KAWUNA
CHAPTER 2
“Suhailat! dube ki ,kina da kyau,kina da tsari kina da ilimi ,kina da komai. inaso kiyi haƙuri kina sona ni kuma ƙawarki nake so!”
Sir Salman ya ida maganar sa yana mai nuni da Abeedah.Kafin ya cigaba da cewa
“Tabbas ita nake so.Kuna kallon a banza na sake da ƴan ajin ku,ina hira da dariya da su?ba dan komai ba sai dan nasa Abeedah a cikin farin ciki.Saboda na fuskan ci tana cikin wani hali na rayuwa ”
Ya cigaba da cewa cikin kakkausar muryar sa:. “Ke Suhailat mai taimaka mata ce ta samu farin ciki a rayuwar ta ,kuma dalilin yanda na sake da ku ni kaina nasan Abeedah ta samu farin ciki .Dan haka kiyi haƙuri ni ƙawarki na ke so.”
Sir Salman ya ida maganar sa yana duban Abeedah dan ganin yadda zata amshi maganar tasa.
Suhailat kuwa hankalin ta yayi mugun tashi yanzun dama duk sakewar nan da Sir Salman yayi da su dan kawai Abee yayi? dama Abee yake so ba ita ba? Ya yake so tayi da Soyayyar sa a cikin zuciyar ta? Mai yasa zuciyar sa zai so ƙawar ta kuma Aminiyar ta?”
Duk wa’innan tarin tambayoyin Suhailat ta gaza mai bata amsar su .Miƙewa tayi da sauri tabar cikin office ɗin .Abee kuwa daskarewa kawai tayi a wajen tama kasa sanin abin yi.
“Wannan wani kalan abu ne?mai yasa Sir Salman zai mata haka?”
Kallon sa tayi rai ɓace za tayi magana ta kasa saboda tsananin kwarjinin data ga Sir Salman ya yi mata .Ƙirjinta taji ya buga saurin sadda kan ta ƙasa yayi shi kuwa Sir Salman ya kanne mata ido ɗaya.
Miƙewa tayi itama tabar masa cikin office ɗin, wuce tayi wajen da ta san zata ga Aminiyar ta.
Chan wajen da Suhailat tayi parking motar ta Abee ta iske ta .Ƙaraso wa tayi jikin ta duk amace ,iske Suhailat ɗin tayi tana ta gurzan kuka kaman ranta zai fita.
Taɓa ta Abee tayi kafin ta shiga lallashin Suhailat ɗin tana bata baki
“Suhailat dan Allah kiyi haƙuri”
Sosai Suhailat ke ƙaunar Abee ta san ba laifin Abee ba ne kawai son rai ne irin na Sir Salman shi yasa yayi mata haka.Tsagaitawa daga kukan Suhailat tayi cikin muryar tausayi ta ce:
“Yanzun ya kike so nayi Abee? Ni ina son shi amman shi yace ke yake so Abee,ni kuma banajin zan iya kishi da shi da wata a rayuwata ba”!
Suhailat ta cigaba da cewa
“Kiyi haƙuri Abee ki bar mun Sir Salman tunda shi har yace yana son ki.Dan Allah kije ki same shi ki fahimtar da shi irin soyayyar da nake yi ma shi”
Suhailat ta ida maganar tana share hawayen daya gama ɓata mata fuska .
Sosai tausayin Suhailat ya kama Abee mai ya kamata tayi ?ta ya zata iya fahimtar da Sir Salman irin soyayyar da Suhailat ke yi masa?”
Bata kai ga bawa kan ta amsa ba ta tsinkayo muryar Suhailat ɗin cikin sauri sauri tana cewa:
“Abee kizo muje wurin Malam Idris na hotoro ai ance yana *duba* muje ya duba mana wannan al’amarin .”
Suhailat ta ida maganar tana jiran jin abin da Abee za tace.Shuru Abee tayi kaman wacce ke nazari ,chan kuma ko tunanin mai tayi? Allahu a’alam ta kalla Suhailat ɗin wacce ta kafe ta da idanuwanta tace:
Story continues below

“Shikenan muje ɗin kawai”
₦
Ba tareda Suhailat ta kuma jiran wani abu daga wajen Abeen ba ta kunna motar ta suka bar harabar makarantar.
*Hotoro*
Abee da Suhailat zube a gaban Malam Idris Wanda suka gama faɗin ma abin da ke tafe dasu .
Shuru Malam Idris yayi kafin ya zuba ƙasa ya shiga dudduba al’amarin nasu.Bayan ya gama dube duben sa ya ɗago ya kalle su yayi gyaran murya kafin yace :
“Toh ai da rabo a tsakanin ki da shi!”
Ya ida maganar yana nuni da Suhailat ,kallan junansu Suhailat da Abee su kayi ,kafun suka ƙara mai da hankulan su kan Malam ɗin.
Idan shi kuma ya cigaba da cewa:
“Tabbas akwai rabo tsakanin ki da wannan lakcaran Suhailat ,kuma duk wanda yayi ƙoƙarin raba wannan rabon dake tsakanin ki da shi toh wallahi zai iya mutuwa .Ni Idris na faɗa maki akwai rabo tsakanin ki da wannan lakcaran ,duk wulaƙancin da zai miki yayi ya gama sai kin aure shi “.
Cike da mamaki Abee da Suhailat suke kallon Malam ɗin babu abin da suke hangowa a fuskar sa face iya kar gaskia da ya gama faɗa masu.
Waiwayowa Suhailat tayi ta kalla Abee wacce itama a dai dai wannan lokacin Suhailat ɗin take kallo . Murmushi Suhailat ta sakar mata kawai.
Godiya suka yi ma malam kafin suka miƙe suka fito.A cikin mota Suhailat ta kalla Abee sannan tayi ƴar dariya kafin tace:
“Toh Kin gani fa ance rabon dake tsakanina da Sir Salman zai iya kashe mutum.Daki kashe kan ki a banza Abee ba gwara kiyi haƙuri ba? karki amshi tayin Soyayyar Sir Salman.”
Suhailat ta ida maganar tana ɗan satan kallon Abee wacce duk jikinta ya gama mutuwa.Har ga Allah ko a baya Sir Salman na burgeta a cikin zuciyarta.
kawai zafin kan sa ne a wanchan lokacin yasa tayi yaƙi da zuciyarta a kan cusa Sir Salman ɗin cikin zuciyarta .
tun kafin ma tasan da Soyayyar da Suhailat keyi masa ɗin.Amman a yanzun da ya sake dasu sai ta fahimci cewa yanada kirki ,sosai yake burgeta ,bata nunawa ne kawai.
Ganin Abee bata da niyyar tanka mata yasa Suhailat cigaba da cewa:
“Ki koma kije ki fahimtar da Sir Salman,kije ki ce masa ina son sa ,kuma ni zai aura”.
A daidai nan Suhailat tayi parking motarta a harabar makarantar.
Ta kalla Abeen tace:”Kije ina jiran ki”
Ita kuma Abee kaman wata raƙumi da akala ta fito daga cikin motar ta wuce offishin Sir Salman taje ta sameshi.
Da Sallama ta shugo cikin offishin,yana zaune yana shan coffee.Amsawa yayi fuskar sa a sake kafin yace:
“Hummm my baby ya a ka yi?”
Ɗan ɓata rai Abee tayi kafun tace :
“Ummm ni kadaina cemun my baby ai ƙawata itace take son ka ,kuma tace na zo na fahimtar da kai wallahi tana son ka.
Bata iya bacci saboda kai,komai nata Sir Salman kowa da komai a wajen ta Sir Salman.Dan Allah ka tai maka ka so ƙawata wallahi ba zaka sameta da wani matsala ba”.
Sai da ya barta takai a ya kafin yaja dogon lumfashi ya lumshe idanuwansa ya buɗe ya zuba su a kan ta.
Kafin yace :
“Wow! dama haka kika iya tsara zance? haka kike mun faɗa mun ? Kina kasa bacci saboda ni ?”
Gani tayi ya miƙe daga mazaunin sa ya zo daf da ita ya tsaya kusa da ita.
Ƙamshin turaren sa ne ya daki hancinta.ta shaƙa daddaɗin ƙamshin sa,nan da nan taji kasala na saukar mata.
Ganin haka yasa Sir Salman kuma matsowa kusa da ita kaman zai rungumeta.
ya sassauta muryarsa ya fara mata magana cikin wata irin kasalalliyar murya ,da ita da shi duk sai da jikin su yayi sanƴi .
Yace :”kai baby naji daɗin ganin ki anan gurin .kaman kin sa cewa tunanin ki nake yi”
Ganin Sir Salman na naiman sata shiga cikin wani irin ya nayi yasa Abee saurin ja da baya cikin sanƴin murya tace :
“Malam dan Allah kayi haƙuri ka matsa”!
Ta ida maganar tana lumshe idanuwanta sannan tana jin wani irin baƙon ya nayi na shigar ta.
Kuma matsowa kusa da ita yayi cikin husky voice ɗin sa yace:
“Na matsa a ina? Ina zan matsa? ce maki nayi zan taɓa ki?ko nace zan rungume ki ne?”
Ya ida maganar yana kallan yanayin da tashiga .
Abee mamakin Sir Salman kawai ta shiga yi.talura shi mutum ne ɗan ɓaro ɓaro bai jin ƙunƴar faɗin duk abin da yayi niyya.
Ya cigaba da cewa:
“Toh idan nace ma zan rungume ki akwai wanda ya isa ya hana?”
Ay kawai sai ya ƙara matsowa daf da Abee har jikinsu na gugan na juna .
Saurin matsawa baya tayi tana ƙiƙƙifta idanu . murmushi yayi ganin duk tana son ruɗewa cewa yayi:
“Ke wasa nake maki ,kwantar da hankalin ki bazan maki abin da ranki baya so ba”
Sai anan Abee ta ɗan saki lumfashi kafun tace:
“Ni ina gaya ma wallahi ƙawata tana son ka…….
Saurin katse ta yayi ,cikin ɗaga murya yace:
“Keeee! rufe mun baki fita ki bani guri .Dan kinga na sake dake ina magana shine zaki zo kina mun maganar ƙawarki? Ni ke nake so .Fita nace ”
Sir Salman ya ida maganar sa yana nuna ma Abee hanƴar ƙofa.a ɗan tsorace Abee ta raɓa ta gefen sa zata tafi taji muryarsa yana cewa:
“Kinga zo nan dawo”
Satan kallon sa tayi ganin babu alamun wasa a tattare da shi ya sata dawo wa ta tsaya .
Yace…….
Sir Salman cikin sanƴin muryar sa ya ce :
” Mai kika iya?”
Kallon sa Abee ta yi cikin mamaki ta ce :
“Na mai?”
Murmushi ɗauke a fuskar shi ya ce :
“Wani irin girki ki ka iya ?”
Kallon sa Abee ta yi ta na mamakin sa kafin ta ce :
” Taliya da manja”
Ta ida maganar ta na sadda kan ta ƙasa . Sir Salman ya ce :
“Hummm uhumm abin da na za ta kenan , taliya da manja.Da kyau taliya da kuma manja!”
Ya ida maganar ya na mai jinjina kan sa .Ganin bai da niyyar sake cewa komai ya sa Abee juyawa don tafiya.
Muryar sa ta kuma tsinkayowa ya na faɗin
“Kee na ce kizo na ce maki ki tafi ne?”
Tsayawa cak Abee ta yi ta na mamakin Sir Salman “wannan wani irin mutum ne wai,yake mata gadara ? ga shi ta na jin nauyin shi ballantana ta yaɓa mai magana.”
Abee ta raya hakan a cikin ranta.Waigowa ta yi ta na sauke idanuwanta a kan sa ,shuru Sir Salman ya yi kafin ya ce :
“Ummm ki dafa mun dambu da man shanu.ƙarfe bakwai na yamma yau zan zo zance gidan ku ,ki dafa mun dambu da kunun zaƙi.Ba kunun aya bafa na ce kunun zaƙi na ce mai sanƴi kin ji?”
Ya ida maganar sa ya na mai kafe Abee wacce tsananin mamakin sa yake bayyane a saman fuskar ta. Tsintar kanta ta yi ta na mai gyaɗa ma sa kai alamun toh.
Murmushi mai narkar da zuciyar duk wanda a kayi wa ,Sir Salman ya sakin ma Abee.
Kafin ya ce :
“Jeki sai nazo”
Saurin juyawa ta yi dan barin offishin na sa a hanzarce.
Dogon lumfashi Sir Salman ya sauke ya na mai jin tsananin soyayyar Abeedah a dukkanin gaɓoɓin jikin sa.A hankali ya furta ” Allah ya bani ke Abee na san za ki SO ni very soon dan ina hango hakan a cikin kwayar idanuwan ki”
Ya ida maganar sa ya na mai koma wa mazaunin sa dan ci gaba da marking takardun ɗalibai.zuciyar sa cike da begen Abee ji yake ina ma su dawwama su ka ɗai a cikin offishin haka.
Abee kuwa ta na fita daga cikin offishin babu in da ta zarce sai kwanan da Suhailat ta faka motar ta .Jefi jefi sauran ɗaliban jami’ar ke tsayawa su na hausawa da Abee kowa ya ganta sai ya tsaya ya ce ma ta “ha’a ta malam ta malam sannun ki “
Murmushi kawai take yi ma su wasu kuma ta amsa ma su da “yauwa”
Da yake tun ranar da Sir Salman ya mata kyautar waya ɗaliban makarantar ke tsokanar ta hanƴar ce ma ta *ta malam ta malam*.
Ta na zuwa wajen Suhailat ɗin ta rasa abin da za ta ce ma ta.Ga shi dai tura ta ta yi taje ta ce mai ta na son shi ,shi kuma ya ce ma ta zai zo gidan su yau ya kenan za ta yi ? mai za ta ce ma Suhailat?
“Kin yi shuru ya a ka yi ki ka daɗe?”
Suhailat ta katse Abeen,Kallon ta Abee ta yi kafun ta ce:
Story continues below

“Ya ce zai yi nazari a kai”
Ta tsinci kan ta da faɗin hakan.Gyaɗa kai kurum Suhailat ta yi sannan ta tayar da motar ta suka bar harabar makarantar. ba mai ce ma kowa uffan har Suhailat ta sauke Abee a gidan su itama ta kama hanyar gidan su.
********************************
“Mancy ni kam muna da nikaƙƙiyar shinkafa ko?”
Dubanta Mancy ta yi kafun ta ce :
“Ka man da a kwai ragowar wanda na ma Abbin ku dambu kwanaki”
Gyaɗa kai Abee tayi sannan ta miƙe ta wuce kitchen.
Abubuwan da zata buƙata dan yin dambun ta fitar,bayan ta kammala komai ta soya man shanu ta sa mai dambun da ya ji kayan haɗi cikin kula ta haɗa komai cikin tray ta fito daga kitchen ɗin hannun ta riƙe da tray ɗin da ta jera komai a ciki.
Da Sallama ta shugo falon Mancy da Farhana da Haris suna zaune suna kallon MBC DRAMA .
Amsa ma ta su ka yi suna kallon tray ɗin da ke hannunta .Kallon su ta yi kafun ta ce :
“Baƙo zan yi Mancy shi ne na ɗan girka mai abin da zai sa a baki ”
Kallon ta sosai Mancy ta yi dan Abeedah tun da suke da ita basu taɓa jin wani ya yi sallama ya zo naiman ta ba,dan bata kula samari sam a cewar ta basu gaban ta.
Cikin mamaki Mancy ta ce :
“Baƙo kuma?”
Gyaɗa kai Abee ta yi ta ce :”E. Mancy baƙo”
Shuru kawai Mancy ta yi ba ta kuma cewa uffan ba.Abee ta wuce ɗakin su ta dire tray ɗin a ƙasan kafet na ɗakin ta na faɗin “wash Allah na ! komai dalilina nayi masa abincin nan ma?oho mun mutum da ma ko gidan mu bai sani ba mtswww mai yasa ma wai na biye ma zuciyata har na yi girkin? In Suhailat ta zo ta gane fa?”
“Sai mai in ta gane?”
Zuciyarta ta watsa mata tambayar .Shuru Abee ta yi ta kasa sanin abin yi miƙewa ta yi ta fito falon ya miƙa ma Farhana 200 ta ce :
“Fareee miƙe jeki gidan maman Abiddin ki siyo mun kunun zaƙi mai sanƴi ki kawo mun ”
Amsa Farhana ta yi sannan ta miƙe dan zuwa aiken yayar ta.Koma wa cikin ɗakin Abee ta yi ,bayi ta shiga tayi wanka ta ɗoro alwala ta fito sai zuba ƙamshin sabulun wanka take.Sallan mafarkin ta kabbara bayan ta gama ta shirya cikin wani baƙin a baya yayi matuƙar yi mata kyau abinka da farar mace baƙi na matuƙar amsar su.
Ta rasa mai ya sa take jin ɗaɗi na ratsata ,ta rasa mai yasa zuciyarta ke matuƙar son ganin Sir Salman yana mata wannan murmushin nasa mai narkar da zuciya .ringing ɗin wayar ta ce ta ƙatseta daga tunanin da ta faɗa .
Miƙa hannun ta yi ta ɗauki wayar ganin baƙuwar lambace ya sa ta sharewa ta a jiye wayar .Shigowan saƙo taji a cikin wayar hakan ya sa ta ɗauka dan ganin saƙon , mamaki shimfiɗe a fuskar ta take karanta saƙon “My baby ki fito ina waje tunda kin ƙi ɗaga wayata”
Ta yi bitar saƙon yafi a irga mamakin yadda a kayi Sir Salman keda lambar ta kawai take yi . Ganin ba ta da amsar tambayar yasa ta miƙewa da sauri taje gaban madubi tana ƙare ma kan ta kallo ta matuƙar yin kyau sosai dan Abee budurwa ce kekkyawa ta bugawa a jarida .
Turare ta ɗan fesa kaɗan sannan ta zira takalmin ta fito.
Mancy ce ta kalleta taga sai zuba murmushi take, duk yadda za’ayi wanda yazo wajen nata mutum ne mai matuƙar muhimmanci a gurin Abeedar dan a yadda ta san ƴar ta macece mara hulɗa da Samari.
“Mancy bari naje wai ya iso”
Mancy ta ce :
“Shin Abeedah gurin wa za kije ?waye shi ?mai ya kawo sa gidan nan da dare haka?”
Story continues below

Mancy ta dire maganar ta ,ta na mai kafe Abee wacce duk kunƴan Mancy ya gama rufe ta dole Mancy ta jero mata irin wa’innan tambayoyin dan basu taɓa ganin ta yi hakan ba dole abin ya bata mamaki.
Murmushi Abee ta yi kafun ta ce :
“Mancy lekcaran mune na makaranta shi ne ya ce mun zai zo gidan mu yau ”
Mancy ta ce :”Lekcaran ku?toh mai haɗin ki da lekcara Abee har zai kawo maki ziyara cikin dare? Soyayya kuke yi ne?”
Saurin rufe fuska Abeee ta yi kafun tayi saurin miƙewa tayi hanƴar ƙofa tana faɗin:
“Mancy dan Allah ki bari zan amsa maki tambayoyin ki anjima”
Mancy ta gyaɗa kai kurum ta ce :”toh ,Farhana miƙe ki zuba mata kunun zaƙin cikin jug”
Miƙewa Farhana ta yi dan aikata umarnin mahaifiyar su .
***********************+********
Can ta iske motar shi a fake ,cikin jin kunƴa Abee ta ƙara so wajen motar ta tsaya cak ba tareda ta yi komai ba.zuge glass ɗin motar yayi kallan ta ya tsaya yi tun daga sama har ƙasa sai ya ga hijab na matuƙar ɓoye kyawun ta.
“Emmata ba zaki shi ga cikin motar mijin naki bane?”
Da sauri Abee ta ɗago ta na duban sa a hankali ta ce :. “miji?”
Da girar sa ya amsa mata alamun yes .Murmusawa kawai Abee ta yi dan ta kasa sanin dalilin da yasa take jin Sir Salman a cikin ranta bayan tafi kowa sanin yadda ƙawarta Aminiyar ta ke mutuwar son shi,anƴa kuwa abin da take yi daidai ne kuwa?
Ba ta kai ga baiwa kanta amsa ba taji muryar sa a kusa da ita da sauri ta waiwayo tana kallon sa tana mamakin yaushe ya ƙara so wajen ta?
“Kin yi kyau miss Abeedah usman ɗambatta”!
Ya na yin yadda ya kira sunan ta in full sai da tsigar jikin ta ya tashi .Dogon lumfashi ta ja kafun ta ce ma sa “muje ciki Sir”
Gyaɗa mata kai kurum yayi dan ya lura da irin ya nayin da yarinyar ta shi ga a ran sa ya ce :
Ya ida maganar yana sakin wani irin murmushi wanda ya barwa kansa sanin ma’anar sa.
Ko da suka shiga cikin gidan su , a tsakar gidan su Abee ta shimfiɗa mai tabarma ya zauna yana ta binta da kallo wanda Abee ta kasa fassara ko na mainene.Abinci ta gabato mai bayan ya ci yayi nak ya ɗago ya saci kallon Abeee wacce itama shi take kallo ya nayin yadda yake cin abincin sa a natse yaji hakan ya matuƙar burgeta.
Murmushi ya yi kafun ya ce:
“Wow yarinƴar nan kin iya girki,ki ce inna aure ki na huta.”
Ya ida maganar sa ya na mai lumshe idanuwansa kafin ya ci gaba da cewa”kin san abin da na ke so? Idan na gama cin abinci in mu kayi aure in kwanta kizo ki ta mun tausa”
Saurin kallon sa Abee tayi a cikin zuciyarta ta ce :”dama wai yana magana har haka?”
“Ummm yarinƴa in mu kayi aure ba zaki riƙa samun hutu ba,kullum muna maƙale da juna a cikin ɗaki muna jin ɗumin juna”
Zare idanuwanta waje tayi tana masa kallon mamaki yanda ya zaƙe ya na ta mata magana kamar ɗan iska abin ya mugun ɗaure mata kai dama wai haka yake?
Shine tambayar da take ma kanta wanda ta gaza samun amsoshin su.
Sallaman Abbi ne ya ƙatse Sir Salman daga shauƙin kalaman da yake furta wa Abee.
Da mamaki Abbi ke kallon su namiji a tsakar gidan sa kuma da alamu wajen Abeen sa ya zo?
“Inawuni Baba ”
Sir Salman ya katse Abbi daga tunanin da ya faɗa “lfy lau”
Abbi ya amsa a taƙaice sannan ya wuce ya shiga cikin falan gidan.
Sir Salman ya kalla Abee wacce tun ɗazun ta kasa ɗagowa su haɗa ido tsaban kunƴar da kalaman sa ke mata.
“Ki mun iso wajen baba inason yin magana da shi”
Sai a sannan Abee ta ɗago suka haɗa ido da sauri ta kauda idanuwanta gefe kafin ta ce :”magana kuma?”
“Eh magana” ya bata amsa a taƙaice
Ba ta san dalilin da yasa sam zuciyarta ba ta son yi wa Sir Salman musu sam.
Miƙewa tayi ta na mamakin kanta sai ka ce ba Abeedah ba ,sam ta soma canzawa .
******************************
Bayan sun gama gaisawa da Abbi Sir Salman ya waiga ya gaida Mancy wacce ta kafe sa da idanuwanta kaman mai son gano wani abu a tattare da Salman ɗin .
Gyaran murya Sir Salman yayi a hankali kafin ya ce :
“Baba ni fa da gaske ina son Abeedah kuma soyayya irin wacce zata kai mu ga yin aure .Inaso ka yarje mun na turo iyaye na ”
Shuru Abbi yayi Mancy kuwa ta ma kasa sanin abin ce wa tun ɗazun in banda kafe Salman da idanu da ta yi .
Abbi ne ya nisa kafin ya ce
Girgiza kansa Abbi yayi haɗe da sauke ajiyar zuciya a hankali yace
“Toh ma sha Allahu abu yayi kyau,ina so ka bani lokaci nima in ɗan yi shawara a kan maganar.kasan maganar aure ba abu bane mai sauƙi Allah ya zaɓa mana abin da ya ke alkairi, Mungode Allah yayi jagora ”
Abbi ya miƙe haɗe da miƙowa sir Salman hannu. “Zan shiga ciki ka gaida manyan naka”
Sunkuyar da Kai sir Salman yayi ya amsa da “zasuji Abba nagode sosai Allah ya taimaka”
Daga haka Abbi ya sa kai ya shige uwar ɗaka.
Sir Salman ya ɗago kan sa suka haɗa ido da Mancy ,murmusawa kawai ya yi dan ya rasa dalilin da ya sa take ta kallon sa tun shigowar sa cikin falon ya lura da hakan.
Miƙewa ya yi kafin ya ce:
“Mama sai da safen ku”
A hankali Mancy ta ce :”Allah shi kaimu a gaida mutanen gida”
Gyaɗa kai kurum Salman ya yi kafin ya sa kan sa ya bar falon.Tsaye ya gan ta bakin ƙofar tsakar gidan ,da murmushi a saman fuskar sa ya ƙara so wajen nata .
“My baby muje na tafi ko?”
Kallon shi Abee ta yi kafin ta ce:
“Baka faɗimun maganar da ku kayi da Abbi ba”
Murmushi ya yi ya ce : “oh my baby so kike ki ji mai muka tattauna a kai?”
Gyaɗa kai tayi alamun eh
” Ok ok toh ki bari gobe zan faɗa miki a makaranta”
Far da ido Abee ta yi kafin ta ce : “Sir makaranta kuma?”
“Uhumm nan fa ko a club ki ka ji na ce?”
Saurin gyaɗa masa kai ta yi alamun a’a murmushi ya yi ya ce :
“Good girl shiga ciki na yafe rakiyar take kia i love u”
Juyawa tayi ta shiga ciki sai da ya tabbatar ta shiga ciki sannan ya sa kan sa ya fita a gidan gaba ɗaya.
****+*++*+*++*++**++*+++++*
Shuru Abee tayi bayan Abbi ya gama zayyane mata dukkanin maganar da su kayi da Salman .
Ni sawa Abee tayi kanta ya matuƙar ƙullewa Abbi ne ya katse ta da faɗin
“Abee ki na son sa?”
Saurin kallon Abee Mancy tayi dan jin amsar da zata bawa Abbi .
Har yanzu ba ta rigada ta gama tantance ko son Sir Salman take ko kuma a kasin haka ? Ta dai san sosai zuciyarta ke mugun son ganin ta kasance tare da Sir Salman amman Suhailat fa?in tama Suhailat haka ta san bata kyauta mata ba.
Miƙewa kawai Abee tayi ba tare da ta bawa mahaifinta amsa ba.Dukkanin su da ido suka bita barin ma Mancy wacce duk hankalin ta bai kwanta da Sir Salman ba tana hango wani abu a tattare da shi wanda in har hakan ya tabbata ba tajin cewa auran su zai iya yuwa da Abee .
Story continues below

********^****************************
Daren ranar kasa bacci Abee tayi ganin tunani bazai amfana mata komai ba ta miƙe ta ɗoro alwala ta shimfiɗa sallaya ta fara gabatar da nafila dan naiman a gaji wajen Ubangijin sammai da ƙasai wanda shi kaɗai zai iya magance ma bawa dukkanin wasu buƙatunsa.
Washegari
Abee ta gama shirinta tsaf ta fito dan zuwa makaranta wanda a yau zasu duba sakamakon su .
Mancy da Farhana zaune a falo suna yanka alayyahu suna hira , murmushi Abee tayi kafin ta ƙara so wajen su ta na faɗin
“Mancy ki shigar da ƴarki makarantar koyon ɗinki zaman ta gida haka bana jin daɗin sa tunda kafin ta yi joining jami’a zai kai nan da wata uku”
“Aiko Anty Abee nima nayi wannan tunanin” Farhana ta bata amsa.
Jinjina kai Mancy tayi kafin ta ce : “hakan na da kyau sosai bari Abbin ku ya dawo sai musan abin yi”
Murmushi Abee tayi kafin ta ce ” toh nidai na tafi sai na dawo”
“A dawo lfy” Mancy da Farhana suka amsa mata a tare.
*************************************
Abeedah da Suhailat zaune a restaurant suna cin abinci bayan sun dawo daga duba result ɗin su,Alhmd duk sunyi passing dan dasu za’a shiga level 3 .
Abeedah ce ta nisa kafin ta kalla Suhailat ta ce :
“Suhay niko kina ganin ba ƙarya wannan malamin ya mana ba?”
Ɗagoda manƴan idanuwanta Suhailat tayi kafin ta sauke su a kan Abee ta ce :
“Ƙarya kuma?mai ya sa zai mana ƙarya Abeee ?kin fara son Sir Salman ne shin?”
Ni sawa Abeedah tayi sannan ta ce :
“A’a nidai mu canza muje gurin wani malamin ya mana Istikara bawai duba ba dan babu kyau gwara Istikaran shi ɗin ma anfi son mutum yayi da kansa”
Murmushi kawai Suhailat tayi kafin ta ce :
“Ok babu matsala kina da wani malamin muje wajen na sa ?dan ni na hotoro kawai na sani ”
Gyaɗa kai Abee tayi “Akwai Malamin Mancy shi ya ke mata rubuta tana sha kwanakin baya da tayi wannan rashin lafiyar.ina gani muje wajen sa”
“Okey muje toh kawai” Suhailat ta amsa mata.
Miƙewa su kayi a tare suka wuce wajen da Suhailat tayi parking motar ta suka shiga suka bar harabar makarantar.
********************************
Malam Muhammad Kabir ya dube su ɗaya bayan ɗaya sannan ya yi gyaran murya ya ce :
“Ma sha Allah sakamakon da Istikara ta ya bani shine tabbas akwai rabo tsakanin Suhailat Yusuf da Salman Ibrahim ɗambatta!”
Saurin kallon sa Abee tayi bakin ta na rawa ta ce :
“Malam Salman Ibrahim ɗambatta ka ce?”
Gyaɗa mata kai ya yi ya ce : “haka naga sunan ko Akwai wani Matsala ne?”
Saurin girgiza kai kurum Abee tayi .tana mamakin yadda a kayi sunan su yayi kamaceniya “Salman Ibrahim ɗambatta?”
Abee ta ruƙa nanatawa a cikin zuciyarta kenan Sir Salman ya nada connection da su kenan? Anƴa kuwa?dole ta yi bincike a kai ƙilan Sir Salman shine silan wanzuwar sanin Asalin su .Amman mai ya sa baya amfani da dmbatta a sunansa dan Salman Ibrahim kawai ya ke amfani. Anƴa kuwa babu wani abu a ƙasa kuwa?
Abee ta ruƙa tambayar zuciyarta .
Malam Muhd ne ya ƙatseta in da ya ci gaba da cewa
“Rabo ne wanda idan a kayi yunƙurin raba shi mutum ka iya rasa ransa.saboda rabone mai ƙarfi akwai zuriya amman fa akwai cakwakiya kafin a yi auren”
Malam Muhd ya dire maganar sa .
Hankalin Abeee in yayi dubu ya gama tashi ita kuwa Suhailat daɗi kaman ya kasheta.
Sallama su kayi wa malam Muhd sannan suka wuce .
A cikin mota kuwa rasa mai cewa ɗan uwansa uffan a kayi .Abee dai tana can duniyar tunanin inda zata fara dosa shin zata fara bin ciken waye Sir Salman ? Ko kuma yaƙi da zuciyarta za tayi a kan cusa soyayyar Sir Salman da take niyyan yi mata shi farat ɗaya? tunda har malamai biyu sun faɗa magana iri ɗaya tasan cewa tabbas Suhailat Sir Salman zai aura sai dai kuma in wani al’amarin Allah ne ya canza hakan .toh ita kuma fa ya zata yi ?Sir Salman zai dai na son tane ko kuwa?in kuma ɗan uwan ta ne wani kalan ƴan uwan taka suke sharing? ”
Maganar da taji Suhailat na yi ne ya sata saurin waigowa tana kallon ta.
Daka kalla Suhailat zaka san cewa tana cikin nishaɗi da jin daɗi sai murna take tayi tana faɗin
“Wallahi Sir Salman dole ka aure ni,ko kana so ko baka so.Ko ban maka komai ba dole sai ka aureni ! Bama asiri kai da kan ka zaka zo ka aure ni ,saboda an rigada ance akwai rabo tsakanina da kai”
Suhailat ta ida maganar tana dakan sitiyerin motar cike da jin daɗi.Abee kuwa hankalin ta ne taji ya mugun ta shi.
********************************
Bayan ta kammala sallan la’asar ta fito ta soma taya Mancy aiki suna zaune su Uku a tsakar gidan su jefi jefi suna hira kowa da aikin da yake yi a gaban sa Abee ta nisa kafin ta waigo ta saci kallon Mancy sannan ta ce :
“Mancy!”
“Ummm Abee” Mancy ta amsa mata
Ni kuwa Mancy mai sunan mahaifin Abbin mu?
Ɗagowa Mancy tayi tana kallan Abee kafin ta ce “mai ya sa kika mun wannan tambayar?”
Murmushi Abee tayi ta ce : “Mancy dan Allah ki amsa mun ya sunan kakan mu?”
Shuru Mancy tayi kafin ta nisa ta ce :
“Toh zan faɗa maki.Sunan sa….
Girgiza kanta Mancy tayi haɗe da sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce
“Bello ɗambatta shine sunan sa”
Abee ta ce “Mancy ya na da yaya ko ƙani mai suna Ibrahim ɗambatta?”
Cike da zaƙuwa a kauda maganar Mancy ta ce “A’a shi kaɗai ne a wajen iyayen sa.Abee tambayoyin sun isa haka.”
shiru Abee tayi tana son sake tambayar Mancy wani abun tana jin tsoro don tasan tabbas bazata amsa mata ba.
“Ko dai kamanceceniyar sunane kawai a tsakanin su da Sir Salman?”
Shine tambayar da ta kasa samun amsar shi .
********************************************
Kwanaki na ta shuɗewa ranaku na ta tafiya har Allah cikin ikonsa ya dawo dasu hutun session lafiya, kowa na cike da farin cikin sake shiga wani matakin karatu .(next level)
A wannan gaɓar kuwa Suhailat da Abee babu wani abu da ya ragu ko ya ƙaru a cikin ƙawancen su ,ta ciki na ciki kawai, soyayyar Sir Salman kuwa na daɗa fisgar ko wacce a cikin zuciyarta.
Abee na yiwa sir salman wani irin so da bata san lokacin da ta fara yi masa shi ba, Sosai take kaunar sa har cikin ranta .
Tafe suke a cikin motar Suhailat. Gidan su taje ta daukota dan zuwa makarantar tare, a bakin gate ɗin makarantar Suhailat ta tsayar da motar sa’annan ta juyo ta kallo Abee dake zaune a gefen mai zaman banza ta ce ” Kinga sauka ki shiga ciki Abee, ni yau bazan shiga makarantar ba tunda bamuda lecture ɗin Sir Salman, dama saboda shi nake zuwa makarantar, yau kuma ko keyarsa na san bazan gani ba tun da bayada lecture.”
Kallonta Abee tayi ba tare data ce mata uffan ba ta saka hannunta ta buɗe ƙofar motar ta fita, Mayar da kofar motar tayi ta rufe ba tare da cewa komai ba, bayan ta rufe kofar motar Suhailat taja motarta ta barta a bakin gate din makarantar. Dogon Numfashi Abee ta ja tana mamakin Suhailat.
Da shigarta cikin makarantar tayi kicibis da Ƙawarsu Hayfa itama zata shiga department ɗin su, Saurin karasawa tayi wurin Hayfar tana murmushi ta ce “Hayfatu.” Waigowa Hayfa tayi don ganin wanda ya kirata, ganin Abeey yasa itama sakin murmushi ta ce ” Abeen Mu ya kike? ina Suhailat yau fa?”
“Bata jin daɗin jikinta ne shiyasa bata sami damar zuwa ba.” Abee ta bata amsa, Murmushi Hayfa tayi a hankali ta ce ” Ayya! Allah ya bata lafiya.”
Abee ta amsa da “Ameen”
Jerawa su kayi a tare dan shiga department ɗin na su.ja tayi ta tsaya Hayfah ta waigo ta kalle ta kafin ta ce
“Lafiya Abee?”
Shiru Abee tayi yayinda ta kauda kanta gefe ta ce “Kinga Hayfa ƙarasa shiga ciki kawai, nayi mantuwa bari na je yanzu zan dawo.” Ba tare da damuwa ba Hayfa ta amsa da “Ok” a taƙaice sa’annan ta ci gaba da tafiyarta zuwa department ɗin.
Juyawa Abee tayi da hanzarinta tabar wajen, ofishin Sir Salman ta nufa, haka kawai taji tana muradin ta sanƴa shi a idonta kafin ta shiga lakca.
Ganin ofishin a buɗe ya sanƴata kutsa kai ba tare da shakka ba,a sanƴaƴe ta shiga office ɗin, daddaɗan ƙamshin turarensa ya daki hancinta, lumshe idanunta tayi tana mai jin wata kalar ni’imtacciyar soyayyarsa na shigarta.
Ɗagowa yayi don ganin wanda ya shigo ofishin nasa, ganin itace ya sanƴashi saurin ajiye biron dake hannunsa yana murmushi ya miƙe tsaye ya ce “Oyoyo My baby” ya ƙarasa maganar yana mai ƙarasawa kusa daf da inda take, a wannan lokacin ya matso kusa gareta sosai har suna iya jin saukar numfashin juna, Murmushi ya kuma saki ganin yanda Abee take kallonsa cike da shauƙin so. kura masa idanu tayi tana kallonsa kamar mai nazarin wani abu a fuskarsa, tunaninta ya katse sakamakon ji da tayi ya ce ” Can i hug you mu Baby?”
Story continues below

Ya ƙarasa maganar yana mai son rungumarta,da sauri Abee taja da baya zuciyarta har dukan uku uku ya ke cikin zafin rai da ɗaga murya ta ce
“Wai wannan wani irin abune ?ni na gaya maka ka rabu dani ƙawata itace mai son ka ,ka fita daga cikin rayuwata ka daina mun irin abubuwan nan bana so”!
Abee ta sauke maganarta cike da jin haushin abin da yayi ƴunƙurin aikata mata da a ce tabasa damar hakan.bata ma san lokacin da ta yaɓa mai wa’innan kalaman da bakinta ya furta su ba,don tasan bai kai har cikin zuciyarta ba.
Sanin halinta ,da kuma sanin cewa ita macece mai zafin rai ya sa Sir Salman kyaleta bai ce mata uffan ba .Abee tajuya tayi tafiyarta zuciyarta na ƙuna ta koma department nasu.Sam bata son wannan halin da Sir Salman ke gwada mata na son taɓa jikin ta.
**********************************************
A tare suka fito daga lecture ita da Hayfa wacce Kawar su ce ita da Suhailat, basu cika fita ko yin wasu abubuwan tare ba shiyasa ma Hayfa bata san da Soyayyar da Abee da Suhailat ke yiwa Sir Salman ba.
Suna tafe suna ɗan taɓa hira jefi jefi .
A daidai nan Sir Salman ya fito da motarsa yana ganin su ya tsaya ya ce masu su shigo, cike da ɗauki Hayfa ta buɗe ƙofar gaba ta shiga ta zauna cike da jin daɗi yau ta shiga motar malam.
Ba dan ran Abee ya so ba ta buɗe ƙofar baya ta shiga dan har yanzu tana jin haushin sa,zama tayi tana bone fuska.Shi kuwa Sir Salman murmushi kawai yayi ya ja motar suka bar harabar makarantar.
Saita mirror ɗin motar yayi a daidai saitin fuskar Abeedah yana satan Kallon ta ,tana wani cika da batsewa ,shi kuwa yadda take da fuskarta ne ya ke ta basa dariya .ya fahimci cewa ita macece wanda bata son abubuwan waye wa (she is not social)
Gyaran murya yayi a hankali ya ce
“Hayfah”
Da sauri Hayfa ta amsa “na’am malam” zata iya rantsewa da cewa yau ce rana ta farko da taji Sir Salman ya kira ta da sunan ta.
Murmushin gefen baki yayi kafin ya ci gaba da cewa
“Yanzun dan Allah idan nace ina son mace za ta iya ce wa bata sona?”
Zare idanu waje Hayfa tayi ta ce “kai! wace daƙiƙiyar yarinƴar ce ta isa ta ce bata son ka ?”
Yana jin Hayfah ta faɗa haka ya tuntsure da dariya ya ce “don Allah fa Hayfa?”
Hayfa ta ce “ai duk macen da ta ce bata son ka toh shasha ce ,ita jaka ce ,a cikin mata ma ina ganin rakosu duniya kawai tayi ”
Shi dai Sir Salman sai kwasan dariya ya ke Abee kuwa tagama ƙulewa,tasan tabbas da ita yake .tana nan tana tunanin yadda zata iya yakice son sa a cikin zuciyarta shi kuwa yana nan ya na cewa bata son shi?.
Hayfa ta ci gaba da cewa “har akwai ƴar iskar macen da zaka ce kana so taƙi son ka?toh malam mai ka rasa ?kana da kyau,gaka da ilimi,ga kuɗi,ga iya ɗaukar wanka .Ai wlh koni ban da an samun rana malam !wlh ka ce ka na sona tsaf zan iya bijirewa naƙi auren na dawo ma”
Dariya Sir Salman yayi sosai ya girgiza kai ya ce “a’a Hayfah bama za’a kai ga haka ba,kin kuwa san wacece taƙi ni?”
Saurin gyaɗa kai Hayfa tayi ta ce “a’a malam ban sani ba”
Murmushi yayi ya saci kallon Abeedah suka ko haɗa ido ta sakar masa harara shi kuma ya maiyar mata da murmushi ya ce
“Gata can a baya ƙawarki”
Mamaki shimfiɗe a fuskar Hayfah ta waigo ta kalla Abee ta ce “malam Abeedah?”
Jinjina kai Salman yayi ya ce “kin ga wacan ƙawar taki,? ita ce ta ce bata sona .nasan ƙarya take yi,ƙawar ta take so wai na SO ba ita ba and I knw she loves me deep down her”
Nan Sir Salman ya shiga bawa Hayfa duk lbrn abin da ya faru ya ida maganarsa da cewa
“Kin san dalilin da ya sa na labarta maki wannan maganar?
Girgiza kai Hayfah tayi alamun a’a ,Sir Salman ya ci gaba da cewa “naga kamar kin fisu hankali ne,ki ba ƙawarki shawara karta bari wannan daman ya suɓuce mata dan kawai bata son alaƙarta da ƙawarta ya ɓaci”
Daidai nan yayi parking a ƙofar gidan su Abee da sauri ta fito ranta a jagule ko sallama bata tsaya ta masu ba tayi shigewar ta ciki.
**************************************
A gurguje pls
Soyayya mai tattare da fahimta da yarda da juna Abee da Sir Salman suka ƙulla.sosai suke gwadama juna so ,hakan kuwa ya samo asali ne ta dalilin Hayfah ita ta tsaya tsayin daka dan ganin ta gina soyayyar Sir Salman da Abeedah. Suhailat kuwa ta zama ƴar kallo ranta tasa a inuwa dan tasan tabbas Sir Salman ita zai aura suyi su gama a ƙarshe ita ce da riba.
Bata gajiya da tunasarwa Abee zancen wa’inan malaman Abee kuwa tayi mata kunnen uwar shegu taƙi sauraron ta.
Abeeda bata jin cewa zata iya rayuwa a yanzun ba tare da Sir Salman ba shi yasa a kullum a ko wani sujaddar ta sai ta roƙi Allah da ya mallaka mata Sir Salman yasa ta zama matar shi kuma uwar ƴaƴan shi.
Yanzun kam kowa a gidan su Abee yasan da Sir Salman a koda yaushe zuwa yake gidan su kai tsaye yana kuma samun tarba mai kyau.
Yauma yana zaune a cikin motar sa yana jiran fitowar Abee . kwankwasa window ɗin motar yaji a hankali ya zuge glass ɗin . yana ƙare mata kallo ,sosai tayi masa kyau nan ya kafe ƙirjinta da kallo yana jin sha’awarsu har cikin ransa. Buɗe motar tayi ta shiga ƙamshin turaren ta ya bugi hancinsa ta na jin yanda ya sauke a jiyar zuciya ya na faɗin “hummm akwai kaya kam”
Taji sa sarai waske wa tayi kawai dan a yanzun kam tana mugun son sa bata son hassasa faɗa a tsakanin su shi yasa ta zaɓa yin shurun.
***********************************
Rungume take a cikin faffaɗar ƙirjin sa bayan sun gama biyama junansu buƙata .sumba ya kai ma goshin ta kafin ya ce
“Sweetheart faɗimun yau ina kike so muje?kin faranta mun yau sosai dole nima na faranta maki kwatankwacin yadda kika faranta mun ”
Murmushi tayi kafin ta ɗaga hannunta tasa a saman ƙirjin sa ta shiga yi masa tafiyan tsutsa shi kuma yana ta faman lumshe idanu. Cikin siririyar muryata ta ce
“My Salman!ai kafi kowa sanin inda nafi so ka kaini”
Ta ida maganar tana mai cire hannunta a saman ƙirjin sa saurin buɗe idanuwan sa yayi ya kalle ta ya ce
“Ina kenan dear?”
Far da idanu tayi Kafin ta shiga shafa shi da hannunwan ta. ta ce “Masallaci zaka kaini a ɗaura mana aure Salman”!
Da sauri Salman ya miƙe har yana bangaje hannunta ya ce
“Shin sau nawa zan gaya maki tsakanina da ke ba aure ?inada wacce zan aura Abeedah itace matata ”
Da sauri cikin haɗa rai budurwar ta ce “mainene aibun aure na?shin kowai kana manta cewa kaine farkon namijin daya taɓa sanina a ƴa mace Salman?!kai ne fa ka maidani cikakkiyar mace !ka mai dani tamkar matar ka shin mai yasa bazaka aure ni ba?”
Cikin tausasa harshe ya ce “ko nawa kike so zan biya ki Sweetheart but pls ki daina cewa muyi aure”!
Murmushin da yafi kuka ciwo ta sake kafin ta datse haƙoran ta ,ta furzar da huci ta ce “kaji tsoron ranar da asirin ka zai tonu Salman !Abeedah da kanta inta gane wanene kai !waye mijin da take shirin aura? fasa auran naka za tayi dan ba mai auren *fasiƙi mazinaci* “!
Ta ida maganar tana mai miƙewa ranta a ɓace tabar ɗakin,dafe kansa Salman yayi a fili ya furta
“Oh my god Su…….
Dafe kansa yayi lokaci guda kuma yana furzar da huci cikin zafin rai ya ce “oh my God Surayyah! mai yasa kike shirin rushe farin ciki na? Abee ita ce wadda nake so ,ita ce farin ciki na! a kanta na fara sanin mainene So. pls Surayyah karki yi wani yunƙurin raba ni da Abeedah ”
Ya ƙarasa maganarsa yana mai jefi da filon dake kusa da shi.
*************************************
Da Sallama ɗauke a bakinta ta ƙarasa shigowa cikin falon,samun wuri tayi ta zauna daga gefen Mancy kafin ta ce “Abbi barka da rana ”
Murmushi Abbi yayi ya ce “barkan mu dai Abeen Abbinta ya lecture?”
“Alhmd Abbi ” Abee ta amsa masa.
Gyara murya yayi a hankali ya ce “Ma sha Allahu,Allah ya ci gaba da taimakawa yayi jagora”
A tare Mancy da Abee suka amsa da “ameen”
Abbi ya ci gaba da cewa “Abee batun maganar wannan lekcaran ne yasa ni kiranki dan in kuma ji daga bakinki kafin musan abin yi a gaba”
Abbi ya ƙarasa maganarsa yana mai jan numfashi kafin ya ci gaba da cewa “Shin Abeedah kina son sa? ”
Shiru Abee tayi duk kunƴa ya gama rufeta ,sunkuƴar da kai kurum tayi ba tareda ta ce uffan ba.
Hakan yasa Abbi murmusawa dan ko Abee bata buɗe baki ta furta ba yasan tabbas tana son Sir Salman.
Abbi ya ce “Abeena kenan toh ma sha Allah Rabbi yayi mana jagora cikin al’amarin”
A tare Abee da Mancy wacce tun ɗazun ba ta ce uffan ba suka haɗa baki wajen amsawa da “Ameen ya Allah ”
Ya ci gaba da cewa “toh in sha Allah nan da zuwa wani lokaci ƙanƙani zan sanar dake ki sanar masa yaturo manƴansa ”
Gyaɗa kai Abee tayi kafin ta ce “tohm Abbi mun gode Allah ya ƙara lafiya da tsawon kwana”
Murmusawa Abbi yayi ya ce “Ameen Abee Allah yayi maki Albarka ya baki zuriya ɗayaba masu zuwa nan gaba ina sha Allahu ,waya ga Abee da yaro tana goyon”
Abbi ya ƙarasa maganarsa cikin sigar zolaya. Dariya Mancy da Abee su kayi a tare ,inda Abee ta miƙe da saurinta tana rufe fuska don kunƴa tayi saurin shigewa uwar ɗauka.
Abbi da Mancy suka girgiza kai haɗida yin dariya irin tasu ta manƴa.
***********************^*************
Ƙare mata kallo tsaf Abee tayi kafin ta nisa ta ce “ina jinki ,mai yasa kika naima ganinsa?a ina kika sanni ?”
Far da idanunta tayi kafin ta saki murmushi ta kallo Abeen sosai sa’annan ta ce “hmmmm duk wa’innan tambayoyin duk na mutum ɗaya?”
Ta ƙarasa maganar tana ɗaukan lemun kwalba dake ajiye a gaban su ta kurɓa sa’annan ta mayar da shi mazauninsa kafin ta nisa ta ci gaba da cewa “da ban sanki ba da bazan naima ganin ki ba so cool down ki bari na labarta maki dalilina na nai manki,sanin ki da kuma zuwan ki nan ”
Abee kam kallon budurwar kawai take ba tare da ta kuma cewa uffan ba .
“Ni sunana Surayyah Adams ni ƴar garin Maiduguri ce ni bafullatana ce a ƙauyen mare dake Maiduguri,ni kaɗai iyayena suka haifa bayan na girma na isa aure iyayena suka naimi yimun auren dole ni kuma sam ban son wannan mijin da suke son haɗani da shi dan haka dajin tabbas fa aurar dani ɗin zasu yi ya sani yanke shawarar gudawa daga Maiduguri inda na yada zango anan garin Kano”
Story continues below

Ta ƙarasa maganar tana sakin murmushi da Abee ta gaza gane kota maicece.
Ta ci gaba da cewa
“Ban san cewa ƙaddara ta bace ta sani barin garin mahaifana ba ! ”
Saurin katseta Abee tayi ta hanƴar ɗaga mata hannu kafin ta ce “toh ni mai nene nawa da zaki zaunar dani kina bani labarin rayuwar ki babu dangin iya bare baba ?!”
Abee ta ƙarasa maganar cike da masifa dan ita sam wannan bafullatanan bata kwanta mata a rai ba.
Murmushi ƴar Fulani ta saki wanda ya sa Abee ƙulewa hakan ya sata miƙewa cike da ɓacin rai zata bar wajen maganar da taji ƴar Fulani ta wurgo mata ya sata tsayawa cak kafin ta waiwayo tana kallon ƴar fulanin wacce keta faman murmushi kaman gonar auduga .
Abee ta ce “mai kika ce?”
Far da idanu tayi kafin ta ce “cewa nayi kece Abeedah wacce Salman Ibrahim ɗambatta keson aura ko?”
Ta ƙarasa maganar tana kafe Abee da idanu .Kallonta sosai Abeedah tayi kafin ta ce “eh sai a ka yi yaa?”
Ni sawa ƴar Fulani tayi kafin ta ce “zoki zauna don Allah inason warware maki wasu abubuwane !”
Ba dan ran Abee yaso ba ta koma ta zauna suna fuskantar juna ita da ƴar Fulani .
Surayyah (yar fulani”) ta ce “kin san mijin da kike son aure wanene?”
Bata jira amsar da Abee zata bata ba ta ci gaba da cewa “Mijinki manemin mata ne! ,yau shekarar mu biyar muna tare da shi tun zuwata Kano ina da shekaru 15 a lokacin kenan .Ya tsintoni a kan hanƴa ya ce zai tai makeni ya kama gida ya sani a ciki Ni kuma tun a wannan lokacin Allah ya ɗora mun son wannan bawan .ya mai dani matarsa ina matuƙar son sa kamar na mutu but yaƙi ya aure ni saboda yana ganin dan shine ya fara sanina a ƴa mace ,kuma banda ni akwai matar uban gidansa da suke tare ”
Surayyah ta ƙarasa maganar tana share ɗan guntun hawayen fuskarta kafin ta ci gaba da cewa “Salman bayan aikin lekcaran da yake yi yana kasuwanci ,Uban gidansa da suke kasuwancin tare matafiyine bai cika zama a ƙasar nan ba,yana da mata ɗaya Hajiya Adama da yara biyu .Zan iya ce maki ita matar Hajia Adama itace ta fara lalata shi ! Idan mijinta ya tafi shikenan babu ruwan shi da buƙatunta sai dai fannin kayan abinci da kayan sawa da ƙuɗin kashewa duk yana aiko da Salman ya kawo mata!”
Ta ida maganar tana mai sake kurɓan lemun hannunta kafin ta cigaba da cewa “a duk ranar da Salman yazo gidan Hajia Adama shigar banza takeyi ta fito wajen sa turarukan tashin sha’awa babu wanda bata sawa kafin ta fito wajen Salman tazo tayi ta masa rangwaɗa ta ce da shi Salman nayi kyau? Shi kuma ya ce mata sosai kinyi kyau ita kuma sai tace da shi ta gode a haka dai kin san halin shaiɗan tazo ta siye zuciyarsa toh wannan shine mafarin lalata Salman da tayi shike biya mata buƙata kuma har rana irin tayau suna tare .”
Surayyah ta ƙarasa maganar tana kallon Abeeedah wacce itama Surayyan take kallo .
Shiru ne ya ratsa a tsakanin su na wasu daƙiƙu kafin Surayyah ta nisa ta ce “yanzun ya rage naki ki san abin da ya dace kiyi nikam na fita hakkin ki nasanar dake iyakar gaskia dan nasan tabbas har ki gama bin ciken ki a kan sa baza ki san da wannan ɓoyayyen sirrin nasa ba ,dan ko ƴan gidan su basu san yana aikata hakan ba dan shi mutum ne wanda ya iya takun sa sosai nasan da wuya ki gasgata maganata dan nasan ƴan jami’ar ku basu ko isheshi kallo ba amma Sir Salman kwallon ɗan iska ne kina ganin sa haka Abeedah!”
Abeedah cikin fusata ta miƙe ta nuna Surayyah da ɗan yatsanta kafin ta ce “hummm really?Sir Salman kika ce kwallon ɗan iska ne ko?toh Nagode sosai bana buƙatar sanin hakan ni shi nagani naji ina so kuma shi zan aura .Babu abin da ke cinki face kishi da hassada dan haka karki sake tunka rata da irin wannan maganar banzar save it to urself”
Daga haka Abee ta bar wajen ranta a matuƙar ɓace.
Surayyah kuwa tsananin mamakin Abee yaƙi barin ta tasan abin yi .
*************************************
A gurguje pls😖
Kwanaki na ta shuɗewa ranaku na ta tafiya har Allah cikin ikonsa ya nufa a ka sa ranar auren Abee da Sir Salman inda a ka tsaida lokacin bikin nan da wata biyu cur in Allah ya yarda.
Murna a wajen wa’innan Masoya ba’a magana sosai suke gwada ma junan su so fatan su dai Allah ya nuna masu ranar da zasu zama abu ɗaya.
Zaune suke su biyu a ɗakin Suhailat suna hira maman Suhailat ce ta shigo cikin ɗakin hannunta riƙe da wani jug murmushi ɗauke a saman fuskarta ta ƙaraso wajen nasu ta ce “Amarya!”
Murmushi Abee tayi kafin ta ce “Momy barka da rana”
“Barkan mu dai Abee ya lectures fa?”
Momy ta amsa ma Abeen haɗida jefo mata tambaya.Abee ta ce “Alhmd Momy ”
Murmushi Momy tayi kafin ta miƙama Suhailat jug ɗin hannunta ta ce “kinga Suhay miƙe kije kikai ma Hafiz wannan jug ɗin yana jiranki a ɗakin sa”
Suhailat na cuno baki waje ta amsa jug ɗin Momy kuma tayi gaba abin ta tabar ɗakin Abee ta ce “wa wai kike cuno ma baki waje?”
Harara Suhailat ta sakar mata kafin ta ce “wlh nasan dan kawai ya ganni ne ya sa shi cewa momy tabani na kai masa jug ”
Dariya Abee ta kyalƙece da shi kafin ta ce “ke mutum yana gwada maki so but Ke ko oho kin ma tsanesa toh ke wai wa zaki so?”
A kufle Suhailat ta ce “ban sani ba chaa nake wanda na ke son kika kwace har kina da bakin tambaya ta wa zan so?toh bari in tuna maki in mantuwa kika fara Sir Salman shi nake so har gbe shi kaɗai zan so kuma shi zan aura.Bazan gaji da tunasar dake ba Abee Salman ni zai aura duk runtsi karki ga dan wai an sa maku rana ki sha kin rigada kin gama mallake sa ke kaɗai ! No mutuwar ki kike gayyata kawai dan ai da kunnuwanki kinji abin da malamai har biyu suka faɗa akwai rabo mai ƙarfi tsakanina da Sir Salman ina baki shawara Abee har yanzun baki makara ba u still have time to decide wlh ko mutuwa ko rayuwa…….