KUSKUREN MU CHAPTER 2 BY ZULAIHAU ALIYU MISAU

 KUSKUREN MU CHAPTER 2 BY ZULAIHAU ALIYU MISAU

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ashty sanye da uniform, ta fito don zuwa gaishe da Yahh, kamar yadda suka saba duk safiya.+

Fitowanta kenan shi kuma yana shigowa. wani hadadden saurayi na gani, Masha Allah, Dogone bashi da kiba, yanada doguwar fuska mai dauke da ma dai_dai cin hanci, mai kyau da tsari, Bakinshi dai dai, ba karamiba ba babbaba idanuwan sa ma dai _dai ta masu haske. Ga yalwataccen gashin gira dana ido, sannan ga zagayayyen sajen sa daya sha gyara, kwance lub_lub, Kanshi ba yalwar gashi, da alama bai dade da aski ba, Amma da gani yanada yalwar gashin kai baki, da santsi, Kana ganin shi kaga bafulatani, Farine tas dashi, ma’a bocin gayu, da kwarjini.  M Zaid kenan yaro Dan kwalisa. Sanye yake da kaftan din shadda Navy blue, da hula zanna bukar, itama Navy blue, Sun yi masa masifar kyau.

Kasa matsawa tayi, zuciyarta na faman bugawa da karfi. Kallonsa take cike da shauki, Kansa ya dago jin da yayi Alamar ana kallon sa. Harara ya watsa mata, ” mayyah ” ya fada a zuciyarsa,  tare da Jan karamin tsaki,  wanda yai saurin dawo da ita daga duniyar data lula. ” ina kwana” ta furta cikin kokarin tattara natsuwarta da kalaman bakinta. Kamar bazai amsaba,  cikin murya kasa- kasa yace “Lfy” ya fada ba tare daya kara kallon ko inda take ba. Don Ya dade da gane take takenta, Ya wuce part din yahh.

A hankali tabi bayansa da kallo, ta bishi xuwa part din. Tana mai farin cikin ganin sa, Ko ba komai zuciyarta ta samu natsuwa, tunda ta ganshi. Da sallama suka shiga, yana gaba tana binsa a baya. Abi ne zaune a dinning table, tare da su Aliyu, Abdullah sai ya salim, da yaya babba, Suna breakfast. Shima kujera yaja ya zauna. Ashty ta gaishe da Abi da sauran yayyen nata Ta wuce dakin yahh.

         Gaishe da Abi yayi, da sauran yan uwan nasa, ya jawo plate ya zuba Abinci ya fara ci. Abi ne yace ” yau meya faru ? Na ganku kun shirya haka a tare?”

Ya babba ne ya amsa mai da cewa ” jiya bayan mun shiga kwanciya, naga text  cewa yau a na neman mu varification na N POWER, da nake gaya maka mun cike.So, same thing da zaid da salim, Da asubannan Abdallah ma yayi receiving text din shima.” ” ok anyi yaka, ni har na manta ma. Allah ya bada sa’a, yasa a dace.” “Amin” suka amsa baki daya.

” kar kuce zaku dogara da aikin government, koda kuka samu wannan N POWER din, Ku rike sana’ar ku da kyau, kuna kallon yadda alamuran kasar ke tafiya.” Duk wanda ya dogara da salary yana cikin wahala, dole mutun ya samu second in comes, Saboda halin rayuwa Samun aikin ma ya zama wahala, In mutun nada sana’ar sa, koda bai samu aikin government ba bashi da matsala, Fatan dai Allah yasa masa Albarka, sai ka samu abinda mai aikin bai samu ba,Kudin da za’a dinga biyan ku, ba wasu kudi bane masu yawa,  dole sai kun hada da Sana’a, So,  kurike sana’ar ku dakyau,  kar kuga kun samu wannan ku wulakantar da sana’ar ku. Abi ya cigaba da cewa, akwai contract din uniform na staff sch. Na samo muku in kun dawo za muyi magana.”

“Godiya muke” cewar Abdullah. “Insha Allah zamu kiyaye.”

Sun fito break kamar yadda suka saba, gidan malan kawu suka nufa cin taliya. Taliyar matar malan kawu tayi suna a sch. Din, Ta samu karbuwa, Taliyar hausa ce taji kayan miya da manja, ruwa_-ruwa. Yanda na hango layin taliyar yasa na tabbatar matan m kawu ta iya girki,
“Duk ku kawo kudin ku ku gani, Don yau na lura layin yafi na kullun.”
Cewar Asma, ta cire hijabinta ta mikawa sim_sim rike ki gani, Dakin matar malan kawu ta nufa, Aisha ce yarinyar malan kawu da kawayenta su na zazzaune da alama suma taliyar suke jira.

“Aisha nemomin kwano babba ki gani, Aisha Tace to, da yake sun Saba,  class dinsu daya, ta nufi dakin dake cikin falon, can sai gata da samira ta kasan, “Gashi Amma don Allah kina gamawa ki kawo min hannu da hannu. ” naji!!!!” Tsayawa tayi tukunna ta kare musu kallo sannan ta nufi wadda ke gaba akan layi ” ina layin da nace ki kama min?”
Yarinyar ta juyo ta ce “ni?” “Eh ke.” ” Ni kam bani ba.” “Karki raina min hankali mana. Yar Butarshayi!!! Ai wallahi baki isaba ana zuba miki ni zaa zubawa.” Nan sauran dalibai suka fara”duk da kina head girl baki isaba kizo kibi layi kamar yadda kowacce take bi, Don baza mu yadda da ojoroba ehe!!!!” Tab ashe baza’a ci  taliya ba yau a gidannan, in har ba’a zubamin ba,  banga yar abu kazan da za’a zubawa ba, Ko don Albarkacin Jan Dan kwalina ai kwa bari a bani tukunna.” Nan fa wuri ya hargitse da haya niya.

Matar malan kawu tace” nidai karku janyomin asara, kuyi hakuri in bata ta tafi, Ina ita kadaice?”Tabdijan bamu yaddaba, Asma tace idan ba’a bani ba yau naga yar gidansun da za’aba, In kuwa an’ba wata, to ba sunana Asmau Abubakar Saleh ba.
W

ani tabarya ta zaro daga gefenta, Yarinya tamatso, mamarta ta haifi wata.

Ganin haka yasa matar m. Kawu ta fige kwanon “na nawa zan zuba miki? Tun da na ganki a wurinnan nasan zaki chazamin, yar neman yarinya, firit dake sai masifar tsiya.”Oho dai. Dalibai kam sai surutansu suke, masu karfi kuma suna hankoron dukanta, Wa’anda sukasan wacece Asma kam cewa suke”ku bari kawai a bata, ai ba duka zata sayeba,wannan da kuke gani yanzunnan zata tada wurinnan duk mu rasa.”

“thanks mamarmu” ta fada tana dora kwanon taliyarta akai, Tayi waje.
H

arta kai kofar fita ta juyo, “hey!!girls”wasu suka dan juyo wasu na kokarin mika nasu ribobi. “Sorry girls forgive me.” Ta fada tana murmushi ta fice.

Wurin zamansu ta nufa, Suna zaune a gindin bishiyar da suka saba zama, tazo ta ajiye kwanon, “Shine kuka gudo, da ammin duka fa?” Dariya sukayi,  Haba dai we trust you,
Sun gama cin abincinsu, tima ta siyo musu rake suna sha kafin a koma break.
“Yauwa ziyya ya labarin business din naki?” Inji Ashty, Kin tunamin ma, jakarta ta tabude ta fito da  leda, bari ku gani, ta zazzage daurin magun guna ne, da wasu a gorar swan kanana, “Kungansu.?” Baki suka rike, “Asma tace ke yanzu ina kika samu wa’annan abubu wa?”

Gyara zama tayi ta dauko kulli daya kunga wannan……..

“Sabara ce, shi zan basu a matsayin nasha da nono, ko ba komai zai musu maganin ciwon ciki, shi kakus ke jikamin in cikina ya baci, ko yana ciwo, Wannan kuma garin kanya ne shima zance susha da nono, Bansan maganin shiba, ta tabe baki, Wannan ma sha da nono ko yoghurt shima ban san shiba, A cikin tarkacen magun -gunan kakus na ganshi, Wannan gumba ne, Gumbar shinkafa ce na zuba ararrabi da garin zogale da sabara na kara suga. Ko ba komai zogale da ararrabi da sabara maganine, Sai dai bansan nameba.

W

annan kuwa, Mazarkwaila da ararrabi, da kayan kamshi na jika, tsumin yargata kenan.”

1

Haba mai zasuyi banda dariya sai da sukayi mai isarsu sa’annan tace “na manta akwai sa maigida ihu, wasu itatuwa ta fito dashi, shi kuma jikawa ayi tsarki.” “Wannan icen menene?” Sim_sim ta tan baya? “Oho duk a jakar tsohuwa na rakitosu Kun san kakus batason asibiti ko kadan sai dai gargajiya.”

“Ke yanzu bakya gudun suyi amfani dashi a samu matsala?” Cewar haly.

  “in kudina yazo hannu ni ina ruwana, can ta matse musu kuma, don ma ban rakito musu na matsiba.”

Asma tace “toke duk ina kika san wa’annan babuwa, naga har sunaye kika sa musu?” “Matar kawuna, lokacin ina minna tana muamala dasu sosai, nasan akwai : gida ko mota, baki ba kishiya, sa maigida tsalle, mummuna da aiki, gasunan dai barkatai. Baza ta iya kyautar naira 100 ba amma sai tasai kayan matan 20,000 a take.”

+

“Allah ya kyauta.” Inji haly ” matan gidan mu ma sana’arsu kenan. Kullun adashin kayan mata, mace bataci a cikin taba batayi sadaka ba, kullun ana babu kudi, amma ana kawo irin wa’annan abubuwa jiki na rawa sai ki rasa inda kudin suke fitowa.”

Sim_ sim ma ta cigaba da cewa “sai ma in kuna social media kowa yanzu ya zama dan mai ganye, sai mutun ya zauna ya kirkiri a bunshi shi kadai ba tare da yasan illar shiba sai ya watsa, yanzu kyaji mata sun rude wuri neman abun, Komai tsadarsa kuwa.”

kararrawar da aka kadane ya sasu tashi, Asma taja ziyyah ” zo muje ki rakani in kaiwa mamanmu kwanonta.” ” ok muje don yau ma biology muke da after break.” Bishiyar da Asma ta saba buya, sukaje, suka samu wuri suka zauna. Asma tace “ziyyah ki zubar da wa’annan tarkacen, in dai maganar anko ne da contribution, i will pay for you.”

Ziyyah tace ” a you serious?” ” Yes I’m serious.” “To ke a ina zaki samo kudin da zaki biya min?” Asma tai murmushi, asusuna zan fasa, ina dan serving saboda bikin su Anty juwaira.

b

ut  kin fini bukata, kuma kin ga Bikin da dan saura, zan iya tara wasu,

In sha Allah.”

Hannunta ziyyah ta kamo idonta tap da kwallah. ” bansan mai zance miki ba? Nagode sosai Allah ya kara zumunci. Maraici ba dadi, Ku gode Allah kuna gaban iyayenku, tun tashina a cikin walagigin rayuwa nake, dawowata gaban kakus ne na samu saukin rayuwa, Har nakan samu farin ciki, Kakus na sona tana kula dani, but problem dinta akwai son kudi, kudin makarantar ma dakyar take biya min, da badon kawuna da shi ke aiko mata da 50k duk wata, na bukatunmu,  yace in har bata biya min sch fees zai daina bata ko sisi, Shiyasa take biya,  don tasan zai aikata. Tunda na mata maganar send up party din tace karma na tambayeta kosisi don baza ta bayarba, Ni kuma bazan iya tam bayar kawu ba, Don nasan yana matukar kokari a kanmu,  ga nashi iyalan shima.”

“Na sani karki damu problem solve.” Cewar Asma. ” Yanzu dai ki zubar dasu, ke bakya tsoron ki siyar musu yaxo ya haifar musu da illah, da zaki iya shiga matsala.? Iri wa’annan abubuwa suna da matukar illah a lafiyar mu, su kansu ingatattun sai munbi ka’ida sannan musamu abin da muke so, balle wa’anda baki da ai’nihin sahihancin su. Magani ko na Hausa a kwai ka’idar hadawa,  da yadda za ayi anfani dashi, In Sana’a kikeso akwai abubuwa da yawa da zaki iya yi a sauka’ke da basa bukatar kudi da yawa. Siyarma mata irin wa’annan kaya marasa inganci zalincine, Kuma musani Allah na yafe komai amma banda zalintar yan uwanmu, muji tsoron Allah, duk abin da zamuyi mu tuna zamu tashi gaban Allah (S.W.A) zamu amsa sakamakon aiyu kan mu in ma kyakykyawa, imma sabanin hakan, Ita rayuwar nan da kike gani ko wanne mutun yana da nashi jarabawar, Sannan ba komai mutun yake nema yake samu ba. The must important shine dogara ga Allah, sannan duk abinda zakayi kasan hukuncin sa a Addini kafin ka aiwatar dashi, Duk abinda zaka sa ko kaci,  ka tabbatar ka samesu bata hanyar zalunci ba.”

“Na gode Asma Allah ya biyaki, da ana dacen kawa irinki tabbas da an zauna lafiya.”

“Ba komai ana tare” “Yauwa yau in sha Allah zamuzo gidan sheikh, so zamu biyo.”

“Don Allah da gaske?” ” Asma tace da gaske mana na taba miki irin wannan al’khawarin ne?”

“A’a. Nima jiya muka je da kakus,” “Hajjajo da kakus ai abin nasu sai su, amma nayi missing, don in har suka hadu sai kaci dariya kamar zaka mutu.”

Ziyyah tace “ki bari kawai kamar kinsan jiya sai da cikina yayi ciwo tsabar dariya.”

“Kin san me?” asma tace “a’a” Labarin lokacin yan matancinsu, da yadda ake zance in saurayi yazo, Ke harda zaurancen da suke yi, Kai na dade banyi dariya ba irin jiyannan.”

Asma tace “shiyasa ai inason zuwa gidan Hajjajo ko ba komai, ka sha dariya.” “Nimafa jiya har tafiya aka koyamin da yadda zan dinga kada ido in ina zance.”

Dariya suka saka gaba daya. “Kin san waya koyamin?” ” Aa” “mairo kawarsu kakus ai kin santa ko?”

“Niko nasan ta, Matar akwai bandariya har tafi su Hajjajo, nida tace in gama iyayi na bazan samu miji kamar nataba, Saboda nace ni nafi son in auri mumunan miji, a she mijinta mummuna ne ni ban sani ba.”

Dariya suka fashe da sai da sukayi mai isar su, tafin da sukaji ne yasa su saurin juyawa, ido suka zazzaro cikin tsoro tare da mikewa da sauri……Displine master ne, tsaye da shar bebiyar bulalarsa. “After noon sir” suka fada cikin rawan jiki. “Afternoon.” Ya fada yana mazurai, “

what a you doing here by yourself ?”

Y

a tambayesu yana zazzaro jajayen idon sa. “Notting sir, just skipping for one boring subject.” Asma ta fada, cikin dakewar murya. “I see! Asmau Asmau Asmau, How many times i call you.” Ya na mai rike kunnuwan sa,

“3 times sir.”

“Last warning if i so you skipping class again!!;, hahhhh sorry for you, I hope u get what I’m saying? Do u here that ?” “Yes sir” suka fada a tare.

“Oya !!! Come and collect 3 Lashers, I cant live u like that.” “Sorry sir, were not doing it again.” Ziyya ce ta kalleshi ta daga hannu ” Sir i will bring u, your favorite on monday in sha Allah.” Ziyyah ta fada tana washe baki. “Eheee !! Good girls, that why i start to miss u o ready, Ok oya !!! Go back to the class, now-now.”

“Wai Allah na, yau Allah ya kwace mu, na tsani bulala a rayuwata.” Ziyyah tace “bar dan is !!! Kwada yayye, ai tun da muka gane laggon sa, mun gama dashi” Dariya sukayi suka tafa. Sun samu Biology ya fita, Nan suka nemi wurin zaman su, Asma note din da akayi ta karba wurin tima, ta fara copy. Ziyya tana basu labarin haduwarsu da Displine master, suna dariya.

Bazanfara ce zaune a wurin da aka tanada don wanke- wanke, Tana dauraye kayan da akaci abincin rana dasu. Asma  ta fito da plate da suka gama cin abinci.

1

Ammys plat

“Mutuniyar ke bakya gajiya ne, wannan uban ranar amma kin kuke sai aiki kike a ciki bakya tsoron ciko ya kama mana ke?”

Bazanfara ta washe hakoranta da sukai ja don cin goro, “yar gidana kenan, har an dawo, yau banji dawowar kuba.?” Asma tace “gudowa mukai ba’a tashiba.” “Amma bance ki fada ba don nasanki” “Haba yar gidana ba maiji, Haryanzu dai ba’a girma ba.” Asma ta harareta to mai za’a fasa?”

Buta bazanfara ta dauka don zaga yawa bayan gidan, da ke tsakar gidan. Murmushi Asma tayi, tayi daki da gudu tana kiran Ashty.

“Ke lafiya kike kirana haka, kamar naci bashi ban biya ba?” Abu ta rada mata a kunne, sukai waje da gudu.

Jikin kofar toilet din da bazanfara ta shiga su ka makala kunnensu, suna kunshe dariya, sai da sukaji alamar ta gama abin da takeyi zata fito sai suka koma brander din part din Ammy suka tsaya suna dariya.

Ammys brander

Asma ta ce “Ashty kin tuna wannan wakar “”” fufufurrr fur furr, gyuitttt, futttt”Ashty tace kin manta na farkon “”buuuttttt fus” suka kwashe da dariya suka tafa. Bazanfara murmushi kawai tayi tare da girgiza kai, Don tasan da ita suke, In da sabo, ta saba. “Allah ya shiya mana ku” ta fada, ta koma ta cigaba

da wanke wanken ta.

Aliyu ne ya karaso kusa da bazanfara ” ki hadasu da Abba, kullun kika shiga toilet in dai sunanan sai sun biki, su makale suna jin abinda kike yi”

“kyalesu babana wataran zasu dai na.”

“Aliyu wallahi in baka daina samana ido a gidannan ba, jikin ka zai gaya mka, Don duk ranar da kazo hannu na, na lahira sai ya fika jin dadi.” Cewar Ashty.

Aliyu ya harare su. “Mutun ya tabani yaga ikon Allah.”

Asma ta rike baki” ki ga min yaro ?”

“Lallai rashin kunyarka ta shahara. Zamu hadu.”

Ya tabe baki, ya wuce zuwa part din yahh. Asma ta kirashi, ya juyo, ” Meye kuma ?” ” Yau zamu gidan Hajjajo ka shirya muje tare kaji.”

Wata harara ya zabga mata kamar wani babba. Aliyu kenan in yayi wani abun baka cewa shekarun sa 8 kawai, kamar wani babban mutun. “Ban zuwa !!!! “

“Haba brother yaushe rabonka da gidan kakus ?” Cewar Ashty.

“Bazan jeba.” Asma tace “Aliyu meyasa kake haka ne hajjajo na sonka amma kai kullun akai maganar ta kamar wata makiyarka ? Me ta makane har haka ?”

Tabe baki yayi tare da daga kafada. ” I don’t like her.”

Daga Asma har Ashty da bazanfara dake wanke wanken ta, tana jin su sai da ta dago tana kallonsa, duk da turancin nata bai nuna ba, amma tana tsinta zamanta a gidan.

“Kakar taka kake fadin haka, karka manta ita ta haifi abin mufah !!!”

tsaki yayi “na sani, but duk da haka ban sonta, tun da bata son yahhh.

Ke mafa i don’t like you, because you look like her.” Ya fada yana nuna Asma ,da tsananin mamaki yasa suka dankare a wurin.

Yahh ce ta kwala masa kira. Duk abin da ke faruwa tana daga falon ta tana jinsu, Tsananin mamaki, don ta matukar kaduwa da jin kalamansa.

2

Yahh plat

“Aliyu wa yace maka hajjajo bata sona ?” Ta tambaye shi cike da mamakin furucin sa.

Aliyu ya tura baki ” ba wanda ya fada min, ni na sani da kai na” tama rasa bakin magana ta zuba mishi ido kawai tana kallon sa.

“Aliyu yaro ne, Amma alamuransa na bata tsoro wani lokacin, in yana abu, bata gajiya da kallonsa.

Tabbas tasan cewa surukar tata bata son ta, hakan yasamo asali ne, tun fara maganar Aurenta da abubakar,

Hajjojo ta so ya auri yar kawunta, amma yaki yace sai ita, An sha gwagwarmaya saida sheikh ya tsaya sosai sannan ta amince da auren yahh. Koda akayi auren ma har tayi haihuwa 3 amma bata samu soyayyar uwar miji ba, duk da tsananin kyautata mata da takeyi, Haihuwar Asma ne ya sa tadan sakko, saboda an samu mai kama da ita, sannan ansa sunanta. Hajjajo Allah ya jarabceta da son Asma, duk jikokinta, Kowa ya riga ya sani, in kanason bacin rai da tashin hankalin hajjajo to ka taba Asma, Haihuwar Asma yasa yahh ta samu saukin tsana da tsangwamar hajjajo, tanada cikin Aliyu, Hajjajo ta tsiro da cewa Tana son Abubakar yaje yaga kanwar Ammy, Tana son ya aureta, Ammy yace ga Abokin wasan hajjajo, baffa isah, Nan ma an’sha gwagwar maya kafin maganar ta wuce, don Abubakar ya nuna bashi da burin ajiye mata fiye da daya, kuma matarsa ba abinda ta rageshi dashi. Sannan rashin adalcine ace ya rasa wadda zai autra sai kanwar Ammy. Wadda suke zama lafiya da yahh duk shekarun nan ba wanda yaji kansu.

Haihuwar Aliyu ya kara sanyaya gwuiwar Hajjajo, Aliyu sak baffanta.

Tana son Aliyu, Amma tun fara wayan sa, Aliyu jinin sa bai hadu da na Hajjoba.

Tirkashiiiii…….Ammy ita ce fevourit din Hajjajo, sai matan Uncle sulaiman.+

Fist wife din shi yar uwar Ammy ce, amaryar kuma yar Abokin sheikh ce.

Hajjajo na son surukanta, bata gajiya da hidimta musu, Kamar su daddawa, kuka, kubewa, yaji, garin kunu, garin danwake dasauran su, Duk ita ke musu ta aika musu. Amma banda yahh Kuma hakan bai taba damun taba, tunda tasan tsakani da Allah take zama da ita, kuma tana iya kokarin ta wurin kyauta ta mata fiye da sauran surukan. Tsakanin yahh da Hajjajo daga gaisuwa, ya yaran shi kenan, In yah zata wuni a gidan surukan nata, Hajjajo bazata ko zauna dakin ba balle suyi dan hira.

Saba nin sauran surukan nata da in sunzo ta fara hidima dasu kenan, ana hira ana dariya. In kaga ta sake da yahh to, tare sukaje da Ammy.

Sheikh na son yahh duk cikin surukan nasa, yafi sonta. Saboda dattakonta, hankali da natsuwa, sannan akwai sanin yakamata, Bata gajiya wurin yi masu alkhairi, musamman turaruka, Sannan lokaci zuwa lokaci zata yi abinci Mai rai da lfy ta aiko musu dashi.

“Aliyu kar in sake jin irin wannan maganar a bakin ka, kaji ko ?” Yahh ta fada tana dan zaro mai ido. Aliyu ya tura baki, tare da daga kai, alamar yaji, Fada yahh tayi ma Aliyu sosai.

Asma da Ashty ne suka shigo dakin sunyi kyau, cikin riga da skeet na atamfa red and yellow, sunyi kyau sosai kamar ka sace ka gudu. Suka daura red din hijab mai hannu. Suka gaishe da yahh, Tare da yi mata sallama, zasuje gidan hajjajo. Daki ta shiga, ta fito da turaren wuta kwalbal bama babba guda biyu, da humra su kaiwa hajjajo. Sannan ta basu humra su kaiwa ummi.

Aliyu na zaune yana home work, ko kallonsu baiyi ba, suma yau basu kula shiba. Asma da zasu fita ta kalli Aliyu, akai saa shima ita yake kallo. Ta watsamai harara, tabe bakin shi yayi, ya cigaba da homework din sa.

Maganar Aliyu ya tsayama asma a rai, Tabbas tasan hajjajo bata son mahaifiyarsu, ita kanta abun na damunta.

Amma yahh kullun takan nuna masu, Ba ruwan su da tsakaninta da surukar tata. Ta sani duk sauran yayyun nata, ba wanda yake shigewa hajjajo kamarta. Don ma yahh na musu nasiha sosai, saboda gudun samun baraka. To amma mai ya sako ta a ciki, da Aliyu zai dubi tsaban idonta yace bai sonta.? Alhali duk yan uwanta ba wanda take jinshi a ranta sama dashi, ko Ashty da suka taso tare, bata mata son da takewa dan uwan nata, yawan tsokalan shi da takeyi ma tanayi ne don son jin muryarsa, da yadda yake shagwaba,

Abin na burgeta, Sai yanzu ta gane, rashin son kulata, da shan kamshin da yake mata, ashe shi son tane bayayi. To laifin tane don tayi kama da hajjajo ? Allah yasa sauran yan uwan nata, basu tsane taba? Ta fada a zuciyarta,  tare da share kwallar data zubo mata.

Sun fito, suka tarar da Ya babba da m bello, Da alama wani wurin zasu. Suka gaishe su. “Sai ina ? “Ya babba yatambayesu”

“gidan hajjajo” cewar Ashty

M b ne yace “ok kuzo mu tafi, in mun sauke ku sai mu wuce.” Asma kam tai kici- kici da rai, kamar zata fashe. Yaya babba yace “oya ku shigo mu tafi kuna bata mana lokaci.” Ashty kam tuni ta bude kofar baya ta shige, ganin ba yadda ta iyah, yasa itama ta shiga.

Ya babba kam hirarsu kawai suke yi,

Banda su Ashty da suka zam kuramen karfi da yaji.

Asma a takure take, don duk lokacin da ta daga kanta, Idon m bello na kanta. Duk haushinsa ya cika ta, Allah Allah takeyi su isa. Dai -dai kofar gidan sheikh sukayi parking su Asma, suka sauka. Ashty ce tace “mun gode.”

M bello yayi murmushi. Tare da kallon mutuniyar tashi da ta hade fuska, abin ma dariya yaso ya bashi.

“No prob” agaishe min da Hajjajo”

Tsokana na cin Asma, Amma tana jin nauyin m bello, da yasa mata ido,  ta madubin mota. harta juya zata tafi, ta dawo dai- dai kunnen yaya babba, da yake glass din window din a sauke yake. “Zanje yan zunnan in ba Amra labarin wannan fitar da za’ayi” tana mai kunshe dariyar ta. Zaro ido yayi, kafin yace komai har ta shige gida da gudu.

“Allah yarinyar nan troble ce, kasan bom din da takeson tada min ?” M b yace “mai ya faru ?” Zataje ta ba Amra labarin wannan fitar tamu, kasan mai take nufi da hakan ?”

Dariya Mb ya fara, “Lallai Asma ta wuce yadda nake tunanin ta.”

“Yanzu dai bar wannan maganar, nasan wasa kawai take maka baza ta iya fada ba.”

Yaya babba ya nisa, ” tama fada, In da rabon in babbala yarinya too.”

“Matar tawa zaka balla?”

Ya babba yace “nafa gaya maka yadda mukayi da yarinyar nan.”

“So ka rabu da ita kawai ka nemi wata, Ga yan mata nan masu sonka, ka zabi daya kawai mutunina.”

Mb ya jefeshi da harara, “Kasan yadda nake sonta kuwa?” Ba zan iya hakura ba, Kawai ka nemo min mafita.” “Asma akwai taurin kai, na rasa wacce irin yarinya ce.” Inji ya babba ya kara da. “Ka cigaba da addua in rabon kace shikenan, don ni kaina zan so hakan.”

A harabar gidan ta tarar  Da Ashty na jiranta. Ashty taja hannun ta, “muje mu fara gaishe da ummi tukunna.”

Asma ta dan tura baki, tare da tsaki.

Ashty dai bata kula taba, inda sabo ta saba, Saboda Asma tsakaninta da Allah taya Hajjjo kishi take, bata son abinda zai hadata da ummi.

Hafsat suka samu a falo tana note, Da fara’ar ta ta fara musu sannu da zuwa, suka nemi kujera suka zauna.

Hafsat tace naji dadin ganin ku wallahi, Ashty tace “akwai labari kenan?” “Not much.” Ta fada tana murmushi. Bari in kawo muku ruwa, ummi tashiga wanka, amma yanzu zata fito. Hafsat sa’ ar su Ashty ce, duka duka wata daya taba Ashty,

yarinyace kyakykyawa, Suna kama sosai da Ashty sai dai ita coculate color ce, sannan tafi Ashty jiki kadan,

Hafsat a kwai kyan jiki sosai.

Hira Ashty da Hafsa sukeyi sosai, jefi jefi Asma na jefa nata, Duk ta kosa tai arba da hajjajonta.

Invitation card ne hafsat ta mika musu,” guest what ?” Asma tace “what ?” Hafsat tai dariya “read the card.”

Wani ihu suka sa gaba daya……..Uncle muhd?” Ashty ta fada, tana tsallen murna. “I cant believe it.” Cewar Asma.+

Fitowar ummi ne ya sa su natsuwa, “ina wuni ummi…” Cike da farin cikin ganin su, ta amsa tana tambayar mutan gidan. “Ummi ashe auren uncle ya zo, Allah ya sanya alkhairi.”

Cikin murmushi tace “amin, ina maigidana baku zo min dashi ba ?”

Asma ce tace kin san maigidan naki ai, sai a hankali.

Ta mika mata sakon yah, “gashi inji yah tace a baki.” ” ikon Allah, ita bata gajiya? Nako gode sosai.” “Bari mu shiga wurin hajjajo, anty hafsat ki shirya, yanzu zamu fito, muje wurin Amaryar mu.” “Ok.”

Da gudu suka nufi part din hajjajo, tare da sallama. Tana zaune a tsakar dakinta, suna cin kwadon zogale ita da best Friend din ta umma mairo.

Ta jiyo kara din su, cike da fara’a ta fara “oyoyooh yan gida na, sannun ku da zuwa.” Da gudu suka fada jikin ta.

Umma mairo ta ce “shike nan zasu karasa ki” tana dariya. “Munyi missing naki sosai kakus.” Cikin tsananin farin ciki, da zai nuna tsantsar son jikokin nata, Tace ku kuka san wanna kalmar, Yara Kiri- Kiri kuna neman komawa,  masu Jan kunne, Fulatanci dai shiya haiffeku eheeee….”

Ashty tai dariya “munyi kewarki da yawa.” “Ko ke da aka Haifa a ruga,  baki fimu jin fulatanci ba.” Asma ta fada Tana dariya. Kan Asma take shafawa da ta lafe jikin Hajjajo, kamar zata shige ciki.

Sun gaishe da umma mairo, suka gaida Hajjajo. “Ina dan tsoho ? Yau bamu ganshi a falo ba?” “Baya nan, kwanan nan hidimomi sun tasa shi gaba.” “Ya kamata fa ya dinga hutawa, kar a fara kwasoshi a baro, In ji Asma tana dariya. Hajjajo tace “wuce nan.”

Ashty tace ” har wani tare masa kike yi, ya tsufa ya kamata ya dinga hutawa.” Ba dole na tarewa mijina ba, yan baka sunzo! Ina tsufan yake a nan? Ko dan shekara ashirin me zai nuna ma malan?” Dariya suka sa dukkan su, umma mairo tace “ido baya mutuwa kwalli ya tadashi, kudai tsaya matsayin ku, Amma banda dan ashirin kam.” Hajjajo tai dariya, ” me makon ki tayani sai ki kwayan baya?”

“Yan neman yara, kuyi fatan kusa mu kwatan kwacin malan dina, don nasan kamarsa kam da wuya a wannan zamanin naku.”

“Wayyo !!! Inah wanda ya fishi zamu samu, in sha Allah.” “Anyah !!!! To Allah yasa.” Cewar hajjajo. Asma tace “kinaji da dan tsohonnan,”, ..

“Ba dole ba !!!! Tunda jajayen sawu ana tare.” “Allah barmana ku…” Cewar Ashty. “Amin.” Suka ce gaba daya.

“A kwai abinci a kitchen kuje ku diba, ga zogale kuma in zakuci, Bismillah.”

“Mun koshi, Amma zamuci zogale gandi.”Suna ci suna hira, suna kwasar dariya. Don in har hajjajo da umma mairo zasu hadu, to sai ka kusa mutuwa da dariya.

Umma mairo makwafciya ce ga su hajjajo, tun zuwan su ungwuwar suke tare. Umma mairo bata taba haihuwa ba, Mijin ta malan lawal, yana da wata matar da yayan shi, Shekara daya kenan da Allah yayi masa rasuwa, Shakuwa da aminci ne sosai tsakanin tsoffinnan, duk da hajjajo ta girmema umma mairo sosai. Gaba daya dangin hajjajo da na umma mairo ansan juna kuma ana zumunci sosai.

“Za muje gidan su Nasma,.” “Ku gaishe min da Hajiyar tasu.”

Har sun fita, asma ta dawo, “Na manta da sakon ki.”Gashi inji yahh tace in kawo miki. A dakile ta amsa, kamar an mata dole. umma mairo ta washe baki, “yar albarka, Allah dai yayi mata albarka da zuria baki daya.” “Amin” Asma ta fada jikin ta a sanyaye, don harga Allah tanajin zafin abin da Hajjajo kewa yahh !!! A sanyaye ta fita daga dakin.

“Gaskiya abinda kike bakya kyautawa, karki manta, duk kiyayyarki da ita anzama daya. Sannan tsakani da Allah menene laifin yarinyar nan ? Kyauta tawa ba irin wanda bata miki, tamafi miki biyayyah akan sauran surukan naki.”

Shiru Hajjajo tayi bata ce mata komai ba.   In da sabo ta saba,. Ta rasa irin wannan kiyayyah, kullun tana mata nasiha amma bata dauka, indai akan yahh ne.

“Abu daya zan gaya miki kamar yadda nasaba fada, Ki daina nuna kiyayyarki gaban yaran nan, Duk son da suke miki, sun fi son uwarsu a kanki. Ki duba ki gani, yaushe rabon da inga su zaid a gidannan ? Har na manta Ina gudun rabuwar kawunan jikokin ki ? Ita kanta Asmaun yadda kikayi, bata ji dadi ba, har fuskarta ta gaza boyewa.”

                     *************

Sun shiga gidan su nasma, da sallama dakin hajiya suka fara zuwa suka gaisheta sannan suka wuce dakin su nasma.Kwance take a kan gado, tana karanta wani hausa novel. Sallamar su yasata dagowa da sauri, a guje ta tashi ta rungumo su. “Kai amma kun kyautamin, yan zunnan muka gama hiran ku da ziyyah.” “Amarsu kina hutawarki wallahi.” Cewar Hafsat.

“Me yafi raina” ta fada tana fari da ido. “Babu kam matar uncle, ci karenki ba babbaka.” “Adai babbake kar haramcin yayi yawa.” Ta fada tana dariya. “Bassimillan ku ku zauna.” Ta kawo musu ruwa, da kunun ayah.

Asma tace, “baki da kirki, sai kawai muga invitation bayan bamu da labarin komai.” Ta rike haba tana yatsina baki, kudai bari kawai, ni kaina abin a sama yazo min,Don har na hakura dayake matar mutun kabarin sa, Last week kawai baba yakirani, cewar sun amince da zabi na har an tsaida rana.”

“Allah sarki uncle Allah kadai yasan halin da ya shiga, da aka hanashi ke wancan karon.” “Oh !!! Ni baku tausaya min ba kenan?” Ashty ta dungureta “so saima muka tausaya muku.” “Alhamdulillah tunda komai yayi normal.” In ji Hafsat.

Uncle muhd kanine ga umma. Asalin su inyamurai ne, Daga Anambra state. Kasuwanci ya kawo baban su (okonko) zaria. A nan suka girma, asalin sunan ummi fatima, Abigel sai emeka (uncle muhd) sai autar su chioma, Sunan mahaifiyar su emu.

Abigel ta karbi musulun ci, saka makon haka iyayenta suka kore ta.

Zaman ta ya dawo gidan sheikh sani mausa. Wanda shi ya bata kalmar shahada, Sheikh mausa da sheikh gyambu abokaine sosai, Zamanta a gidan sheikh mausa yasa ya kula da kyawawan dabi unta, Shine ya shawarci amininsa gyambu da son aurad da ita ga daya daga cikin dali bansa, Nan take sheikh gyambu ya nuna yana da bukatar aurenta, in dai har abokin nasa ya yadda da ingancin ta.

Abigel( fatima) tayi na’am da zabin uban gidanta, Cikin lokaci kan kani akayi auren su…..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *