Magana take yi a nutse tana lumshe ido “Uncle Son So”

Tun daga kanta har kafa yake kallo “na’am Son So”

Fari tayi da ido “nayi kyau?”

“Mun fasa zuwa wurin muje dakina na sake ganin kwalliyar sai na fada miki  ko kinyi kyau”

Juyawa tayi wurin da Fattu take sai dai tuni tayi falo ganin yadda Awaisu ya rude da yaga Rumana. Ita kuwa ta kyabe fuska “Hajiya Fattun nan ce fa tace inyi maka haka idan mun fito zaka ji dadi. Daurewa nayi sosai kuma gashi ta janyo kace an fasa zuwa”

Hannuwansa yasa a kugunta yana sake kallonta. Wani irin rolling Fattu tayi mata bayan ta daura mata wani dankwalin ta ciki kalar rigar saboda kada maikon gashinta ya bata mayafin. Fuskarta sai ta fito sosai. Ga wani kamshi yana fizgarsa ko ta ina. Ba don ana jiransu ba sai ya bata kwalliyar nan a sake wata.1

Da kyar ya saita kansa suka fito falo yayiwa Fattu godiya yace kuma idan babu damuwa gaskiya zai turo mata Rumana ta koya mata kwalliya. Dariya tayi tace tana jira sai sun zo.

Kusan tare suka shiga mota ta fara fita suka bi bayanta. Awaisu tuki yake kawai hankalinsa yana kan Rumana. Ita kuma kunyarsa saboda kallon da yake yi mata yasa ta kasa sakewa.

Motoci suka gani a wajen da yawa har yana tunanin anya duka masu amsa gayyatarsu ne kuwa? Wani matashi ne yayi saurin komawa ciki ya sanar da isowar amarya da ango.

Wata waka suka ji tana tasowa daga ciki ana ambaton sunayensu ana wasa amarya Rumana da angonta Awaisu. Kafafunta taji sun soma rawa kamar bazasu dauketa ba Awaisu ya rike mata hannu a hankali yace “yau taki ce Son So kada kiji tsoro ranar farinciki ce”

Sake damke hannunsa yaji tayi suka soma tafiya a hankali Mudan Dan Arewa yana wakesu don gabansu ya dawo yana wakar suna tafiya har suka je mazauninsu suka zauna aka hau tafi.

Maman Gimbi bata je ba amma ita da alhaji Mudi sun fadawa yaran babansu ya auri Rumana yanzu itama mamansu ce. Nasiha tayi musu yadda kwakwalwarsu zata dauka banda rashin kunya ko raini tsakaninsu sannan ta saka musu kayan da Awaisun ya kai yace su yake so su saka yau. A wurin su Baaba suka zauna sai da suka ga zaman su Awaisu suka tashi duka su hudun suka tafi wurinsu.

Mazan na jikin babansu Daula ta rungume Rumana tana cewa tayi kyau akayi musu hoto a haka.

Shuhada ma tazo kwanansu biyu da dawowa daga Singapore. Har wurinsu taje suka yi hoto tace da Rumana sai ta kawo mata ziyara gida. Yadda taga Awaisu bai iya boye soyayyarsa ga Rumana ya tuna mata da T dinta ta sake dankawara Anti Bebi Allah Ya isa.

Taro yayi kyau sosai anci an sha kowa ya tafi cikin farinciki.

Duk da ba’a tashi daga taron da wuri ba amma washegari kafin shabiyu mutan Fika sun kama hanya bayan doguwar nasihar da aka sake yiwa Rumana. Kuka take yi sosai idanunta sunyi ja kamar an zuba barkono. Sai da motar karshe ta tashi ta koma ciki ta bar Awaisu da maigadi suna magana.

Hanyar dakinta da ta fara shiga yau da safe Baaba tayi mata fada shi ta nufa. Tana tafiya taji an damko wuyan rigarta an shake. Da sauri tayo baya ta juyo Gimbi ta gani gabanta ya fadi.
“Yau na tabbatar danginku kwadayayyu ne sannan kuruciya tana cinki shiyasa kika amince kika dawo gidan nan. Tun motarsu batayi nisa ba kice su dawo su daukeki kafin jikinki ya gaya miki. Abban Haris bazai taba zama dake ba. Yarinya baki fi cikin cokali ba na tsaya ina magana dake saboda wulakanci. Ki bani numbar uwarki da bata san ciwon haihuwarki ba inyi da ita”

Rumana taji haushi kamar tayi kuka ta daure ta tattaro duk wata dakiya da take da ita ta yiwa Gimbi wani kallo shekeke
“Anti kenan ni din dai cikin cokalin da na sace zuciyar Son So nice daidai dake.”

Zuciyarta har tsalle take yi kada Gimbi ta kai mata duka tayi saurin fara tafiya sai kuma ta tsaya “Anti dama ina son muyi maganar rabon kwana. Idan Son So dina ya kiramu nasihar kishiyoyi ni dai kwana uku-uku zan ce ina so saboda gaskiya biyun nan da aka saba yayi min kadan. Ukun ma dai maneji zanyi kada na shiga hakkinki.” Kafin ta amsa da sassarfa ta bar wurin kada ta saki fitsarin da ya kamata na tsoro.
Tamkar an kafe Gimbi da guduma haka taji. Wai ita Rumana take yiwa zancen rabon kwana. Tashin hankali da ba’a saka masa rana. Gumi ne ya rinka tsatstsafo mata ta rasa me zata yiwa yarinyar nan ta huce.

Tafi taji daga bayanta ta juya taga Awaisu yana dariya. Ashe duk abin da sukayi akan idonsa ne. Shi ya taho da sauri ya rarrashi Rumana ne ya samesu a wannan yanayin.

A harzuke tace “Ka jawa yarinyar nan kunne wallahi bazan dauki raini ba.”

“Tsuntsun da yaja ruwa..”ya fada ya yana wuceta.

Tsoro ne ya kamata kada zuciyarta ta fashe saboda bakin ciki sai ta koma dakinta kawai.

Rumana najin an murda kofar dakinta hantar cikinta ta kada tsoro ya cikata tana tunanin Gimbi ce. Ganin Awaisu ta tashi da gudu taje ta rungume shi tana ajiyar zuciya.

“Yaya akayi Son So?”

Har lokacin jikinta na bari tana jin kamar Gimbi zata zo ta sameta  nan “Uncle kasan me nayi kuwa? Taba zuciyata kaji ina jin jinina ne ya hau”

Dariya sosai ta bawa Awaisu yana rungume da ita ya dagata yana tafiya hanyar gadonta “ba rabon kwana kike so ayi ba Son So, nima kwana biyun gaskiya sunyi min kadan”

Kokarin sauka daga hannunsa tayi jin abinda yace. Wannan karon banda tsoro harda kunya. Jikinta sanyi kalau lokacin da ya kwantar da ita akan gadon.
“kaji abinda nace?”

Yayi murmushi yana zama a kusa da ita.

Tashi tayi zaune “to wallahi wasa nake yi kuma…kuma ma…kuma ni ban san meye rrrabbbon kwanan ba”

Janyota yayi tana ta zillewa “ki nutsu ma’anar rabon kwanan zan fada miki”Faduwar gaban Rumana ta tsananta ganin yadda Uncle Awaisu ya riketa ga abinda bata taba tsammanin faruwarsa ba wato hada wurin kwanciya dashi. Shiyasa gabadaya ta rikice har take ganin gara ace a gaban Gimbi take a tsaye tana jiran ta kai mata duka da wannan katuwar kunyar da ta lullubeta.+

Idanunta ta runtse sosai tana fitar da numfashi da sauri shi kuwa ya danneta da rabin jikinsa saboda ta dena kokarin tashi yana kallon fuskarta. Murmushi yayi ya ja hancinta da yatsu biyu

“Wai waye ya firgita min amarya ne na kula tun safe yau wani tsorona ma kike ji”

Shiru tayi kirjinta yana dukan uku uku saboda numfashinsa da take ji ya kara yin kusa da fuskarta.

“Kinga ni kawo kunnenki yadda na fada miki wacece kwaila zan fada miki meye rabon kwanan da kike so ayi kwana uku na maneji”

Jin yayi saitin kunnenta ta dago hannu a tsorace ta dora akan bakinsa saboda ko kadan bata shirya jin me zai fada ba. Har yanzu bata manta kunyar da ya bata ba da ya fassara mata kwaila a Fika.

Cikin sarkewar harshe tace “na tuna ashe ma na sani ba sai ka fada ba”

Lumshe ido yayi yana shakar kamshin tafin hannunta mai laushi akan bakinsa ta kula da yadda yake yi ta zame hannunta a hankali zata tashi ya kara sakin jiki ta danyi kara cikin sanyin murya  mai dadi tace.

“Wayyo Son So zan karye fa”

Har kasan zuciyarsa maganar ta shige shi ya rinka jin sonta yana kara fizgarsa ya rungumeta sosai a jikinsa yana mamakin wannan so da yake mata.

Ita kuwa kara tsorata tayi ta rasa yadda zatayi tasa ya tashi kawai sai tace masa tana jin yunwa. Tashi yayi zaune ya dagota a jikinsa.

“Me kike son ci?”

“Su Anti sun ce akwai komai na girki a fridge da store bari naje na dafa mana” tana magana tana sauke kafafunta daga kan gadon.

Wata irin janyowa Awaisu yayi mata ta fado cinyarsa ya kalleta fuskarsa kamar zaiyi mata kuka yace “ki rufa min asiri Son So har yau bakina bai manta yajin nan da kika gasa shi dashi ba”

Dariya sosai Rumana ta rinka yi harda rike ciki shi kuwa yana binta da kallo cike da jindadi.

Idonta harda hawaye don mugunta ta dan  bata rai “kowace amarya mijinta yana son cin abincinta amma ni tsoron nawa ma kake yi. Nasan ma cewa zakayi ban iya girki ba”

Hawayen dariyarta da ta mayar kamar tana kuka ya hargitsa masa lissafi ita kuwa tana ta dariya a ranta.

“Waye yace miki amare suna girki? Daga gidan su miji ake kawo fa. Tunda mu munyi nisa na yarda zan siyo miki har ki gama kwana bakwai dinki a fara rabon kwana” ya kashe mata ido yana murmushi.

Sake bata rai tayi bakin nan ta turo shi gaba tana wasa da yatsun hannunta kamar da gaske bata ji dadi ba “Iman jiya ta koya min wani girki tace yana dadi aci as breakfast. Ko yi banyi ba kana cewa zaka siyo bayan na iya”

Ajiyar zuciya yayi shi dai gaskiya baya marmarin sake cin abincin Rumana nan kusa sai ya tabbatar da iyawarta.

“Fada min naji irin abin da ta koya miki din sai na rakaki kitchen din ma muyi tare”

“Yeeeyyhh” ta tashi daga cinyarsa dama a dofane take ta danyi tsalle tana dariya.

“Sunansa Indomie mai romon dadi”

Awaisu ya koma yayi kwanciyarsa yana tunanin sawa ta hakura don dole. Ko ta iya girki yafi son su yini tare ba wai ta tafi kitchen ta barshi ba.

“Kiyi hakuri Son So ni ba mai son Indomie bane dama.”

“Wannan fa mai dadi ce…nama ake yankawa kanana sosai amma da yawa sai yayi laushi a jajjaga attaruhu da albasa…… “

STORY CONTINUES BELOW

Zama yayi ba shiri jin ta ambaci attaruhu “ina jinki Iman din nan da gani ta koyi mugunta a zaman boarding da tayi. To kuma attaruhun nawa ake sawa? “

Ba karamin dakewa tayi kada ta fashe da dariya ba saboda yadda yayi da fuska.

Da yatsun hannunta take masa lissafi “tace idan guda daya ce karama attaruhu biyu da rabi sai rabin albasa. Idan biyu ce kuma attaruhu biyar cif da albasa madaidaiciya daya. Soyawa ake fara yi sai a hada a ruwan naman a saka indomie din. Amma tace idan superpack ce guda hudu ake sawa a daya”

Daga labarin kawai yaji kamar dakin ya fara daukar zafin yaji ya taso gabanta ya tsaya. Kasa cigaba tayi saboda yadda yayi mata kwarjini sai ta ganta ta koma yar karama a gabansa. Kafadunta ya dafa tare da daidaita fuskarta da tasa

“Zanyi komai domin faranta miki Son So amma wannan romon azabar ba dani ba…naga alama a gadon asibiti kike so muyi amarcin nan”

Tun kafin ya daga kansa Rumana ta soma dariya harda kyakyatawa. Sosai taji dadin yadda ta ruda Uncle Awaisu ya mika hannu zai kamata ta zille ta haye gado. Ganowa yayi tsara shi kawai tayi don tsokana ya rinka binta yana cewa zaiyi maganinta tunda ya zama abin tsokana. Da kyar ya damkota suka fada kan gadon tuni idanunta suka raina fata da yace mata ya tuna yana da maganin yaji. Bai sake bari tayi magana ba ya hade bakinsu wuri daya yana jin yadda zuciyarta ke tsananin bugu. Don kansa ya kyaleta yana son su hada ido taki.

“Ashe ma duk cika baki ne tsokanar taki. Nafi so idan kinyi tsokana ki shiryawa abin da zai biyo baya. Muje kitchen din nima ina jin yunwa idan mun dawo zaki fada min me da me aka fada miki da yasa kike tsorona haka har nake jin bugun zuciyarki yana neman fin karfin kwailan kirjin nan naki”

Da muryar shagwaba tace “Ni dai ba kwaila bace”

“Mu gani” ya fada yana dago hannu ta tashi a guje ta fita.

Dariya yayi yabi bayanta sai dai dakin Gimbi ya fara wucewa.

*****

Waya take yi yana tura kofar tayi saurin katse kiran. Tabe baki yayi yana girgiza kai. Tunda Rumana ta tare lafiya lokacin da zai mayar da yakinsa kan Gimbi yayi. Shi kadai yasan me yake kudurawa a ransa game da ita.

Kallon banza tayi masa ta watsar duk kuwa da yadda zuciyarta take tsallen murnar ganin sa da jin kamshin turarensa mai sanyaya mata rai.

“Uhmmmm angon kwaila me ya fito da kai? Nayi zaton ni da sake ganinka sai zaku asibiti nakuda ta kamata. Ko ka fito da ita goye a bayanka”

“Me kike ci na baka na zuba. Muna nan dake wannan da abinda ya fishi duka zaki gani.”

“Ka dai ji kunya auren yarka…woooooo” ta rinka masa ihu.

“Ke kinfi kowa sanin Rumana *halal dina* ce. Anyway nazo fada miki ne gas cooker dinki da wasu cikin kayan girkinki suna nan a gefe daya a kitchen. Kina da damar daukar duk abinda kike so a store ki dafa amma iya cikinki ke kadai. Ina rokonki tun muna fahimtar juna kada ki kuskura ki taba komai na Rumana”

Wani daci taji a wuyanta na bacin rai. Ita da ta taba yiwa Rumana iyaka da kitchen dinta yau itace akayi mata iyaka dashi.

“Dama maza da dama baku san adalci ba musamman idan kuka dauki budurwa. Kai naka gigin yafi na kowa ma tunda an hadaka da kwaila”

Rike baki yayi tamkar baiji haushin kalmar da ta fada ba “Me? Idan ma Son So kike yiwa kallon kwaila kije a wanke miki ido. Matata duk inda ake bukatar mace ta kai har da kari…ai kin gane me nake nufi” ya daga gira yana mata murmushin mugunta.

Ta kuwa hau ta cika fam ranta ya sake baci. Ta rasa yadda zatayi rayuwarta ta koma daidai. Hawaye taji ya sauko mata ta sharesu a fusace. Ta tsani Awaisu yana ganin hawayenta tamkar ta gaza ne

“Kaga Malam kaje ka dafata ka cinye karewar soyayya amma ka dawo min da ‘ya’yana gabana. *Banda rashin adalci da rashin sanin darajar haihuwa* me zai sa ka rabani dasu”

STORY CONTINUES BELOW

Tafi Awaisu ya rinka yi ya shigo dakin sosai ya dawo gabanta ya tsaya “Gimbi ashe kinsan meye darajar haihuwa? Nayi zaton kinyi nisan da bakya jin kira. To bari  kiji na fada miki ” ya nuna ta da yatsa wanda ya kusa shigar mata ido “ni Awaisu Kabir Fika nasan daraja da kimar da Allah Yayiwa mahaifiya. Shiyasa dana dauke yaran na kaisu gidan iyayenki. Gimbi ko a lahira bana fatan su Haris su taba sanin matar da tafi kowacce mace daraja a rayuwarsu ta taba yin shirka, ta taba taka kafafunta taje gidan boka. Ni shaida ne kina cikin matan da suke matukar wahala wurin haihuwa musamman ta Mu’allim na kuma gode Allah babu haihuwar da kikayi ina nesa. Ciki da rainonsa da haihuwa duka babu wanda bansan yadda kika yishi ba. Wannan darajar ita tasa har yanzu kike amsa sunan matar Awaisu dan Maamu. Ke da na kai naki wurin naki iyayen kike jin haushina ki tuna abinda kika yiwa matar da baki san da yadda ta haifi nata dan ta raineshi ba.”

Idanunsa a lokacin sun kada sosai sunyi ja yana kukan zuci saboda tuna halin da Maamu ta shiga bai sani ba. “Har yau ban ga alamun nadama ko dana sani a tattare dake game da hakkin uwa da danta da kika daukarwa kanki ba. Bana jin zaki taba fahimtar halin da kika jefamu sai kin wayi gari matar daya daga cikin yaranki ta gasa miki wulakanci kwatankwacin yadda kika yiwa Maamuna”

A zafafe tace “Allah Ya kiyaye wallahi wannan mugun fata naka ka gani a kanka”

Lebensa ya dan cije “ai na riga na gani Gimbi tunda na aureki. Ke naki jiyewa dai kinsan duniya tamkar gona take. Abinda ka shuka shi zaka girbe. Mutum bazai shuka dusa yazo ya girbe ciyawa ba….kiyi tunani”

Daga haka ya fita daga dakin yana tuno wasu lokuta da yake ganin Maamu a wulakance amma baya iya magana bare daukar mataki saboda an kawar masa da hankali.

Gimbi kuwa jikinta ne ya hau bari babu gaira babu dalili ta kama kofar dakin ta rufe tana fizgar kanta saboda yadda taji duniyar tayi mata zafi. Ina zata ga Anti Bebi ne?

*****

Rumana tana blending din kayan miya Awaisu ya shigo sai dai babu wannan fara’ar a fuskarsa saboda yadda ransa ya baci. Daga bakin kofa ya tsaya ya harde hannuwansa a kirji. Kallonsa tayi ta kula da yanayinsa wanda ta tabbatar dakin Gimbi da yaje ne ya mayar dashi haka. Tana son tambayarsa me ya same shi ta tuna da nasihar Mama da take cewa kada ta taba saka kanta a tsakiyar matsalarsa da Gimbi. Komai wuya komai dadi uwar ‘ya’yansa ce saboda haka duk abinda ba’a saka da ita ba ta dauke kai sai taji dadin rayuwar gidan miji.

Shiru duka suka yi na yan mintuna har ta juye kayan miyar a tukunya ta dora akan gas cooker dinta. Hantar da ta fitar daga freezer ta dauka zata yanka sai ta sake kallonshi ta dora hannuwa biyu a kanta.

“Nayi mantuwa”

Karasowa yayi cikin kitchen din yana kallon yadda take bata rai.

“Me kika manta? Mu gyara kafin ki hada mana jagwalgwalo”

“Attaruhu goma Iman tace na saka na manta na sa tara yanzu yaya zanyi da dayan?”

Yana kallonta tana gimtse dariya yayi murmushi “Son So kin mayar dani kakanki ko amma nasan maganinki. Shi guda dayan da kika manta na yarda ki tauna ki zuba shi a ciki….bude bakin…haaaa” ya nufota da shi a hannu ba shiri ta fara bashi hakuri tana neman hanyar fita ya tare. Cikin dan lokaci ya ware suna dariya wayarsa ta soma ringing. Nuru ne yake kiransa ya sanar dashi suna hanya da matarsa Kubra zasu zo.

“Baki zamuyi su Nuru da matarsa kin ganesu ko?”

Ta gyada kai tana murmushi.

“Sun kusa isowa kije ki dauko hijab ki ajiye a kusa”

Fita yayi tabi bayansa da kallo tana jin wani irin yanayi mai cike da ni’ima idan tana tare da shi. Bata taba zaton hankalinta zai kwanta da auren nan ba sai gashi tun ba’aje ko’ina ba zuciyarta tana son tabbatar mata da cewa Uncle Awaisu ya cancanci ta kira shi Son So ba don ya dage sai ta kira shi da sunan ba. Kirjinta ta dafe saboda yadda zuciyarta take bugu da karfi. A hankali tace

“Washhh zuciyata….Uncle kada kasa min heart attack”

Juyo da ita taji anyi har ta firgita saboda tasan ita kadai ce a kitchen din. Fuskarta yake kallo yana kokarin kallon idanunta ya soma magana a hankali yana rungume da ita

“Me ya sami zuciyar taki?”

Kasa bashi amsa tayi saboda matsananciyar kunyar da take ji ta soma sunne kai.

“Umm Ruman ki bani amsa please….kin bani wurin da nake son samu a cikinta ne?” Fuskarta kawai yake kallo ya sanya hannunsa a saitin zuciyarta mai bugu da mugun sauri. Hannunta ya kama ya dora a nasa kirjin har lokacin idanunta a rufe amma tana jinsa.

“Idan baki yi min magana ba ni a yanzu heart attack din zai kamani”

Zancen zuci ta kama yi tana yiwa kanta fada yaya akayi tayi magana da karfi har yaji. Suna wannan yanayin sai kaurin kayan miya suka ji ya saketa da sauri taje ta kashe. Zai sake magana suka ji kararrawa tana cewa _assalamu alaikum_.

Sai da yaje bakin kofa ya juyo “Ina binki bashi”

Ya kuma juyawa Rumana tace “Uncle…” ya sake waigowa sai kawai tayi masa wannan alamar ta _I love you_ da hannuwanta hagu da dama. Baki bazai iya kwatanta yadda yaji a zuciyarsa ba wannan lokacin. Yayi taku biyu da nufin dawowa gareta kararrawar gidan ta sake sallama yayi guntun tsaki su Nuru dai basu iya zuwa ba.

Sai da taga ficewarsa hankalinta ya kwanta ta bi bayansa tana dafe da kirji. Dakinta ta wuce ta sako sabon dogon hijab ruwan kasa mai hannu har kasa ta sake komawa kitchen.

******

Da sallama ta shiga falon dauke da tray wanda ta doro musu juice mai sanyi da cake.

Kanta a kasa ta gaishesu don duka kunyarsu take ji musamman Uncle Awaisu. Su Nuru kuwa suna janta da  tsokana ta kasa sakewa.

Awaisu ya kula a takure take yace su shiga dakinta da Kubra. Da saurinta kuwa ta mike suka tafi.

A dakin ma dai a saliharta ta fitowa Kubra. Da yake babba ce kusan sa’ar Gimbi tasan yadda zata bi da Rumana. Da wasa da dariya ta rinka janta har ta sake. Kusan minti ashirin sukayi sannan Nuru ya kira wayarta yace ta fito su tafi. Ledar hannunta ta mikawa Rumana.

“Ga wannan amarya ki tabbatar yau kika fara sha. Yana da kyau sosai in sha Allah zan rinka baki abubuwa masu amfani. Ki daukeni kamar Antinki ko yaya kinji”

Rumana hannu na rawa ta karba tana ji Kubra na cewa ta saka a fridge dinta tunda akwai a dakin. Jikinta a sanyaye suka rakasu har bakin mota tana tsoron me Kubra ta bata. Dama saboda sakon Kubra ta nace sai taje gidan a ranar. Itama saya tayi wurin kawarta Maman Farida shine ta kawowa Rumana don tausayinta take ji. Yarinya karama girma ya hauta.

Awaisu na rike da hannun Rumana ya kira drebansa ya bashi kudi ya siyo musu abinci. Suna gama cin abincin wanda ya siyo har Gimbi aka kira shi ba don yaso ba ya fice bai dawo ba sai da akayi Isha.

*****

Kafin lokacin Rumana ta sake fitowa dora abinci ta ga Gimbi ta dasa kujera a kitchen din ta zauna. Ko bari ta ganta bata yi ba ta lallaba ta koma dakinta. Duk abinta tana tsoron duka wanda ta tabbatar idan Gimbi ta damketa to kashinta ya bushe.

Awaisu kamar ya sani ya dawo gidan da abinci. Dakin Rumana ya ganta a kwance yayi mata murmushi.

“Sorry na barki ke kadai uzuri ne ya taso min”

Tashi tayi tana masa sannu da zuwa yace ta kashe komai na dakin ta taho dakinsa. Kafin ta iya amsawa yayi gaba. Wani guntun zazzabo ne taji yana barazanar kamata. Ina ita ina zuwa dakinsa a daren nan. Ita fa tunda gari ya fara duhu tsoro ya sami gurbin zama a zuciyarta.

Kamar dazu da rana abinci ya mikawa Gimbi saboda baya son ko kadan ya shiga sahun masu tauye hakki sannan ya wuce yayi wanka. Ya kusa rabin awa babu Rumana babu dalilinta. Katan din su viju da juice da ya siyo  mata ya dauko daga mota ya shiga dakin dasu. Tana takure akan gado jin ya taba kofar ta tashi a guje zata shige toilet harda bigewa da gefen gado ta saki kara amma duk da haka bata tsaya ba. Kansa kawai ya girgiza ya bude karamin fridge din ya fara jera mata lemukan. Dama saboda zuwa makaranta ne ya siyo mata. Karamar jarka ya gani da wani abu kamar zuma ya dauko ya kare masa kallo sannan ya fice ya tafi nasa dakin dashi. Ita kuwa wanka tayi saboda zaman bandakin ya isheta. A hankali ta leko ganin baya nan ta fito ta shirya cikin kayan baccinta ta haye gado ta kwanta tana fargaba kada ya dawo. Da Awaisu ya gaji da jiranta ya dawo dakin sai ya ganta tana bacci. TV din da ta bari a kunne ya kashe ya koma dakinsa yaci abinci yana tunanin Rumana da ta kwanta bata ci komai ba. Shima da kyar ya iya bacci yana ta tunanin maganganun da sukayi da ita a kitchen yana murmushi. Maganar Malamin da yaje ya gani ne ta fado masa tunaninsa ya karkata kan Gimbi har bacci ya dauke shi.Ana kiran assalatu ya farka yayi alwala sannan yaje dakin Rumana ya tasheta. A firgice ta tashi duk a tunaninta bata dade da kwanciya ba

“Uncle yanzu zan taho”+

Gefen fuskarta ya shafa yana kallonta cike da so “kin yiwa kanki, kwana bakwai din da aka baki kin cinye uku a gudun miji. Ki tashi kiyi alwala asuba tayi”

Maganarsa ta farko tasa ta jin kunya amma jin yace asuba tayi ya sanya jikinta yin sanyi. Tsoro take kada ya fara ganin kamar tana masa gardama ne. Fita yayi gidan da yake jikin nasa akwai masallaci nan suke sallah dayawa mazan unguwar.

Da ya dawo dakinta ya sake komawa ya sameta akan abin sallah. Tana ganinsa ta gaisheshi ya mika mata hannu ta tashi tsaye. Gani tayi kawai ya rungumeta yana shafa kanta dake kwance a kirjinsa

“Jiya kin barni ina ta tunaninki da kyar nayi bacci. Naso in fada miki yau zaki fara zuwa sch na tarar kinyi bacci”

Kanta ta kara turawa jikinsa a hankali tace “kayi hakuri”

“Its ok gobe sai kije. Ni zani office muje ki tayani shiryawa”

Hannunta yaja ta bishi cikinta har wani kadawa yake yi. Ta tayashi shiryawa fa yace. Ita kam yau taga boni ta fada a zuciyarta.

Suna shiga yace ta dauko masa tawul a toilet ta wuce ta dauko yana binta da kallo. Da zata bashi hannunta har rawa yake yi ta rufe idonta ta mika masa saboda tana fitowa ta ga yana cire jallabiyar. Hannunta ya riko da tawul din “muje ki tayani kada na makara”

Ai tuni da bude idanun a rikice “Wa? Ni din?? Don Allah Kayi hakuri”1

Wuceta yayi yana cewa “lokaci ne dai nima zanyi miki yangar nan” ya shige bayan ya fada mata ta ciro masa kayan da zai saka.

A iya saninta suit yake sawa idan zaije aiki. Bude wardrobe dinsa tayi ta gansu kala kala an jeresu makale a hanger. Guda daya ta dauko dark green tayi sa’a kowanne akwai matching shirt da tie shiyasa bata bata lokacin nema ba. Turaruka ta samu a kan dressing mirror ta fesa wannan ta fesa wancan a jiki. Jin motsin kofa yasa ta koma bakin gado ta zauna tare da rufe ido harda janyo hular kanta ta sake rufewa.

“Allah idan baki bude idonki ba zamuyi fada. Don ma kinyi sa’a ina sauri bance muyi wankan tare ba”

Wani yawu ta hadiya ta bude idon amma ta kasa daga kai. Da sauri sauri taga yana shiri kanta a kasa ita dai har ya gama. Kayan da ta dauko ya saka ta dan dago kai tana juya hannuwa

“Uncle…uhmm Son So me zan dafa maka kaci kafin ka fita?”

“Kada ki damu ina da uzuri ne da sassafen nan zan sha tea a office idan na nutsu. Ke dai ki tabbatar kin sami abinci kinci zan turo miki na rana sai na taho da dinner idan na taso. I may be late amma kiyi hakuri zan kira ki. “

Kai ta gyada ya nuna mata kumatunsa ta dan daga gira alamar rashin ganewa yace “goodbye kiss”

Gani yayi zata kuma sunkuyar da kanta yayi saurin dago habarta “please Son So i need it, kuma kinsan sauri nake yi dai”

Rufe ido tayi yace yaga alama makauniyar Awaisu zai koma kiranta. A hankali ta matso harda dagenta sai dai lips dinta na karasowa ya juyo da fuskarsa sosai tayi masa a baki maimakon kumatu. Kunya sosai taji shi kuwa ya rinka dariya ya rike kugunta suka fita tana dauke da briefcase dinsa. Daga falo yace ta koma baya so ta fito a haka. Daga masa hannu ta tsaya yi har ya fice sannan ta koma dakinsa ta hau gyara.

*****

Yana shiga mota yace da Gambo drebansa su wuce police station na zone 4. Da zuwa ba bata lokaci bayan ya gabatar da kansa aka kaishi wurin D.P.O. Bayan sun gaisa yace da Awaisu dalilin wayar da yayi masa jiya sun ga mota wadda ta dace da kwatancen motar matarsa da yace an dauke.

STORY CONTINUES BELOW

Waje suka fita kafin ma a bude motar ya tabbatar ta Gimbi ce. Ciki suka koma a gabansa aka kira mutumin da ya saya shi kuma ya sake jaddada musu ba sata yayi ba da kudinsa ya saya. Nan dai aka nemi ya fadi a inda ya saya ya basu kwatancen gidan Ovi.

DPO ya tabbatarwa Awaisu zasu je kamasu idan sun kawosu station za’a neme shi. Jikinsa a sabule ya fita yana fatan Allah Yasa Gimbi ba da kanta ta bada motar ba saboda ta sami kudin zuwa wurin boka. Haka ya wuni ranar baya jindadin aikin ga tunanin Rumana da ya addabe shi. Wuraren la’asar bayan Gambo ya dawo daga kaiwa Rumana abinci mutumin da Awaisu ya tura neman Anti Bebi ya kira yace bai sameta ba a Niger din da akace musu ta tafi. Inda aka kwatanta masa yaje wurin wani tsohon malamin tsibbu ne amma ance ta dawo Nigeria kwana biyu da suka wuce. Godiya yayiwa mutumin ya aje wayar.

Nemanta yake yi dama saboda ya hadata da Gimbi ya kaisu gaban malamin da Nuru ya rakashi wurinsa. Mutumin babban limami ne a garin Abuja wanda ya tabatarwa da Awaisu idan suna son rayuwarsu ta tafi cikin kwanciyar hankali batare da fargabar wani sihiri ko cutarwa daga Gimbi ba sai ya kaita anyi mata nasiha da wa’azi da dukkan wani abu da za’a iya yi domin tsoratar da ita laifinta da azaba da kuma kwadayin rahamar Allah. Sosai ya gamsu da bayanin malamin saboda ko ba komai Gimbi uwar ‘ya’yansa ce. Baya fata wannan halin nata yayi naso ya taba masa zuri’a.

Shida da rabi ya isa gida ana gab da kiran magariba. Alwala kawai yayi ya fita.

Kafin ya dawo Rumana tayi sallah ta fito falo jiransa. Kwalliya tayi kamar yadda Fattu ta koya mata tana sanye da riga da skirt na material ta rike dankwalin a hannu saboda yaki daurowa.

Gimbi ce ta fito ta watsa mata mugun kallo Rumana ta dauke kai.

“Wato kinyi aure kin girma shiyasa bazaki iya gaisheni ba ko”

Kamar tayi shiru sai dai tace mata ina wuni.

Kwalliyar da tayi da komai nata suka tsayawa Gimbi a rai. Duk wannan wai mijinta Awaisu Rumana tayiwa ya gani yaji dadi.

“Rumana ki taimaki kanki ki bar gidan nan tun ban lahanta ki ba. Ki bar ganin na kyaleki har kinkai wannan lokacin. Duk ranar da na waiwayeki banajin za’a sake samun mamora a tare dake. Banza ‘yar gidan masu zuciyar kare makwadaita”

Rumana taji zafin maganar sosai ta tashi ta kalli Gimbi “karo na karshe da zaki sake zagar min iyaye kenan na kyaleki.”

Gimbi ta hayyako mata a fusace “nice kike kyalewa? Lallai Rumana bakya kaunar kanki shiyasa bakinki ya bude saboda kina ganin mun zama sa’anni mijinmu daya amma zanyi maganinki ina zuwa….”

Ciki ta koma ashe kitchen ta shiga. Rumana tana tsaye zuciyarta na radadin zagin da akayiwa iyayenta sai ji tayi an kwara mata wani abu da bata gane ko meye ba da farko. Jikinta ne ya hau bari ganin danyen manja yana binta tun daga kanta har kafa. A daidai lokacin Awaisu ya shigo idanunsa suka gane masa Gimbi da galan din manja ga Rumana a tsaye ta gama baci.

Ya harzuka karshe ya karaso gabansu sai dai ko kala bai cewa Gimbi ba zuciyarsa kawai ke masa zafi.

“Son So tsaya a nan ina zuwa”

Dakinsa ya tafi sai gashi ya dawo da roll din tissue har uku. Ya wuce kitchen ya dauko leda sannan ya tattare hannun rigarsa ya fara goge mata jiki yana rage manjan. Kuka take son yi amma ya makale jikinta ne kawai yake rawa. A zuciyarta tace dama me take tsammani daga Gimbi. Sai da ya karar da tissue biyu da kusan rabi yana goge mata jiki da wurin da take tsaye sannan ya dauketa har lokacin tamkar babu Gimbi a wurin suka shige dakinsa. Bai sauketa a ko’ina ba sai cikin baho ya tara ruwan zafi a bokita yace mata yana zuwa.

Kofar dakin ya sakawa mukulli ya rufe sannan ya cire rigarsa daga shi sai dogon wando da ya nade zuwa gwiwa ya koma bandakin.

******

Wata irin kururuwa Gimbi tayi ta saka kuka mai cin rai. Ji take kamar son Awaisu zai kasheta. Wannan wulakancin da tayiwa Rumana tayi ne kawai don ya kulata ko fada ne yayi mata taji dadin muryarsa. Wannan wace irin masifa ce take masa so fiye da wanda take yi masa a da. Kuka take sosai tana rike kirjinta da yake zafi sosai.

STORY CONTINUES BELOW

Daki ta koma ta shiga laluben numbar Ovi. Tayi sa’a ‘yan sandan da suka je kamasu basu samesu a gida ba suna kasuwa taje sayar da sarkar gwal din da Gimbi ta kaiwa boka. Suna gudun tusar nan ta dafeta ko bokan bai sani ba. Kuka Gimbi takeyi kamar ranta zai fita.

“Ovi kece gatana ki taimaka ki fada min yaya zanyi da rayuwata. Kullum son Awaisu tamkar ana hura wuta nake jinsa ga wannan tsinanniyar yarinyar ya fifita ta akan komai”

Ovi taja gajeren tsaki ita fa Gimbi ta isheta ta hanata sukuni. Karya kawai ta sharowa Gimbi da sawa ranta zata jefar da sim card dinta ta sake wani. Idan sun sayar da sarkar gida zasu sake gabadaya ta nemesu ta rasa

“Boka yace matar nan da akayiwa aiki na karshe itace nata aljanun suka hana komai yiwuwa. Yana tsammani itama boka gareta mai karfin gaske”

Gimbi tayi shiru tana tunani. Tabbas biri yayi kama da mutum. Lokaci lokaci sai taji ana ja mata gashi ko ta kwanta a makureta akan gado. Abubuwan dake faruwa da ita sun wuce hankali ashe itama likitan ‘yar hannu ce shine ta tona mata asiri a asibiti? Murmushi tayi ta ajiye wayar. Abinda tasan inda zata sami Dr. Yana. Komai zaizo mata da sauki. Iyaka dai ta bata hakuri akan ramuwar da tayi na bata mata aiki da Yana tayi duk da bata san me aka raba Yana din dashi ba.

*****

Inda ya barta a tsaye haka ya dawo ya sameta. Tausayinta fal a zuciyarsa ya fara kokarin cire mata kayan da suka gama baci da manja ta rike masa hannu. Fuskarta ya kalla idanunta suna kyallin hawayen da yake barazanar sauka a kowane lokaci.

Kai ta ga ya girgiza mata “Umm Ruman kada kiyi min gardama kuma kada kiyi kuka kinji ko. Raina a bace yake fiye da yadda kike zato. Kokari nake na danne fushina saboda bayyana shi bashi da wani alkhairi. Biyayya da hakurinki shine zai bani strength din cigaba da daurewa”

Jikinta ne yayi sanyi sai ta koma tausayinsa ba ita da Gimbi tayiwa aika-aika ba. Duk da yanayi da suka tsinci kansu na tsantsar bacin ran da Gimbi ta kunsa musu bai hanata jin matsananciyar kunya ba. Tun daga kanta Awaisu ya soma wankewa sai da ya kusan karar da sabulu guda saboda yadda manjan nan ya sami wurin zama a cikin gashinta. Yafi rabin awa yana wanke mata jiki bandakin kansa ya fita hayyacinsa da mai sannan da ya gama yace tayi alwala ta jirashi a dakin.

Kafin tayi alwalar ya fita tana gamawa ya dawo ya rufa mata tawul ya kaita daki sannan ya rufe kansa a toilet  din. Sai a lokacin yaji wani hawaye mai dumi ya sauko masa. Zuciyarsa ta karye sosai daurewa yayi a gaban Rumana. Tuhumar kansa yake yi ta yaya akayi ya kwashi shekaru tare da Gimbi bai san haka zuciyarta take ba. Dubban mata sunyi abinda yafi watsawa kishiya manja saboda kishi, ya tabbatar ita ba kishin bane kawai a ranta. Son zuciyar da tayi ne yake bata masa rai ace maimakon nadama sai kara botsarewa take yi. Ashe kaddara bata fi karfin kowa ba. Duk inda kaji aure ya lalace sau tari ma’auratan suma sunyi zama na soyayya da yarda da juna. Sai wani tsatsayi ya gifta kaddarar rayuwarsu ta bayyana komai ya lalace. Har zuciyarsa yake jin wani irin tsoron Allah Yana kara shigarsa. Babu wayo fa babu dabara, kowanne bawa zai taka yaje inda Allah Ya rubuta masa. Yanzu da shi Allah Ya jarabta da son wani abin duniya har ta kaishi ga shirka don neman biyan bukata shikenan ya bata. Kenan idan kaga bawa a yanayi na sabon Allah ba tozarci bane ya kamata ya shiga tsakaninku. Addu’ar neman shiriya gareshi da nemarwa kanka kariya daga tarkon shaidan ya kamata kayi. Lallai Allah Ya soshi da Maamu bata mutu tana fushi dashi ba. ya tabbata da tuni sunansa ya dade da shiga cikin littafin tababbu wadanda sukayi asarar lokacinsu a duniya.

Abinda ya jima baiyi da kansa ba yayi wato wanke bandakin sannan yayi wanka da alwala ya fito. A zaune ya tarar da Rumana ta takure jikinta wuri daya. Tana ganinsa ta sake matse jikinta yayi mata murmushi

“Son So kwaila”

Baki ta soma turowa “wallahi ni ba…..uhmmm… sai na fadawa Maamu” ta kare tana shura kafa.

Murmushinsa ya fadada “ni kuma zan fada mata yau wanka ma don shagwaba ni kika sa nayi miki”

STORY CONTINUES BELOW

Ai kuwa taji kunya don rufe kanta tayi da bargo ya rinka dariya. Ganinta kawai ya sassauta masa bacin ransa. Tana ta turjewa a haka ya shafa mata mai ya saka mata wata t-shirt dinsa mai girma tazo mata har kusan gwiwa.

Duk tabi ta tsargu da yadda yake kallonta ta koma ta zauna har ya gama shiryawa ya sake fita. Ba jimawa ya dawo da hijab dinta da zani yace tasa suyi sallah yasan an idar a masallaci. Bayan sun idar abincin da ya siyo ya bata suka ci sannan ya koma gaban kujerar dake kallon tv a dakin ya zaune a kasa yace tazo.  Da rarrafe ta iso don bata so ya ganta a tsaye. Fuskarsa ce ta dan sauya babu wannan fara’ar sosai sai alamun tausayi ya kama mata hannuwa ya rike.

“Son So don Allah kiyi hakuri da abinda Gimbi tayi miki. Na rasa kalmar da zanyi amfani da ita na kawar miki bacin ran da kika ji dazu.”

Ko ba’a fada mata ba tasan yaji babu dadi saboda duka yanayinsa ya canja. Ji tayi itama ya kamata ta faranta masa kamar yadda yayi mata. Sai ta mayar da abin wasa. Matsowa tayi gabansa a kunyace “idan ka sake cewa nayi hakuri kukan da na boye zai fito na kwana ina yi”

“To me kike so nayi miki kiji dadi ?”

“Ka goyani”

Gabanta yazo ya durkusa yaji shiru “hau mana”

Baya ta matsa “wasa fa nake yi”

“In durkusa din kice wasa kike yi, bazan yarda ba”

Gani tayi da gaske yake ta dauki zaninta tace masa zata je ta kwanta. Yace daga ranar duk girkinta a dakinsa zata kwana. Da gaske tsoro ne ya kamata ta kama kofar zata fita ya soma magana

“Yanzu har kin fara kin yin abinda nace? To jeki dakin sai da safe.”

Kawar da kansa yayi yana murmushi saboda yadda yaga jikinta yayi sanyi tsoron nata ya koma na gudun bacin ransa. A sanyaye ta dawo ta tsaya daga gefe

“Kayi hakuri bazan kara ba”

Zaune dama yake akan gadon ya nuna mata cinyarsa “zo ki kwanta muyi magana”

Ba musu ta kwanta ta dora kanta a cinyarsa gabanta na faduwa.

“Umm Rumana!”

“Naam”

“Ina so ki saurareni ba a matsayin mijinki ba. Ki dauki maganata daga bakin Uncle Awaisu. Gidan nan ba bakonki bane sannan Gimbi a gabanta kika karasa girma. Kinga yadda lamura suka koma tsakanina da ita duk da irin son da muke yiwa juna. Rayuwar aure is more than mata da miji suna kwana a daki daya ko gado daya. Rayuwa ce ta taimakon juna da rufawa juna asiri komai wuya komai dadi. Ko da wasa ban taba tunanin abubuwan da suke faruwa yanzu zasu ziyarci rayuwarmu ba sai gashi mun wayi gari a wannan yanayin. Shawarata gareki don Allah kada ki taba bari son zuciya ya kaiki ga aikata dana sani. Kina da hankalin sanin mene ne aure saboda haka idan kinga abu ya faru ba yadda kike so ba ni mijinki ne kiyi min magana ta fuskar da ya dace mu fahimci juna. Kada ki kuskura tsoron wani abu da bashi da tabbas ya kaiki ga afkawa haram “

Maganganunsa sun tsaya mata a rai tunda ya fara take kuka. Nasiha sosai ya rinka yi mata saboda ya tsorata da yadda Gimbi ta rufe ido daga gaskiya lokaci guda. Yasan yanzu duk wani wa’azin da zaiyi mata bazata taba sauraronso ba ko don kishin Rumana. Shiyasa ya sami wannan limamin wanda yayi masa alkawarin yana dawowa daga tafiyar da’awa da ta kaishi Lokoja zai fada masa yazo da Gimbin gidansa.

Kukan da Rumana take yi ne yasa ya fara shafa mata kanta wanda yake a jike har lokacin. A hankali rarrashin da yake mata ya juye zuwa soyayya mai wuyar fassara inda wannan rana ta kafa tarihi a rayuwarsu wanda bazasu taba mantawa ba.

*****

“Sleeping beauty asuba tayi”  shine abinda Rumana taji yana fada mata a cikin kunne. Motsin da tayi ne ya tuna mata da wahalar da tasha daren jiya ta sake kudundune jikinta tana hawaye.

Dama sai da ya dawo daga masallaci ya tasheta don ko ba’a fada ba yasan yau kam akwai daru shi da Rumanansa. Dagata zaune yayi yana cewa ta tashi tayi wanka ga ruwan zafi can ya tanadar mata.

Idanu a kumbure saboda tasha kuka bata ma san lokacin da tayi bacci ba ta mike sanye da rigar baccinsa wadda bata san lokacin da ya saka mata ba ta dan saci kallonsa suka hada ido. Murmushi yayi ta maka masa hararar da batayi niya ba a hankali tace ” kuma na dena yi maka Son So”

“Wanda nake miki ya ishemu”

Baki ya rike yana kallo ta shige bandakin tana ta tura masa baki yabi bayanta tayi saurin saka mukulli ta rufe. Yace ta bude zai taimaka mata ne kawai tace ita ya barta zata iya. Dariya yayi yace mata yau zai karbi kowane hukunci amma tayi masa sassauci. Daga haka tashi yayi ya gyara gadon ya zauna jiranta.

Tafi minti ashirin a ciki tana gasa jikinta kamar yadda Anti Umma yayar Mamanta ta fada mata ya kamata tayi. Da ta fito ko kallonsa batayi ba ita a dole tana fushi. Duk irin kukan da tayi masa bai tausaya mata ba bare ya kyaleta.

A zaune tayi sallah tana idarwa taji yana dariya yana cewa aiki ya sami mata. Wani kukan ta soma ya zagaya gabanta ya zauna. Kunnuwansa ya rike yana kallonta

“Tuba nake my sweet Son So bazan kara saki kuka ba. Kin hakura?”

“A’a nima ba nayi ta rokonka ba kaki hakura”

Shiru yayi kamar me tunani yace “to kada ki damu ki dauka kin kawo karar Son So wurin Uncle Awaisu ne zan miki maganinsa. Bulala nawa kike so ayi masa”

Murmushi tayi saboda yadda yake tsokanarta. Wani baccin taji yana neman daukarta tace masa sai ta tashi zata fada masa. Akan abin sallan ta soma gyangyadi ya mayar da ita kan gado ya soma shirin fita. Yaso kwarai ace yau ba ranar aiki bace ya zauna ya kula da ita don niyyarsa sai ta gama jarabawa gabadaya ma zata zama cikakkiyar amarya sai kuma ya kasa. Bayan ya gama shirinsa takarda ya samu yayi rubutu ya ajiye mata a gefen pillow sannan ya fita.

******

Karfe goma ta dan wuce ta tashi jikinta ya danyi sauki ba kamar dazu ba. Ganin rana ta fito ta san ya tafi ko abinci bata bashi ba. Takaici ne ya kamata ta fara neman wayarta zata kira shi tace yau kada ya aiko mata da abinci zata dafa. Takardar da ya ajiye mata ta gani ta dauka tana karantawa tana murmushi son Uncle Awaisu yana kara shigarta. Sake karantawa tayi ta rungume takardar tana dariya ita kadai.

*_I love you so much. Thank you for being mine._*

Tashi tayi ta gyara dakin tas ta fita falo nan ma ta share tayi mopping musamman inda manja nan ya zuba. Dadinta daya ba kafet a wurin da tasan da wuya ya fita gabadaya.

Tana aikin Gimbi ta fito dauke da handbag mai dan girma cikin shiri. Wani mugun bugun zuciya taji ganin Rumana da rigar Awaisu.

Tunawa tayi da nasihar Awaisu da kuma rashin maganar da yayiwa Gimbi wanda ta tabbatar yana da dalilinsa na yin hakan sai kawai ta gaisheta.

Ga mamakinta fuska a sake Gimbi ta amsa sannan tace mata ta tabbatar ta mori zamanta da Awaisu kafin ta dawo daga tafiyar nan da zata yi. Rumana bata fahimci kan zancen ba tace adawo lafiya ta cigaba da aikinta.

Gimbi na fita ta dokawa maigadi harara ya matsa ya bata wuri yana daga mata hannu “a sauka lafiya Hajiya”

Tsaki tayi ta wuce shi ta tsayar da taxi ta tafi tasha. Hankali kwance motar da zata Damaturu ta shiga tana kara rungumar jakarta. Babu komai a ciki sai kaya set biyu, kudin mota da takardun wani fili da Alh Mudi ya saya mata a Kano. Idan bokan Dr. Yana zaiyi mata aiki shine kadarar da zata iya bashi domin biyan bukata. Ita dai Awaisu ya sota ko da zai cika gidan da mata ya dauko duk danginsa na Fika.Kafin azahar Rumana ta gama girki da gyara kitchen. Gidan ne taji yayi mata shiru da yawa  kewar mutan gidansu ta kamata. Wayar Abba ta kira aka rinka zagaye sai da ta gaisa da kusan kowa har tana rokon Maamu akan ta dawo su zauna tare. Ta matsu lahadi tayi Awaisu ya dauko su Daula gidan ya dan farfado. Gashi sun rabu da Yusra kawarta bata da waya lokacin bare ta kirata yanzu.+

Awaisu ne ya kirata bayan ta gama waya da Iman yace zai turo dreba akwai kudi a dakinsa zaa kaita saloon a sake wanke mata kai sai tayi kitso. Godiya tayi masa kafin ya iso ta shirya. Wani hadadden wuri ya kaita duk ta tsargu saboda rashin sabo. Haka dai ta zauna aka gyara mata kan akayi mata kitso mai kyau. Sai laasar Gambo ya mayar da ita gida.

******

Kamar ta karbi motar tayi saurin kaisu Damaturu haka Gimbi ta rinka ji. Abin takaici sai magaribar fari suka isa. Daga tashar kai tsaye asibitin su Dr. Yana ta wuce tayi sa’a tashinta kenan zata tafo gida wata mai aikin shara ta rakata office dinta saboda tayi musu karyar yar uwarta ce ita kuma ta kasa samun wayarta.

Dr. Yana tana kama hannun kofar office din Gimbi ma ta kama suka bude tare. Wata muguwar razana tayi cikinta ya duri ruwa ta koma ciki babu shiri. Gimbi kuwa tayi murmushi tare da shiga ta rufe kofar.

“Wannan karon rayuwata kika zo nema ko me?” Dr Yana ta fada tana dan dakewa.

Gimbi ta zauna ta dora kafa daya kan daya tana karkadawa “ko daya, kawance nake so mu kulla. Nasan komai game dake Doctor saboda haka mu manta da komai domin karuwarmu mu duka”

A tsaye Dr. Yana take don bata san da me Gimbi tazo ba. Addu’a take yi kala kala a zuciyarta na neman tsari.

“Ban fahimci me kike son fada ba”

“Doctor kenan, kina zaton bansan ke kika turo min Gogojiya ba…sunan aljanar da take min aiki kenan idan banyi kuskure ba.”

Dariya tayi ganin Gimbi tazo mata da rainin hankali sai dai kuma tabbas tasan daga ina Gogojiya take.

“Kina zaton kowa ma irinki ne mai nema daga wanin Allah?”

Tebur din Gimbi ta dafa da hannuwanta biyu fuskarta a tamke “kinga kada ki munafurceni don nazo neman taimako wurinki. Idan ma aikin da nasa akayi a kanki ne ya bata miki rai ke kika shiga gonata gashi kinyi sanadin sake rabani da mijina. Yanzu haka Rumana yake aure wannan ‘yar budurwar da sukayi zaman asibitin nan da babarsa”

Sai a lokacin Dr. Yana tayi murmushi tana cewa ikon  Allah yanzu Rumana tayi aure. Ashe hasashenta ya zama gaskiya.

“Idan kin gama murna da bakincikina sai ki saurari me ya kawoni”

“Baki isa na saurareki ba malama. Ni da kikayi sanadin rabani da abinda yafi komai soyuwa a gareni”

Gimbi tayi dariya “munyi draw inji ‘yan ball. Anyi 1-1.”

Ranta ya soma baci tace “kanki daya kuwa? Ki sa nayi barin cikin da na kwashe shekaru ina jiransa sannan kice wai munyi draw?” Hawaye ne ma ya sauko mata.

“Kizo ki fita kafin na kira miki security”

Jikin Gimbi ya danyi sanyi jin cewa bari Dr. Yana tayi ta dan sassauta murya “kiyi hakuri nayi zaton kema rabaki akayi da mijinki kamar yadda akayi min. Yanzu da kika ganni babu wanda yasan na taho. Mutumin da yake min aiki yace Gogojiya tafi karfinsa kuma ta hana ayyukana kama Awaisu. Shine nake so ki kaini wurin naki. Da shirina nazo ko me yake so zan bayar a mallaka min mijina”

Ga mamakin Dr. Yana takardun fili Gimbi ta nuna mata. Tsoro ta bata don tasan lallai tayi nisan da sai anyi da gaske zata ji kira. Wayarta ta dauka ta turawa Mujahid dogon text tana masa bayanin Gimbi. Lokacin yana tare da Haj Fanta. Ganin ya tashi a firgice ta tambayeshi lafiya shine ya fada mata abinda Yana tace. Ta jinjina lamarin sosai tayi murmushi sai tace yaje ya daukosu da kansa a kawota Gimbi. Dan makotansu yasa ya dauko shi a babur tunda Yana da mota taje asibitin yaje ya daukosu.

STORY CONTINUES BELOW

Sai lokacin da suka isa gidan hankalin Gimbi ya kwanta tana ganin hakkanta ya kusa cimma ruwa.

******

Da tunanin halin da ya bar Rumana a gida yake ta sauri ya kammala aikinsa. Ba don shine Manaja a bankin ba ya tabbatar yau da sai dai ya buga waya ya nemi alfarmar bazai je ba. Biyar saura ya fito yana ta sauri Gambo ya taso zai bude masa mota aka kira shi. Ko da ya duba DPO din da yake kula da case din wadanda aka kama da motar Gimbi ne. Ya sanar dashi cewa anyi nasarar cafkesu a hanyar zuwa kasuwa inda suke son ganin mai sayen sarkar Gimbin.

Ba yadda zaiyi dole ya wuce station din bayan ya kira Rumana ya sake bata hakurin jinkirin da zai yi.

Su Ovi ana zaune tsuru sun kasa gane mene ne yake faruwa sai ga mai sayen mota da Awaisu sun shigo. Yana ganin Rita ya gane fuskarta. Shi dama tuntuni ma ya tsaneta bare da ya dawo hayyacinsa ya tabbatar akwai abinda take yiwa Gimbi shiyasa ta barta a gidan.

Kowa cikinsu yayi bayani inda su Ovi su so nuna taurin kai, sai dai bayan jikinsu ya fara fada musu sunci duka suka tabbatar wa ‘yan sandan cewa motar suka sace  Rita harda karawa da cewa akwai sarkarta a jakarsu saboda kada a sake dukanta. Ovi kuwa ta rinka harararta. Da sarkar da motar duka an bawa Awaisu kayansa sannan kudin mota kuma ance su Ovi zasu biya mutumin da ya saya tare da kara masa wasu kudin na tara saboda sun janyo masa zaman cell.

A gajiye sosai Awaisu ya isa gida ga bacin rai sai dai yana ganin Rumana yaji hankalinsa ya kwanta.

A bakin kofa ta tsaya da murnarta tun da taji ana bude gate. Tana ganin ya fito wata kunyarsa ta kamata sai ta tuna ai fushi takeyi dashi shine ta juya ta koma dakinta ta kwanta. Tsoron hada ido take dashi gara tace masa kawai tana fushi don ya kyaleta.

“Son So rigima” taji yace bayan ya ajiye jakarsa yana sassauta daurin necktie.

“Na dawo shine kika kwanta harda juya min baya ko”

“Ban huce bane. Kuma na dena yi maka magana” ta fada har lokacin bayanta yake gani.

“Yau a shirye nake kizo ki rama bazan ce komai ba…amma kafin nan a taimakawa bawan Allah da ruwan wanka na gaji.”

A hankali yake jan maganar ta sake lafewa taki tashi a shagwabe tace “ni ba cewa nayi zan rama ba”

Shima muryarsa kamar zaiyi kuka yana kwaikwayonta yace “ni dai sai kin rama”

Kamar ta shige cikin gadon don kunya sai murmushi kawai take yi. Shi kuwa don ta taso ya tuna jarkar da ya dauka a fridge dinta yayi murmushi zai tsokaneta

“Naga wata jarka a fridge me kike yi da ita?”

A gigice ta tashi jikinta yana rawa. Dama tsoron da taji kenan kada ya gani yace ko itama tana amfani da kayan asiri. Idonta har ya ciko da kwalla har ya soma zubowa

“wallahi Son So matar abokinka ce ta bani kuma ko sha banyi ba. Nima nasan babu kyau”

Daure fuska yayi ya zauna akan gadon

“wato duk abinda na fada miki jiya kin watsar ko. An baki abu baki fada min ba”

Kara tsorata tayi amma wannan Anti Kubra bata kyauta mata ba. Haka kawai zata janyo mata zargi. Durkusawa tayi a kasa kusa da kafafunsa tana share hawaye da bayan hannu

“ba rokonta nayi ba, ban san ko na meye ba haka kawai ta bani. Amma yanzu zanje na zubar”

Tashi tayi da sauri ta bude fridge ta nemi jarka sama da kasa ta rasa. Hankalinta ya sake tashi tana juyowa ta fada hannun Awaisu da yake tsaye kusa da ita.

“Shikenan na yarda amma kada ki kara, muje ki tara min ruwa nayi wanka”

Ba musu tace to don sauri ta rigashi zuwa dakin nasa ma. Yana biye da ita yana ta dariya a hankali. Tana fitowa daga bandakin ya sake daurewa

“mata kuyi ta daukowa kanku abu mara amfani…anyway ki fiddo min kaya sannan ki jira idan na fito ki shafa min mai”

STORY CONTINUES BELOW

Yadda hankalinta ya tashi sosai bata son fushinsa to ta sake cewa jikinta duk yayi sanyi. Indai zai hakura ko me yake so zatayi.

Tana zaune ta rafka tagumi ya fito ya kusa kwashewa da dariya ganin yadda tayi saurin tashi tayo kansa da karamin tawul.

“Bari na tayaka goge jikin nasan ka gaji”

Kansa ta goge masa sannan ta dauko man zata shafa masa hannunta yana ta rawa ta kasa taba shi. Tausayi ta bashi ya dagata ya sauke akan gado. Hancinta ya ja yana kare mata kallo tayi kyau sosai cikin riga da skirt na atampa da ta saka 

“matsoraciya nima na rama abinda kika yi min shekaranjiya akan attaruhun indomin azaba”

“Da gaske wasa kake yi?” Ta tsare shi da idanunta suna kyalli har yanzu da kwalla.

“Tarkacenku ne na mata ta baki ko shima sai nayi miki bayani?”

Kunya taji ta rufe idonta. Amma gaskiya ya tayar mata da hankali sosai don ba karamin tsorata tayi ba. Kafafunta ta fara bugawa tana masa shagawaba wadda take kara tafiya da hankalinsa

“Ni sai na rama”

Bakinsa ya kai saitin nata “dama ramuwar nake so kiyi tun dazu kin kasa fahimta” daga nan ya hanata tashi.

******

Suna isa gidan Dr. Yana da Mujahid suka yiwa Gimbi jagora zuwa dakin Haj Fanta. Tuwo take ci suka yi sallama ta amsa amma hankalinta yana kan Gimbi.

“Sannu da zuwa Gombo”

Gimbi ta kalli Dr. Yana ta murmusa

“wato ke taki a gida take ma. Lallai kin ma fini. Gashi har sunana ta sani”

Dr. Yana bata amsa mata ba don gani take da kyar idan Gimbi tana da hankali. Gaisawa suka yi da Hajiya sannan tayi musu alama su fita.

Hankalin Gimbi a kwance  tana ta jira matar ta bata damar fadin abinda ya kawota taji shiru sai cin tuwonta take yi.

“Doctor tayi miki bayanin me ya kawoni ne ko har kin sani?”

“Na sani shiyasa gobe da sassafe zamu wuce Maiduguri. A nan ne nake da wanda zaiyi miki maganin matsalolinki”

Kayataccen murmushi Gimbi tayi

“dama kuwa ina jin labarin Maiduguri suma ba daga nan ba wurin irin wannan taimakon. Yanzu ke sai a goben zan biyaki ko inda zamu je din zasu sallameki a abinda zan bayar?”

Haj Fanta tace mata kada ta damu yiwa kai ne. Abinci tasa Dr. Yana ta kawowa Gimbi taci tuwo zuciyarta fes tana jiran gobe tayi maganin makiya.

*****

Awaisu da Rumana na kwance tana ta shagwaba yana biye mata tace su tashi suci abinci. Kimtsawa sukayi zuwa falon ma tace ita bata da lafiya duka jikinta na ciwo sai kawai ya dauketa.

A kujerar dinning table ya ajiyeta sannan ya zauna ta zuba musu farar shinkafa da ta dafa da sauce din hanta wanda yaji kayan lambu. Awaisu ya zuba santi don babu yajin nan irin na girkinta na farko.

Lokaci lokaci tana kallon kofa ganin har tara ta wuce Gimbi bata dawo ba. Tana son fada masa amma tana tsoron kada ya zama gulma tayi kila ya riga ya sani ma. Bayan sun gama ya zauna yana kallon news tana kwance a jikinsa yana cewa ita da school sai monday ta zauna rabon kwana taki karatu. Dariya tayi  amma hankalinta ba a kwance yake ba.

“Son So me ya sameki ne? Da safe kinyi min gardama zaki iya kula da jikinki amma na kula kamar jan kafa ma kike yi.  Tashi mu tafi dama nasan ba wani iya kula da kanki zakiyi ba”

Da sauri tace

“ni lafiyata kalau dama naga Anti bata dawo bane kuma ina tsoron yi maka magana ko gulma ce” ta tashi zaune.

“Gimbi ta fita?” Ya fada ransa ya soma baci har muryarsa ta canja.

Tsorata tayi dama haka take gudu. To amma dare yana kara yi shiyasa tayi tunanin fada masan shi ya fi.

Fita yayi waje ya tambayi maigadi wanda ya tabbatar masa tun goman safe ta fice. Nan da nan kan Awaisu ya dau chaji. Wai me Gimbi take nema a rayuwarta ne? Ya tabbatar wurin wani bokan kila ta tafi saboda ta bari shaidan ya gama fitsare mata kai tayi nisa bata waige.

STORY CONTINUES BELOW

Rumana na zaune ya dawo yace ta fada masa yadda sukayi da zata fita. Ita duk ta tsorata ma da yanayinsa ta fada masa abinda Gimbin tace.

“Shikenan kije ciki ina zuwa” yace mata kawai bayan ta gama fada masa.

Magana taso yi ya sake cewa ta tashi da dan karfi.

Jiki a sanyaye ta tashi ga ciwon jiki da yake damunta wanda ya kara mata. Dakinta ta wuce ta je ta sami ruwa mai zafi ta zauna a ciki ko zata ji saukin jikinta. A hankali ta soma kuka tana tausayin kanta.

Awaisu yayi ta buga wayar Gimbi tana shiga bata dauka ba. Hankalinsa ya kara tashi ya kira Alh Mudi ya fada masa. Ce masa yayi su jira zuwa wayewar gari. Tunda rayuwar da ta zaba kenan lokaci yayi da duka har shi zasu zare hannuwansu daga kanta. Shi dai haka ya ajiye wayar zuciyarsa tana zafi. Me zaice da ‘ya’yansa nan gaba gamw da mahaifiyarsu don ya tabbata bazai taba bari ta kusance su yadda zasuyi sabon da zata koya musu mugun hali ba.

Sai kai kawo yake yi a falon wayarsa tayi kara. Yana dubawa yaga Gimbi ce ya amsa da sauri.

Lokacin ma Haj Fanta ce tace ta kira maigidanta ta fada masa tana lafiya tunda da bakinta tace mata babu wanda yasan inda take.

“Naga kana ta wani kirana har amarcin ya kare ne? Kada ka fara murnar na tafi zaku sha iska dawowata daidai take da saituwar lamurana yadda nake so. Wannan yarinyar kuma tun wuri ka fada mata ta fara hada kaya watan zawarcinta ya kama” kit ta kashe wayar ko *a* bai  sami damar fada ba. Ajiyar zuciya yayi tunda lafiya take bari ta dawo gidansu zata koma ya gaji haka. Rumana ce ta fado masa ya tashi yayi ciki da sauri.

Fitowarta kenan daga bandakin daure da tawul idanunta sun kumbura sunyi ja. Bata san yadda akayi ba sai gashi a gabanta ya rungumeta.

“Kiyi hakuri Son So nayi miki fada akan abinda bai shafeki ba”

Dan ture shi tayi ta dago kanta. Sai lokacin ya kula da idanun

“Subhanallah kuka kika yi? I am realy sorry bana son bacin ranki. Dazu na rasa tunanin da zanyi ne kawai nace ki tafi kada nayi abinda bazai miki dadi ba. Ashe ma na riga nayi”

Ita dai bata ce komai ba har ya zaunar da ita ya tallafi fuskarta da hannunsa daya, dayan kuma yana wasa da yatsunta ya zauna daga gabanta.

“I love you so much Umm Ruman. Kinga sakona da safe?”

Kai ta gyada wata bakuwar kunya na shigarta.

“Ina so ki zama mai hakuri da juriya akan rayuwa. Yadda na daga miki murya dazu bai kamata ba….”

Girgiza  kanta take yi saboda a ganinta bai dace mutum kamar Awaisu yana ta bata hakuri irin haka ba.

“Ka dena cewa nayi hakuru ba fushi nayi ba fa ni bani da lafiya ne.”

“Bayar da hakuri yana da mahimmanci a zaman tare.”

Saitin zuciyarta ya dafa itama ya dora hannunta a nasa kirjin.

“Yanzu kece nan dina nine nan dinki. Mun zama daya saboda haka kada ki rinka boye min duk abinda yake ranki. Ina reply din sakona na safe ko babu?” Ya tayar da ita zuwa gaban mudubi zai shafa mata mai.

Murmushi tayi kanta a kasa “yana dakinka”

“To muje ki bani”

Turjewa tayi zata masa kuka “ni dai tsoro nake ji Son So ka barni a nan bani da lafiya fa nace”

“Naji ai muje magani zan baki”

Wani irin tausayinta yaji. Yasan yarinya ce dole sai yayi da gaske wurin lallabata. Sonta yake har kasan zuciyarsa baya son yana ganin hawayenta.

“Bacci zamuyi idan kin nuna min reply din naga kin fara tsorata….I promise” ya kare da dariya

Sai lokacin da saki jikinta ya taimaka mata ta shirya suka koma dakinsa. Haka suka kwanta yana rungume da ita a kunne ta rada masa

“I love you Uncle Awaisu Son So”

Nan ya manta da komai ya shiga karanta mata wasu darussan da bata san da irinsu ba a zamantakewar aure.

******

Kiran sallar farko ya tayar da Gimbi ta tashi ta ga Haj Fanta tana sallah. Alwala tayi da sallah amma a ranta tana mamakin ashe dai masu zuwa gun bokaye suna ibada sosai.

Da sukayi wanka suka shirya Haj Fanta taci abinci amma ta fadawa Gimbi tun jiya sako yazo daga Gogojiya kada tasha ko da ruwa ne. Gimbi babu musu tace to tun yanzu ta fara jiyo kamshin sa’a a tafiyar.

Da Mujahid da Yana suka tafi da yake sun fita da wuri goma a cikin Maiduguri tayi musu.  Haj Fanta tasa ya kaita unguwarsu Yakura mahaifiyar Yana tace su tafi gidan daya daga cikin yayyensa mata su jirata. Duk su biyun suna son mata tambayar me zata yiwa Gimbi amma babu fuska.

Kafin su sauka tasa Mujahid ya kira kanin Yana mai suna Bukarti ta karbi wayar cikin yaren kanuri ta kwatanta masa Gimbi da inda zai ganta sannan tace yasan yadda zaiyi ya sace mata jakar hannunta batare da ta kula ba. Gaban su Yana har faduwa yayi jin me tace ita kuwa ta matse abinta. Shiyasa suna ajiyeta suka wuce wurin Malam wanda yayi nasarar rabata da aljanunta.

Da yake safiya ce unguwar babu mutane sosai Haj Fanta ta nunawa Gimbi wata hanya wanda idan aka mike zata kai mutum filaye da gonaki ne.

“Gogojiya tace ki dora jakarki a ka sannan kiyi ta tafiyar minti ashirin babu waige a kan hanyar nan. Idan minti ashirin ya cika ki dawo nan inda kika fara sannan ki sake maimaitawa har sai inuwarki ta karkace tana kallon Yamma maso gabashin arewa”

“Me kika ce?” Gimbi ta fada a rude.

Sake maimaitawa tayi sannan tayi dan murmushi “aikinmu tamkar yankan wuka yake”

Jikinta ya fara sanyi tace “to yanzu batun biyan fa”

“Haba Gombo aljanun gaske ko kwandala bai kamata su karba ba. Su da suke bawa mutane sun fi karfin abin. Idan kin gama zaki ga wani yaro matashi zai kwatanta miki gidan da zaki sameni. Na barki lafiya “

Gimbi na gani ta juya tayi gaba ta saita agogon wayarta ta fara tafiya. Ga rana ta take cikin dan lokaci ta fara gumi ga yunwa. Duk wanda yazo wucewa sai ta tambaye shi ko inuwarta ta karkata yamma maso gabashin arewa sai ayi mata dariya. Wurin shadaya da rabi ta tambayi wani mutum shi kuwa gani yayi kamar bata da hankali yace eh. Murna ta kamata ta sami wani tudu ta zauna kenan taga zugar samari suka rufo kamar zasu daketa kawai Bukarti ya sunkuce mata jakar da ta sako takardun filinta.  Ihu ta rinka kurmawa ba jimawa sai ga wani yaro yazo bisa umarnin Haj Fanta ko magana baiyi mata ba ya kama hannunta suka tafi gidan Yakura.

Ta gaji sosai kafafunta sunyi futu-futu suka shiga gidan. Haj Fanta ta gani da kanwarta wadda take ta yi mata fadan abinda tayi.

Haj Fanta ta dago ta kalleta cikin bacin rai “Gombo kinyi babban kuskure da kika kawo kanki gidana. Nice mahaifiyar Mujahid mijin Yana wadda kika zubarwa ciki. “

Yakura tace “haba Ya Fanta me zai sa ki biyewa jahila wadda bata san me takeyi ba har ki daukarwa kanki hakkin cutar da ita? Ke Gombo kike ko me fita ki koma inda kika fito”

Gimbi ta tsaya turus tana kallosu. Me suke nufi? Duk wahalar da tasha dama karya ne. Ranta yayi masifar baci ga tsoro sai ga hawaye babu shiri.

Haj Fanta ta harareta “au kuka kike yi tun yanzu? Baki ga komai ba a abinda nayi miki tanadi. Gogojiya kuma yanzu ta fara min wasan kura dake”

“A gaskiya Fanta kin bani mamaki”

Dukkansu ukun suka dago kai suna kallon Dr. Yana da Mujahid sai kuma wani farin dattijo mai shekaru. Fuskarsa ma’abociyar kwarjini da haiba ya hade yace a nuna masa inda zasu zauna magana ce yake so suyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *